daka mata tsawa ya sanya ta nutsu ta sha jinin jikinta.
A fusace ya fara magana
“Ban damu da in san me kika ce mata tukunna ta yarda ba,
tunda dai har ta yardan
to ta yi proving kanta ba as selfish kamar ke da d’anki ba!
Abu d’aya nake so in yi miki gargad’i akai
ko kuma ince In umarceki ki yi…
Ina so ki tsame hannuwanki a lamarin nan…ko da wasa idan kika sake yunk’urin had’a Maryam da Usman su koma su yi zaman aure
wallahi!! Kin ji dai na rantse
sai na datse igiyoyin aurena kaff! Da su ke a kanki!”
A zabure ta ware idanuwanta tana kallonshi.
“Tabbas!”
Kaka yace cikin gasgasta maganar tasa sannan ya ci
gaba
“Tunda na lura son kan naki ya yi yawa..
Tun farko kike gwada son kai har yau kin k’i ki saduda Talatu
Usman d’a ne haka itama Maryam y’a ce!
Amman wani abun takaici
tunda kike Talatu
not once kika tab’a duba farin cikin Maryam
kullum kawai ke Usman!
Baki damu da kowa ba sai d’anki.
Kamata yayi ace yanzu kin nuna masa tsananin b’acin ranki
kallafa
k’aryar mutuwa yayi amman kina k’ok’arin yin burus da al’amarin saboda..........”
Shiru yayi sakamokon ido biyu da suka yi da Baba.
A hankali cikin mutuwar jiki ya k’araso cikin d’akin ya durk’usa a gaban Kaka da Baaba Talatu
ya fara hawaye a hankali ya ce “ku yi hak’uri, na san na yi
laifi amman ku yafe min
dan Allah kar ka bari su Abba su ji wannan maganar,
tunda har ita Maryam d’in ta yarda zata koma kawai ku kyaleta, daga baya duk abunda.........”
Marin da Kaka ya d’auke sa da shi ne ya sa ya yi shiru!
Cikin tsananin b’acin rai ya ce
“Usman inaso ka tattara kayan ka ka koma inda ka fito!
Kuma kar ka kuskura ka dawo
har a gama d’aurin auren Maryam a kaita gidan Abba!
Dan na lura imaninka ya fara rawa so zaka iya yin komai.
Ka tattara ku koma kai da Jamilu har a k’are tukunna ka dawo.
And one more thing..
Ko ka san cewa y’arka ciki ta yi?
Kuma Sadiya ta tura ta gidan su shi Yaron ta zauna
ta yiwa kowa k’aryar tana gidan Hansai??
Baka sani ba ko?
Badaban cikin ya zube ba
na tabbatar da sai ta haifi shege a cikin zuriata!.
Saboda kawai Yaron ya kasance mai kud’i
shiyasa tsananin buri irin na Sadiya ta gwammaci jikata ta je ta haifa shege
dan kawai ta dinga turo mata da kud’i!
Kana nan sake da baki kana k’ulla ta yadda zaka dawo da Maryam
instead of
ka tsaya ka kula da iyalinka Usman!!
Kaf y’ay’anka da matarka
babu wanda za a kalla a nuna a yi alfahari da shi! Dan shi
kansa Junaidu abun a bincika ne!
Amman daga kai har Jamilu da ya kamata ace kun tashi kun tsaya akanshi kun yi bincike,
kun zauna kuna k’ulla makirci da k’arya kamar mata! Kun zuba mana ido ni da Madu tsofai tsofai da mu mu za mu yi komai..
To Ina so ka sani nima yanzu ta kaina nake yi, abunda kawai zan yi focusing akai bayan d’aurin auren Maryam shine ibada!
In samu in gyara tsakanina da Ubangijina kafin In koma gareshi..
Duk wanda yaga zai gyara iyalinshi
to ya gyara
wanda kuma ya ga ba zai gyara ba shi ya sani kar ya gyara ya zauna ya ci gaba da shirme yana biyewa so da buri.
Abu d’aya zan yi maka na taimako da ga shi ba k’ari!
Kasancewar Jalila y’a mace kuma yanzu na san tunda zance ya fara fitowa in an kwana biyu ba lalle ta auruba, dan haka zan rufa mata asiri
In nema mata miji kamar yadda na yi da farko.
