Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
riga da wando blue jeans, riga baka. Takalminshi sau ciki bakake, sumarshi tanata sheki baka wuluk. Kamshin turaren jikin shi ya cika gurin, ya shigo shadad ya kwaso da gudu ya nufo shi. Sama ya dagashi yana cewa, serious student, har ka shirya? Nace, bari nayi maka shin fida. Yace a a zo mu kaishi tukunna. Na saka hijabi muka fita, muna direshi a makaranta yace min shifa yunwa yakeji, nace to yanzu yaya za‘ayi? Mukoma gida inmaka indomie. Yace an ta cin abu 1 kenan? Muje gurin abinci nikam yau masa zanci, nace nifa bana son abin siya, nafi son komai inyishi da kaina, yace zakiyi min masa? Muje kasiya lokaci ya kure.a zatona in yasiya gidanmu zamuwuce, sai naga mutum ya nufi wata hanyar, masaukin sa ya kaimu na dube shi gaskiya sadeek ba zan shiga hotel ba, babu mutunci gareni matsawar aka gani cikin nan. Yace nafiki kishin hakan, ba dan dani bane zamu shiga nan ba zan aminbe ki shiga ba. Muka shiga daki tamkar a gidanka. Ya zauna wai muci waina, nace a a ba zanci ba. Yayi nace ni bana cin masa, nama karya fa. Yace ban yarda ba kice dai kina jin kunyata, nace nifa na kosa inji maganar da zamuyi, inada kagara. Yace, bari in gama. Sai da ya koshi ya dora da ruwan shayi da yasa aka kawo masa, sannan yace to kafin inyi maganata, zanyi maki tambaya 1 rak! Nace to, kina da aure? Nace a a, yace to gaskiyar magana ba wata kwana ko dogon turanci, ina sonki zan aureki nan da yan watannin da basufi 2 ba....da sauri na mike saboda zantukan da naji suna yawo a kwanyata, na nuna shi, kana sona? Ni kake so? Na bubuga kirjina, yace com down my hafsy, ki tsaya mu fahimci juna. Jikina ya soma bari, jin ya ambaceni da hafsy, sunan da munnir ke kirana dashi, da ina son sunan aman yanzun in da sunan da na tsana to shine. Nace, nina sani, dole dawainiyar da kayi ka nemi ka fanshe, to karya ne kakeyi ba kai bane wannan bawan Allah mai tai mako don Allah, kaima cutata kake sonyi. Da gudu na nufi hanyar fita ban san ya akayi ba kawai na tsince shi gaba na yayi key din kofar. Yace, ki saurare ni, bana nufinki da komai sai Alkairi, nace bana so. Jikina kake bukata. Tsaki yaja ya koma ya zauna yana kallona, na jingina da kofar ina kuka, har na gama bai hanani ba. Yanata dan ne dannen wayar shi, nagaji nace ka bude mun kofa, yace in kinga kin fita anan to kin saurare ni, kuma amsar cewa kina sona zaki aure ni, nace bana sonka. Yayi murmushi, karya kike kina sona, haushi ya kara kamani, nace ni bana sonka, Allah ka bude mun kofa in tafi abina.Maimakon amsa da naga ya mike ya nufi gadonsa ya cire rigarsa da farar singileti, ya hau gadon ya kwanta, kauda kaina nayi ina tura baki, ina cewa indai sai nace ina son ka sai dai mu shekara a haka. Wasa wasa har lokacin sallah yayi, ina kallon shi lokacin na gaji da tsayuwana tsuguna, yayo alwalar shi ya tada sallah. Nazo kan gadon na dinga neman key har ya idar ban gani ba, na koma inda nake, ya kira wayar Sagir wai don Allah ya fadawa Rahma karfe biyu taje makarantar su Shadad ta dauko shi ta tafi dashi gidansu, mu munyi tafiya. Ya dube ni, ki shiga kiyi sallah, na ce in naki fa? Ya ce ki gamu da Allah. Ya fada kan gadon shi ya ci gaba da bacci. Ina ta neman makullin ina sanda, amma Allah baibani ikon ganin