Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
shi kuma ya zauna saitinta, ta ce In zuba mana? na ce Ban san cikinku ba, yaja plate ya zuna musu. Ya ce ke kuma zuba naki, Ya kalle ta ya daga mata gira tare da kashe mata ido daya. Ta kai masa dan duka cikin wasa, ya cafe ke hannun ta ya sumbaci tsakiyar hannun. Tayi wata 'yar kara na dauke kaina ga barin kallonsu wayata ta soma ringing a cikin pos dina. Na mike na nufi kujear da na taso don nan ma na bar pos din. Ya dube ni Ina za ki? Na ce Amsa waya zan yi. Na dauka, yaya Umar ne. Nayi kasa da murya muna gaisawa ya ce Dama Inna ce za kuyi sallama, suna gidana yanzun zan je in sha mai in maida su." Na ce To yaya Umar. Ya ba Inna muka gaisa. Na ce Ashe tafiya zaku yi?" ta ce," Eh, mun shirya ma yanzun zamu tafi. Dama ina so ne in sake yi miki nasiha Hafsatu!!kiyi zamanki a dakinki, kiyi ta hkr don Allah na roke ki duk rintsi ko yaji bn amince kiyi ba. Ki rufa ma kanki asiri, kin dai ga gatan da Ubangiji ya miki, ya baki miji dan mutunci, ki rufa min asirin nan da Allah. Na fashe da kuka, na ma manta ko a ina nake, take lkcn baya ya fado min lkcn d Innarmu ke rokona cewa in lura da kaina in tsare mutuncina,amma bn yi hakan ba. koda dai ba son raina ba ne, na ce Inna in sha Allahu mutuwa ce kadai zata raba ni da gidan Abubakar. Na miki alkawarin duk rintsi ba zan ta6a yin yaji ba. A hankali nake maganar cikin Kuka. Abubakar ya tsura mata ido daga in da yake yana fuskantata ne. can ya taso ya nufo ni daidai lkcn da muka yi sallama nayi musu fatan sauka lafiya. Na saka fuskata cikin cinyata ina yin kukan takaici, da me zan ji? Da wulakancin Abubakar ko da kishinsa? Ga furucin da mahaifiyata ta min. Muryarshi naji daf da ni. Me ya faru?" ya tambaye ni . Da sauri na dago kaina tare da share hawayen naki kallon in da yake,amma sai na ce dashi. Ba komai. Ya dauki wayata ya shiga duba lamabr da na gamawa wayar yanzun nan. Ya kira hr lkcn wayar na hannu Innarmu. Ta daga ya ce Salamu alaikum, Umar. Inna ta ce, Ba shi ba ne yaje shan mai, mahaifiyarsa ce, Abubakar ya kara rage murya tare da zama. Inna ina yini? Abubakar ne mijin Hafsat. Ta ce Lafiya lau, kuna lfy ko? Ya ce lafiya lau, dama naga Hafsan ce naga ta gama waya kuma tana kuka shi ne na biyo layin in ji ko lafiya??Inna ta ce, Lafiya lau ban kwana muka yi da ita na kuma yi mata nasiha. Ta dan saurara kadan, sannan ta ci, gaba da magana, kai ma don Allah ina son kayi hakuri da ita. ka kuma yi adalci tsakanin matanka,Allah ya tayaka riko. Ya ce Na gode Inna Kuma in sha Allahu zan kula. Ya dube ni bayan ya kashe wayar. Da yake ba kyason gaskiya shi yasa ki ka hau kuka don kawai an miki nasiha. To kiyi yanda ki ke so tunda nasihar ce ba ki so, ai ba yau ce rana ta farko da tace kiyi kaza ki bar kaza ba ki ka ki. , Don haka kiyi son ranki kamar yanda ki ka saba. Ya aje wayar a kan ciyata ya nufi gurin matarshi. Wadda dama duk hankalinta yana gurinmu. Sai dai bana zaton cewa taji abn da muke tattaunawa, sun gama cin abncin su suna ta hirarsu cikin harshensu na Fulatanci suna dariya. Hakan yasa na tsargu cewa zancewa suke yi don haka na maida kaina baya na dora kan majinginar kujera. Na lumshe ido ina son tuno kowace Amarya ce tayi rahin dace irina a cikin dimbin amaran da suka yi aure a ranar dana yi bana zaton za a samu Allah ka bani hakurin da juriya daure wannan abn. Ina gidan hr lkcn da aka kira Sallar La'asar ya wuce