Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kada ki ki zuwa, na ce kin sanni Rahma in har na ce zan yi abu bana fasawa, ta ce shi kenan, ki gaida min Shadad. Na tafi ina hawayen rabuwa da Rahma, don ita wani bangare ne na farin cikina. Gidan su Maman Rahma naje na dauko Shadad, jikinshi naji da dumi, ina zuwa gida na bashi (paracetamol) Na kwantar da shi. Sannan na shiga gyaran gida. Ina zuwa na samu ma yayi bacci, nayi Shafa'i da wutiru nima na kwanta. Cikin dare na farka don yin nafila kamar yanda na saba, sai dai kawai naji jikin yaro sharkaf da zazzabi. Na cire masa riga na dunga goge masa jiki da ruwa mai sanyi. Sanna na kara bashi magani, kafin safe Allah ya taimakeni jikin yayi sauki. Sai dai yan rigin gimun da yake yi na shiga gidan su Rahama muka gaisa da su mama, ina zama Kiran Rahama na shugowa, ina ji dama nasan ita ce, dan bani da number kowa a cikin zumu dina na daga ina cewa hajiya kenan, amarsu ta ango. Ta katseni da cewa, ba wata hajiyarki, shine ko ki kirani da safe ko? Nace shi kenan sai na hau doka maki kira da safe kisa angonki ya ji haushi na. Tace wane ango? Kin san Allah ba nan ya kwana ba, tare da su hadiza kawaye na muka kwana, ba ke kinki ba? Nace ai gara da na dawo, dan na sami shadad da zazzabi haka muka kwana. Amma yanzu Alhamdu lilahi. Tace to Allah ya kara sauki. Tace don Allah ina sa ido gurin programme din nan, wlh in baki zoba bikin zai baci, don kina da muhinmanci matuka a gurin. Nace to zan kokarta duk da shadad nata yan rigingimu, kin sanshi in baya jin dadi sai yayi ta rigima, tace yaro kenan Allah dai ya kara sauki,nace amin, yace kizo da wuri dai. Sai da na fara yima shadad wanka, sannan na shiga na fito naga gari ya soma hadari, nayi alawala dan yin sallar la‘asar, haka kawai yau naji ina sha‘awar shafe shafe a fuskata. Na fito da kayan shafa da rahama ta di bar min na lefenta, har da jaka da takalmi da mayafi ta bani duk pink, tun asali ni mai son yin kyale kyale ce, halin da na tsinci kaina ne yasa na daina, nafi minti 30 ina kyalekyale a fiska ta. Na dinga kalon kaina a madubi nasan nayi kyau sosai, har shadad yana kallo na, nace nayi kyau? Ya daga kai ina kulle gida rahama na kira na, na daga tace aminiyata ki tai makeni kada kisa naji kunya, wlh guri yayi guri amma ke kadai muke jira da wani abokin sagir da ya sauka daga adamawa state, anje daukoshi daga filin jirgin don Allah kiyi sauri. Nace to zubaina ganin zuwa amma fa garin akwai hadari, Allah yasa in sami abin hawa da wuri. Tsaye nake a bakin titi duk wani dan a daidaitan da yazo yana dauke da mutane, masu son banza watan yan rage ma mata hanya suna tsayawa Amma ni ko kallon su bana yi. Wata jibgegiyar jeep ta zo ta gifta, sai kuma ta dan dawo.sai tin inda nake ta tsaya, gilashin motar ya sauka a hankali,naga mai tukin saurayine yana sanye da shadda yar gaske blue mai duhu, hularshi itama blue ce, amma kalar sararin samaniya. Ta gefen ido na kaleshi, sannan na dauke kaina. Yace, yan mata ina zaton guri daya zamuje in na lura da shigar da ke jikin ki ko? Na kaleshi nace ba dole hakan ta kasance. Yace, yace ki shugo muje kinga hadari. Nace kuje na gode. Glashin baya ya sauka, naji saukar galas din ne da wani sauti da yayi, amma ban waiga ba, saima na dan kara