Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
mukayi, kunun gyadane da lafiyayyen kosai, da kuma kayan tea gamai muradi.natashi nashiga wanka bayan mungama, kayan rahma nasaka cikin sabbabin kayanta, rahma tace bari tadan fita cikin gdan tagani, jim kadan tadawo tace, wai gaskia babban gdane, gasu da tarin zuri'a, nace hum! Allah yasa mudace, rahma tace amin, can saiga wasu yanmata 3, 2 manya, 1 karama, ina zaune bakin gado suka shigo har ciki, biyun sunyi kama da abkr, duk yanda akayi kannensane, duk suka tsuramin ido, bayan mun gaisa, su kuma sai mgn suke cikin fillanci harda daria, (nidai nagane gulma suke) karamar cikinsu ta matso kusa dani tana cewa cikin harshen turanci, aunty sunana ummi, wannan kuma sunanta rukayya, yayatace, wannan kuma sunanta husna, abokiyar wasanmuce, dukkanmu kannen hamma ne, nace to sannunku da zuwa, ta dubi sauran tana sauraron abinda suke cewa, sai naga tahade rai, sanna itama taci gaba dayi musu mgn cikin fillancin, abinda nake zargi ni suke kushewa ita kuma bahaka tasoba, saina samu kaina da tsarguwa, su 2 suka tashi suka fita suna daria, nace musu sai anjimanku, sukace to, ita kuma ummy tadawo kusa dani tazauna, tacemin hammansu yana sona da yawa, dan Allah na kula dashi, nayi yar daria nace to ngd ummy, kuma zanbi shawararki, sai naji yarinyar tashiga raina mai hankalin manya, tace kinyi kyaufa, anjima za'ayi budan kai nace, ya akeyi? Tace kubakwayine? Nace a'a, tace yanada kyau, zaku zaunane sai a bude fuskanki inkin rufe, anayi ana gada, daga nan sai dangi suyi fansa, nace mekenan? Tace kudine za'ayi ta zuba muku, sai kuma a kawo faute daga gidan amare, nace shikuma mene faute? Tace ba ankai muku suddajeba? Na tsura mata ido, mene suddaje? Tace kayan dangi mana, ba ankai mukuba? Nace eh, tace toshine suddaje din ai, nace to menene faute? Ina nufin me akeyi dashi? Tace kayane su kuloli dasu. Kaya dangin amarya suke badawa wasuma harda gado sukeyi, nace to, rahma tace in kuma mutum bai sanibafa? Tace ai duk zuri'armu sun sani, rahma nace abinda mukeyi acan zamuyi sai mubasu hkr muce bamusan sunayin hakaba, tace, ai baza'a damuba, tunda an sani cewa baku saniba, karfe 4 daidai lkcn gdan yacika dam kidan sarauta ke tashi, kai zuri'ar abkr akwai kyau, sunata shigowa kallona, ummi taje kiran da abkr yamata, don tuni sunyi waya yasan cewa tana gdan, ta shigo dauke da katuwar leda, tace anty canza kaya donga adda fadi nan sun iso, kuma nasan hamma da abokanshi ma sunata shiri, shine yace in baki kayan nan, muka bude nida rahma nace, kila dai a dinken yasiyo, rahma tace, daga gani don gasunan a ledarsu, nace Allah yasama to sumin daidai, daya leshine da aka hada da swis, dayan kuma leshine zalla, sai shadda doguwar riga taji aiki, sai atamfa, nace toni wanne zan saka? Rahma tace kisa leshin nan, ummi tace aunty kisa shaddar nan mana gata ja tunda keba fara bace, zakiyi kyau, nace rahma duba akwatii akwai takalmi ja cikin kayan can? Saiga ja takalmi gami da mayafi, ummi tace kiyi amfani da bakake, kuma hamma yanason jan abu ga mata, don in zai saya mana zani dole saikaga