Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
bare suyi masa bayanin danayi musu, nace, kinbasu lbr komai game dani ne9 tace, sun bukaci nafada musu, shine kawai yaki sauraro, na jinjina kai nace, toba ance shima bashida lfy ba? tace eh, saidaya bada jini ko sallamarshi ba'ayiba, wani sanyi naji cikin raina, jinin abk yana gauraye da nawa? na sauke ajiyar zucia na kalli rahma, anjima zan kirashi, to waima in nakira nace masa me? rahma tace kirashi yanzun, nacije nace to bari nakira, nalatsa lambarshi ta tafi, nace to rahma mexance masa ne don Allah? wayar tasoma ringing, daidai lokacin yana zaune a babban falonsu, yana tare da wasu daga cikin danginsa sunzo dubashi, aciki harda fadima, ya kalli number dake jikin wayar, tamkar yashare, amma saiya kasa, don lokacin ma itace azuciyasa, ya amsa sallama ta bayan ya daga wayar, na kalli rahma mexance? ( amma da hannu nayi mata alama) ta harareni, ku gaisa mana, ta fada a hankali, nace ina yini, ka isa gda lfy? ba zato naji yaja tsaki, sannan yakashe wayar, na dubi rahma nace, tsaki yaja sannan yakashe, tace duk kece kika jama kanki, yaxa'ayi ki dora ma kanki halin daba nakiba? nace magana zarar bunu, na riga nafada ta fito bamai iya maidata, wasu zafafan hawayen son abk tsantsa suka soma sulalomin, ina sonshi rahma, idan yabarni dakyar in zan moru, bansan hakaba sai bayan dana furta kalmar datajamin tsana a gurinsa, tace kidaina kuka, duk abinda yasamu bawa daga Allah ne, kuma abk yana sonki, na tabbata zai aureki, na sauke ajiyar zucia tare da share hwy, koba gaskebane zancenki nadanji sanyi, kitayani da addu'a, rahma tace, tuni nake tayaki, nace ngd, Allah yabar zumunci, bari inje in dauko shadad in wuce gda, nasan yana jirana, tace to saimunyi waya, na daukoshi sannan na nufi gda, raina cunkushe, kunnuwana basu daina amsa kuwwar tsakin da abk sadiq yaminba, duk da tsananin son danake masa amma baxan juri wulakanciba, ban taba tunanin wata rana zatazo da namiji zaimin hakaba, domin banmayi tunanin cewa zan kalli namiji a matsayin mutum ba, tun bayan abinda munnir yayimin, ina yan aikace aikacena, lkc zuwa lkc inajan tsaki sbd abinda abk sdq din yayimin, dakuma tunanin cewa nidashi mun rabu kenan? Sallamar mamansu Rahma naji nafito daga kitchen ina amsawa turus na tsaya na tsaya ina kallon matar da suke tare, itace ko kuwa dai mafarki ne? bakina ya furta Inna! sai kuma na juya daki da gudu na zauna ragwaf,na kifa kaina cikin cinyata, kuka na saki wanda ya farkar da shadad daga bacci Mama tace ji wani sakarci shigo daga ciki" ta umarci inna,inna ta shigo ta zauna itama ta zauna shadad ya taso yazo ya dafa bayana yana son yayi kuka yana cewa Anty wanene ya dukeki? mama tace kyale wannan antyn taka mai kukan tsiya harsai an doketa? mama ta ci gaba to wannan kukan na menene? inna tace na rashin son gani nane, don haka ma yanzun zan tafi Da sauri na fada kanta ina cewa inna ki yafeni inna ban kyauta miki ba, inna na tuba natuba" inna kawai sai tasa kuka, mama tace haba maman hfsa, yaya kuma zaki taya ta?Da kyar ta lallashe mu. Na kasa hada ido da inna,duk da dadin da naji na ganinta. shadad na zaune a cinyarta, muryata a dusashe nace "yaya umar ne ya kawoki? tace ehh shine amma ya juya sbd suna da bakin da zasuje kd din gobe. Lkcn da muka zo kina mkrnta, shine yace bari ya kaini gdan maman taku" Na sauke a jiyar zucia, ina su kawu?tace kowa lpia. ina