Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
hakuri kwana nawane zan gama? Baba yace nifa ba kin karatun nake ba, nafiso tayishi a can dakinta inaso kisani har in yarinya ta soma tsayawa da saurayi mafi kyawu shine ayi mata aure. Inna tace za ayimata malam, wannan yaro da ka ganta dashi shene yake son auranta na lura itama tana sonshi yace to ba sai ya turo magabatan shi ba muyi zancen manya! Inna tace yo shima ai karatun yake sai ya gama itama ta gama kafin nan. Shuru yayi bai sake tankawa ba shurun ba yana nufin ya yarda bane, shurunsa yana nufin mukarata can shi ba ruwansa. Kwana 2 tsakani muka shirya ni da inna muka nufi manunfashi kananta kawu sha‘iabu da kawu bashir harda wanta kawu kabiru sun sunji dadi sun kuma tsaya har saida nasamu shiga ss1. Haka baba ya hakura ya zuba muna ido, na cigaba da karatu cikin nasara da kwazo, yan gidanmu kam da makota sai gulma da tsegumi, ba mu damu ba. Fatan inna shine inzama abin kwatance nan gaba. A duk lokacin da nazo hutu munnir nazuwa, haka duk lokacin ziyarar dalibai in yana da sarari yakan zo. Hidimar karatuna shi yake yinta haka nan duk wani kaya na yan mata shi ne yake siyan min, wanan shine yasa na kara sake wa dashi. Matsalata dashi son taba jiki na, kawai lokacin da wani hawaye yayi min wai in bishi muje dakin wani abokin shi, niko nace a a muji tsoron Allah ba don son da nake yiwa munnir ba a tuni na hakura dashi. Cikin haka na gama karatuna na secondary. Na dubi likitar idanuna suna zubar da hawaye nace, anty ko lokacin da na gama karatu na baba ko gai suwa nayi baya amsawa, kannena yaran kishiyar mama na guda 2 ya musu aure. Sannan karatuna kafin na tahoshi sai da ta kai yace in har wani abu ya biyo baya abakin auran innata, sannan in nemi uba..... Kuka ya kwace min mai karfi, ina fadin na shiga ukuna zan kashe auran iyaye da kaina. Munir ya cuceni fyade yayi min anty ki taimaka ki cere cikin nan. Yan gidanmu da yan unguwarmu duk dariya zasuyi mana. Kalo kawai likitar keyi cikin tausayi har nayi kukana mai isata na gama ba wanda ya bani hakuri. Daga ita har asabe tace to, ke hafsat ki koma makaranta gobe kizo, keko asabe ki kwana nan nace anty don Allah nima zan kwana nan din, ko naje makarantar ba zan iya komai ba, tace shikenan. Ta mike sannan ta nuna mana wani daki, ku shiga nan kuyi sallah da komai a ciki. Ba tare da ta jira amsa ba ta nufi dakin ta, kaiwa da kawowa kurum take yi. Ta ina zata bullowa wayanan yara? Sam bazata cire cikin ba, bazata kuma bari suje su cire su zubar ba. Ta lura Asabe tafi saukin kai don haka da ita zata fara. Yanda naga rana haka na ga dare, alwaula kawai nayi na yi nafila. Daga bisani na koma istigifari, washegari bayan ta lalabemu mun karya, sai ta bamu wasu magun guna tace kada in damu in koma makaranta insha, suna da karfi na sati 3 ne, ta tabata cikin zai fita nayita godiya na komo. Sai da daktar hindu ta sami shugabar kungiyar kare hakkin bil adama. Tayi mata bayanin komai game da halin da asabe ke ciki, Shugabar Hjy Adama ta ce, to za su samu Hjyr Yasir su fara neman sulhu, in ta ki kuma to za a maka Yasir a kotu. Doctor Hindu taji dadin haka, don haka ta tambayi Asabe yaushe aka fi samun Hjy Mairo a gida? Asabe ta ce Lahadi