Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
tasa nake ganin kamar son shi nake. Karshe ya cuceni, shima dama ba sona yake yi ba sha‘awa ce. Gashi dalilin abin da yayi min yasa na rasa abubakar sadeeek. har aka watse cikin aji ban sani ba. Da yake ni ba kawa ko aboki gareni a makaranta ba, babu wanda ya kulani. Kasancewar ko yaushe cikin daure fuska nake, masu son kulani ma tuni sun watsar dani, saboda rashin fuska. Ringing din wayata ne ya dawo dani daga tunanin da nayi zurfi acikin sa. Jikina lakwas na dauka. Nasan rahama ce, tunjiya take min nacin inje tana nemana, ba tare da na duba fuskar wayar ba na kaita kunnena. Muryar da tayi min sallama ce tasa naji na watsake. Bansan na mike tsaye ba, ina cewa. Wa‘alaikumus-salam. Yace, ina kike ne? Sai na samu kaina da wani jan aji, ina tambayar wanene? Da sauri yace, kina nufin baki ganeni ba ko? Nace, eh. Yace, good! Ki fada min inda kike sai inzo in sameki. Nace, ban gane kowanene ba ya za‘yi in fadi inda nake? Sai kurum ya kashe wayar shi. Take naji haushin kaina, mutumin da nake son gani ruwa a jallo amma yanzu na tsaya salo. Da sauri na fita na nufi gida, ko in biya in dauki shadad wai ina zaton yana kofar gidanmu. Ganin bashi na juya da sanyin jiki na nufi makarantar su shadad na daukoshi muka nufo gida. Hashim ya kali sagir yace, kaima kazo muje mu 3 don mu sami galabarta. Sagir yace, nifa shaknar hafsat nake ji, gashi tana bani girma kada taga zamu matsa mata. Rahama tace, ka daure kuje, kila ganin idonka ta sausauta. Abubakar yace, nifa hafsat nasani tana sona. Dalilin da take fadin cewa ba zai bari muyi aure ba shine nake son ji. Sagir yace, to ku tashi muje. Suka mike yana mitan cewa dan miskilanci irin na hafsa waima nine bata gane ba yau. Hashim yace, kai dai wannan abu yayi maka ciwo. Kasani ko kila bata gane kadin bane? Sagir yace, wannan yanuna kai kadai kake sonta, ita bata sonka kamar yanda kake zato. Abubakar yace tabbas tana sona, amma ku muje dai. Misalin karfe 8 na dare, Shadad ya yi barci, muna kan tabarma a tsakar gida, ni kuwa lokacin zuciyata ta kekashen idanuna sun bushe ina ta tunanin ina cewa, "Ya Allah, dama haka so yake?" Na tashi zaune, na mike tsaye, na jingina da bango duk banji dadi ba dai, zuciyata tana tuhumata da cewa nice na bar dama ta, me yasa na nuna ban gane shi ba? Sai kuma wata zuciyar tace ki daina saka kanki cikin matsala, ba zai aureki ba, keda kika yi cikin shege?!!! Na koma na kwanta, hawaye na sintiri a idona daga gefen idona zuwa kumatuna, so matsala ne, dama ban san Abubakar ba, dama ban zo Kano ba, dama ban je bikin Rahma ba. Bugun kofar ne ya sani na dawo cikin hayyacina, da sauri na mike cike da fatan shine, ba tare da na saka takalmi ba na nufi kofa, ban bukaci na san waye ba na bude kofa. Ganin shi tsaye ya sa na sauke wata nannauyar akiyar zuciya, sai kuma Miskilanci ya motsa na ce, "Daga ina? Ka canja ne ba kace ba zaka kara zuwa ba?" "Au korata kike? To shike nan bari na koma." Da sauri na ce, "Ni bance ba, ai ance bakonka Annabinka, ka iya shigowa." Ya ce, "Zaki ji da gulmarki. Hashim ku shigo." Na shimfida musu tabarma suka zauna, shi kuma ya zauna kan tabarma ta kusa da Shadad yana shafa masa kai, na kawo musu ruwa cikin jug, na nemi kujera 'yar tsuguno na zauna. Na gaishe su suka amsa, sai dai shi daya kafe ni da ido yana kallona, duk da ba wuta sai hasken farin wata, ya ce, "Ni