Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kara yi wa Innarmu yawa, ga Yayana Umar kudin jarabawa yasa makarantar tsaya. Sai dai karen mota ya koma yana yi wa wani mu2m a layinmu,kasuwa-kasuwa.Inna ta zaunar da ni ta ce Hafsatu,kin san yanda zamu yi? Na ce A'a na me? Ta ce, na karatunki, kina so ko? Na ce "Tab so kai ba ki ga su Saliman ajinmu na su suna ta zuwa, ta ce to dagewa za ki yi zan dinga alala da safe ki dan zaga. Sai kuma ki zo ki dauki gyada, na ce Innarmu ni wlh Na gaji da talla,wata rana mu2m ya yi ta yawo a ki sayar ta ce sakarya kin zaga tas za a saye. Asusu zan yi riba ko nawa aka ci sai mu zuba kafin gama zangon farko mun tara kudin da za ki shiga, na ceto,gwangwanayen gyada muka fafe wasu tayi alala.Nan da nan ya kare, Ta dafa min gyada na dauka ta ce maza Hafsatu, Allah ya bada sa'a kin ji, kan lkcn Ismaiyya ki saida. Na ce to, Ta ce bn da wasa fa, don na san ki, na ce to.Wasa kam inadashi,kowa ya sani har na gama primary duk report card dina ba wanda ba a rubuta min na cika wasa ba, a haka kuma nake karatuna. a haka kuma nake karatuna haka kuma na dage da talla na wata ranar litinin ina tafiya nice har baban titi na tsallaka, sai ga wata yarinya tana tallan kwakumeti, tace ke ina kike zuwa? Na ba ko ina yawon talla nake. Tace zomuje (governmeet college) ana cinikin gyada in yan makaranta suka tashi nace, to muje tafiya ce sosai har gidan gwamna ta nuna min. Muna isa agajiye muka zauna gin din bishiyoyi ga yan talla nan kala-kala har da masu gyada babu abin da yafi mun dadi irin yanda naga yara nata wasa saboda yan makaranta basu tashi ba. Masu carafke masu yar gala gala nayi, wasu na tayin ziro-ziro duwatsu na tsinta nima nashiga yin yar carafke, batare da na huta ba koda dalibai suka taso nan kowa yasaki wasa suka shiga saida kayansu, ni ko ban damu ba na cigaba da wasa na sai da takowa ta kare sanan aka shiga siyan nawa. Washe gari nacewa innarmu a kara mai makon mudu hudu a dafa biyar. Yau ma wasa na dora haka nan sai da ta kowa ta kare don su suna zaune, a gaban kayan su niko ina can ina wasa na. Zuwa yanzu na saba da dabar hanya zuwa (government college) wata rana ina zaune kan duntsen da na dasa a matsayin abin zama na, gaban tirena hannuna zarene ina ta wasa dashi na hada injin nikan barira inata yar waka ta. Sai naji magana kusa dani ance ke gyadarki ba ta saida wa bace? Ba tare da na dubeshi ba nace ta saidawa ce mana,ya ce, "Sa min daya a leda sarkin wasa." Na ce, "Zaba." Ya ce, "Zabar min." Sai lokacin na kalle shi na dan kara zare ido saboda kyawun shi. Haka nan ba Uniform a jikin shi, kenan ba dan Makaranta ba ne. Na mika mishi ya ciro wani farin kyalle ya shinfida akan jijiyar bishiya ya zauna ya soma cin gyadar. Ni kam kallonshi nike a raina ina cewa, "Dama 'yan gayu suna cin gyada?" Ya dube ni, "Ki yi wasanki mana kada ki sa na kware." Na dauke idona daga bisani na tashi, na soma 'yar gala- gala ta. Yana lura da yadda kowa ke tsaye kan kayansa banda ni, da ya mi'ke zaya tafi ya ce, "To sarkin wasa ga kudinki." Sabuwar naira biyar ya bani a mike, a rayuwa ta babu abinda ke burgeni irin sabon kudi, na ce, "Amma na gode, kalleta