Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
mana tunda shi ba mai haya niya ba ne, Mun je naga dakin, karami ne ta ce dubu shida shekara, dari biyar kenan dk wata, na ce ba komai, zan biya. Naje banki na ciro dubu ashirin cikin kudina nazo na bata shida, naje kasuwa na siyo kayan abnci da yar tukunuya da dan risho na dawo. Zaman mu da Hjy Iya ba matsala, don ina bn ta sau da kafa,daga ni sai ita a gidan tun Asubahi in na tashi zan wanke mana bandaki, in share tsakar gidan, komai na dafa zan bata. In ko zan yi wanki na kan ce kawo naki Hjy, kullum sai dai ka ji tana shi min albarka, Shadad kuwa dama tuni ta ce in dinga bar mata shi tunda in bana nan ba shi da matsala, musamman in ya gane cewa gidan muke kwana. In ko unguwa na fita dashi kiwa ce dashi, sannan ya yi ta 'yan rigime-rigime. Mun zauna yanzu albashina da kyar nike kai dubu biyar banki a wata, saboda hidimomin gida wanda a da ban san suba, kai ko kan wannan ba zan manta da Doctor ba, domin ita ce ke yi min komai. Burina na gaba shi ne, in koma makaranta, amma yaya zan yi da aikina wanda shi na dogara da shi? Wata rana da dare na shiga gurin Rahma muna hira, na ce mata ina son na koma makaranta, ta ce aikin fa? Na ce shi ne matsala, amma ina son in samu ko 'yar Diploma ba sai nayi jami'a ba, ta ce hakan ma yana da kyau. Aikina daga karfe takwas din safe ne zuwa hudu na yamma, sannan wasu su zo masu kaiwa dare, na ce Rahma ko in koma aikin dare ne. Ta ce albashinsu fa bai kai namu ba kuma yawan cinsu duk maza ne, na ce to ya zanyi? Haka nan zan hakura in dai manaja zai yarda ta ce matsayaci ba, sai shegen iko sai ka ce gurin shi. Na ce ai dama ba shi ne da gurin ba? Ta ce ba shi ba ne, na wata Hjy ce mai kudi, ina zaton ma ba a kano din nan ta ke ba. Na ce to Allah dai yasa in dace zan tare shi in masa mgn, Rahma ta ce to in ya ki fa? Na ce ki taya ni addu'a ya yarda, Rahma ta ce to Allah yasa a dace, in za ki masa magana sai muje tare .Haka ce kuwa ta faru, domin washegari muna tashi daga aiki sai muka nufi ofishin manaja, yana zaune gabn shi laptop ce. Muka gaishe shi, cikin daurewa ya amsa, na ce "Yalla6ai nazo neman uziri ne. Ya harare ni,wannan karon ko me kika zo nema kuma kowa ya mutu ba zan ba ki wasu kwanaki ba, sai dai in ki nemo wadda zata zauna madadinki. Rahma ta ce, Sir, ba mutuwa akayi ba, tana son koma mkrnt ne. ya ce, to sai ta bar aikin. " Ya ci gaba da abn da yake yi. Muka kalli juna ni da Rahma, na ce ko zan iya komwa akin dare? ko kuma in zo duk lkcn d nike free hr dare? Ya ce wace makaranta? Na ce poly zan shiga, ya kalle ni dama ba ki riga kin shiga ba? Na ce eh, ya ce to in kin shiga sai muyi magana. Ni da Rahma muka yi godiya, bai amsa mu ba, mu dai muka fita muna mamakin yanda ya saurare mu. Ina jin an fara saida form na garzaya na sayo. Rahma tana ta min dariya wai na cika zumudi, Allah shi ne mai shirya ma ba wa al'amuran shi. Yau gani na samu gurbin karatu a poly, daga karfe daya zuwa biyu nake tashi, uku in zo shago, bn damu da rage min dubu biyun da aka yi cikin Albashina ba, saboda na samu shiga makaranta. Kuma na samu irin course din da nake so, wato (Mass comm) Rahma da murnarta take