Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ba komai ba, ni Allah kadai nake tsoron na sabawa ba mutum ba, zan je kuma zaka ji sakamako." Har ya fita Hashim ya ce, "To yaushe zamu je wajen Fadin?" Tsaki Abubakar yayi sannan ya yi gaba. Lamido ya tarbe shi cikin fara'a, ya ce, "Ubana ka iya zabe, domin ko da ni ka bari to da wuya na zaba maka irin wannan Babban kamu, lallai kun dace." Abubakar ya sunkuyar da kai cikin daure fuska ya ce, "Ni fa ba nine na ce ina son Fadi ba." Ya ce, "Duk wanda ya hada ku yayi maka gata." Abubakar ya ce, "Ni wadda na zaba daban, bana son Fadi." Ya ce, "To kila ka gaji takwaranka Mahaifina kenan, tarihi ya nuna mana duk cikin zuri'ar nan shine mutun daya taba auren mata 2 lokaci daya. Fada min wadda ka zaba ita ma yau akai mintinta, rana daya duk a sa su a lalle." Abubakar ya yi shiru, Lamido ya ce, "Duba, taso ka matso nan, ka fada min wadda kake so." Abubakar ya matso, ya dubi Lamido, "Wata yarinya ce a Kano, sunanta Hafsatu, bata daya daga cikin zuri'armu....." Wani wawan mari Lamido ya sakar masa da bayan hannu, ya mike tsaye cikin fada mai tsanani yana cewa, "Tir da kai, ba zaka surka mana Zuri'a ba, tunda muka taso zumunci iyayenmu suke yi, don haka muma ba zamu daina ba har bayanmu, don kana takama da boko, bokon banzanka, na yi tunanin shine yasa kake zagaye-zagaye, kana juyamu kamar waina (masa), to kaje da Iyayenka zan yi, don ina girmamaka saboda sunan Ubana, zan ajiye uban a gefe in kamata inci mutuncinka, baka wuce duka ba a gurina, FITA!!!!! Abubakar ya tashi ya fita. Kafin wani lokaci ya kira dukkan manyan 'ya'yanshi ta waya ya fada musu yana nemansu gobe da safe. Abban Abubakar yana jin kiran ya sha jinin jikinshi kan batun Hamma ne, domin Dada ta fada masa komai game da abin da Abubakar ya ce. Ummi ta shigo dakin yana ta sintirin kai kawo, ta ce, "Hamma!!!" Ya dubeta ta ce, "Ka ja surutu cikin dangi, ko a Makaranta surutunka 'yan uwa suke yi, wai ka canja hali yanzu baka da biyayya, ni kam ka yarda da Fadin mana." Abubakar ya kama hannun Ummi ya rike kam, "Tun farko ina rokon Allah ya bani macen da nake so, zuciyata ta san da Fadima, amma ta kama son Hafsa ranar da na fara ganinta, nasan kema zaki so ta Ummi." Ummi ta ce, "Hamma ina son duk abinda kaima kake so, sai dai bana son matsalar dangi, zaka yi kallon halin da su Dada zasu shiga, tunda kace Lamido yana nemansu." Ya ce, "Ki taya ni addu'a, so baya barin mutum ya ji tsoro, ni da kaina na fadawa Lamido batun Hafsa, jikina yana bani zan yi nasara, kullum cikin mafarkin Hafsa nake." Ummi ta ce, "Allah ya amsa." Lamido ya mike yana kai kawo a tsakanin 'ya'yansa wadanda suke zaune akan kafet. Dukkansu manyan mutane ne masu fada aji, domin wannan yana wane wannan ne a kudi. Ya dubi Mahaifin Abubakar ya ce, "Ibrahim dauki wayarka ka kira min danka Abubakar." Nan take Abba ya aikata haka, shima Abubakar nan take ya bar komai ya nufi gidan Lamido. Abubakar gabansa ya fadi ganin daya yiwa Iyayanshi kamar masu neman gafara. Dakin yayi tsit sai karar agogo, jiki a sanyaye shima ya zube tare da sunkuyar da kai, sai dai duk da haka bai ji a zuciyarshi cewa zai canja daga batun son Hafsa ba. Lamido ya ce, "Abubakar!!!" Cikin zafin rai ya ambaci sunan. Abubakar ya dago da kai ya dube shi, Lamido ya nuna su ya ce, "Su waye wadannan?" Abubakar ya kalle su ya ce, "Iyayena ne." Ya ce, "Da