da rana, sauran ranakun sai dare ake samunta. Sun same ta cikin Kasaitaccen falonta tana shan kayan Marmari, suka sanar da ita dalilin zuwansu. Ta ce, sam ita dai ba danta ba, ai ta ja mata kunne, nan suka nuna mata cewa zata amsa kira a kotu gobe Litinin. Yasir na dawowa ta hau shi da fada, ya ce tayi hakuri sharrin shaidan ne, ta daka mishi tsawa ta ce, yi min shiru,wawa kawai. Ta tausasa murya a bin da nake so da kai, za su shigar da mu kara, saura in mun je ka saki baki ka nuna kai ne, ina so ka bata rai ka hade fuska ka nuna sam ba ka sam ba ka san zancen ba. Ni kuma zan tsaya maka, Babanka zai tsaya maka, domin duk Alkalin garin nan ba wanda zai ketare bukata mahaifinka. Yasir cikin murna ya ce, "To Hjyta. A daran ranar ta kira mahaifin Yasir ta shaida mishi abn da ya faru, wai me aikinta tayo ciki tazo ta ce Yasir ne, yanzun haka kungiyar kare hakkin dan adam ta shigo cikin lamarin sun ce za su shigar da kara,Ni kuma na ce su shigar, ya ce amma ba ki da hankali, kina fa da masaniyar ina da burin tsayawa takara a siyasa mai zuwa, ko kin manta? Kin san cewa abokan gaba za su iya fakewa da wannan su ci zarafina har suyi nasarar kada ni? Ta ce to yanzun yaya za'ayi? Ya ce bani Yasir din a waya, ko ba ya kusa? ta ce ba ya kusa, ka kira layinsa. Yasir ya daga kiran wayar Mahaifinsa, ko gaisawa ba su yi ba ya jeho masa tambaya, gaya min gaskiya kai ne kayi cikin? Yayi shiru, fada min na ce kai ne ka min shiru? Uban ya fada cikin daga murya. Yasir ya ce "Dad ba zan kara ba, Mahaifina ya ce, Ok kai ne kenan? Ya ce Tsautsayi ne. Alhjn yayi shiru yana nazarin abn yi. Can yaja tsaki, in ka kuma ranka zai 6aci fiye da zatonka. Abn da zan maka sha mmki, kila ma kayi zaton ko ba ni ne na haife ka ba. Ya ci gaba da fada. In ma ba iskanci ba duk nawa ka ke 25 years amma ka iya jarabar mata? Yasir ya dinga ba wa Mahaifin shi hakuri, Alhjn ya ce shi kenan, ya kira Hjy Mairo ya ce, kada su shiga kotu, su nemi sulhu duk yanda aka yi su fada mishi. Washegari da kanta taje ofishin shugabar kungiyar don neman sulhu. An kira Dakta Hindu sun zo tare da Asabe, sharadin 2 suka gindaya wa Hjy Mairo, aka c ta za6i daya.Na farko ko dai dan nata ya auri yarinyar bayan ta haihu, na 2 kuma in ba zai aure ta ba, to zai dauki nauyin cikin tun daga yanzu hr zuwa lkcn da za a haife shi a yaye shi. Daga bisani su dauke shi. Hjy Mairo ta nemi saukin Asabe ta rike danta za su ci gaba da mishi komai,amma shugaba ta ce a'a ba za su yarda ba, domin Asabe in ta samu miji aure zata yi. Ba zai yiwu ta tafi da dan wani gidn wani ba. Nan ta take ta kira mijinta ta mishi bayanin komai, ya ce su dauki za6i na biyun in yaso zasu yi shawara in ya dawo. Ta ce to. Nan dai aka yi dogayen rubuce-rubuce, kowa yasa hannu Daga nan ta tafi........ Zaharaddeen SHOMAR WHAT'S APP 08168575100 SANADIN BOKO 1-5 Posted by ANaM Dorayi on 11:57 AM, 12-Sep-15 Under: SANADIN BOKO Nan dai aka yi dogayen rubuce-rubuce, kowa yasa hannu Daga nan ta tafi. Likita ta dubi shugaba ta ce, " Amma ko da Asaben zata ba su dan su sai an sake zama, don kada suje su halaka shi, kin san mutane ba imani. Shugaba ta ce, wannan ka'ida ne, yanzun ki dauki yarinyar nan ki koma da ita gidanku,gobe zamu je mu samu iyayenta. "Doctor ta ce, Insha Allahu." Washigare suka nufi kauyen kurje, iyayen Asabe sunyi murna da zuwanta, amma da suka ji dalilin zuwan nan suka soma kuka tare da yiwa Asabe Allah ya isa. Asabe na ta kuka, Doctor suka yi ta bai wa iyayen baki tana rokon su yafe ma Asabe. Da kyar suka shawo kan su, sannan suka yi musu bayanin komai game da yanda suka yi da Yasir. Mamanta ta ce, to ni dai ba za ta zauna min a nan va, kauyen nan suyi ta zagina suna yada ni 'yata tayo ciki. Ta sake rushewa da kuka, Likita Hinda ta ce zan tafi da ita in zauna da ita hr ta haihu, in ta yaye sun dauki dansu sai ta samu miji tayi aurenta, ko a nan ne. Maman Asabe tana ta gdy, shi ko Babn tunda yayi waje hr suka tafi bai dawo ba, suka dauko hanya bayan sun ba uwar Asabe sha tara ta arziki. ***** ***** ***** Sati 3 daidai babu alamun cewa cikin jikina zai zube,duk da cewa kusan kullum sai na je gun Likitar, ita kuma sai tayi ta kwantar min da hnkl, wai in jira sati 3n su cika,don ba za ta iya bani wani magani ba tunda aikin wannan bai kare ba. Sam lkcn bn san yaya Asabe take ciki ba, don nima ina cikin nawa tashin hankalin, gara ma Asabe. Bana iya cin abnci,yunwar ma ba jin ta nake ba,karatu kuma ina mantawa cewar shi na zo yi, don ko na shiga aji ba na fahimtar komai, ga laulayi mai tsanani. Munir kuma bai kuma zuwa ba,wayar ma sau 2 ya kira ni, cikin sati 3 da likita ta bani yau kam ko sisin mashin bani da shi, a kafa na sabi hanyar zuwa gidan Doctor. Asabe tare da me yiwa Likita aiki wata gyatuma ana kiranta Yalwa, su na samu. Asabe ta ce min Likita tana cikin asibiti zama nayi don jiranta. Sai uku da rabi muna sallar La'asar ta shigo, da fara'ar ta tare ni tana cewa? na dai san bukata ta biya tunda ban gan ki ofishina ba. Kamar ko yaushe,sai hawaye suka soma zuraro min, na ce wlh Likita ya ki fita, ni dai a kwakule min shi. Ganin tashin hankalin da na shiga, sai ta lallashe ni da cewa, nayi hakuri bari ta dan huta. Na koma na zauna ina kuka,wanda ya zama abn yina koda yaushe, tun da Asabe ta bani lbrn yanda aka kwashe da tata rigima hankalina ya kara tashi. Addu'ata Allah yasa nima kada Likitar ta ce haka za a yi, domin zancen cikin ne sam bana kaunar Innarmu taji bare Babana. Sai shida saura ta fito, na dora sabon kuka Nan ta hau ni da fada,wai in tashi ni tafi kukana ya min magani. Na share hawayena, tare da bata hakuri,ta ce "Hafsatu! Ina son ki bani aron hankalinki, ki saurare ni, na ce to. Ta ci gaba da magana. Cikin nan naki ba zaya fita ba, domin na baki duk wani magani mai karfi,amma a banza. In ko ki ka ce a kwakule shi akwai yiwuwar ki rasa ranki. Da sauri na ce gwara na mutu zan fi son akai gawata ga iyayena fiye a kai ni gaban su da ciki. Ta ce, To naji amma kin shirya abn da za ki fada wa Mahalccinki? Kin mutu gurin kisan kai ko in ce ma kin kashe kanki? Kin fi son kunyar lahira fiye da ta duniya? kada ki manta, kin ce fyade ya miki ko? Na daga kai cikin kuka, ta ce to ki dauki wannan abn a matsayin kaddara. Kada ki manta, Ubangiji ya kan jarabci bayinsa don ya gwada Imaninsu, ke me zai hana ki rungumi kaddara? Allah ba ya dora ma wata rai abn da ba zata iya ba, Zufa ta rufe ni, na ce Likita ba za ki gane ba ne.Innata da Babana