Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
fita suka hadu da Hashim, yake gaya masa yadda suka yi da Dada, ya ce, "Kaima ka yi laifi, kana so ka jawowa Hafsa tsana a dangi ko? Ka bari kaga iya gudun ruwansu, ai sun san komai a kai." Ya ce, "To shikenan to!!" Tabbas familyn Lamido auren farko yi maka za'a yi, in kuma ka cika zakewa yanzu za'a ce maka rashin kunya, balle Hamma da yayi fice tunda ya dauka 'yar waje (bare). Bayan sun gama magana da Hashim, yana kashewa sai yaga text din, ya bude ya duba ya ja tsaki, ya mike ya zauna bakin gadon tare da dauko wayarshi, nan take ya ga ya dace ya bata amsa don haka ya rubuta cewa, "Ban damu ki soni ba, asiri fa zan rufa miki, in bani ba dinma wa zai auri 'yar gagara? Zancen aiki kuwa, kya iya komawa, baki ji maganar Iyayenki ba ni zaki ji tawa? Kya iyayin duk abin da kike so tunda kina da 'yanci, barikin kenan."Lokacin da sakon ya shigo wayata kuka na saka, Mijin da zan aura ke fadamin haka? Na kira Rahma ina kuka wiwi na fada mata komai, ta ce, "Ki yi hakuri zan kirashi." Na ce, "Kada ki yi masa magana, illa kawai ana daura aure zan kama gabana." Rahma ta ce, "Ki yi hakuri ina nan zuwa." Su da Sagir suka zo da dare, lokacin na idar da Sallar Isha'i kenan, Shadad yana kwance kusa da ni, ko abinci na kasa ci. Suka yi sallama na amsa, suka zauna Rahma ta ce, "Wai mai ya faru?" Na ce, "Rahma duba text din nan." Na mika mata wayar ta karanta, tana gamawa sannan ta mikawa Sagir, shima ya ce, "Ki yi hakuri, wallahi ni nasan Abubakar yana sonki, kiran kanki Karuwa da kika yi shine silar fushinsa." Rahma ta ce, "Kuma yaki ya saurari kowa ya ji yanda abubuwa suka faru." Na ce, "Ni dai gudu zanyi matsawar aka ce yau shine mijina, duk da cewa nasan ina son shi." Sagir ya ce, "In kin gudu me Iyayenki zasu dauka? Wace rayuwa zaki samu a gaba? Kuma zaki sake samun wanda kike so kamar shi? Duk wadannan tambayoyin ya kamata ki yiwa kanki su, sannan ki amsa su duka." Na fashe da kuka, bani da zabin da ya wuce hakuri, domin Sagir gaskiya ya fada min, Allah ka shige min gaba. Rahma ta ce, "Ya zo ne akan batun wane irin shagali zamu yi saboda katin da za'a bugo, na san dai baki wuce Walima ba shiya sa na fada masa haka." Na ce, "Wa na sani da za'a buga kati? Ni walimar ma ba zanyi ba." Rahma ta ce, "Ka jita ko? Shiya sa nake ta gaban kaina, na san ba zata bada hadin kai ba." Sagir ya ce, "Yanzu dai Hafsa a shawarce ki zuba mana ido, naki bine kawai." Na ce, "A'a, kun zo da abinda ya sabama shari'a ba zan baku goyon baya ba." Suka yi dariya, haka suka yita lallashina tare da kare Abubakar har dai na danji sanyi suka tafi, bayan Rahma ta yi delete din text. Ana saura kwana 10 biki, danginsa suka nufi Kaduna da lefe, saitin akwati mai 5 dauke da kaya masu tsadar gaske, Goggonninsa sunyi mamaki gadin gidan da Abubakar ya nemo aure takalawa ne lis, sai dai an karbesu cikin karamci, da kayan abinci da nasha masu kyau wanda Murja Matar Yaya Umar ta yo. Dakin Baba aka share aka shimfida darduma, bayan sun ci sun sha sukai sallah, sannan aka bude kaya. Matan gidan suka shigo sunata yabawa saboda irin wannan kaya haka, daya daga cikin 'yan kawo kaya ta ce, "Ina amaryar ne?" Baaba ta ce, "Tana can Kano tana karatu a can." Umar ya kawo dubu 10 na tukuici tare da cewa su yi hakuri sun gode. Ko da suka dawo sun ce an karbesu hannu bibbiyu, kuma suna da karamci Iyayenta sai dai