kar-kar bazan kashe ta ba." Ya ce, "Mai zaki yi da ita?" Na ce, "Ajiyewa zanyi ba zan sashi cikin asusu ba bare har na lankwasa ta." Murmushi yayi sannan ya ce na bashi daya. Ba bashi ya ci rabi ya bar saura, na ce, "Ji fa baka cinye ba." Ya ce, "Na koshi." Da zai tafi ya kuma bani sabuwar naira goma wai in bashi canji na ce, "Wai don Allah kai kuwa a ina kake samun sababbin kudi?" Bai amsa ba yana ta kallona. Na ciro tsohuwar biyar na mika mishi. Ya girgiza kai, "Ba na amfani da Tsohon kudi." Na ce, "Saboda mene?" Bai amsa ba ya ce, "Gobe zan amshi gyada." Na ce, "Toh"Ku san kwana 2 ban ga mu2min ba, sai ranar 3. Yau ma shigar shi ta 'yan gayu kamar kullum. Ya amshi gyada zai tafi ya kuma bani sabuwar 10. Na ce a, ka manta ne kana bi na canji? Ya ce haka ne, to rike wannan don ni in na ciro kudi bana maida su. Na ce ko? Tab, amma dai sun maka yawa ne ko? Ya dube ni ba alamar wasa, ya ce "Mu ne ai muke kera su. Na zaro ido ina kallon shi, cikin matukar mmk "Kana nufin ku ke buga kudi? Ya sake dubana, kwarai kuwa, na Maida hankalina duk a gare shi. Ka ce kana da su lodi? Ya saka hannu cikin aljihu shi ya ciro sabababn dal 'yan naira ashirin da goma-goma na zaro idanu. Tabbas yanzun na yarda na ce kai ko kaji dadinka, ina ma ni ce. Ya ce da me za ki siya? Na ce na farko zan biya kudin makarantana, kuma na dinga sai mana kayan dadi da su nama da mota, su mashin.Kai komai sai na sai mana. Ban lura ba, ashe shi kam dariya na ba shi, ya ce to ai ni kin ga duk na siya abubuwan da ki ka ce, na yarda kam, shi yasa gaka nan dan gayu da kai, ka ta6a zuwa kasar waje? Ya sake darawa, sannan ya ce eh, da yawa ma. Ya tafi ina ta kallon shi. Sa'a da Zaituna wadanda muke tafiya tare dasu, da na basu labarin dan gayun nan na ce ashe sune suka buga kudi kin yarda suka yi. Suka ce to in shi ne me zai kawo shi nan yana karyawa? Na ce shi ne ya fadamuku karyawa yake yi? Suka ce min tun yaushe suka san shi a nan Makarantar. Na ce ko dai yana koyarwa ni na yarda su ke buga kudi, Ga sabbin kudi nan dami a gunsa, Lura da su Sa'a suka yu cewa ba zan yarda da su ba sai suka bar ni. Sau dai suka ce min ni wawiya ce, sai ka ce bn yi zaman aji ba, sunan na gama aji 6 bn san komai ba, na ce naji din. Su Innarmu a da Baba na kuke ina ba su labarin dan gayu mai buga kudi, amma wai sai suka ce zolayata yake yi, nayi duk wani kokari na wai don su yarda da ni cewa gaske ne,amma sun ki. Sai dai na dauki alwashin zan masa tambayoyin da zai gamsar da su. washegari jumma‘a ba mu cika jimawa ba, saboda ana sallah juma‘a a masallacin da ke kallon makarantar amma kin bin su Sa‘a nayi na fake da cewa sai gyada ta ta kare. In tashi yan makaranta tuni sun watse ina ina zaune gaban gyada yar ragowa ce ma, sai kalke kakle nake. Can na hangoshi zai shiga makarantar, ya sanye da wani ubansun yadi fari kar hatta takalminshi da hular kanshi. Duk da yau ce na soma ganin shi da manyan kaya ban kasa ganeshi ba. Da gudu na bishi ina cewa tsaya tsaya ban san sunan shi ba bare na kira. Shiko bai san dashi nake ba a haka mukayi nisa cikin makaran tar sai dai wani ya lura shi nake bi sai ya tai maka ya tsai da mun shi. Na