A yanzu Mati ya riga ya cike ta hud’u if not wallahi da tun a jiya da Zainab ta bani labarin ta
da tuni na aura masa ita.
Dan haka
yanzu zan bada sanarwa this time around ba a fili ba a b’oye
saboda kar Sadiya tace na yi talla da y’arta kamar farko..
Duk wanda ya zo ya ce yana so
daga nan zuwa ranar asabar rana ita yau
to za a had’a a d’aura aurenta
tare da na Maryam da Abba, in sha Allah.”
Yana gama fad’in haka ya juya ya fita dan yana so ya sanar da Madu an saka rana.
A ranshi ya gama rayawa
‘Ko Madun bai yarda ba wallahi sai dai kawai ya ga ana d’aura aure ranar Asabar!
Ai Maryam bazawara ce yanzu
sannan ba Yarinya bace ba, kowa ya san Abba take so
ba Usman ba dan haka
Madu
bashi da hurumin yi mata dole’.
BULAMA ✍️
So da Buri
Free Book
68
Mikiya Writers Association.
Tabbas Mommy taso ace ta gyara Huda kafin ta tare
amman jin bayanin gramma yasa kawai ta hak’ura
ta k’udurta a ranta zata had’ata da Gwaggo Asabe na kwana biyu. Allah yaso ta taho da wayarta dan haka ta d’auka ta danna kiran Ummu.
Da sallama Ummu ta amsa kafin ta ce “Ina wuni Mommy ya gida”
“Alhamdulillah Ummu ya Yaran”
Mommy ta amsa ta.
Sai da taji amsarta tukunna tace
“To fa aikin gaggawa ya samemu.....”
…………
Lokacin da ta shigo d’akin Huda na toilet tana wanka
Gramma bata gaya mata komai ba daman ta fi so sai Mommy ta zo su yi mata bayani tare.
D’aure da d’an guntun towel ta fito gashinta a jik’e gaba d’aya wani ya zubo ta gaba wani kuma yayi baya
Yana reto yana d’igar ruwa.
Sam bata ma lura da su waye a d’akin ba saboda duniyar tunanin da ta lula
‘Tabbas ko ta halin yaya ne yau dole ta je ta samu Mama!
They definitely need to talk..
She can’t believe abunda Maman ta gaya mata jiya
sannan Sakina ta tabbatar mata wai gidan Baba za ta koma!
Mai ya faru?
Ko dai gaba d’ayansu sun samu shigar aljanu ne!
Dan in ba haka ba
tayaya za ai ga Abbanta amma azo ace wai gidan wani Baba za ta koma!
Granpa fa dakanshi ya je ya samesu….
Wanne irin abune wannan?
Tun jiya ta kasa gane kanta har kawo yanzun nan…..’
“Dota”
Mommy ta kirata tana d’an kallonta ganin gaba d’aya hankalinta baya a kansu.
Firgigit! Ta yi ta d’ago, suna
had’a ido kuma sai ta tuna da towel kad’ai ne fa a jikinta shima kuma guntu
dan haka da sauri ta juya ta koma toilet d’in
tana cewa
“Mommy Ina kwana”
Bata jira jin me za ta ce baa ta rufoo k’ofar ta shiga neman bathrub.
Tana shigewa Mommy ta sauk’e ajiyar zuciya
kafin a fili tace
“Ko sai yaushe Hudan zata saba da ni kamar Maryam?
Sai Allah.”
Tana gama fad’in haka ta kalla Gramma tace
“Bara in je In fara shiri kafin su Ummun su zo.
Dan na san ba lalle ta iya sake fitowa ba balle ta sake mu yi maganar.
“Ok”
Kawai Gramma ta ce mata
daga haka Mommy ta juya ta fita.
Tana fita
dede Hudan tana fitowa itama sanye da bathrub.
Ba k’aramin dad’i ta ji ba ganin bata d’akin, dan har ga Allah tayi mugun jin kunya.