talakawa ne lis. Dada ta ce, "Shi dai ya sani kuma ya jiyo." Waya Rahma ta kira Sa'adatu ta makarantarmu, take gaya mata batun aurena yadda zasu shirya, sannan ta ce don Allah gobe zata zo har makaranta ta bata kati dan ta rabawa kawayenta. Sa'adatu ta ce, "Allah ya kaimu." Rahma ta dubeni ta ce, "Kin ga illar kin shiga jama'a, wallahi ki canja hali, dan family din da zaki shiga suna da yawa." ...... Zaharaddeen Shomar whatsapp 08168575100 Sanadin Boko 3-05 Posted by ANaM Dorayi on 05:56 PM, 28-Sep-15 Under: SANADIN BOKO Abubakar ya zo gurin Rahma ya kawo mata katin biki da duk wani abu da zamu bukata, sai hotuna da yace ta bashi dan can dangin sun matsa a kawo hotuna saboda suna son kalanda da memo. Rahma ta kirani a wata ta ce na shirya zan rakata gidan Matar kwamishinan ilmi, ta ce pls na kure adaka saboda sutura itace mutum. Ban kawo komai a raina ba, na ci kwalliya na saka after dress akai, ita ce da kanta ta ja motar tare da yi mata tsiwar cewar har kin kware da zaki cire (L) din? Ta ce, "Hannuna ya fada kinsanni da karambani." Muka tsaya wani gidan hoto mai kyau, anan ta ce min, "Hoto zamu karba ki shigo." Naje wajen hoton muka shiga, Rahma ta je tai magana da wani mai hoto na ga suna magana amma ban san me suke cewa ba, na dai tsaya a ciki. Da ta zo na ce mata, "Ina hoton?" Sai ta ce, "Wai sun kone sai dai a sake wani." Ina zaune gefe aka yi mata wajen kala 5, ya nuna mata ta ce yayi. Ya ce to nifa? Ta ce, "A'a, Hafsa ai ita bata hoto." Ya ce, "To shike nan." Na ce, "In gani Rahma." Ta ce, a'a ba zan gani ba, muka zauna zaman jiran karba, akai editin dinshi na ce, ka wanke mai kyau sosai fa. Muka karba muka fito. Muna hanya na ce, "Ina gidan Kwamishinan?" Ta ce, "Daman hoto ne, nasan idan nace miki ki raka ni ba zaki ba." Na ja tsaki tare da cewa, "To kai ni gida." Bayan la'asar lis ina duba wani littafin masu fasaha wanda yake burgeni na Ikilima, Shadad na gidan Mama na tura shi dan in nutsu ina son in samu wani abu da zan karu da shi cikin halayen Ikilima. Duk da ciki-ciki ya yi sallamar sai da kunnena ya dauko daddadar muryarsa, hannunsa rike da Shadad, na dan kauda kaina na ci gaba da duba littafin dun da na kasa fahimtar komai a cikinsa. Shadad ya rugo yana cewa, "Aunty ga Uncle." Na ture shi tare da cewa, "Waye haka? Da Allah ni matsa can." Ya bata fuska, "Aunty kin ganshi nan fa." Don kada Shadad ya fahimci wani abu sai na ce, "Sannu da zuwa." Bai amsaba sai ya bata fuska tare da tabe baki, "Na zo ne kawai in ganki, tunda kina lafiya shikenan ni na tafi." Ban motsa daga inda nake ba na ce, "A gaishe su."Ya ciro kudi ya bawa Shadad, "Je ka zauna sai na dawo." Ya ce, "In ka dawo zaka tafi da ni?" Ya ce, "Sai kayi hutu." Ya juya ya fita, na bishi da kallo hatta tafiyarshi ta lafiyayyun maza ne, komai nashi birgeni yake yi. Daidai soron ya juyo idanunmu suka kalli juna har ciki, ya zare nashi idanun ya kalli gabanshi, sannan ya bude kofar ya fita. Na lumshe ido tare da shakar kamshinsa, tsam! Na mike na nufi kofa ina leken shi, ya mike da nufin fita daga layin ina zaton ba da mota ya zoba, na bude kofar ina lekenshi har sai da na dena ganinshi. Shadad na samu yayi wada-wada da kudin da ya bashi, 'yan dari 2-2 ne guda goma, na kwashe su na koma daki na zauna bakin gado ina tunani, damuwa ta ban san zaman da zamu yi ba. Cikin kwanakin shagali na karatowa kuma karatuna na kara daukar zafi, don