Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
cikinki wata nawa ne?Da sauri na kalli Abubakar sannan na sunkuyar da kai.Ya ce "Fada min mana "Na ce na zaton cewa xai kai shidaa."Abubakrya dago idona ina da yaro dan wata shida a gurinki, ina me ban sani ba?likitan yayi daria,'kila tana son ta baka mamaki ne ko?na ce"Ina son in ci abincin. Da sauri likitan ya ce me xa ki ci?na ce "Tea xan sha.Nan da nan yayi waya a kawo min tea.Abubakr kuwa cikin rigata ya xura hannu yana shafa cikina yana min magana a kunne."d only me yasa kika rufe min?na ce To kana fama da mara lfy sai nima in kwanta mu taru mu daga maka hnkl?Ni ba xan iya ba, bana son in ganka ckn damuwa,shi yasa na daure. ya ce "Allah yi miki albarka, dama nasan kece mai son kwanciyar hankalina. bayanna huta ya sallame mu muka nufi gida sai yau naga gidan da aka sai masu Baba a nan dai Abuja Road din ne amma can kasa gurin sabon guri ne kuma gida mai kyau flat. .. Abubakar kam da ya fita sai ya je ya kama masauki, sai dare ya dawo. Ya ce na zo muje, bansan ko ina bane na cewa su Baba ina zuwa. Sai kurum ya kaini masauki, wai nan zamu kwana, na ce "Haba Mr Cool, ka maida ni gida mana su Baba zasu ga rashin kunyata." Ya ce, "Bazan iya barinki ba, bakiji Likita ya ce na kula dake sosai ba?" Sai waya nayi wa su Baba na ce munje gidan wani abokinsa can zamu kwana. Suka ce to, kwanan mu uku, kullum da safe zai kawo ni amma da dare zai zo ya tafi dani. Wata sabuwar soyayya da tarairaya Abubakar ya soma yi min, da zamu koma gida jirgi muka bi. Muna isa ya fara yadawa ina da ciki, dama Likita yace in mun dawo na soma yin awo. Shine ya kaini asibitin ya yankar min kati, a dakin scanning Likita ya ce "Madam kin san cewa 'yan biyu ne?" Na zaro ido "'yam biyu?" Ya ce "kwarai kuma kin gansu duk maza" Na ce ba a fi sati daya ba da akayi min scanning a Kaduna ba a fada min haka ba." Ya ce to yanzun dai gashi nan" na ce to don Allah ka taimake ni kada ka rubuta a cikin sakamakon" Ya ce "don me?" Na ce "Don haka ta faru ga kishiyata, a karshe sai ta haifi mace guda daya."............ Zaharaddeen Shomar whatsapp 08168575100 Sabadin BOKO 4-07 Posted by ANaM Dorayi on 05:21 AM, 29-Sep-15 Under: SANADIN BOKO Ya ce to shike nan, ya rubuta komai lafiya amma bai rubuta mace ko namiji ba, bare ya saka 'yan biyu.haka naci gaba da samun kula, yanzun da asiri ya tonu sai cikin ya fito yayi rum. Da da ba a sani ba kuwa lakwam, har cikina ya kai wata takwas ban taba yi masa batun kayan haihuwa ba. Shi ne da kashi ya ce "wai the only baza mu sayo kayan haihuwa ba? Na ce to, sannan muka je ni da shi da Ummi. Wata safiya na tashi da matsanancin ciwon ciki da mara, gashi ya je Lagos amma ranar zai dawo. Da ya kira duk da koakrin da na ke na nuna masa bani da wata matsala sai da ya gane. Ya kira Dada ya ce a zo a duba ni lafiya? Ummi ce ta zo har ta tafi ban bari ta fahimci wani abu ba, tunda ciwon yana yi ne yana lafawa. Kafin dare na jigata, lokacin da ya shigo fayata ta fashe haka suka kwashe ni zuwa asibiti. Da Lamido na fadan me ya sa naki fadin banda lafiya, sai su Gwogwal suka ce ai kunya ce. Lallai ni yar mutunci ce, ni ba fulani ba amma ina da kunya. A raina na ce kunya ai ta dan sunna ce bata Fulani ba. Don haka duk Musulmi mai Imani zai zama yana da kunya. Da kaina na haihu, dana kato zuwa can kuma sai sabuwar nakuda, sai kuma ga wani dan. 