Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ni ya kalle shi, sam bamu sani ba, sai dariyarshi muka ji sannan ya ce...Uncel ashe kuma kun iya kallon kuda?" shine yayi saurin janye idanunshi, ya dubi Shadad. Me ka ce? Shadad ya ce, Irin kallon kudan da yaran ajinmu suke yi, wai kada a kyafta ido.. Ni kam lumshe ido nayi, bn so shadad ya katse mu ba, domin ina karanta abubuwa da dama a cikin yalwatattun idanunshi., Jikana a mace naja filo na sulale na kwanta, Jim kadan na jiwo wayata sbd jin shigowar text. Na kalle shi, sbd ganin lambr shi ce mai dauke da sakon,shima ya dan kalle ni sannan ya maida kanshi ga Shadad. Na bude sakon,cewa ya yi "KIN YI KYAU." Murmushi ya su6uce min,dadi mara misltuwa ya rufe ni. A hankali na dago kai na kalle shi, shima ya dan saci kallona, sannan ya dauke kai tamkar ba shi ba. Na dinga kallon kyakkyawar fuskarshi, Shadad na ta krt, bana zaton ma Uncel din yana tare da shi, don waya yake dannanwa. Wani sakon ya shigo wai "KALLON FA NA NAWA NE? na kuma dubn shi, sannan na rubuta cewa. KALLON SO NE.na tura mishi,ya dago muka hada ido. Nayi saurin sunkuyar dakai. Ya mike tare da cewa, "Shadad zo muje." Na dube shi, Ina za ku?" ya ce, Tadi gurin budurwata." Na tsuke fuska,ya ce "Shadad zaka gurin Antyn nan me baka ice ream?" Da gudu yasa takalmi "Za ni Uncel, zata bani da wannan biskt din mai dadi?" Gabana ya fadi, ko dai gaske ne? nayi shiru raina 6ace . Abubakar yayi murmushi mai sauti, cikin jin dadi ya ce Zata baka. Suka fice. Na rasa me ke min dadi, Rahma ta kira ni tana min tsiya,wai miji ya dawo in dai kokarta in shawo kanshi. Cikin yanayin tausayi na ce, "Uhm! Wane shawo kai? Mu2min da ke nemn wani auran? Rahma ta ce, Daina fada min wannan zancen,tsokanarki kawai yake yi, duka-duka yaushe aka yi abin? Amma kada in katse ki, menene dalilin da yasa kika fadi haka?" Na ce, "Tun kafin yace yana sona ina jin shi yana cewa za shi tadi, su fita shi da Shadad. To yau ma yana ce ma Shadad za shi gurin Aunty yaro ya hau murna, har da cewa za'a bashi irin wannan biskit din mai dadi!" Rahma ta ce, "Kika sani ko wata mai sai da kayan kanti ce da suke sayayya yake ce mata AUNTY?" Ta ci gaba, "Ke ko bama haka ba Abubakar ba zai tarki wani aure yamzun ba, kiyi aiki da hankali mana. Kishi ya rufe miki ido, baki ga ko ke baki soma cin amarcin ba?" Na yi murmushi na ce, "Ni ko da har naji haushi." Ta ce, "Don Allah kiyi amfani da matantakarki ki fizgi mijinki." Na ce, "To Rahma duk na kasa gane mishi ne, amma yau da sauki tun da har yaba kwalliyata ya yi." Rahma ta ce, "Ki yi wadda tafi ta kafin ya dawo, ki ajiye duk wani taurin kai ko shariya da jan aji, ki zuba basirarki ki samu ki kwato shi gare ki." Na ce, to na gode. Dambun shinkafa na mishi wanda na cuda shi da nama, karas da kabeji gami da koren wake. Gida ya dime da kamshi, na hada mishi jus din kokumba da abarba da kwakwa, na nike su a blender na tace, na saka kankara da flavour. Bayan