shaida min saurayinta Sagir zai turo magabatan shi, na ta6a baki tare da cew. "Yau an yo odar kaya a shop din nan, kin lura? Tace eh na lura mana. Amma me yasa kullum na dauko batun Sagir sai ki daure fuska? Haka nan ranar da na ce kuje ku gaisa kikaki.Shi ko kullum sai ya ce in gaishe ki. Na ce, um, ki dai yi hattara da samarin yanzun. Ta ce, Sagir yana da kirki kuma aurena zaiyi, na kafa mata ido, kada ki ba wa namiji amana fa, in kin yarda kenan. "Ta ce, to zan kula. Wata rana ta ce min za su je gidan Yayar Sagir, zata gaishe ta, wai tayi 6ari, na shirya muje na kalle ta dabadan Rahma ba ce dana zabga mata ashar. Amma Rahma ta wuce in zage ta, kema da zan fada miki ki ji da sai na ce miki kada kije, ta ce ko zan san dalili? na ce yaudarar mazanzamani.Tayi 'yar dariya, "Hafsat me yasa kin matukar tsanar maza ne? Me suka miki har haka?" Murmushin takaici ya subuce min na ce, "Sun min da yawa." Ta ce, "Kada ki manta shekararmu 1 da Sagir kuma kudin gaisuwarshi na gidanmu." Sam ban san lokacin da maganar ta subuce min ba sai ji nayi ina cewa, "Shekaru 3 da watanni muka yi ni da Munnir, amma hakan bai hana shi yaudarata ba."Hawaye suka soma zuba daga idona. "Rahama zan fada miki amanar sirrina, in kin boye min kin kyauta, in kin tona min don kanki ke da Allahn ki." Nan na kwashe komai na labarta mata, ni kuka Rahma kuka, ta rungumeni babu mai ba wani hakuri sai da muka gaji da kanmu. Na ce, "Rahma zan koma boko ne kawai don faranta Ran Mahaifiyata, Insha Allahu zan kawo haske cikin zukatan Iyayena SANADIN BOKON nan." Rahma ta ce, "Ina bayanki, Allah ya shige mana gaba. Lallai zan ja baya da Sagir kuma ba zanje gidan Yar tasa ba." Na ce, "Na kula Sagir dinki kamar bashi da matsala, duk daba anan take ba. Ki ci gaba da mishi yadda kika saba amma ko da wasa kada ki bishi wani guri. Amma ni a kan kaina na gama soyayya, na kuma sha alwashin duk namijin da yayi gangancin cewa yana sona zan ci zarafinsa matuka. Rahma ko kinga laifina?" Ta ce, "A'a."Rahma 'yar amana ce, ko Mahaifiyarta bata fadawa labari na ba, haka na ci gaba da Karatuna tare da aikina, na tsare mutuncina ko a makaranta nasha jin ana zagina wai na cika girman kai, daga ganina ni ba 'yar kowa bace sai shegen Iyayi, ga daure fuska. Sam ban damu ba, sai dai mutum in ya isa ya zo gabana ya fada. Kwanci tashi har na hada Diploma, kuma ina da burin ci gaba da HND,shekara 2 kenan. Cikin shekara 2 har Shadad ya isa shiga Makaranta, kuma na lura zaya dauki Karatu sosai, shekarunshi 4 kenan da 'yan watanni. A hanyar zuwa gurin aikina naga wata Makaranta Al-Iman, boko ce da Islamiyya don haka na je Makarantar na karbar masa form, sun ce yaro ya zo tun 8 na safe sai 6 na yamma. Duk da Islamiya da hadda, sati da lahadi sai karfe 2 zai je. Alhamis da Juma'a karfe 2 zasu tashi. Tsarin makarantar ya min daidai domin zan samu lokacin daukan shi, sati na zagayowa ya soma zuwa, da dare kuma inai masa bita. Tambaya daya ya min wadda ta sa ni kwana kuka, tare da tunanin me zai faru nan gaba? Ko ba komai nasan nan gaba akwai kura, abin da ya faru ranar da ya fara zuwa Makaranta ya dawo muna yin home work ya ce, "Anty." Na dube shi, "Menene?" "Me