ba zaki gaidani ba?" Na kalleshi irin hararar masoya, na maida kaina kasa. Ya ce, "Shine na kiraki dazu wai kike cewa baki gane ni ba." Shiru nai ban tanka ba Ya ce, "Ka gani ko Hashim ta gane ni." Sagir yayi dariya, "Kila bata gane ka din ba." Abubakar ya ce, "Bani aron hankalinki nan. Shi yasa na kwaso abokaina dan su zama shaida, da farko ina sonki, kuma ki ban amsa. Ta dago ta ce Abubakar bana sonka, ba aibu bane dan kince baki sona, in yaso sai sonki ya zama ajalina, amma daga yau idan har kinki amince min ba zaki kara ganina ba koda cikin mafarkine. Gabana ke faduwa, na ce, "To ai ban ce bana sonka ba." Hashim ya ce, "Pls Hafsa, magana daya zamu yi tunda kina da hankali tin taba aure bai kamata mu tsaya muna wasa da hankulan juna ba." Abubakar ya ce, "Magana daya ce Malama, kina sona?" Kalma daya ce da Hashim ya fada ta dagan hankali, wai na taba aure? Inama na taba auren ai da bazan damu ba, sam banji maganar da Abubakar yake min ba, su duk sun dauka aure nayi na haihu, to tun kan na samu matsala gwara na rabu da shi, sai dai sonsa ya zama ajalina, na ma rabu da iyayena ballantana shi? Tsawar da ya dakamin ita ta dawo dani daga tunanin da nake ya ce, "Kin maidani dan iska ne ina magana kin min shiru?" Hashim ya ce, "Ki yi magana mana Hafsa." Muryata ta soma rawa irinta masu kuka, "Lallai ina son ka har ba zan iya kwatanta son da nake maka ba. ..... Zaharaddeen Shomar whatsapp 08168575100 Sanadin Boko 2-08 Posted by ANaM Dorayi on 11:28 PM, 19-Sep-15 Under: SANADIN BOKO Domin sonka ya shigeni ne a lokacin da nake tunani na ha'ka dogon rami na saka so a ciki na rufe shi, ina fatan kowa ya mutu ya huta. Amma abin bakin ciki sai da ya fito har ya zo ya kama ni, a bisa adalci Abubakar bai cancanta na zam matarka ba, matsayinka na kamili, kada ka so kaji dalili ko ka matsa min na fada maka." Na kifa kaina a tsakanin cinyoyina ina kuka irin wanda yake sa jiki motsi, gidan ya yi tsit, gidan shiru kamar ba mutane.Abubakar ya ce, "Malama ki nutsu ki fiddamu daga tunani." Hashim ya ce, "Baiwar Allah ki nutsu ki mana bayanin komai, da kin san irin son da wannan bawan na Allah yake miki hakika da baki masa haka ba, ni abokinsa ne kuma dan'uwansa ne na jini, Mahaifina wan Mahaifinsa ne, tare muka taso kamar 'yan 2, ya san sirrina haka na san nashi, tunda muke da shi ban taba jin ya ce yana son 'yan matan da suke nacin sonsa ba, na kosa na ganki mai sa'a." Na dube shi na ce, "Ina son sa, kuma ina matukar farin ciki ace na samu mutum kamar Abubakar ya zama Uban 'ya'yana, amma kash!!!" "Amma kash me?" Sagir ya ce, "Dan Allah ki daure ki fada mana Insha Allahu za'a samu mafita." Na mike tsaye, "Ba wai ka aureni ba, da zarar ka ji matsalar, sirri ne zan fada muku." Na yi shiru, na yi ajiyar zuciya cikin kudurin gaya musu, "Amma ina so na gaya maka Abubakar ina sonka, kuma duk lokacin da ka tuno da ni ka tuna cewar na soka, zan ci gaba da sonka har karshen rayuwata." Na kalli Hashim na ce, "Za ka so dan'uwanka ya auri karuwa? Wadda ta bar gidan iyayenta saboda cikin shegen da tayi? Ta shiga duniya tana zaman kanta?" Abubakar ya mike zumbur ya ce, "Cikin in, in, wa? Wa kenan kina nufin ke karuwa ce? Cikin shege kika yi kika haifi Shaddad?" Na ce, "Kwarai kuwa, ciki nayi." Ban ankara ba naji saukar mari wanda idanuwana suka daina gani na wucin gadi, ya ce, "Tur da haihuwarki, kin cuceni da kika bar ni na fada