Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
aljihu kafin yace “A’a, direct daga airport nan nayo” A hankali tace “Bata da lafiya” Bata ida rufe bakinta ba yace “I know!” Ta lura da yadda yanayinsa ya chanja amman hakan ba zai hanata yi masa nuni da gaskiya ba dan haka tace “Arshaad no matter what, ko me tayi maka Mahaifiyarta ce! She’s sick! Very sick! She needs you! Aiima bata nan ita kad’aice. Ajiyar zuciya ya sauk’e yana kallon Ummin ido cikin ido yace “Abba baya nan ne?” “Eh, yayi tafiya shi da Daddy business trip sannan za su bud’e branch d’in construction company d’insu shi da Aslam a UK sun ma bud’e It was successful sannan trip din nasu was also successful shiyasa jibi za mu yi double celebration in sha Allah.” Ummin ta zayyano mishi dan so take su yi magana kar ya samu question d’in da zai sake jifanta da shi as an excuse. “Ma sha Allah Allah ya k’ara d’aukaka” Yace, daga nan ya mik’e. Itan ma mik’ewa tayi tace “We are not done” Sai da ya lumshe idanuwansa ya bud’e kafin ya kalleta yace “Ummi ko In koma inda na fito ne? Although i came for Shuraim and Sudais but it’s like bakya murna da ganina!” Da sauri tace “Arshaad ba haka ba...” Cikin katseta da d’an b’acin rai yace “To na rok’eki da girman Allah ki daina yi min maganar Mammy Ummi kina so inje In zauna Ina ganin suna fad’a kullum ita da Dad ko yaya?” Tausayin sa ne ya fara rufeta dan haka ta k’arasa inda yake ta kamo hannunshi ta rik’e a nata tace “Ba haka bane son, ka fahimceni” Kamar zai yi kuka yace “Me kike so inyi yanzu?” Har ta bud’e baki za tayi magana sai kuma tace “Ba komai, nothing” A hankali ya zame hannunsa a cikin nata ya juya ya shige dakinsa. Ta d’an jima a tsaye kafin ta sauk’e ajiyar zuciya ta juya ta nufi kitchen ta fara setting dining table. A hankali itama Huda ta mik’e ta k’arasa ta shiga tayata. Sai da suka gama tukunna Huda ta wuce d’aki, ita kuma Ummi ta zauna anan kan dining d’in ta rafka tagumi. A gaban dressing mirrow ta sameshi yana taje gashinsa.. Sanye cikin pyjams dark ash da suka yi mishi kyau matuk’a!. A hankali ta k’arasa bakin gado ta zauna ta d’auki wayarta da ta mak’ala a charge ta danna kiran Sakina Bayan ta zare wayar a charging. Tana d’auka tace “Yanzu Ya Auwal ya tafi” “Um” Kawai Sakinar tace, a hankali. Ajiyar zuciya Huda ta sauk’e kafin tace “Yayi matuk’ar bani tausayi, har da kuka fa yayi. Da kin sani baki gaya mishi yanzu ba” Shiruu, ta ji Sakinar tayi kafin chan tace “Ya dameni da kira da massages! At least yanzu zan huta sannan i don’t want him to have any false hope.” Cikin son kawo k’arshen maganar Auwal d’in tace “Za ki zo goben?” Sai da ta kalli Aslam wanda yanzun yake zaune akan sofa yana k’ok’arin kunna computer tukunna tace “Ya hanani” Da d’an k’arfi ta yadda ta san zai ji. “Ki lallab’ashi” Shine kawai abunda Sakinar tace. Har zata kashe wayar sai kuma tace “Jiya su Shuraim ma sun biyo nan daga school, sun kawo mana invitation d’in birthday d’insu Su Mama dai ba zasu zo ba amman ni da Sumayya za mu zo goben In sha Allah.” Cike da murna Huda tace “Allah ya kaimu da rai da lafiya. Ku zo da sassafe dan Allah ayi shirye shiryen komai da ku” Murmushi kawai Sakina tayi tace “Ai