ja aciki, na sake yo wanka na zauna gaban madubi nadauki kwalliya, harsu ummi suna cewa gaskia nai kyau, na saka sarka da sauran tarkacen karau, suk su rahma da sakina kowa yayi kwalliya, zuwacan abokan wasansa suka shigo sunamin tsiya wai in fito, yan'uwana suka takamin baya muka nufi gurin. Katuwar darduma ce shimfide, tun kafin mu karaso na hangi hamma sanye da shadda blue mai kyau da tsada sai sheki take, gefenshi fadima ce wato kishiyata, tana sanye cikin wani yadi, tsananin kyan yadin ne yake bayyana tsadarsa, taci gwargwaro, ga gwala gwalai, gabana ya fadi don kyawunta ya wuce misali, ina isowa kanshinsu yadaki hancina, duk sai na jini na zama wata ga daini nan, donko nasan ko a kyau baxan kama kafa da itaba, muka kalli juna nida ita ido cikin ido sannan na dauke kaina na zauna, guda ta soma tashi, sai aka umarcemu da mu rufe fuskokinmu da kyau, duk muka rufe sai aka kira kannenshi wai su fara bude uwargda, rukayya ta bude fadi, mai guda tafarayi sannan danginta suka shiga zuba kudi, daganan saini, ummi ce ta bude fuskata nima, nima dai dangina sukadan watsamin abinda ke garesu, bandamu da kudin da aketa zuba musuba, musamman abkr don al'adace da addiniba, (inama ni suka bawa kudin nan) can kuma saiga iyayen fadi sun kawo faute wajen dangin abkr, kayan gado dan italy na kwali, da kuloli da sauransu, aka shiga sanarwa, rahma ta duko kusa dani tace ya za'ayi? Nafito musu da garar nace suma abasu, buhunan shinkafa talia, dasu dubulan da alkaki da yan samirun damukazo dasu, haka kuwa sukayi, basuce komaiba da aka basu, rahma tace suyi hkr bamusan yadda suke abubuwansuba shiyasa, nan naga anata raba kalandu zuwa jakunkuna da memo da jota, dadi sauransu, hotuna nake mamakin inda akasamu nawa, kamar tare muka dauka? To suna nufin tare muka dauka? Yana tsakiyarmu ya kwanta bayan fadima, nikuma na kwanta a bayanshi, dukkanmu muna daria. ina sanye da jallabiya, al'ajabi ya cikani, sai daf da magrib aka tashi, muka koma dakina, dama na kosa mu koma, na janyo daya daga ciki jakunkunan da akaba dangina nace, yaushe ne har mukai wannan hotunan ni hafsa? Rahma tai daria tace lkcn daxamuje gdan kwamishina, idan nace kizo muje baxuwa zakiyiba, shiyasa nahada baki da mai hotan yamiki baki saniba, computer kuma tatsara abubuwa, daman fuskarki kawai muke bukata kuma gashi munsamu, rahma tabude jakarta tace ga hotunan yanzu kigani, tabani na kalla, amma nace Allah ya isana amma, nace dubi yanda nayi acikinsu kamar wata yar aikinsu, badai shine yaji kuma ya ganiba inji rahma? Nace ga yanmatan nan kannenshi zasuyi rainin wayo, rahma tace, kedai tsakaninki da kowa mutunci, nace shima sai wani shareni yake, shiyasama da ana hotunan nan da danginsu ban cusa kainaba ciki, nayi zugum ina kallon fadima, kishinta nacin raina, nace rahma, fadima tana da kyau, ina zaton abkr yafi sonta, me kamar wannan mezai damu kansa dani kila ya aurenine don wata manufa, rahma ta mike cewa, saikiyi kuma, nikinga tafiyata zan sallah, gara ke hutu kike, saiki zauna kiyi tayi ke kadai, bayan sallar isha'ine aka kawo mana abinci cikin kuloli, nan