sa ba, don haka naje nayo alwala nayi sallah. Ina zaune ina tunanin anya kuwa wannan dan tahalikin cutata zaiyi? Amma bari ya tashi na gwada yi masa dabara duk da naga shima kar yake kallo na, amma da macucci ne da tuni ya aika abinda zuciyarsa take so. Daf da la'asar ya farka, ya shiga bayin nake zaton ruwa ya watso da naga ya jima kuma ya shiga da wasu kayan, ya fito yayi sallah, sannan ya ce nifa ina jin yunwa. Na hada rai na ce to ni ina ruwana, ya ce ke mijinki yana jin yunwa zaki ce ina ruwanki? Na ce ni dai ka bude ni in tafi. Ya kira waya wai a kawo masa jalof din shinkafa da farfesun koda. Ya dube ni me zaki ci? Na ce nidai burin in bar nan, ya share ni. A raina na kudurce ana kawo masa abincin zan fice koda tsiya, amma ana danna kararrawar kofar sai naga ya zuge gilas din window yayima ma'aikacin magana ya amsa, ya zauna yana ci yana waya da Hashim cikin fillanci jifa jifa yakan sako hausa, anan ne na gane zancena yake yi, lokacin da yake cewa Allah Hashin in zamu shekara anan sai randa ta saurare ni zata fita, ya sake juyowa ya ci gaba da fillanci. Ni kuwa nayi zugum kamar wacce take neman gafara, ganin yamma tana kara yi bansan abinda zai biyo baya ba idan dare yayi, don haka na ce bari na saurare shi, kafi sannan bari na gwada dabarata ko da lalata yake sona. Sai da ya gama wayar na ce to naji zan saurare ka, amma banda yau. Don yau ina azumi ne, in ma jiki na kake so ka bari gobe zan baka. Ya dube ni da sauri, jikinki? Ina jikin kin yake? Ya ja tsaki banga jiki anan ba, ni ke nake so, zatinki na ke so ba jikin ki ba, kin tsaya kina zabga min karya wai kina azumi. Ki tsaya muyi magana shine mafita, amma har wani jiki kike dashi? Na ce in ba jikina ba me kake so? Ya ce halayenki da ke kanki nake so, inna sauraroka, yi batunka. Ya ce tashi ki matso nan dan bazan iya daga murya ba kamar fada. Na dan matsa ya ce bana bukatar sai kince kina sona, na riga naga sona a idon ki, fada min inda su Baba suke in tura magabata na, nayi shiru, tunani nake ga garin zuwa amma babu zanin daurawa, lallai zanso haka sai dai nasa in Abubakar yaji labarina bazai aure ni ba. Sannan in shi ya yarda iyayen shi baza su yarda ba. To ni da na shigo duniya ma yaya za'ayi mutum mai mutunci ya aure ni? Yanzun ma ina zan san inda iyaye na suke? Tunda nasan ba gidan kanshi yake ba, gidan haya ne kila yanzun ya tashi... "Ba ki bani amsa ba." Ya katse ni. Na ce ni fa kaga ka kyale ni, bazan aure ka ba, ya ce nasan kina tunanin ki fada min kin taba aure kada in ce bana son bazawara, to kin min kuma zan aure ki a haka. Shike nan? Takaici ya sa wasu hawaye zubo min, nace a raina da na taba aure me zai hana ni fada?" Ya ce ki fada min damuwarki bana son kuka. Na ce, ina rokon wata alfarma a gurinka, don Allah ka zauna a matsayin yayana, mai bani shawara in bukatar hakan ta taso, ka zam mai min fada a duk lokacin da nayi ba daidai ba, na dube shi in nayi abin duka ma ka doke ni....." Na fashe da kuka tare da sa kaina cikin hajabi. Ya zo ya tsuguna a gabana, ban sani ba sai da naji muryarsa dab dani. Abin zaifi armashi idan kika amince na zama mijinki majibancin lamuranki, mai saki cikin farn ciki, mai kare lafiyarki da mutuncinki, hanyar shiga aljannar ki. Hafsat ina so da kaunarki, ki amince. Wallahi