Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kofar falon suka yi sallama, Yadikko ta amsa tare da bude kofar, ganin su Abubakar ta fadada fara'arta, tana masu sannu da zuwa cikin harshen fillanci. Sun zauna a falon suka gaisheta, ta amsa tare da tambayar mutanen gida, suka ce lafiya, cikin hanzari ta nufi dakin 'yan matanta guda biyu, tace Maimuna ga baki can falo su Hamma ne ku kai masu abin sha. Jamila ta mike da hanzari, haka ita ma Maimuna kowacce tana fatan gurinta yazo. Tun fitowar su ya tsaida hankalinsa gurinsu, tabbas da don kyau zaiyi aure da ya zaba, amma ba ra'ayinsa kenan ba. Cikin yanga Maimuna ta gaishe su, yayin da Jimila keta rawar kai gami da tsuga surutu. Maimuna kam tun daga gaisuwa ta ciro waya tana ta yin abinda bai sani ba, chattin ne ko game. Hashim yayi kasa da muya yace wacce tayi? Kafin Abubakar ya bada amsa, Jamila tace Hamma don Allah inga wayar ka. Ba tare da ya bata wayar ba ya mike. Hashim tashi lokacin sallah yayi, ya dube su ku kira ta muyi sallama. Maimuna ta dube su har zaku tafi? Ko ruwan kai Hamma baka sha ba. Yace zan sha wata rana, yau kam na gode. Yadikko suka jero da Jamila nan dai suka yi masu sallama, a hanya ne Hashim yake ta damun shi da son jin wacce ya zaba, yace ni fa babu wadda tayi min. Hashim yace don me? Ga Jamila, Abubakar yace bana som mace mai yawan surutu da rawar kai, gami da bincike, wannan ya nuna in na aureta zata dinga daukar wayata tana min bincike ko kuma tana min bincike a daki. Ya ce, Maimuna fa? Ita ma a'a ban cika son mace mai shiru sosai ba, sai yawan danna waya, hankalina bazai kwanta ba, domin zata iya share ni tayi ta mu'amularta da waya. Hashim yace, tab, to wallahi bada ni za a gurin Lamido an jima ban don haka kaje ka masa bayani. Abubakar yace tare zamu je, zaka ga kamar bazan iya yi masa magana ba ko? Hum, bari mujem suna gaban Lamido duk sun yi shiru, shi kanshi Abubakar yana jin zuciyar shi na rawa, tamkar bazai iya bayani ba. Amma ya daure yace babu wadda ya zaba, ya kawo dalilansa. Lamido ya tsura masa ido, zuciyarsa na zargin Abubakar nason kawo masa sabon salo ne cikin zuri'a, amma sai ya danne yace naji. Hashim tun daga gobe Asabar har zuwa rana irin ta yau, ku zaga duk zuri'ar mu Abbab ya zabi wacce yake so in na Yola basuyi ba ku tafi har Adamawa, kai har 'yan Kaduna da Abuja da Kano kuje ya zaba. Tsahon sati biyu na baku, ina jiran amsa. Abubakar yace to mu gode sai dai a duba yanayi ayyukan mu. Lamido yace wannan ya rage naku, ku zaku cire lokacin da kuka ga zai dace ba tare da kun shiga lokacin aikin ku ba, ku tashi kuje. Sun ajiye bayan isha zasu dinga bin dangin kila a dace. Sati guda suna zagaye gidajen dangi, amma ko ina sai Abubakar yace bata yi ba, wannan yace kazama, wannan yace zatayi rowa, wannan yace ta cika yawo. Hashim yace to muje gidan mu ga kanne na, su kuma yace basa jin magana, irin su daya da Rukayya kanwata. Hashim yace haka ne amma fa bazaka samu mace dari bisa dari da irin halin da kake so ba, su dama da kashin hakarkari akayi su kaga kenan a karkace suke, in ka dage cewa zaka mikar dasu sai su karye. Abibakar yace, look bance maka dama ba, amma irin matar da nake so nasan zan samu. Hashim yace kasan me zamu yi? Tunda yau goma ga watan daya, saura kwana biyar ayi