ma Huda da Abba gaisuwa.
Ranar sadakar uku,
Huda tana d’akin Gramma dan a nan take ita da su Shuraim
ta ji wayarta tana k’ara!
Tana d’auka Auwal yace
“Ta yi bak’o yana waje a bakin estate, wai ya zo mata gaisuwa, yace ‘sunan shi
Junaidu’ Ta sanshi
a barshi ya shigo?”.
Bata san lokacin da ta diro daga kan gadon ba
tace
“Eh Ya Auwal na sanshi sosai yayana ne!
A barshi ya shigo.”
Daga nan ta zari hijabinta
ta yi waje tana adduar Allah yasa Ya Junaidun ne da gaske.
Bata samesu a compound d’in Granpa ba daman bata yi expecting hakan ba!
Dan haka ta fice daga gidan
ta nufi tsakiyar main compound na estate d’in.
A inda ake parking motoci ta hango Auwal sanye cikin bak’ar jallabiya fuskarsa tayi fayau! Idanuwansa da suka ci kuka sun yi jaa sun k’ank’ance
yayi tsananin rama sannan kana ganinshi ka san bashi da lafiya….
A tsaye tare da wani ya juya baya sanye cikin shadda fara d’inkin boda da bak’ar hula
ya jingina a jikin booth d’in wata bak’ar mota Jeep!
Yanayin takalmi da shadda da kuma hular kansa kad’ai sun isa su sa ka san cewa kud’i sun zauna…
Da Auwal suka fara had’a ido
yana shirin yin magana
a hankali yaji tace
“Ya Junaidu”
Shiruu yayi da maganar da yake yi kafin ya gyara tsayuwarshi daga nan kuma ya juyo gaba d’ayanshi yana murmushi…..
Kusan daskarewa Huda tayi,
a hankali hawaye na gangarowa akan kumatunta ta ce
“Ya junaidu”
Murmushi yayi yace
“Na’am Huda”
Cikin share hawayenta tace
“Where have you been? Yaushe ka dawo?
Me ya faru?
How have you been..”
Murmushi ya saki mai d’an had’a da dariya kafin ya shafa k’asumbar da ya tara tayi mishi tsananin kyau yace
“Ya muka ji da hak’uri?”
A hankali ta sunkuyar da kanta tace “Alhamdulillah”
Cikin sanyin murya.
Ajiyar zuciya ya sauk’e kafin yace
“Allah ya ji k’anta yasa chan tafi nan”
A hankali ita da Auwal suka ce “Ameen”
Kafin Auwal d’in ya juya ya yi mishi sallama ya wuce.
Gyara tsayuwarshi yayi yana kallonta kafin yace
“How are you?.”
Congratulations
you have finally found your Dad”
Jijjiga kai tayi sanann tace “Thank you”
Tana mai d’ago da kanta sannan ta sake jeho mishi tambayar
“Where have you been?”
Dede nan Arshaad wanda dawowar sa kenan daga airport d’auko Aaima suka k’araso wajen shi da Aaima.
Murmushi Junaidu yayi kafin yace “Arshaad!”
Da sauri Huda ta juya dan ita bama taga tahowarsu ba.
A hankali ta k’arasa inda Aaima take ta rik’e mata hannu tana kallonta kafin ta yi hugging d’inta.
Bata iya ce mata komaiba
Har ta cika ta ta d’ago.
Ahankali Aaima da muryarta ta d’an dishe tsabar kuka tace
“Ya hak’urin mu?”
“Alhamdulillah” Huda tace
Daga nan Aaima ta d’an d’ago ta kalli Junaidu wanda
ya kafe Arshaad da ido
tace
“Ina wuni”
Ajiyar zuciya ya sauk’e kafin ya juyo ya kalleta a hankali yace “Alhamdulillah.
Ya hak’uri?”
“Alhamdulillah” tace, daga nan tace “Ya arshaad bara in wuce ciki, thank you.”
Tana gama fad’in haka
ta juya ta wuce ciki.
A hankali Huda ta d’an juya ta maida hankalinta akan Arshaad kafin tace
“Ina wuni”
Ba tare da ya kalletaba ya ce “lafiya”
Junaidu Hudan ta kalla
wanda tun wucewar Aaima ya maida idanuwanshi a kan Arshaad tace
“Ya Junaidu baka bani amsa ba”
Ajiyar zuciya ya sauk’e kafin yace
“Actually..
