Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kwance na dawo daga gurin aiki wata makaranta aka turani ta 'yan mata nake koyarwa. Na yi abinci na gama nayi wanka na kwanta, ya zauna na tashi na mishi sannu da zuwa, na dire mishi abinci. Yana ci ya ce, "The only, ina son ki yiwa Fadima taimako daya." Na ce, "Na me?" Ya ce, "Bata samun bacci don Rukayya ta fada min cewa zaune suke kwana. To tana son in dinga kwana gurinta har ta dan murmure."Zancen ya bani mamaki, sannan na fahimci cewa makirci ne, amma sai na ce, "Ba komai." Ya ce, "Dama na san ki baki da matsala." Da dare kuwa ya tafi, haka-haka har sati uku. Sai dai fa in yana da matsala ya yi min sammako ko kuma in ina gurin aiki ya zo ya dauko ni daga baya ya dawo da ni. Ban taba nuna mishi damuwata ba. Lamido ya kira shi ya ce, "Ubana an fada min baka kwana a gidan nan ko?" Ya ce, "Eh, saboda bata samun bacci ne in bana na." Lamido ya yi murmushi sannan ya ce, "An fada min kuma tana zuwa hurin aiki ko?" Abubakar ya ce, "Eh, ai matsalar tata da dare ne." Lamido ya ce, "To, daga yau na hana, kowacce ka dinga kwana gidanta a ranar kwananta, kanta aka soma ciki? An ce ta samu sauki ba shike nan ba?" Abubakar ya ce, "Shi kenan." Har na soma bacci na ji kwankwasa kofa, na zo na ce, "Wane ne?" Ya ce, "Ki bude." Na bude na ganshi na ce, "A'a baka tafi ba?" Ya ce, "Ke ce kika fada ma Lamido cewa Fadima ta ji sauki amma ban daina zuwa ba ko?" Na ce, "A'a bani ba ce." Ya ce, "To wanene?" Na ce, "Ka tambaye shi." Ya ce, "To ni bana son kai kara, don ban soma zuwa ba sai da izininki." Na ce, "To gaskiya ba ni bace." Ya ce, "In ma ke ce din ai yana zuwa kanki, tunda an ce ai haka ciki ke yi muku." Na yi masa shiru don haushi. Abinda bai sani ba nima lokacin ina manne da nawa cikin wata biyu, ina kuma laulayina sai dai bai yarda ni ba, sai dai amai kuma nafi yin shi da rana, kuma ban fasa komai ba. Azumi ya kusanto ya zo ya same ni wai in zo muje gidan Fadi, zai yi wata shawara, na ce to.......... Cikinta ya fito, amma yanda take tike kugu gami da turo cikin ko watan haihuwarta ne sai haka, tana yi da kyar take daga kafa, a dole ga mai ciki shi kuma kallonta yake yana murmushi, ni sai suka ma bani dariya. Ya kamata ta zauna yana yi mata sannu, ita ko sai faman cije-cijen lebe take, na yi 'yar dariya nace, "Maman twins an fito?" Ta ce, "Umm na fito." Muka gaisa ya ce, "Dama saboda zuwan azumi ne ina son in bada sadaka wa kuke ga ya dace in ba?" Fadima ta dube shi, "Kawai honey ka bamu mana, ni ga ma sayayyar da ke gabana na kayan baby." Ya dubeni, "Ke fa?" Na ce, "Ka kai Masallaci ko ka samu mabukata ka basu tunda Alhamdulillah mu muna cikin wadata." Ya yi murmushi, "To dama nima tunanina kenan, don haka zan bai wa masu bukata Zakka, sadaka kuma zan baku ku bada, ko cikin family dinku ko nawa."ta zobaro baki, "Kenan shawarata bata yi ba?" Ya ce, "Eh." Ta yunkura, "To ai da ba'a kirani ba." Ya ce, "Hakkinki na baki da ba sai na zo ba din, don nasan ita zata iya bani shawara ta masu ilmi." Kudi ya zube min dubu dari uku da dari biyar, wai in raba ma masu bukata. A zatonshi zan tafi da shi gidanmu ne in raba ma dangina, sai na tambayeshi