ni ya nufi Masallaci, itama ta nufi dakinta ba tare da ta kalle ni ba,tamkar in fita in tafiyata, duk da cewa bn san hanya ba, amma na cije.Me aikinta ta fito na ce ina ne gurin Alwalarsu? Ta ce Duk a bayikan daki suke yi. Na ce, ba ku da ko famfo a waje? Ta ce, ita ma bakuwa ce, jiya ta zo amma taga can fulawoyin can ana basu ruwa, kila akwai famfo a gurin. Na ko samu famfo nayi alwala nazo nan in da na tashi nayi sallata. Ina zaune ya dawo. Ya kalleni, kamar zai yi magana amma sai ya fasa, ya nufi ciki koda suka dawo falo suka zauna. Sam nayi nisa cikin tunani ban san me suke fada ba, suyi da yaransu suyi da turanci, wani lkcn har da hausarsu kamar ta 'yan koyo. Da Magriba ma da ya fita dakin ta nufa da ya dawo ina azkar ya zauna sannan ya kirata da wayarshi. Ta fito ta sake wanka da sabon ado cikin koren yadi mai ratsin ja, doguwar riga ce, tayi kyau sosai, ga kamshi turaren amarci na tashi. A raina na ce, Lallai wannan sai na dage a gurin kwalliya. Ya zuba mata ido, hakan ne yasa na saki baki, kai Hafsa bata yi sallah ba? ta dube ni.ta ce, Gidan ba bakonta ba ne, ita ce ta ki ta shigo, Ya ce, A"a fadima Fadima gidan nan bakonta ne a yanzun,don bata san in da zata shiga ba sai in ki mata jagora. Nan da nan sai tahade rai ta soma magana cikin Fillanci, shi kuma ya ci gaba da magana da Hausa, yana cewa. Ba wani son kai ko bambancin da na nuna miki, in dai kina son gaskiya. Na ce, don Allah ku bar magana laifina ne, ni ceban bukaci shiga cikin ba. Ya ce, mata,To shi kenan zan nuna mata komai ni. Har zuwa lkcn da muka baro gidan ban sake cewa komai ba. Mun biya gidan su Hashim, matarshi mai kirki, daga nan muka nufi gidan iyayenshi. Ummi tazo da gudu ta rungume ni. Rukayya kam tana ta danna waya ko kallo ban ishe ta ba. Na zube a kasa na gaida Daada, sannan na zauna a gurin .Tayi tayi in hau kujera na ce mata kasan yayi. Ta ce masa daga ina? ya ce Gidan fadi ya kai ta. Ta ce, ya hada mu ya yi mana nasiha? Ya ce, eh, ni dai na sunkayar da kai ina tuna nasihar da ya mana,wai mu zauna lafiya, muyi kishi irin na gidan Annabinmu (S.W.A.) Ya ce wai in bi Fadi don ita ce ya za6a uwargidansa, sannan in girmamata baya son raini, ita kuma wai ta kama girmanta, sannan ta dinga hakuri. Ummi ta katse min tunanina, Anty tashi muje ki gaida Abbanmu yana falon shi. Na mike na bita,shima nayi cikin kunya da girmamawa na gaida shi, yayi mun nasiha da in yi hakuri, in yi biyayya sannan in saba da zuri'arsu. Kada kuma na yi wani abu na 6atanci wanda zai sa zuri'arsu suyi da sun sanin shigowata cikinsu. Nayi godiya tare da yi mishi alkawarin kiyayewa. Da zamu tafi har bakin mota suka raka mu. Daada da Ummi, amma Rukayya sai da ya yi mata magana sannan ta gaida shi. Kafin mu iso gida sai da muka tsaya a wani super store muka yi parking ya shiga. jim kadan ya fito da ledoji kuda biyu ya shiga muka wuce.shine ya ruko ledar har dakina.Na fada bandaki donyin alwalar sallar ishai ina fitowa yacemin shifa xai wuce nace toh,har ya kai da kofar daki nace masa ledar ka manta ya waiwayo sannan yace taki ce.na dauka na duba kaxa ce da kayan lashe lashe na zaki nace ka kara muku ni yayi min yawa tunda kaga ku uku ne duk da yar aikin gidan nikuma ni daya ce.ya juya tare da cewa na fiki sanin mu uku ne ai! ya atfi abinsa na tada salla ta.A randa na cika kwana biyar, misalin tara na dare yace in shiri gobe da taran safe xamu wuce kano ,ina murna harda da dan