Ni kaina ba zan iya ce miki ga a inda nake ba.
Forget all that bana so ma In dinga tunowa…”
Sai kuma yayi murmushi yace
“Congratulations
Na ji kin yi aure!”
Ya fad’i hakan yana kallon Arshaad kafin ya ce
“And kamar ba Arshaad kika aura ba ko?
Mai yasa?”
Da sauri Huda ta d’ago ta kalleshi, ganin ba ita yake kallo ba gaba d’aya hankalinshi yana akan Arshaad d’inne yasa tace
“Ya Junaidu”
Juyowa yayi ya kalleta,
a hankali ta jujjuya mishi kai
alamun ya bar maganar.
Murmushi kawai yayi yana maida idanunsa akan Arshaad still kafin yace
“No i was just curious ne
He has done so much
and a lot
for and because of you!
I wonder why bai samu aurenki at the end of the day ba…”
A hankali Arshaad ya d’ago jajayen idanuwanshi wanda har sai da suka so firgita Huda ya watsa su akan Junaidu
kafin yace
“Did you come here to mock me?”
Da sauri Huda ganin Junaidun yana sake shiri yin magana tace
“Ya junaidu ka daina mana.
Gaisuwa ka zo ko?
To kayi iya gaisuwar please.”
Shiruu yayi
ya d’an sunkuyawar da kanshi yana kallon k’asa
kafin ya d’ago yace
“Forgive my manners”
Yana kallon Arshaad
sannan ya juya ya kalli Huda yace “Allah ya ji k’an Ummi.
Bara in wuce, su
Umma ma basu ganni ba
dan ban je ko gida ba
I came here straight.”
Hudan gaba d’aya lamarin Junaidu ya d’aure mata kai!
Bai je gida ba?
Tou a Ina ya san Ummi ta rasu?
Sannan waya gaya mishi ta yi aure?….
“Sai anjima”
Ya ce yana d’an murmushi yana kallonta.
A hankali tace
“Na gode ka gaida su Umma”
daga nan ta juya ta wuce.
Wani abun mamamkin..
har ta kai gate
Arshaad da Junaidu suna tsaye suna magana
kuma da ga yanayin yadda suke demonstrating har da hannayensu zai sa ka fahimci serious magana suke yi.
Har ta hau sama d’akin Gramma ta lek’o ta window sai da ta gansu kafin chaan Junaidu ya bud’e motarsa ya shige ransa a mugun b’ace ya ja yayi gaba ya bar Arshaad nan tsaye a wajen….
Tana shirin juyawa sakamokon
k’amshin da k’ofofin hancinta suka jiyo mata, ta ji anyi huggin d’inta ta baya.
Runtse idanunta tayi da k’arfi!
A hankali dede setin kunnenta ta ji ya ce
“Haramun kike kalla fa”
Muryarshi na d’an rawa.
Da sauri ta d’an ture shi
kafin ta juyo tana kallonsa
sai kuma tayi saurin yin k’asa da kanta dan gaba d’aya
sa taji ba dad’i
especially ma yadda taga kamar ranshi bai so ba!
Sannan ba lalle ya fahimci kallon me take yi wa Arshaad d’in ba.
Tana shirin yin magana ya katseta ta hanyar cewa
“Who is the other guy?”
A hankali ta d’an sunkuyar da kanta kafin tace
“Ya Junaidu. Tare muka taso.”
Ajiyar zuciya ya sauk’e
kafin ya matso kusa da ita sosai kamar zai shige jikinta
yayi cupping fuskarta
a hankali ya d’ago da fuskarta yadda za su kalli juna sosai yana kallon cikin idonta yace
“Kar ki sake abunda kika yi yanzu, please.”
Yadda yayi mata magana
da yadda taga idanuwanshi sun yi da yanayin voice d’inshi
ya sanya ta kasa cewa komai
ta lumshe idonta kawai
tana jin yadda
jikinshi yake karkarwa a hankali…
Ya dad’e yana kallon fuskarta kafin ya cikata a hankali ya juya ya fita.
Tana jin fitarshi ta bud’e idanuwanta tana sauk’e ajiyar zuciya a jejjere….
Bayan rasuwar Ummi
Idan akwai abunda yafi damunta ya fi rikitata
tou Ya Aslam ne!