na kammala na je na tsala wanka tare da yin Sallar Magriba, nayi shafa, wata jar atamfa (java) na saka mai fulawa blue, na gyare gidan tsaf na yi shimfida a tsakar gida na jera masa, na kunna masa turaren wuta ko ina ya dauki kamshi.Shi da Shadad kawai suke 'yan zantukansu, ko nace yake taya shi shirme. Kusan goma saura ta ce, "To Madam ni zan tafi na kwanta." Muka yi masa rakiya, na yi Sallar Isha'i tare da Shafa'i da wutiri na kwanta, zan soma addu'a sai naji shigowar sako, wanda na zata shine wato Abubakar. Na bude, cewa yayi, "Ban taba cika ciki irin na yau ba, abincinki yayi dadi, zan zo in miki kyauta kuma ina son ki zabi abin da zan baki." Na yi murmushi na lumshe ido, zuciyata tana wassafo burina, na rubuta cewa, "Duk abin da ka zaba min da zaka barni ma sai in ce yaba min din da kayi ma kyaute ce a gurina." Da ya karanta sai ya ji dadin lafazin, don haka sai ya sake rubuto cewa, "In sai miki turare? Ko in canza miki waya? Ko kin fi son in canza miki wani gida kafo mai tsarin zamani? Don lafazinki yasa naji cewa dole ne ma in miki kyauta." Na yi shiru ina nazari, wato Abubakar yana so na dinga nuna kulawa gare shi, in ko haka ne zan yi ta nuna kulawata a gurinsa, sai na rubuta cewa, "Duk wannan basu yi min ba, tunda kace in zaba aba abu daya nake so, ka yarje min in fada?" Da sauri amsarsa ta shigo ya ce, "Eh, fadi." "Son ka da kulawarka kurum nake so, in zan samu sun fi duk wani abu na kawa ko na dadi da zaka bani." Ya yi shiru yana maimaita zantukan, sai kurun na ji kira, na daga tare da yin sallama kasa yanda ko wani na kusa da ni ba zaya ji ba, ya amsa min sallama shima cikin wani sauti mai nuna cewa muryata ta ratsa shi ya ce, "Hafsah!" Cikin wani irin sauti ya kirani, har yatsana naji nima nace, "Sadiq!" Ya ci gaba, "Ni naki ne, sona ke kadai yake naci, kuma zan kula dake, wannan kawai kike so?" Na saki ajiyar zuciya, "Wannan kawai shine burina, na gode." Ya ce, "Nima na gode. Ki yi bacci.......... Zaharaddeen Shomar whatsapp 08168575100 Sanadin Boko 4-03 Posted by ANaM Dorayi on 06:39 PM, 28-Sep-15 Under: SANADIN BOKO Ki yi bacci mai dadi tare da yin mafarkina." Na ce, "Kullum cikin yin mafarkina ni ke, ina sonka sosai." Na kashe wayar don jin nauyin furucina, na dauki filo na rungume na lumshe ido ina tuno fuskarshi. Shima a nashe gefen ma filon ya manna a kirji yana jin dadi. Nan take kuma sai wata zuciyar ta ce masa, "Yanzu kai saboda yarinyar da ta tabbatar maka da cewa ita karuwa ce ka ke wannan?" Nan take kuma sai ya saki tsaki tare da yin jifa da filon, zuciyarshi ta ci gaba da wassafo mishi cewa, "Ba wani son da take maka, wanda take so shi daya ne, tunda har ta bashi kanta. Kila ma da zai dawo yanzun da ta nemi ka barta ta koma gurinshi." Take ya nemi farin cikinsa ya rasa. Lokuta da dama wannan tunanin ke sa shi jin haushin Hafsah....... A zato na zai shigo da wuri, don haka na shirya masa abin kari, sai ga sakon shi ya shigo, "Madam