family meeting mu jira ranar in kowa yazo sai ka duba Abubakar yace Allah ya kaimu Duk shekara suke yin mitin na zuri'ar su, suna yin taron ne a gidan tsohon wato Lamido, suna tattauna matsalolin 'ya'yansu da su kansu a taron, duk wata kowanne mai matsala yana fada ta kudi ko ta wani abin da yake suna da asusun da suke tara kudi duk wata. Sai a dauka ayi maganin matsalar da shi, tunda kuma ba duk dangin bane masu kudi, sai dai masu kudin sunfi talakawan yawa. Tun ana gobe taron ake kada shanaye biyu saboda yawansu, Lamido ke bada su, yayin da wasu daga cikin manyan 'ya'yan zasu yi ta kawo kulolin abinci manya kala daban daban, yan nesa irin su Abuja Kaduna tun Juma'a suke dauko hanya. Dada ta shiga dakin bayan ya amsa sallamarta, ta ta ganshi kwance cikin bargo kasancewar lokacin sanyi ne tace, ka tashi fa Abban ku fa ya tafi dasu Ummi da Aliyu da Kasim. Usman da Umar kuwa na tabbata yanzun sun tafi da iyalansu. Shiri yayi tsaf cikin kayan alfarma, in ka ganshi zaka yi zato cewa sarki ne, shi da Dada ne kadai. Gidan ya cika makil, filin da aka saba yin taron tuni an shirya shi da kujeru, gurin zaman iyaye daban, na 'ya'ya daban haka ma na jikoki. Dole su baka sha'awa, yanmata da samari ga sunan, wasu dama anan suke hada kansu shikenan, Lamido hakan na daga cikin abinda yake sashi jin dadi a taron, gurin su Hashin Abubakar ya nufa, a gabaki dayan tsararrakin sa babu wanda bashi da yara........ har saitin su usman da umar duk sunyi aure, hatta usuma da umar suna da matansu matar usman tana da tsohon ciki, ta usuman kuwa tana da danyen goyo, dukansu suna aiki ne a kar kashin abubakar don mutun ne mai adalci, kansu umma a hade yake. Hashim ya soma yi mashi tsiyar cewa ya makaranta, salisu yace ba dole yayi maka ba, tun da bashi da mai tashin sa. Sani yayi tsagal yace, azumin nan mai zuwa sai munyi mashi kidan tazuru, yace zakuyi ku gama. Hashm ya turo mashi kujera zauna dai dai nan ka samu damar kalon yan mata gasunan iyaka gininka. Ya zauna tare da cewa ku tayani duba, sun bude taro da adu‘a kamar yanda suka saba, sannan aka gabatar da marasa lafiya dan ayi masu adu‘a sannan sauran abubuwan suka ci gaba. Daf da karshene wanin baffan su mai suna yusuf yace ya kamata kafin a tashi daga taron nan a saka ranar abubakar, dan kowa ya san lokacin, duk iyayen sun amince da hakan. Lamido ma yayi na‘am. Abubakar dai zuface ta rufeshi, yayin da a bokan wasa suka ta masa dariya. Sukuwa yan mata kowace tana son taga wacece mai rabon nan. Shi kuwa tuni taron ya gundire shi. Anci ansha samari sun sami yan mata wasu kuma sunyi kari, amma abubakar duk basuyi masa ba. Hashim yace gasu khalisat yayan baffa na abuja, yace wadan nan yaran masu salon tsiya, barni kawai. Kamar daga sama yaji lamido na kiran shi tacikin abin magana, Hashim yace to kaifa kila yau ta yan tatsuniya za a yi maka, irin na 'ya'yan sarakunan nan ace mata su jeru namiji yaje ya zabo. Abubakar ya mike ya mufi gurin Lamido, yace ina so yanzun nan ka shiga cikin 'yan matan nan yanzu ka fitar da mata ka, nasa ranar auren ka wata biyar daya ga watan. In kayi lissafi zai zama wata hudu da kwana goma sha biyar kenan, kafin lokacin kun fahimci juna." Nan da nan dangi suka sheda suka shiga murna, shi kuwa gurin zaman shi ya koma. Hashim