kyau." Ya ce, "To ina son ka fada musu abinda ka fada min jiya." Abubakar ya sake dubansu gabanshi na faduwa, musamman da suka hada ido da Baffa Magaji, Lamido ya ce, "Ka fada musu nace." Abubakar ya kasa magana. Ya ce, "OHO!!! ni ka raina kenan da ka zo ka same ni kafada min saboda ba nine na haifeka ba?" Baffa Magaji ya ce, "Ka yi magana mana, wane ne sa'anka a nan?" Abubakar ya ce, "Dama kan batun yarinyar da nake so ne, wadda ba 'yar cikin zuri'armu ba." Dukkansu suka hada baki gurin tambayarshi, "Me ka ce?" Illa Babanshi da ya sunkuyar da kai cikin matsanancin takaici. Baffa Magaji ya ce, "Kai ko Shaidanin yaro ne, zaka kawo mana sabon al'amari cikin zuri'a." Lamido ya daga ma Baffa Magaji hannu, sannan ya ce, "Ban taraku kwanakin baya ba na gaya muku cewar kar wani daga cikin 'ya'yayenku ya kawo mana wani sabon al'amari a cikin zuri'armu ba?" Duk suka ce hakane. Ya ce, "To lokacin ina zargin Abubakar zai aikata haka, gashi zatona ya zama gaskiya. Don haka yanzu kai Ibrahim tunda ka kasa tankwasa danka ba ka iya bashi tarbiyya ba, ina son ta bakin ka kafin kuji ta bakina." Abba ya nisa ya ce, "Lamido Allah ya huci zuciyarka, na jima ina fama da Abubakar akan wannan matsalar, sam ya ki bin umurnina, don haka ina son 'yan uwa da suke zaune ku zama shaida, daga yau na cire shi daga cikin 'ya'yana. Ina son Lamido ya cire shi daga cikin zuri'armu don girman Allah. Baffa Sa'adu ya ce, "Ina rokon alfarma gurin Lamido, da ya ba Abubakar dama muji uzurinsa kafin a yanke masa hukunci." Lamido ya ce, "Gashi ga ku." Baffa Sa'adu mai rike da sarauta a yanzun wato Mahaifin Hashim ya dubi Abubakar ya ce, "Dana fada mana dalilinka na son ka saki layin da ka same mu a kai?" Cikin karfin hali ya ce, "Baffa duk ciki ban samu mace mai irin halayen da kamannin da nake so ba." Abba ya ce, "Ka ji ko? In ba rainin wayo ba ace duk zuri'armu masu kyau da ilmi da tarbiyya amma ace ya rasa matar aure? Sai ya je yayo mana rore-rore?" Baffa Magaji ya ce, "Muna jin shi ai, ya fada mana irin matar da yake so muji dame yake takama." Abubakar ya ce da su Baffa, "Bana son macen da an kalleta za'a san kyakykyawa ce, nafi son baka kuma zuri'armu kusan duk kyawawa ne farare, game da batun halaye kuma, nafi son mace da bata cika wayewa ba, sai wadda bata cika buri ba, mai ilmi duka 2, mai tarbiyya da hankali da natsuwa, sannan kuma 'yar talakawa wadda za taji magana ta, ta girmama Iyayena da duk wani nawa, mai tsoron Allah a duk inda take, mai hangen na kasa da ita ba na sama da ita ba, wadda bata da rawar kai. Baffa kada ku yi zaton na raina tarbiyyar 'yan matan zuri'armu, ko ba za'a samu mai irin wannan hali a cikinsu ba, a'a za'a samu matsalar daya ce, ina son na auri wadda nake so kuma take so na, ba wacce take sona ni kuma bana sonta ba, Manzon Rahama ya hana auren dole, don yana da illoli, bana son a cikin zuri'armu akwai dayawa wadanda zaman hakuri da biyayya kawai suke yi, alhali babu biyayya ga abokin zamansu, hatta dan sabawa mahalicci." Baffa Magaji ya taso ya ce, "Wato auren zumuncin ne sabawa Mahalicci? To sarkin iya magana fada mana inda aka ce ya haramta?" Abubakar ya gyara zama, "Aure bautar Ubangiji ne, a duk lokacin da aka hada Ma'aurata dan dole ba so da kauna, to ba zasu yi wannan bautar ba yadda Ubangiji ya ce, maimakon lada sai kaga zunubi ya samu. Mu dauki misali da gidan Yaya Saleh, duk family