'Yan biyu masu kama da juna, sannan duk wanda ya kalle su yasan 'ya'yan Abubakar ne. Tunda Nurse ta kawo na farko Abubakar ya ke ta murna da su Hashim, sai ta ce zaka bani goron albishir ina zuwa. Da tazo da dayan sai suka kama murna, kafin ka ce haka, dangi sun cika asibitin harda su Rukayya. Ni dai na ga lele, Fadi ko leke don ko da ta sami labrin ina da ciki bata zo ba. Lamido har asibiti ya zo, kwanana daya aka sallamoni zuwa gida. Tun a ranar Lamido yasa aka kada Sa aka yanka, nima yan uwana washe gari suka zo tare da su Rahma. Abubakar tamkar ya goya ni don kauna. Ranar suna kuwa fadar shagalin da akayi bata baki ne. Kyauta dai mun samu Masha Allahu, nayi kyau mai zane fulawa ta yarfa min nayi kyau har na gaji. Mun sha hotuna, Abubakar kuwa da abokansa tare akayi suna dasu. Na cii gaba da shayar da yarana kuma ana basu madarar M.S.A, suka yi tubarkallah. Mijina kullum kara son mu yake. Fadi kuwa na sama kanta damuwa, kullum ita kenan fada da miji ko a gaban waye sai tayi ta karta masa rashin mutunci. Yanzun ma sun raba jiha da Rukayya, dangin mijina tamkar su cinye ni don so. Tunda na gama service na samu aiki a gidan TV na Yola, amma Abubakar ya ce sai yara sunyi kwari. Ban ja musu ba, watansu shida na soma zuwa aiki na, bayan ya mallaka mana mota ni da Fadi kowa da tashi. Bani da matsalar rainon yarana don rubibinsu ake yi. Account na bude ina zuba albashi na. Domin akwai burin da naci dasu, tunda ba abindana nema na rasa. Daidai da katin waya sai Abubakar ya zuba min dubu biyar dubu goma, nayi kyau da ka ganni kaga matar so. Gyaran jiki kuwa da sabbin girki ba a magana. Shi kanshi mijina duk wanda ya kalle shi yasan matarsa tana son shi. Kusan in mutun yana cikin kwanciyar hankali daka kalle shi zaka gane, musamman namiji. In kaga namiji a hargitse a rame ton ba halittarsa kenan ba to kila bai dace da mata ba. Duk ranar da babu aiki na kan ce ya kawo min Nana Fiddausi, ina son yarinyar don ina son mace. Fadi bata son ya kawo mata 'yarta gurina. Amma bayanda zata yi, tunda baza ta iya hana shi daukar 'yarshi ya fita da ita ba. Sannu a hankali rayuwa tana tafiya kwanukan mu suna karewa, lamurra suna canzawa. A hankali na rika dora mijina kan hanyar taimako dukda cewa yana yi dama. Lokacin da ya gina sabongida Lamido yace ya saka ni a ciki saboda ya yarda ni na zama daya daga cikin zuri'arsu. Na cancanci in sakata in wala a zuri'arsu, komai sabo ya saka min, gado dan italiya, kujeru na alfarma, kayan kicin na gani na fada. Itama ya sa aka mata fenti ya canza mata kayan daki.Nayi walima ta alfarma har su Rahma sai da suka zo, gidan ya tsaru harda gurin wasan yarana. A ranar farko da zamu kwana a gidan yana zaune yana waya a bakin gadon dakinsa na alfarma. Na shigo sanye da kayan bacci, da hannunshi ya nuna min cinyarshi in zauna, ya ce "Alhamdulillahi, gida ya dace dake." Na ce yanzu saura ka gina dakin Allah (Masallacin Juma'ar) ungwar nan ka sabunta shi. Sannan ka gina wanda za a dinga kamsus-salawati, a wannan layin da muka dawo. Ya ce "an gama gimbiya, yanzun sai ki zabi wanda za a ba kwangilar ginin." Na ce duk wanda ranka ya kwanta dashi. Mai amana." Ya ce "To zan duba." Hakan ce kuwa ta faru nan da nan aka soma gini. Taimako marasa lafiya, gajiyayyu da marayu duk na kwadaita masa yasan zakinsu. Yana mutunta iyayena tare da taimaka masu. ********** Shekarar yarana daya da wata biyu, naji ban gane kaina ba. Hankalina ya tashi matuka. Ranar Abubakar yana gidan Fadima, na mashi text cewa zanje asibiti, ya ce Hassan ne ko Hussaini ba lafiya? Na ce "Ni ce" ya ce sai ga kiran shi, ya ce meke damunki the only? Sai kawai na saka kuka na kashe wayar.Minti ashirin sai gashi ya zo. Kayan bacci ne ma a jikinsa, me aiki na ya samu tana