mun kusa mu fara Jarabawa.Rahma ke shirya komai na game da walima, ana gobe daurin aure na dawo Makaranta wujiga- wujiga, na iske gidana dam da jama'a. Rahma ce da makota har da dangin mijinta suna ta aiki, wasu na wankin naman kaji, wasu na wankin kayan miya. Turus! Na yi yayinda makota suka soma fadin ga AMARSU, guntun murmushi nayi tare da gaishe shi sannan na shige daki, a zuciyata na ce, "Kai su Rahma da karfin hali." Ita kuma sai hada murhu take yi. Ta zo daki ta sameni, "Don Allah kada ki nuna fushi ko wata alama da za'a gane da wata matsala." Na ce, "Wai ni duk ba wadannan ba, a ina kika samu kudin yin wannan shagalin?" Ta ce, "Daga taskar ango." Na ce, "Shagali, Allah ya baku sa'a."Dazu Inna ta kirani tace min tun jiya suna Kaduna ita da danginta, tace min ya kamata na taho." Rahma ta ce, "Mama ta ce gaskiya can ya kamata a tafi, to sai dai mu bar walimar sai ranar lahadi, ko me kika gani?" Na ce, "To ni dai gobe sammako zan yi." Kafin dare an gama suyar kaji an yi miya, duk ta ba wadanda suka tayata aiki. Da duku-duku muka gama shiri ni da Shadad, sai ga Rahma da direbansu, Mama ma ta shirya, Rahma ta ce, "A dibi naman da drink a tafi da su ko?" Na ce duk yanda ta gani, tunda kajin da yawa, sai ta debo sosai, goma daidai muna Kaduna.Allah Sarki Baaba! Ashe har anko suka fitar, gidan cike yake da mutane ban zaci ganin haka ba, ashe Baaba gayya ta yo, dakin Baba nan Inna ta sauka da danginta, na ji kunyar ganin 'yan uwanta, amma ganin basu nuna komai ba sai na saki jikina, suka gaisa da Mama, Baaba ta shigo muka gaisa, ta ce, "Ga fa abincin 'yan daurin aure can nasa a dafo shi a gidan wata mata da ke yin na kudi." Baaba ta ce, "Ko ko za'a sayo 'yan holokon nan ne da dan cokali na robar nan a zuzzuba a ciki?" Na ce, "Oho." Rahma ta mike, "Baaba kin tambayi wannan ita dake jin haushi sai kace wadda za'a yiwa auren dole? Bari inga abincini." Suka tafi. Inna ta ce da Mama, "Baiwar Allah nan tana kokari, Allah ya saka mata da alheri." Su Mama suka ce Amin. Rahma ta dawo tana cewa, "Abinci yayi kyau, ta zuba wadatattun kayan lambu, yanzu bari a dauko naman nan a zuba a kai, na bada kudin take away din." Nan suka zuba abincin da naman kaji, ga drinks, Innarmu ta ce, "To shi Babanku kinje kun gaisa?" Na ce, "A'a." Ta ce, "Yana dakin Malam Garba ki je." Nan na fita, Shadad ya biyoni na rike masa hannu, ina jin lokacin da wasu ke cewa, "Hala wannan shine dan nata?" Ban damu da in juya inga ko su waye ba, na fita. Mun gaida da Baba, ya dauki Shadad tare da cewa, "Muhammadun ne wannan?" Na ce, "Shine." Ya ce, "To Allah ya yi masa albarka." 'Yan daurin aure sun zo ance nan suka kwana gidan aminin waliyyinsa ko?" Na ce, "Eh." Duk da ban sani ba, ya ce, "To Hafsatu, ke dai ba kankanuwar yarinya ba ce, Allah ya kawomu lokacin auranki, don Allah kiyi hakuri ki zauna da Mijinki lafiya tare da ladabi da biyayya, ni dai in kin min haka kin gama min komai." Yayi mata nasiha sosai, ya ce, "To Alhamdulillah, Yayanki Umar shine ya sai miki gado da kujeru daidai karfinsa, Baabarku kuma ita ce ta sayi duk abinda aka dafa, sadakinshi da shi aka sai miki katifa da fuloli. Sai dai Innarki da tace ta zo da kudi sai kin zo za'a shawarceki, nima ta gefena dangi sun zo daga Maiduguri sun bani gudummawa dubu goma ce na ba Umar." Na ce, "Oh Allah! Mai rufawa bawa asiri, Allah ya saka da alheri." Ya ce, "Amin, Allah ya baku zaman