ba wanda bai san tashin hankalin da suke ciki kullum ba, banda kuma sauran dangi da ba'a sani ba." Baffa Magaji ya ce, "Lallai Abubakar, boko ya sa ka fitsare idanunka, kana rigima damu saboda aurenka." Abba ya ce, "Duk wannan zantukan naka basu isa su zama hujja ba, tunda ba littafin da yai hani ga auren zumunci." Lamido ya ce, "Ikon Allah!!! Ashe tun ina da rai zan samu wani a zuri'armu da zaya kalubatanceni akan al'adarmu? Dole ne na dauki mataki, in ko ba haka ba in na mutu zumuncinmu rushewa zai yi." Abubakar ya ce, "Ku yafe ni, ba zan zama sanadiyyar rushe zumuncinmu ba, haske na zo mana da shi cikin zuri'a, ku kwatanta dani zaku gane nufina nan gaba. Ma'ana ku barni na auri bare." Baffa Sa'idu ya ce, "Abubakar mene ne dalilinka na cewa ba zaka auri mace mai kyau ba? Alhalin shine burin duk wani namiji." Ya kalli Abba, "Da ban san yin wannan batun ba, amma yanzu ya zama dole na fada, dalilai 2 ne suka sa nace ba zan auri mace dan kyau ba. Na 1 Yaya Mansur in baku manta ba lokacin da aka ce ya nemi Waslia bai ki ba, ya ce ko ba komai ai tana da kyau, da suka yi hadari fuskarta ta lalace, har yau ba wanda bai san irin wulakancin da yake mata ba. Abu na 2, lokaci mai tsawo daya gabata. (Abba ka yafe min abinda zan fada, ina dan yaro lokacin kun dan samu hargitsi da Dada, na ji kace mata abu 2 ne suka sa kake zaune da ita, na farko biyayya ga Lamido, na 2 dan kyanta da take da shi. Ta yiwu ka manta, kayi min afuwa ban so na fada ba) A lokacin in zaka tuna ina karami amma raina yayi matukar baci kwarai, da muka je Makaranta nake fadawa Hashim sai ya ce Ai shi jiya ya ji Dadarsu tana fadawa Abbansu zaman hakuri kawai take yi da Abbansu, don ita ba shi take so ba, daga lokacin na kudurce a raina bazan taba aure ba, sai wadda nake so take sona. Ina son iyayena ku taimake ni, ku duba hujjojina, in kunki ni zan hakura in yi biyayya amma har abada ba zanyi farin ciki ba. Duk jikinsu yayi sanyi, kuma sun tabbata kowannensu yanada shigen wanan matsalar ko shi bai son matar ko ita bata son shi, amma wanda suka hada kansu su suna zaune lfy. Baffa sa‘adu yace, ina rokon lamido yayi mashi izini yatafi, mukuma munyi shawara. Lamido yace, ya iya tafiya. Abubakar ya mike cike da kwarin guiwa ya fita. yasan adu‘a bata faduwa, don tashi yake tun 2 dare ko 3 yana fadawa Allah matsalar shi. Lamido ya dubesu daya-bayan-daya, kuna nufin kun amince da batun sa? Baffa jume yace, a a sai yanda kace. Baffa sa‘adu yace, da zai yuwu hujjojinsa sun isa a duba lamarin, koda a gaban kotu ne. Amma in zancena ya bata ran lamodo aimun afuwa. Lamido yace ban gamsu ba har yanzun, biyayya muke bukata kuma kuje kuci gaba da shirin biki duk suka watse, kowa zuciya cike da nazari. Da dare ya sake zuwa gidan Baffa sa'adu don ya lura shi mai saukin kaine, kuma zai iya taimaka masa har yaga ya ci nasaram ya ce Baba na zo ne naji ko kun gamsu da bayanin bayan tafiyata? Baffa ya ce, Lamido bazai taba amincewa ba, ni kaina na cutu da wannan hadin da ake yi tsahon lokaci, sai da na sake Aure sannan na sami nutsuwa. Dalilin musgunawar da mai dakina take min duk dan ranta baya son auren mu. Aure na da Bilki ita ma 'yar dangi ce amma ni na ganta na ce ina sonta, ta yarda. Daga kanta ne na gane aure kina so ina so shine aure, in mace tana sonka tana kaunarka da ka sami matsala zata fara tausayinka, zata yi komai don ta faranta