lura yaji mama kin ganina yace, sarkin wasa ina zaki haka? Na tsaya ina haki saboda gudun da nasha yace sannu na ce yauwa, dama kai nake ta jira zan tam bayeka ne. Yace na me? Nace wai dan Allah da takarda kuke yin kudi? Yayi dariya har hakoranshi farare suka fito yace eh, da takarda ne to in na baka zaka iya yi min saboda mutane sun kiyarda ne dani in nace naga masu buga kudi sai ace karya ne zolayata kake yi. Yace zanyi maki in kina so nace innaso kai, to da wace irin takarda kuke yi? Yace ta rubutu nace gobe zan duba jaka ta da in dauko. Yace ba ayi fa da tsohon littafi ko kina son tsohon kudi ne? Nace a a taf na fison sabo yace to shike nan ki kawo sabo nawa za abuga maki yawan kudin? Nace zaka iya min dubu malala gashin tunkiya? Ga mamaki na sai naga yana dariya har da rike ciki nima na soma dariyar ya numfasa ya ce,in ban da abin ki sarkin wasa wane ne ya san yawan malala gashin tinkiya, Na ce to ko dai nawa ne ina so yanda dai ishe ni na gama karatuna. Ya ce,wai dama nan kin yi karatu? Na dube shi, ba na fada maka ba cewa na gama primary? ya ce ban ji ba lokacin da ki ka fada,yanzun JS1 za ki shiga? "Eh tallar da nake ai kudin rijista muke nema, kaga in ka bugo min kudin na daina talla, ina gama secondry har ta gaba in je in fara aiki. Ya ce "Wane aiki ki ke son yi,? Ina nufin me ki ke son ki zama? na daga kaina sama ina nazarin ya ma ake ce musu? Ya ce ba ki san me ki ke so ki zama ba? Na ce, "Ya ma mutanen da ke yin labarai a Talabijin ko Rediyo? Ya ce, " Media ki ke so? na ce yawwa, haka zan zama 'yar media,yayi murmushi, to ni zan wuce, ina kayanki? Sai lokacn na tuna da tirena da kudina cikin ledar gwangwani, na ce to sai gobe. Na tafi ina waiwayanshi, ina cewa kai,wannan mu2min dan gayu ne,ga kamshin turare yana yi. Ranar Litinin tsawo naga ta min,yau kam d murna na iso,na nutsu ban yi wasa ba,saboda wata zuciyar da ke ce min in ya ki zuwa fa, ga shi na zo da sabon littafina, ba karamin damuwa nayi ba da na ga lkcn tafiyarmu yayi ban gan shi ba. Ina kulle gwangwanaye sai gashi, na ce hr na cire rai, ya ce ai zan zo, na ciro littafi na ba shi, tare da cewa wannan takardar ta isa? Ya ce eh, na ce na gode, na mika mishi gyada tare da cewa na rage mishi ne. Ya ce ya gode ya tafi. kai, kuruci dangin hauka, nifa tsakanina da Allah na yarda suke buga kudi. Daga ranar ban kuma ganin shi ba, Kusan sati 2 hr na soma tunanin ya gudune da kudina kun ji shirme. Wata ranar Jumma'a ranar za a yi wa dalibai hutu hr cikin Makaranta muka shiga muna ta ciniki,mun saida mun fito sai na hango shi tsaye gurin zaman mu. Da sauri na isa gurin shi, me bugakudi...... Zaharaddeen shomar whatsapp 08168575100 Sanadin Boko 1-04 Posted by ANaM Dorayi on 09:56 AM, 10-Sep-15 Under: SANADIN BOKO @* NA Maryam Abdullahi K/Mashi "Da sauri na isa gurin shi, me buga kudi ina ka tafi na daina ganinka? Ya ce aikin kudin ki ne ya 6oye ni, na ce Allahu! Har ina cewa ka gudu. Ya yi dry, na gudu da kudin ki ki ke zato Na ce eh, nima ina dry. Ya ce kai kina da bn dry, to ga kudinki,amma muje gidan ku na bawa iyayenki kada wani ya bi ki ya kwace. Cikin murna na ce to daga nan ma in sun gan ka sun