inaga 3 hours ma kawai za mu yi, za mu zo 2 mu tafi 5 haka, ba lalle ma mu samu event d’inba kawai dai za mu zo ne dan naga sai wajen 10 ma tukunna za a fara, so kawai za mu d’an lek’o.” Da sauri Huda tace “To ku kwana mana” Dariya Sakina tayi tace “Bara in yi sallah. Sai anjima” Dan so take ta kashe wayar sakamokon kanta da yake mata tsananin ciwo da kuma rud’anin da zuciyarta take ciki! Dauriya ce kawai take yi da har aka samu take iya yin magana. “Okay, ki gaida Ummu da Sumayya” Hudan tace daga nan suka katse kiran. Ita bata ma san Aslam ya fita ba sai da ta d’ago tukun taga ba ya nan “Hmm, mutum sai basirar iya san’da kamar munafuki” Ta fad’a a ranta. Tana mik’ewa tayi haramar kimtsawa domin ta gabatar da tata sallar dan taji an shiga masallaci. Tana idarwa ta fita da sauri ta d’ebo abinci a plate ta d’auko ruwa ta shigo har da d’an gudu dan taji kamar mutum zai fito a kitchen. Da wuri tayi ta cinye ta sha ruwa ta yi brush, ko plate d’in bata d’auke ba ta kwanta ta k’udundune a cikin bargo! Ala dole Ita tayi barci kenan saboda gudun kar ma wani ya shigo yace ‘taje tayi dinner’ Saboda ita har ga Allah kunyar had’uwa da Arshaad take yi after what he saw daga zuwanshi gidan bata jin zata iya sakewar had’a ido dashi balle zama waje d’aya. Kusan kamar 40 minutes wayarta ta fara k’ara! Dan haka ta tashi ta d’auka, tana ganin sunan Abba ta d’auka da wuri cike da zumud’i tace “Abba, Ina wuni, kun taho ko?” Murmushi yayi yace “A’a tukunna, yanzu dai muke shirin isa airport. Gobe around 7:00am in sha Allah za mu k’araso saboda muna da transit” “Okay, Allah ya kawoku lafiya” Murmushi yayi yace “Ameen princess, Ina Aslam?” Sai da ta d’anyi shiruu, tukunna tace “Yana waje, suna dinner” Da sauri yace “ke fa?” A hankali tace “yanzu na gama a d’aki” Zai yi magana ya ji tace “Ya Arshaad ma ya dawo.” Shiruuuu, taji Abban yayi kafin yace “Okay, sai mun k’araso goben in sha Allah” A hankali tace “Safe fligh Abba” Murmushi yayi yace “Thank you princess” Daga nan suka katse wayar, tana shirin ajjiyewa Aslam ya shigo! Hannunsa rik’e da plate a da ruwa. Ta ji shigowar tasa amman bata d’ago ba, har ya tako ya zo inda take ya zauna a gefen gadon kusa da ita. Sai a sannan ta d’ago tana kallonsa da plate dinsa.. a ranta tace “shima a nan zai ci abincin yau ko me?” A hankali taji yace “Kin ci abinci kena?” D’agowa tayi tana kallonshi taga yana kallon plate d’in gefenta wanda ta ajjiye akan side drawer. A hankali ta d’aga masa kai alamar ‘eh’. Shiruuu, suka yi chan taji yace “Ya za muyi da wannan??” D’agowa tayi taga shima itan yake kallo! Da sauri ta sunkuyar da kai dan yau wani kalar kallo taga yana yi mata wanda ya sanya kwata kwata bata son had’a ido da shi. Shirun ne ya sake biyowa baya kafin ta ji ya bud’e plate d’in da ya rufa a kan na abincin ya fara tab’a spoon d’in…. Bata gama tunanin me yake yi ba taji yace “Haa” Tana juyowa taga ya d’ebo fride rice d’in wadda taji hanta ya kawo kusa da fuskarta. Sai da ta sauk’e ajiyar zuciya sannan ta kawar da kai tace “Na k’oshi” Ji tayi kawai ya kamo hannunta ya d’an matse a cikin nasa a hankali ya sake cewa “Haa” Yana sake matso da cokalin. “Ya subahanallah! Wannan wanne