auran zai mutu SANADIN BOKONA. Alhakin Babana ne kash! Hakika da na san haka zata faru gare ni da na yarda Babana ya aurar dani, in yaso sai in ci gaba da karatun acan gidan mijina. Likita ta ce, Yanzun dai shawar da zan baki ita ce, kije ki samu shi saurayin ki tunda yana sonki, ku sulhunta, in kin haihu a daura muku aure. In kuma kina son sako hukuma kamar na Asabe to in sako, za su tsaya miki a kwatar miki 'yanci. In ta kama hr kotu kuma ko su waye iyayenshi. Na ce A'a zan fi son in same shi muyi magana don bana son asirina ya tonu a unguwarmu. Likita ta ce, yauwa, in kun sasanta ni kuma zan fahimtar da iyayenki, na rike kai, Boko! Boko!! Na jajirce sai nayi boko,yanzun kuma gashi tun ban je ko ina ba bokon na tsane ta. Likita ta ce, "Hafsaty duk wanda ya dauki boko sama da aure a karshe sai yayi nadama, saboda halin da ki ka shiga ina son ki kwana a gidannan anjima zan baku lbrna, don ki san kinyi kuskure kema." Tara na dare da 'yan mintina Likitar ta shigo sanye da kayan bacci masu kauri riga da wando, tire ne a hannunta dan karami mai dauke da kayan marmari, lemo da ayaba da abarba. Ina zaune zugum kan sallaya Asabe na kwance a tsakar daki ta dubi Asaben "Tashi! "Tashi!! Tun yanzy kin soma bin sanyin kasa? kada na kuma ganinki.Asabe ta tashi, Likitar ta ce In bacci ne ki hau gado mana. Ta zauna bakin gado ta turo mana plate din kayan marmarin bayan ta dauki abarba guda daya dama ina jin bakina babu dadi sai shiga bayi nake ina zubar da miyau Na dauki lemu guda daya ina dan lasa, Asabe ma ta dauka. Likitar ta dube ni Tun ranar da naji lbrnki naji ina son in fada miki nawa. lbrn. Amma kafin na fada miki ina son ki sanar da ni daga ranar da ki ka fara ganina zuwa yau me ya birge ki a tare da ni? Na gyara zama, Na farko iliminki,sai kyan halinki,ga shi kina da kyau,ke ba kya tare da matsala kina da kudi. Tayi guntun murmushi,sannanta dubi Asabe ta ce, Asabe ban yi kama da mai matsala ba ko? Asabe tayi murmushi. Anty ai ke ba ki hada hanya da damuwa ba, bare matsala. ke kam kin ji dadinki. Likita tayi shiru na dan lkc sannan ta ce. "Sunana Hindu, mahaifiyata Bafullatana ce, mahaifina yana da kudi sosai,don lkcn da aka haife ni ma yana matsayin Sakataren Gwamnati. Mun taso cikin daula da gata, haka nan muna da kyau 'yan gidanmu tamkar mu ne muka hallice kanmu. Yayyena 2 maza,sai kuma kannena guda 5. Mu 8 ne gurin mahaifinmu, amma a gurin Mamanmu mu 5 ne, Kishiyar ta ke da 3. Tun da na taso nake da tsananin son BOKO burina kullum in zama Likita,wannan yasa mahaifina ke matukar sona,don shima dan bokon rikau ne. Shi irin matanan nan ne wadanda za su iya hana cikinsu su ba ma boko,takarda komai tsadarta in dai ta boko ce zai siya. Wannan tasa nake zaton dama an halicce ni don nayi Boko. Lokacin da na gama secondary ina da shekara 18, kyawuna ya kara fitowa Nan fa samari suka min ca 'ya'yan manyan mutane,masu kudi da sarakuna.Ni kam lkcn wani faifai na bude na walakanta samari, don in fito in zage saurayi ko dan wanenr baya damuwata.Bana manta wani saurayi Nasir,Babanshi shi ne Gwamnan jiharmu wancan lkcn tamkar zai yi hauka don sona, kullum sai ya zo gidanmu ya min kuka,amma na ce ni fa sai na zama Doctor. Babana ya daure min