aka shiga ci tare da lbrn karamcin mutanen yola, dan bikin nasu ya burge dangina, tabbas yola nima zance sunada karamci, ina kwance tunanin yanzu abkr yanacan tare da matarsa, sai mukaji sallama, rahma ta amsa, tace rufe fuskarki ga angonki nan, nace mezaizo yayimin? Rahma tace inya shigo saiki tambayeshi magulmaciya, koda baki fadaba nasan tunaninshi kikeyi, nace kada kimin sharri, tunanin me zan tsayayi? Kafin tace wani abun sun shigo, hashim yace sai mun sayi bake kenan? Naga amaryar tasha lullubi, rahma tace dame kake zato? Nan dai sukayi addu'oi tare dayi mana nasiha, sannan suka mikawa rahma kudi da ledar kaza, daya daga cikin wadanda bansaniba yace, to tunda anbiya saiki bude mana fuskarki mugani, nayi musu shiru, haka nan naki bude fuskar sugani, nayi shiru sannan suka mike dukkansu, abkr ya dubi rahma, saiku zama cikin shiri, kunayin sallar asubahi in Allah yatashemu zaku dauki hanya, tace to, abokan suka fita, rahma ma tafice, saini saishi, duk mukayi shiru, yana dai tsaye, yace, inbaki da mgn nizan tafi gurin amaryata, uwargidanki kenan saida safe, da sauri na dubeshi bayan na janye mayafin kaina, shima ni yake duba, bansan me yake zuciyarshiba, nidai tawa zuciyar kishine fal, na kauda kai cikin takaici nace, to dama akwai wanda yace ba amaryarka bace? Allah yabamu alheri, na mike tare da tura kofar toilet na shige, banjin fitsari amma dole nayishi, don banason tsayawa kusa dashi, dana fito yatafi, ina jiyosu sunayiwa sauran yan'uwana sallama afalo, Rahma tashigo, har kunyi sallamar? Nace na lura bazaki rike mijinki da kyauba, kada dai kimanta cewa ku 2 ne, nace um! Niba shine agabanaba, kuma bazan wulakanta kainaba, don na lura bana cikin yan kayanshi, abinda nasani shine, duk zaman daya zaba shi zamuyi, rahma tace shikenan, in kinyi tunanin yanda zaki kama mijinki a hannu kya kirani a wayata, tajawo ledar gabanta, bari mu tayaki cin kajin tunda ba ango, nace ke ango ya dama, niko ajikina, tace, abakiba, nan tafito da kaza daya, nace su dauka suka tace a'a, bansan meya hanani bacci ba wannan dare, alwala na dauro nazo na duka inata nafila, sai naji raina yayi sanyi harma bacci yana dibana, kacaniyarsu rahmace ta farkar dani, sunata shirin tafia, nima na tashi nahau shiri, rahma tace, waike inazaki naga kina diban kaya cikin karamin akwati? Nace kano mana, karatuna zanyi wasa dashine? Tace kun shirya hakan keda mijinki? Nace um! Zancen kikeso.Sai gasu sun shigo, waisu fito yan kd, nace ni yan kn zanbi, damasu mama sun tafi da shadad sbd makarntashi, na zura hijabina, yan gdan sun shigo sunata godia ga yan kd, tare dayi musu alheri wai inji lamido, turaman zannuwa ne da kudi na shan ruwa a hanya, har sun shiga motoci saiga abkr akan mashin ya tuko, yana sanye da farar jallabiy mai gajeran hannu, dama ina cikin tunanin watonba zayazo yayi sallama da yan'uwanama, kallo daya nayi mishi nakau dakai, duk sai naji haushi yake bani, musamman da zuciyata take rayamin cewa daga ganinshi yasha amarci, ina kallo shima yaciro kudi ya mika musu, motarsu tatashi ta nufi gate, na juya nabarsu nan tsaye dasu rahma, ko