Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ga ku gata nan. Jami'ar da aka ce 'ya'ya suna lalacewa? Yarinyar ta fada a gabanki sama da shekaru amma baki damu ba. To magana ta ni uku ce, bata kai hudu ba. Na farko duk abin da ya faru da ita SANADIN BOKO ba ruwana, zai shafe ki ne da ita. Na biyu ba zan yafe hakkina da ku ka tauye ba, matsayina na Ubanta, kuka hana ni in sauke nauyin da Allah Ya dora min. Na uku kuma ta nemi Ubanta ke kuma ki nemi mijinki, duk ranar da wata ashsha ta samu SANADIN BOKO. Ba innarmu ba, ni kaina zancen ya girgiza ni. Baba kishiyar Innarmu ta fito daga uwar dakinta, ta zo kusa dani ta zauna. Tasa hannu ta dan dake ni, "Tashi Hafsatu. Na tashi zaune jikina sharkaf da zufa, ta ce "Nasan kin ji duk zancen da Malam yake yi ko? Na ce, "Eh. Muryar Innarmu ta katse ni, ta ce, "Insha Allahu Malam karatun Hafsa zai zama alkhairi garemu da kai gaba daya. Ya ce "Ruwanku. Cikinsu ba wanda ya sake magana. Babah ta ce, " Hafsatu ki bar Babanki yayi iko da ke, ki ce ma Innarku kin fasa karatu. Kalamanshi ba baki yayi miki ba, amma ina ji miki tsoron alhakinshi kada ya kama ki. Na ce, "Babah wanda zan aura karatu yake yi, ba yanzu zai yi aure ba, kuma Iyayenshi ba za su yarda ya auri mara ilimi ba. Babah ta ce, "Sai shi? Akwai masu sonki da yawa, kuma sun ma Babanki magana. Nayi shiru ina nazari, nasan Babah gaskiya ta fada min, amma ya zan yi da son Munnir? Na dube ta, "Babah ki duba irin hidimar da Munnir yake yi da ni, ba zan mishi adalci ba in na ce ba zan jirashi ba. Ta ce, "To yanda ki ka gani, amma karatun nan tunda ba na Muhammadiyya ba ne, banga dalilin naci ba. Kuma ni sai in ga yaron nan tamkar yaudararki yake yi. Anya auranki zai yi? Na ce, "Allah Babah aurena zai yi, ki dubi dadewar mu da hidimar da yake min. Ta ce, "Ba ta a nan, amma fa shawara ce." Na koma na kwanta, ita kuma ta mike ta nufi cikin dakinta. Zancen Babah ya taba zuciyata, illah magana daya da ban kama ba, wai tana ga Munnir ba zai aure ni ba. Nayi guntun murmushi, me zai sa shi ya yi ta dawainiya da ni ba zai aure ni ba? Yanda na raba dare ban yi bacci ba, na tabbata Mahaifana biyu ma haka ne, duk SANADIN BOKO. Da safe ina zaune da kofin koko sai juya shi nake yi na kasa sha, Innarmu ma sukuku take. Lokacin da ta zauna tana shafa ma gwangwanayan alalarta manja, na ce "Inna ko dai zamu hakura da batun bokon nan ne? Ta dube ni, "Saboda me? Na sunkuyar da kai na ce, "Naji duk yadda ku ka yi da Baba jiya. Tayi shiru, can ta ce, "Abu daya zuwa biyu nike so ki min. Na zuba mata ido, na farko ki tsaremin kanki da mutuncinki, kada ki banzantar da kanki, na biyu kiyi abin da ya kai ki makaranta, wato karatunki wanda nike fata ya zama sanadin alkhairi. Ta haka ne za ki wanke wa Mahaifinki tsanar da ya yi wa boko, har kannanki suma su samu dama suyi cikin kwanciyar hankali. Yayanki da bai samu damar ci gaba ba yana jin haushi. Ke tunda kin samu dama kada ki bani kunya. Na hada ki da Allah, ki rufamin asiri. Tausayin Innarmu ya cika ni, na ce, "Insha Allahu zan kula sosai, kuma zan fidda ki kunya, SANADIN BOKOn nan kowa zai huta, Baba zai yi alfahari da ni. Munnir yayi tsayin daka har na zama daliba a jami'ar Bayero da ke Kano, har lokacin