gindi, ina ta tsulawa samari tsiya. Yayuna maza sukan suna son aure,mma Babanmu ya ce suma ba yanzu ba. Amma shi a wannan lkcn ya sake dallo wata amaryar wadda bata wuce sa'a ta ba.Sam ban damu ba, Su Hjy kam ransu ya 6aci,haka yayuna. Babban sai ya shiga dibn mata yana kawo su wai don Babanmu ya gani ko zaya mishi aure,amma sai Baba ya kira shi yana zagin shi. Abn da in na tuna yake bani mmk lkcn Baba hr d cewa in zya nemi matan shi yaje can ya nema,amma ya daina kawo masa gida. Na ce Alhj fada zaka masa ya daina,ya ce kyale shi Hindu, yaje yayi ta yi,wata rana kan shi zaya bari. Ni dai har na tafi Jami'ar Ahamadu Bello,ba suyi auran ba.Karatu gurina ba sauki,sam bana wasa da BOKO. Shekarata 3 a Jami'a sannan aka yi wa yayuna aure, shima da kyar suna ta hada Babanmu da mutanen da yake jin kunya. Kwanci tashi na kammala karatuna,tsawonshekara 7. Lokacin ina da shekara 25. Saboda kwazona, na samu damar zuwa wani kwas kasar Germany na tsawon shekara 2. Hjyta hr d kuka,don bata son tafiyar burinta in yi aure,amma na kekasa kasa na ce ko na gama karatu sai na fara aiki. Haka kuwa, ina gamawa ban jimaba na soma aiki a babban asibitinmu a matsayin babbar Likita. A lokacin Shekarata 30 babu kadan,sai a wannan lkcn ne hankalina ya dawo jikina. Nayi boko na zama Likita,yau gani inna aiki. Nan fa maza suka sake min ca! amma duk wanda na ta6a babu na aure,sai dai in zan yarda a lalace,daga wanda zai ce in zo in raka shi Abuja,sai me cewa in zo in raka shi Dubai. Da na nuna ba haka nake ba, sai na dinga nemansu daya-bayan-dayaina rasawa,daga karshe duk suka gudu. Lokacin ne kuma idona ya raina fata,wasu suka dan soma zuwa amma fa ba yaro,don ko wani ma zaya girmi Babana, na ce tab, ni kan ai saurayi sabon jini. Kafin shekara na nemi suma tsofaffin na rasa.Bana manta wani dattijo da ya soni na ki, sai gashi ya kawo min wata 'yar yarinya ba za ta fi sha takwas ba, ba ta da lfy tana laulayin ciki. Ya ce min, Matarsa ce. Sai na soma tunanin cewa in nemo samarina na da mana,duk wanda na bncika sai in samu lbrn cewa yayi aure. Hankalina ya tashi matuka, yanzun gurin mu2m daya nake sa rai,wato Nasir wanda ya soni tamkar ransa, duk in da zan samu lbrn Nasir naje amma bn samu lbrnshi ba. Wata safiyar Asabar, misalin karfe goma na safe,na nufi supre markte don siyan kayan shafa, domin nawa sun kare. Ina sa kafa daya kan na dago dayar,wata 'yar kyakkyawan yarinya 'yar kimanin shekara sha biyo ko sha daya ta rugo da gudu daga ciki sai ko ta rungume kafata tana cewa . Anty 6oye ni Fadil za ya kwace min (Teddy)na. Na daga ta sama,daidai lokacn da yaron ya iso, daga gani kaninta ne yana da kiba. Ya ce, Anty nima ki ce ta bani boll dina. Na dube ta, ina boll dinsa? Tana dry ta ce, Anty boll dinsa fa tana mota. Na ce to dauko masa, zan sauke ta ta sake kankame ni. Anty Fadil yana da karfi zaya ture ni ya kwace (Teddy) na. Dry na ke t musu, ga shi sai naga sun shiga raina, na ce to muje in sai maka wata boll a ciki. Muna isa daidai gurin kwallaye na ce za6i wadda ka ke so, yarinyar ta ce Anty nima zan kara (Teddy) daya. Muryar Babnsu naji ya ce, sannu da kokari sun dame ki ko? Ina daga ido na sauke kan Nasir, da sauri na ce Nasir! Da alama sai lkcn ya gane