son ki, Allah ya isa!" Ya fice fuuu!!! Sagir da Hashim suka bishi. Shadad ya farka a gigice sakamakon kukan da na fasa, na zauna kasa ragwab, ya zo ya fado jikina muna kuka tare da ina fadin "Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un. Allahumma ajirni fi musibati wa'akhlifni khairan minha." Mun yi kuka ya ishemu, amma har daga bisan Shadad ya yi bacci, ni kuwa tuni zazzabi ya rufeni hakanan hawayen idanuna bai kafe ba, abin da nake tsoro kenan rabuwa da Abubakar gashi nan kuwa, Ya Allah! Ya ma aka yi na fada masa zancen a baibai? Kafin safe ko motsi na kasa yi don zazzabi da ciwon kai, Ga fuskata ta kumbura sumtum saboda marin da Abubakar yayi min, ga kuma kukan da nayi, haka muka kawan gidan ko sakata ban iya samu na sa ba saboda azabar ciwo. Da asuba da kyar na iya tashi nai alwala, a zaune na yi Sallah, Shadad ma Sallah kawai yayi dan ba zan iya yi masa wanka ba, har 8 ina kudundune ban san me zai biyo baya ba. Shin Abubakar zai iya rabuwa da Hafsat? Ko Munnir yana sane da cikin da yayiwa Hafsay? Baba fa da bangaren Inna kuwa suna ganin Hafsa? Duk amsar tambayoyin nan Sae kun biyo mu a littafi na 3 Godiya gareku Zaharaddeen Shomar whatsapp 08168575100 Sanadin Boko 3-01 Posted by ANaM Dorayi on 11:29 PM, 19-Sep-15 Under: SANADIN BOKO Jikin abubakar sai bari yake, lokacin da suka shigo mota shida Hashim ne a baya, yayin da sagir ke tuki. Yace, innalillahi wa ina ilaihi raji'un, lallai na fada cikin jaraba. Dama Hafsat karuwa ce? Ya kifa kanshi ta baya. Hashim yace cool down my broos. Ka bi ahankali. Yace, Hashim daina cewa inbi a hankali, ka dai san promise da nayi dasu lamido kafin su yarda in aure ta, kuma ko yanzu ina kar kashin dokokin ne. Me kake zato in suka tashi bincike suka gano wanan matsalar? Sagir yace, amma sai dai in da ne tayi karuwancin, yanzu dai bisa tarin alamu batayin harkar. Abubakar yace, zazzabi nakejifa, ku kaini Asibiti. Hashim yace please Hamma kayi cooling mind dinka mana, wane irin Asibiti kuma? Yace Sagir dan Allah muje zazzabi nake ji. Sagir yace naso muje gurin Rahama, zamuji gaskiyar magana. Abubakar yace please, ku daina min zancenta, bana sonta, ba zan auri karuwa ba,zuwa wani lokaci bacci ya dauke shi, suka je office din likitan dan amsa kiran shi. Bayan sun zauna ya dube su a natse yace, ya shiga wata damuwa ne wadda lokaci 1 ta kumbura zuciyarsa, kokuma ya tsorata. Ya dan saurara, kafin ya cigaba da ce musu zai kwanta na dan kwanaki don kauce ma abin da zai biyo baya, sanan dole ne ya kaucema duk wani abu da ka iya tashin hankalinsa. Suka ce, to in sha Allahu za‘a kula. Suka dawo gurin shi suna dan tau tauna maganar Hafsat. Sagir yace, nayi zaton Hafsat tayi haka ne don Abubakar ya rabu da ita. Hashim yace, anya? Ni kam ina ganin rabon ba za akai mana bara gurbi cikin zuri‘a bane. Iyayenmu ba zasu amince da wanan auren ba. Sagir yace, amma Abubakar zai shiga wani hali in kayi la‘akari da matsanancin son da yake mata, dube shi fa lokaci kan kani yanda ya zama? Baka ganin zai iya mutuwa, zai fi masa sauki, in dai akan ya auri karuwa ne,zuri‘ar mu suna da tsuri, auran shinnan shine na farko da za‘ayi auren bare, kuma in yazo da matsala zasu kafa shi hujja ga yan baya. Sagir yace, hakane. Kusan 11 saura sagir yaje mota ya fito musu da dardumar sallah, sannan ya tafi taredacewa sai dasafe. Kusan karfe 4 dare Abubakar ya farka, jikinshi lakwas yake jin