da zan tafi Innarmu bata daina rokona in rufa mata asiri in lura da kaina ba. Nan na tafi na barta da surutun 'yan gidanmu, da 'yan unguwarmu. Wasu suce tana so ne ta auri mai kudi, shi yasa muka nace boko, wasu su ce dan kyan nawa bai fi cikin cokali ba, amma mun kuke sai nayi boko. Wasu su ce dan-dan masu hali ke sona, duk dai ta toshe kunne watan kwaram daya ne. Baba har fushi yayi da ita, sun jima kafin ya soma amsa gaisuwarta. Karin haushi yakai kararta ga danginta, maimakon su bata rashin gaskiya suyi mata fada, sai suka ba shi hakuri suka ce wai karatun yana da amfani. Ya ce, shi ba ya ce babu amfani ba ne, a'a tayi shi can gidan mijinta. Aure shi ne sama da karatun ta, sai suka ce ya yi hakuri 'yan kwanaki ne zata gama, don haka sai ya dawo ya zura mana ido ******* ********** ********** *********** ********* Jami'a wata rayuwa ce da ta sha bamban da secondary, banga laifin Baba ba yanzun don ya kyamaci boko, sai dai na sha alwashin kula da kaina, don haka na tsare gida bani da kawa ko aboki. Duk da Munnir na shirin tafiya Dubai karatu don kammala Masters dinshi, haka bai hana shi zuwa duk bayan sati biyu ba. Tafiyar tashi bata yuwu ba har muka samu hutun first semester, sati biyu dai za mu yi amma naji dadi, sai dai wannan hutun ne hutun da ba zan taba mantawa dashi ba a rayuwata. (Kuma shi ne dalilin rubuta labari na "SANADIN BOKO" . Sauran kwana biyar na koma Makaranta duk da inata dokin zuwa gida amma zaman gidan bai mun dadi ba, ko gaisuwata Baba baya amsawa har ta kai da naji muryarshi zan boye. Bello Abokin Munnir shi yayi sallama da ni, na sha mamaki don bai taba zuwa shi daya ba. Ya ce, Munnir ya aiko shi muje tare bashi da lafiya. A rude na je na fadawa Inna, ta ce, "Yana asibiti ne?" Duk da ban sani ba sai na ce mata, "Eh." A zatona yana asibiti ne, sai da yaja mota sannan nace, "Wane asibiti ne." Sai ya ce, "Ai yana gida." Har gefen su Munnir Bello ya raka ni, ina shiga sai yace mun, "Toh yana ciki ni na wuce ki fada masa don ya dameni in kawo ki har ciki. Na ce, "Toh!" Na nufi ciki da tafiya cikin dari-dari. Tsakiyar falon na tsaya na zabga Sallama, ga mamakina sai ga Munnir ya fito daga kitchen sanye da gajeren wando da vest duka farare tas, hannunshi dauke da ruwa (C way) yana sha. Na ce, "Ah! Ka samu sauki ne?" Ya ce, "Eh, A'a." Ya nuna min kujera, "Zauna." Na zauna ina kallon shi tare da son jin karin bayani, "Ban gane eh, a'a ba?" Ya tsugunna a gabana, "Ciwon ya dade yana ci na, ga shi zan iya tafiya Makaranta cikin kowane lokaci ba tare da na samu maganin ba." Na ce, "Wane irin ciwo ne?" Ba tare da shakka ki tunani ba ya ce, "Ciwon sha'awarki....." Gabana ya fadi, na mike tsaye da sauri. Shima ya mike, "Hafsat kin san ina son ki, wallahi na gaji da sha'awarki. Ki so ni kamar yanda nike son ki." Na ce, "Munnir ka san ina son ka." Ya ce, "To ki nuna min." Na ce, "Ban gane ba? Sau nawa nake cwa ina son ka? Ka sani." Ya ja tsaki, "Kin dai gane nufi na, ina son yau daya ki taimaka ki nuna kaunarki gare ni." Na ce, "A'a ba zan iya ba, domin haramun ne." Ya ce, "Ni fa zan aure ki!" Na soma tafiya don fita ina cewa, "Sai ka jira sai ka....." Maganata ta tsaya sakamakon murda kofar da naji nayi ta a rufe gam. Na