nan ina malumfashi kika ki nemanmu shekara da shekaru? Ina cikin bakin cikin kunan rai yanda kika gudu yafi bata min rai abisa cikin da kikayi. abinda ya kona min rai dake kenan Allah yasani hfsa banso kika guje min baNace inna bazan iya hada ido dake bane abnda kike min fada akanshi kullum na kiyaye ban kiyayeba. Amma wlh ba da gangan na aikataba munir fyade yamin ta karfi inna " inna tace umar ya fada min komai,Allah zai fidda ke ta shafa kan shadad Allah yayi maka Albarka ya tsareka da hali irin na munir, shi kuma Allah shine yasan yadda zaiyi da shi, mama tace komai dama mukaddari ne ga bawa Allah ya shige mana gaba. sannan game da yaron nan mai sonta kuyi mata fada,dan mutuncine tayi auranta tare da yin karatunta adakinta. Aure da haihuwa basa hana neman ilmi, yanzun baga rahma ba! da bamu bata goyon bayan taci gaba da karatu ba Amma yanxun da tayi aure mijin yace shifa matarsa fa makrnta zata koma, Nace dama rahma nason karatu gashi ta samu" mama dai ta tafi gda ta barmu. ranar kwana mukayi hira nida inna hirar bayan rabuwa, munyi kuka mun gaji. Da safe muka je makaranta nida shadad muka bar inna,duk wanda ke makarantarmu yau yasan ina cikin farin ciki, shi kuwa Abbkr lkcn dana kira dinnan ya min tsaki, yana kashewa ya mike ya nufi dakinsa ya kira umar suka gaisa. yace, umar don Allah idan iyayenmu sun zo gobe kada ka bar wata baraka da zata nuna cewa yarinyar nan ba a gda take ba" umar yace To insha Allahu ba wata matsala yace sannan ku amshesu da karamci suna son haka" umar yace insha Allahu, haka nan da dare suna tare da hashim yana sake fada masa cewa "Don Allah in sunje kada ya bada wata kofa da Za a gano yarinyar nan ciki tayi" hashim yace Haba nawa, Insha Allahu komai zai zo da sauki, ka kwantar da hnkalinka, babu wanda zai fahimci komai, Tunda yaya umar ya dawo daga kano ya sanar da baba zuwan baki, don haka baba yace ya kira masa Amininsa Malam garba da malam mamman. suna zuwa ya shaida musu komai,suka ce To insha Allah goben bazasuyi nisa ba, sannan sukayi masa murna da dawowar yar'sa HAFsat.Sun shawarta a amshi bakin A shagon gdan malam garba ,don yana da girma,don haka tun ranar yasa ya'yansa su gyara shi,umar kuwa kaji ya siyo da cefane akayi sa'a matarsa murja tana 'yan karance2 ltattafai don haka taiya grki. ya siyo lemuka kaloli aka zuba a ckin frdge.tun safe Babah ta kimtsa baba,yanxun ma yakan dan kokarta wanka da kanshi tun baya n da akaga hafsa ta fito masa da kayan sallar da umaryayi masa lkcn yana cikin ciwo bai sasu ba, yar ciki da malum malum yasaka an shimfida manya manyan tabarmi. umar yakawo chines carpetdinshi aka shimfida. Babah kuwa harda turaren wuta ta zuba a kasko tace akai shagon da za a sauki baki,Tun asubahi Abbkr ya rbuta txt ga baffa sa'adu, bayan gaisuwa ta girmamawa yace"Baffa ina fatan zakuyi hkri da yanda zaku samu gdansu hafsa, ina nufin talakawane.Da fatan wannan ba zai zama matsala ba,ka yafeni innayi rashn kunya" murmushi baffa yayi lkcn da ya karanta sakon,yayi kiran layin Abbkr. ckin grmamawa ya dauka tare da gaishe shi ,Baffa yace "Hamma kada ka samu damuwa, talaka da mai kudi duk dayane a gurn Allah,in talaka yafi mai kudi tsoransa ma to yafi mAi kudi agurinsa, Lura da cewa kudi ba komai bane face jarabta,duk da mafi rnjaye cikin zurarmu masu kudine amma muna da talakawan,so kada kadamu" Abbkr yace, Na gode BaffA Allah yakai ku lpia ya dawo da ku