nasha alwashin zama dake har karshen rayuwata, bazan sake ki ba yanda mijinki na baya yayi, zan rike danki tamkar ni na haife shi." Na dago ina kallon shi, shi zatonshi na taba aure mijina ne ya sake ni, ina ma ace haka ne? Da tuni nayi magana. Na ce kayi hakuri duk ba wannan bane, don Allah ka kyale ni kawai yanda ka ganni." Shima shiru yayi. Can ya ce. "To naji, yanzun ki fada min inda mahaifanki suke kawai." Na ce ban sani ba, wallahi ban san inda suke ba. Ya ce to shike nan share hawayen naki in maida ke gida. A cikin mota ni dashi kowa tunanin shi daban. Motar tsit kamar babu kowa a ciki. Shi a tunaninshi kila bayan nayi aure baban Shadad ya sake ni nabar gida, kila Iyayena suna son in koma gidan mijina ni kuma naki. Ni kuma tunani na shine zanso matuka Abubakar ya zama mijina, don wannan gata ne Allah yayi min in dai na same shi a matsayin miji. Amma nasan da wahala in zai ji labarina ya aure ni. Ya tsaya kofar gidan mu jikin sa sanyaye, ya kifa kanshi a sitiyarin mota. Na bude kofar motar tare da cewa sai anjima. Ya zaro wayata daga aljihunsa na baya ya mika minn ni na manta ma ina da wata waya, na karba jiki babu kwari na shiga gidan sukuku, nayi sallolina na zauna cikin tagumi , Allah nake roko ya zaba min mafi alkhairi. Misalin karfe takwas suka shigo shi da Shadad, yau har cikin dakina ya shigo, Shadad ya zauna a jikina shi kuma ya tsaya da leda a hannun shi. Ya ajiye min ledar. "Kici wani abu zan kira wayarki anjima. Gobe da safe zan wuce kila na biyo." Sai naji har raina bana son tafiyar tashi, sai dai bani da izinin hana shi. Na bude ledar kaza ce da madara mai sanyi, rabona da cin kaza tun lokacin Hajiya Hindu Likita, Allah ka yafe mata har in gushe bazan daina mata addu'a ba. Na ci na koshi, Shadad dama da guntun baccin shi ya shigo, yana zuwa yayi bacci. Nayi shafa'I da wuturi na kwanta. Sam bana jin bacci zuciyata ce ma take ta azazzala ta tare da fada min bazata juri Abubakar ya subuce mata ba gara ma in san abin yi. Na kosa ya kira ni, sai gurin sha daya da rabi lokacin na debe tsammani da kiran sai ga wayata na ruri. Na daga da sauri don marmarin jin muryarshi. A tare muka yi sallama, sannan muka kara hada baki gurin amsawa. Ya ce kin fara bacci ne? Na ce a'a" ya ce ki fada min tsakani da Allah ki kasa bacci saboda menene?" Na ce bazan iya ce maka ga dalili ba." Yayi shiru, can yace sona ne ya hanaki bacci kamar yanda sonki ya hana ni. Muna son juna mezai hana ki bani hadin kai muyi aure? Duk abinda kike so zan maki Don Allah ki tainake ni Hafsat." Muryata can kasa, jikina yayi lukwi nayi juyi zuwa ruf da ciki. Sannan na ce in nace ba jin wani abu mai kama da so a tare dakai, hakika nayi karya. Sai dai in na saki jiki zuciyata tazame da sonka, a karshe zan sha wahala, duk ranar da kasan who I am. Ya ce ki fada min komai, bazan taba gudar ki ba, don kin sami wata matsala ko kina da matsala da iyayenki zan fahimce ki sosai. Na ce zan fi so in kabar batun aurena, ya ce in yi yaya da sonki to?" Na ce hakuri mana, nima hakuri zanyi." Ya ce amma da gaske kina sona? In na duba wasu abubuwa zan iya yarda cewa ina sonka, kai kadai ne kasa ni in manta alkawarin da na dauka na cin mutuncin duk wani namiji da yayi min kallo fiye da daya. Kaine kake sani inyi abinda