dube shi yana murmushi ya ce, "Ki bani hadin kai don yau ta karfin tsiya ma zan iya biyan bukata ta." Jikina ya soma bari na ce, "Wallahi Munnir zan maka ihu, ka bude min kofa." Ya zauna, "Ko kin yi ihu ba wanda za ya ji ki. Mom bata nan tana gurin aiki, Dad ma haka, su Nana da Suhaila suna Makaranta." Na zube gwiwoyina biyu a rude ina cewa, "Ka min rai kada ka sa ni cikin matsala, don Allah." Na soma kuka. Ya ce, "Nima ki taimake ni na gaji, wanene za ya gane me muka yi?" Na ce, "Allah ya sani, na tabbata zai kama mu." Amma da yake Shaidan ya hura ma Munnir kaho sam ya ki karban uzirina. Muka yi ta zaga falon har na fada wani daki, sai dai kafin na rufo tuni ya banko, mun yi damben bala'i dashi kafin ya samu nasarar aikata mummunan nufinshi a kaina, bayan ya bi duk wata gaba ta jikina ya bugeta, fuskata kuwa ta sha mari sai na ga kamar ba Munnir dina ba. Kuka iya kuka na yi shi, na mike ina gyara daurin zanina, da kyar nake tafiya na fito falon, ya ce, "Duk kin sa mun wahala, a yanzu wa zau sani in ba kin fada ba?" Na ce, "Bude min kofa kawai ni dai na tafi." Ya nufo ni, "Come on kiyi wanka sai na kai ki." Ban san lokacin dana daka mishi tsawa ba, "Budeni mana" Sabon kuka ya kwace min na ce, "Allah ya isa tsakani na da kai, Insha Allahu sai Allah ya saka min." Ya tashi ya bude tare da cewa, "Sai na zo." Ban kulashi ba na fita, dole na share hawayena saboda Maigadinsu, na fita ko ina a jikina ciwo ya ke. A haka na kai gida, kallo daya Inna ta min tace, "Lafiya?" Jikina ya soma bari, ta ce, "Ba dai jikin nashi ba? Na ga duk kin rude fuska a kumbure." Na ce, "Umm jikin ne." Ta ce, "To shine na kuka? ki masa addu'a." Na ce, "To." Na nufi ciki. Ta ce, "Hafsa zo nan, menene wannan a zaninki?"mummunar faduwar gaba ta ziyarce ni, zufa kuma ta shiga keto min, amma sai na yi saurin cewa, "Fashin Sallah ne." Duk da ban juyo ba kuma ban san mai ta gani jikin zanin ba. A gani na in muka hada ido zata gane, ta ce, "Haka kika ratso titi? Ga ruwa da na daura chan kan wuta na tuwo ki diba ki maida min sai ki dauraye jikinki." Cikin bayi ina wanka ina kuka tausayin Innarmu ya cika zuciyata, na karya alkawarin da na daukar mata, Allah ya isa Munnir. Cikin kwanakin da suka biyo baya ko Munnir ya zo bana fita, ranar da zan koma Makaranta har goman safe ina kwance a tsakar daki, Innarmu ta ce, "Ke da naji kina cewa sammako zaki yi? Har yanzun kin kasa tashi?" Na ja tsaki, yanzun na soma tsanar boko bani da daman in tona asirina... Yaron gidanmu ya shigo ya ce, "Hafsa wai in kin shirya wani mai mota ya ce ki fito yana can saman layi." Na ja tsaki, "Ka ce masa ya tafi na san hanya." Innarmu ta ce ma yaron, "Kai zo, je kace tana zuwa." Yana fita ta fara min fada wai bani da hankali, ta lura kullum zai kirani in 'ki fita, haka ake yi? In ma sabani kuka samu ba sai kiyi hakuri ba tunda shi har ya zo? Na kalli Innarmu a zuciya na ce, "Da kin san abinda ya min sai kin fini tsanar shi." Ban ce komai ba na ci gaba da shiri. Inna ta kwance habar zaninta kudine 'yan hamsin hamsin dubu uku na adashena na kwasa, sannan cikin robar can tumatir ne na tafasa shi ga sabulu can inji Baabarki..... Na ce, "Ki bar kudinki." Ta ce, "A'a na dai baki ne, amma badan zasu