karyawa na kasa, duk tsananin son masa (waina) danakeyi, sagir yana kiran rahma waita shirya, nima na hau kintsi, rahma sai daria takemin. Can suka shigo dasu abkr, sai kamshi tare da kyallin goshi yake, daga ka ganshi ango dai sosai, yasha boyil mai ruwan kasa, hula minista baka, takami ma haka, suna gaisawa rahma tace, waida hafsa zamu wuce kn? Na zabga mata harara, wai nema? Ya dubeni da mamaki, mexakije yi kn? Nayi farin rashin kunya tare da murguda baki, menakeyi da jarabawa na tahowa zaman me zanyi anan? Rahma tace zaman aure, nace hum! Sai naga yayi murmushi, sagir yace, kibari ai angon zai kawoki ida lkcn zana jarabawar yayi, nace nidai gaskia tafia zanyi, idanuna suka kawo kwalla, sagir yace to abkr amaryar nan shagwaba takeji, abkr yace, tayi son ranta, amma tafia sai nai niyya, rahma tace ni tunaninama Allah yasa miyar nan bata lalaceba, sannan walimarmu tasha ruwa. Nace in kinje kirabawa makota, rahma tace to, narigasu isa wajen motar, nakama murfin zan bude, abkr ya dallamin harara, na matsa ya bude musu suka shiga.bayan tafiyarsu rahma, ina tsaye na cije lebe ina kallonsu, zuciyata tana tukuki, da sauri na juya daki, nafada gado ina kuka tamkar yarinya, tausayin kaina nakeyi, bansan irin rayuwar dazanyiba, kamshin turarensane ya cikamin hanci, don haka saina zaci yana tsaye, da sauri na dago kaina tare da waiwayowa, shine kuwa, yace sbd kina zaton za'a cinyeki shiyasa kikeson tafia ko? Na zuba mishi ido ban tabkaba, shima ni yake kallo, ya dauke kanshi daga kallona, koda yake dama bani kike soba, na sunkuyar dakai, yace gaba, ance so dayane tak! Kuma tuni kin dorashi kan wani, na dago da sauri muka hada ido, na juya mishi baya cike da suyan rai, kana nufin bana sonka? Yace basaina maimaitaba, in kuma ba hakaba, menene dalilin kukanki? Nadubeshi, duk wata amarya tanayin irin wanan kukan a wannan ranar, dole nayi kewar yan'uwa, yace ko? Amma dana zaci ba yauce rana ta farko dakika soma rabuwa dasuba? Gabana yafadi don na fahimci mgn yajefamin, ka iya fadin duk abinda ranka yaso game dani, don naga kamar don hakan ka aureni, na zauna bakin gado cikin bakin ciki tare da tausayama kaina, yatako ya matso kusa dani, don haka na aureki, kuma zanci gaba da fada miki duk mgnr da tazo bakina, sbd baki iya tauna mgn ba kafin ta fito daga bakinki, duk sanda na kalleki saina tuna cewa ke karuwa ce ada, na mike a fusace, zamanmu bazai yiwuba matsawar zaka dinga kallona wa wannan fentin, ya zauna kan madubi yace, waya shafa miki fentin? Inace kece da bakinki kika shafama kanki? So yajaki kika zubar da kimarki, kuka ya kufcemin, cikin kukan nake cewa, nikam tafiya zanyi, kasakeni.Yayi yar dariya ' ina sonki tsakanina dake babu batun saki. Tafia ce dai in kince zakiyi ta bazan sha mamaki ba tunda mahaifanki ma kin tafi kin barsu bare ni. Yanzun ma kya iya tafia in kinso ya juya ya fita, nace 'subhanallah' wannan wace irin rayuwa ce? Nayi kukana na qoshi sannan na share hawayena babu me bani haquri. Na kira Rahma suna hanya cikin dusasshiyar murya nace Rahma Abubakar yazo yaci mun mutunci ni gsky bazan iya