yace tashi mu duba, yace dan Allah ka bar ni ka ji." Haka taron ya tashi ba tare da Abubakar ya zabi mata ba, hakan ya kona ran mahaifansa da Lamido, daga bisani kakarsa Gogwal kodai bashi da lafiya ne? A bincike shi, sun tsare shi ya ce shi kam lafiyar shi lau, amma bai samu kawai mai irin halayen da yake so bane. Cikin bacin rai Lamido ya ce sun zura masa ido amma ya sani rana baza a daga ba ko ya sami mata ko bai samu ba, in lokacin yayi zasu daura aure da duk wadda suka ga dama. Abubakar kuwa ko a jikinsa, cikin hakan ne bikin abokinsa Sagir ya taso a Kano, yaje yayi arba da yarinyar da ya santa a Kaduna lokacin da yaje (Bautar Kasa), tana talla mai yawan wasa, kusa shekaru goma baya. Yana son sanin abubuwa game da yarinyar kuma yana jin wani abu a ranshi game da ita, sai dai abin tambaya ta tara halayen da yake so matar shi ta kasance? Ya iso gida daga gida Hashim, gaban iyayan nashi ya zauna a kasa, Abban ya dube shi yau in ni na haife ka ina son ka fada min nufin ka damu. Dada tace dazun su Yafendon shi da suka zo dukan su kowa na cewa yazo ya sasanta da 'yar gidanta, na ce masu dai kun sanshi in ya yarda shike nan, amma fa ni bazan maku alkwarin ko ya yarda ba. Don haka ka fitar da mata kada ka hada ni da 'yan uwana, Abba yace yama fada mana nufin shi kawai, in yana da wata matsala ne sai ya kawo uzurin sa muji, in ko lafiyar shi lau to raini ne da walakanci, baka jin kunya kannan ka duk sunyi aure cikin dangi ko ina lbarinka ake, fada min nufinka." Ya danyi dim don yasan abinda zai fada yanzu zaya girgiza su. Dada kayi magana mana. Ya dan numfasa yace, naga wadda nake so." Abba yace, ko kai fa, fada min wacece yanzu na sanar da Lamido ta waya." Yace tana Kano." Suka hada baki gurin cewa, Kano? 'Yar gidan Goggonka Furera?" Ya ce a'a ba dangin mu bace. Suna hada baki gurin cewa, ba dangi ba? Eh, ya dago ya dube su, ba zato sai yaji saukar mari gefe da gefe, sannan ta rufe shi da duka. Sunkuyar da kai kawai yayi tayi ta dukan shi. Abban su kuwa sunkuyar da kai yayi ba tare da yace Dada ta daina dukansa ba, har sai da ta bar shi don kanta. Cikin tashin hankali take cewa ba zaka jawo mim abin fada a cikin dangi ba, kai ne mutum na farko da zai kawo matsala a zuri'ar mu? Tur! Ba dani za a yi ba, ta fice daga falon rai bace, yana nan zaune Abba yace kasan dai kazo da abin da bazai yuwu ba ko? to ka cire wannan tunanin a ranka in dai kana so kaci gaba da zama danmu. ya mike shima ya fita dàga falon, Abubakar yana zaune cikin halin da baza yace gashi ba, yafi awa daya saññañ ya fito ya tafi dakinsa. washe gari sam iyayen basu amsa gaisuwar sa ba, wannan lamari ne mai girma. Ya zama dole ya faranta ran iyayan sa, yasan idan tasu ne zai iya shawo kan su, tsoron lamido da sauran dangi suke yi. Shi kuma yana so ya kawo karshen wanan auran, domin wasu na cutuwa, an hada su da wadanda basu so. Sannan ko mai mace zatayi wa namiji ko shi yayi mata babu rabuwa, yasan ba wai haramun bane auran zumuncin, to amma yanda zuri‘arsu suka dauke shi tamkar ibada, shine yake son su gane auren bare ma ba haramun bane. Akan gadon shi yake ta juyi tare da neman mafita, ya kalli agogo 11 a fili ya furta Allah yasa hashim bai yi bacci ba, ya daga wayar sa yasa a kunne, bayan ya laluba num hashim din. Tayi