ishe ki wani abu ba ne. Yaron nan dake dawainiya da ke Allah ya gwada min aurenku." Yana zaune yana latse-latsen waya ya diro, "Gimbiyata, amaryata har yau fushi kike da ni? Gashi doguwar tafiya za muyi? Don Kano zan kaiki." Ban tanka shi ba ya amshi robar hannuna da leda ya daga but ya sa. Ni dai tamkar na haushi da duka nake ji, ya bude mun gaba na shiga don bani da yadda zan yi. Tunda muka dau hanya yake mun magana amma ban tanka shi ba. Ya ciro waya daga gefen shi ya ce, "Ga wayarki." Sai lokacin na yi magana, "Bana so." Ya daurata kan cinyarshi, "Dole ki so ta Hafsat don in na tafi karatu ta yaya zan dinga jin muryarki? Ki saki ranki, abun da ya faru ba wata matsala bace saboda ni zan aureki..." Na zabga mishi harara tare da cewa, "A ganinka kenan, amma ni addinina bai yadda don zaka aure ni kayi ZINA dani ba." Ya katseni, "Ki daina cewa Zina." Na daga murya na ce, "Ka biya sadaki na ne? Iyayenka sun nemi aurena gun iyayena ne an basu? Ko jama'a sun shaida." Ya ce, "Ba daya." Na ja tsaki ban kara tanka shi ba har muka kai. A dakinmu ba yadda bai yi ba na'ki tankashi, ya aje mun kudi da waya ya tafi. Na saka kuka nayi ma ishi na, tunanina in Allah bai yi aurena da Munnir ba fa? Ya sakani cikin matsala kenan don ban san mai zance ma mijina ba yayin da yace ina nakai budurcina? Dole in dauki hakuri in lallaba Munnir ya aureni. -Yana kiran wayata sosai, tun ina sharewa har na hakura don ban san yadda zan yi ba, sai dai bashi da wata daraja ko kima a ido ba, ko na aureshi gani nake ba zan girmama shi ba, tunda na ga irin nashi rashin Imani. Sai mene? Tun jiya sha hudu ga wata ya dace in ga al'adata amma har yau sha biyar shiru. Wannan ya tilastamin shiga rudani. Dora John dakinmu daya har ta gane ina da matsala ta ce, "Hafsy yaya ne?" Na ce, "Ciwon kai ne." Ta bani panadol da sauri na sha don kuwa kan nawa na ciwo. Kwanaki uku suka biyo baya gashi banji daga Munnir ba cikin 'yan kwanakin, naje na sai kati na kira shi, yana dagawa na soma kuka, ya ce, "Mai ya faru?" Na ce, "Banga period dina ba yau kwana uku." Ga mamaki na sai na ji bai damu ba ya ce, "Zan shigo wannan ba wani abun damuwa ba ne." Washegari sai gashi da wani abokin shi, yana shigowa na soma kuka nan take ya bata rai, "Kukan nan ya soma isata, zan barki ki karata in dai ba zaki daina mun kuka ba." Abokin shi Bello ba karamin tsanarshi nayi ba har da cewa, "Daga sau daya sai ciki?" Munnir ya ce, "Nima dai nayi mamaki bata fa tsaya ba ma, gaskiya in anyi bikin mu juya Mahaifarta za'ayi don bana son yara su wuce biyu tsanani uku." Tsabar bakin ciki ya hana ni tankasu, ni dai burina ya san yadda zai yi dani. Bello ya kira wani abokin shi anan Kano wai shi Nasir, ya zo suka tafi suka yi magana sannan suka ce inzo mu je asibiti. Mun shiga office din Likita mace 'yar kimanin shekara arba'in tana tsaye da farin gilashi, ta tsareni da ido bayan duk mun zauna ta kalli Nasir, "Me ke tafe da ku?" Duk muka yi shiru, Munnir ne mara kunya shine ya ce, "Mun kawota ne bata ga period dinta ba, so muna so a gwada ta." Ta tsareshi da ido, "Kanwarka ce?" Ya ce, "Budurwa ta ce." Bakin ciki ya cika ni, na sunkuyar da kai ina hawaye, "To ku dan bamu wuri." Suka fita. Ta zabga min