fi yarda. Na kama hanya a kafa ya ce ga mota can zo muje, in kin san hanya direbn mu sai ya kai mu, ba tare da wata shakka ba na ce to. Sam na manta da su Sa'a, sai da zamu shiga motar naji muryarsu,suna cewa ke Hafsatu ki ka sani ko dan yankan kai ne? Na dube shi, shima ya ji amma sai yayi tamkar bai ji ba, na ce ba wani dan yankan kai na shiga motar da dan tirena, shima ya shiga ya ce kawarki fa,shawara suka baki nace tame? Yace kin san ni ko dan yankan kai ne? Duk da gabana ya fadi amma sai na dake nace, bakayi kama dasu ba yace suna da kama ne? Nace oho amma kai bashi bane yace, dama sunanki hafsatu? Nace eh abakin su sa‘a kaji ko da suka kirani dazu ko? Yace eh nace yan bakin ciki ne, dan fa nace masu kana buga kudi sai suka ce mun karya ne, kai malamin makaran tane. Yace gaske ne ni malamin makaranta ne, amma daga yau na gama nace, duk da kudin da kuke bugawa basu ishe ka ba sai kayi koyarwa? Yayi dariya yace bautar kasa aka turoni daga jahar mu. Nace bautar kasa kuma? Yace kema watarana zakiyi in dai kikayi karatun da kike fadi, gwamnati zakiyi wa aiki na wata tara ko shekara. Ban gane nufinshi ba amma nace Allah yasa naga lokacin. Da gudu na shiga cikin gidan mu ina cewa inna fito kiga mai buga kudi ya bugo min inna ta saka hijab ta fito tana cewa ni ban gane wanan shirmen naki ba, ina mai buga kudin? Wannan yarinya da wautar tsiya kike inna tayi turus lokacin da tayi arba da rantsatsiyar motar tace hafsatu aina kika jajibo wadan nan...? Cak! Maganar ta tsaya lokacin da saurayin ya bude motar ya fito kyawunshi yasa inna tunain ko aljani na janyo, ta soma karanta (ayatul kursiyu) zata juya gida na rike mata hannu. Inna dan Allah ki tsaya mana zo muje gurin su tace a a hafsatu muje ciki bana tsamanin wadannan bil‘adama ne nifa nasan banda aljan ke ina kika isa kiga mai buga kudi, sai dai in jabun kudi. Saurayin yatako har gaban inna ya dan rusuna ya gaishe ta, ta amsa tana dan dari dari, nace to wanan ce inna ta sai ka bata kudina inna tayi ta maza tace samari daga ina? Ni fa ban fahimci surkulen da yarinyar nan take yi min ba? Yayi mur mushi ya dube ni jeki kawo min ruwa nasha, da gudu nayi ciki ban saurari inna ba da takecewa in dibi na baba yafi sanyi ina tafiya ya dubi inna yace mama zolayarta nake yi, ni dan bautar kasa ne an turo ni daga Adamawa state, ina koyarwa a makaranantar da take zuwa talla. Yawan wasanta ke burgeni har na shiga sabagarta, sai kuma na fiskanci cewa tana son karatu amma rashin hali ya hana hakan. Dan ta fada mun tana talla ne dan kawai ta tara kudin makaranta. To ni nazo ne in ba damuwa zan taimaka mata don ni daga yau in sha Allahu na bar kaduna kenan, don na gama abin da ya kawo ni, dai dai nan na taho da ruwa na ce masa gashi. Inna tace mika mashi yace a a dama basha zanyi ba bakiga na sha ruwa a mota ba? Nace eh yace to maida. Yaci gaba da cewa dama nawa ne kudin nata? Tace ni ban tambayi nata ba amma lokacin na wanta inaga dubu uku muka kashe? Ina ga ba zai wuce hakan ba. Ya ciro yan daurin nera goma gama guda uku sababbi fil ya mika mata ga wanan mama dan Allah ku biya mata kudin makaranta, ku cika burinta har tazama abin alfahari