kuka har ta katse ba‘a dauka ba, don haka ya ajiye wayar yana miyar hashim har yayi bacci sai kace mace. Kusan minti 30 wayarshi ta soma ruri, ganin sunan hashim ya daga da wuri,ya soma korafi ka cika baci kamar mace. Hashim yace ina tare da iyalina ban san tayi ringin ba, duk da tana kusa dani in ka fahimce ni ka kira lokacin ina duniyar ma‘aurata, bana tare da ku. Abubkar yace ban tam bayeka ba, sannan Allah dai ya tsine ma mai tona asirin iyalansa, don haka sai kai hattara. Kasanan dalilin kiran da nayi maka? Hashim yace sai ka fada? Abubakar ya gyara kwanciya sannan yace, kila kaji mamakin cewa wadda nake so ba a cikin zuri‘armu take ba ko? me kake son fada mun? Hashim ya mike ya nufi falo dan kada matarshi shatu taji abin da zasu tau tauna. Kada kace zaka shugo da bidi‘a cikin zuru‘ar anan, kasan hakan zai jamaka matsala kai da mahaifin ka? Abubakar yace haba hashim kai fa ba jahili bane, abinda kake kira bidi‘a ba haramun bane. To auren zumunci sunna ne? Ka fada mun a matan monzon Allah wacece yar uwarsa ko a kwai bata wuce guda 1 ba, kuma duk matansa yan kabilar sa ne?Dashi fa muke koyi, don haka matar da aura ina nufin ba haushiya ce, ina zoton ma ba zawara ce, kaga kenan zanyi sunna. Hashim yayi tsaki, wannan karan bana tare da kai, matsawar baka canja tunani ba. Me hausa sukafi yaren mu na fulani? Kyau ko asali? Abubakar yace look! Hashim ka fahim ceni sosai, ba al‘ada ce a gabana ba, addini nake son awa agabana, yarenmu suna da kyau da asali da kuma tarbiyya, amma ban ga wadda tatara irin halin da nake so ba. Ok inji hashim. Ita wannan ta tara duk abin da kakeso? Abubakar ya tashi zaune, ba zan saniba sai dai na ga 1 daga ciki, saura sai ta bani dama mun zanta. Hashin yace kana nufin baku taba zantawa ba? Abubakar yace ni ke sonta, ita bata san inayi ba, domin bata so in kusanto ta, na dai taba sanin ta da. Hashim dan Allah ka natsu, ina so ka taimaka mun yanda zan shawo kanta, zanfi tsayuwa kan ra‘ayi na inna tuna wanda nakeyi dan ita, ta san ina yi. Hashim yace, abinda zai fi kaje ka fada mata nufinka, ka ce mata kana sonta kuma zaka aure ta, na san zata girmama zan cenka don matan da suka san abin da suke yi, suna girmama zancen aure. In dai ba wani ya riga ba. Abubakar yace ta tsani maza, ina zaton namiji yayi mata laifi. Hashim yace kaje, in baku sasanta ba ka sanar da ni, sai mu koma tare. Kai dai kasan yan da zakayi mahaifanka kada su shiga fushin lamido. Yace zan ga me zanyi. Sukayi sallama. Arana ta 3 ce daada ta shigo dakin shi, da wowarshi kenan daga office, tace ka sauya ra‘ayin ka ne ko kanan kan bakanka? Ya kwantar da murya. Dada kiyi hakuri, wlh wace nake son aura musulma ce mai tarbiyya. Tace amsa kawai zaka bani, ba. Tace amsa kawai zaka bani, bana son dogon turanci, ya ce to duk yanda kuke so haka zanyi, tace uhm! Isa da kai kaje ka cire mata a dangi, ta tausasa murya, da zakaji tawa ma, ka sami lamido ka fada mashi ya zabo maka. Na tabbata zaka wanke lefukan da kowa ke ganin ka dashi. Muma zaka ciremu a zargin da lamido ke mana, na san baka sami lbr mitin din da lamido ya kira su abban kuba ko? Ya dube ta, na sami labari sai dai ban san abun da aka tau tau na ba, duk da nasan dan ni akayi shi. Tace to ya tara yayan shi maza ya sanar dasu cewa bai yafe ba duk wanda ya bari dan sa ya kawo bakon lamari a cikin zuri‘armu ba, yace za‘a yanke mumunan mataki a kanshi da yayan ta hanyan yanke zumunci da su Zaharaddeen Shomar whatsapp. 