taku biyu ta baya na. Muryar da naji ne tamkar in waiga, amma sai na dake yace shugo mana ga hadari nason zubo da ruwa gaki da yaro. Na dubeshi dan son in tuna inda na san wanan muryar, kyawunshi yasa nayi saurin kauda kaina, tare da cewa kuje ni ba zan shiga ba.daga cikin motar naji wani yana cewa don Allah mutafi amma za a taimaka mata tana yiwa mutane yanga,da sauri na kallesu cikin bacin rai, idanuna har kan kancewa sukayi don ta kaici, cikin kalon hadarin kaji nace taimako? Ce muku nayi ina neman taimako? Na dan duka tare da leka motar, kai me fadin taimakon nan kasani bana neman taimakon wani abin halita sai ma halincci, ni ban tsai da ku ba. Na kara rike hannun shadad da kyau, na soma tafiya dai dai da ruwan ya kece, kamar da bakin kwarya, ba tsanmani sai naga kofar ta wangale na bakin kofar ya sauko kafa tare da sauko hannu ya dauki shadad zuwa cikin motar, a gigice na dubesu yace ki shigo in kuma ba zaki shigoba ki samemu a can. Amma shi kam ruwa ba zai dake shi ba. Bani da zabi, tunda sun daukar min yaro dole na shiga. Gashi bana son dukan ruwan, don haka sai na shiga. Shadad na ciyar mutimin da muryarshi ke sani faduwar gaba, kamar na taba jinta ada innaso in tuna inda nasan muryar ko mai irinta. Muryar ta sake katseni da tunanin da nake yi, yace ma shadad boy ya sunanka? A zatona shadad ba zai yi masa magana ba, saboda shi yaro ne mara son ma gana, musanman in bai san mutun ba, sai naji yace shadad. Mutumin ya mai maita sunan shadad, sunanka yayi dadi, to wanan fa? Ya nunani ya sunanta? Shadad ya kalle ni, na zabga mashi harara, amma ga al‘ajabi na sai yaron nan ya kauda kai yace anty. Mutumin yace to kana zuwa makaranta? Yace eh al‘iman sunan makarantar mu, kuma muna yin (A B C D) har da(1234). Na rike baki inata al‘ajabin yaron nan, tunda nake dashi ban taba jin yana rarata surutu haka ba, harda kin kalona shida ko abu aka bashi da ya kali fuskata zai gane, in ina nufin ya karba ko karya karba amma sam ya ki kallona tunda ya gane ina hararan shi. Mutumin yace gud, kana yin kokari? Yace eh mana, har ma naci number one, aka min kyautar books. Anty na kullun tana koya min karatu, da su home work harda ma islamiyya, ban san sanda nace shut up stupit boy! Mutumin ya kalle ni, shikuma shadad ya kwanta lakwas a jikin mutumin. Ya tsorata dan bana mashi tsawa, ko yawan zaginsa. Na daga can gefen yace. Ke! Wai wane irin hayaki kanki ya keyi? Ko kuwa ance maki wani kyau ne dake? Ko ance miki sonki ake yi? Ko kuwa burgewa ce wannan masife masifen da kike yi. Nace kai saurareni bana son shishshigi da katsalandan cikin lamari na, nayi magana da kai? Ko nace ka kalle ni ne bare ka tan tance kyauna?gani na kayi a filin gasar kyau? Balle kace nace ina da kyau ne? Masifa kuma dole ku jita tunda ku ka nace sai kun dauko ni, haka nan bana bukatar burge kowa cikinku na fison in burge kaina. Don haka yi ta kanka dan dukanku bakwa gaba na, zaiyi magana mai dauke da shadad ya daga masa hannu alamun yayi shuru. Shi kuma yaci gaba da shafa kan shadad wanda yayi kwance a jikinsa. Wayata ta shiga ruri, ban ko kula ba dan nasan rahama ce, sai yi take tana katsewa, ana 5 din na daga a kufule, don itama haushinta nakeji ba don bukin ta bane wa za ya hadani da wayanan gardawan. zaharaddeen