zuwa kasuwa ya yarda. Ni da Ummi muka je. Shinkafa kawai na lodo da taliya sai kuma zannuwa, Ummi ta ce, "Aunty me zaki yi da shi?" Na ce, "Sadaka." Ta ce, "Don Allah akwai wasu dangin su Daada dake can wata ruga talakawa ne, jiya ma Abba ya aika musu da gero da sugar na kunun azumin." Na ce, "To." Daada din naje na samu na ce, "Sadaka zan raba ta abinci saboda neman falalar wannan wata, to ina so in cire na dangi na can Ruga shine nake so ki cire musu nasu sai na ba makota sauran." Ta ji dadi sosai, tayi ta shi min albarka, duk da ta san cewa shi ne ya bamu kudin, ta ce min ya shawarceta, ita ce ma tace yayi shawara da mu, ta ce ya ban kai dangina ba? Na ce, "Da ku da dangina Daada ai duk daya ne ba wani bambanci." Ta ce, "Allah ya shi min albarka. Ta cire musu sannan na saka 'yan samarin gida mua yi ta mika wa makotanmu wadanda ke da karamin karfi. Dama kananan buhuna ne. Lamido har kofata ya zo yayi min godiya tare da shi min albarka. Abubakar kuwa da ya dawo ya ga makota na ta mai godiya tare da addu'a sai kuwa kanshi ya daure, da yai zaton geron da Lamido ya raba ne, sai da ya je gurin Lamidon shi ne ya bashi labarin abin da nayi sannan ya ce, "Ka rike matarka hannu 2, don ka samu macen da babu irinta cikin yaranmu, Allah ya azurta ku da Yara masu albarka." Abubakar rungume ni yayi tare da min godiya na ce, "Allah shi ne abin godiya." Ashe zakkar shi can ya kai ma su Babana bayan ya dibar ma Innarmu. Shima bai fada min ba sai da Ya Umar ya kira ni ya fada min wai mijina ya kawo wa Baba zakkar kudi naira miliyan 2, Inna dubu dari biyar, in masa godiya sannan yana son mu yi shawarar abinda za'a siya. Na ce, "Yaya Umar ku nemi dan madaidaicin gida ka sai ma Baba kawai." Ya ce, "Nima haka na ce, kuma shima Baba zai so hakan. Allah ya saka masa da alheri." Na ce, "Amin. Kuka na saka da muka gama wayar, ban san ko kukan me nake yi ba, na farin ciki ne? na son mijina ne? na barin iyayena baya ne? Oho. Inna ma ta kirani ta ce in masa godiya na ce to. Da ya dawo kuka na sa tare da rungume shi, ya rude ya firgice yana tambayata, "Me ya faru D Only? Wa ya taba ki?" Na ce, "Ba kowa, na gode da taimakon da ka yiwa Iyayena, Allah ya saka makada alkhairi, Allah ya kara budi, ya tsare ka daga dukkan sharrin abin ki, ya kuma bani ikon binka sau da kafa." Ya shafa kaina, "Amin Masoyiyata, game da batun Zakka kuwa ba sai kin min godiya ba hakki ne na Allah na cire." Na ce, "To da ka cire din da kaga dama ai wani zaaka ba." Ya ce, "To shike nan." Da dare muna kwance ya ce, "Wai ya za'ayi da sayan kayan Sallanku? Kudin zan baku kuje kasuwa ku siyo?" Na ce, "A'a da kai zamu je saboda ka zaba mana son ranka." Ya ce, "Bari sai na ji ra'ayin Fadima." Ya janyo wayarsa ya kirata, "Sweet heart." Ta amsa da, "Na'am Sweet honey." Ina jin muryarta, don ina jikinsa ya ce, "Gobe zaku shirya ne mu shiga kasuwa tunda bani da aiki?" Ta ce, "To, daga nan sai mu siyo kayan Babys din tunda an ce mace da namiji ne?" Ya ce, "To sai ki shirya zamu shigo wuraren 11am saboda kada ki sha rana ko?" Ta ce, "To Honey sai kun zo." Ya ce, "Yauwa, ki shafa min Babys." Suna yin sallama na kankame shi, "Yan biyu zamu