yasa da kika kaina Makaranta baki sa min sunan Babana ba? Duk 'yan ajinmu ana kiransu da sunan Babansu, ni kuma ana kirana da Shadad H." Gabana ya fadi, amma da yake shi karami ne yanzun ba zai fahimta ba sai na ce, "H din nan farkon sunana ne Hafsat na sa maka ko baka so?" Ya ce, "Anty kowa sunan Babanshi yake sawa, wani yaro yace min wai menene H? Wai Hamza sunan Babana?" Na ce masa, "Ban sani ba, nace ba sunan Babanka ba ne, sunana ne kaji ko?" Ya ce, "To." Can kuma sai naji ya ce, "To shi Babana ya sunan shi?" Gabana ya sake faduwa na daure na ce, "Na manta, amma in na tuna zan fada maka." Na mike don kar ya sake yi min wata tambayar. Shadad karamin yaro ne amma in ya maka magana sai kayi zaton Babbane. Ina tsoron nan gaba kadan ya tsareni don in fito masa da Ubansa, abu 1 na sa a raina, shine zan zama uwarsa kuma ubansa, zan yi masa komai da uba zai ma dansa. Tun da na bar gida har yau ban daina kuka ba, ban daina tunanin iyaye da 'yan uwana ba, kullum sai na zubar da hawayena tare da yin Allah ya isa kwando dubu ga Munnir, ba zan zagi Boko ba sai dai ba zan gaji da cewa itace sanadin shigata matsala ba. Haka kwanaki suka yi ta shurawa Allah ya taimake ni na koma don samun HND sai dai manejin rayuwa nike, albashina yayi karanci ya dauki nauyin karatuna da na Shadad, don ma na tara kudi da farko lokacin Dr. tana nan. Sai dai na dauki alkawarin ko zamu kwana ba mu ci ba bazan taba neman taimakon abokin halitta ba, sai dai in nema a gurin Mahalicci. Cikin wannan halin yarinyar Hajiya Iya wadda ke zaune a Saudi ta zo ta dauke ta tare da barin amanar gidan a hannun Babban Yayan Rahma. Amma ni Hajiya Iya ta ce in yi zamana kyauta har sai lokacin da Allah ya daga, don ta ce ina lura da ita, kuma duk abinda na ci sai na bata koda bata san da shi ba. Na ji dadin samun wannan rangwame duk da cewa kudin ba wasu yawa bane dama, amma sauki yana da dadi. Na dawo ni 1 a cikin gidan, in zan fita na kulle, in sati ne ko lahadi ko dai wane lokacin ne Shadad ba zai je Makaranta ba sai na kai shi gidan su Rahma gurin mama, in ko ba nisa zanyi ba nakan yi kasadar kulle shi ya taka kujera ta ciki ya sa sakata, in na dawo sai na kwankwasa ya bude. ****** ******** ******* A garin Kaduna tun da aka wayi gari Hafsat ta gudu, bakin ciki ya karu ga zuciyar Innarta, don haka ta tattara yanata-yanata ta fice ta bar su Ummi suna ta kuka, Baba tana lallashinsu. Har ta isa Malimfashi idanunta basu kafe da hawaye ba, bata boyewa 'yan uwanta komai ba,sunji bakin ciki suma saidai sun bata shawarar tayi mata addu'a kada ta mata baki.Haka ta ci gaba da zama har zuwa lokaci mai tsawo. Wani abokin wansu Babba ya zo ziyara daga Huntuwa ya ganta ya ce yana sonta, bata da zabi tunda duk yayyinta sunnuna sun amince, kuma aurenta da uban 'ya'yanta ba kome. Alhaji Danlami Matarshi ta rasu wurin haihuwa, amma yana da yara kuma yana zaune tare da su ne, shekarunsa 3 kenan rabonsa da aure, ta tare a gidansa dake Nasarasa Funtuwa, dole ta koyi hakuri domin zama da yara sai hakuri, in ta kalle su sai ta tuna da nata da ke can wani gida. Sai ta kyautata musu ko don a kyautata ma nata, yadda take kula da Yaran sai suma suke son