Kwata kwata ta kasa gane gabanshi ta kasa gane bayanshi ta rasa me yake nufi da ita, sannan ita kanta yanzu ba zata ce ga tak’ameme abunda take ji a kansa ba!
Adduar ta d’aya ‘Allah yasa ba ta yi masa ko da d’an mitsitsin so ne’ Dan in dai haka ta kasance to tabbas ta zama butulu!
She is trying very hard ta ga ta yi nesa da shi amman idan yaso ganinta duk inda take sai ya shigo ya ganta ya fita.
A ranar sadakar bakwai
suka tashi jikin Auwal ba dad’i sosai.
Daman tun lokacin da aka yi rasuwar dauriya ce kawai yake yi amman sam ba lafiya gareshi ba…
Tun yana yi a b’oye dan baya so a fahimta har Mom ta gano
dan haka suka dangatashi da asibiti…
Ba k’aramin tashi hankalin ahalin gidan yayi ba
da ga jin Auwal ya kamu da ciwon zuciya!
Da farko Daddy Huda ya fara kira yayi mata maganar Sakina
dan tashi d’aya ana tambayarshi mene damuwarshi ya ce “Sakina”
Tun kafin aje ko’ina jikin Daddy ya sake yin sanyi
jin ‘an bada ita bikinta bai ma kai wata biyar ya rage ba’.
Jiki a mace haka Daddy ya sallameta ya shiga nemawa tilo d’an nasa wata mafitar..
Kafin 5 days hankalin kowa ya sake tashi
saboda idan ka ga Auwal dole sai ka tausayi masa..
A take mazan suka yanke shawarar tura shi wani waje treatment sannan ya d’an huta.
A cikin kwana biyu aka gama shirye shiryen komai…
A ranar da za su tafi har an sakashi a ambulance dan zuwa yanzu ko zaman kirki baya iyayi! Auwal d’in ya nemi alfarmar ganawa da Granpa da Arshaad.....
Granpa ne ya fara shigowa tukunna Arshaad..
Duk wani abu da Auwal ya san ya tab’a yi mara kyau sai da ya zaiyyanewa Granpa
sannan ya fad’i yadda yayi framing Arshaad har Granpa yaso yin shariah da shi!
Duk wasu kud’ad’e da ya tab’a d’iba sai da ya maida mishi, a take ya yayi signing ma company account.
Daga nan ya ruk’o hannuwansu yana hawaye ya nemi yafiyar Granpa da Arshaad.
A hankali Arshaad ya matsa yayi hugging d’inshi, yace
“ba komai komai ya wuce
ka kwantar da hankalinka”.
Cikin sauk’e ajiyar zuciya Granpa shima yace
“Komai ya wuce Auwal, kar ka
damu na yafe maka.
Allah ya baka lafiya
Allah yayi maka albarka.
Ka kula da health d’inka please
ka kwantar da hankalinka
Allah ya baka lafiya”.
A hankali yace
“Na gode Granpa
but please inaso in bawa Arshaad shares d’ina, to
makeup for all the things da nayi ta masa”
Murmushi Granpa kawai yayi ya shafa fuskarshi
kafin yace
“Allah ya baka lafiya”
Daga nan ya mik’e ya fita daga cikin ambulance d’in.
Bayan fitar Granpa da kyar Arshaad ya lallab’a Auwal ya hak’ura amman still yace “idan Allah yasa yayi rai ya warke
to ya na dawowa ya shirya karb’ar shares d’inshi
Idan kuma ya mutu bai dawoba tou ya bashi halak malak!”
Auwal was very emotional gashi sai hawaye yake yi
hakan yasa Arshaad kasa ci gaba da zama da shi
dan haka ya mik’e ya fice
bayan Auwal d’in ya ce masa “ya turo mishi Aaima please”
Da “to” kawai ya amsa shi ya fita.
Har airport Aaima ta rakasu shi da Mom.
Mom driver ya jata shi da Aiima kuma a ambulance.
Itama Aaiiman hak’uri da neman yafiyarta yake ta faman yi……
A hankali tana hawaye tace “ta yafe mishi”
Ya ji dad’i sosai dan haka ya d’an gyara kwanciyarshi ya fuskanceta sosai sannan yace
“I saw your message tun kafin rasuwar Ummi.
Aaima inaso ki fahimci wani abu guda d’aya..
Right now you are confused!