Tana shirin nufar gaban madubi Gramma tace
“Zo nan Huda”
A hankali ta k’arasa ta zauna a gefen ta tace
“Gani Gramma”
Sai da ta sauk’e ajiyar zuciya tukunna tace
“Shawara nake so in baki…
Ki daina nunawa Mommy kamar suruka take a wajenki
Instead ki d’auketa kamar Mama ki sake da ita. Tana matuk’ar k’aunarki, ki saki jinkinki ku saba sosai,
za ki ji dad’in hakan.
Magana ta biyu…
Ki shafa mai ki jirani zan kawo miki kayan da zaki saka yanzu!
Granpa ya ce akaiki gidan ki
za a gyara kina ciki.”
Da sauri ta d’ago ta kalli Gramma.
D’aga mata kai tayi alamar gasgatawa sannan tace
“In kuma kinada ja to
mu je in raka ki wajensa”
Ta fad’i haka tana d’an b’ata rai
saboda ta lura In ba hakan tayi mata ba to fa sai an sha drama da ita
dan gashi idanunta har sun ciko da hawaye.
A hankali ta girgiza kanta alamun ‘a’a’
Sai kuma ta mik’e ta nufi gaban mudubi hawaye na bin fuskarta.
Tana gama shafa man Gramma ta shigo da wasu had’add’un kaya
riga da zani da alkyabbarsu
sai kyalli suke yi
sannan
kamar wanda aka yi design d’in edges d’in da gwal!
Tana ajjiyewa ta juya ta fita.
Bata dad’e ba ta dawo da kasko da wata robar Kaplas,
sannan ta sake komawa ta d’auko kujerar tsugunno.
Ita dai Hudan tana zaune kawai tanata binta da kallo
dan tunda ta gama shafa man ta dawo kan gadon ta zauna ta yi shiruu tanata tunani.
Gramma na gama shigowa da kayayyakinta ta sa kwaskon garwashin a k’asan kujerar
sanann ta bud’e kaplas d’in…
Wasu y’an k’ananan robobine masu murfi a ciki!
Sai da ta bud’e kusan duka ta d’eba wannan ta d’eba wannan tukunna ta tara akan murfin roba d’aya, ta kalla Hudan tace mata “tashi”
Sai da ta tashi tukunna ta k’arasa ta d’auko k’atoton bargon kan gadonta sannan ta dawo ta wareshi ta ajjiye a gefe
kafin ta d’auki had’in da tayi na kan murfin robar ta zuba a cikin kaskon wutar ta saman kujerar
tukunna
ta umarceta da ta zauna da wuri.
Sai da ta rufa mata k’aton bargon tukunna ta ce ‘ta kwance bathrobe d’in jikinta ta bata’
A hankali ta warware ta mik’a mata sai kuma ta fara k’ok’arin tashi dan wani zafi ne ta fara ji yana ratsa ta saboda hayak’in ya fara turnuk’e koina a cikin bargon.
Sai da Gramma ta yi da gaske tukunna aka samu Huda ta zauna, har da hawayenta kuwa fuskarnan ta yi jajawur.
Tana nan zaune suka ji ana knocking!
Sai da Gramma ta kora mata warning d’in karta motsa tukunna taje ta bud’e k’ofar.
Murmushi tayi sanann tace
“Ashe ma kishiyar tawa raguwa ce nake ta jin tsoro?
Shigo ki ga kuka wiwi a iya tsugunno kawai.”
Tana jin murmushin Ummu ta fahimci itace, ai kuwa ta fara zillo tana lek’awa nan suka had’a ido. Tana shirin tashi Ummu tace “dalla zauna”
Cikin sigar tsokana.
Wani sabon farin cikin ta sake ji ya lullub’e ta sakamokon ganin Sakina sun shigo ita da mommy suna yi mata dariya suma.
Cikin mutunta juna aka shiga gaggaisawa daga nan Gramma ta fita tace musu
“Ku k’arasa shiryata
dan ni kam ragwanta da shagwab’a take ta yi min”.
Ummu ma da nata ta zo,
dan haka bayan ta tashi a na Gramma sai da ta kuma wani zaman
sannan kafin awa biyu suka sakata ta shanye tsumi wajen roba uku!
Ita kam gaba d’aya ma fitsari take ta ji sai faman zaryar toilet take yi, da tayi magana kuma Ummu ta rufeta da fad’a!