ranka. Amma in mace bata kaunarka, Abubakar akwai matsala babba. Ni yanzun shawara daya zan baka, ka gwada. Kaje ka sami Limamin Masallacin Juma'a kasan aminin Lamido ne ko?" Abubakar ya ce eh, ya ce to kaje ka same shi kayi masa bayani da neman tainakonsa, kila a dace. Kasan mu 'ya'yansa ne bamu da wani karfin tankwara shi, ga rikicin tsufa. Muna son mu lallaba shi ne har mu rabu lafiya. Abubakar ya ce za shi. Sai da kafa ta dauke sannan ya shiga gida. Don yana tsoron haduwar shi da mahaifinshi. Yana maida kofa ana turowa, sai da gaban shi ya fadi, zaton shi Dada ce, amma ai yaga Ummi ranta a bace. Ya matsa ta shiga, ya dubi agogo sha biyu ta gota, ya ce Ummi kina menene baki bacci ba? Ta zauna "Hamma ka janye auren kan nan mana, Dada ta yini kuka, hawayenta ba sauki bane a wajenka." Ta zamo ta durkusa, "ka dubi Allah kayi hakuri ka yarda cewa haka Allah ya so ganin zuri'armu. Ya kama ta, "Tashi Ummi Dada da Abba zasu fahimce ni da zarar komai ya daidaita, kije ki kwanta, fata na daya ki taya ni fada ma Allah shine kadai mai maganin matsalata. Baffa Sa'adu ya bani dama ta karshe, idan har na gwada bata yi ba, na dauki alkawarin cewa na hakura." Ta ce "zanci gaba da yi maka addu'a," Ta fita. daga sallah asubahi bai dawo ba saboda tsoron haduwa da mahaifansa, gidan Hashim ya karya duk da ruwan tea ne ya sha. Yayi wa hashim bayani, hashim yace, sannu namiji. Kayi kokari, zan rakaka gurin liman. Bayan la‘asar suka sami liman agida, sun gaisheshi sannan suka gabatar da kansu, yayi murna da jin jikokin amininshi ne, daga nan suka kora mashi jawabin komai. Liman yace, to zan ganshi in Allah yaso zamu tautauna batun, in kuma ya sausauta ra‘ayinsa to akan nada kyau, don nasha yunkurin in fada mashi wanan al‘adar tayi tsuri, musanman in yana bani lbr matsalar gidan yayansa ko wasu daga jikoki wadanda basa zaune lfy. Amma nakan fasa in na tuna yanda ya dauki lamarin. To yanzu tunda dama tasamu zanyi kokari in nusar dashi. Sukayi godiya sannan suka tafi. Duk aranarce dai liman yayi tattaki zuwa gurin lamido, sunyi murna da ganin juna, duk da cewa ko yaushe suna haduwa. Sun gaisa sannan liman ya soma da cewa, aminina gurinka nazo da batu mai matukar muhinmanci, duk dacewa batun nawa ba zaiyi maka dadi ba. Amma inaso kakali lamarin ta fiska 2, addini da kuma zamani. Ni da kai dukanmu musulmai ne, muna koyi ne da manzon tsira (s a w) addini ya amince muzabawa yayanmu maza na kwarai amma bai yarda muyi musu auran dole ba. Idan muka dubi fiskar zamani zamuga cewa, mubar yayanmu suyi auren so da kauna, zaifi bamu kwanciyar hankali. Lamido yace, oho! Abubakar ya kawo maka karata kenan? Liman yace a a yazone yanemi da in rokyaka ka amince, yayi aure da wada yake so, wai shin ma wane dalili yasa ku rike wanan al‘adar sai kace bauta? Lamido ya ce iyaye da kakaninmu suna gudun hada iri da wani ne saboda kada mu gauraya da mugun iri. Liman yayi dariya sannan ya ce, da kai dani da bature da balarabe da igbo da hausa da duk wani yare daga mutum daya muke shine Annabi Adamu Alaihissalan. Sannan Manzon Rahma ya fada mana Musulmi 'yan uwan Musulmi ne. Lamido ya ce, amma nasha ji daga bakin ka kana cewa mai yanke zumunci ba zaya shiga Aljanna ba, wata rana kace ba mai shiga Aljanna sai mai sada Zumunta. Liman ya ce to ai ba ana nufin ka kamo wannan ka ce sai sunyi aure ne zumunta ba. Abinda ake nufi shine