shi, kansa da kirjinsa kuwa sun masa nauyi. Ya dora hannu a kirjinsa, sam baya san tuno abin da ya faru ko kadan. Amma zuciyarsa ba zata iya amincewaba ko na sakon. A fili ya furta Hafsat! Hafsat!! Karuwa!!! Yai juyi ya kwanta akan hannun damansa. Allah ya cire min sonta, don ina da matukar kishi a kanta. Tabbas yana kishinta dayawa, da ya tuno ta taba aure sai yaji kuna a ransa, ina ma shine mijinta na fari! To ashe ma ba haka bane, ita Dattice, Bolace da kowane kazamin zai zo yazuba shararsa. Tir! Tir!! Da shi ya aureta. Ya sake juyawa. Tabbas nasan cewa idan ina son abu ina yimasa so tamkar rai, amma in naga zai bani matsala ina hakura dashi, nasan zuwa jibi zanji ta fita daga raina.Da wadannan tunane tunanen ya jiyo tada sallah daga massallacin da ke cikin Asibitin ya kai hannu ya dafa kan Hashim wanda ya jingina kansa bisa gadon yana bacci a zaune kan kujere Hashim ya bude ido Abubakar ya ce cikin fulatanci an kira sallah shima ya yunkura zai tashi sai yaji jiri yana diban shi ya komaya zauna bayan fitan Hashim da kyar ya lallaba ya tashi ya nufi toilet ruwa ya sakar ma jikinshi kafin yayi alwala sallar ma a zaune yayi ta don bazai iya tsayuwa ba kafin ya idar zazzabi ya rufe shi da likitan ya shigo ya yita masifa meyasa zai watsa ma jikin shi ruwan sanyi da safen nan? Lokacin da sagir ya isa gida Rahama na zaune, don duk ta damu sunyi dare. Ya shigo jiki babu karfi, ta dubeshi Hafsat takiko? Ya zauna yace, dauko mun ruwa in sha. Ta kawo tare da tsiyaya masa a kofi ya sha, sannan ya dube ta. Dama Hafsat ba yan uwanku bane? Tace, me kagani? Yace, ta fada mana cewa ita karuwa ce, zaman kanta takeyi. Rahama ta zabga salati, mai ya kai Hafsat yiwa kanta shairi? Ta rike haba cikin al‘ajabi. Yace, ga dai Abubakar can a gadon asibiti sakamakon furicin da tayi. Rahama tace, kuma? Yace, to wai menene labarinta? Nasan kinsan komai tunda tayi wanan furucin yanzu ke kadaice zaki wanke ta a gurin Abubakar, domin ance magana zarar bunu, in ta fito ta fito kenan. Rahama tace, gobe zaka yarje min inje gidanta dan muyi magana, idan ta bani izini to zakuji komai, ina zaton tace haka ne don ya rabu da ita. Sagir yace, in ko sun rabu zasu sha wahala, don itama ko da bansani ba yanzun haka tana cikin damuwa. Rahama ta shigo gidan, shadad tagani kan tabarma lamo da alamu yunwa yake ji, ko kuma damuwa bai da lfy. Tace, yau babu makaranta ne? Ina antyn taka? Yace, tana ciki. Ganin halin da take ciki ya tsorata Rahama, har tadau waya ta kira sagir, tace ta tashi su tafi asibiti, tace a a ta bari mutuwa zatayi, amma ga amanar yaron ta nan. Tace, in kinje kaduna inda na fada miki lokacin da nake baki lbrina, zaki sami lbr iyaye na, ko da baki samesu ba kice suyafe mun. Ki nuna musu dana shima ya san dangina. Rahama tace, haba hafsy, kitashi wanan ba ciwon mutuwa bane, ciwon son Abubakar ne, kuma in sha Allahu zaki sameshi. Ta fita, sagir kazo kayi mata magana. Da kyar ta yarda ta bisu saboda magiyar da sagir ke yi mata. Asibitin da yake suka kaita, likita ya dubani wai nima zuciyata ta motsa, kuma jinina ya hau.daga nan sagir ya tafi dakin da Abubakar ke kwance ya sami Hashim na waya, shi kuma yana kwance. Yaba hashim hannu suka gaisa. Sanan ya nufi gun abubakar bashi hannu shima suka gaisa. Duk da cewa abubakar din da kyar yake magana, yace Sagir kasa Rahama ta kawoma Hashim abun karyawa, saboda yana da ulser. Sagir