Dan ma Mommy tana d’an kareta. Sakina kam tana gefe
kawai a zaune ta yi shiruu
sai da murmushi kawai
kamar ba Sakina ba.
Aaima na zaune a parlour ita kad’ai tana karatun Alqur’ani
Aslam ya shigo.
Dama itan yake nema kuma yaci sa a ya sameta ita kad’ai
dan haka ya k’arasa ya zauna a kusa a ita.
Sai da ta kai aya tukunna ta d’ago tana kallonshi tana murmushi.
Murmushi ya mayar mata kafin yace
“Can we talk?”
A hankali ta jinjina kai alamun ‘yes’.
Sai da ya sauk’e ajiyar zuciya tukunna ya ce
“Huda zata tare yau”
Shiruu ta d’anyi ta sunkuyar da kanta.
A hankali yana nazartarta yace
“You are my only sister Aaima..
Relationship d’in dangin Miji da Matar wa yana lalacewa ne idan akai rashin sa’ar samun rashin jituwa tsakanin Sister’s d’inshi da Matar tasa!
Ko da ace uwar Miji bata son surukar indai Sister’s d’in suna k’aunarta to su kan iya bata shawara a zauna lafiya
kuma itama uwar Mijin in dai taga surukar tana jan y’ay’anta a jiki tou za a zauna lafiya.
Ke ce mace a tsakanin mu duk kan mu har Auwal da da su Shuraim, although Huda is also our sister
amman kasancewarta wife d’ina ya sa dole ta
amsa sunan suruka a tsakaninmu
Ni Ke Arshaad Mammy da Mommy…
Mommy is morethan good with Huda being my wife
amman ban san ke ko Mammy ba!
Ke, za ki iya gyara tsakaninta da Mammy
sannan za ki iya b’atawa
but first Aaiima please
Inaso ki goge haushinta da kike ji na zuwan Mammy cell tunda ba ita ta kaita da kanta ba, ina so ku koma kamar daa,
Arshaad yace min kuna shiri sosai da farko
ku zauna lafiya please
hankalina zai fi kwanciya
daga nan kuma sai ki yi aikin gyara tsakaninta da Mammy dan na san za ki iya.”
Tunda ya fara magana Aaima ta yi shiru tana sauroronshi,
sai da ya dire aya
tukunna ta d’ago ta kalleshi tace
“Ya Aslam,
komai ya wuce.
A b’angarena komai ya wuce,
na yi maka alk’awari za mu koma kamar da ni da Hudan in sha Allah after all she’s my only sister sannan sister in-law..
Gaskiya Ya Auwal ya fad’a a ranar da zai wuce shi da Mom, kafin ya tafi, ya ce min
‘I really need to relax
In daina biyewa duk abunda zuciyata ta yi karo da shi a karon farko na b’acin rai ko akasin haka!
In bud’e idanuna da kyau!
There is more to life
than holding onto the past’
Agaskiya nima sai yanzu na fahimci ba laifin ta bane”
Sai da ta d’anyi murmushi sannan tace
“I owe her an apology,
In sha Allah zan bata hak’uri
wannan duk ba wata matsala bace
In sha Allah.
Ka kwantar da hankalinka
Hudan and I
will be good.”
Ta fad’i hakan tana murmushi.
Kamar kuma wadda ta tuna wani abun sai tayi shiruuu ta shiga tunanin,
chaan! Ta sauk’e
wata k’akk’arfar ajiyar zuciya kafin tace
“Matsalar a nan shine
Ya Arshaad!
Ba zan b’oye maka ba
Ina jin tsoron wani abu…
Not that wai Ina tunanin Ya Arshaad bai hak’ura ba or something like that
amman so makaho ne
kuma inaso ka san cewa
har gobe
Ya Arshaad yana son Huda
so mai tsanani!!
Ban san abun yi ba
ban san abun cewa ba
saboda gaskiya ni kaina I’m confused and broken akan lamarin nan
Ina tausaya masa…
Jiya kusan a parlourn nan na kwana ba wanda ya sani saboda Ina so in kammalawa Ummi sauk’ar da nake yi mata
a yau
shiyasa jiya around 12 na sauk’o na fara karatu dan ina
buk’atar chanjin waje…
Da farko magana sama sama na fara ji, sanin da na yi cewa shi kad’ai ne yasa na k’arasa dan inji ko lafiya, sai da na je bakin glass door d’in naji ashe waya yake yi…
A hankali na d’an tura na ganshi a tsaye a parlourn yana waya yana safa da marwa gaba d’ayan shi a rikice!.