zama dashi ba. Rahma tace meya fada miki? na sanar da ita komai tayi shiru na dan lkc can tace kiyi haquri duk laifin kine da kika sanar dashi ta bai baishi kuma mutun ne mai mita tare daqin saurare. Munyi munyi ni da sagir kan cewa ya sauraremu dan muyi masa bayanin gsky lamarin sai yace"Ai kin gama magana shi ba zaya iya jin wata kwaskwarima ba sannan yayanki umar yace masa da soyayya ya yaudareki kika bada kanki don haka yanzun shawarata itace kiyi shiru da duk abinda zai ce kada ki tanka shi. Na kula yanada mugun kishi ne nace ko gidan karuwai ya ganni yace yana so bai dace yazo kuma ya dinga ca6a min magana ba. Rahma tace kada ki damu zai zo ya yi nadama nace kinga dai ga jarabawar mu tazo bana zaton zan zana ta. Na sake rushewa da kuka shekara ta ta qarshe Rahama tace ki daina damuwa addu'a itace kadai mafita Allah zai kawo sanadiyyar da zaya fahinci gsky nace shi kenan. Ranar har magriba ban kuma ganinshi ba abinci daga cikin gida ake kawominsanda saudatu ta kawomin na dare na rana ko bude shi banyi ba. Tace ke kam baki san cin abinci gashi kina ta kuka kiyi haquri aure kenan zaki saba damu in kin saki jiki. Mu kam bamu da wata matsala nace to nagode nayo wanka don na fara sallah. Nayi shafa'i da wuturi sannan nayi shirin bacci sam bana kojin yunwa na hau gadona kwanta. Text ya shigo cikin wayata na duba shine angon nawa. Yace bazan samu shigowa ba don fadi bata san in fitavqila sai gobe. Duk suyan da raina ke yi sai na rubuta cewa Allah ya kaimu ka gaisheta. Na share hawayen da ya zubomin sannan naje na rufe qafata. Abubakar dake kwance kan gadon shi tsararre tun da ya shigo daha salkar isha'i yake kai kwance. Gaban mudubin dakin fadi ce tana fesa turaruka shi masu qamshi sanye take da rigar bacci me shegen kyau tare da ma'ana. Daga inda yake kwance yana kallan ta zuciyarshi fadi take ina ma ace hafsat ce haka a gabanshi. Me yasa ta fadi mishi cewa ita karuwa ce? Me yasa ta kasa adana masa kantahar zuwa lkcn da zai aureta?.Shin maza nawane suka kwanta da ita? Abinda ke sashi ganin ba zaya kusanta kanshi da ita ba kenan. Dalilai 2 suka sa shi auranta na 1 tsabar santa da qaunarta na 2 kuma..... Zaharaddeen Shomar whatsapp 08168575100 Sanadin Boko 3-07 Posted by ANaM Dorayi on 06:01 PM, 28-Sep-15 Under: SANADIN BOKO Na biyu kuma yanda yayi yaqi da danginsa don ya samu ya aureta. To sai da damar ta samu sannan yaji wannan muguwar maganar ba abin yace ya fasaba lamido ya ce don me? In kuma ya fadi dalilin shi zasu qara qarfafa al'adarsu tare da kafa misali dashi. A duk lokacin da wani yayi yunqurin auro yar waje a cikin family kai yasan sai lamido yasa an rubuta shi cikin kundin tarihin family dinsu. Gsky bai so hafsat ta furta zancan nan ba gaba daya haushinta yakeji shine mafarin daya tura mata wannan saqon don ya qara bata haushi. Zaman Fadi a bakin gadon yayi daidai da shigowar amsar dana bashi koda ya karanta sai kuma tausayi ya kama shi tamkar ya rubuta ban baki amma sai ya fasa. Ni kuwa sallah ke nutsar dani a duk lkcn dana samu kaina cikin damuwa don haka ita na duqa yi har nisan dare sannan na