nan gaba. Allah ne kadai ya san al‘ummar da zasu anfaneta. Innarmu jiki yana bari ta amshi kudi tana ta zubo mashi godiya ma, sai daka tsale nake tamkar yarinya karama, ina cewa shi kenan na huta talla. Innarmu ta harareni tana cewa to kiyi mashi godiya mana, nace na gode yayi murmushi ya tafi yana daga mun hannu nima haka. Sai dai kash nayi mantuwa ban tambayi sunan shi ba, a lokacin ban damu in san sunan shi ba muka nufi cikin gida da murna innarmu bata da rufi, don haka a tsakar gida ta fada musu cewa wani bawan Allah ya taimaka min da kudin makaranta. Wasu suka taya mu murna ciki harda babarmu, wasu kuwa sun nuna bakin cikinsu a fili don Ade ina bayi naji tana cewa, maman abba yau kinji matar nan mu zata rainamawa hankali ta dai tura yarinyar ta maula. Maman abba tace ai shegen son kudi irin na maman hafsatu ya isa, ace mata sai rashin godiya Allah duk fa kokarin mujinta ta raina. Daga can asabe ta sako baki shi wannan mujin nata ai tuni ta gama dashi katsinawa kuma da shegen asiri? Dubi fa fada irin na mutumin nan sai da tasha karfin shi ga kishiya kuma sai yan da akayi da ita Ade ta ce, ayi dai mu gani, kina nan yarinyar zata janyo mata abin kunya, Maman Abba ta ce ta dage sai yarinya tayi boko, za su ga boko ai. Na fito cikin takaici ina kallon su, sai nan da nan suka canza mgn. Asabe ce suna ta zagin ki,wai kina asiri ke Bakatsina,wai zan ja miki abin kunya. Inna tana da fada, balle in an ta6o ta, ta fita da sauri Yayana Umar ya hau ni da fada,wai don ubana ni mahaukaciya ce da zan fada mata, na ce ka ji gulmar da suke yi ne? Hayaniyarsu ce ta fito da mu, Umar ya je yana cewa, Inna ta bari ta dawo daki, nan dai haka gidan kan rikice wani lkcn. Musamman in ana fada kan yara, ko gulma. Innarmu tana da fada kowa a gidan yana shakkar ta6o ta. Bayan komai ya lafa, muna daki ta ce "Hafsatu kin dai ji da kunanki, ina so ki baiwa mara da kunya, ki kare min mutuncinki, kiyi karatunki ki zama abn sha'awa da kwatance na ce to Inna. Cikin kwazo na soma karatuna, kudin dan gayu mai buha kudi ya bugo min sun taimaka min kwarai. Inna tayi musu kyakykyawan adani,sun ishe ni har zuwa lkcn da na gama JS 3, lkcn shekaruna 14 girma ya soma zuwa min 'yan alamu sun bayyana. Na kan ji mutane suna cewa, wai ban cika kyau a fuska ba, sai dai jiki. Yawan fadin ina da diri shi ne ya sani jin cewa ni mace ce musamman in nayi kwalliya. Wata safiyar Jumma' naje fitsari sai naga jini, cikin fargaba nazo har da hawaye nake fada wa Inna. Ta ce, Hafsatu girma ne ya kama ki yau nawa ga watan bature? Na ce 7. Ta ce to duk 7 ga wata za ki ga wannan jinin. Ta iya yiwuwa yazo kafin 7, ko bayan 7, amma duk wata dai za ki gan shi. In kuma ba ki gan shi ba hakan na nufin kina da ciki. "Na zaro ido ta ce ai ba a samun ciki haka sai in kin kasance me wasan banza da MazaNa sauke ajiyan zuciya,don nasan bana yi. Na ce ni dama ba ruwana da maza, ta ce na sani, amma ki kara.sannan ki kara sa tsoron Allahn ki cikin zcyrki. Daga yau din nan an bude miki fayil dinki, duk aikin alkairi ki ko akasin haka za a rubuta miki, don haka sai ki kula, ki kuma san me ki ke ciki. Tun daga wannan lkcn nasa ma raina