ni, ya ce a'a Hjy Hindu BOKO uwaka ubanka ya karatu? Sai naji tankar ya min habaici ne, na ce Alhmdulillah, mun gama hr na soma aiki,ya ce lallai kam buri ya cika, na ce yaranka ne wadandan? Ya ce, eh Fadil da Fadila,sai kanwarsu Yasmeen. Na karkata kai tare da cewa, Allah ya raya su. Ya ce Amin. Na ce, yanzun kana ina ne? yace muna Abuja ne mun zo hutu ne, ke fa? kafin nayi magana wata mata kyakkyawa ina ga zan girmeta ta iso tana sanye da after dress me shegen kyau. Ta ce Beby ka gan su? Ya ce ga su nan sweet heart, ta dube ni ta yatsina baki tare da cewa, wannab fa? Ga mmkina sai na ji ya ce,Ina tsohuwar budurwata Hindu,? To ita ce wannan. Nan take ta watso min wani mummunan kallo, sannan ta figi yaranta gami da cewa, mijin mace daya zo muje. Yayi murmushi tare da daga min yatsu 2 gami da cewa bye. Ban iya tsayawa siyan komai ba na fita. A gida ma ina shiga kai tsaye dakina na nufa,na fada kan gadona ina kuka. Tambayar kaina nake, wai dama gaske ne da Bature ya ce dama sau daya take zuwa ma mu2m a rayuwa? In ko haka ne na cuci kaina na bar damata ta wuce. A ranar ne na soma tsanar BOKO akida, tun daga nan na koma ga Allah, ko yaushe nayi sallah addu'ata ita ce Allah ya ban miji. Kawayena, sa'annina duk sunyi aure da yaransu,kuma bn tsere musu a karatu ba,tunda aina aiki suma suna aiki. Amma sun tsere min don suna da aure ga kuma 'ya'yansu. Doctor Hindu ta dube ni, Hafsatu kin ganni nan da kama aikina yau shekara goma sha biyu kenan,amma babu miji. Har Malamai na shiga don kawai in samu miji. Daga wanda zai ce Aljani ya aure ni, sai wanda zai ce asiri aka mini,suka yi ta cin kudina suna min karya, daga karshe naga babu wani ci gaba na watsar da su. Yanzu na rumgumi kaddarar da nawa kaina, mahaifina ya rasu shekaru hudu da suka wuce abin da yasa nabar gida katsina na dawo nayi asibitin kaina shine, kannena yaran amaryar babanmu duk sun raina ni gashi ba mu cika shiri da hajiyata ba. Shiyasa da aka raba muna gado na yo nan na gina asibiti da gidana, sai dai ina zuwa gida kan lokaci in duba su hajiya ta. Share hawayenta nima sharar kwalla na ke tayi, dan murmushi me kika fahimta ko nace wane darasi kika samu cikin labari na? Nace na farko ba kyau wulakanci, sannan mu daina sanya boko ya zama gaba da aure kamar yanda nima nayi. Tace hafsatu naki mai saukine dan ke kin kama saurayi shi ne dai wanda kika kaman ya cuce ki. Amma ni abinda nayi saboda boko! Ta jin jina kai sanna tace ko rabi ban fada maki ba kuma halin da nake ciki yanzun nima na kirashi SANADIN BOKI, nace auty haryanzu baki wuce aure ba. Tace to in ban wuce ba hafsat ina mijin? Kwata kwata na daina burge maza, sam ba sa jin sha‘awa ta sai yan yara wanda da nayi aure kan ka ida na rantse miki hafsa da yanzu inada kamarki koma wanda yafiki don haka sha warata dake ki daure ki haifa dan cikinki baki saniba ko shi kenan kwanki a duniya. Sannan kiyi aure tun da kuruciya, aure ba zai hanaki boko ba kamar yanda mahaifinki yace. Magana daya zan fada maki, kada ki sake yarda saurayi ya taimaka miki game da komai na kudi, zai iya anfani da hakan ya cutar da ke, duk da nasan akwai masuyi don Allah. Asabe da ke gefe cikin tagumi sai yanzu ta tsoma baki, anty wallahi ban taba