harara, "Kin bashi kan ki ko?" Murya ta a sarke na ce, "Wallahi... Zaharaddeen Shomar what's app 08168575100 Sanadin Boko 1-03 Posted by ANaM Dorayi on 09:47 AM, 10-Sep-15 Under: SANADIN BOKO NA Maryam Abdullahi K/Mashi To ku dan bamu wuri." Suka fita. Ta zabga min harara, "Kin bashi kan ki ko?" Murya ta a sarke na ce, "Wallahi Anty fyade yayi mun." Ta ce, "Tun yaushe?" Na ce, "Za'a kai wata daya." Ta bani wata 'yar roba ta nuna min wata kofa, "Shiga toilet ki bani fitsarinki." Ina fitowa naga wata nurse tsaye ta ce, "Don Allah sister ina son result yanzun nan." Ba jimawa ta shigo, Likitar tayi ta juya takardar sannan ta dube ni ta ce, "Kina da cikin wata daya da kwanaki." Nan da nan na soma zufa, zuciyata na kwadayin ina ma mafarki ne? Cikin tsananin kuka da kunan rai na ce, "Ya cuce ni. Mai zance da Innarmu? Abun da Baba yake tsoro ya faru. Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un." Kuka na ya shigo da su, ta mika mishi result ya duba sannan ya kalle ta, "To yanzu doctor ya za'a yi tunda gaskiya ni da ita karatu muke yi, bamu shirya taron Baby yanzun ba." Na dube shi yana magana hankalinshi kwance kamar wanda ya aikata abin arziki. Ta ce, "Baka shirya tarban Baby ba mai ya kaiku aikata haka?" Ya ce, "Tsautsayi ne." Ta ce, "A'a ku ji tsoron Allah, aure shine ya fi dacewa da ku, karatun boko ba zai hanaku aure ba. Amma sai kaga ana wasa da Sunnag kun zabi boko sama da raya sunnar Manzo (S.A.W), to ku sani Manzon Tsira (S.A.W) ya ce aure Sunnar shi ne, duk wanda ya ki sunnarshi baya tare da shi. Kun fi yadda kuyi ZINA fiye da aure." Ta nuna shi da biron hannunta, "Musamman irinku 'ya'yan 'yan boko, Iyayenku sun rike wuta sai kunyi karatu mai zurfi basu damu da halin da zaku shiga ba kasancewarku balagaggu, burin su ku iya turanci tare da kawo musu kyawawan sakamako lokutan jarabawar ku. Ba su damu ku san addininku ba bare kusan illar ZINA."munir yace to doctor, yanzu menene mafita? Don matsala ne cikin nan don Allah a cire shi tayi suru tana tunani. Bello yace in bazaki iyaba muje wani asibiti doctor hindu tayi shuru tana nazari, tace to zan tai makeku sai a lokacin naji sanyi ya ratsa zuciya ta. Ta bani wasu kwayoyi wai kafin nan da sati daya zai fita, suka ce nawa? Tace dubu goma nan take suka biya. Sun saukeni makaranta sanan suka wuce, da alkawarin zaya rinka kira yaji abinda ke tafiya. Yau kwana tara shuru sai laulayin da nasoma gadan- gadan, ga sheka amai nan ga zazzabi na kwasa na koma wajen doctor hindu ana kai mata kati na tace a turo ni duk da yarinyar da naga ta shiga bata fito ba, itama yarinyar duk a firgice take, taci kuka ta gode Allah nace sannu doctor. Tace yauwa ya jiki? Cikin saurin baki nace da sauki amma fa har yanzu bai fita ba. Ta mikye tare da diban wayoyin ta ce ku biyo ni. Muka biyo ta cikin harabar asibitin muka nufi wani gida kirar zamani dan madaidai ci. Ta umurce mu mu zauna kan kujerum da ke kayatacen falon,ta shiga wani daki daga cikin dakunan biyu dake cikin falon. Jim kadan ta fito ta canja shigarta zuwa doguwar riga ta atanfa. Ta shiga kicin yafito da doguwar gorar ruwa (swan) da kofuna guda biyu. Ina takure cikin hijabi na, zazzabi ne ya rufe ni ta tsiyaya ruwan ta miko min, sha ruwa