08168575100 Sanadin Boko 2-3 Posted by ANaM Dorayi on 07:34 AM, 19-Sep-15 Under: SANADIN BOKO Abubakar yayi shuru, yayin da jikinshi yayi sanyi lakwas. Al‘amarin mai girma ne, yace dada kada ki damu, zanje gurin lamido amma ina so ku daina fushi dani. Tace to mu dama fushin mu don kaki bin abin da muke so ne, da kabi shi kenan mun huce. Yace to zanyi duk me kuke so. Har zuciyar shi ya san ya amsa ne kawai, amma ba dan zai je wajen lamido da batun a zaba mashi mata ba, zai jene da batun wanda yake so amma sai yaje kano ya dawo. Tun dare ya shaida wa mahaifan nasa cewa zai shiga lagos a gobe, don tau taunawa da wasu abokan kasuwan cin sa a bisa wata cinikayya da zasu yi. Sukayi masa adu‘a da safe karfe 9 ya hau jirgin kano. Sai da ya huta a masaukin shi sannan ya daga waya ya kira layin sagir yace yana kamo don Allah ya kawo masa mota. ******* ******* ***** Tun dare zazzabin shi ya tsananta, kwana mukayi babu bacci, gashi bani da ko parasitamol bani da kudin saya cikin yan satitikan tsananin babu ta dameni, jiya ko girki banyi ba. Da dadare garin rogo muka sha muka kwanta, jikin sa ya tsanata sosai da safe har da safe har ta kai numfashin sa na futa dai dai. Nace ka bari dai in watsa ruwa sai mutafi asibiti tunda kan da kati, ko da bani da na mota, ina saka hijab na lura ya mike idanun sa sun kafe hakoransa suna datsewa, dukda ban san suma ba tabbas suma ne wannan. Cikin matsanancin tsoro da firgici na sunkuce shi da gudu nayi waje ina fadin innalilahi wa inna ilaihir raju‘un! Kamar daga sama na ganshi tsaye jikin mota, da gudu na nufeshi ina cewa, ya mutu! Ya mutu!! Da sauri ya karbe shi yasa a mota bai jirani ba ya figi mota kamar dama abinda yake jira kenan. Na koma cikin gida ina zagaya ina kai kawo, kusan awa 3 sannan naji tsayiwar mota da gudu na fita, shi kadai ne ya fita fiskar shi mur tuk, ko bai fada ba nasan shadad ya cika.da gudu na juya cikin gida ina kuka, hakika nayi rashi. Na zube kan katifa nayi kuka na gode Allah, sai nace Allah yasa mai cetona ne. Ina fitowa sai nagan shi jingine a bango, na daure nace ka daukosh bari naje na fadawa su maman rahama. Yace ki ce musu me? Ya rasu mana, yace inji wa? Na kara matsawa kusa dashi me kake nufi? Yace ya far fado nazo ne in kaiki gurin shi. Likita yace typort ne ya kamashi da kyau. So, yanzu in kin gama kukan ki shirya ki dauki duk wani abu da zaku bukata a can. Yan kayan shi kawai na diba, sai nawa guda 2, da daudumar sallah da alkur‘ani. Na fito yace kin dauki komai? Na ce eh. Amma kafin muwuce bari na sanar da maman rahama, kada suji shuru. Yace to ina jiranki a mota. Sai da na kule gida sannan naje. Asibitin kudi ne mai tsari dakin mu kadai ne har da kayan kalo ga na‘ura mai sanyaya daki da taruwa. Na kafe shadad da idanu, duk ya rame yanata bacci. Hawaye sai sauka suke a idanuna, yace min yana zuwa. Bayan fitarshi likita yazo muka gaisa, ya tambayi mai jiki nace da sauki, yace bai tashi ba ko? Nace eh yace to idan ya tashi ki bashi abinci ko da ruwan tea ne, sai ki bashi magungunan shi an siyo? Nace banga ta kardar maganin ba ai, yace