zaton kina da matsala ba, duk kalon da nake maki mijinki da yaranki suna kasar waje. Maganarta sai ta dan bamu dariya. Har likitar ta barmu ta koma dakin ta ban daina mamakin lbr ta ba, duk kyanta duk kudinsu duk bokonta ta kasa samun miji lalle kuwa boko yaja mata. Wata zuciyar ta ce min ba boko bane wulakancinta ne ya jamata, koma mene yanzu na fiskanci aure yana sama da komai. Washe gari gida na shirya wucewa kaduna, sai dai kudin mota bani dashi amma ba zan iya fada mata ba. Dan haka nayi shuru dari biyar ta bani wai nasha ruwa a hanya. Makaranta na koma na canja kaya na dauki kwalin wayata na nufi kasuwar masu waya ni dai ban tsaya ciniki ba, dan ba a cikin nutsuwa nake ba, yace dubu 6 inji mai siyan wayanr, bani kudin kawai nace don na kosa insami munir inji yadda zamuyi. Kai tsaye gidansu na dosa ko unguwarmu ban sauka ba, koda mai gadinsu yace min sun fita da maman shi sai nasami can gefen gidan na zauna. Ko shekara zasuyi sun dawo su same ni, na fada cikin raina. Kusan awa 3 sanan motarsu ta dawo tayi hon, mai gadinsu ya bude ban bata lokaci ba na mike na rufa musu baya. Daga inda nake tsaye ina hango kannanshi mata suna sanye da gajerun wanduna, kai ba dan kwali suna ta shiga da kaya. Dayarce ta hangoni sai naji tace mom ga wata can ko mai aiki ce? Matar ta waiwayo, kamanninta sak da munir haka ma kannanshi. Ta nufoni lafiya? Warin munir yayana ya aikoni, tace wai me? Nace abokinsa ne zan amsar masa sako ne, sunyi magana da munir din. Tace ok ta nufi ciki tana kwala mashi kira. Yafito daga cikin gida yana cewa yes mom.... ganina yasa shi yin wani turus! Tace gawata can wai yayanta ya aiko ta." Da sauri ya ce, "Oh na gane sako zan bata." Ya iso gurina fuska daure, "Lafiya Hafsatu kika biyo ni gidanmu?" Na ce, "To ciki fa bai fita ba." Da sauri ya dora yatsanshi a lebe tare da cewa, shishsh. Ya nufi gefensu gami da cew Zo. Muna shiga ya ce, "Kina nufin cikin bai fita ba?" Na ce, "Wallahi." Ya ce, "To ki koma gida zan zo anjima da dare in kaiki wani asibitin a fitar da shi, wannan bata san aikinta ba." Na ce, "A gaskiya ba zanje a kasheni ba, don Likitar tayi duk wani kokari don ganin ya fita amma abin ya ci tura. Ta kuma fada min in na matsa cewa sai an cire to zan iya rasa raina. In je in cema Ubangiji na me?" Ya ja tsaki, "To me kike nufi?" Na ce, "Shine na zo mu san abin yi." Ya ce, "To me kike ganin za'a yi?" Sanyi na ji cikin raina, Allah ya sa ya yarda na ce, "Ina ga mu hakura in zauna can gidan Likitar, ko Inna ba zan fadawa ba in na haihu sai muyi aure." Ga mamakina sai na ga yana dariya, a zato na zancen ya masa dadi, kuma shawara ta ta shige shi. Amma sai naji ya katse tunani na da cewa, "Amma ban taba sanin baki da hankali ba sai yau. Kina zaton ko aure na yi yanzun nan da shekara goma zan haihu?" Ya girgiza kai, "Ba zan haihu ba, saboda haka dole ne a cire wannan cikin, in kuma kin dage to kije can ki nemi Uban danki." Da sauri na dube shi, "Munnir ka san me kake fada?" Ya ce, "Eh, ina da ja kan wannan cikin, cewa nawa ne. Daga sau 1 shima ba cikin kwanciyar hankali ba amma shine ciki zai shiga?" Bakin ciki ya hana ni magana, idanu kawai na tsura mishi, shima ni yake kallo cikin harara gami

Chapter 4 of 22