lpia" shi kuma yace ameen, shi yasa yake son baffa sa adu akwai saukin kai ba irinsu Baffa magajiba. Hashim yazosunyi sallama a inda ya sake sanar da shi damuwarsa, bayason suji cewa tayi ciki, ko ta bar gda,Hashim yace kada ka damu" tun da suka tafi yake cike da fargaba,tafiyarmaitsawo ce tsakanin yola zuwa kd. duk da sammakon da suka doka sai kusan mmagrb suka iso, don haka baFfa sa'adu yace da hashim bari ya kira amininsa dake zaune kd don su sauka gurinsa. washe gari sai su shiga gdan da suka zo,Hashim yace to. A nan take baffa ya kira abokinsa, basu samu matsalaba don yace gashi nan zai zo ya taho dasu da kansa. direba ya jawo shi har zuwa by-pass,shi ne ya gano su dai dai inda yace su tsaya. baffa da abokinsa sunyi murna da ganin juna,don sunfi shekara goma basu hadu ba sai dai waya sbd yanayin aikin kowannensu, Tare suka yi karatu a jami'a (ABU) a gdan shi da ke makarfi road ya saukesu a sashin baki, umar ya kira HAshim yace to "to yanzu ya zamuyi da abincinku? ko ka sanar daniunguwar da kuke sai na kawo maku"Hashim yace makarfi road dai naji ance amma bari in tmbyi yaran gda ya fada wa su baffa sai baffa yace.To ba laifi, in ankawo din dama su nan ba su san da zuwanmu ba,Baffa ya sanar da abokinsa sai yace haba dai su barshi yanzunnan za a yo musu take away, Yace a a bari dai su karboan nan take hashim tare da direban gdan suka nufi layinda hashim ya fada masa ashe babu nisa, umar ya fito suka gaisa,sannan ya fito musu da kulolin tare da samiru har da kayan shaye2 marmari masu dan dano, Baffa magaji yace ashe babu nisa da nan?sai da sukayi sallah sannan suka zauna zaman cin abncin. duk da babu wanda ya furta koMai amma kowa ya yaba wannan sauka tare da dadinn grkin, sunci sunyi kat har sun rage. nan gdan ma matar gdan ta gabatar musu da ciye ciye, sun dai dan taba sannan yace hashim yaje gdan dansa munir ya hada shi da direba yace ya kaishi shi can. sannan su baffa su ka zauna zauna zaman hira. inda abokin baffan yace sai kaji rasuwar 'ya'yanka ko? baffa yace suwa? su munir? yace a'a su bashir, banayi maka txt ba? baffa yace subhanallah, wlh ban ji ba,banga kuma txt ba duk tsawon lkcn nan ,baka ga banyi maka ta'aziya ba,tun yaushe ne? yace sun kusa shekara 2 baffa yace Allah ya jikansu hadari ne? yace a'a kasan yaran nan da rashin jin mgna can ne a malesia gurin karatu suka yi ri gima suka harbi junansu,yanzu saidai munir kadai, baffa yace auzubillah Allah ya yafe musu,mukuma ya kyautata tamu. Daddy ya ce Amin, Baffa ya ce, "Shi yasa fa nafi son mu dinga barin yaranmu suna karatu a gabanmu, saboda irin wadannan matsaloli shaye-shaye da harbe-harbe bashi da amfani gurin matasa, ba 'afi mu jami'oi ba, amma sai mu dage mu dinga raina namu, mu daukesu mu fita da su ba maisa muna ido a kansu, mu tura musu kudi, kuruciya tana dibansu, dole ne su ringa sheka ayarsu san ransu." Dady ya ce, "Nima sai yanzu na gane haka, kaga shima Munnir din gurin bin matanshi yanzu haka yana fama da (HIV/AIDS), matan ne kawai na tsira da su." Baffa ya ce, "Allah ya kyauta. Amma ya kamata mu farka, boko tana da kyau matuka, amma mu daina sakin 'ya'yanmu sakaka saboda tana da nata illolin, mu tsaya mu gyara skul dinmu na gida, kuma mu bar 'ya'yanmu su yi karatunsu a nan a gaban mu. Haka zai basu damar ci gaba da karatun addininsu, muna yin wani kuskure." Dady ya ce, "Wane iri?" Baffa ya ce, "Muna fifita boko kan na