Shomar what's app 08168575100 Sanadin Boko 1-09 Posted by ANaM Dorayi on 12:23 PM, 18-Sep-15 Under: SANADIN BOKO Don itama haushinta nakeji ba don bukin ta bane wa za ya hadani da wayanan gardawan. Cikin fada nace wai meye ne kika dame ni da kira, ina hanya in kuma zaki matsa min sai na juya gida abina. Tace mai da wukar Allah ya baki hakuri, da ma ruwan da ake shekawa ne nace bari naji ko kin koma gida ne saboda ruwan sai direban su sagir yazo ya daukeki. Nace na hutar dashi, gani nan zuwa na kashe wayata tare da tsaki.Harabar hotal dam yake da jama‘a, ko ince motoci jama‘a sun cika holl din suna tsayawa na kama kofar zan buduwa. Ashe daga gaba ne direbab zai bude mu. Yana budewa na fita, sanan na nufi ciki mai surutun tsiya nan shadad ba tare da na kalesu ba na nufi wata yar baranda ina ta yi mashi fadan irin surutun da ya dinga tsugawa acikin motar, sai ya bale mun da kuka yana fadin.uncle! Uncle!! Nace yi min shuru ko in mareka, sarkin shishigi, bai daina kukan ba, na na ciro wayata na kira rahama gani nan fa ba zan iya shiga ba, mutane sunyi yawa. Ta ce mun ganki kin tsaya ga Aisha nan tazo zata taho dakegurin mu tare zamu shiga. Nice a gefen amarya sauran kawaye suna bayan mu,haka nan ango da abokan shi suna biye da mu, ina reke da hanum shadad, wanda har lokacin bai daina gunjin kuka ba, muka shiga. Kidan da ke tashi kamar zai fasa kwanya yasa naji tamkar in bar gurin kai tsaye. Wani mai dauke da abin magana yace, ango da amarya sun shigo, kowa da amininshi zai zauna, sagir ya zauna gefen shi wanan mutumin, ni kuma ina gefen Rahama tare da shadad ta dube ni, mutuniyata wa ya taba ki ne, naga fuskarki ta kasa boye fushinki, nace uhm! Ke dai bari, abokanan muijinki ne wlh, sai kuma shadad yaron nan ya kular dani yau. Tace to dan saki fuskar mana saboda guri ya kayatu, kisan fushinki zaisa gurin ya dishe. Na harareta tare da dan murmushi, tace ko kefa. Sagir yace ranki yadade, ya gajiya? Na nace tana gurinku ya jama‘a? Yace gasu muna tare nace Allah yasa alheri, da ganan na maida hankalina gun mai abin magana, yace za mu kira baban bako kuma baban abokin ango don yayi mana jawabin maraba tare da dan fada mana wanene sagir. Sai dai kafin nan babar kawar amarya hajiya hafsat sai ta bude mana taro da adu‘a, na kali rahama tace please, tashi kawai. Na mike cikin natsuwa na isa gurin na amshi abin maganar. Shadad yazo ya rikeni yana kuka, sai wai abokin ango ya taso ya daukeshi. Bayan n gama adu‘a na dora da karanbanin nawa, ina bawa jama‘ar da ke gurin nan shawar kada suyi liki, almubazaranci ne ga duk mai sha‘awar ya burge ango da amarya su dan ka musu a hanun su, amma ba dole bane kuyi yanda nace,sha wara ce. Na koma na zauna, bayan sun bini da tafi. Shiko da zaije yin jawabin maraba tare da shadad yaje yana rike da hanunshi. Cikin jawabin ne naji yana jaddada maganata cewa abinda na fada yayi kyau, don haka ba‘a son liki, duk wanda zai lika yazo ya ba ango ko amarya a hannusu. Wanan ma yasa aka kashe rawa da za‘ayi, rahama ta dinga yi min dariya wai a gaisheni da karfin hali har ta sanima na dinga dariyar. Sagir cewa yayi nazo na hanasu rawa, to wane rawa zasuyi ba liki? Nace tai makonku nayi ai rawa haramun ce ko? Haka aka ta gabatar da abubuwan da za ayi har lokacin