ta. Cikin haka ta samu ciki ba don san ranta ba, amma ba zata butulcewa kyautar Allah ba. Ta haifi danta namiji ya ci sunan Rabi'u. Umar ya kan kawo mata ziyara da 'yan kannanshi, mijinta yanada kara don in zasu tafi yanai musu shatara ta arziki. Shi kuwa Babansu Hafsa har yau yana bakin cikin tafiyar ta duk da shine ya koreta, yana kuma addu'a Allah kada ya bashi mai irin halin Hafsa cikin 'ya'yansa, ganin halinta ne da na Uwarta, ko wani buri suka ci na son abin duniya shiyasa suka dage da boko, boko har taje ta yi abinda taga dama.Ni kuma lokacin rayuwa ta min tsanani, zuwa wannan lokacin kudin da ke cikin account dina sun kare, albashina ya min karanci, karatuna ga na Shadad, ga abinda za mu ci, omon wanki, sabulun wanka har da suturar sawa, duk a dubu 8. Don ma bana biyan haya. Yau na wayi gari ko na karyawa bani da shi, ga shi wannan watan shine zan bada kudin term na Shadad dubu 4, gashi zan yi registration, gashi bamu da komai na abinca ga kudin dan adaidaita sahu. Hakika komai ya tsananta gare ni, kukana ya karu, nadamar barin gidan Iyayena ta sake shigata sai dai ba zan iya komawa gidan yanzu ba, duk da kuncin rayuwar da nake fuskanta. Lallai babu komai cikin barin gida in ba takaici ba, danabi Mahaifiyata na san danginta za su saurareni za kuma su fahimceni, zan samu gata ni da dana kafin Allah ya min sakayya akan Munnir. Bana ba duk wata 'ya mace shawarar barin gaban iyayenta don gudun zubewar mutuncinta. Hawaye na bin kumatuna ban damu da na share su ba, domin da hawaye na karewa da yanzun nawa sun kare. Muryar Shadad ce ta katseni, "Antyna menene yake damunki kullum kike kuka?" Na share hawaye tare da kakaro murmushi, "Babu komai." Ya dafa cinyata, "Kina tunanin Iya ne?" Na ce, "Eh." Ya tambayeni ni don ya san kalmar da zan fada mishi kenan, a duk lokacin da ya tambayeni haka nake ce masa. Ya bata rai, "Anty to muje gurin Iya din, ni bana so kina kuka." Na ce, "Da nisa jirgi ake hawa kuma bani da kudi." Ya ce, "To ina girma zan saya mana jirgi muje ko?" Na ce, "Allah ya sa." Kicin na shiga ina dubawa, ko zan ga dan wani abin na baiwa Shadad, duk da nasan cewa bani da komai. Shiru na yi tare da tunanin abinda zan bashi. Rahma ta yi sallama, na amsa, ta shigo kicin din tana cewa, "Ina Hajiyar gidan nan?" Na yi guntun murmushi tare da cewa, "Rahma kenan, duk tsokana kin santa." Ta ce, "Na zo shan tea din kin nan mai kayan kamshi." Na ce, "Sai dai na baki kayan kamshin ki je ki dafa." Ta zuba min ido cikin sanyin jiki, sannan ta ce, "Hafsa kin 'ki daina kukanki ko?" Na ce, "Ina kika ga ina kuka?" Ta ce, "Haba Malama, ga idonki nan?" Ta shiga bude-bude, bata ce min kala ba ta fita. Ina cewa, "Rahma zo ki ji." Bata juya ba ta wuce. A zuciyata na ce Rahma kenan, ita dai ta tsani ta ganni cikin damuwa, ina son zama da ita don ita kadai ce kan sani murmushi. Jim kadan sai gata da kunshin kosai da jug dauke da koko, bata min magana ba ta zuba ma Shadad. Na ce, "Rahma koko kuka dama?" Ta zabga min harara sannan ta ce, "Ai wallahi Hafsat kina bani haushi, ina lura da ke duk matse-matsen da kike yi cikin satin nan, har ta kai baki da abinda za ki ci amma ba zaki iya tambaya ba? Ni