Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
idan ta je dubata har kuka take yi saboda Umma ta zama abun tausayi. Duk k’asar da take ji da kwararrun likitoci Junaidu sai da ya kaita…an yi maganin Hausa da turanci amman har yau babu ci gaba sai ma abun da ya k’aru dan wasu lokutan har duka take yi. Anty Zainab itama bata koma gidan Mijinta ba! Ganin tana zaune haka ba wanda ya fito mata yasa itama Junaidun ya bata nata jarin suke zaune ita da Baaba Talatu a gidan Kaka wanda nan ma ya gyara musu sosai. Idan ka ga Jalila ba zaka ce ta tab’a yin rashin ji ba! Ta nutsu sosai. Bayan aurenta sai da ta yi sauk’a yanzu haka a islamiyyar da Mijinta ya bud’e take koyarwa. Ta rungumi Mama a matsayin Uwa Sakina da Huda da Sumayya kuma a matsayin y’an uwa sannan ta rik’e Mijinta wanda ta fahimci shine gatanta kuma shine masoyinta na gaskiya. Tabbas Jalila tana cikin matan da za ace sun yi sa’ar samun Miji mai tsananin k’auna da tausayinsu tsakani da Allah. Wani lokacin har ce mishi take yi ‘ya k’ara aure’ saboda duba da a yanda ya sameta ita! Amman duk sanda ta yi mishi wannan zancen sai taga fushinshi a cewarshi ‘shi ita yake so ba wani abun ba kuma ya tabbatar ba zai tab’a iya had’ata da wata y’a mace a zuciyarshi ba.’ Ibraheem irin mazan nan ne masu zuciya Mahaifiyarsa ta rasu itama two years back k’anwarsa ma ta dad’e da yin aure. Dukda Ubangiji ya rubuta mishi rayuwar middle class zai yi hakan bai hanashi siya mata y’ar k’aramar mota ta mata ba! Sannan ya tashi daga gidan Junaidu ya yi gidansa Ita ma kuma tana business d’in kaya daga India Dubai wanda Junaidu ne yake kawomata duk zuwanshi, itanma kuma ta tab’a zuwa sau d’aya da kanta ta je ta sari kayan ta dawo bayan Hajji da Umara da Junaidun ya biya musu suka je ita da Mijinta tun farko farkon aurensu. Ya’yan ta biyu mace da Namiji, ta farkon sunanta Maryam mai sunan Huda tana ce mata didi na biyun kuma mai sunan Kaka, Bashir. Sai kuma tsohon cikin jikinta maybe su haihu tare da Huda ko kuma Huda ta rigata. Tsakaninta da Aaima akwai zaman lafiya da friendship da mutantanta juna ga zumunci...... Tunda aka fara bikin su Sumayya Hudan take nak’uda sama sama.. Sanin da ta yi lokacin haihuwar ta bai yi ba yasa kawai ta yi shiru a tunaninta juyi ne! Sai dai ranar da za a kawo Amarya jikinta ya motsa sosai! Dama Sakina ta fahimceta tun jiya dan haka ta yi rushing nata zuwa asibiti ba tare da ta gayawa Aslam ba dan ya ce ‘ba a nan yake so ta haihu ba, tunnda haihuwa ta uku tana zuwa da complications gara ya fita da ita waje’. Kuma ta san in dai ya ji Huda tana nak’uda ne amman ta yi shiru to zai ji haushi sosai. Tun kafin su k’arasa asibitin faya ta fashe, ko minti talatin baayi da shigar da itaba ta haifo y’ay’anta biyu kyawawa maza masu kama da Aslam sak..... Sai after one week tukunna Granpa ya had’a walima iya family kawai na welcoming Sumayya da twins waenda suka ci sunan Arshaad da Auwal (Abhi da dada). Takanas Granpa ya aikawa su Shuwa nasu invitation d’in. A compound d’in tsakar gidanshi aka yi decoration manya manyan dining table masu seat 20 guda biyu aka k’awata D’aya na manya d’ayan kuma na Yara jikokin gidan. Wajen 5:00pm kowa ya hallara, tun rasuwar Kaka Granpa ya zama shine Abokin Madu, shiri suke yi sosai….Allah ya arawa Granpa tsahon rai tubarkallah, sai dai fa ya tsufa sosai dan baya ma iya takawa a kan wheelchair yake. Haka aka fara gabatar da walimar bayan Madu ya bud’e taro da addua. In ka gansu kowa cikin farin ciki da walwala da annashuwa Mama na zaune kusa da Abba Mom da Anty Kaulat sun saka Daddy a tsakiya Mommy a kusa da Dad Hudan kusa da Aslam sun d’au twins d’insu a hannu Arshaad da Jihad Sakina da Auwal Aaima da Junaidu sai Jalila da Mijinta. D’ayan dinning d’in kuma Yaran ne tun daga kan Arshaad har kan Abbakar Saddik. Ana gama cin abincin Granpa ya yi gyaran murya ya ce “Hudan Maryam Aisha inaso in sake baku hak’uri” Da sauri Madu ya ce “Dan Allah ka yi shiru. Yanzu haka kana ganin akwai grudges? Komai ya wuce, mu yafi juna Allah ya yafe maana.” A hankali ya sauk’e ajiyar zuciya yana kallonsu Mama one by one… Cikin had’in baki Mama da Mommy suka ce “Granpa iyaye basa laifi a wajen y’ay’ansu, komai ya wuce.” A hankali Huda itama ta ce “Mune za mu nemi yafiya da albarkar ka. Komai ya wuce ka manta komai kamar bai faru ba! Ka sanya mana albarka dan mu samu haske a rayuwarmu.” Ajiyar zuciya Granpa ya sauk’e sannan ya russunar da kanshi k’arasa yana jin yadda hawaye suka fara taruwa a tsofaffin idanuwanshi da suka ga jiya suka ga yau. Cikin zolaya Madu ya ce “Stop being emotional mana old man!” Da sauri Granpa ya d’ago ya ce “Ai ka fini tsufa!” Dariya aka saka saboda ansan dama sun saba, duk cikin su biyun ba wanda yake so d’an uwanshi ya ce mishi tsoho! Watarana ma Granpa cewa yake yi Madu ya girmeshi kuma ya tubure! Dole a hak’ura a tafi akan an yarda Madun ya girmeshi……. A hankali Huda da Mama suke kallon family d’in nasu.. Tun daga kan tebur d’in su har na su Arshaad kowa kawai dariya da farin ciki yake yi. A tare Mama da Huda suka share kwallar farin cikin da ta zubo musu ba tare da kowa ya gani ba sannan a tare a hankali suka ce “ALHAMDULILLAH!”. Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!!… Na godewa Allah da ya bani ikon kammala littafina mai suna ‘So da Buri’. Kuskuren da na yi a ciki Allah Ubangiji ka yafemin, darussan da suke a ciki kuma Ubangiji kasa mu amfana. *Godiya ta musamman tare da fatan alkhairi ga Anty Aisha Gadanya, Ina godiya kwarai Anty, alkhairin Allah ya Isar miki a duk inda kike* *jinjina tare da godiya ta musamman ga y’an group d’in So da Buri da H B’s palace masoyana bani da bakin gode muku sai dai Addu'a wallahi, na gode na gode sosai Allah bar zuminci ya kuma kare min ku kullum da koda yaushe na gode sosai* *Godiya tare da fatan alkahairi ga duk wani member na Mikiya Writers Association, Ina godiya kwarai sisters Allah ya barmu tare ya ci gaba da kare min ku* Taku har kullum Humaira Bulama. ............ An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 26 of 26