irin mutum ne?” Ta yiwa kanta tambayar a cikin ranta. Ji tayi ya murza tafin hannunta da nashi hannun still a hankali taji ya sake cewa “Haa” Da sauri ta juyo ta bud’e bakin ta lumshe idanunta numfashinta na fita da sauri sauri. Murmushi yayi ya saka mata cokalin a baki ita kuma ta karb’a ya juye mata tukunna ya zare. A hankali ta shiga taunawa, har yanzu idanuwanta a lumshe suke. Kamar wanda ya samu tv haka ya nutsa ya maida hankalinsa wajen k’arewa kyakkyawar fuskarta kallo. Sai da ya ga ta had’iye tukunna ya mayar da cokalin ya fara k’ok’arin d’ebo wani, da sauri ta d’aura hannunta a kan nasa ba tare da tayi laakari ba, tace “Nafa ci abinci Mai yawa. Please Ya Aslam kar in yi amai” Sannan ta fara k’ok’arin bud’e kyawawan idanuwanta da suka taru da kwallah. Tana gama bud’ewa taga ya ajjiye spoon d’in ya na k’ok’arin bud’e robar ruwa… Ba yadda ta iya haka ta yarda ya bata a baki ta sha tukunna ya mik’e ya d’auke plate d’in da ta ajjiye a kan side drawer ya had’a da wanda ya shigo da su ya fitar. A yadda ya fita ya barta a haka ya dawo ya sameta, bai kalletaba bai ce mata komai ba ya nemi waje ya zauna ya ci gaba da aikin da yake yi d’azun kafin ya fita sallah. Ya d’an jima yana aikin, kafin yaga ta taso ta k’araso ta zo inda yake. A hankali ta zauna a gefensa tace “Ya Aslam” “Um, Anty Huda” Ya ce ba tare da ya kalleta ba, yana mai ci gaba da typing d’in da yake yi. Ajiyar zuciya ta sauk’e kafin tace “zan je dan Allah, goben.” “No” Yace, still bai kalleta. Turo baki tayi kafin tace “Na dawo fa d’akin” This time around dariya yayi kafin ya rufe computer gaba d’aya sannan ya juyo gareta yace “Ki yi hak’uri, baza ki je ba.” Kamar da wasa kawai sai yaga ta fashe ta kuka! Ajiyar zuciya ya sauk’e kafin ya matso ya kama hannunta yace “Mama ce tace kar a barki ki sake fita sai nan da wata d’aya. Idan kina son fita ki kira Hajiya Shuwa idan ta barki sai ki je.” Da mamamki take kallonsa tana rage sauti da yawan kukan nata. Jinjina mata kai yayi alamar tabbatarwa. A hankali ta shiga share hawayenta tana sauk’e ajiyar zuciya a hankali. “Yanzu zaki kuma yin wani yajin kenan? Tunda dai kinga ba damar fita gobe Ba ni zan barki ba Hajiya da Mama ne” A hankali ta girgiza kanta tace “Ka yi hak’uri, a kan abinda nayi” Murmushi yayi yace “Ai kuwa na hak’ura! Tunda har kwalliya da turaren wuta aka saka duk dan saboda ni. Ko ba dan ni akayi ba??” Murmushi kawai tayi ta sake sunkuyar da kanta k’asa. A hankali yana kallonta kafin yace “Je ki kwanta. Gobe tashin asuba ne, ko?” Ba tare da ta d’ago ba tace “Kaje ka kwanta kai, ni a nan zan kwana. Da bananan ai a gadon kake kwana.” Sai da yad’an k’ura mata ido tukunna yace “A nan d’in nake kwana.. Har gyara miki gadon nake yi kullum thinking you will come back A haka bacci yake d’ibana kullum.” Shiruuu suka yi duk su biyun kafin yaji tace “Ka fini tsayi, ina gani kullum kujerar bata isar ka, ka je ka kwanta don’t be stubborn” Dariya taji yayi kafin yace “In da acting stubborn nake miki yanzu ai da na san tuni kin fita a d’akin nan da gudu” Bata fahimci kan zancen nashi ba dan haka kawai ta basar da zance ta sake cewa “Ya Aslam barci nake ji, ka je ka kwanta.” A hankali yan