kam ko yaushe gidan ki nake cin abinci, saboda ina daukarki 'yar uwa ta jini." Na ce, "Rahma dama ni dake ai babu wani bambanci duk daya ne." Tsaki Rahma taja, sannan ta dora min dari 5 kan cinya, zan yi magana ta ce, "In kin ce tak Allah ya isa." Da kallo na bita har ta fita sannan na saka dariya, Rahma kenan. Karatuna ya shiga wani hali, har ina ganin in ba wani ikon Allah ba tsayawa zaiyi. Cikin wannan matsatsi aka sa ranar auren Rahma da Sagir, kullum tunani na me zanyi ma Rahma lokacin bikinta? Da dare Rahma tana min kitso muna hira na ce, "Rahma kin san me nake tunani?" Ta ce, "Kudin Registration?" Na ce, "A'a, so nake ki fadi abin da zan miki lokacin biki." Cikin tsokana ta ce, "Italian bed da leader sit." Muka sa dariya, na ce "Allah ya hore, har kayan kicin sai na miki." Ta ce, "Ni dai Hafsat nafi son ki bada hadin kai lokacin bikina kin ga dai bani da wata aminiya sai ke, sauran duk kawaye ne." Na ce, "Tabdijan! Rahma kada ki sani yin abinda ba zan iya ba." Ta saki kaina, "Kin san Allah?" Ta nuna ni da kibiya, "In bikina ya yi kyau ke ce in ya baci ke ce, kuma yanzune zan san matsayina a gurinki." Na ce Zaharaddeen Shomar what's app 08168575100 Sanadin Boko 1-8 Posted by ANaM Dorayi on 12:13 PM, 18-Sep-15 Under: SANADIN BOKO , "Maida wukar, Allah ya kaimu. Yauwa dama ina son in miki batun da ke raina. Ina son in samu manaja ya bani koda rabin albashina ne in sai ma Shadad takardu." Ta ce, "Kin san rashin mutuncin sa, abinda zai fi dai in tambayar miki rance gurin matar Yayana." Na ce, "A'a ki bari zan same shi in yaga dama zai yarda." Rahma ta ce, "Hafsa kenan, ke bakya son bashi sam! Kuma ai naga bashi hanji ne yana cikin kowa." Na yi 'yar dariya. Haka kuwa na yi, na samu manaja da bukata sai ya ce, "Kin cika daure fuska, da ace kina da fara'a har karin albashi zan miki. Banda kyautukan da zaki yi ta samu a kai-a kai." Na sake hade fuska, "Bana bukatar karin ko wata kyauta. Hakkina kawai nake so." Ya ja tsaki, "To sai ki jira lokacin baki hakkin ya yi, ke bazaki taba ganewa ba. Wai me ma zakiyi da kudin?" Ban amsa shi ba har sai da ya sake maimaita tambayar, Na ce, "Zan biya kudin littafan makaranta ne na yaro."Ya yi tsaki, "To sai ki jira lokacin don in kin ga na yiwa mace mutunci itama ta yi min ne." Na mike ba tare da na sake magana, don Manzon Allah ya ce ka fadi alkhairi ko kuma ka yi shiru, amma na so in zabga masa ashar in ya so ya kore ni gaba 1 daga aikin. Cikin kwanakin sai manaja ya soma shige min, duk da dinke fuskar da nayi masa, ya zo ya kawo min albashina wai gashi nayi bukatar da zan yi, na ce ya barsu ai ni na ma hakura. Kwatsam! Rannan sai naji ana buga min gida, lokacin 9 ta gota na dare, don har na soma bacci. Na zo na bude, nayi mamakin ganin manaja a gidanmu na ce, "Lafiya?" Ya ce, "Kalau, na zo ne mu gaisa." Na ce, "Na gode da gaisuwa. Sai da safe." Na juya ya ce, "Kina nufin har mun gaisa? Bai dace ki yi min haka ba." Na ce, "Za a min fada an hanani fita." Na fadi haka da nufin karema kaina mutunci. Ga mamakina sai naji ya ce, "Haba yarinya, ni zaki yi wa karya? An ce miki bansan cewa zaman kanki ki ke yi ba? Ni zaki saki jiki ki ci arziki ki