kara goge kicin. Ya ce "ina take?" Ta ce ina ciki sai gashi na tasa 'ya'yan idanuwana jajir, ya ce wai lafiya? Na soma sabon kuka, ya zauna ya jawoni jikinsa yana lallashi na, wai in fada masa meke damuna? Na ce nifa banga al'adata ba, ya ce ban gane ba? Na ce ina da ciki ne fa gashi kuma ban yaye su Hussaini ba. Sai naji ya hau fadin Alhamdulillah, Allah ya amshi addu'ata, don Allah wannan karon ma don Allah twins, na harare shi banfa yaye yarana ba. Ya ce goben nan za a yaye su, na ce tab! Wata ashin da uku fa zasu yi. Ya ce "in basu yi kani ba ba?" Na ce ni dai zanje a bani magani." Ya fita ya ce "Me kika ce?" Nan take ya hada girar sama da ta kasa. "To shike nan kije ki cire" ya fita washe gari na tsi da amai, na sheka shi har na gaji. Nayi ta kuka karshe na kira Rahma na fada mata, ta ce lallai Hafsat samun guri, ni yanzun dakyar na samu Allah ya bani kinsan dai yawon asibitin da nayi. Amma yanzun don Allah yayi maki kyauta shen zaki butulce? To kiyi kokari ki batawa mijinki rai. Sai ta kashe wayarta. Ina kwance jikina zazzabi yaran nata kuka ko wanka ban masu ba. Ranar shine yayi masu wanka ya shrya su, sannan ya zuba su cikin mota da abincin su, sai gidan Dada ya ce mamansu bata da lafiya ina ga ma yaye su za a yi, ta ce me yake damunta? Kai tsaye ya ce ciki ne, tana can tana tana ta kuka ma. Ni dai na kawo su zan kawo kayansu. Dada ta ce to Allah ya bata lafiya. Gidana ya dawo yayi ta lallashi na. "Haba Hafsat, ke da nike kallonki mai ilimi da sanin yakamata? Bai dace kiyi irin wannan tunanin na jahilai ba. Kinsan matsayinki a gurina? Duk yanda kike tunanin matsayinki ya wuce haka a gurina. Kada ki zubar da kimar ki a idona, ina alfahari dake, kuma yayin da kike haifa min 'ya'ya lokacin ne nake kara so da kaunarki." Kunya ta kamani, lallai naso nayi wauta. Yanda mijina ke nuna min baikamata inyi masa haka ba. Ni da na kasance mai bada shawara ba girmana bane in yi haka, don haka sai nace kayi hakuri Mr Cool. Tausayin yaran ne." Ya ce "yanzun ma kayansu zaki hada suna gurin Daada, mu kuma sai muyi rainon wannan ko? Na ce ya zaka kaima Daada aiki, kasan fa barna suke dashi." Ya rike tafin hannu na ya ce "ni suka biyo Dada ta ce lokacin da ina yaro nayi barna, ai kin san kuma ga Ummi ga Rukayya ina kaisu kowacce ta zabi nata, na ce Allah ya raya su." Fadi taji cewa an yaye twins sai ta zargo ko ciki ne dani, don haka hankalinta ya tashi. Har gida sai gata da yake bata taba zuwa ba, tayi ta bin ko ina da kallo, sannan daga bisani muka gaisa. Na ce "Maman Nana yaune kika taba zuwa gidana." Ta ce "to bama zama ko nazo kina gurin aiki, nima haka." Na ce "Amma koda dare?" Ta ce "da dare kowa ya gaji, yanzun dai ba gashi nazo ba." Na ce to na gode" ta ce "can naga su husaini a gidan Daada, wai an yaye su, na ce me ya jawo maki yaye yanzu?" Na ce Abban su ne ya kwashe su ya kaisu. Ta tabe baki lallai sweet heart shine lokacin da zan yaye Nana ya hau yayi ta fada. Na ce to ai kinga ita mace ce, dole ya tausaya mata, ta ce kodai kin sake kunsar wani cikin ne? Na ce to inma hakan ne meye aibu tunda mijina na so? Ta ce kedai fadi gaskiya, kina son kiyi ki cika gida da yara saboda kiyi gado." Ta mike tsaye, "kiyi haihuwarki a sannu dan mu mungaji kudi, so kinga banda matsalar su. Na ce gaskiya ne baki da matsalar kudi, shi yasa na ganki zaune a gida bakya zuwa aiki, sannan suna nan cike da daki a gidanki sai dai ki bude ki diba. Ta ce "inma kina yi min ba'a ne nasan dai na fiki." Ta fita fuuu, na ce "sauka lafiya." Tare muka je asibiti dashi, inda likita ya