kallonta yace “Are you sure? In je in kwanta ba damuwa?” Da sauri ta d’ago ta d’aga mishi kai sannan tace “Sai ka fi sakewa achan da kyau” Ajiyar zuciya ya sauk’e kafin yace “Thank you Hudatie” Haka kurum ta tsinci kanta da murmushi dan ba kad’an ba sunan ya yi mata dad’i matuk’a. Murmushi shima yayi kafin ya mik’e ya fara d’ibar throw pillows d’in kan sofar.. Iya yadda hannunshi zai iya d’iba ya kwasa ya nufi gadon. A ranta tace “Ikon Allah! Neman magana yake yi wannan ko mee? Bayan pillows d’in da suke kan gadon wajen guda 4 masu laushi mai kuma zai yi da throw pillows??” Tunaninta ne ya katse ganin yana jera throw pillows d’in yana raba gadon gida biyu da su. Tuni! Kwakwalwarta ta bata me yake shirin yi dan haka tana gani ya gama ya tunkaro ta ta mik’e ta fara magana ba tare da ta kallesa ba “Ai ni nace maka anan zan kwanta Allah kar ma kayi tunanin haka! Idan kuma neman maganata za ka yi to wallahi zance na fasa sai da ka dawo ka cigaba da kwana a sofa kuma ko zanga k’afafuwanka suna lankwashewa kana tafiya da kyar ba zan sake y......” Dip! Maganarta ta d’auke sakamokon d’aukarta da yayi tashi d’aya in a bridal style…… Ba tare da ya kalletaba ya fara tafiya da ita towards the bed. Tsoro da mamaki da kuma yanayin da ta tsinci kanta a ciki ne suka sanya ta kasa magana ko yunk’urin zamewa.. In banda kallon gefen fuskarsa ba abunda take yi har ya isa bakin gadon ya sunkuya ya kwantar da ita rigingine a kan gadon ya d’aura mata kanta a kan pillow ya zame hannuwansa. Ba tare da ya d’ago daga sunkuyon da yayi a kanta ba fuskarsa dan da tata ya d’ago da idanuwanshi ya sanya su cikin nata a hankali yace “Sleep here. Dan Allah” Sannan ya mik’e tsaye ya zagaya d’ayan side d’in ya kwanta. Sai a lokacin ta samu ta sauk’e wata siririyar ajiyar zuciya mai vibration kamar mai jin sanyi. A hankali taji yace “Ki yi addua, good night”............ Ita dai Hudan a yadda ya barta nan rigingine tana kallon sama a haka ta farka ta ganta lullub’e da bargo, daga cikinta zuwa k’asa..ba ta san lokacin da barci ya kwasheta ba. Ko ba a fad’a mata ba ta san Aslam d’in ne ya lullub’eta. Kiran sallar da ta ji ne ya sanya ta fahimci tabbas yau ta d’an makara dan kamar ma har an shiga masallaci, ta ji. Addua ta yi tukunnan ta d’an juya ta kalli side d’in da ya kwanta. Ga mamakinta sai ta gansa kwance a kan gefen damanshi yana facing d’inta.. Bacci yake yi peacefully kamar kuma da murmushi a kan fuskarsa. Kamar yadda ya rufe mata rabin jikinta haka nan shima ya rufu da bargon. Jin an tada ik’ama yasa ta d’an matsa kusa da shi ta fara kiran sunanshi… A hankali yake bud’e idanuwansa, kafin ya k’arasa bud’e su tarr a kan fuskarta! Murmushi ya sakar mata a hankali taji yace “Lucky Morning” Shiru tayi taana kallonshi shima itan yake kallo chan ta d’auke idonta da sauri tace “Zaka makara fa, har an shiga sallah.” Da sauri ya mik’e ya d’an dafe kansa yana mutstsika idonshi kafin ya sauk’a akan gadon ya fad’a toilet. Ko da yaje har an tafi ruku’u dan haka raka‘a d’aya ya samu. Haka nan suka dawo tare da su Shuraim da Arshaad Sudais yana cewa Arshaad “Ya kamata ya yiwa Ya Aslam bulalar makara sallar asuba yau” Murmushi kawai Arshaad d’in yayi ba tare da yace musu komai ba ya wuce d’akinsa. A shirye ya tarar da Huda, suna gaisawa ta fice zuwa kitchen don had’awa Abba abunda ta san yafi so. A kitchen d’in ta tarar da Ummi don haka suka taru suka had’a masa lafiyayeyyen breakfast.. 