saki, in ba zaki saki ba talauci sai ya yi ajalinki." Jikina ya yi sanyi lakwas, na maimaita kalmar zaman kaina! Na ce, "Ni ce mai zaman kaina?" Ya ce, "Sharri na miki? Kowa ya san ke kadai ce ba kuma a san iyayenki ba." Ya ja tsaki tare da cewa, "Banza mara rabo." Ya tafi. Ranar na yi kukan da ya isheni, wato kowa ya san zaman kaina nake? Wata zuciya ta ce, "To yanzun ai an daina kiwon dabba mutum ake kiwo." Sai dai da mutane zasu min adalci ya kamata su san cewa bana hulda da maza, da ace ina da wani aikin lallai zan bar super market din nan, sai dai bani da zabi. Da safe duk da kirkiro fara'ar da nike yi sai da Rahma ta gane cijewa nake yi saboda damuwar da ke raina. Ta kafa min tambayar me ke damuna? Nanfa na fada mata, na kara da cewa, "Dama duk mutanen unguwar nan kallon da suke min kenan? Ina zaman kaina?" Rahma cikin muryar lallashi ta ce, "Sam, shi dai yabi diddigi ya ji cewa ke 1 ce anan. Amma ba maza kike tarawa ba, kowa yana yabonki a unguwar nan don kin tsare kanki, kuma shi ya fada hakane don takaicin bai samu abinda yake so ba. Ki barshi da Allah." Nace, "To in ban barshi da Allah ba yaya zan masa? Ai bani da yanda zan yi dashi. Da ace ma ina da wani aikin barin musu wurinsu zan yi." Rahma ta ce, "To ai ba gurinshi ba ne shima cin arziki yake yi, don haka ba inda za ki je." Daga wannan lokaci muka sa 'yar tsama da shi, ya bi duk ya tsane ni, nima kuwa ya kara dasa min tsanar maza, yana son ya ga nayi wani dan kuskure ya tozarta ni, niko duk wata hanya da zata ja min cin mutuncin shi na 'ki sakaci da ita, lokacin zuwa aikina baya cika nake isowa, musamman in zuwan safe zan yi. ******** ******** ***** Munnir an kammala karatu an kuma dawo gida. Tuni ya manta da wata Hafsa da labarinta. Ya iso gida cike da soyayyar Mina, yarinyar wani kusa ce a gwamnati, sun kulle ne tun a yanar gizo ta (Facebook), sun jima suna soyayya kafin suga juna, bayan ya zo hutu itama ta dawo daga inda take karatu, suka hadu. Sun yaba da juna, sai dai sanin cewa ba za ayi musu aure da wuri ba suka kazanta soyayyar su ta hanyar biyan bukatar zukatansu. Sam! basu dauki hakan laifi ba, nasu ganin duk cikin soyayya ne a nasarance suke koman su don boko suka sani, shi suka iya, kuma shi suke yi. Sun dai kulla alkawari ga junansu cewa za suyi aure in lokacin yinsa ya zo, Allah ka shirye su shirin Addinin musulunci. (Ameen). ¤¤¤¤¤¤¤¤¤ Bikin Rahma ya gabato don haka na ciro dubu goman da na makale na ce mata na ba da rabin kudin Registration naje nasai mata sestin kula da jug. Dubu bakwai na kashe, nazo na kai mata gida, batan hakan ya min dadi. Su Mama suna ta gdy, ta ce yanda garin nan babu kudi shi ne zaki ta wannan dawainiya har haka? Na ce Mama ta kama ne. Da dare ina krtn Alkqur'ani,sai gata ta ce, Yayi kyau Hafsa, ina kika samu kudin sayan kayan ban masu tsada?Na ce Daga Sarki Allah. Ta ce, ba dai kudin Registration din ba ne? Na ce in sune fa? Don Allah zo ki zauna muyi batun anko. Ta ce ba zama nazo ba ki zo in ji Sagir da wani abokinshi, ki fada musu kudin abubuwan da zamu yi. Da karfi na ce " What? hum........ hum..... Rahma kada ki sani cikin hulda da maza. kije kawai ki amsa, na yarda zamu je