gwada ni ya tabbatar cikina wata uku. Kuma lfy lau, sai murna gurin mijina. Munje Umara tare harda ita, haka nan aikin hajji lokacin cikina ya tsufa. Mun dawo bada jimawa ba ba haihu, 'yar budurwa mai kyau, tamkar inyi tsalle don murna. Ina son 'yar budurwa, itama anyi sha'ani, don lokacin Abubakar ya kara zama (Don). Yarinya taci sunan Daada, Abubakar yace ya yarda in kana taimako Allah yana taimakonka. Budi ta ko ina, sai yanzun na binciki kudin account dina, lallai kudi wawaye ne, in da zaka tara su zasu taru, don haka na kuduri niyar yin abinda zanyi dasu. Kaduna naje yawon arba'in, na dauki babana na kaishi aka yi masa hoton fita, wato international passport. Lokacin aikin hajji kuma na biya masa. Abubakar ya fara min fada wai yana cikin lissafinshi a bana zai biya masu. Na ce yayi hakuri alkawari na dauka, SANADIN BOKO sai na kaishi makkah. Ya ce "Allah ya biya ki" shi kuwa baba da na fada masa na biya masa kujera da kudin aikina sai ya sa kuka. Ya ce gashi SANADIN BOKON nan da nayi ta tsana zanje daki Allah, inda ban taba zaton zuwa ba. Ki yafe ni Hafsa, tuni na gane boko ba dukka ta ba ce illah, tana da amfani." Ya ci gaba da cewa Hafsa na gane hakan ne ta hanyar taimako da wata likita mace tayi ta mun lokacin da na kwanta a asibiti. In shaa Allah su Ummi zasu yi karatun boko, dama dai na addini wajibi ne, zan bisu da addu'a Allah ya tsare su yasa su sami ilimi mai amfani. Ya raba su da sharrin ko hadarin da ke cikin boko, na ce ameen Baba. Ya ce in da zaki yi adalci Innar ki ya dace da wannan kujerar, don ita ce tasha wuyar iliminki." Na ce "ita ma Abubakar ya bata kujerarta da Yayana Umar, kai nidai na gode Allah da nasha wahala yanzu kuma ina cikin gata. Wata rana na matsawa Abubakar muje katsina ina son in sami labrn yaron dr Hindu da yake munsha zuwa gidan nasu lokacin tana raye. Sai ban sha wahalar gano gidan sosai ba. Cikin sa'a ma yaron an kawo shi hutu. Duk sunyi girma, naji dadin ganin su, na karbi adireshin dinsu na Abuja. Nasha alwashin zuwan sannan nayi masu kyauta mai tsoka. A kwana na biyu na nemo Asabe tayi aure da yaranta biyar. Sai dai gaskiya basu dashi, na taimaka mata sosai. Ta ce min tana son zuwa gurin yarta tana tsoro, na ce zanje mata. Wata rana munje Kano Rahma ce tayi haihuwa ta biyu muka je, daga nan ta tambayi inda zan sami hajiya Mairo, Da dare naje gidan bayan isha'I cikin shiga ta alfarma da dankareriyar motar mijina. Da kima ta marabce ni domin tasan daga ganina taga matar gwaska, falon alfarma ta kaini muka gaisa bayan an cika teburin gabana da kayan shaye shaye. Ta ce ban gane ki ba, na eh baza ki gane ni ba daga Yola nake, ni 'yar uwar Asabe ce wadda ta taba maki aiki kuma take da da tare da danki mai sunanki, shine nazo na ganta." Ta ce Allah sarki sai ta soma kuka, na ce "lfy? Ta ce ai dan tilon dan nawa tuni ya mutu, tunda ya dawo daga kasar waje ba lfy inda yaje karatun boko." Na zaro ido "shima sanadin bokon ya rasa ransa?" Ta ce wallahi yar nan can abokai suka bashi wata kwaya mai karfi yasha. Tunda ya kwanta tashin da bai yi ba kenan sai a kiyama." Na ce tabdijam, yanzu ina ita takwarar taki? Ta daga waya ta kira wata tace jeki ki kira min Ummi, ta dube ni yanzu ita nake gani naji dadi. Kinga da na salwantar da yarinyar nan da nafi haka bakin ciki."yarinyar ta shigo cikin kayan bacci, mai kyau da ita, girmanta bai wuce na shadad ba, na rungume ta ina murna. Na ce Allah ya albarkace ki. Hajiya ta ce ameen, na dubi haji kada a barta ba ilimin addini, domin inda addini, boko bazai batar da bawa ba sai wanda