6:30am, Aslam ya fice tare da Sudais suka tafi d’auko su bayan shi da Hudan sun yi wishing d’insu ‘Happy birthday’ sun basu gifts d’insu shi da Shuraim. Kafin 8:00am suka dawo, Daddy direct side d’insa ya wuce Abba ma suka nufi side d’inshi shi da su Aslam. Da gudu Hudan taje ta yi hugging d’inshi tana murna haka ma Shuraim, daga nan aka shiga gaggaisawa. Ummi, ba kad’an ba tayi matuk’ar jin dad’in yadda Abba ya yi mata faram faram! Dan haka ta samu kwarin guiwa ta hau gabatar masa da abinci kala kala ita da Hudan. Cike da farin ciki yake karb’a yana ci dan Huda da Shuraim da Sudais ke bashi a baki one by one duk da Sudais yana ta yi musu kwange….. A haka suka ciyar da Mahaifin nasu cike da tsananin so da k’aunar juna. Sai da ya k’oshi aka tattare wajen ya fara shirin mik’ewa tukunna Arshaad ya fito. Cike da kulawa Abba yayi welcoming d’insa daga nan ya wuce sama bayan ya bawa Ummi briefcase d’insa yace ta kai masa dakinsa Shuraim kuma ya ja masa trolley d’inshi. Bai tarar da Shuraim a d’akin ba, sai Ummi ita kad’ai ya tarar ta juya baya tana k’ara turaren wutan da ta saka tana d’an fifitawa… D’akin ya sha gyara ba kad’an ba gwanin sha’awa. A hankali ya k’arasa inda take tsaye yayi hugging d’inta ta baya. A mugun zabure ta juyo dan sam! Ko da wasa bata yi expecting haka daga Abban ba. D’an guntun murmushi ta gani kwance a kan fuskarsa, a hankali yace “Ko ba a shirya yi min wannan tarbar ba?” Ummi bata san lokacin da ta fashe da wani kuka ba, ta fad’a jikinsa cikin kukan tace “Abba ka yafe min dan Allah kayi hak’uri ka yafe min” Hugging d’inta yayi a hankali dede setin kunnenta yace “Shiii, komai ya wuce. Ki manta da komai! Just think about me”. ....…….. Ana cewa mutum yana kasa dai na murmushi bata tab’a yarda ba sai yau da ta faru a kanta. Shi kanshi Abban ya lura da tsananin farin cikin da take ciki! Yaso ya gaya mata cewa Maryam ce ta rok’esa akan ‘ya yafe mata ya zauna cikin kulawa da ita’ dan shi bai iya kwana kwana ko b’oye b’oye ba amman yadda ya ganta cikin tsananin farin ciki ne ya sa ya fasa gaya mata ya kuma yi alk’awarin rufe maganar tsakaninshi daga shi sai Maryam d’in. Tabbas shima yana cikin farin ciki ba kad’an ba dan yanzu Maryam ta kan kulashi, jiya har Friday massage ta mayar masa bayan tayi mishi replying nashi message d’in da ‘Ameen, jazakallahu khairan’…… A hankali ya lumshe idanuwansa yana adduar ‘Ubangiji ya sake mallaka masa ita a karo na biyu’. Har Ummi ta gama drying gashinta ta fita dan ana buk’atar ta urgent a k’asa bai saniba Sai da ya tashi shiga toilet tukunna ya lura bata nan.... Shirye shiryen birthday ake yi na y’an gata! Gaba d’aya compund na mansion d’in ake decorating, an kwashe motocin duk an fitar wasu kuma an kaisu baya. Hudan bata tashi sanin abun na gaske bane sai da taga ana rubuta ‘Happy birthday Sudais&Shuraim’ da grass carpet tun daga farkon mansion d’in har wajen k’ofofin shiga mansion d’in sannan ta sama ma