tsoron maza, nake kuma duba duk wani aiki da zan yi zunubi zai ja min ko lada. Marubuciyar tace'Yan uwa mata zan dan mana wani tuni nan gurin, mu nutsur da 'ya'yanmu muyi musu bayani mai kyau tare da nutsa tsoron Allah cikn zukatansu, lkcn da suka samy kan su a irin wannan yanayin na balaga.....Allah yayimana jagora Ba zan manta da Jumma'ar ba, misalin 4 da mintina na yamma gari yayi sanyi La'asar, nayi kwalliyata da riga da wandon pakistan da Inna ta sai min a gurin wata mai gwanjo. Kore ne kalar lemun tsami da gyalanshi, Sakina kanwata yarinyar Baba kishiyar Innarmu ta ce " Yaya Hafsatu zan biki." Na ce, zo muje gidan kanwar Innarmu zan je Hayin Malam Bello na kai mata kudin dashin sabulu da suke yi. Ko can gidan matan gidan suna ta yaba yanda kayan suka yi min kyau.Dai-dai kan layin Biliya wasu matasan samari suna tsaye jikin mashin, kallo daya na musu na dauke kaina ban kuma kawo komai a raina game da su ba. Sai naji takun tafiya, ana cewa 'yanmata ji mana,maza sun sha yi min haka bana tsayawa, don Innarmu ta fada min karatu basa haduwa da soyayya, kada na sake na kula kowa. Ya zagayo ta gabana Beby saurare ni mana. Na' kalli fuskarshi,sai zcyta ta buga, ina son mu2m mai kyau, daga ganin shi dan gidan 'yan gayu ne. Na harde hannuwana a kirjina, ya sake dubana daga sama kuwa gsa kasa, "Wow! Ya sunanki?" na ce "Hafsatu." Ya ce "Nice name, Hafsy ina ne gidanku?" Kawai sai na samu kaina da yi masa kwantance, can kasa muke Abuja Road, layi na shida marar kwalta, kana zuwa layin ka ce ina ne gidan yawa za a nuna maka. Ya dan yi shiru don ya fahamice a geto take amma sai yace zan zo anjima ko gobe zan samu ganinki? Nace eh yace to sai kin ganni na tafi ina wai wayanshi sakina tace yaya hafsat mijinki ne? Cikin yar dariya nace eh mijinane wasa ne ya ruda ni na kasa sukuni, tare da boyiwa innarmu don kada ta hanani fita, sai dai har tara banji ance ana kiran hafsa ba,har fita nayi gurin bakin titi ina tunanin wai ko yazo bai gane layin ba na dawo daf da zan shiga gida na ganshi tsaye kofar gidan mu. Wani sanyi naji acikin zuciyata, sai na soma tunanin zan jene na ce mashi gani ko ko ce mashi zanyi ni kake nema? Sai na yanke shawarar na bi ta gabanshi, har na daga labulen buhun da yake kofar gidadanmu zan shiga, sai naji yace hafsy sai na tsaya tare da sauke a jiyar zuciya, sannan na wai wayo na tako cikin irin tafiyar da ban taba sanin na iyata ba. Duk da yake dare ne a kwai kwan lantarki a kofar gidan, yace nafi minti 5 ina jiranki nace ina yini? Yace lfy da farko dai sunana munnir jafar dalibi ne a (A B U) zariya ina shekara ta 2. Sanan muna zaune ne a nan makarfi road son munnir ya kara shiga ta, don a rayuwa ta inaso in auri miji dan boko nace ni kuma na gama js3, yace me ya hanaki cigaba? yanayin garin ne. Haka muka ta fira sam bansan dare yayi ba har 10 ta gota ba sai da naji karan raidiyon baban mu ya nufo gida. Ya tsaya tare da cewa wacece nan? Ke hafsatu me kikeyi haryanzu? Na dubi munir nace ga baba na. Ya cire hular kansa hana sallah yace ina yini baba? Ya dubeshi lfy lau zo ki shige muje, nace to sai anjuma yace zan zo gobe nace to. Tun kafin mushiga daki baba