Ta yiu burgeki nake yi
ko kuma tausayina like ji
amman one thing is for sure
ba sona kike yi ba!
Nasan tun kina k’arama da tunanin hakan kika taso amman tabbas ba kya so na
Za kuma ki ce na gaya miki..zaki fahimci hakan a ranar da kika had’u da matching pair d’inki…
Ki nutsu, you deserve better
dan
ko da ace na aureki wahala kawai zaki sha
saboda zuciyata already ta Sakina ce ba zaki tab’a samu ba!
Rasa zuciyar Miji a rayuwar aure kuwa is the worst thing da mata zata fuskanta a zaman aure.
I don’t want that for you,
Ina miki kwad’ayin ki auri wanda kike so yake sonki.
Tabbas na san zan yi aure wata rana idan na samu na tashi daga wannan ciwon wanda In ba da kyar ba shine ajalina..
A ko da yashe In na tuno zan yi aure wallah in banda tausayin matar ba abunda nake ji
saboda na san gangar jikina kawai zata aura!
Bana so ki kasance wannan matar besides ba zama ki iya jira na ba
dan tunda na rasa Sakina
I don’t think zan yi tunanin yin aure in the next 10 years ma.”
………………..
Sun tattauna sosai
Ya ji dad’in yadda Aaima ta fahimci shi.
Har akazo za sakashi a jirgi tana yi masa alk’awarin she’ll speak with Sakina
for him.
Murmushi kawai yayi
dan shi kam zuwa yanzu ya hak’ura dan ya san su Daddy ba za su tab’a nema masa aure cikin aure ba!
Sannan after abunda ya faru a birthday d’in su Shuraim tsakanin Sakina da su Mom
Ya san ba zata tab’a yarda da shi ba!.
A yanda yake jin zuciyarsa kuwa ya riga ya sadak’ar…idan bai mutu ba tou tabbas tashinsa ba kwana kusa ba.
Gaba d’ayan su sun kasa kunne sun zuba ido suna jira suji daga bakin Granpa!
Dan ya cewa Gramma ta gaya musu su zauna a nan ayi zaman makoki for sometime amman har aka shafe kwana ashirin shiru, bai sallamesu ba kuma bai ce su zauna ba.
Sai dai In za su yi wanka suka je su yi achan mansion d’in, su kwaso kaya set biyu ko set d’aya su dawo wanda a haka haka har sun kusan had’a wardrobe amman Granpa bai ce komai ba.
Daman ita
Hudan bata ma tab’a zuwa ba
dan tun washegarin rasuwar Aslam ya kawo mata akwatin ta, kamar ya sani.
A kwana na ashirin da biyar ne
Mommy ta nemi Huda ta dawo wajensu side d’in Aslam inda aka kaita tun farko.
Gramma ba k’aramin dad’i ta ji ba amman k’iri k’iri
Hudan ta rufe ido a gaban Aslam d’in da Mommyn tace
“Ita a wajen Gramma zata zauna”
Mommy tana shirin fara lallashinta ta fashe musu da kuka!
A hankali jiki ba kwari Aslam d’in ya tashi ya fita
haka itama mommy..
Bayan fitar su Gramma lallashi da tambayar duniyar nan amman Huda ta kafe
tace “dan Allah ta bar ta
ta zauna a wajenta”
Haka nan ta hak’ura ta kyaleta
bayan Mommy ta kira Gramma d’in tace mata
“Kawai ta bar Hudan a wajenta
tunda bata so. Aslam d’in ma tafiya zai yi akwai wani abu da ya taso a company d’insa na sarrafa takalma da yake a chan UK so yana so zai je”.
Sam Gramma bata ji dad’in abunda Huda tayi ba
amman
rashin lafiya da rashin kuzarin da yake damunta kwana biyun nan yasa kawai tayi mata shiru ta rabu da ita.. Tun ranar da Ummi ta rasu take rashin lafiya a tsai tsaye ba tare da ta bari an fahimta ba, ba abunda yafi d’aga mata hankali irin yadda family d’inta ya koma
‘Poison!!’
A cikin ahalinta aka samu wani yayi poisoning
wani!….
Wannan tunanin shi ya haifar mata da high Bp ba tare da ita kanta ta san ya hau d’inba.
A ranar da zai tafi tana d’akin Gramma, ta Idar da sallah kenan ta jiyoshi a parlour suna gaisawa da Gramma!