Islamiyya." Baffa Magaji ya ce, "Sosai kuwa, in ka yi la'akari irin kudin da muke kashe wa karatun boko, Islamiyya bama kashe mata, duk da cewa kudin Islamiyyar baifi kudin takardun Bokon ba, sai muke kyashin biya." Baffa ya ce, "Kuma in munyi kokari sunyi wannan 'yar saukar ta zamani shikenan sun gama, maimakon nan ma mu dafa musu su ci gaba."Dady ya ce, "Um!!! ai nayi kuskure Sa'adu sosai, don kuwa Bokon zalla yarana suka yi, sam ban damu suje Islamiyya ba." "Kash!!!" Inji Baffa Magaji, "Kayi kuskure, Allah fa baya turo mu duniya mu yi boko bane, ya turo mune dan mu bauta masa, to baku nemi ilmin bauta masa din ba bare kusan yadda zaku bauta masa din, don Allah kayi kokari har kai kanka ka shiga Islamiyyar manya." Baffa ya kara da cewa, "Ubangiji ya umurcemu da mu kare kanmu da Iyalanmu daga wata wuta, to Basu san Allah ba, ba ka koyar da su yanda zasu bauta masa ba, kenan kare su daga wannan wutar ba. Wadda aka ce makamashinta mutane ne da duwatsu." Haka dai sukai ta masa fatawa har yace ya gane kuma zai gyara sosai, zan dauki malami harda ita Mominsu ana koya mana. Baffa Magaji ya ce, "Da kuwa ka kyauta."Dady ya ce, "Sa'adu danka ne zai yi auren?" Ya ce, "Eh dan kanina ne, suka hadu da ita a Kano tana Makaranta." Dady ya ce, "Yaushe kuka soma auren waje?" Baffa ya yi dariya ya ce, "Wannan ne karo na farko." Dady ya ce, "Lallai to, shi wannan dan gurinka ne naga kuna kama?" Ya ce, "Hashim dana ne, shi tuni yana da Iyalansa harda 'ya'yanshi." Dady ya ce, "Lallai kaji dadi, nima dana bar wadan can sunyi aure yanda suka nuna min suna son auren, aida tuni ina da jikokina., to me zai hana ga yara nan cikin 'ya'yanka Sa'adu a samu wani ya duba?" Baffa ya ce, "Ai kusan duk wadanda suka isa auren suna da matansu, sai dai nan gaba in Allah yasa da rabo." Zaharaddeen Shomar whatsapp 08168575100 Sanadin Boko 3-04 Posted by ANaM Dorayi on 06:15 AM, 28-Sep-15 Under: SANADIN BOKO Shi kuwa Hashim da suka je gidan Munnir yaron Dady yana kallonshi gabansa ya fadi, domin suna matukar kama da Shadad, a ransa ya ce, "Ko dai wannan ne Munnir din da yaci amanar Hafsa?" Sai yaron Dady ya cewa Munnir Dady ne yace na rako shi nan, wai dan aminin nan nasa ne na Adamawa. Munnir ya ba Hashim hannu suka gaisa, sannan ya ce da direbaa ya tafi, su kuma suka shiga.Matar Munnir wadda ya kira da Baby ta mike ta ce, "Angel bako muka yi ne?" Ya ce, "Eh." Suka hada ido da Hashim ya yi sauri ya kawar da kansa gefe, domin tana sake da gajeren wando da ya dame shape din mazaunanta, da kuma karamar riga da ko cibinta bata sakko ba, ga wani karin gashi buzu-buzu, kumbarta duk farata zako-zako. Hashim dai a ransa ya ce, "In dai wannan ce wayewa to gaskiya bata da wani amfani." MUnnir ya cema Hashim, "Ga matata Hasina." Itama ya ce mata, "Ga Hashim dan abokin Dady na yola." Suka ci gaba da magana cewa daman ku ne Dady yaketa bani labarin Yola yana da amini, amma saduwa tayi wuya? Ya ce, "Wallahi, haka ne daman." Hashim dai a dadare yake saboda sam ko ruwa ya kasa sha, kyankyamin farata da gashin Hasina yake, da ya gaji dai ya ce masa yana so ya huta, shine ya kaishi masauki. Yana shiga ya fada toilet domin watsa ruwa, sai da ya gama sannan ya kunna wayarsa saboda Abubakar, ai kuwa yana kunnawa sakon Abubakar ya fara karo da shi na cewar sun isa lafiya? Kuma ya yi masa bayanin yanda ake ciki.Ai bai gama karanta sakon ba sai ga waya daga Abubakar, ya