tana hannun baban shi, yace dan Allah kada kiyi masa wasa da magani, nace to. Yana fita na soma tinanin ina zan sami kudi? Gashi ko abincin da zan bashi bani dashi in ya tashi. Nace oh Allah na gode maka a wanan hali da kasa ni, Allah ina mai naiman sauki a gareka. na dauki wayata na kira Rahama na fada mata muna asibiti an kwantar da shadad, tace taji gurin Abubakar, gasu nan zuwa dashi da sagir ma. Kusan minti 25 da yin maganar mu sai gasu. Rahama ce gaba dauke da katon kwando da kulolin abinci da filas na ruwa zafi, Abubakar da Sagir suka shigo da ledoji. Ya nufi yar durowan da ke gefen gadon ya jera kalolin jus ne da ruwa. Sannan sai magun gunan shadad ne ya zuba su a wani kwando dake jikin gadon, kila an tanade shi ne dan zuba maganin dama. Sagir ya koma ya shiga da dadduma mai girma, ya shinfida ta can gefe suna fiskantar gadon, rahama ta dauko kwandon ta zuba musu da fadukan shinkafa da kayan lambu, sai farfesun kifi. Ta zo ta daukar musu ruwa tana cewa bari na sashi a fridge saboda naji babu sanyi. Ni dai sai bisu nayi da idanu. Rahama ta dube ni, bari in sa mana, nace zuba dai dai cikin ki. Abubakar wanda ya zauna saiti na da na dago fiska sai mu hada ido, na daure fiska Rahama ta sani ni magana 1 nake yi shiyasa bata matsa min ba, ta zuba nata ta juyo kujera kusa dani, ina bakin gado ne ta soma ci. Ya kurbi ruwa me yasa ba zaki ciba? Na dan tsuke fuska, sannan na dube shi haka kawai. Ya kali kofar shigowa, kamar mai nazari. Can ya sake duba na, amma ba don kin karya ba, kuma ba don baki jin yunwa ba?ban karya ba kuma ni bance bana jin yunwa ba. Rahama ta ce, Alhaji abubakar dama ka barta, domin duk abinda tace tana nufin hakan. Abubakar ya dubi Rahama, yace kina nufin bata karyawa? Rahama tace a a ina nufin duk maganar da ta fada ba zata canja ba, shi ne dalilin da yasa kaga da tace ba zata ci ba, ban matsa mata ba. Ya ce ok. Duk kamshi ya cika dakin sagir da Abubakar kasa kasa suke hirarsu. Wayata ta shiga ruri, nayi tsam tare da son in tashi taro da son inhasashi ko wanene, ina dubawa sai naga number super markert din mu. Gabana ya fadi, sam na manta da wani aiki. Ida nuna suka kai kan Abubakar, ya kafe ni da ido da alama yana so yasan wanene ya kirani? Nikam a zatona manaja ne, na daga da sanyin jiki. Ba muryar shi ba ce, nace ishak ne ko musa? Yace ishaq ne yace munjiki shuru ne kuma manaja yace baki ce bazaki zo da yanma ba, tun dazu yace kina zuwa ki sameshi ofis. Ya numfasa yace ranshi fa ya baci, wai shi kin soma isarsa. Nace ishaq don Allah kace yayi min uziri, yaro nane ba lafiya duk na rudene shiyasa ban tuna da aikin ba, yanzu haka muna asibitin anbashi gado. Yace to kikirashi ki fada mishi, dan kada ya gane nine na kiraki. Nace to na gode. Na dafe goshi na, Rahama tace ya akayi? Kin san cewa na manta da batun aiki? Shine Ishak ya kirani. Na shiga dan na wayata ina son in duba account dina, duk da nasan bani da kudi, ko ina ziro ziro, nashi gshi bani da kudin ma da zan kira manaja sai in na sa. Rahama ta ce ga wayata ki kira shi, na harare ta kina hauka ne, zan kira wani namiji da wayar ki, bayan kinyi aure? Ta ce to menene, ba da nima Ogana ne ba? Nace sam, da kika ce, ki tuna mijinki har canza maki layi yayi don kada mutane su dinga kiranki, kuma hakan yayi