Yana gama wayar ya kama hanyar d’akinsa ya shige
ni kuma na zuge na bishi a hankali na tsaya a bakin k’ofar d’akin!
Wallahi Ya Aslam
kukan da na ji yana yi sai da na tsorata!”
Da sauri Aslam cikin katseta ya ce
“Ki je side d’in Gramma
Ku shirya ki raka Huda
Ta shi ki je yanzu na san
sun kusan kammalawa”
Za ta yi magana ya ce
“Aaima please, je ki!
Ki mata rakiya
Mommy ne kawai achan ata wajena”.
A hankali ganin yadda idanuwanshi suka kad’a suka yi jaaa, ta mik’e ta ajjiye Alqur’anin akan side table ta nufi sama domin chanjawa.
Tana shiga ta cire hijabi da y’ar kantin doguwar rigar da suke jikinta ta saka atamfa ta fesa turare ta d’au mayafinta ta fita.
Har ta zo ta wuce bai ma sani ba! Ya rufe fuskarshi da tafukan hannunshi
banda “innalillahi wa inna ilaihirrajiun” ba abunda yake maimaitawa cikin tsananin tashin hankali.
Ya dad’e kafin ya samu kwakwalwar shi ta gama lissafi, a hankali ya mik’e ya nufi side d’in Arshaad, sai dai
yana zuwa ya bincika koina amman babu shi ba alamunshi
kamar ma babu abubuwan amfaninshi…
Haka ya fito kanshi a hargitse
ya nufi gidanshi
dan yana so ya sallami cleaners d’in da suka gyara suka goge su tafi
kuma yana so ya duba
waenda suke sauk’a tare da shi ko sun gama nasu
suma a samu su wuce
kafin su Gramma su k’araso.
Yana shiga ya tarar da su Dad da Daddy tare da masu gadaje
anata faman jere…
Cikin girmamawa ya shiga gaidasu yana mamakin su dan
kusan komai an kawo.
Daman kuma shima ya siya wasu kayan a nan Kano d’in saboda ba lokaci d’azu!
Dan haka nashin ma suna isowa aka hau kafi.....
Hudan na gama shiryawa Gramma tace “su tafi a kaita”
Dede nan Aaima ta shigo.
Cikin fara a suka gaisa da Sakina bayan ta gama gaisawa da su Ummu
daga nan suka fito gaba d’ayansu….
A k’ofar gidan suka samu Junaidu a cikin mota a zaune, gefe guda kuma motar drivern da Mommy tace ya zo ya jira su, dan haka suka shishiga.
Har cikin gidan Junaidu da drivern suka kaisu
tukunna suka fito.
Ummu ce rik’e da ita suna zuwa bakin k’ofar shiga tace “ta shiga da k’afar dama da bismillah”
Anan suka tarar da su Dad da masu d’aura kaya..
Royal chairs har set biyu ta samu a parlourn k’asa
da dining da tv stand da centers show glass duk komai na royal d’in.
Dad ne ya ce ‘su kaita main bedroom na chan sama an gama shiryawa’
da “to” suka amsa daga nan suka nufi saman…
Duk d’akuna biyun an gama kafa gadajen dan haka suka nufi nata d’akin.
D’akin da gani Aslam ne ya sa furnitures d’in saboda favorite color d’inshi ne.
Tsayawa fad’an had’uwar d’akin ma b’ata baki ne.
A bakin gadon suka ajjiyeta
suka yi mata Nasiha mai ratsa jiki daga nan Gramma da Mommy suka wuce
Ummu ma ta mik’e ta tafi tace “Junaidu anjima zai dawo ya d’auki Sakina.
Saboda kar taji shirun yayi yawa kafin a gama jeran Aslam ya shigo.”
Da kyar kuwa Huda ta barta ta tafi itama Ummun har da y’ar kwallarta.
Daga nan d’akin ya rage saura su uku
Ita Aaima da Sakina.