daga tare da Sallama, Abubakar ya ce, "Iskanci ne ya saka kashe waya ko me?" Hashim ya ce, "Na sani saboda kai na kashe, domin zaka dame ni." Abubakar ya ce, "Ai hankalina ya fara tashi saboda ina tunanin likin da nai ya balle." Hashim ya ce, "Ko daya, domin ko gidan ma bamu je ba." A nan dai ya gaya masa yadda aka yi. Abubakar ya sauke ajiyar zuciya ya ce, "Shi kenan, sai Allah ya kaimu. Pls abokina ka tsare komai." Hashim ya ce, "Kai Malam sa Allah a ranka." Abubakar ya ce, "Da kai na sa a ran? -ya ce- Pls ka dan yimin kokari nasan zaka iya komai." Washegari misalin karfe 10 na safe bayan sun karya, sun kintsa Hashim ya kira Umar cewa suna tafe, nan take ya iso gidan Babansu, Umar ne yayi jagora har shagon da za'a karbe su, sun gaisa cikin mutunta juna inda suka nemawa Abubakar auren Hafsa akan sadaki dubu 10, sannan suka sanar dasu Matan 2 zai aura nan da kwana 23, don haka suka ce ahada Iyayen Hafsa. An yi komai cikin mutunta juna, sai dai suka fito Dady ya ce, "'Yar talakawa haka? Ai da kun sani kun zo gidana kun duba." Baffa Magaji ya ce, "Kai yaron nan da rore- rore yake, dubi Anguwan nan kasan talauci yayi katutu a cikin ta." Baffa Sa'adu ya ce, "Tarbiyyarta ya yaba, sannan na fada muku gwagwarmayar da akai akan auren nan da yakin da Abubakar yayi, don haka kawai ku bar zancen nan. Allah dai ya shige mana gaba." Suka ce Ameen Koda suka dau hanya Hashim yana ta yaba musu halayenta, lokacin da Abubakar ya kira Hashim sun yi nisa a titi, ya ce, "Hashim yaya?" Ya ce, "An gama komai, muna hanya yanzu, an baka auren Hafsa." "Masha Allah." In ji Abubakar, yanzu kam baya da wata matsala. Ni kam zuwan Inna gurina ya dawo min da farin cikina ta wani bangaren, musamman ma dana dawo school na samu har girki tayi mana, sai da nayi kukan dadi, gashi yau ina cin abincin Innata, ashe zan sake cin abincin Inna ta? Kwananta 3 Umar ya zo suka tafi, sannan ya sanar da ita zuwan Iyayen Abubakar.Hafsa ta ce, "Yaya Umar ya fa fasa aurena, me zaya kai Iyayenshi gidanmu?" Umar ya ce, "Kawai abinda zan fada miki shine kibi Iyayenshi, sannan ki amince masa ki rufawa kanki asiri, mutum ne nagari dan mutunci, mafi yawan Mazan yanzu suna yin auren tamore ne, basa bin abinda addini ya ce, ka aureta dan addininta, nasabarta, dukiyarta, kyanta, wannan samun Abubakar sai an tona." Inna ta ce, "Samun miji kamar Abubakar dace ne, dan haka ki nutsu." Suka min nasiha suka tafi, sun barni cikin kewa, nan da nan naji kaunar gidanmu ta isheni, don haka na hada kayana da cewa wani satin zan tafi Kd. Gidan Maman Rahma na kai Shadad, ni kuma na tafi, a hanya gani nake KD tafiyar tamin nisa, ganin nisar hanyar na yi, tunda na zo garin ban kuma bin hanyar ba. Ina sauka tashar Kawo na samu motar anguwarmu, ina shiga layinmu na ga canje-canje daban-daban, na yi Sallama a gidan aka amsa. Wanda suka sanni suka fara fadin, ""Hafsa ce yau a gari?" Sai suka shiga kallon kallo tsakaninsu, wasu suka fara shiga daki kai gulmata na dawo. Baaba ta fito da gudu ta rungumeni, sai naji wasu suna cewa, "Wannan ita ce Hafsan?" Labarin duk ya bazu cewar na zo, ana ta min sannu da zuwa, naga yara kanana da na tafi na bari duk sun girma, abubuwa duk sun canza.Dakin Baaba na shiga muka gaisa, nace mata ina Baba ta ce, "Yana dakin shi, sha ruwa ki je ku gaisa." Na tashi na shiga wajen Baba, ina zuwa naje gare shi ya ce, "Hafsatuna ke ce?" Na ce, "Ni ce