ya batar da kansa. Ta ce haka ne 'yar nan ai naga darasi, in sha Allah yarinyar nan zan mata tarbiya irin ta addini,na ce Allah ya sa. Na kawo kudi na bata na ce ki sayi sweet sannan na amshi lambobin wayar su na ce zan ba mamanta. Nima zan dinga kira muna gaisawa, ta ce don Allah ki kaima uwar tata don ta zo ta ganta. Na ce in shaa Allahu ***************** Rayuwata ta zama abin sha'awa a idon wadanda zuka kyamace ni da. Duk wanda na sani taimakonsa nake yi. Mun sami daukaka ta fannoni da dama, 'yan uwana suna hutawa a dalilina. Abubakar yasa na bar aiki na koma makarantar jami'ar Yola, hatta kishiyar mamana sai da Abubakar ya bata kujera. Zaharaddeen Shomar whatsapp 08168575100 Sabadin BOKO 4-08 Posted by ANaM Dorayi on 05:28 AM, 29-Sep-15 Under: SANADIN BOKO Taimako kuwa a danginsa duk me son wani abu da ya same ni an gama. Fadi ta sakar min ragamar uwar gidanci, kuma na rike, 'yan uwanshi tamkar nawa na rike su. Iyayenshi kuwa tamkar su suka haife ni. Bikin Rukayya ya taso, ta zo ta same ni, ta ce "Aunty dan Allah ki ce ma Hamma kayan kicin dina ina son a sayo min a Dubai." Na ce "an gama" ta ce "Na gode" guri aunty Fadi ta soma zuwa, ta ce duk kayan kicin din kasar nan zan ce sai waje?" Na ce kada ki damu zamu je" Da asuba ni da shi muna kwance cikin bargo ranar asabar ce bashi da aiki, nima ba makaranta. Na ce "Ga biki na zuwa Mr Cool me muka shirya ne? Ya ce to ya za a yi?" Na ce zamu je Dubai sayen kayan kicin" ya ce keda wa?" Tunda kinga aiki yamin yawa yanzun?" Na ce "zamu da Rukayya da Ummi" ya ce "To yaushe?" Na ce zamu shrya" Na yaye baby na gurin Daada na bar su muka tafi Dubai.Mun yo sayayya ta gani ta fada Daada sai shimin albarka take, biki kuwa nice uwar biki, hatta Daada dani take shawara, matan Usman da umar ma suna bina a matsayin matar wan mijinsu. Fadi sai ta koma baya a wajen bikin. Mun kaita Abuja, dan Baffa na abuja ta aura, Ummi kuma Kabir take so kanin Hashim, Umminmu tazo bikin Aliyun su abubakar ya ce yaga mata. Su Daada suka ce koba 'yar uwata ba indan na santa to sukam sun amince. Nidai murmushi nayi tare da godewa Allah. Ina kicin ina hada Zuma ta amfanin kaina Abubakar ya shigo, the only yaufa zamu fita ne. Zuwa ina? na tambaye shi. Hutu na samu na wata daya zmu tafi Abuja, daga nan mu wuce England" Na ce "kana dai sane bani kadai ba ce ko? Ya rke kugu, to nidai dake zani, na ce a'a kayi kuri'a kuma in tafiya ta fado kaina saudiyya zamu. Ya ce "to shike nan, yanzun ya zanyi da maganar kuri'ar? Kayi rubutu a cikin takarda guda daya sauran kuma ba rubutu ka bamu mu zaba, wanda ya dau mai rubutu tafi dashi zaa yi. Kuma kayi tskani da Allah, da ya samu Fadi sai ta ce ita ba inda zata tabar aikinta. Saudiyya muka yada zango, muyi soyayya muje ka'aba munyi addu'a. Nidai yanzu duk abinda nake so a duniya na samu, saura lahira kawai nake rokon Allah ya bamu, kasa Aljanna ita ce makomarmu gaba daya da dukkan musulmi. Ameeen TAMMAT BI-HAMDULLAH! Taku har kullum Halima Abdullahi K/Mashi. ******************************** Alhamdulillahi dukkan gogiya ta tabbata ga Allah madaukakin sarki da ya bamu ikon kammala wannan littafi SANADIN BOKO, tsira da Amincin Allah su kara tabbata ga Shugabamu Annabi Muhammad SAW, Allah yasa mu amfana da darasin da yake ciki. Godiya ta musamman ga marubuciyar wannan littafi Halima Abdullahi K/Mashi Inna godiya ga dunbin mabiyana ta blog,pls kidinga kokarin yin comment ta yanda lallai zanfagimci muna tare Zaharaddeen Shomar whatsapp 08168575100 An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 22 of 22