Suna gama fita Aaima ta mik’e ta k’arasa inda Huda take ta yaye mata hular alkyabbar jikinta tana murmushi tace
“Amaryar Ya Aslam”
K’asa Hudan ta yi da kanta tana goge hawayenta.
A hankali Aaima ta sa hannu ta shiga goge mata hawayen
sanann tace
“Amaren yanzu fa basa kuka,
haba mana kar ki bada girlss”
Dariya suka saka gaba d’ayan su har ita Hudan tana d’an share hawaye tana dariya.
A gefenta ta zauna suka sakata a tsakiya kafin tace
“Kwanakin baya mun d’an samu misunderstanding…
Uwa daban ce Huda, therefore
i hope za ki fahimceni
Sannan ku yi hak’uri daga ke har Sakina”
Sannan ta d’an lek’a Sakinar ta ce “I know i was rude that day
da kika kirani a
waya, i shouldn’t have talk to yo.....”
Cikin katseta Sakina ta ce
“Haba Aaima,
dan Allah ki manta da komai ya wuce, mun fahimci situation d’inki.
You will lways be our big sis sanann kuma friend at the same time”.
D’agowa Hudan ta yi itama ta d’an kalleta sannan ta ce
“Ba komai Aaima ya wuce.”
Ta yi maganar tana kamo hannunta.
A hankali Aaima ta ce “thank you”.
Murmushi suka yi dukkan su
kafin Aaima ta ce
“Sakina daman ina son ganinki.
Na ma shirya zuwa inje In sameki sai kuma gaki yau Allah ya had’a mu.”
Da mamaki Sakina take kallonta kafin ta gyara zamanta ta bata dukkannin attention d’inta”
Sai da Aaima ta sauk’e ajiyar zuciya kafin ta ce
“A kan Ya Auwal ne”
Da sauri Sakina ta lumshe idanuwanta ta yi k’asa da kanta…
Tun ranar da Huda ta ce mata ciwon zuciya gareshi shikenan ta rasa nutsuwarta
Ta tabbata itama yanzu haka maybe ta kamu da nata ciwon zuciyar..
Aaima ba ta tsaya jira ba ta ci gaba da magana
“Tun ranar da za su tafi
mun yi magana da shi a kan ki!
Sanann jiya ma sai da muka yi chattinga da Mom!
Shi kam yama daina chat zuwa yanzu
tun shekaran jiya
da oxygen yake iya numfashi!
Bar ganin muna raha a cikin gidan nan wallahi kowa kawai k’ok’artawa yake yi
amman dukkanmu hankalinmu a tashe yake.
Sakina na san Ya Auwal farin sani!
Ba zan b’oye miki ba har dating d’inshi nayi…
Tunda nake a rayuwata ban tab’a ganin Ya Auwal yana soyayya bilhakk‘I da gaskiya ba sai a kan ki!
Kinga na farko
Saboda ke ya shiryu, duk wani bad habit da yake yi yanzu ya daina.
Sannan ranar da zai tafi duk wani abun da ya tab’a yi a company da sharrin da ya yiwa mutane duk sai da ya fad’awa Granpa!
Ya nemi yafiya.
Na uku,
ki duba kiga mawuyacin halin da yake ciki! Duk fa a kanki ne fa Sakina. Wallahi na manta rabon da inga mutum yana tsananin rashin lafiya akan soyayya sai a lamarin ku!
Dan Allah ki duba halinda yake ciki ki san abun yi
tun kafin mu rasa shi. Jiya Mom cemin ta yi
ciwon ya motsa
jininsa ya hau
ga ulcer!
Sakina ki taimaka….
Ni ko number Ashraff d’inne ki ba ni, ni na san me zan gaya mishi..
Please Sakina.”
Ta k’arashe maganar cikin karyewar zuciya.
Da gudu Sakina ta tashi ta shige toilet ta rufo k’ofar…
Tana shiga ta fashe da wani irin gigiceccen kuka.
Ahankali Huda ta sauk’e ajiyar zuciya kafin ta ce
“Me za ki cewa Ashraff d’in in kin samu numbershi?”
Kawai zan rok’esa ne akan ya je ya ga halinda Ya Auwal yake ciki.
Zan iya biya mishi kud’in jirgi ma kawai ya je yaga halinda ya ke ciki!