kwanta zucita wasai. Gsky ko yaushe ina alfahari kasantuwa ta musulma kuma ina roqan Allah ya kashe ni cikin musulunci. Da safe bayan nayi wanka na rufe jikina da hijabi na nufi 6angaren mutanan gidan daki daki na gaida su. Tsohuwa gwagwal itace tace min lamido yana gefanshi inje mu gaisa.Kan kujera na sameshi da carbi a hannunshi na zauna gefe sannan na gaida shi cike da ladabi yace yarinya hafsat ko? Nace eh yace to kina jin dadin zama damu? Nace eh yace to madalla kiyi ta haquri har zuwa lkcn da zaki saba damu. Sannan in kinga wani abu baki gane ba ki samu gwagwal zata yi miki bayanin komai. Nace to nagode ya ce babu komai na tashi na nufi sashe na na samu abin karina Kunun tsamiya da qosai nakai kicin na aje da yake ya kawo kayan tea sai na hada ruwan lipton na sha. Ai kuwa tamkar na tsokano yunwar don haka sai na tsiyayi kunun na sha da qosai Na shiga gyaran dakina na tsaftace ko ina sannan na saka turaren wuta na koma gado na kishingida. Can wayata ta soma ruri na duba Rahma ce na dauka muka gaisa tare dayi mata bangajiya. Ta sake bani haquri tare da shawarwari sannan tace min miyar nan da kaji duk tabai maqota sannan ta basu haquri game da batun walima kan cewa bamu zaci zaa wuce yola ba. Nace shikenan muka dan zanta sannan mukayi sallama.Ummi ta shigo da sallama cikin fara'a na tareta. Ta gaida ni cikin girmamawa sannan tace Dada da Abba suna gaishe ni nace ina amsawa na ce ga kunu da qosai a kicin tace ta qoshi don yanzunnan ta karya muka zauna muna hira. Tace aunty hammana yana sanki da yawa kiyi kallan yanda yayi rigima a cikin family dinmu dan ya aure ki? Nace haba wace rigima yayi? Nan ta shiga bani lbrn na jima ina mamakin wannan irin al'ada Nace kenan ba kwa sona? Tace muna sanki mana sai dai yanzu aikin kine ki koyama danginmu sonki da son duk wani bare dazai shigo cikin mu bayanki,nakalli yarinyar qarama da hangen irin na manya nace ta yaya zan koya musu haka? Tace aunty ke zaki fini sanin hanyoyin da zaki bi don su soki kadan din dana sani shine halayen kirki yin kyauta tare da sakin jiki damu Saura kin fini sanin halayen da zaki nuna a gaba in mun kawo bare in munce zamu aura baza a hana mu ba tunda basuga wani mugun abu daga gareki ba Nayi dan murmushi ummi kenan insha Allah danginku ba zasuyi takaicin da kasantuwata cikin ku ba. Kusan qarfe biyu ya shigo lkcn ummi ta tafi ni kuma na soma bacci A jikina naji cikin bacci ana kallona ko nace ana tsaye a kaina a hkl na bude idona Qamshi turaren sa ya daki hancina sanye da qananan kaya yayi kyau matuqa, bai san cewa na farka ba Ni kawai yake kallo ba wai fuskata yake kallo ba amma a hkk na yunqura na tashi ya dubi fuskata kin dai yi sallah ko kike bacci? Nace nayi sannu da zuwa yaya Fadima? Ga mamaki na sai naga yayi murmushi tare da cewa lafiarta kalau kenan yafi santa? Wayata tayi ruri ko ban sani ba Rahma ce wayar tafi kusa dashi don tana kan mudubi ya daga ya duba sannan ya ajiye nazo na daga muka gaisa tace na jiki sanyi dayawa har yanxu dai? Nace Rahma me zqi canja ni dai ki tayani addu'a Tace insha Allah taci gaba dama na kiranki ne in