daidai, don ya nuna kishin ki. Yanzu sai na kira Manaja? Alhalin yanzu baki da wata alaka dashi?, tace to naji. Sagir wanda bansan suna jina ba, yace a to fada mata gaskiya. Na dube su, idanun Abubakar su suka sa na sunkuyar da kaina.Yace, "ga wayata ki kira, na girgiza kai, ka barshi na gode, ya shiga danna lambobi, ban sani ba sai naji yana cewa Manaja yarinyar nan Hafsa tana da uzuri, don haka bazata samin zuwa aiki ba sai bayan wani lokaci da bazata iya cewa gashi ba, don haka tana son uzuri.Na tsura masa ido, a raina ina cewa ji mutum zaya balgace min aiki na, bayan dan shiru kadan da yayi sai yace, to shike nan. Ya dube ni "menene na zare min ido? Ya yarda, nace na gode. Amma ba haka ya kamata ka tambaya ba saboda shugabanane a gun aiki. Ya ce yanzun nayi laifi kenan, na girgiza kai alamar a'a, sannan nakai dubana ga Shadad.Sai bayan munyi Azahar sannan ya farka, naba bashi tea. Abubakar ya bashi magani, naji dadin yanda ya bashi don ni idan na bashi kuka da su amai yake yi, amma shikam ya bashi cikin lallashi kuma yasha. Amma sai yace masa Uncle bazaka kara guduwa kabarni ba, ya ce eh amma sai kasha magani. Cikin rawar jiki yasha, na kanyi al'ajabin irin son da Shadad yake yiwa Abubakar, domin ba shine mutum na farko da ya fara masa magana ba, bai taba zuwa gurin kowa ba sai shi.Sun fita sai ni da Rahama na kasa rike abin da ke ciki na nace, Rahama wai me wannan abokin mijin naki yake nufi da ni ne? Ta ce baki tambaye shi ba? Na harare ta in ya bani amsa zan zo ina tambayarki ne? Na jima ina tambayar sa bai bani amsa ba nifa gaskiya bana son shishigin nan ki fada masa. Ta ce ke me ya hana ki fada masa, ta gyra zama Hafsat ki nutsu da kyau ki lura. Abubakar yana nemanki da alkhairi ne, koda bai fada min ba nasan kila sonki yake. Na dubeta da wani irin kallo cike da masifa nace sona? Don Allah ki daina wannan sabon, in har yayi kuskuren furta min kalmar so ai sai yayi nadamar yin hakan.Tace maida wukar, tambayar ki zanyi. Cikin harara nace, ina jinki, ta ce kina nufin laifin Munir ya shfi sauran maza? Tsakani da Allah zaki bani amsa, na ce kusan haka ne, ta ce kina dai da ilimin addinin musulunci, ance laifin wani yana shafar wani? Na ce baya shafa amma na dade ina ji a bakin iyaye na cewa maza ba yan goyo bane maza rigar kaya ne, maza basu da tabbas, maza mugun ice da dai sauran sunayen da ake kiran su da su, da ban yarda ba sai gashi namijin yayi min, don haka ni layi guda na ajiye su. Zaharaddeen Shomar whatsapp. ,08168575100 Sanadin Boko 2-5 Posted by ANaM Dorayi on 03:15 PM, 19-Sep-15 Under: SANADIN BOKO "Amma wanda ya bada wannan shawara ya kyauta, dan kai da Fadi kun dace, kuma ina zaton tana da wasu irin halaye da kake so." Ya ce, "Na rasa dalilinku na cewa mun dacen." Ya ce, "Ya kake son nayi da Hafsatu?" Hashim ya ce, "Kun daidaita?" Abubakar ya ce, "Akwai alamun nasara. Abba ne ya sani na dawo da gaggawa, saboda wasu takardu. Sati na sama zan koma ko da kwana daya ne, daga nan in mun daidaita zan kai ka ka ganta. Amma ka shirya anjima zamu je gurin Lamido." Hashi ya ce, "In dai kan yarinyar da zaka shigo da ita cikin zuri'armu ne zaka masa to ka tafi kai daya ba zan je ba." Abubakar ya ce, "Na rasa me yasa kuke tsoron Lamido haka, shi ba dodo ba

Chapter 10 of 22