Da gudu ta mik’e ta fad’a band’aki ta rufo k’ofar,
dai dai yana shigowa ita kuma tana rufewa, dan
haka ya k’arasa k’ofar band’akin ya tsaya.
Ya dad’e a tsaye
kafin ya lumshe ido ya fara magana
Na san saboda ni kika b’uya, kuma na san kina jina…
I just come to say good bye!
Tun da yanzu naga kamar na zame miki dodo.
Naso ache tare muka tafi
but iya yadda kika nuna ranar da Mommy tace ki dawo wajena ya isa ya fahimtar dani idan ma nace ki bini kunya kawai zaki sake bani.
Idan wani abun na yi miki wanda ban san da shi ba
ki yi hak’uri ki yafe min..
If by any chance kinji ra’ayinki ya d’an sauyu akan fushi da wasar b’uyan da kika d’auka da ni to ki yi min magana in sha Allah zan sa a shirya miki komai sai ki zo ki sameni achan d’in.
Ga numberki na karb’a a wajen Gramma, zan yi miki message da tawa ta chan once i settled.
Kar ki damu ba zan dameki da messages ko calls ba!
Na fahimci you need some space so think and decide wisely.
Hudan i can’t stay under one roof with you kina guduna kina b’oye min ba
ba zan iya ba..Ni kad’ai na san what I’m going through.
Ina fata kafin in dawo
kin yi figuring out whats going on with you.”
A hankali yace “I’m going to miss you”
Yana gama fad’in haka ya juya kamar mara lakka a jiki ya fice.
Ta dad’e a cikin toilet d’in kafin da kyar ta bud’e k’ofar ta fito....
Kamar yadda ya fad’a
yana isa ya turo mata
“Arrived safe, Aslam.”
Da numbersa ta chan.
Tun daga ranar bai sake nemanta ba, itama
kuma bata nemeshiba.
Bayan kwana goma sha uku,
yau Ummi ta cika kwana arba’in da rasuwa.
Ahalin gidan kowa ya ji rasuwar Ummi sosai
sun girgiza matuk’a!
Hakan kuma ya zamo izina ga wasu, wasu kuwa da zuciyoyinmu suka ruga suka daskare ba abunda ya chanja a lamari da tsaurin su.
Sai a ranar sadakar arba’in d’in tukunna Aslam ya dawo
da safe, dan haka bai samu damar shiga cikin gidan ba ya tsaya a wajen da ake addua.
Bayan an ida an kammala sauk’a aka raba sadaka aka fara watsewa…
Sai a sannan Granpa ya yafito shi da hannu.
Cikin nutsuwarshi da class ya mik’e ya k’arasa inda yake ya durk’usa ya gaidashi ya sake yi mishi gaisuwa.
A hankali yasa hannu ya shafa kanshi, kafin ya amsa.
A hankali Aslam d’in yace
“Allah ya jaddada rahama a gareta”
“Ameen” Granpa yace
yana mai sauk’e ajiyar zuciya sannan ya zare hannunshi daga kanshi yace
“Taso muje akwai inda nake so ka rakani.”
Driver d’inshi yana ganin sun nufi wajen parking motoci ya mik’e da d’an sassarfa ya k’arasa inda suke.
Hannu kawai Granpa ya mik’a masa!
Ya gane me yake nufi dan haka ya zaro key d’in Gwagon d’in da suke tsaye a gabanta ya bashi.
Ya na karb’a ya mik’awa Aslam ya ce “mu je!”
Daga nan suka k’arasa duk su biyun suka shiga Aslam ya kunna ya ja suka fice daga estate d’in…..
“Gidan Madu Mahaifin Maryam za mu je!”
Granpa ya fad’a yana mai gyara zamanshi ba tare da ya kalli Aslam d’in ba.
Wata nannauyar ajiyar zuciya Aslam ya sauk’e wanda har sai da Granpa ya jiyo shi
kafin ya lumshe idanuwanshi ya bud’e ya gyara zama suka d’auki hanyar gandun albasa.
A dede k’ofar gidan ya yi parking ya kashe motar ya juyo yana kallon Granpa wanda yake kallon gidan yana sake kalla, a hankali Aslam d’in yace
“Mun iso Granpa”
Lumshe idanuwanshi Granpa ya yi, kafin ya bud’e ya sauk’e ajiyar zuciya
yace “mu je”
Yana mai sa hannu ya bud’e k’ofar motar.