yace, Rahama tana gurin Hafsa a nan asibiti, ta je tasamu halin da take ciki takirani muka kawota nan. Da sauri ya mike me ya sameta? Sai kuma yaja tsaki ya koma ya kwanta. Sagir suka bari suje suyi take away. A hanya sagir yake ba hashim labarin abin da ya faru har suka kawo hafsa nan . Hashim yace yanda za‘ayi yanzu zamu samu Rahama ta bamu duk abin da ya faru. Sagir yace, kaji batu. Ko kallon inda suka ajeyi abincin da suka suyo mashi bai ma yiba, ya damu kwarai. Wayarshi dake hanun hashim tayi kara, hashim din ne ya dauka. Abba ne. Yace tuk da kuka kiramu da kuka sauka har yanzu shuru, ko lafiya? Hashim yace, Abba akwai matsala fa. Da sauri Abubakar ya duro dakarfin da bai san yana dashi ba, a hankali yace kada ka fada mashi komai game da Hafsa please. Hashim yace, abba kace me? Bana ji? Abba yace me ya faru nace, kun samu wata matsala ne game da yarinyar? Hashim yace, Abubakar ne bashi da lafiya, yanzu haka anbamu gado muna asibiti. Subuhanalilahi!Me yasameshi har haka? To likitan dai yace ciwon zuciya ne, zuciya ne e dan kumbura. Inji hashim. Abba yace, ikon Allah! In sha‘Allahu gobe muna zuwa. Hashim yace to Abba sai kunzo. Abubakar yace kace da sauki, ni kam ba sai sunzo ba. Duk da haka Abba yace zasuzo. Zuciya ai ba abun wasa bane, da suka gama wayar Abubakar yace, kai dai banza ne, wa ya fadanmaka ana fadin ciwo? Hashim yace, da fa zan fadan mishi matsalar Hafsa ne kace a a ba dole in fada mishi ciwo ba, tunda bani da mafita na riga dai na fara fada.Abubakar yace, ko sunzo kada kayi musu maganar hafsa, na san yanda zan warware matsalar, domin insukaji Hafsat karuwace to fa zasu kara reke wanan al‘adar da hannu biyu. Kaga kokarina na baya ya zama banza, har yan gaba ba zasu amfana da komai ba. Amma in munyi shuru koni banyi ba kannan mu zasu iya yi. Hashim yace, shikenan. Amma itama zamuyi bincike. Abubakar ya kalleshi da sauri, zakuyi binciken me? Bana son wani bincike, ni na hakura da ita. Hashim yace, gama malam bana son gadama, yanzu bagaka a gadon asibiti kana ciwon so ba? Abubakar yace, inji uban wa yace maka ciwon so ne? Ai ni tun jiya na daina sonta, ciwon daga Allah ne, sai kace wani wawa zan tsaya ciwo akam mace kamar a film? Film din ma na indiya? Sagir da ke jinsu yayi dariya tare da cewa, kai da ita duk cutar so ke damun ku, don haka ku nutsu zamuyi bincike. Abubakar ya hade rai kunsan Allah, wlh na fasa. Hashim yace harda rantsuwa? Abubakar yayi tsaki ya kwanta. Washegari su Abba suka iso su 5, harda dada, amma yan da suka ganshi duk sun damu. Bawai jikinsa ya tsananta bane, amma yana cikin damuwa. Likita ya fada musu matsalar zuciya tana da girma, subishi a hankali, kuma damuwar da yake ciki suyi kokari su kau da ita, sukace basa zaton yana cikin wata damuwa, aMMA zasu zauna dashi. Abba da baffansa guda 2 da dada da kuma gogonsu kuma surukarsa, wato gogo jami, suka sashi gaba bayan sun gama cin abincinda Rahama ta girka musu. Sukace ya sanar dasu damuwar shi, nuna musu yayi ba komai, ciwo ne kawai.Goggo jami tace, ina hafsatun? Da sauri yace taje kaduna, dama nan ai karatu tazo, to bamu sameta ba, amma zata zo gobe don ban fada mata bani da lafiya ba. Hashim ya saki baki yana kalon Abubakar, amma bai ce komai ba. Sagir shine ya sauke su yayi dawainiya dasu. Su dada gidan Rahama suka kwana, yayin da maman rahama ta zauna dani. Dada ke tam bayan rahama game da halayane, wai