da akayi sanarwar ango da amarya tare da da masu tayasu zama dan dibar abinda suke son ci da kansu, kasancewar dibi da kanka ne za ayi a gurin. Muka hadu muka jeru amarya tana biye da ango yayinda ni kuma nake biye da abokin nashi, shi kuma yana dauke da shadad a kafada tamkar wani danshi. Ango yasa abida yake so sai fruit ya ce ko zaki tai maka min? Inji abokin ango tamkar ince a'a amma sai nace me zan sa maka? Ganin yana sabe da shadad yace ki samin ko menene, zan ci. A raina nace kaji dashi, ba tare da tsayawa tunani ba ko mai hanu na yakai shi nake zuba masa, sai da na shake plate din sannan na bi bayanshi da plate 2. A gabanshi na dire tare da samashi cokali, na koma ma zaunina. Sai kurum naji sarkin surutun nan wato mai rike da abin magana yana cewa, kai gaskiya ango da amarya kun burge ni, kun zauna da aminan ku kuma mata da miji har da dansu, to yace ke amarya yaya bakiyi koyi da kawarki ba kema ki zuba ma ango da kanki? Kai abokin angon nafa yi maka murna, matar kada kayi mata kishiya, dubi yanda ta cika maka plate da kaji da kifi kila abinda ka fi so kenan, wanan ya nuna ko a gida ba a barinka da yunwa. Sai kurum naji gurin ya dau tafi. Da sauri na dubi plate din, lallai kam kaji ne da kifi, sai dan cosilo a gefe, na dubi fuskarshi yana dan murmushi. Rahama da sagir kuma dariya naga suna ta shekawa nan take na hade rai tare da kin kai komai bakina. Shiko shadad sai uban cin naman nan yake yi, shi da mutimin tuni gurin ya rikice da ciye ciye kowa na diba da kansaRahama tace to kici mana,nace mata ke ni nama koshi, ba yan haka ma ni ba zan iya cin komai a taron nan ba, kowa yana kallona. Haka nan bayan an tashi duk na matsu naje gida domin magariba ta yi, ina so inyi sallah sai dai tun da muka fito banga shadad ba, ban ga mutumin nan ba. Nace rahama ina suke? Tace suna cikin jama‘a in dan jira. Can nesa na hango wani shago naje na siyo ruwan naira 10 nayi alwala, nasami gefe dama da hijabina a jaka, nayi sallah ta. Rahama tazo tana ce min sun dawo? Nace ke zan tam baya, ina mijinki? Kune kuka sanshi ku zaku nemo shi. Takira sagir tace sun ko dawo? Hafsat tana son zuwa gida. Yace a'a na kira wayarshi kuma a kashe, tace a a to ina ya shiga? Kai kana inane? Yace gani nan kusa da shago ina kallon ku ai. Muka nufi girin ango, hankalina ya tashi da rahama take fada min wai wayanshi a kashe.rahama ta dubi angon ta tace, ba kace min bako ne ba? Yace eh amma kano ba bakuwa bace a gurinshi. Ki kwantar da hankalinki, yauwa gasu nan zuwa ma, duk muka kai duban mu gurin shi. Yana rike da hanunshi, shi kuma yana reke da leda. Suna tafe suna yan zan tukansu har suka isko mu, nace kai ka cika shegen yawo, ina kaje? Na finciko shi yace anty munje masalaci ne da uncle, ba kin ce mun wai in dinga sallah a farkon lokacinta ba? Nace naji ni dan Allah wuce muje na dubi rahama sai watarana, tace dinner din fa, anjuma karfe 10 naja tsaki ke kinsan ba zan iya wanan galafirin ba, gara ke sai dai nazoo. Sagir yace ki bari a kaiki don Allah, gari yayi sanyi ga duhu, nace nagode, sai anjima nayi gaba.Wani daga cikin abokan da suke tsaye wanda har dashi muka shigo motar nan da zamu zo, ya dubi rahama yace kai wanan kawar taki ta cika masifa, ita ba kyau ba rahama tace a a kada ka zagar mun