samu?" Ya ce, "Eh, dazun da ta dawo asibiti take fada min wai an ce 'yan biyu ne mace da namiji." Na ce, "Kai na yi farin ciki, ina son twins shi ne baka min albishir ba?" Ya ce, "Na same ki kina kuka yaya zan tuna da maganar 'yan biyu?" Na ce, "Allah ya sauke mana ita lafiya." Ya ce, "Amin, kema Allah ya baki ina son in ga kin haihu, duk wannan dina har yanzun ba ciki, ko dai zamu je asibiti ne?" Na ce, "Haba dai, duka yaushe aka yi abin? Ko fa shekara banyi ba." Ya ce, "Don Allah ki daina zancan nan, yara nake so sosai, yanzun kin ga zan fara da biyu na zo daidai da Kanina Usman, in kin haihu ko da daya ne kin ga na fishi ko? Balle ma kema biyun zan baki." Na ce, "Oh! Kai ne ma kake badawa?" Ya ce, "Allah ne zai bani ni kuma in baki." Na ce, "Dama kun gaji 'yan biyu ne?" Ya ce, "A family ni zan fara, shi yasa kowa ke doki, jiya kinga yanda 'yan uwa ke murna?" Na ce, "Ai abin so ne, Allah ya bamu masu albarka." Har zuciyata na taya shi murnna. Katon super market muka shiga, gefen zannuwa, lesuka da shaddoji zuwa yaduka, ya ce mu zaba, na ce, "A'a ka zabo mana." Sai cewa Fadima ta yi, "Ni zan zabi abina." Na ce, "To ni ka zabo min." Duk wanda ya miko min ko bata kamfanin ba amsa nake in ce yayi kyau. Ya ce, "To dama atamfa ce nake da irin wadda nike so, amma sauran zabi." Da muka gama sai na zabar wa Ummi atamfa da Shadda da leshi Rukayya ma haka. Daada kuwa yawan namu na daukar mata, ya bini da kallo itama haka ya ce, "Wannan fa?" Na ce, "Na su Daada ne, ta ce, "Su Daada ne za'a sai ma kaya?" Ya ce, "Shi ne ai, su Daada da ke da super market zuwa fa zasu yi kawai su zaba..........."....... Zaharaddeen Shomar whatsapp 08168575100 Sanadin Boko 4-06 Posted by ANaM Dorayi on 05:20 AM, 29-Sep-15 Under: SANADIN BOKO Na ce, "Za ka biya ko in biya?" Na fada cikin daure fuska, ya ce, "A'a zan biya in basu amsa ba sai kin san yanda zaki yi da su." Fadima ta ce, "Neman gindin zama." Ban ko kalle ta ba shima bai ce komai ba. Da muka isa gurin da ta sai Shaddoji da Yaduka sai na dibar ma Abba, ya ce, "Dama kin daina wahala na fa san ba zasu amsa ba." Don haushi ban kuma tanka su ba, don Fadi sai dariya take yi, ban fasa dibar musu ba, har turaruka na dibarma Abba, su kuma kayan shafa. Ita kuma muna zuwa gurin kayan Babys nan tayi ta jida, kowanne bibbiyu ni ko nayi ta taya ta. Da muka je gurin takalma da jaka na zaba musu. Da zai sai nashi na zaba ma Abba har huluna ya ce, "Ke baki san lambar takalma ka kina ta diba har da hula." Na ce, "Ido ba mudu ba ya san kima." Ita kuma ta ce, "In da rabon ka tafka asarar kudi ai shi kena." Ni sai na sharesu kawai na ci gaba da lamurana.Mun dawo gida cike da lodin kaya, but din mota shake, kujerar baya shake, da kyar na dan samu gurin rabawa. Dama hakima ta gaje gidan gaba, ita muka soma saukewa sannan muka wuce gida. Muka yi ta jidar kaya zuwa ciki, har lokacin fuskata daure saboda yanda yayi ta gwasale ni, don kawai na ce ya sayawa Iyayenshi kaya. Ba gidan zai sha ruwa ba yau, don haka ina yin sallah na kwanta sai bacci, ban san lokacin da ya tafi ba ma ni. Sai da ya dawo Asham sannan ya biyo gurina, ya samu ina sallar Asham din nima, ya zauna yana