lafiya." Na dawo gida na bar Shadad gurin Baba, Innarmu ta ce, "Ya miki bayanin komai ko?" Na ce, "Eh." Ta ce, "To ni nan gurina kawunanki da sauran dangi sun hada dubu hamsin, ni kuma nayi adashi na dauki na dubu sittin, sai na bada hamsin, goma kuwa na basu Ummi saboda anko da suka ce tunda Yayanki hidima ta masa yawa.Sannan ta ce, "Shi kuma Babansu Rabi'u (mijinta kenan) ya bada dubu hamsin, nan dubu dari da hamsin kenan gaba daya sai asan yadda za'a yi da su." Na ce, "Ni dai Inna duk yanda kuka yi daidai ne." Muryata ta soma rawa zanyi kuka, "Ban zaci zaku kula ni kumin wannan gatan ba, dan na riga na watsa muku kasa a ido." Kanwar Innarmu ta ce, "To komai ya wuce Hafsat." Innarmu ta ce, "Kayan kicin zaku je ke da Rahma kasuwa ku sayo yanzu tunda an ce ana gama daurin aure zaku wuce da kayanki." Na ce, "Da an sani ba'a sai kayan anan ba, don tafiya yola da kaya aiki ne, in naje can a siya." Inna ta ce suma sai da aka siya sannan suka zo, amma an ce su zo da motar dibar kaya, dan Umar ya fada ma angon cewa su zo da ita. Na ce, "To yanzun me za'a siyo?" Ta ce, "Ke kika san abinda ya kamata." Na ce, "Tab, to ni ai bani ma da komai tunda Karatu nake yi banyi tunanin auren nan kusa ba." Ta miko min kudin nace Rahma ta karba. Mun fito zamu tafi muka ga Sakina kanwata 'yar wajen Baaba nace ta zo mu tafi. Muka je a motar Rahma nan kasuwar bacci, na sai kayayyaki su TV da kayan kitchen duk na amfanina da su blender da sauransu. Mun kashe dubu chasa'in, ragowar kudn na sai kayan gara dan ma Inna ta yi cincin, dubulan da alkaki. Muka sai shinkafa buhu 2, taliya 3, semi 4 manyan galan na manja da na man gyada 2-2. Nan dai muka kashe kudi, sannan muka nufi gida. Mun samu ana loda kaya wai motar kaya zata yi gaba, don haka Rahma tace ma Yaya Umar ga wasu a saka a tafi da su. Ya ji dadin ganin garar da nayi ya ce, "Dama ita yake ta tunani ina zaya samu kudi ya saya?" Ni kam na shige gida guri tunda ya soma cika.Misalin karfe biyu aka daura aurenmu da Abubakar, lokacin da wata marokiya ta shigo tana rangada guda, jikina yayi sanyi lakwas, yau na zama matar aure, sai dai nayi missing din al'adunmu, kamar sa lalle, kamu, ko fulawa ba'a zana min ba bare gyaran kai. Na watsa ruwa na zo na zira Jallabiyyar cikin akwatin da mayafinta. Rahma ta zo ta sani sai da nayi kwalliya na shafa turare, sannan ta taya ni na zabi sarka da 'yan kunne da abin hannu zuwa zobuna, nan take na yi kyau. Jallabiyyar ta sha ado. Ta ce, "Ki zo ku gaisa da su Hashim da Sagir za suyi Yola, mu sai gobe da Asubahi. Kinge kenan muna da lokaci yau da yamma sai muje muyi gyaran kai tare da yin fulawa.Na ce, "Ke nifa in dai da Abubakar ba zan fita ba don kada ya yarfani a cikin mutane." Ta ce, "Suna wani shago can da Umar ya kaisu, suna cin abinci." Muka nufi shagon gurin su Hashim, Abubakar bai zo ba Sagir ya soma min tsiya, "Gata ango, gata Ango, cancadin shagali." Hashim ya ce, "Yi ma Umar waya ya turo mana mai hoton nan dole Ango ya ga hoton wannan shiga, sai kace Balarabiyar Sudan Masha Allah!" Na ce, "Kuna dai zagi na ne, kuma na gode." Muka gaisa Hashim ya ce, "Baffanmu sun tafi don Jirgi zasu bi mu kuma da ku Asubanci zamu yi." Na ce, "Gaskiya mun fa shirya Walima a Kano." Rahma ta ce, "To sai dai randa kika dawo kuyi." Na dubi Rahma, "Gobe zamu bar Yola ko? Don ina son yin karatu nan da kwana goma zamu fara zana Jarabawa." Hashim ya