fada miki cewa na rabar da duj niyar nan da naman kada ya lalace. Sai dqi na rage miki kadan a gidana in kinzo sai kiyi amfani da shi Nace ki barshi kawai Rahma ta yiwu nazo kenan sa'adatu sulaiman ma dazu ta kirani ta fadamin cewa wai tamin test dina da suka rage nace mata to nagode Sai dai bani da tabbacin zanyi jarabawar Rahma tace insha Allah zakiyi nace Allah yasa nagode ki gaida mama da shadad baya rigima? Tace ai yaqi zama tunda ya ganni yaqi mama nace Allah sarki to sai anjima mukayi sallama Na dubeshi bazaka xauna ba emm......akwai abinci ya tabe baki am okay ba zama zanyi ba ki shirya inkaiki kuga juna da fadimana,na maimaita fadimarshi? Amma sai na danne na miqe na fada bandaki wanka na soma shi kam dakin yayi ta bi da kallo tare da shaqar qamshin turaren dana turare dakin dashi tun safe idanunshi suka sauka kan rigar baccina wadda na ninke ta kan gadona Ya dagata ya warwareta ruwan hanta ce mai santsi kalar ta mishi kyau zaya so ya ganta sanye a jikin hafsat Ya kai rigar ya dorata a fuskar sa a hankali yake shaqar qamshin ta irin wanda yasoma ji tun ranar da suka rage mata hanya motsin qofa ne yasa shi jefar da rigar ya kuma juya ma gadan bayatare kuma da sake hade rai. Na zauna gaban mudubi duk da cewar kayan ne a jikina wato da nayi wankan ban fito ba sai da na saka rigata. Na janyo mai na soma shafawa yace wai wanka kikayi? Ni fa ba nazo dogon zama bane Na dubeshi ya wani tsare gida bance komai ba naci gaba da murza mai a qafata ina yan shafe shafen su eye pend ya kuma katseni Kada ki 6ata lkcn gurin yin wani shafe shafe don bazaki tsorata Fadima ba a kyau " turqashi mu hadu a kashi na "4" na qarshe" Alhamdulillah. Wannan shine karshen littafi na "3", godiya ta musammam ga masoya kuma mabiyan Hausa Novel Zaharaddeen Shomar whatsapp 08168575100 Sanadin Boko 4-01 Posted by ANaM Dorayi on 06:21 PM, 28-Sep-15 Under: SANADIN BOKO Kalmar ta dake ni tamkar saukar aradu jikina yayi sanyi matuka.Tsam na mike daga gabn madubi na koma gado na zauna cikin matsanancin kunan rai.Sai naji tamkar mazaunan nawa ba zasu iya rike ni ba, don haka sai na kashingida tare da lumshe ido. Duk iya kokarin da nayi don na tsaida hawayen idona abn d yaci tura,sai da suka sulalo ta gefen idona, idon haguna kuma hawayen ya biyo ta karan hancina. Yayi dan murmushi ba shi da burin da ya wuce yaga 6acin ran Hafsat,duk da son da yake mata.In ya tuna yanda ta mike tana fada mishi cewa ita karuwa ce sai ya ji tamkar ya binne kanshi don takaici. Ya dubi ni Ki tashi mana kin wani kwanta. Na sauke ajiyar zuciya cikin sanyin murya na ce. Ban san cewa gasar kyau zamu je ba da ban 6ata lokacina gurin shirin tafiyar ba., Kaje ka bata Award din da ka tanada na mika wuya. Ya dan yi shiru. Kila yana nazarin maganar da na fadane can sai ya fita da cewa in kin gama ina jiranki a mota in har ina da izinin bada umurni. Tamkar kada na tashi,amma bani da damar yin haka,dole na koma gaban mudubi. Jallabiyata na saka baka mai ratsin ja, tana da tsukakken hannu shima ja, na nade kaina da dan mayafin, shima yana da ratsin ja. Takalimi da 'yar post