Ziyara, kwana biyu ka dade baka ga dan uwanka ba, shirya kaje ku gaisa kuyi zumunci, wannan shine sada zumunta. Yanke zumunta kuwa shine kace wane baya zuwa, don haka nima na gaji da binshi bazan je ba, kowa ya zauna a inda yake. Shine yanke zumunta, don haka ka sassauta ra'ayinka ka tafi dashi daidai da zamani. Sannan daidai da turbar addinin Musulunci, cewa aka yi in zaku yi aure ku nema wa 'ya'yanku Uwa ta gari. Sannan ana auren mace saboda abubuwa guda hudu, asalinta, kyawunta, kudinta da Addininta, Manzo SAW ya ce na hore ku da ma'abociayar Addini, don haka shawara anan sai ku duba, suwaye iyayenta? Kuma wanne irin hali gareta? In mai Addini ce shike nan. Ku hakure ku cebakomai saikuga ci gaba, ku cire 'yar wani dangin kusa ta cikin naku shine karuwa, shine zumunci dangin ku sun zama 'yan uwa da danginta, kuma ko bayan ranta zaku yi ta zumunci da danginta. Liman ya dinga bashi misalai tare da Hadisai zuwa Ayoyi, har jiki Lamido yayi sanyi, ya ce to zai gana da 'ya'yanshi, in yaso za a bincika aji asallinta. Amma fa sai dai in ya yarda ya hada mata biyu, domin baza a fasa Fadi ba. Liman ya ce, "Wannan ba laifi ba ne." Lamido ya kuma tara 'ya'yansa ya gaya musu cewa, sakamakon zuwan da Liman ya yi yayi masa bayanai da dama akan wannan lamari, dan haka ya nada Baffa sa'adu da su binciko masa 'yar wane ne? Sannan ya ce da Abba in yaje gida ya turo masa Abubakar. Ko da Abba ya dawo gida bai samu Abubakar ba, sannan duk wayoyinsa a kashe suke, ya kira Hashim yake gaya masa in ya ga Abubakar ya fada masa Lamido yana neman sa. Tare suka je gurin Lamido ya ce, "Hakika kana da sa'a, zan amince da auren in naji cewa Iyayenta masu mutunci ne, itama 'yar mutunci ce. Sannan kuma in ka yarda ka hadasu 2 ka auri Fadi itama. Sannan ita yarinyar tunda bakuwa ce anan gida na zaka kawota mu zauna da ita muga irin nata dabi'un." Har zai ce wani abu sai Hashim ya zungure shi, sannan ya ce ya amince. Lamido ya ce, "Shi bashi da baki ne sai kai?" Sannan Abubakar ya ce, "Na amince." Lamido ya ce, "To sai kuje, in mun shawarta lokacin da za'a je zaka ji."Farin ciki gurin Abubakar baya misaltuwa, ya isa gidansu da karfin gwiwa. Dada tana zaune suna hirarsu da Rukayya, ya zube gabanta yana neman gafararta, sun ji komai daga bakin Abba, sai dai ta ce, "Shawara daya zan baka, kada ka yi rawar jiki akan bakuwar da zaka kawo cikinmu, ka nuna kamar kafi son 'yar uwarka a kanta, ka tashi mun yafe maka. Ka samu Abba ka bashi hakuri, sannan ka samu Hashim ku je gurin Fadi." Ya ce, "To." Ummi cikin murna ta ce, "Ni kam in zaka Kano zan bika muje na ga Hafsat." Ya ce, "To, Amma sai na fara zuwa in na dawo sai muje tare."shi da Hashim suka nufi gidan Goggo Jami, sun jero ita da Fadi zasu fita, hannun Fadi rike da makullin mota, sai ga Abubakar. Suka tsaya Goggo da fara'a ta ce su shiga. Fadi ta musu sannu da zuwa, suka gaisa sannan Goggo ta koma ciki tasa a kawo musu abin sha duk da cewa da safe ne. Fadi ta gaishe su, Hashim ne ya ce, "To Fadima, kin san dai dalilin zuwanmu tunda magana ta yi nisa, yanzun ma yana kan hanyar tafiya ne muka biyo. In ya dawo zamu zo zuwa na musamman." Ta ce, "OH, zashi gurin KISHIYATA ko? In kaje ka gaidata." Ta mike, "Nima zan je office ne." Suka mike suma, Abubakar bai yi magana ba, Hashim ne ma ya mata sallama. Suna hanya inda Hashim zaya kai shi filin jirgi don zuwa Kano. Ya ce, "Kuna