kawa masa‘udu, hafsat bata da masifa,tana da kirki sosai na jima banga mace mai saukin kan hafsat ba, ita dai abu 3 ta tsana a rayuwarta, inko mutun ya kiyaye ba mai jin su. Ni da ita bamu taba yin fada ba koda munyi sai dai ni ni na ta sababi na amma bata biye min. abubakar lamido yace yanzu kai kaga masifarta? Ya dubi masa‘udu masa‘udu yace au yanzu duk abinda take maka baka gani ba? Yace ni kam me tamin? Bata min komai ba, duk abubuwan da takeyi sun matukar burgeni. Ya dubi rahama, ni kam in tambaye ki? Rahama tace ina jin ka, yace amma dai ba matar aure bace ko? Rahma tace a a daga nan bai sake magana ba. Duk abubuwan da Abubakar Lamido ke gani daga hafsat bai taba ganin wani aibunta ba, tunani 1 ya dameshi, ina ya santa? Shi dai yasan cewa koda a hanya ne ya taba ganin ta. Anashi ganin Hafsat ta san mutuncin kanta shiyasa take wanan dabi‘un. Acikin masauki ya kasa zaune da tsaye, baisan meyasa ya damu kanshi da dabi‘un hafsat ba, bai taba ganin mace da ta burge shi irin ta. Yasan daga ganin halayenta za asha wuya kafin a samu soyayyar ta, duk da bashi da tabacin sonta yake ko burgeshi take. Ya dai san ko ma dai menene ya damu da ita. Kafin kwana 3 ya damu da son sanin wacece ita? Alwashi ya sha ma kansa ba zai bar kano ba har sai yasamu cikaken labarinta, wanda yasan gurin rahama ne kadai zai san haka, haka a rana ta 4 ya kira sagir yace gashi nan zuwa, zaya ci dinner tare dasu. Duk da tulin kayan da aka tara a gaban shi na lashe-lashe da tande-tande, sam basu dameshi ba, ya dubi sagir cikin hausarshi na fulanin yola ya ce, nikam ka bani dama inyiwa amaryarka wasu tanbayoyi game da kawarta nan sagir yace wace ba dai hafsatba? Bai san da lilin fadiwar gaban da yaji ba, haka nan bai san lokacin da kalma ta fito daga bakinshi ba, tana da miji ko? Ya tsare sagir da idanun shi masu kama da na mata.Sagir ya ce bata da miji, amma fandarrarun halayenta ne zasu gundire ka, yace bana zaton haka, yanzu dai nafi so ka min izinin zantawa da matarka, yace to ya kirata tazo ta zauna tare da cewa ba dai har ka gama cin abincin ba?Yace ai kafin abincin ya samu shiga nikam sai naji batun kawarkinnan hafsa. Rahama ta dubeshi da sauri tace me kake son sani game da ita? Yace unguwarsu da kuma dan lbr ta haka rahama tace unguwarmu daya, sannan ita daliba ce a Poly yanzu haka tana HND dinta ne. Iyayanta fa mutanen kirki ne? Rahama ta danyi din sanan tace eh yace ta taba aure ne? Kuma shadad dan tane? Nan take zufa ta karyo mata, amma bata da amsar da ta wuce eh ya jijiga kai, dama nayi zaton danta ne duk da batayi kama dashi ba sun rabu da mijinta ne ko ya rasu ne? Nanma tace eh, yace Allah sarki inaga shiyasa bata son hulda da maza, dama ance mace in mujinta ya rasu kafin ta manta da wuya. Iyayan ta din sunan layinku? Rahama tace eh, a a karatu tazo suna kaduna. Gurin aikinmu daya ne super market ne, yace to zan iya samun number dinta? Rahama tace wai gaskiya yallabai sai dai kayi hakuri, in na baka number ta zai iya zama sanadin rabuwar mu kwata-kwata. Ya dan yi shuru yana nazari, Rahama tace duk yanda kake tunanin hafsat ta wuce nan. Yace amma ina zaton bakinki naji yana fadin tana da saukin kai da dadin zama, kuma bata da fada? Rahma tace gurinmu mata ba, amma game da maza sam bata