ki yi hakuri, kila ki zaci zan shigo, zan duba ma Dada wasu daga cikin (super market) dinta. Idan mun gama da wuri zan zo da wuri, in bamu gama ba ki dubi hanyata da rana. Ina fata kina cikin koshin lafiya?" Lallai Abubakar zai cika alkawarinsa na kula da ni, to nima Insha Allah zan kula da shi. Na bashi amsa da cewa, "Lafiya lau (Hayate) rayuwata, Allah ya sa ka gama abubuwan da zaka yi lafiya, ya kawo min kai cikin kwanciyar hankali.".. Duk da cewa har Abubakar ya bar Kano babu wata mu'amala ta auratayya da ta hada mu, ban damu ba saboda ya nuna kulawarsa gare ni. Ya bani kudi, ya canza min waya zuwa (BB), ya kara min abinci. Haka nan ko da ya tafi ya kan kira ni sau 3 a kullum, nima kullum na ke kiran Mahaifanshi da safe in gaishe su, haka nan Lamido da Matanshi kullum sai na kira su cikin girmamawa na gaishe su har muka kammala Jarabawa. Lokacin yayi tafiya zuwa India akan harkokinsa, na ce mishi, "Tunda muna hutu har da Shadad ina son inje Kaduna da Funtuwa da Malumfashi." Ya ce shi kam bai yarda in je Kaduna ba, amma in je Funtuwa gurin Inna in kwana 2, Malumfashi kwana 2. Sagir zai sani jirgi in wuce Yola. Na ce masa, "To na gode." Don na lura baya son gayya. Washegari Sagir ya zo ya bani kudi dubu talatin, wai inyi tsaraba in ji mijina. Na yi godiya shima na tura masa da sakon godiya, sannan na ce, "Ko zan iya zuwa kasuwa mu yo musu tsaraba?" Ya ce, "Ki je amma ga sharudda na, ki saka katon hijabi, sannan ki kausasa murya yayin cinikayya da maza." Dariya sosai na yi, sannan na tura masa cewa, "Zan kiyaye Insha Allahu." Innarmu ta yi murna sosai da ganina, mun yi hira sosai mijinta da 'Ya'yanshi ma sun nuna jin dadinsu da zuwana tamkar sun sanni. Na bata tsarabar ta, kwanana biyu na wuce Malumfashi, daga can na dawo Kano. Sagir da Rahma suka sani a jirgi sai Yola. Hashim ne na samu yana jirana ni da Shadad, masu aiki ne suka taya ni gyaran sashen. Daga nan na fitar ma da 'yan gida tsarabarsu. Washegari da muka yi waya na ce masa, "Zan je gidan su Dada." Suma na kai musu tsarabar su Sabulai, turarurruka da 'yan kunnaye. Ummi kuma na sai mata wata doguwar riga mai kyau, tayi ta tsalle tana rungumeni, Rukayya kam sai fushi da harare-harare. Ban so jikina ba na amshi Dada da girki, dama ita da Rukayya ne, da kyar ta barni, Rukayya na ganin Daada ta fita itama sai ta bita, ta ce, "Koma mana ku gama." Ta ce, "Toh!" Da ta dawo sai ta samu guri tayi zamanta tana latse-latsen wayarta. Ummi ta shigo, "Aunty yaronki yayi bacci." Na ce to. Ta ga ina yanka albasa ta amsa. Shinkafa ce fara da miya, kuma ba mai yawa bace tunda basu da yawa a gidan, nan da nan muka kammala. Lallai girki hannu ne ba cika kayan miya ba ne, to duk abin da suke sawa suka bani amma sai gashi suna ta santi, illa Rukayya da takici wai ita sai dai ta dafa Indomie. Daada kuma ta ce bata isa ba. Na kai har bayan la'asar sannan na shirya muka koma. Daada da Abba sunata shimin albarka. Ai