fitilun da ake decorating da su sunan su ne aka rubuta ‘Happy birthday Shuraim and Sudais’ Gurin zaman su ma ya sha decoration ba a magana ga cake d’insu anata jerawa guda biyu iri d’aya each one ya kai kusan hawa biyar. Compound d’in kuma inda guests za su zauna kujeru ne guda biyu da table a tsakiya shima ya sha decoration Irin haka wajen guda 70 a daban daban. Abinci kuwa sai shigowa ake yi da su kula kula drinks da ruwa ma ba a magana cupcakes desert soaked cakes abun dai sai wanda ya gani. Tun 3:00pm Aka fara kawo Yara, friends d’insu maza da mata y’ay’an masu kud’i masu fad’a a ji, daga yanayin motocin da drebobin da suke kawo Yaran za ka gane abun na manya ne. K’awar Ummi d’aya ce tak! Ta zo. Dan mutum d’aya kawai ta yi inviting saboda yawancin k’awayenta ta lura a yanzu halayyarsu ba d’aya ba so ta san tasu ba zata ci gaba da zuwa d’aya ba. Mammy kam kaff sister’s d’inta sai da suka zo tare da y’ay’ansu, Mom itama tayi gayyata sosai amman kuma tunda suka zo ko Ummin ba su lek’awaba sun mak’ale a side d’in Mom wadda suka ja gefe Ita da Mammy sunata k’usk’us! Daga ganin fuskar Mammy ka san ba alkhairi dan ko kallon mutum ma da kyar take iya yi In banda cika da batsewa ba abunda take yi........... Har aka kira isha su Sakina basu zo ba gashi sai kiran su take yi basa d’auka! Haka nan ta mik’e tanata k’unci ta gabatar da sallar isha ta mik’e ta fad’a toilet. Fitowarta a toilet kenan sanye cikin bathrobe gashin kanta wanda ta wanke kuma ta nad’e da towel.. Kusan tare suka bud’e k’ofa suka shigo cikin d’akin ita da Aslam wanda ya shigo rik’e da wani k’aton box! Had’a ido suka yi dan haka ta sunkuyar da kanta k’asa tana gyara zaman bathrobe d’in jikinta. A hankali ya tako yazo inda take nan tsaye tak’i gaba tak’i baya, yace “Mu je ki shirya” Da sauri ta d’ago tana kallonshi kafin tayi k’asa da kanta tace “To ka fita mana” Dariya yayi ya juya ya ajjiye kwalin a kan dressing mirrow ya kwashi kayanshi da zai saka yace “Ki jirani i have a gift for you, kar ki fita please” Ajiyar zuciya ta sauk’e a hankali tana kallonshi ya zo ya wuce ya shige toilet d’in. A hankali ta sunkuya ta bud’e wardrobe ta jawo akwatinta ta d’auki mai ta shafa ta mayar ta day inner wears d’inta ta saka ta maida bathrobe d’in sannan ta d’au turaren jiki da misk ta shafa. Powder eye liner da mascara ta fitar ta ajjiye a gefe sannan ta fidda wata doguwar riga b’aka da mayafinta. Sai a lokacin ta lura bata da takalmin da zata saka sai dai tayi using wanda take yawo da shi a cikin gida saboda duk takalmanta na lefe da wanda take da su gaba d’aya suna gidan Ya Arshaad. Shiruu, ta yi ta shiga tunani….. A hankali taji ya bud’e k’ofa ya fito dan haka ta d’aga kai tana kallonsa… Ba yau ta fara ganinshi da suite ba amman ta yau special ce dukda bai d’aura suite d’inba amman kyawunshi ba k’aramin fitowa ya sake yi ba! Wandon dogo ne Baki kamar pencil wanda ya yiwa dogayen k’afafuwansa tsananin kyau! Rigar kuwa longsleeve ce itama baka yayi tucking cikin wandon. “Na yi kyau har haka ne?” Taji muryarsa ba tare da ya kalletaba. Da sauri ta sauk’e idanunta k’asa, ta shiga kiciniyar mik’ewa sai dai kuma har ya k’araso yazo ya tsaya a wajen