Baba, kayi hakuri ka yafe min, nice duk na jawo muku." Ya ce, "Hafsa laifina ne da nayi miki baki, da ace ban miki baki ba da haka bata faru dake ba, maimakon nasa miki albarka akan abinda zaki yi sai na biki da mugun fata, na yi da- na-sani, tunda na koreku bani da kwanciyar hankali, lafiya bata isheni ba, ki yafemin Hafsatuna." Sai kuka shima Baban, itama Hafsa sai kuka, ta ce, "Ka yafe min Baba." Ya ce, "Na yafe miki 'ya ta.Na ce masa, "Baba ya jiki?" Ya ce, "Jiki da sauki, daman akwai ciwon rashinki, amma yanzu gaki kin dawo Alhamdulillah." Na sauna na ci abinci cikin jin dadi da ganin gidanmu, na kira Umar nace masa na sauka lafiya, ya ce to yana nan zuwa gare ni. 'Yan gulma an fara shigowa gana Hafsa wai ta dawo, akwai wata kawar Innarmu sai gata ta zo, "'yar nan ke kuwa mai yayi zafi haka zaki tafi kawai a wayi gari baki nan? Ina kika tafi? Ina cikin da kika tafi da shi? Me kika haifa?" Raina ya baci da tambayoyin ta amma sai na ce mata, "Yana can inda yake yaron." Baba ya ce, "Tabawa ai komai ya wuce tunda ga Hafsa gare ni, kuskure ne aka samu." Ta sake cewa, "To yanzu ina ki ke?" Cikin kosawa na ce, "Kano kuma karatu nake yi." Maza na shiga kiran wayar Rahma don bana son wadannan tambayoyin, na kara wayar a kunnena ina ji tana cewa, "To gun wa kike? Kuma duk tsawon lokacin nan baki yi aure ba?" Na yi mata shiru, Rahma ta daga na ce mata ga Babana, ta ce haba? Na ce, "Kina shakku ne? Gashi ku gaisa." Na mika masa tare da cewa, "Rahma ce wadda nake tunanin ka samu labarinta a gurin Umar." Ya ce, "Kwarai kuwa, mutanen arziki." Suka gaisa, daga nan na tashi na koma dakin Baaba, na bar Tabawa nan zaune tana damun Baba da tambayoyi, anan ne yake fada mata cewar zanyi nan da lokaci kankani, ta fito tana cewa, "Abu yayi dadi, ai gwara tai auren." Ta fito tana maganar, matan gidan suka ce ai gwara auren ina amfanin zaman bariki? Su a zatonsu yawon dandi nake, raina na ce kanku ake ji Lokacin da nazo fita ni da Faty zata rakani gidan Yaya Umar, ina jin Ade tana cewa, "Duk yanda aka yi dan Bariki ne irinta, ko kuma kara da kiyashi za'a yi." Asabe ta ce, "Daukar mara sani kenan." Na wuce ban tanka musu ba. Gaskiya Baaba mutum ce domin bata shaida musu batun aurena da zuwana ba, gidan Yaya Umar na kwana, da safe na zo gida Ummy ta makale min dan itace wadda muka shaku, sauran kuwa basu dokin zuwana, domin an gaya musu nice sanadin tafiyar Innarsu, Ban ga laifinsu ba don kuwa ni ce naja musu, duk zancen da muke da Baaba da Baba tare da Yaya Umar, duk magana ce akan na daure na yiwa Abubakar halacci, na rike shi amana, dan mutum ne mai sona, yayi jihadi a yadda nake ya aureni, har suna cewa samun kamarshi sai an tona. Sai nake tambayar kaina, "To wai saninshi suka yi suke masa haka? Ko kuwa zuwan da yayi ne suka yanke masa wannan hukuncin?" Haka na shirya na koma Kano, inata karatu da zuwa aikina. Wata ranar Juma'a ina zaune gaban computer ina latse- latse na gurin aikina, kawai sai naga Manaja ya miko min doguwar takarda, na ce, "Me ya faru?" Ya ce, "Masu gurin ne suka buka ci a sallame ki." Na ce, "Ni kuwa me nayi za'a sallame ni? Me nai musu?" Ya ce, "Wannan kuma sai ki tambaye su." Na ce, "Shike nan." Na tashi nayi bankwana da su Musa.Gidan Rahma na je da kuka na, dan aikin da nake ji dashi yake rufan asiri an tsigeni akai, dariya ta saka min wai gurin fa na Maman su Abubakar dinki ne. Na ce, "Ai nawane