A hankali Aslam wanda tsananin farinciki da fargaba suka lullub’e a lokaci guda yasa hannu ya bud’e k’ofar side d’inshi ya fito
zuciyarshi cike da fargabar abunda ya kawo Granpa nan
sannan kuma yana addua da tsananin farin ciki In Allah yasa alkhairin da yake tunani ne ya kawo su..
Kame kame Aslam ya fara yi da dibi dibi dan shi dai ya san bai kamata su shiga kai tsaye ba! Rashin sanin kan al’ada da lamarin garin Hausawa kuma yasa ya rasa abun yi.
Suna tsaye Junaidu ya bud’e k’ofa ya fito..
Kallon kallo aka tsaya kafin Junaidun ya k’arasa ya mik’awa Aslam hannu.
Bayan sun yi musabaha yace mishi “Dan Allah suna son ganin Abba Madu idan yana nan.”
Da mamaki Junaidun ya kalleshi kafin yace
“Wa za a ce mishi?”
Sai da yad’an kalli Granpa wanda still har yanzu gidan yake ta kalla tukunna ya d’an sunkuyar da kanshi kafin ya d’ago yace
“Kace mishi Mijin Maryam ne, Huda.”
Murmushi Junaidun yayi ya sake bashi hannu suka gaisa sannan yace
“Ashe k’anin namu ne”
Ya fad’a cikin raha da barkwanci
sannan cikin ladabi ya juya ya gaida Granpa! Ba yabo ba fallasa ya amsa shi
daga nan Junaidun
ya juya da d’an sassarfa yace
“Minti biyu dan Allah”
ya shiga cikin gidan.
Bai rufe second talatin ba suka ga ya bud’e wata k’ofa ta waje ta cikin gidan sannan ya fito ta k’ofar yace musu
“Ku shigo, bismillah”
Sai da suka zauna ya d’auko ruwa da lemo a cikin babban fridge d’in da yake a parlourn bak’in ya jere musu
tukunna ya juya ya fita ya ce “bara yaje ya kira musu Abba Madun, yana gidan Kaka.”
Ba ayi minti biyar ba Madu da Kaka suka shigo
da sallama.
Cike da kamala suka k’arasa cikin parlourn suka nemi waje suka zauna a kan 3 seater d’in su biyun wadda take facing 1 1 seaters d’in da Aslam yake zaune a k’asan d’aya Granpa kuma ke a kan d’aya.
A hankali cikin girmamawa Aslam yad’an sunkuyar da kanshi ya shiga gaidasu….
Da kulawa suka amsa shi
kafin su maida hankalinsu a Granpa suka soma gaidashi cikin girmamawa
zuciyoyinsu fal mamaki da tunanin abunda ya kawo shi garesu.
Ba yabo ba fallasa ya amsa su
kafin yayi gyaran murya ya gyara zama sannan ya kalli Madu yace
“Ina son ganin ku ne amman first Ina buk’atar Maryama a nan”
Ajiyar zuciya Madu ya sauk’e kafin yace
“Ok ba damuwa” daga nan ya mik’e ya fita.
A parlourn k’asa ya sameta ita da Shuwa suna tattaunawa a kan al’amarin Junaidu!
Bai bi ta kansu ba yace mata “ta taso ta d’auki hijabinta ta zo”
Ganin yanayin shi ta san koma menene it’s serious dan haka ta mik’e ta nufi sama,
bata wani dad’e ba ta sauk’o daga nan suka fice a tare.
Suna fita ya kalleta ya ce
“Kun yi magana da Abba ne?
Akan aure ko wani abun?
Kuna magana da shi sosai yanzu?”
Da mamaki ta d’an kalleshi kafin ta sunkuyar da kanta tace “A’a!
Na dai kirashi washegarin ranar da Ummi ta rasu nayi mishi gaisuwa”
A hankali ya sauk’e ajiyar zuciya kafin yace
“Tou Allah yasa lafiya”
Dede nan suka k’arasa bakin parlourn dan haka bata samu damar tambayar shi komai ba
suka kutsa kai suka shiga yana gaba tana biye da shi…
Da Granpa suka fara had’a idanu tana shiga
dan an ci sa a k’ofar yake kallo.