nace a a sanyi nake ji ta koma takawo min paracetamol na sha. Ta zauna ta zuba mana ido, ta dubi dayar tace asabe ko? Yarinyar tace eh, menene labarinki? Yarinyar ta ce, Sunana Zainabu,amma an fi kirana da Asabe.Mu 'yan asalin nan kano ne, a karamar hukumar kunci can wani kauye ana ce masa kurje. Wata mata mai suna Gambo tana zuwa kayaunkan garinmu tana diban yara 'yan aiki, wata rana taxo gidanmu ta ce da Babata su bada ni ana samun kudi sosai, wai can zan samu kudin kayan daki. Sai na ce ni ba zani ba, nafi son nan don ina talla kuma ina zuwa karatun allo. Sai Babata ta ce to abar shi, don Babanmu in ya ji ba zai yarda ba, ta ce can ma ana karatun Muhammadiyya, kuma za su saki ga cima mai kyau za ki canza. Haka dai ta zuga Babata hr ta yarda, sai da suka yi rigima da Babana sannan ya yarda. Gidn Hjy Mairo aka kai ni, ba wani aiki sosai kuma bata da tukara. Ba ta da Matsala in kaga damuwarta to ran danta ya 6aci, don shi ne dan ta kwallin tal. Yawancin aikin nawa duk nashi ne don tana zuwa aiki shi ma yana zuwa makaranta, amma ya fi ta zama gida.Ba mu cika shiri da Yasir ba, don shi yana da fada. Watana 3,ranar wata Litinin ina kicin, ya shigo wai in dafa masa Idomie, nan na bar komi na shiga dafa masa, don Hjy ta ce kome nake yi in yazo da nasa in bari in masa don a zauna lfy. Ba ta so ta ga yana zagina, na ce to. Da na gama na nufi dakinsa, na aje zan fita ya ce in dawo, cikin sauri na dawo don ina matukar tsoronsa, kawai sai ya ce in cire kayana. Na soma zare ido, ya ciro wuka da sauri na cire ya kwantar dani ya aikata alfasha da ni, sannan ya hana ni kuka. Ya kuma ce idan wani ya ji sai ya kashe ni. Naja baki nayi shiru, duk uwar wuyar da na sha tun daga nan muka daina fada, Yasir ya maida ni tamkar matarsa. In Hjy bata nan sai ya kira ni dakinsa, akwai lkcn ma da Hjyn taje Umra ta barmu tare da wata 'yar uwarta don ta lura da mu, da kuma gidan,amma Yasir cikin dare zai zo ya buga in kofa, dakinshi nake kwana. Nan da nan nayi wani girma, kirjina ya cika. Daku abn da ya gani zai sai min,wata rana na tashi ba lafiya,sai amai nake shekawa,Hjy ta kira Likitansu tun kafin ya gwada Ni ya ce yana zaton ina da ciki,ya ce amma bari dai ya gwada. Gwajin Farko ya nuna ina da ciki, nan ta shiga salati da sallallami, ta tsare ni wai in fada mata wanda ya min, na ce Yasir ne. Nan ta hau ni da duka wai na masa sharri, dan shekara ashirin da biyar dinne yaya iya yi min ciki? Da ya dawo ta tambaye shi da har ya musa sai yaga ta watso min kayana, wai na tafi zan yi ma danta sharri, sai ya ce mata shi ne,amma tsautsayi ne. Ga mamakina, bata yi masa wani fada ba, sai dai ce masa tayi kada ya kara, kuma Babanshi zai dawo. Ta kai ni wani asibitu aka cire min shi ta dinga min fada wai ko ya kira ni kada naje. A cewarta, wai bashi da laifi ni ce mai laifi. Sati biyu ina jinya, Sannan na gyagije, ganin ta sa mana ido, sai ya ce in dinga barin dakina a bude zai ringa zuwa. Na ce Hjy ta ce mu daina. Ya sake zare min ido, dole na bi yanda yake so, wai baya so Hjynshi ta sani, don ta ce mishi in ya sake sai ta aura masa ni, shi yasa duk ya tashi hankalinsa yanzun. Doctor ta ce, To shi baya son ya aure ki ne? Asabe ta ce, tab ita ma nasan tana tsorata