ban niya ba. Ya ce har kin sani naji sanyi a zuciyata, don Allah ki taimaka muyi aure. Gidan mu an matsa min in fito da mata, yanzun haka an bani lokaci." Na ce dama baka da mata? Ya ce ina da mata, na ce to bazan taba auren ka ba don na san wata rana zata yi min gori. Da saure ya ce bani da mata wasa nake maki. Na ce duk da haka kayi auren ka ni bazan iya aurar ka ba, hirar mu daga jayayya sai zance soyayya, tare da magiya. Abin al'ajabi sai na jiyo kiran sallar farko. Na ce, "Sadeek kaji abinda naji kuwa? Ya ce me? Na ce, kiran Sallah fa." Ya dubi agogo yanzun nan fa muka fara magana, na ce shi ne nima na gani, to zaka shigo kafin ka tafi? Ya ce bazan shigo ba, kuma bazan sake zuwa kano ba tunda kince baza ki aure ni ba, kin kuma ki fada min dalili. Bance komai ba har lokacin da yace min sai wata rana, ya kuma kashe wayar shi. Zaharaddeen Shomar whatsapp 08168575100 Sanadin Boko 2-7 Posted by ANaM Dorayi on 11:27 PM, 19-Sep-15 Under: SANADIN BOKO Munir ya dubi mahaifiyar shi, fuskar shi babu walwala. Ta ce ya akayi? Ya mika mata takardar hannun shi, sakamako ne na gwaji ya amso, da sauri ta mike tsaye HIV? Subhanallah! Muje wani asibitin, ya ce Momy tun daga Dubai suka fada min ban yarda ba, sai da nazo nan na sake yi har kashi biyu, ta dauki waya jiki na bari ta kira Dady a waya. Kuka ta saka masa tana fadin Munir yana da kanjamau. Shima Munir din kuka ya saka, a sukwane Dady ya baro ofishinsa zuwa gida, ganin su cikin halin damuwa harda kannan shi, sai hankalin Dady ya kara tashi. Ya ce ku kwantar da Hankalin ku zan shirya mana zuwa America za a duba shi." Momy ta ce, zan fi son haka. Shi kadai ne ya rage min yanzun tunda yayanshi suka yi fada suka kashe kansu a Maleshiya, yanzun kuma a ce shima yana da kanjamau?" Cikin kankanin lokaci suka shrya suka tafi. Sai dai kash! Can ma sun tabbatar yana dauke da ita. Sai dai sun basu wasu maganguna cewa ya dinga sha, sannan idan sun zo nan ma ya dinga shansu. Jiki babu kwari suka dawo. Sannu a hankali ya hakura ya cigaba da zuwa aikin sa, yana shan magani. Sai dai koda yaushe yana zargin mahaifansa sune suka ja masa wannan halin, SANADIN BOKO. Da sun bari yayi aure ya tabbata baza ya zama daya daga cikin masu neman mata ba, gashi yayyanshi sun mutu su biyu. Shi kuma ga halin da yake ciki. Ya hadu da wata yarinya 'yar mutunci, Usataziyya a rufe cikin hijabi da nikabi, ya ce yana sonta. Tuni ya fara zuwa shira. Yarinya mai suna Nanah A'isha ta amince dashi, sam bai fada mata yana da ciwo ba, kuma ya gama sheke ayarshi, kuma yanzun 'yar mutunci yake son ya aura don cuta. Iyayenshi ma basu nuna masa abinda zaiyi bai dace ba, sai ma suka shiga lamarin suka yi dumu dumu suka yi ta barin kudi aka sa bikin. Wani daga cikin abokan Munir yayi mata text ta waya wai Munir yana da kanjamau, ko ya fada mata? In kuma bai fada mata ba to ta sani yanzun. In kuma tana musu to ta gayyace shi suje ayi gwajin jini. Nanah ta firgita kuma ta sanar da mahaifanta. Sune suka nemi Munir da ya zo suje ayi gwaji, nan da nan ya zuke daga nan kuma sai ya samu Nanah yana borin kunya, wai ya fasa tunda iyaynta basu yarda dashi ba. Ta ce to menene don sunce muyi gwaji, ai ba sai ta mummunar hanya ba ake dauka, ko malamai sunce ba laifi bane don anyi gwaji. Ya ce