yake min fada tare da tambayata wanene wannan yaron ya dame kugu? Nace dazum ne muka hadu dashi. Hayaniyar shi ne ta tashi inna daga dan baccin da ta soma, tana tam bayarshi lfy malam kake fada da tsohon daran? Yace amma dai ke sakaryar uwace, 10 ta wuce yarinyarki tana can tana zance da wani kato ke kuma kin hamgame baki kina bacci Inna tace hafstu na can tayi baci tuni dakin babarsu, ba ita kagani ba ita da bata fita zance ma yace to ga tanan ma bare ki karyata ni. Inna tace hafsa zance kika fita? Ya mukayi da ke? Baba yace ni dai tashi ya turo mun iyayensa dama ni burina in aurar da ita. Inma shi bayi zaiyi ba akwai mutane da dama sun min magana. Inna tace je ki kwanta itama ta maida kai ta kwanta alamun zancen baba bai shigeta ba. Da safe ta tsareni da son jin wajen wa na fita? Nace inna wlh jiya ne fa da kika aikeni ya ganni shine yazo. Tace amma nace maki ki fita hanyar samari ko? Kin san babanki matsawar zaki rinka tsayawa zance kina son karatun nan zaki barshi ko nace inna naga shi wannan yana son karatun, don su gidansu yan boko ne. Maman shi da baban shi duka aikin gwamnati sukeyi yace min jami‘a yake yi (A B U) zariya tace to ni dai banaso kurinka tsayawa nace yama ce zai bani kudi nacigaba da karatu na. Inna tace to indai ko haka ne sai dai kitafi makarantar kwana, saboda kin san babanku sarai. Koda munnir yazo washegari, haka na zauna na fada mashi komai dangane da ma haifina game da kin boko. Yace taf kice cutarki zaiyi? Tun kina karama zai kasheki da aure ai gaskiyar innarki ne kada ki yarda. Nace kudine matsalar mu sai dai in shiga ta kwana yace haka ne, yace zan baki kudi bari dad dinmu zai bani kudi in yadawo tafiya. Nayi ta masa godiya yace a a shidai abinda zanyi mishi kada in saurari kowa kuma na saki jikina dashi, nace kada yaji komai cikin sati 1 na gama yarda munir na sona, nima kara sonsa nake duk zuwa yakan zo min da wani abu, turare ko dan zobe ko dan wani abun kwalama. Bana manta ranar lahadin da yazo min sallama zai koma makaranta ya kuma bani kudi naira dubu 20 har kuka nayi mashi dan bana so rabuwa dashi. Ranar shida abokin sa sukazo wai shi faisal, kawai sai naji munnir ya rumgume ni, wani abu naji tun daga tafin kafata har tsakiyar kaina,shiko sai cewa yake inyi shuru in daina kuka hannun shi kuma na zaga sassan jiki na, fadan inna ya fado min cikin rai inda take cewa. In kula da kaina wasan banza da namiji zai iya sawa in sami ciki, nayi sauri na janye jiki na daga gareshi, yasa hannu yana share min hawaye muka yi ban kwana na shiga gida. Suna tafiya faisal yace munir dagaske kana son yarinyar an? Munir yace da dai nazo na dan kwashi rabo nane, sai kuma na gane yariyar ba yar hannu bace. Sannan kuma nasamu kaina da sonta na gaske faisal yace ka dai san dadinka ba zai barka ka auri yar geto ba ko? Yace kai nif zan zaba da kaina ba zan yarda ace min naje ga yar wani ba. Nikam ina shiga gida muka soma murna da inna, nan muka shiga tsara yanda zamuyi wa baba bayanin munir. Washegari inajin inna tana cewa baba wai kananta da yayansu sunce ta kaini zasu nemmar min makarantar kwana. Baba yace a a shifa bai yarda ba, tace yayi

Chapter 3 of 22