kallona. Na idar na gama addu'a ya taya ni shafawa na dube shi, "Sannu da zuwa." Ya ce, "Yauwa, na zo ne inga ko kin huce, naga yau an yi bacci an share ni." Na ce, "Ai bani fushi da kai Mr Cool." Ya yi murmushi na ce, "To yanzun dai sai na dauko maka ka kai musu." Ya ce, "Sai dai ki zo muje tare, dan kuwa ba za'a sace min gwiwa ni daya ba.Na mike na dauko hijabi zan sa ya ce, "Zo nan." Na zo ya dubeni sama da kasa, "Wai wanna kibar fa? Sama da kasa duk kin cika?" Na shafi kumatunshi na ce, "Ka iya kiwo ne." Na mika mishi ledar dan in bagarar da maganar, "Ga wannan mu je." Ni kaina na san cewa na yi kiba, cikina a kirji da hips ya tsaya, marata ba me cewa ina da cikin wata biyar da 'yan kwanaki. Duk a falo muka same su suna kallon Tafsir din Sheikh Amin Daurawa, na zube na gaishe da Daada da Abba, Ummi da murna ta hawo jikina, Daada na mata fada da fillanci. Rukayya ta tabe baki ta gaisheni a dakile. Abba ya ce, "Daga gida ku ke?" Na ce, Eh! Ya ce, "To sai ki basu." Na ciro ledar Daada na yunkura naje gabanta na ce, "Gashi in ji shi." Dama bana iya kiran sunanshi a gaban Iyayenshi. Ta ce, "Me muka samu?" Na ce, "Kayan sallah ne ba yawa." Na mika ma Ummi da na Rukayya sai suka hau murna, Rukayya ta daga kai ta ce, "Hamma ya aka yi kasan kalolin da muke so? Ni komai ja Ummi komai pink." Ya kalleni, Daada ma sai murna take yi tana fadin, "Allah ya shi maka albarka ya baka zuri'a ta gari wadanda suma zasu fita hakkinka." Ya dube ni na kauda kai ina fadin, "Amin Daada." Na mika ma Abba nashi wanda ke kallonmu yana dariya tare da fadin, "Masha Allah." Ya ce, "Har da ni? Ikon Allah Abubakar an yi hankali." Muka sa dariya. Bayan an nutsu ya ce, "Wato Hamma abin da yasa kaji na ce ashe kayi hankali shi ne, ka sani duk kudinmu muna da hakki a kanka, kuma na gode Allah ya kara budi." Muka ce Amin. Ya ce, "Ni fa da har ba zan sai muku ba naga kuna saidawa." Daada ta ce, "Don muna saidawa shi kenan bazaka fita hakkinmu ba?" Ya kalle ni, nayi maza na kauda kai don bana son ya ce nice. Abba ya ce, "Bari Usman ya zo ya kai ma telana su, don da su zan je Idi in Allah yasa mun kai lokacin." Haka suka yi ta shi mishi albarka, tare da yi masa fatan samun zuri'a tagari. Da zamu tafi Rukayya har mota, Rukayya ta ce, "Hamma Allah ya kawo mana 'yan biyu lafiya..." Muka ce Amin. Har lokacin wani gani-gani take min suka juya. Ko nisa ba suyi ba ya wani kankame ni ya rungumeni ya ce, "Na gode D Only, na gode da sani a hanya da kika yi, ni a zatona tunda iyayena suna dashi fiye da ni ba sai nayi musu wata hidima na sai dai in ma danginsu marasa shi daga ciki." Na ce, "Ko sune suke kera kudi wajibi ne ka basu hakkinsu, yi musu biyayya na san kana yi, yi musu alheri kai har abinci ya kamata ace duk wata kana sai musu ko buhu dai-dai ne." Ya ce, "Zan soma daga wannan watan Insha Allah, kai yau naji dadi ashe haka mutum ke samun farin ciki in ya faranta ma Iyayenshi?" Na ce, "Sosai ma kuwa.Ya ce, "Na gode Allah da ya bani mace ta gari, yanzun fada min bayan su ko akwai wadanda ya dace in sai ma kayan Sallar?" Na ce, "Su Lamido da duk kanne da yayin Babanka, ka sai musu kowa wanda ya dace da shi zasu ji