din da na saka duk jajaye ne. Na feshe jikina da turare, da na kalli madubi sai nayi dan murmushi don nayi kyau. Zuciyarta ce dai ba dadi sakamakon maganganun da ya ya6a min. Na isa gefen direba in da yake zaune cikin sanyin murya na ce, bari nayi ma su Gwagwal sallama. Ya dago ya dube ni, muka kalli juna cikin ido. Da sauri na rausayar da kaina gefe tare da harde hannuwana a kirji, ya ce to kije mana kin tsaya min kerere. Na dubi shi, "Ai dama umurninka nake jira. Duk sai da na bi kowa gurinta na ce sai mun dawo,duk sun ji dadin cewa gurin Fadima zani. Abin da na lura shi ne, suna son a girmama 'yar uwarsu.Na dawo na shiga gaba kamar yanda ya bude.Tsararran gida ne mai matukar kyau, ga furanni masu bn sha' awa, ina biye da shi hr kyakkyawon falon. Wani dankareren zanen hotonsu ne yake fuskantarka an jingine shi da bango a kasa. Kallo daya na yi wa hoton na kauda kai, tamkar jinsin Larabawa ko Indiya. Ya dube ni ya ce," zauna, bari in kirata."Ya tafi yana fadin "Sweety.," Tamkar in toshe dodon kunne na don kishi. Na nutse cikin kujerar ledar mai kalar siminti. Na dinga bin ko'ina da kallo. Wasu abubuwan ma bn san su ba, ban ta6a ganinsu ba, daga karshe na maida kaina ga dankareren TV bangon da wasu Indiyawa suke ta rawa. Ba rawarsu ce ta birge ni ba, da har na tsura musu ido,tsabar takaici ne ke cina. Amma na lallashi zuciyata da cewa tayi hakur, na sani wata rana dai labari. Hannuwansu sarke da juna suka fito, kama suke sosai da shi,wani abu yazo ya tokare kirjina tamkar in rufe su da duka. Wata zuciyar ta ce, Tashi ki shaketa. Da sauri na ce, "A'uzubillahi minasshaidaninrrajim" sau 3 sannan na ce, Allah ka yaye min wannan duhun da ke zuciyata, ka bani ikon yin dauriya,kasa nafi karfin zuciyata. Suna isowa na mike tsaye,take naji zuciyata wasai, na saki wata fara'a wadda bn san ma ina da ita ba,tare da mika mata hannu. Na ce, Amincin Allah su tabbata a gare ki da rahamominsa da albarkatunsa. Itama ta miko nata tare da cewa, Amin kema amincin Allah ya tabbata a gare ki. Muka sarke hannu.Sannan muka saki na zauna itama ta zauna, ta ce, kullum ina son ki zo mu gaisa. Na ce"To ai yau gani nazo." Ta mike ta nufi gurin da nafi zaton kicin ne, shi kuma ya dauki remote yana canje-canjen tasha. Ya kuma ajiye ya nufi dakinshi, ta iso da kofin tare da kwalin jus a hannu fara'arta dai ba sosai ba. Ta dora kan stool ta dauko shi ta kawo gabana,sannan ta zauna. Na dauki kofin na jingina da kujerar ina kur6a ina kallon TV.Ta mike ta nufin ciki,dakin da ya shiga nan ta nufa. Dakin shi kenan,suka bar ni nan zaune. Tuni na dire kofin jus din don sai naji ya daina zakin sai daci, don tsabar takaici. Kusan minti 10 sannan ta fito shima haka. Ta shiga dakinta shi kuma ya nufo gurina, na kalli agogon bangon falon wanda hoton sune a jiki. Na ce, Tunda mun gaisa zan tafi gida."Ya dube ni "Nan ma gida ne. "Yar aikinta ta soma jera abnci kan dinning. Ta fito ta iso gurinmu "Honey kuzo muci abnci." Ya dube ni " tashi muci abnci . Na ce Tuni naci abnci. Ta ce, Ai kam ba ki isa ba, dole sai kin ci. Ni da ita muka jeru,

Chapter 17 of 22