ance ni kawarta ce. Rahama tace tana da tabbacin ina da halaye masu kyau da biyayya. Washegari suka juya tunda yana tare da Hashim, ni kam ban san yana Asibitin bama, bana ganin kowa daga maman rahama sai sagir da rahama.shadad ma yana can gidan su maman rahama da mahaifiyarta. Hashim da sagir sun fita sun bar abubakar kwance yau har kwana 3, amma baiji son Hafsa ya girgiza daga zuciyarsa ba, sai ma son ganin halin da take ciki da yake. Tunda aka ce mashi bata da lafiya tana kwance a Asibitin. Yaji ranshi ya kasa kwanciya, gashi tun da yace masu sagir baya son jin labarinta suka daina zancenta. Dan haka bai san koyaya jikin nata yakeba yanzu. Ya mike jiki babu karfi yafita, da nurse suka ci karo yace mata wane daki ne aka kwantar da wata Hafsa? Ta nuna mishi ta wuce. Ya nufi gurin, ta window ya tsaya yana kalonta tana bacci. Ta rame matuka. Gadonta na jikin window ba kowa a dakin, tamkar ya shiga a fili yace, me yasa kika cuceni? Me yasa kika zama kazamar rijiya wanda kowane kazami zai jefa kazamar gugarsa? Ya lumshe ido tare da sauke ajiyar zuciya. Ina sonki Hafsa, ban taba ganin abin da nake so ba irinki. Ya juyawa window din baya, wasu kananan kwala masu dimi suka biyo gefen idon shi,kin cuceni. Ya sa hannu ya share idon sa, dai dai lokacin da ya hango su Hashim, nan take ya soma tafiya dan barin gurin. Sagir yace, ina kaje? Ko gurin Hafsa kaje? Tsaki yaja, inje in mata me? Na dai dan taka ne. Suka kalli juna sukayi murmushi, Sagir da Hashim. Sannan sagir yace, Abubakar ba‘a yiwa so miskilanci, ka nutsu a warware komai. Hashim yace, daga gurin Rahama muke, tayi mana bayanin gaskiyar lamari. Abubakar ya dubeshi da sauri ta taba aure ko? Tana tsokana tane dan na barta ko? Hashim yace a a bata taba aure ba Abubakar yaja tsaki. To ba zan saurareku ba, in bata taba aure ba ina ta samo yaro? Agurin karuwanci? Ya nufi cikin daki yana fadin ada na tsani inji an ce ta taba aure, duk da ina matuka son danta, amma yanzu har fata nike so nake inji an ce auran ta taba yi. Sagir yayi ma Hashim alama da hannu, wai ya kyale shi. Ni kam dama ina da tsohon ciwo na a jiki bai taso ba, sai yanzun da yaji ni a gadon asibiti. Yau in likita yace nan ne ciwo kaza ne, gobe sai yace har da kaza ma, yau da ya shugo kuma ya gama duba ni, wai zama asamin jini. Na bude ido da kyar, jini? Na fada a hankali, yace, eh mana, jininki ya tsotse, dama tunda kukazo baki da ishashen jini. Maman su Rahama tace, saya za‘ayi ne? Yace, eh to, da dai tana da wasu yan uwa haka sai su bata, in da wanda zai iya bata, don ba mu cika son siyan jini ba. Mama tace, to bari su shigo muji. Bayan yafita nace, mama wai wanene ke dawaibiya dani? Mama tace, to ni dai ban sani ba, ko wanene cikinsu? Oho! Ni dai likitan bai taba kawo kaza ba. Zai kawo magani, kuma zaizo ya dubaki, don haka bansan wanene ke daukar nauyinki ba. Lokacin da sagir suka shugo da hashim, mama tace likita yace sai an sa jini a jikinta,suka ce, sagir yayi mana bayani, anjuma zamuzo a gwada jininmu. Nace nifa zanfi son ku barni in mutu. Mama tace, kuje ku kyaleta. Aikinta kenan zancen mutuwa, kuma nasan da zataga mutuwa guduwa zatayi. Su sagir suka sa dariya, ina so in tambaya shi wanan dan uwa Abubakar dama a nan yake in kuma tare suka zo in Abubakar din? Ina son sanin halin da yake ciki, ina ma wayata? Bansan cewa a fili nayi yambayar ba, sai da naji mama tace. Wayarki tana