da sauki, ta tsani namiji ta kijinin ace anason ta sanan bata son taimako daga namiji, ko wannen abu 3nnan ba taso. Yace to me tafi so? Rahama tace abinda tafi so shine kada kashiga harkarta, in kuma kashiga kayi tsananin dace ta kula ka to kada ka tam bayeta ko wace irin tanbaya, sannan kada kace kana sonta, ban san me zakayi ba ta saki jiki da kai ba, don naga maza da yawa wanda suka sota amma dole suka hakura rashin sakin fuskarta yasa maza suna tsoranta. Da zaka hakura da ya fi maka lada don ko taji hau shin abinda MC yace mata a gurin bikinmu inda yace ku miji da mata ne. Abubakar yace niko sai naso ace gaske naji dadi maganarsa. Rahama ba zan iya hakura da hafsat ba don ina jin wani abu game da ita wanda ban taba jinshi a wata yarinya ba ina zaton shine so. Su Rahma suka sa dariya sagir ya nisa yace lalle sonka din nan ya iya jan rigima ya fada inda zaku sha wahala Abubakar yace sona yayi daidai don yasan bama ra‘ayin mata marasa aji wadanda ke bin maza da kansu suce suna so zanje in gwada sa‘a ta kafin na bar kano zanga yada zamuyi. Sukace Allah ya taimaka yace kasan ban sami daurin aure ba so bansan gidansu rahama ba bare insan nasu hafsa din. Yace bari inje in nuna maka daga nesa suka fita suna dariya ba tare da yace komai ba shi tuni ya manta da menene a gabanshi ko da sagir ya nuna mashi sai yace ba yanzu zanje ba sai gobe da safe. Ni kam tuna ranar da muka dawo daga bikin rahama kulin shadad bashi da magana sai ta uncle dinshi tun ina jin haushin shi ina mai fada har na dawo lallashinsa, saboda har lokacin yana fama da zazzabi nakan lallabashi da cewa kayi hakuri zai zo ya daukeka ranar cikin dare har da cewa to anty kirashi a waya nace to ka bari sai da safe yanzu yayi bacci, cikin kwana ukun nan da kyar na samu ya manta da maganar uncle sai jifa-jifa. Da safe yana sanye da kayan makaranta ni kuma nayi shirin gurin aiki. Yau bani da lecture da safe don haka gurin aiki zanje dama ka‘idar da manaja ya bani kenan dan a daidaitanmu yana jira, shadad ya fita da gudu ni kuma na kule dakin na fita. Ina rufe gida naji muryar shadad yana cewa anty ga unclena anty na wai wayo baya na datse kwado, ilai kuwa yana tsaye jikin wata yar kyakyawar motar blue kiran kanfanin (toyota) sanye da t-shirt da wando jeans baki, riga baka da ratsin ja. Ta kalmin kafarshi baki ne sauciki. Na dauke fuskata daga kalonshi bacin nayi fuskar shanu shadad wanda tuni ya daneshi, murna yake yana cewa unclue kazone? Da ma anty tace indaina kuka zakazo, takaici ya kamani. Shi kuma sai ya dubeni anty antashi lfy? Ba tare da na kaleshi ba nace kalau na daga labuln dan a daidaita na shige. Sai naji yana cema dan a dai daitan, ungo nan malam kaje sai bayan kwana 2 ka dawo tun da nazo ni zan rinka kaisu kafin in tafi. Ya mika mushi yan dubu dubu sababi fil guda 3 ya amsa yana cewa na gode yalabai to sai zuwa yau she zan dawo yace nan da kwana hudu haka nace sannu da karfin hali menene gamina da kai? Da har zakaso ka min iko? Bai ce kala ba ya juya. Na cema dan a daidaita sahu muje na leka nacewa shadad zo mutafi ko nayi tafiyata. Mutumin ya kaleni shima fuska a kame ki fito muje ban san sanda nace to ubana! Sai kazo ka jani ya kara matsowa saitin dan a daidaita yace ka sauketa katafi abinka. Sai kawai