ma Abubakar din?" Ta ce, "Eh mana, jiya ya zo nasan dai kun sasanta." Na ce, "Ni ban ganshi ba."Cikin mamaki ta ce, "Bai zo gurinki ba?" Na ce, "Ban ganshi ba." Ta ce, "Dazun nan yayi sallama damu ya koma." Na ce, "Um, to don Allah a haka zaka auri mutum?" Rahma ta ce, "To har bikinku ya kusa don haka sai ki soma shiri." Na ce, "Rahma abubuwan da suke faruwa a kaina tamkar a mafarki, to yanzun auren dole za'a min ko kuwa? Ban san komai ba akan auren." Rahma ta ce, "Saura sati 2." Na ce, "Um!!! Ni dai zanga ikon Allah." Ina zuwa gida na tarar an canja min kwadon kofata, na yi turus! Na jiya na nufi gidansu Rahma, cikin fara'a Mama ta tareni muka gaisa, ta turo min kwanon danwake tana cewa, "Maza ki ci mutumin naki." Na ce, "Mama ba ta cin danwake nake ba, na zone naga an canjamin makulli." Ta ce, "Yaron nan Abubakar ya kawo, ya gaya min ai kunyi sallama ko?" Na dubeta ina so na fahimci Abubakar ya zo ne? Ta ce, "eh, harma ya bani dubu 2 kyayi masa godiya ma." Na ce, "To, amma nifa ban ganshi da idona ba." Mama ta ce, "Ya hausar baki ganshi ba? Ya ce min kun zanta yanda bikin zai kasance saboda lokaci ya kure." Na ce, "To bansan an yi ba." Mama ta hauni da fada, wai in dai nutsu ina sone in kishi. Na dai ce a bani Makulli, ta bani na nufi gida na bude kofar, buhun shinkafa ne karami sai sabulun wanka da na wanki, sai kayan tea da kudi dubu 5 na gani, sai takarda akan kayan, ga abinda takardar take cewa, "Na san cewa kin san komai game da auranmu dake gabatowa, wadannan kayan abincinki ne, na san zasu isheki kafin bikin, sannan na haramta miki zuwa gurin aiki, Makaranta kawai na aminta ki je."Duk son da nake yiwa Abubakar sai da naji haushi ya kamani, wace irin kaddara ce wannan? Wane irin iko ne Abubakar yake min? A haka zan je gidansa yana min wulakanci? Ni fa Allah ya sani ba zan dauki wulakanci ba. Ni kadai na dinga Jaraba ina mita, daga bisani na yanke shawarar kiransa a waya, sau 2 tana yi tana katsewa yaki dauka, na kara cika dan takaici, na zauna na rubuta masa text, "Ka sani fa bana son ka, sannan ba zanyi auren wulakanci ba, don kawai kana sona saika dinga nuna min iko? Don kasa an sallameni a gurin aiki ko kana takama naku ne? To zan nemi wani, kuma ban ce ina neman taimakoba har da zaka kawo min abinci tare da karfin halin canzamin kwadon kofa." Ina kammalawa na tura masa sakon text din, zuciyata cike da fushi da takaici.yana jin shigowar sakon amma bai duba ba, domin yana zaune gaban Dadarsu, yana so yayi mata batun dake tare da shi, ta ce, "Ina jinka." Ya ce, "Daman Dada ina so nayi magana ne akan kayan lefen da za'a kai, inaso idan naje Dubai na karo wasu." Dada sai ta saki baki kawai tana kallonshi, lallai Abubakar ya zo da sabon salo, sai ta ja tsaki ta ce, "Kai yanzu yaron nan har kayi girma da kudin da zaka zo kace zaka hada kayan aure? Ka manta kenan duk abinda Lamido yake yi kai bai ma be kenan? Sanin kanka ne duk wanda zai yi aure a cikin zuri'armu Lamido ne yake mishi komai, shine ni zaka zo kace wai zaka yi wani kaya, to shike nan kaje kayi amma ba da yawuna ba, kai baka da tunani ne? Wace irin yarinya kake nema da kake rawar kafa a kanta haka? Ni dai ba zaka jawon magana ba, ka tashi ka bani wuri."yal tashi jiki a sanyaye, tare da cewa, "Ki yi hakuri." Ya ce, "Kuma duk abinda kuka yi daidai ne." "Sai ka zuba ido kaga abinda Lamido zai yi, shike nan jeka." Yana

Chapter 15 of 22