shi ne, domin ba ta da burin yayi aure yanzun. Burinta shi ne ya yi karatun boko mai zurfi,kuma ya zama wani abu a kasar nan SANADIN BOKO." Na jinjina kai, tuni zazza6ina ya sauka. Labarin Asabe ya ta6a ni, kallo na dinga bn ta da shi, Yarinya ce ba zata wuce Shekara sha uku zuwa sha hudu ba. Wanna ma ai child abuse ne, ya kamata a hukunta su shi da Hajiyar shi. Doctor ta katse min tunani da cewa Hafsat me ya faru da ke kuma, menene labarinki?? Na zuba mata ido, hawaye suna zubowa, ta ce fada min ina so ne in taimake ku, na ce zaki cire min cikin? Ta ce Eh, zan cire miki in har naji labarinka, kin cancanta a cire miki.Ina nufin in ban da son ranki hakan ta faru ba. Na share hawaye,sannan na ce da ita. "Sunana Hafsatu, Mahaifina dan asalin jihar Borno ne, ya fito daga gida tun zamanin yana saurayi, a kano ya yada zango, nan yake 'yar sana"arshi.Sun hadu da Mahaifiyata a can lkcn tazo gidn yarta a Na'ibawa. Babana Shi ne ta tambaya ya yi mata kwantancan gidan Malam Ma'aru me Almajirai mijin yarta kenan.Daga lkcn ya nuna yana sonta, ta amince hr yaje Maliunfashi jihar Katsina, unguwar Fayamasa. Ya samu kar6uwa cikin dangi, don yana da nutsuwa da ilimin addini aka ce ya turo magabatansa.Mahaifanshi sun rasu sai babban wansu Babagana, shi ne ya zo suka hadu da wani uban dakinsa. A nan kano suka zo, sune suka amsar masa auran Innarmu.Ba su jima a kano ba ya soma zuwa kaduna, ya fara sana'ar saida lemo da Ayaba,daga bisani ya nemi gida a hayin rigasa ya dawo da Innarmu,lkcn tayi haihuwar farko wato Yayana Ummar. Gidanmu gidan haya ne, Mai girma gaske a layinmu kaf ba gidan da ya kai namu yawa don gidan yawa ake ce mana. Mata goma sha ne, kowace da 'ya'yanta wasu hudu wasu shida,wasu goma sha. Babana ya sake auro wata matar daga kano, itama nan gidan ya samu daki kusa da na Innarmu., Babah tana da kirki da nutsuwa, shi yasa duk yanda Innarmu taso suyi rigima bata biyewa, dole itama ta saki suka zauna lfy. Yanzun Babah 'ya'yanta 6, Innarmu 8. Ni ce 'ya ta 2, masu bina 3 duk maza ne, sannan mata. Innarmu gidan su 'yan boko ne, ko na ce kowa yasan Katsinawa da boko. Don haka tana da burin mu 'ya'yanta muyi boko, shi ko Baba ba ya da burin mace ta wuce primary. A nashi ra'ayin nayi saukar Alkur'ani mai girma ya min aure. Tun muna kanana Innarmu ta kwadaita mana boko, don haka ni da yayana mun taso muna son karatun boko,Primary 5 Umar yake lkcn da ni ma aka sani. Babanmu bai cika biya mana kudi Makarnta ba, don bai cika samu ba.Amma in yana da shi yana ba mu,ganin haka ne yasa Innarmu ta kama sana'a. Gyada take soya mana ni da Yayana in lkcn dafaffiya ne kuma ta dafa mana da wannan muke samun rufin asiri. Cikin haka Yayana ya gama Primary aka kukata ya shiga Junior. Kwanci tashi nima na gama primary, sai dai lkcn ne Baba ya ce Bokona ya isa haka, izifina ishirin a Islamiya ya ce da na sauke za a min aure. Innarmu ta ce ina, yanzun kai ya waye ko ita tayi makarantar gaba da primary balle 'yarta. Sun yi hatsaniya hr abokinsa makocinmu Baba Garba, ya saka baki kan cewa Baba yayi hakur ko aji 3 in yi wato karamar Sakandire. Baba ya ce, shi kenan,amma fa ba ruwan shi, ko yana taka kudi ba zaya ba ni ko na fensir ba. Abubuwa suka

Chapter 2 of 22