dadi."ya ce, "To gobe zamu koma kasuwa kenan." Haka ya kaini gida yana ta shi min albarka, sannan ya tafi gidan Fadima ya kwana. Washegari mun shiga kasuwa harda list din mutanen don kada a manta, lallai kudi sun mutu a ranar, alheri sai bawa ya dage, amma in kayi dadi ka ke ji, shi kuma wanda ka wa yana jin dadi. Ya ce, "To wanene zai kai musu?" Na ce, "Ka samu Hashim ka ware rana kayi ta kai musu." Da suka dawo kuwa Hashim sai labarin yanda Iyayen suka yi ta murna da godiya ya ce Abbanshi, Sarki kenan, har gori ya mishi ya ce, "Hashim kalubalenka, sai ayi koyi da Hamma." Na yi murmushi, na san kowa zai yaba don kaya ne na alfarma da takalma da hula. Hashim ya ce, "Allah ya nufe ni nima." Ranar ma godiya yayi ta min, su Lamido ma suna ta shi masa albarka, wanda ma baya nan in ya dawo gida ya gani sai ya kira waya yana sa albarka. Allah kasa mu dace amin. Saura sati biyu Sallah Abubakar ya ce min yana son ni da shi mu tafi Umara, don haka ma in tashi muje inyi fasfot. Na ce, "A'a da Fadi ya dace kuje." Ya ce, "Ba zata iya zuwa ba." Na ce, "Ina tsoron abin da zai ja min bakin jini cikin zuri'arku, amma ka je ka shawarci Daada." Ya ce, "Shi kenan" Ko da ya samu Daada da batun sai ta ce mishi ya bari mun je aikin Hajji dukkanmu, kada ya zama abin tsegumi ace ya kai bare, amma Hajji kafin lokacin ta haihu. Ya dawo ya ce min bakinku yazo daya da Daada. Na ce, "Ka gani ko? In kaje ka samu a addu'a." Ya ce, "Wannab ba sai kin roka ba. Ni dai na so inje da ke ne saboda mu dan shakata." Na ce, "Wata rana zamu shakata. Koda yanzun ma ai mun sha iska." Ya yi 'yar dariya.da xai tafi ya bar ma kowa komai, na ce xan je kaduna da salla, ya ce a'a in bari ya dawo ma je tare na ce to.su Ummina sun xo min da salla har da Yaya Umar, nayi murna sosai kwanansu 2 suka tafi da Shadad, na ce su bar min Ummi in xamu xo sai mu xo da ita. Bayan sallah da kwana 3 xaya dawo,nasan kuma gidana xaya sauka, domin yana fada min irin yadda yayi missing dina,ko na ce muka yi missing din juna.Tun safe na soma shirya masa girki kala-kala da abin sha, jus nayi mas kusan kala 3 n akuma hada nawa hadin mai kyau nayi ta sha tun safe.misalin 3 ina tsaye gaban madubi nayi adona ckn 1 daga ckn atamfofin daya siya min,sam banji shigowarsa ba,sai dai ji nayi an rungeme ni ta baya kamshin turarensa yasa na gane mijina ne.da sauri na juyo muka makale juna cikn murna, ya sumbaci lebunana, sannan ya ce bari mu isa gidan Fadi, sai in dawo. In na xauna ba xan iya tafiya ba.xamu wuce ne da Hashim daya dauko ni naga ba xan iya wucewa ban ganki ba,na ce to in ka san ba xa ka dawo ba to ka wuce da abinci.Cikin marairaita nayi maganar,ya shafi kumatuna. kada ki damu d only yanxun xan dawo naji gidan na kamshi na ce to "Da sauri ya shige mota suka tafi.kafin ya dawo na kara gyara gidan, na canza kaya doguwar rigar leshi nasa mai kalar sky blue, su hudu suka shigo duk da Hashim.na jera musu abinci da na sha, in adaga daki ina jiyo su suna santi.Hashim ya ce, Hamma gaskiya xan kullo ma Hafsat kawance da Shatu, ina son taxo ta koyi kalolin girkin nan, Dayan ya ce na riga ka a xuci ka riga ni a baki, shi ko dayn ba shi da mata, cewa yayi