hannun rahama, ta kira gurin aiki ma ta fada musu ma. Shuru nayi ina tunanin tare da fatan bataji sauran zantukar zuciyar tawa ba. Suna fita suka nufi gun Abubakar, can kusan minti 30 likita ya shugo ya dubi Abubakar yace mishi ina ganin kai zuwa gobe zamu sallame ka. Yace, Allah ya kaimu. Ya dube Sagir, ku kuma muje a gwada jininku din. Abubakar ya dubesu da sauri, lafiya? Hashim yace Hafsat tana bukatar jini. Abubakar ya tsurawa Hashim ido, jini kuma? Kikita yace kwarai kuwa. Daga nan bai sake magana ba, ya dauki wayarshi yana dan danawa, amma cikin zuciyarshi a rikice take, kadafa ta mutu! Suna fita yaga sun nufi gefab dibar jini da gwajin su, nan da nan ya nufi dakin da take. Bai shiga ba ta window ya tsaya yana lekenta. Tana kwance, amma da alama idonta biyu. Rahama tana zaune tana cin abinci. Yayi tamkar ya shiga, amma sai ya fasa. Ya fita harabar asibitin ya nemi guri ya zauna karkashin wata bishiya. Ya saka fiskarshi cikin tafukan nannayenshi, yanzu ya gama gane cewa soyayayarsu da Hafsa wata mai wahalar fassara ce. Muhimmiyace kuma hamshakiya. Ba zai taba daina sonta ba har abada. Menene mafita? Wata zuciyar tace mafita kenan, ka aureta. Hashim ya fada a bayan shi. Abubakar ya dago kai, idonshi jajir. Hashim yace, don Allah ka sama kanka salama, kana son Hafsat ka aureta. Abubakar yace, ba zan iya kwantar da hankalina ba, kasan kuma aure da zargi yana bata aure ko? Please, bar maganar aurenan ba zan iya ba. Ya mike ya bar Hashim a gurin, cikin ta kaicin rashin sauraran shi da Abubakar baiyi ba. Kai-tsaye ofishin likita ya nufa, yana zaune kan katon tabirin shi yana ta hada wasu fayal. Ya dubi abubakar. Ranka ya dade ya kakara gyagijiwa kenan? Abubakar ya zauna kan kujera batare da ya nemi iziniba. Ya dubi likitan. Likita wai me ke damun yarinyar nanme? Likita ya tatara hankalin shi gurin Abubakar, kana nufin sister dinka? Abubakar yace, eh. Likita yace, gaskiya bata da lafiyap gaban Abubakar ya fadi. Me ke damunta? Likita yace, tanada hawan jini, ga zuciyarta ta dan tabu, typoid ma tana dashi, dan muna zaton shinema ya tsotse jininta. Yanzu haka tana bukatar jini, muna gwada na sauran yan uwanka ba zai yi ba, amma da irin naka ne zaka iya ba kowa jini. Sannan mun sami jininta dan da ya hau ya sauka. Abubakar yace, likita ina so kudibi jinina kusa mata. Likita yace, kaima baka da lafiya, don haka ba zamu dibar maka jini ba. Yace, bani da ishashen jinin ne? Likita yace, kana da jini don jini. Yace, to a diba saboda ko ba ku diba ba zanje wani gurin su dibain kawo,in ma shi kenan ya rage min zan hakura ita ta rayu.shuru likitan yayi, can yace in na diba zan fasa sallamarka gobe. Yace dama ko ka sallameni sai na jira ta. Likita yace, matarka ce? Abubakar yace, ina fatan haka in Allah yaso. Sanan don Allah kada ka fada ma yan uwa na nine zan bada jini, shi kuma abu na gaba, inaso kayi mata gwajin (H I V) don Allah. Likita yace, in sha Allahu zanyi. Yace to jinin yaushe za‘a diba? Likita yace, gobe ne. Yace to in Allah ya kaimu sai adiba. Amma jikin nata yana sauki ko likita? Ya cigaba don Allah aluran min da ita sosai. Likita yace, tunda ka fadamin ko ita wacece to za a duba ta fiye da da. Yace to na gode, game da kudi ba matsala, na fada maka ai. Yace, nasan haka. Washegari sai dai sukaga basu ganshi ba da safe. An dibi leda 2 suka tace, duk da sunce ba komai a cikin sa. Aka

Chapter 13 of 22