ce, "Ture batun komawa Kano gobe don Yola goben ne zamu soma namu biki." Sagir ya ce, "Mu ma sai an gama biki zamu wuce, na fada gurin aikina." Na ce, "Um!" Tunani na daya ban dinka komai ba, waton bani da sabon kaya, Rahma ma tayi wannan tunanin, amma bata ce komai ba lokacin wayar Hashim ta yi ruri ya daga kawai sai na ji ya ce, "Yawwa Munnir, ka shigo layin? In ka shigo layi na 3 din muna nan a wani shago jikin masallaci." Tsigar jikina ta soma tashi, kafafuwana suka yi rauni har na kasa rike kaina, na jingina da bango. Duk sakamakon sunan da naji an kira "Munir." Duk da bani da tabbacin akan cewa wanda na sani din ne. Ban ankara ba na ji muryarshi a kofar shagon yana sallama, numfashina ya yi sama da kyar na kwato shi, yana shigowa gurinmu ya soma jeho idanu shima mutuwar tsaye ya yi yayin da muka kalli juna ido cikin ido.Hashim da bai kula ba fadi yake, "Abinda ka makara, tuni an daura auren." Sam Munnir ya kasa kauda kanshi daga dubana, ban san nufin kallonshi gareni ba, amma ni kallon tsana ce da kiyayya mai tsanani nake masa, zuciyata ta shiga fadi min cewa, "Tashi ki shake shi, wanke shi da mari." Tsam na mike na fice a fusace, Hashim ya ce, "Zo mana Hafsat lafiya?" Rahma ta mike ta kwala min kira, "Hafsat! Hafsat!" Sam ban saurara ba ko ganin gabana bana yi, da ganin Munir gara ganin mai daukar raina. Na share zufa bayan na zauna, sam ban ji me su Innu suka cewa ba, ashe wai ina ta tsallake mutane ina wucewa.Rahma ta zauna tana tmbyata "menene? sai alkcn hawaye suka soma sin tiri akan fuskata. ckin kunnena tasa tana cewa shine baban shadad ko? naji sunansa munir tunda hashim ya ambata" Ban tanka taba, sai da nayi kukana ma'ishi, tun mutan dakin suna tmbyata har suka hkra. Rahma tace, fada min idan shine' nace shine me zaki masa? ta mike nace koma ki zauna" tare da riko ta. Na sauke numfashi Rahma barshi, abu daya nake son san menene dangantakarsu da abbkr? indai yan uwane to fa in sama da kasa zasu hadu ba zan zauna da shi ba, Rahma tace daina msalin nan babu kyau yanzun ki bari zan kirasu gashim anjima Na ce ki barsu kawai zan bncika a sannu, sukam su sagr mamakin hafsa ne ya cika su,sai dai shi hashim ya zargi wani abu.Lallai shadad yana matukar kama da munir ya dubi munir wanda ya kasa zaunawa yace zauna mana ranka ya dade, ga abnci, munir ya zauna bayan ya ciro hankici yana share zufa,sagr ya mika masa hannu suka gaisa, haka ma hshm. Nan dai suka juya hira,ya nuna sagr "wannan ne angon? Hashim yace a'a yana yola, kasan na fada maka mata 2 zaya aura. shadad na rike a hannun yaya umar, dawowarsu kenan daga gdan yaya umar din. yace kawu bari in je gurin antyna, tana can dakin? umar yace "Ehh don shigarsu dakin ne yAya umar ya fita shi da shadad sai yanzu suka dawo. ya shiga da sallama jikin sagr ya nufa yana me fadin Uncle ina antyna? sagr yace tana gda. munir ya tsurama yaron ido,gabanshi yana wata irn faduwa ya bi yaron da ido lkcn da yaron ya fita a guje. tamkar ya cafko yaron yakeji don ya sake kallonshi da kyau,ko kuma duk cikn firgicin ganin hafsa din ne? ya mike cikin tashin hnkali,yace to Hashim Allah yasanya alkhairi, nizan tafi. Hashim yace da sauri? munir yace em inada dan wani uzurine, suna fita yi masa rakiya sai waiwaye2 yake,ya shiga motarsa ya tada tafe yake yana zantuka shi kadai, tmbayr kansa yake" shon wannan yaron mai matukar kama da shi dan hafsa ne? cikin sane kenan ta