xaya kawo budurwanchi ta yi hadda.shi kuma Abubakar sai murna da cika baki. fadi ya ke "Matata yar baiwa ce, duk abubuwanta cikin ilimi ne da daraja girkin Hafsat daban ce.Amma fa ba xa ku takura min mata ba, da Ummi taxo tana kwashe kayan bayan sun gama,Hashim ya ce ko dai xan tsaya nan ne Hamma ka tsaya min a bani wannan in kiwatat?Abubakar ya ce "Katon banxa wa xai baka?suka sa daria.Misalin karfe tara saura muna ta shirin kwanciya, Fadi ta kira shi ya daga ta ce"sweet hrt ba nan ka ke ba?ya ce "In ji wa?ta ce Eh!! mana yi lassafi.Ni dai wlhy kada ma ka ce xaka kwana can, don ba xan yafe ba.Duk ina jin su, kuma ba gidanta xai sauka ba, saboda randa xai dawo gidana ya tafi.Na ce to koma can din , ya ce ba xan koma ba, tana xaton ban san me nake yi ba?ya share ta muka ci soyayyarmu, dama mun yi rashin juna.Wata juma'a misalin 3 muna cikin bacci wayarsa ta soma kuka, ni ce na farka na daga.Sweet hrt na gnai a jiki na daga, Muryar Goggo Jami naji tace, "Ina Hamma din?N ace "yana bacci "Ta ce to tashe shi Fadi bata da lfy shi bacci ma yake?a raina nace kada yayi? Namatsa kusa dashi na shafa fuskarshi, ya rike hannuna zuwa kirjinshi, nayi masa rada cikin kunne. Mr Cool ka tashi yau twins zasu fito, Fadi zata haihu." Firgigit! Ya mike ya zura jallabiyya ya dauki key din mota. Na ce yanzun zaka fita?" Ka bari a kira Sallah." Ya ce ba komai kada ki damu, na ce to Allah ya raba su lafiya." Ya ce "Ameen the only." Takwas na safe na kira shi, ya ce har yanzu dai shiru, na ce gani nan. Na isa gurin na samu 'yan gidan su, sai su Rukayya. Shi kuma can na hange shi tare da su Hashim da Usman kaninshi. Na gaida su Goggo Jamin, sannan na nufi gurinshi. Rukayya harda cewa 'yan biyun nan suna ba mamansu wahala, Allah yasa kada zuwan wasu yasa abin ya sake rikicewa. Wata da ban san ko wacece ba, ta ce ai mun rike Allah, kuma sai ta sauka lafiya da izininshi. Ban da lokacinsu bare amsarsu, don nasan dani suke, gurin mijina ma ni na nufa. na dube shi har yanzu ko? Na yi maganar ne cikin nuna tausayawa da tausasa murya. Ya ce, wallahi, na matso na kama hannunshi na dama na matsa kadan. Ka da ka damu samu ruwa a tofa mata addu'a, In shaa Allah zata sauka lafiya. Goran Ruwa ya kawo na karanta mata, YA HAYYU YA KAYYUM, YA ZULJALALU WAL IKRAM, BIRAHMATIKA ASTAGISU, sau bakwai na ce ya bata tasha. Da kanshi ya kaimata tasha, ya fito, ko minti ashirin ba a yi ba Nurse ta fito da murna tana fadawa su Goggo Jami ta sauka. Kawai sai naji mutum ya rungume ni a bainar jama'a yana fadin "Alhamdulillah." Usman ya ce "Aunty na Allah ya amshi Addu'armu, sai dai kuma me? Maimakon biyu sai aka fito mana da yarinya katuwa mai kyau. Sai kace mamanta tayi kaki, aka amsa da murna ana cewa ina dayan? Wannan ce Hassana kenan.Nurse ta ce ai daya ce, ita kenan aka haifa. Yanzun haka mai jegon ana gyara mata jiki. Gaba daya sai naga jikinsu yayai sanyi, har shi kanshi angon karnin. Usman ya ce amma 'yan asibitin nan sun cika shegiyar karya, shine suka ce biyu? Doctor ya fito, su Hashim suka bishi suna tambayarshi, "dama daya ne? Ya eh ai dama daya ce duk scanning dinta bai taba nuna biyu ba, wa ya ce biyu ne? Abubakar ya ce "ita ce" likita yayi tsaki ya ce "haka wasu matan suke yi ban san amfanin hakan ba, alhalin sun san cewa akwai ranar irin wannan da za a kure su. Ya dafa kafadar Abubakar "kada ka damu, ka yiwa 'yarka addu'a Allah yasa mai albarka ce." Duka suka ce "Ameen" Masu habaici da rawar kai kowa dai baki tsuu, shiru kake ji. Kullum nake zuwa gidan mai jego har ana jibi suna. Ranar da ya kawo mata zannuwan fitar suna ta ce basu yi mata ba, ranar ce ya amayar mata da takaicinshi a gaban 'yan koran nata. Ya ce "ki bini a sannu, banza makaryaciya, zan maganinki, kuma in na dawo baki dauki kayan nan ba sun zama ba rabonki ba. Ki sani ko bari kika yi zan so shi, bare dan mutum. To meye ribar karyar da kika yi kika sa muma muka yi? Mutuncin ki ya zube a gurina da sauran mutane. Sannan baki isa ki juya ni ba, kinfi kowa sanina. Zata yi magana ta rike kugu, ya ce yi min shiru, in kin furta wata magana zan bata maki yanzun nan. Ta yi tsit, ya fice. Nan ta shiga kuka suna bata hakuri, Rukayya tana cewa sai ta fadawa Dada da Abba. Yarinya taci suna Nana Fiddausi, in da ni kuma na shiryawa Abubakar kalolin girki kusan bakwai da kayan drinks. Suka yi walima, Ummi da kanwata Ummi sune yan taya aiki. Bayan suna da sati daya muka je Kaduna don maida Ummi tare da dauko Shadad daga gurin babanshi. Har da Umminsu ta mana rakiya don sun kulla kawance da Umminmu,saboda xaman mota sai kafafuna suka kumbura,sannan nayi ta shar amai,duk Abubakr ya rude hankalinsa ya tashi.kafin kace haka na kwana shrkaf.muna isa kaduna asibitin Garkuwa ya wuce dani, da gudu-gudu aka kawo gadon tura mara lafiya aka yi ciki dani,likitan yana duba ni yana mishi tambayoyi,tana da ciki ne?ya ce kai bana xatao, sai dai ko in yanxun. likitan ya maida allurar da yayi niyar yi min ya aje,yasa aka tura ni xuwa dakin scanning, kusan min 30 aka fito dani yaxo ya dauko ruwa aka yi wasu allurai a ciki, sannan aka dora ni ,ana da nan bacci yayi gaba dani,likitan ya kalle shi"matarka tana da ciki kusan wata 5 ko ma fi,sai in ta farka nayi mata wasu tambayoyi tukunna. Abubakr ya tsura mishi ido,kace tana da ciki wata 5? likitan ya ce kila ma ya fi. Abubakar dai yayi shiru,amma ba don ya yarda ba, ya kira Umar ya fada masa kusan minti 30 suka iso dasu Baabah.Sannan ban tashi ba, ya ce don Allah yaya umar ya kai su Ummi gida don suna ta kuka,kujera Abubakr yaja ya xauna ya rike min hannu su Baabah sai waje suka fita don kunyar yanda ya tasa ni gaba kamr xai cinye ni.ya kira su Hashim ya fada mishi su Daada ma ya sanar da su,kusan wa daya na farka.Da sauri ya tashi yasa hannunshi a kuskata, yana cewa "Sannu Hafsat sannu.Na ce yauwa Na yunkura xan tashi ya kama ni na xauna ya xauna gefen gado. Ina ne ke miki ciwo yanxun?nace "Ba ko ina yunwa nike ji, bakina ya cika da miyau,na ce xan xubar "ya miko min wata yar tasa sannan yace bari in kira likitan.Da sauri ya fita ya ce ma su Baabah na farka, suk shigo suna min sannu, na amsa na ce ni babu gurin da ke min ciwo,yunwa kawai nake ji (dama cin abinci a gurina tun dana samu cikin nan kmr gara)suka shigo da likitan aka ce su fita Abubakar kuwa xama yayi kusa dani likitan ya ce "Madam

Chapter 21 of 22