bata mik’e d’inba! Murmushi kawai yayi ya bud’e wardrobe wajen kayansa ya d’auki agogo da belt sannan ya zaro suite d’in da zai d’aura akai da necktie ya wuce gaban mudubi. Sai a lokacin ta samu damar d’aukar y’ar mitsitsiyar hair dryer d’in da take buk’ata ta mik’e ta nufi bakin gado da kayan da ta ware… Tsaff ya shirya ya shafa mai kad’an ya fesa turarurruka ya gyara gashinsa, sannan ya d’auki kwalin ya nufi inda take zaune har yanzu ko kwance kan bata yi ba ballantana ta busar Ita ala dole jira take sai ya fita tukunna. Yana zuwa ya d’aura mata akan cinyarta ya nemi waje ya zauna a gefenta. D’agowa tayi ta kallesa, da gira yayi mata alamun ta bud’e! A hankali ta shiga warware bow d’in da yake nan a saman kwalin wanda an yi amfani da igiyar ne wajen d’aure kwalin, tana kwancewa ta d’an d’aga ta zareshi gaba d’aya a jikin kwalin ta ajjiye kafin ta kama gefe da gefen ta d’aga shima ta ajjiye murfin a gefe. Bata san lokacin da tace “woow!” Ba. Wata had’add’iyar riga ce a ciki, duk da a nunke take ta fahimci princess gown ce dan gata a jikin wata a gefe an manna da alamun anaso masu siya su san yanda take ba tare da sun bud’e ledar sun warwaretaba. Gefe guda kuma y’an kunne ne masu kyau da bracelet da anklet, sai takalmi shima an yi mishi gurin ajiyar sa daban mai matuk’ar kyau kalar y’an kunnen da kayan RED!. Chan k’asa kuma wani d’an k’aramin lipstic ne an yi rapping d’inshi da leda garai garai da alamun gift ne shi aka bayar. Banda murmushi tana kallo tana sake kallon katon kwalin, ba abunda take yi. A hankali ta ji yace “Do you like it?” Murmushi tayi mai d’an had’e da dariya kafin ta juyo ta d’aga masa kai tace “Yes, na gode sosai” Kallon idanunta yake yana hango farin cikin da take ciki a hankali ya jinjina kai ya d’an motsa bakinsa yace “Welcome” Sannan ya mik’e ya karb’a dryer d’in hannunta ya bud’e ya mak’ala comb d’in ya jona a socket. Har zai kunna sai kuma ya koma gaban dressing mirrow ya d’auko hair cream ya dawo. Takalmansa sau ciki ya cire ya bar iya safar ya hau kan gadon ya tsugunna ata bayanta sannan yace “ta mik’o mishi dryer” Juyowa tayi da d’an mamaki a fuskarta kafin tace “Me zaka yi?” Tana d’an zaro ido. “Bani sai ki gani, ko?” Ya fad’i hakan yana k’ok’arin b’alle murfin hair cream d’in da ke hannunsa. “Ko kina buk’atar cuddling ne sannan ki mik’o?” Ya fad’i haka yana zare towel d’in da ta nad’e gashin da shi. Tun kafin ya ida rufe bakinsa tayi sauri ta mik’a masa dryer. Karb’a yayi yana dariya k’asa k’asa sannan ya d’an d’ebo man ya mulke mata jik’ak’k’en gashin nata da shi ya fara busarwa yana tajewa. Hudan, ba k’aramin mamaki ta sha ba game da yadda akai ya iya gyaran gashi dan har wani massage yake mata da taji tana shirin fara barci. Gyaran gashin yake yi amman cikin nutsuwa da aji. Kasa hak’ura tayi tace “A ina ka koyi gyaran gashi?” Sai da yayi murmushi tukunna yace “Internet. I always dreamt of making my wife’s hair..gashi is one of the things da nayi ta adduar Allah ya sa matata ta kasance tana da shi, I love it! Sai gashi Allah ya amsa adduar tawa.” Ya fad’i haka yana me kashe dryer dan har ya gama. Dariya Huda ta fara ganin yadda ya dawo gaban gadon

Chapter 10 of 26