haifa?a fili yace lallai zan amshi dana dubi yanda kaunarsa ta zirga ckin jinina,amma kuma.... ya doki kan styarin motar tare da cwa tab nasan za'ayi rigima,yanxun wama zan tunkara da wannan magnar? tunda iyayena ba wanda yasan zancen? ko gdansa yakasa zaune da tsaye,duk ya damu gashi badama ya fadawa matarsa. sai dai ya yanke shawarar dadynsu da zancen, Nikam ban da tursasawar Rahma bazan yi wani lalle ba,amma haka tasa sakinarmu da ummi suka nemo mai zanen fulawa ta yarfa min a hannuwa. tasiyo man shamfo sbd anwuce da akwatunana (lefa) dama kayan dangi daban suka kawo wai suddaje. don haka ba'a taba nawa ba,tayi min don tayi tayi nace bazani saloon ba, na manta da wani abn takaicin da rahma tamini tarkacen mata ne wai sai nasha. Nace matama gwara takwashe tarkacenta inba hakaba zatayi asarar kudinta, don zubarwa zayi, tace gashinan cikin jakata in naso naje nazubar, inkuma na shirya sha to inkirata taimin bayani yadda ake amfani dasu, nace kanki akeji, gdan yaya umar mukaje kwana, sam na kasa bacci, gaskia bansoba naga munnir sai naji nakara tsanar maza, Allah ya sani indai dan'uwan abkr ne toba zan zauna cikin zuri'arsuba, ke amarya tashin manta doguwar tafia ke garemu? Wanka kawai nayi don ina fashin sallah, na kintsa jikina sosai muka fita tare dasu ya umar, ummi da matar ya umar duk tare zamu tafi dasu, dangin inna duk tare muka tafi dasu, nida sakeena da rahma a motar hashim da sagir, harda shadad aka tafi, lallai yola akwai nisa, tun muna tafia ina hira har nai bacci dan bantaba doguwar tafia irin hakaba, bamu isaba sai gaf da magrib, tunda karfe 6 na safe, kuma wai haka dinma sai naji ana cewa munyi sauri, dankareren gate ne muka dosa, sai kace na gdan yari, muna shiga gdan dam da mutane haske ko'ina, mayafi naja na rufe fuskata, lkcn naji gdan yadauki guda anata fadin gasu nan sun iso, rahma ce take rungume dani, har zuwa kofar shiga tace, kishiga da kafar dama kiyi addu'a, hakan nayi, sannan aka zarce dani can dakin, nan da nan zugar dangin suka cika falon, har dakin da nake, sai fillanci ke tashi, daidaikune suke mgn da hausa irin wadda bata goge din nanba. wata ta duko kaina, amarya bude fuskarki muganki, ke kam wane irin kyaune dake har hamma yafita hayyacinsa danke? Na sake sunne kaina cikin cinyoyina, wata tace, nana ke kam baki ganta acikin hotunan kalanda ba? Tace nagani, sonake inganta afili, rahma tace, sai kingaji da ganinta, tunda nan zamu bar muku ita, ankawo kulolin abinci, shinkafa da miya da nama, sai kunun gyada da sauran drinks, suka dan rage nan muka shiga cin abinci, nikam wanka na mike zanyi, bayina acikin dakina yamin kyau, nafito na zura kayan bacci, sukuma suka shiga sallah, rahma tace, shine zakisa kayan bacci? Nace ina naga sabon dinki, tsofaffinma banzo dasuba, na saka katon hijabi, sukuma cikin daren nan suka hau yin jeren dakina, sun saka kujeru a falo ina juyosu suna tababa, anan za'asa, anan zaifi kyau, suka dawo daki suka hada gado, suka dibi na kicin sukaje suka jera wanda shima kenan falon, matsayina na yar talaka amma iyayena sunyi kokaro, suka hau gado suka kwanta nikuma nakwanta kan kafet dan nasaba da kwanan kasa, rahma tazo kusa dani takwanta, sai wayarta tashiga ruri, nace to masoya ga angonki nan, ta fito da wayar tana cewa, yanzun nanfa muka gama dashi, kurum sai naji tana cewa, ango_ango, munyi fushima, baka kira ba muna hanya, mun iso tuni ka