hutun nan na saki jiki cikin dangin mijina don jan su nake jikina, na kuma saki hannuna, kyauta tana sa dangin miji su soka.Wata rana matar wani wansu ta haihu,ya kaira ni na fada mishi, yace duk abin da ya faru nan ckn danginsa to inje.ummi ce taxo muka je barka,ranar suna ma ita ce taxo kafin na shirya na bata kudi ta siyo min kayan baby na hada da turmin xani na shirya muka je.Mai jego tana ta godia,duk wanda yaxo sai a ce ga kayan barka da Amaryar hamma ta nbata,sai godiay ake min.can muna shirin tafia sai ga Fadima ta shigo cikin isa da jin kai,da muka hada ido sai na fadada fara'ata,duk da cewa gabana ya fadi.Itama nata gaban ya fad, in anyi la'akari da aynda nan da nan ta canxa.ta zauna can kusa da yan'uwansu,huk da haka na bita na gaisheta,da kyar ta amsa ba tare da ta kalle ni ba kuma ciki-ciki.Sai yatsina taka tana harare-harare,ni dai sai mana mike nayi musu sallama na fita na kira Ummi muka tafi.Duk wata kulawa Abubakar yana bani,ko da ya dawo gidana ya sauka,gadona ne kurum baya kwana.Ni kuma ban taba nuna mishi ba,du da cewa hakan yana damuna,hutuna ya kare ya maida ni Kano.Ya siya min gado da sauran abubuwan bukata,ya kuma yimin alkwarin cewa in yaxo xaya dinga koya min mota saboda ya saya min don xuwa mkrtn.duk da cewa karatun nawa karashe ne kowa ya ganni sai yace nayi kyau Wata rana Umar ya kira ni yace jikin Baba ya tashi, yanxu haka suna asibitin Dutse.A rude an kira Abubakar a ways, yace in jira shi yaxo gobe muje, sai nasa masa kuka tare da cewa yayi hkr in je yau.Ina ta rokonshi yace shi dama baya son motar haya ne, amma in tafi in kuma kula da kaina,tare da shadad muka tafi,Baba yana jin jiki,na yi ta kuka su Babasuna ta bani hkr,wai ai jkn ma da sauki.WashegariAbubakar ya iso,nan take ya kira liktansu don suna da asibiti nan kaduna.Cikin awa guda aka canza masa asibiti.Masha Allah, zuwa washegari jiki yayi kyau. ABUBAKAR YA XUBE MIN KUDI MASU dama sannan,ya tafi.baba dasu Baabah sai godia. Na zo na zuna ina tunanin dame xan saka ma Abubakar, abubuwan da yake min? gashi yaki ya bani dama in nuna masa irin dumbin son da nake masa. na fito dga asibitin ina rike da hannu shadad muna jiran mashin don xuwa gidan Umar. Wata dirkekiyar mota ta tsaya gabana, nan nan na hade rai tare da cewa yan'iskan mutane ba dama suga mutum su kyale. kofofin motar suka bude a lkcn guda,sai kawai naga Munnir. nan take wani irin bacin rai ya xiyarce ni. Yace"Hafsy manya" nace cikin ihu kai!kai! mallam kada ka akra kiran sunana. naja hannun shadad muka yi gaba, ya biyo ni. Ki tsaya ina so ne muyi mgnr dana? Cak!na tsaya tare dayi mishi wani mugun kallo."Ba ka da daa gurina, ka fita hanyata in ko ba haka ba xaka hadu da nadama. Na tare dan mashin muka hau ba tare da an fada masa in da xanje ba. Dare muna gidansu baaba sai gashi da Mom dinsa da dadynsa,muna cin abinci da sakina itama taxo tana jiran mijinta xai xo ya dauke ta da mashin... Raina ya baci,suka gaisa