kasuwa siyayyar tare. Zata yi mgn na rantse mata da girman Allah cewa ba zani ba, ta juya ba tare da ta ce kala ba. Nasan tayi fushi, amma sam fushinta bai dame ni ba, in dai akan abin da zai sa nayi hulda da maza ne har nai musu dry. Don ni nasha alwashin namiji ya gama ganin hakorina. Mun je kasuwa, duk abn da zamu bukata gurin walima mun sayi, don Walima kadai zamu yi kayatacciya, sai dai ta ce, Sagir za suyi (Dinner) kuma za su yi (Pink & blue day). Kullum rokona take in je har dai na amsa mata zani. hakan ya tilasta min siyan shadda kamfala (pink) mai ratsin bulu,yayin da Shadad na dinka masa(blue) din shadda, atamfar walima kuwa Rahma da kanta ta sai min., Bikinmu yayi kyau, komai a gidana aka yi duk da cewa ina zuwa gurin aiki da mkrnt, kin yi wa Manaja mgn nayi don ba zan sake yi mishi wani zance ba, ko neman wani abu. Ranar daurin aure kam ban je makarantaba, kuma banje aikin ba, saboda aubuwan sun kwa6e min. Malamai sun halarci walima, sun kuma yi nasiha akan mahimmancin yin aure tare da falalar da ke tare dashi. Sun ja hanklin iyayen yara masu cewa su dole sai 'ya'yansu sunyi boko mai zurfi, ko sai sun kama aikin kafin suyi aure. da cewa wannan ba koyarwa addinin Musulunci ba ce. Suka ce, ita mace babu abinda yafi daraja da mutunci a gare ta irin aure. Sun ce boko ba ya hana aure, kamar yanda aure baya hana boko. In 'ya'yanku suka lalace saboda kun hana su aure sai boko, hakika laifin zai fi ta'allaqa a kanku iyaye., Nasihar da suke yi ta sani shiga dogon tunanin, ni kaina misalice SANADIN BOKO gani yau na zama 'yar kaina, domin da ace ban ce bokoba nabi zancan mahaifina nayi auran da yaso, da yanzun ina tare da dangina da ban kashe auran iyayena ba, da ban haifi shege ba, da maxa ba su dinga latsa ni suna son mu lalace ba. Ban san hawaye na sauka daga idanuna ba, sai dai hannun Rahma naji a kumatuna tana share min tare da yi min rada a kunne. Haba Hafsa cikin fa taro ki ke, ya ya za ki ba mutane damar yin tunanin ke wacece? Please ki share don Allah. Walima ta tashi lfy, na ce da Rahma bari na leka shop, kin san ban dauki uxiri ba, ta ce min ba damuwa. Naje na samu su Ishak, ya ce nasan kuna biki shi yasa ban tashi ba, na fada mawa manaja cewa zan zauna madadin ki har ku gama biki, ya kuma san auran Rahma ne shi yasa bai ce komai ba.Ya kara da cewa, ki koma har sai kun gama ki mata fatan alheri, mun so muzo daurin aure amma kin san Manaja. Na ce na gode, ya ce a'a ba komai, wata rana irin haka zata iya faruwa da mu, na dawo nake fada ma Rahma ta ce, Ishak da Musa suna da kirki sosai, dn dai kin kasa Fahimtarsu ne. Na ce, Ba zai sa don sun kar6ar min aiki in sakar musu fuska ba, gaisuwa kawai ke hada mu ko da, kuma ita zan ci gaba da yi kadai. Anje anyo ma Rahma danki(jere) an zo ana ta lbrn kyan gidan an ce ango ma ya zuba labulaye da kayan wuta, Sai an kai Amarya sannnan za'ayi sauran shagalgulan da ango suka shirya, wai ba a son mutane suyi yawa, sai ka nuna pass sannan zaka shiga. Da muka kai amarya unguwar Sharada, gidan kam ko ni ya min sosai, taso in kwana na ce mata ta min hakur sai gobe in mun hadu gurin (pink & blue day' . Ta ce don girman Allah

Chapter 7 of 22