ta fadin Fadi nada mutunci, dubi irin tarbar da tayi mana." Hashim ya ce, "Kishi ne, taga kowa a family ita daya ake aure, amma ita su 2, dole ta damu." Abubakar ya ce, .... zaharaddeen Shomar what's app 08168575100 Sanadin Boko 2-6 Posted by ANaM Dorayi on 11:25 PM, 19-Sep-15 Under: SANADIN BOKO "Ummi fa dole ta tsani auren Fadi, saboda ita bata da kirki, da ace ina da yanda zan yi to ba zan auri Fadin ba." Hashim ya ce, "Na kula ai da zaka yiwa Lamido musu ne, shiya sa nayi saurin amsawa." Haka suka yita hira har ya kaishi filin jirgi, yau dai da farin ciki ya nufi Kano, kuma baya jin zai samu matsala da Hafsat. Tunda bawan Allah nan ya tafi na kasa sukuni, ga rigimar Shadad yana Aunty Uncle fa? Tun ina cijewa har ta ni da kiran layin wayarsa, amma abin takaici ana fada min yana kashe. Daga bisani nayiwa kaina fada na watsar da lamarinsa. Shadad ya murmure ya koma makaranta nima na koma bakin aiki na. Na yi mamakin Manaja da bai ce min kala ba, su Ishak ma sai mamaki suke yi, na kuma ci gaba da zuwa makarantata. Tun mun horu da shan garin rogo, yanzun ma shi na jika ma a matsayin abincin dare. Na shimfida mana tabarma a tsakar gidan kasancewar lokacin zafi ne ga Kano akwai zafi. Muna cikin sha naji bugun gida, na tashi naje na tambaya wanene? Muryar da ban tsammace ta a lokacin ba ce. Ya ce ni ne Sadeek, jiki yana bari na bude, ta re da haska wayata, na ce "Sannu da zuwa, shigo." Ya shigo Shadad har yana faduwa garin gudu yana fadin "Uncle." Uncle ya daga shi sama, na kakkabe masa tabarma ya zauna.nakawo masa ruwa, nazauna ina cewa ina yini? Yace lfy, ya jikin shadad? Nace ya sami sauki. Don ya latsani yaji ko na damu dashi yace, shine tun da natafi ko flashig nace ai bakamin sallama ba,kuma wayar taka ai akashe take. Yayi murmushi, yau naga canji anty. Kina ta min fara‘a yau ba daure fuska ba harara, why? Nace ina sa ran zan sami lbr mutumin kirki a gurinka, wanda ya taimakeni tsawon lokaci da ya wuce, mutumin da ya fara gina karatuna, yace meyasa kike tsamanin samun lbr sa gurina? Nace, kun dibi kama, sannan kayi mun batun da yayi min a lokacin baya, wato na buga kudi, yace, fada mun yanda kukayi dashi, na kalmashe kafa. Na zaiyana mushi yanda mukayi da shi, yayi dariya. Banyi mamaki ba lokacin da yace, wai hafsat me na kara ne kika kasa ganeni. Alhalin ni kuwa tun lokacin da muka daukeki zuwa wajen buki rahama da sagir na ganeki, duk da da yarinyace kwarai kuma siririya, in kina yar gala-gala takar yar siririyar kafar ta karye. Nace dama kaine? Sunanka abubakar sadeek? Nce wallahi ban ganeka ba, idanunka dai in nakala sai inga kamar na taba ganinka, kai gaskiya fa tunda muka hadu kake taimako na, na gode Allah ya saka maka da mafificin Alkairi. Sannan ina so ka yafemun rashin kunya da rainin da nayi ta maka bisa rashin sani. Yace, nifa bakiyi min komai ba, asalima burgeni kikayi, ya kali kofin gari bance ki daina shan gari ba? Nace shi muke dashi, yace ina indomie da na sai muku? Ace ba ajiya ka bani ba? In zan kwana ban ci ba ba zan taba abin wani ba, yace naku ne fa, banaso muyi jayaya yasa nace maki nawa ne. shadad yace uncle bakace ka daina guduwa ka barni ba? Yace, tafiyar gaugawa ce ta sameni. Ya dube ni yace wannan zuwan na musan man dan ke, duk da zuwan da na dun gayi abaya suma dan kene, ki shirya gobe zamu tauna muhimmin zantuka zan shigo, nace to. Ya mike ki dafa ma