da mutan gida. Mom tace "Don Allah Hafsa nake nema, nace gani. Sakina ta bata kujera Ta kure shadad da ido,da kyar na amsa gaisuwar da take min,tace "ikon Allah!! Lallai wannan yaron Munnir ne,kamannin har ya baci."Ta dube ni"yar nan nazo ne mu daidaita, wannan yaron dai jikana ne, "cikn daga murya na ce "Dana ba jikanki ba ne. na fasa kuka nan mutanen gida suka taru nace "ki fitar mana daga gida.na daga waya na kira yaya umar, sai ga shi ban taba ganin fadansa ba irin na ranar.ya ce sun san dansu ne can da ba su xo ba sai yanxu?nan fa itama Mom ta shiga masifa har waje,Munnir wai shi sai ya shigo gidanmu ya dauki dansa. Umar ya ce, shigo mu rusa maka kai, dan iska mara kunya"kai, ranar naga tashin hnkl shi kanshi shadad din ma kuka yake, ganin ina yi.Na kira Abubakar ina kuka na fada masa cewa sun xo wai xasu dauke shadad. Yace "xa suyi me?to kan me?na ce nima ban sani ba, yayi shiru can yace "xan shigo gobe. Washegari ko asibiti na kasa xuwa, sai kusan sha biyu Abubakar ya iso.lkcn kuwa Munnir suna waje tare da Umar,wai ko a ba su yaro ku su kai kara kotu,kuma su dauki lauya.Abubakar ya kalli Munnir tsaf,nan take ya ji ya tsane shi.ko shakka babu wannan shine Baban shadad.Ya ce " kan wane dalili kake son a baka yaro?"yayi mishi wani duba,sannan kai tsaye yace, Dana ne"Abubakar yace "ka taba aurenta ne?ya ce ai kowa yasan cewa budurwata ce a da. Ran abubakar ya sake baci,ya ce"don kawai tana budurwarka a da yanxun sai kazo kce danta naka ne?yace ita tasan komai ai.Umar yace to sai dai in ku ku kai karan mu amma babu wanda xai baku yaro.Abubakar yace ina Hafsat din? Umar yace tana ciki.ya shiga gidan ranshi a bace,ya same ni dakin baabah. Cikin fushi yace"wannan kadan kika gani kin xabi son xuciyarki kin bar tafarkin Allah, dole kiga kaico.Sai ma wani ya sake xuwa yace shima dansa ne tunda kin xama bola mai dibar sharar kowa, ba ki san adadin maxan daki ka bi ba a rayuwarki."Namike tare da fashewa da kuka na ce,"sam ni babu wani namiji dana taba bi a rayuwata, ko shima fyade ya min ai shi ya sani."Ya ce to da bakinki kika sanar dani cewa ke karuwa ce kuma a yawonki ne na karuwanci kika yin ciki,ko ba haka kika ce ba? Na ce "Ni fana fadi haka ne saboda kawai saboda ina son ka barni.Ya ce"ke dai kika sani,wanda bai ji maganar iyayen shi ba ai dole ne yayi nadama in ko ba haba ba ni ba da aure na ba xa'a je kotu,sai ki tattara dansu ki basu.Na xube gwiwa biyu a gaban shi tare da rike kafafunshi na ce"Don Allah ka taimake ni,in na bashi yarona ya cuce ni,ya toxarta ni a baya. Abubakar xan yarda in ka rabu dani saboda ya xama ajalina akan in ba da yarona. Ya fita fuu a fusace ,kamar minti 15 ya dawo ya dauki shadad ya fita. Na bi shi da gudu har gurin motar Yaya Umar, nace "Ina xaku dashi?Yaya Umar bai tanka ni ba,sai Abubakar da yace ckn fushi.koma ciki ki jira,duk ranar da kika koyi magana sai ki kira wayata,yaron kuma xan kai shi gurin uban nashi,in yaso kije ki