sharemu, ina jiyo muryarshi ....... Zaharaddeen shomar whatsapp 08168575100 Sanadin Boko 3-06 Posted by ANaM Dorayi on 05:57 PM, 28-Sep-15 Under: SANADIN BOKO yana cewa, ai munata yin waya dasu sagir, sun tabbar min kuna lfy, na tabe baki yace, to yaya kuke? Tace lfy, mungama shirya muku komai, gobe asubanci zamuyi gda, yace au, kuna nufin baxaku tsaya ayi budan kaiba? Tace ai mun gama budan kai tunda munkawoma ita. yace to nawa zan fansheta? Rahma tace mekenan? Nima na tashi zaune tare da kara matsowa, sannan na kara kanga kunnena, yace, toni kam bansan yadda zan muku bayaniba, amma zaifi kyau ku tsaya dan kar kubar mata abin gori, kunsan halinku dai mata, rahma tace, to zamu tsaya, sai daifa mu bamusan yanda kuke gabatar da al'adunkuba, sannan amarya bata da dinkakken kaya, yace meya hanata dinkawa? Kodai bata shirya aurenaba? Tunda tun asali bani takesoba? Rahma tace, wannan batun aiya wuce, don dama bata da wanda takeso, zuwankane kakoya mata soyyaya, yace rahma kenan! Ai ina zaton soyyayar da kawarki ta iya niban kai gurinba, amma dai ya wuce ta bakin naki, sannan kuma za'a kawo mata kayan sawa, mu nan garin dama haka ake kai kaya, don amare basa amfani da kayan akwatin sai dai ayi musu a gidajensu, rahma tace, hali keyin haka, mukam talakawa irinmu kuwa lefen muke amfani dashi, ta canza batun da cewa, ina angona? Yace mun saidashi, tace tabdi! Ba'a kake, da kunga gayyar kanawa, don Allah yana kusa banishi inji muryarsa kona samu nai bacci, ya saki daria, na lura kin shagwaba sagir dayawa, shiyasa yadamemu da tadinki, na sulale a hankali na kwanta, da alama bata fahimci abinda yake nufiba, suka gama surutunsu da mijinta sannan sukai sallama da hirar soyyayarsu, dare ya tsala, kowa na kwasar baccin gajia, amma niban dani sbd hakikanin gaskia kalaman abkr sun soki zuciyata, mutsu mutsu nane yatashi rahma, tace a hankali lfy? Nace rahma mekika fahimta da mgnr abkr? tace namefa? Na juyo da cewa, yace damacan bashi nake soba, sannan yace soyayyar dana sani shi baikai gurinba? Lkcn dakikace zuwanshine ya koyamin soyy, rahma tace, kinsan nifa bakoda yaushe nake zama nazarin mgn irin hakaba, amma ke mekika fahimta? Tace wlh rahma koyaya mutum yai zance nasan meyake nufi, inada wata baiwa tadaban akan karantar mutum, ko zolaya yayi ina gane manufarsa, nufin abkr damacan munnir nakeso bashiba, sannan na iya soyyayar da baikai gurinba, to sbd soyyaya nasakarwa munnir kaina har na samu ciki shiko bai taba hakanba, rahma tayi shiru itama ta fahimta, amma don kada na tashi hankalina agane inada damuwa sai tace, kada kiyi masa wani zato, ta yiwu ba nufinsa kenanba, (kai abkr na gasawa hafsa mgn gaskia, yan'uwa kuja mai kunne mana) nace hum! Rahma tuni na hararo irin zaman da zamuyi da abkr shiyasa nake gudun aurena, yanda na fahimci halinsa, shi mutum ne mai tausayi dason kyauta, sannan mai jajircewa ne akan abinda yakeso, wanda bai kaucema addini, sai dai kash! Yanada naci tare da mita idan an masa laifi, sannan baya bincike bare saurare, kinga kozansha wuyar zama dashi in nayi la'akari da irin halayen nan, sannan zai dinga jefamin mgn, hwy suka soma zubomin tare da sintiri afuskata, Rahma tace, duk wannan hasashen nakine, don haka kibar mummunan zato a kanku, kiyi fatan alheri, nace to Allah yaxaba mana mafi alheri, sai kusan assalatu sannan nasamu bacci ya daukeni, da safe karin kumallo mai kyau

Chapter 16 of 22