shadad indomie, zakaci ko? Shadad yace eh, yace to ni zan tafi kada kayi rigima, zan zo da safe in kaika school. Yace, to uncle, suka rakashi bakin kofa sannan suka rufe gidan suka dawo. Tun da na kwanta bayan nayi shafa‘i da wuturi na kasa bacci. Tunanina wacce irin magana zamuyi? Nasani ba zaya wuce zai yi mun batun bayan rabuwa ba, domin nasan zaya iya cewa zai mai dani gida. Niko anawa ganin lokacin komawata gida baiyi ba, duk da ina ceke da son kannena, da yaya umar, harma da shi babanmu. Inna kuwa ita nafi son gani, ina so kafin na hadu da ita sai na zama wani abu a SANADIN BOKO. Zan wanke laifina zanyi abun da na kasa a baya, a fili nace banyiwa inna adalci ba, Allah kada ka dauki raina sai ka hadani da ita na roke ta gafara. Kuka ya kwace min, da dakina zaiyi magana da zaice yasani lokacin kuka na kenan.ringin din wayata ne ya ka tseni, na dauka ina kalon numbobin, nayi mamakin yanda na hadace numbobin shi aranar da na fara ganin shi. Nayi salama muryarsa kasa-kasa bani son ya fahimci nayi kuka, ya amsa kin soma baci ko? Nace a a yanzunan na gama shafa‘i da wutiri, yace shadad fa? Nace yayi bacci shi tuni. duk mukayi shiru har saida na duba naga wayar na kunne, nace kana jina? Yace ina jin ki, muryarki nake son ji ki min hira. Nace wace irin hira? Yace ko wace, ina jinki. Me kakeso mu tautana gobe? Yace wannan sai gani gaki, nace to Allah ya kaimu, yace amin. Yauwa, ummi tace in gaisheki, bansam me yasa naji faduwar gaba ba, nace wacece haka? Yace kanwata, itace autarmu. Nace to ina amsawa. Ya akayi ta sanni? Yace, duk dangina sun sanki, labarina ka basu? Yace, eh, to me kace masu? Yace, zan fada maki shi gobe. Nace, to wai meyasa ka damu da ni tun farkon ganina ina yariya kake ta taimako na? Yace kila Allah yayi nine kawai don in taimakonki, kila watarana kayi min gori, shiyasa bana karbar taimakon maza, ko kasa in saka maka da wani abu wanda bani da izini a kansa. Yace, me kike nufi? Yaci gaba, kada ki damu kanki, ni bakince rance nake baki ba, zaki biya ni, nace dame zan biyaka? Naci gaba da cewa, kai baka cikin wadanda zasu cuceni, kai na daukeka yayana ciki 1. Yace a a kada ki dora min dutsin da zai shiga tsakanin halas da halas, nace kamar yaya? Yace sai dai nazo gobe, yace kiyi bacci dani a ranki zakiyi mafarki innazo kifada min, goog night. Ya kashe wayar. Nayi shuru ina so in tono abubuwan da mika tau tauna, amma na kasa, illa kalmarshi ta karshe da yace kada nashiga tsakanin halas da halas, dan kawai nace shi yaya nane na daukeshi uwa daya uba daya? Kamar yanda na saba duk bayan sallah asubahi sainayi azakar, haka da magariba. Yanzuma na gama namike na cika bokiti daruwa na nufi wanka. Da nafito nazo na tashi shadad, yana bude ido nace mashi adu‘ar tashi daga bacci kada ka manta. Nan take ya karanta. Na sunkuce shi sai bayi, nai masa wanka nasashi yayi alwala, na zura mashi jallabiyar sa mai gajran hannu wanda na sai masadon yin sallah. Nace to maza yi sallah kuma kayi adu‘a yace to. Na koma na dauko sabulun da mukayi wanka dama na wankine nazo na wanke muna kayanmu, cikin raina ina mitar kayan shadad duk sun kode inna sami kudi zan sai mai wasu. Tsaf na shiryashi cikin kayan makaranta na dafa mashi indomie, na share ko ina gyara. 7 da rabi na gama komai, sai kurum naji bugun gida, nazaci dan a daidaitana ne sai da na bude naga Abubakar tsaf cikin

Chapter 11 of 22