dauko shi.Umar yaja mota suka tafi.Kai tsaye kano suka nufa,gidan Raham suka kai shi,sannan Umar ya dawo ,ni ko ina nan sai kuka nike mutanen suna bani hkr,wasu na cewa,in hkr mana,muna huta lkc da abin ya faru baabah taje gurin Babah a asibiti. Da ta dawo kuma sai ta same ni ckn kuka da tashin hnkl,nace"Umar da Abubakar mijina sun dauki Shadad sun kai ma Munnir. Baabah tace kiyi hkr,ki kuma gode ma Allah,dmn wannan wata mafita ce ya baki. kin san hatsarin ba yanxun bane,sai nan gaba yaro yayi girma sai ya tsare ki ina babanshi,me xa ki ce mashi? Don haka kiyi hkr,wannan ma wanke ki ne Allah yayi.Na nisa."ni kam baabah ba xan fa yarda ba,ni kadai nasan halin da na shiga tun daga lkcn da Munnir yayi min fyade har xuwa yanxun,in na bashi yarona yaci bulus. Ta ce "to me xa kiyi?kina ganin kin fisu tunani ne?kada ki manta mijinki ne fa da wanki."na hada kai da gwiwa ina kuka tace."bana son ki sake yin wani abu da za a ce baki kyauta ba,ko yan'uwanki suyi fushi dake..."Yanxun ya ya xanyi"Na katse ta, ta ce "ki nutsu ki bisu,duk yanda suke so.Na ce, shi kenan" Na kira Innarmu na fada mata komai game da abin dake faruwa,har xuwa abin da Baabah ta ce.Innarmu ta ce."Ki kwantar da hnklinki shawarar da Baabarki ta bada ita ce ya kamata ki bi,sannan ki tuna cewa mahiafinki yana kwance a gadon asibiti kada ki kara masa wata damuwar."Na ce "to shi kenan,na hakura.Da dare kuma guraren 9pm,na kira Rahma ashe lkcn suna tare dasu Abubakar shadad kuwa yayi bacci. Tace, gata ta kira, yace kada ki nuna mata cewa mun xo.Bayan mun gaisa ta ce"Ya jikin baba?na ce da suki sosai.Ta ce "ya ya naji muryarki wat iri? "na ce Um! sai kuka tace lfy?nace Munnir yana son kashe ni da raina.Kinsan yanxun ya kunna min wuta wai in ba shi dan shi? su kuma Umar da Abubakr dina suka dauke shi suk kai shi.Ta ce " To yanxun yaya xa kiyi?na ce "Rahma ba ni da abin yi daya wuce addu'a in xura musu ido.Tace "hakn in kika yi shine abin da yafi dacewa."na ce "Um,wai Abubakar ha da cewa ban iya magana ba.Wai in xauna a gida in na koyi magana in kira shi a waya,wai da gaske ne Rahma don Allah ban iya magana ba?Ta ce "to kila shi ne kika sakr ma magana son ranki "na ce "Rahma xan iya rantse miki cewa ban taba sa'in sa d ashi ba tunda na aure shi. Ta ce. To ki lallaba shi sai ya fada miki maganr da kika fada masa mara dadi.Na sauke ajiyar xuciya."shi kenan na gode.Na koma na kwanta.Bayan na yanke ma kaina hukuncin cewa ba xan kira wayarshi ba har sai lkcn daya neme ni.Sam daren ban runtsa ba,washegari jkn Babah yayi sauki,aka sallamo shi ya dawo.Can kusan karfe 4 aka yi sallama,mun xata masu duba baba ne,ashe wai kara iyayen munnir suka kai kotu.Tirkashi!Sai lkcn baba yaji komai, na kira Yaya Umar na ce "To gashi sun yi kararmu to ta me bayan kun basu dansu?ya Umar ya ce kara kuma?na ce kwarai kuwa,ga magatakardar babban kotu yaxo.Ya ce"Ina xuwa ya kira Abubakar lkcn ya koma Yola,bai ko hutu ba don saukar shi