shi ya hakura, ta ce Allah ya hada kowa da rabonsa. Gida uku yana neman aure amma ana dagaoshi, bakin cikinsa ya karu. Dole ya koma wajen tsohuwar budurwarshi wadda suke rigima suna zargin junan su. A nashi tunanin ita ce ta sak mishi, ita ma tana tunani shi ya saka mata. Ya ce mata suyi aure kawai tunda suna shan magani, ta amince nan dai iyayen su suka shiga barin kudi tunda duk suna dashi. A yawon amarcin su ne suka je America aka duba su in da Likita ya tabbatar masu zasu iya zama indai suna shan magani, sai dai yana gani da wuya su sami haihuwa. Su basu damu ba, amma da suka zo gida Momy ta damu. Ta fadawa Dady cewa ita yanzun ba za ta samu jika ba a wurin yaranta maza? Ya ce kada ta damu, tunda ga 'ya'yanta mata. Haka suka ci gaba da zama shi da matar shi a unguwar Kinkinau. Sai dai kullum yana cike da bakin cikin ciwonshi, wanda yake danganta shi da iyayenshi duk SANADIN BOKO. *************** Baba ya dubi Umar ya ce, "Tunda ka yi aure ka kwashe kannanka baka son zuwa duba ni, gashi bani da lafiyar da zan fita nema. Ya ce "wallahi Baba bana son zuwa ne in ban sami dan abinda zan riko muku ba, yaran nan kuwa na kwashe su ne dan kuji saukin kudin haya. Nima can kasan buga buga ce kawai. Bus din tawa kwanan nan kudi kawai take ci kullum sai nayi gyara, Allah ya taimaka. Umar ya ciro dubu daya ya bashi tare da cewa "Ga wannan sannan ga doya nan" ya ce na gode Allah ya saka da alkhairi" Baba ta shigo ta ce, "Mun gode Umar Allah ya ba da lada." Har ya mike zai fita, ya ce Umar zomana" Ya dawo ya zauna. Baba ya yukura, Babah ta kama shi ta sa mishi filo a bango ya jingina. Ya dube shi dakyau. "Umar wai har yanzun babu labarinHafsatu ne?" Umar ya daure fuska, shi kam in karatune wannan tambayar to ya jima da haddace ta. Babah ta ce "Malam kai ne fa da kanka ka kore su, ba dole suyi nisan kiwo ba? Gara ma innar su sunsan inda take, amma Hafsa yanzun wayamasan tana mace ko a raye oho. Umar ya mike tare da cewa, "In da rabon ganawa za a gana." Baba ya ce, "Umar ina cike da nadamar abinda na aikata. Hakika ina zaton nine na yiwa Hafsa baki har kaddara ta fada mata, da ina mata addu'a da bata shiga wannan halin ba, ko dai zaka sa cigiya ne? Umar dai gani yau Baba yafi kullum rudewa akan batun Hafsat, sai ya lallaba shi da cewa. "To Baba, za a cigita kada ka damu" ya ce to Umar, a cigita. Allah yasa a dace." Tabbas tun bayan rabuwar shi da innar su Hafsat yaga matsaloli kala kala, ga ciwo ya sa shi a gaba, wai suga ya kwanta a asibiti har sau biyu. Umar ne ke ta fama dashi, don ma Allah ya taimaka Innar su ta sa shi ya saida mashin din ta cika masa ya sai Bus ya diban lodin kasuwa daga Rigasa. na dama ta shige shi yanzu tun da ya rasa matar shi fatansa ya samu yar. Cikin haka ne umar yaga yar uwar inna mai suna murja a wata ziyara da ya kai munanfashi. Yace yana sonta itama ta amince, nan aka kare komai inda aka sha buki,tare da dan madaidai cin gidan da ya kama mai daki 3 don haka ya kawo kannan shi zuwa gidan. Tun baba yana dan fita har ta kai baya iya fita din ma, ga ka‘idojin abinci, gashi ba kudi. Yanzu baba bashi da burin da ya wuce yaga hafsat, shikam umar ya kance bai san inda zaije yaga hafsat ba, domin yayi bakin cikin abin da ya faru. Kuma hafsat itace silar rabuwar iyayen