Daga nan ya san abun yi.
Wallahi Huda zan iya dafa alqurani akan
Ashraff baya yiwa Sakina kwatankwacin son da Ya Auwal yake yi mata.”
Ajiyar zuciya Huda ta sauk’e kafin tace
“Kuma itama Ya Auwal d’in take so”
Da sauri Aaima ta juyo tana kallonta sosai.
Jinjina kai Huda tayi kafin tace
“Ni dama na dad’e da fahimtar hakan.
Tou kuma jiya Ashraff d’in ya sake tabbatar min…
Ya min complain akan
Ko kiranta idan yayi bata iya d’auka wani lokacin
sannan In zata kira sunanshi sometimes sai ta ce masa Ya Auwal!
Wani lokacin in ta fahimta ta yi saurin gyarawa.
Kwata kwata bata bashi time..
Shine ya kirani akan wai In na samu time yana son mu yi magana
face to face sannan kuma wai
waye Ya Auwal?!”.
Cikin rashin jin dad’i Aaima ta ce
“To ai za su cuci kansu ne daga ita har Ashraff d’in!
Kawai kamata yayi ta fito ta gaya mishi gaskiya shi kuma ya hak’ura.”
A hankali Huda ta sauk’e ajiyar zuciya kafin ta ce
“Bara in baki number tasa ku yi magana”
“Okay ba ni”
Aaiman tace tana mik’a mata wayarta.
A hankali Huda ta zaro wayarta wadda ke nan rik’e a hannunta daga cikin alkyabbar jikinta ta bud’e ta juye mata nambobin Ashraff a wayar ta mik’a mata.
Message ta tura mishi….
‘yau an kai Huda gidanta
so ba zata samu damar sauraronshi ba
amman ta fad’a mata komai game da issue d’in da yake facing ta b’angaren Sakina!
If he’s free ya zo su tattauna’.
A hankali Huda ta mik’e ta k’arasa k’ofar toilet d’in ta fara yi mata knocking..
Ta d’an jima kafin Sakinar ta bud’e k’ofar ta fito
a hankali tana tsane ruwan fuskarta da hannunta
alamun ta wanke fuskar ne.
Bata ce mata komai ba ta rab’a ta gefenta ta wuce..
Inda take zaune a kan gadon ta je ta gyara pillow ta koma chan k’arshe ta jingina da jikin gadon ta lumshe idanuwanta
bata ma bi ta kan Aaima da take cewa
“Yace gashi nan zuwa har ta bashi adreess”
ba.
Kamar minti talatin ya kira number Aaima ya ce “yana bakin estate d’in”.
……..
Aiima bata yi minti ashirinba
ta dawo.
Tun da ta shigo suka lura da yadda jikinta ya yi sanyi over.
A hankali ta nemi waje ta zauna a gefe ta yi shiruuu, ita kad’ai!
Sai ta d’an yunk’uro za tayi magana sai kuma ta koma ta yi shiru, dan ita ba ma ta san ta ina za ta fara ba.
Su dai su Hudan ido kawai suka dinga binta da shi
kafin Huda ta yi k’arfin halin cewa
“Aaima lafiya kuwa?”
Dan suma yanayin nata ya saka su a rud’ani.
Har ta yunk’uro za ta yi magana kamar farko
sai kuma ta sake yin shiru kafin tace “ina zuwa”
Ta fad’i hakan tana d’aukar wayarta.
Gallery ta shiga ta hau bincike har ta nemo hoton da take nema! Kamar za ta mik’a musu
sai kuma ta ce
“Bara in baku wani d’an tak’aitaccen labari……
Akwai wata k’awar mu
da muke department d’aya level d’aya d’aki d’aya da ita a Nile! Mu hud’u ne a group d’in mu, ni da ita da ragowar friends d’inmu su biyu
tun farkon zuwanmu tare muke har yanzu da muka zo k’arshe.”
Ajiyar zuciya ta sauk’e kafin ta ci gaba
“Wadda muka fi shirin da ita
ita ce
‘Suhailat’
K’ut da k’ut muke ni da ita sosai.
Akwai wani saurayinta da suke tare tun farkon zuwanmu Nile
ta ce min tun a secondary school ta san Abokinsa
tare
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 16 Chapter of 26