kenan,ya ce to yanxun ranar yaushe ne shiga kotun?Umar yace "Monday"Abubakrya ce . to xan xo jibi da lauyana."Umar ne ya fada wa Innarmu komai,itama tace tana xuwa.Inna wanka najiyo muryar Abubakar suna gaisawa da mutan gida.Sannan ya shiga gurin Babanmu , na tashi na dan kintsa jikina,ya ce ya shigo suka gaisa da Baba sannan ya koma gurin Baaba suna tattauna batun rikicin.N ashigo na xauna gaida shi,ba tare da na dube shi ba,ya amsa sannan ya tambayi jkn baba, na ce yaji sauki.Daga nan yace ,to nazo da lauyana xumu kwana nan tunda ance gobe ne shari'ar ko/na ce eh!ya ce ki shirya yanxun muje yayi miki tambayoyi.Ya dubi baba ya ce,Baba ayi mata fada ta fada mishi gaskiya,dmn da ita ce xa'a yanke miki duk wani hukunci.Baba yace."kwarai kuwa in kin fadi gaskiya to kin hutar da kanki,kin hutar da kowa,Allah ya ba da sa'a.Muka fita xuwa mota,lauyan ba xai wuce sa'anshi ba,baki mai yar'kiba kadan,yana amsa suna Barista murtala.In da suka yi masauki nan muka je, amma gurin shakatawar muka zauna.lauya Murtala yace in fada mishi sunana,na fada mishi.Daga nan ya tambaye ni tarihina,Abubakar na xaune na xayyana ma lauyan komai,tun daga haduwata da Munir har xuwa yau.Lauya Murtala yace "kin tabbata haka ne?Na ce ko ckn bacci ka tashe ni xan maimaita maka wannan don ba xan manta da wannan bakin tarihin nawa bah.Abubakar ya ce?Kada dai ki fada man karya,don ke baki iya magana ba.ya ci gaba da cewa."yaya batun xagawa duniya da kika yi?Na ce,"banje ko ina ba,kuma ban da shi da ya min fydae ban taba hulda da kowane namiji ba.Ya ce "in har hak ne fyade yayi mata barista sai in ga kamr shari'ar xata yi sauki ko?Murtala yace "inshaAllau in an gam matsalar yaron sai tayi karan cewa fyden da ya mata,tana son abi mata hakkinta,tunda nasan dole xai amsa laifinsa.Bayan gama gabatar da shari'ar a ranar litinin din da muka gurfana a gaban kotu lauyoyi suka fito,lauyan shi ne yafi bani mamaki, yanda ya kuke kan cewa a ba shi danshi xai biya duk abin da aka kashe.ni dama koda aka tambaye ni dans ne?na ce dan shi ne,ban bata lokaci ba.Lauyana ya bukaci in ba da labarin dangantakata da munir,mijina ne?na vce a'a saurayina ne ,ya ce to saurayinki ya ya aka yi kuka haihu har ma ki ka hana shi danshi?ya dubi Alkalin ya amince nan na xayyano komai har xuwa yau.Jama'a da dama sun xubar da hawaye don tausayin min aka tamabyi munir shima bai bata lokaci ba ya amsa da cewa tabbas fyade ne yayi min.kuma duk abin da na fada haaka ne,sai dai shi bai san cewa na shiga wani hali ba,sannan ko nawa na kashe wa dan xai biya ni.nan dai lauyoyi suka yi ta kafsawa,daga bisani na ce ina son a bi min hakkina na fyaden da yayi min .nan Alkali ya daga kara xuwa sati biyu masu xuwa,kuma ranar ne za'a yanke hukunci,haka muma Alakli ya bukaci a xo da yaron.Muka fito ,Abubakar sai kallona yake yi tamakr yau ya soma ganina,ya ce Umar ya wuce da su Innarmu saboda shi xai tafi tare da lauyan,don in sake mishi karin