su, shi sam bai ga laifin baba ba, tun da dai dai gwargwadon ilimi ta samu, sun dage sai tayi jami‘a, to ga abinda ya biyo baya yanzun. ************** Haka inna anata ban garen tana zaune lafiya gidan mijinta, da yayan taguda 2. Kuma duk sanda umar yazo takan tambaye shi ko ya sami labarin hafsat. Yace, inna ki daina batun hafsat, babu inda za‘aje nemanta. Ita tasan inda muke, inda muna ranta kamar yanda take ranmu da tuni tazo koda zamu kashetane. Kum inna ya kamata ki sauwaka ma kanki batun ta, dubi yanda tabaki kunya, ta zubar da kimanki ta kashe aurenki, dan kawai kin tsaya mata ta sami gishirin zamani, wato ilimi. Ta miki sakamako da haka. Inna tace, ina zaton kadarace ta fadawa hafsat, yanzu da tatafi ba asaniba ko tana raye ko tana a ma ce, kilama ta mutu gurin haihuwa. Umar yace, to muyi adu‘a kawai Allah ya yafe mata. Inna tace, amin. Amma nafi dora laifin kaina. Don da lokacin da mahaifinku yace bayaso tayi boko da na hakura da yanxu ban bar yaya na ba. Da yanzu bata gudu ba. Umar yace duk mu bar wanan ga kadara, Allah shine mafi sanin da lilin da hakan ta faru,tsakaninta da mijinta akwai mutiny's juna, haka nan ya yansa ta hada da nata yayan ta sunguma. ********* Abubakar ya dawo gida cike da rashin kwarin gwiwa. Cikin kwanakin duk ya canja ba kwanciyar hankali. Ummi ita ce ta fara gano haka acikin gidan su, ta dunga matsa mashi da son jin matsalar shi. Yace, kinyi kan kanta da in fahimtar dake halin da nake ciki. Tace zan gane hmma. Yace nida hafsat muna son juna, sai dai a kwai wani dalilin da take ganin zai hana mu aure wanda ban san dalilin ba. Kiyi shuru da bakinki kada wani a gidan nan yaji wannan zancen. Ummi tace, hmma ina tunanin zaka iya shawo kan kowace matsala da zata hanaka auren anty hafsa. Tunda ka iya shawo kan lamido ya yarda ka aure ta. Abinda ko iyayenmu ba zasu iya kwatanta hakan ba. Kai sadauki ne, kana da nasara a kan duk abinda kasa a gaba.ina ji ajikina zaka auri anty hafsa. Dadin kalaman ummi sun karfafa mishi gwiwa sosai, har ya bata kyautar wayar da take ta nacin ya bata. Da yace sai ta gama secondary. Amma yana bukatar ya kara natsuwa kafin yagane ta in da zai shawo kan matsalar. Ko da ya fada ma Hashim cewa hafsat taki, tace ba zata aure shi ba saboda wasu dalilai nata. Hashim yace, kada ka damu zamuje tare kuma zata yarda. Amma yanzu abinda nafi so ka nutsu, iyayanmu su san ka karbi fadi. Dan haka yau dadadare zamuje zance. Daga ofis super market ya wuce inda ya siyo kayan shafe-shafe da tande-tande dan suyi tsaraba. Lokacin da fadi ta nufo su abubakar, ya zuba mata ido. Gaskiya tana da kyau, sai dai baya jinta a rai kamar hafsa. Ta zauna suka gaisa, tace ya dawo lfy? Yace lafiya lau. Hashim yace, mun zone dama mu dan gaisa. Amma yanzu bari in matsa ku zanta ke da yallabai. Abubakar yace kaje ina, kamar dai zamu shekara? Bai saurari Abubakar ba, ya fita. Fadi tace, don baka sona shi ne zaka ce wai sai kace zaku shekara? Ni to ina son ka. Ya dube ta kin ji abakina cewa bana sonki? Tace, banji ba, amma naji yanda kaita kokarin doje ma aurana. Ni kam ko wane lokaci nayi sallah ina fada ma Allah cewa ya bani kai amatsayin miji na, gashi ya amsa. Ranar da aka kawo mintin bai kon mu da sa rana ban iya bacci ba don murna, gani nake daga bacci