A take gabanta ya yanke ya fad’i! sannan ta fara tariyo had’uwarsu da irin kalar warning d’in da yayi mata!
Sai yanzu ta gane dalilin tambayoyin Abba Madun
da kuma dalilin damuwar da ta hango shimfid’e akan fuskarsa.
“Shigo mana Mama”
Muryar Kaka ta katse mata tunani…
A hankali ta taka ta k’arasa cikin parlourn k’irjinta na dukan uku uku!!!
A k’asa kan kafet ta zauna gefen kafar Madu,
muryarta na d’an rawa tace
“Ina wuni Daddie”
Wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauk’e, kafin ya ja wani yawu ya had’iye
sanann ya d’ago ya zuba mata idanuwanshi yace
“Alhamdulillah, Maryama”
A hankali ta sake cewa
“Ya hak’uri”
Bata jira jin amsarshi ba
dan bataso maganar tasu tayi tsayi kar ya ga zak’ewarta kuma bataso ya kasance batayi mishi gaisuwa ba dan ta san yanda yake da Ummi d’in,
dan haka tace
“Allah ya gafarta mata yasa Aljannah ce makoma”
“Ameen” ya ce.
A hankali Aslam ya gaidata cikin girmamawa, da
kulawa ta amsa
kafin Granpa yace
“Marigayiya ta bani sak’o wajenki”
Da sauri Mama ta d’ago kai tana kallon shi..
Shima itan yake kallo kafin yace “A ranar da zata rasu tace ‘In sake nema mata yafiyarki’.”
Da sauri Mama tace
“Na riga na yafe mata
tun ba yau ba mun gama wannan maganar da ita.
Mun yafe mata daga ni har Huda fatan mu Allah ya ji k’anta da rahama”
A hankali Granpa yace
“Ameen”
Sannan yad’an sake muskutawa ya gyara zamanshi
kafin yace
“A ganina ya dace ace nima na zo na nema yafiyarki tun kafin azo a nema min”
Ba Mama ba hatta su Kaka da Aslam
Granpa suka kalla fuskokinsu d’auke da tsananin mamaki!
Bai damu da yadda suke kallonshi ba yace
“Shekaru 29 ko ace 30 baya!
Na san na baku wahala ke da Abba…
Ban san halinda za ku shiga ba
na biyewa b’acin rai da zuciya na turaku chan wata k’asa sannna bayan shekaru goma duk irin shak’uwar da kuka yi ban duba ta ba na sa Abba ya sake ki!
Ki yi hak’uri….”
A hankali ya kalli su Madu yace
“Kuma ku yi hak’yri ku yafe min abubuwan da na aikata muku”
Da kyar Madu wanda ya shiga shock yace
“Ba komai ya wuce Allah ya yafe mana gaba d’aya.”
“Na gode” Granpa yace,
sannan ya maida idanuwansa kan Mama wadda ta kasa cewa komai.
Ganin ta yi shiru yasa ya sake cewa
“Ki yi hak’uri Maryama ki yafe min dan Allah....”
Da sauri Mama
wadda sai yanzu ta dawo haiyyacinta tace
“Daddie dan Allah ka daina bani hak’uri..
Gaba d’aya am not comfortable with you apologizing.
Ka yi hak’uri dan Allah ka daina bani hak’uri.
Na hak’ura na yafe na manta komai, mu yafewa juna
muma mun yi laifi ni da Abba dan kamata yayi ace dole muma mun tsaya mun bi zab’in iyayenmu…
Ku yi hak’uri ku yafe mana”
Ta yi maganar tana kallonshi sanann ta juya ta kalli su Madu.
Ajiyar zuciya Granpa ya sauk’e kafin yace
Na gode Maryam
amman in dai da gaske kin yafe min ke da iyayenki
To
a yanzu Ina so mu d’aura aurenki da Abba!”
This time around k’amewa Mama tayi k’am!
Hatta numfashinta sai da ya kusan d’aukewa….
Ganin ya sake yunk’urowa zai yi magana yasa kawai ta fashe da kuka sai kuma ta tashi da sauri ta fita a parlourn
tana kuka sosai.
Da sauri modu ya mik’e zai bita
Granpa ya hanashi ta hanyar cewa
“Barta, kyaleta.
Dawo ka zauna mu k’arasa magana.”
Ahankali ya koma ya zauna
jikinsa duk ba laka.
Ajiyar
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 13 Chapter of 26