bayani.Tunda muka xo daidai dakunan su Barista Murtala ya shige nashi,ya rike hannuna xuwa ckn nashi masaukin.tsakiyar dakin ya tsayar dani ya rike hannuwana tare da kallon fuskata ckn matsanancin tausayi ya ce min."Hafsat me ya hana ki sanar dani ainahin abin da ya faru ki ka sa ni ckn kunci nima ni dinga kuntata miki? Na tsura ma fuskarshi ido."Abubakar a lkcn na furta maka haka ne don kawai ka rabu da ni,sam ban san xa ka zama makusancina ba,lkcn bana bukatar wanda xai kusanto ni da gida,ban san lamura xasu xo da sauki haka ba,ya manna ni a kirjinsa, lokaci guda muka sauke ajiyar zuciya, ya ce ki yafe ni, na nisance kine saboda in ina tuna cewa bansan adadin mazan da kika yi hulda dasu ba, ga kuma kishin ki mai wahalar dani...... Zaharaddeen Shomar whatsapp 08168575100 Sanadin Boko 4-04 Posted by ANaM Dorayi on 05:15 AM, 29-Sep-15 Under: SANADIN BOKO Na soma kukan farin ciki. "Na yafe maka, dama kuma ni ko kusa ban rike ka da komai ba, saboda ba duka namiji ne ne zaiji furucin da nayi ma kaina lakabi da shi ba, sannan ya saurare ni, sai sadauki, jarumi irinka mai taimako don Allah." Na sake kwantar da kaina a kirjinsa, na ce "Nima ka yafe min bata maka ran da nayi." Ya dago fuskata, ya sumbaci goshi na, sannan ya tsurawa kwayar idona nasa idon. "Na yafe maki, sannan ya sake maida ni kirjinsa da wani kalar salon nuna soyayya. Wayar shi ce ta katse ni, sanda muka yi nisa cikin wata duniya muka sake ajiyar zuciya, sannan yasa hannu ya zaro wayar a aljihu. Ni kuma na zauna, zuciyata kuwa farin ciki ne maras misaltuwa. Ya daga wayar, mahaifinshi ne suka yi magana cikin fillanci na tsahon minti goma sannan suka yi sallama. Ya zo ya zauna kusa dani, sannan ya kira Sagir ya bashi labarin yadda shari'a ta kaya, sannan ya ce zama na gaba ya zo da Shadad. Suka yi sallama, ya ce "To mu fa zamu wuce ne, yanzun haka Abba na jira na saboda tafiyar dake gaban mu zuwa Pakistan." Na ce "To ni in zauna a nan?" Ya ce "Kano za ki koma, ki kwantar da hankalinki, In Shaa Allahu za a bi maki hakkinki, domin na kula Alkalin yana da kokarin kamanta gaskiya." Ya ce, "Amma fa ki barshi gurin sagir kada a zo a dauke shi, na ce to" ya soma hada kayan shi ina taya shi har muka gama. Ya rike hannuwana, "Ko in raka ki Kanon ne?" Na ce "A'a, ka ta fi kiran Abba din." Sai da suka kaini gida, ya cika ni da kudi, sannan ya roki Umar da cewa ya kaini gida baya son na shiga motar haya. Su Baba ma yayi masu alkhairi, sannan ya tafi. Abinda yayi wa zuciyata dadi, yanda na samu mutan gida suna tattaunawa akan shari'armu. Wasu sunje kenan ku yau sunji da kunnan su cewa Munir fyade yayi min. Ade ta dube ni, "Hafsat ina maki murna, Allah ya dora ki a kan shi." Na ce "Ai dama gaskiya tana halinta komai daren dadewa. Sannan masu zagina da masu cewa nayo ciki SANADIN BOKO duk na barsu da Allah." Asabe ta ce "Ba a yi haka ba Hafsat, zance na gaskiya ko mu gidan nan ba wanda bai yi da ke ba,

Chapter 19 of 22