ya debe ni zan farka in ga cewa ba gaskiya bane. Zugun abubakar yayi yana kalon kasa, wannan al‘adar tana cikin al‘adun da ya tsana a mata. Ba wai haramun bane mace tace tana son namiji, amma a kalla kijira ya fara furtawa. Shi yasa yake son hafsa, don tana da kamun kai. Shi a nashi ra‘ayin in dai mace zata fito tace tana son namiji ba mijinta ba, ko kuma shine yazo da da‘awar son shi gurinta ta amsa mashi ba. To wannan bata cika mace ba a nashi ra‘ayin.........ta katse shi. Na san waccen yarinyar da kake nema ta kano din tafi ni kyau ne ko? Ya dago kai, please ki muyi maganar da ta shafeni da ke, bana so kina saka hafsat. Tayi dan diM, can tace shi kenan. Yanzu wane shiri zamuyi? Ya kamata bukinmu yazo da sababin salo na burgewa acikin zuri‘ar mu. Yace, ko? Tace, sosai kuwa. Yace, to ki rubuta duk abinda kikeson ayi, in yaso in nazo zan gani. Ya mike zan tafi gida, ga yar tsaraba nan. Ya nuna mata lader. Cikin doki tace, amma na gode. To yanzu har zaka tafi bamuyi wata fira ba sosai. Wani lokacin in nazo zan dade. Ta rako shi har bakin gate in da hashim yake tsaye da jamilu yayan fadi. Suka gaisa da jamilu, inda ya shiga jin jina masa da cewa ya gode da wanan jahadin da yayi a gurin lamido, inda ya samo musu yanci. Abubakar yace au! Kai ma kayi farin ciki ne? Jamilu yace, ba dole ba, don yarinyar da nagani zuciyata ta so ba yar zuri‘ar mu bace. Son yarinyar ya shige ni a kudu muka hadu da ita lokacin da muka je (N Y S C) Allah ya shi maka albarka bayan bukinka zanyi maganar tawa. Abubakar yace Allah ya taimaka, mu kam bari mu tafi. sati 2 tsakani da zuwan shi kano, lamido ya kirashi to kasan lokaci yana gabatowa, don ha sai kafadi inda iyayen yarinyar nan suke saboda aje a kammala da su suma. Zufa ce ta soma tsatsafo ma Abubakar, amma sai yace, am.....dama mahaifinta yayi tafiya ne shi yasa. Amma idan ya dawo sai in fada muku saboda ya riga ma ya san da maganar, kuma su a shirye suke. Lamodo yace, to cike da damuwa ya fito, dole ne ya koma kano gobe sai sai ya takurawa hafsa don yasan abinda take ikirari zai hana auren su. Ya kira phone din hashim yace, ka shirya gobe juma‘a zamu shiga kano, sai mujuyo ranar sunday. Hashim yace, to ******* Nikam tun ranar da abubakar ya tafi na shiga halin kunci da damuwa. Na rasa dan ragowar farin cikin da ke tare dani. Ina zuwa makaranta da gurin aiki, amma bana iya cin wani abu. Ban amince ina son abubakar ba sai yanzu. Har shadad yafini hakurin rashinsa, duk da cewa sun shaku matuka. In nayi kamar in kira lanbobin da ya bani sai in fasa. Nace, kai gara in koyi yanda zanyiwa kaina fada, in hori zuciyata ta saba da rashin sa kada in zurma da yawa in kamu da ciwon zuciya a banza. Don nasan babu mai hankali da zaya aureni. Kai akwai daran da na rabashi ina kuka. Ba zance irin kukan da na saba bane, wannan kukan son abubakar ne. Yau satin mu 2 rabon mu dashi. Ina zuwa ne cikin aji, duk da hankalina yana gurin malamin amma har yayi ya gama ba zance ga kalma 1 da yake fadi ba. Tunanin Abubakar sadeek kawai nake yi. Na san abaya na so munnir amma ban shiga irin wannan ma tsanancin halin ba. Wani irin abubuwa nake ji game dashi, waddanda ba zan iya fasrasu ba. Kenan da ba son mannir nayi ba. Kenan da shirme nakeyi. Ya rintace

Chapter 12 of 22