mai a daidaita yace kiyi hakuri yar uwata, ki sauka ban tankashi ba bankuma sauka ba,gani nayi zamuyi latti nace yanxu kai malam haka zamuyi da kai? Duk tsawon lokacin da muka dauka yau kace bazaka kaini ba? Yace to Alhaji ne yace ki sauka ai, kuma ni bansan dangantakarku ba kada in shiga hurumin da banawa ba. Nace to bawata dan gantaka a tsakanin mu, asalima ni ban sanshi ba da muna da alaka da baka gan shi ba ko sau daya? Yace ki sauka mana nasan duk yanda akayi kunsan juna. Ganin zai bata min lokaci sai na sauka na dauki jakata nace shadad ya wuce muje, a mota yasaka shi amma ya tada mota sukayi gaba. Na tare mai mashi muna ciniki yazo yace mai mashi tafi abinka, in ka dauketa zaka gamu da hukunci... kafin ya rufe baki yaja mashin ya kara gaba. Na kaleshi nace me kake nufi dani? Yace gurin aiki zan kaiki kawai,nace banaso dan Allah kai mayene? Yace a'a ni ba maye bane, to bin me kake min? Nifa ba yar iska bace. Yace nasani ai, to dan Allah kafita hanyata, in kanawa darajar mahaifinka. Yace don girman Allah ki shiga motar nan mu tafi, kada shadad yayi latti, sannan inaso ki bani lokaci nazo mu dan tautauna, nace bani da lokacin da zan iya baka, ka fita harkata please, nacigaba da tafiya. Ranar dai a kasa na tafi gurin aiki, shikuma sukayi wani guri shida shadad, nasan sai dai suyi tambaya amma shadad ba zai iya gane makarantar ba, ganin nakusa bansha wahalar hawa abin hawa ba na karasa, takwas ta gota ina shiga ishak yace yau bamakaranta kenan? Nace eh, gashi ma nayi latti, musa yace manaja kuwa yazo yananan ya zagaya ciki nasan sai yayi maki surutu, nace uhum sai dai yayi tunda dai latti na riga nayi shi.Ina zama yana isowa, ban ko kalleshi ba na jawo takarda dake kan teburina zan fara duba abubuwan da suka fita da safen nan, sai ya ce, "Kin san zaki zo da safe me yasa zakiyi latti?" Na ce, "Abin hawa ne ban samu ba." Ya ce, "Amma ai ba'a wahalar mai ko?" Na ce, "Kamar yaya?" Ya ce, "Ballantana ki ce ana wuyar abin hawa." Na ce, "Akwai abin hawa mana." Ya ce, "Baki da kudi ne?" A kagare na ce, "Ina da shi." Ya ce, "Ok kin soma gajiya da aikin kenan?" Na san shi sarai zai iya cewa ya koreni, kuma dai Allah ya sani da aikin na dogara, don haka nace, "Tunda ba halina bane lattin amin uzuri." Ishak yace ayi mata hakuri Sir. Ya ce, "Kune kuka iya bada hakuri ita bata iya ba ko? To ba zan mata uzuri ba, sai dai in taimaka mata." Cikin sauri na ce, "Bana son taimakon kowa sai na Allah, nace dai amin azuri." Ya ce, "To ki je gida ki huta na sati 2 don ki koyi yadda zaki dinga zuwa aiki." Muryarshi muka ji ya ce, "Uzuri za'a yi mata manaja." Ya dubeni har na mike, "Koma ki zauna. Manaja akwai uzuri a rayuwa, ko tana latti?" Ya ce, "A'a ranka ya dade bata dai da mutuncine, in banda rainin hankali tana fada min akwai abin hawa kuma tana da kudi amma ta zo latti?" Ya ce, "Duk da haka ka mata azuri da tace baka san dalilin ta ba, so tayi zamanta." Na dube shi ina mamakin karfin halinsa, sai naga ya nufi Ofishin manaja na ce kila ya san shi ne. Ni dai na zauna na ci gaba da aikina. Ina jin Musa da Ishak suna mitar rashin mutuncin shi.Abubakar ya dubi Manaja ya ce, "Ka daina yiwa mutane haka, musamman na kasa da kai, a rayuwa dole ne mutum ya dinga hakuri, yanzun

Chapter 8 of 22