tsalle na.Allah na gode maka da har nacire rai da karatuna,nan take na soma hada shirgi na.da safe dana gama shiri naje na gaida mutan gida na kuma fada musu xan koma mkrtn yau.duk suka min addu'ar fatar alkairi don doki kasa break din kirki nayi.ya iso sanye da na kalar sararin samaniya.yayi kyau,ni na shirya ya kalli kayana.Uhumm dama duk kin kosa ki koma koh?saboda mu cin namar jikin muke yi koh?na sunkuyar dakai bance komai ba ya dauki babbar jakar niku na dauki karamar da ta ratayawa.duk yan gidna sun min ftan alkairi da sauka lfy usaman kanishi ne yaja motar.shi da hashim suka kaimu filin jirgin sama gabana sai faduwa yake.yau ce rana ta farko da xan fara hawa jirgin sama jikina sai bari yake tayi.ina xaton abubakar ya dagoni sai ya tallafoni xuwa gefen kafadarshi ,na lumshe idanu har muka shiga muka xauna sannnan ya sake ni.jikinsa mai laushi da kamshi wani sonsa ne ya ratsa ni tamkar in kwanta a jikinsa...ckn lkc kankani muka sauka a kanon dabo inda rahma da sagir ke jiran mu.ckn murna na rungeme rahma sukuma suka kama hannu suka gaisha.gidan sagir muka je sai d akarfe uku sannan muka fita. na kosa muje gidan dana ke don inje gidan maman rahma inga shadad. Kai tsaye gidan maman muka wuce muna shiga naga shadad na wasn kwallo.da gudu ya taho sai na bude hannu amma sai yaron nan ya wuce wurin Abubakar ya daga shi sama nikam nayi ciki.mun gaisa da maama inda na amshi dan mukulli sannan nayo gaba.su kuma suka biyo cikin motar sagir daya amsa.mun hadu da wasu makota daidai ku, sun mun murnar aure nayi godia.na bude gidan cikin xakuwar shigarsa.yana nan yadda na barsa.na bude daki xan shiga shikuma yace toh ni xan tafi.nace toh sai ka dawo shi da shadad suka tafi.na gama na sa turaren wuta,shawarar rahma ta fadomin lkcn da muke kulle ckn daki.kafin ya tafi kiyi kokarin janyo shi gare ki ta hanyar ado da sauransu yasan ke mace ce "nace hmm shi da matarshi tamkar india,ga iya ado tamkar dawisu ,har wani burge shi xanyi.tace tabbas xaki birge shi yasn da mai kmr indaiyar yanace sai daya same ki,nace toh hum xan gwada. bayan maghrib suka dawo yana dauke da ledoji suka ajiye suak ce sun tafi yin ishai nima sallar nayi na sake fenta fuskata na sake kaya.riga ce doguwa rahma ta yadi ta bani mai rawa ce sannan ta ilahir jikin duk motsin dana yi sai ya bayyyana.yau ce rana ta farko daya shigo ckn dakin gefen katifa ya xauna shadad ya xauna kusa dashi.ya kalli abubakar yace anty bata ci abinci bah"yace xata ci ya kara cewa uncle in xaku kara tafia ku tafi dani.yace toh xamu atfi da kai.haka suka yi ta hirar su ina ta kallon shi yana satar kallona.na xauna tare da janyo ledar na duba madara mai snayi ce.na dauka na sha.na kalleshi muka hada ido sai ya kauda kai ya ciro waya yana kirar layin matarshi.ya kishingida yana magana cikin fillanci haushi ya kama ni.sai kawai na fita tsakar gida.ya jima sannan ya fito lokacin shadad yayi bacci, yace na kam na tafi masaukina.da suari na dube shi nace masauki?bansan ma ya fito bah yace eh masuakina nace hum!!sai da safe.yace toh takaici ya isheni me yake nufi dani?me yake son mai dani.ina kwance dare ya tsala amma na kasa bacci juyi nake yi kurum a kan katif.ni mutum ce kuma mai lfy ina matukar son ganina kusa da maigidana.naja tsakin takiaci me yasa da ban damu da wani namiji ?wata xuciyar tace lokacin ba kida aure, yanxu kuma kina da miji wanda kuma kina so.daga karshe dai na mike nayo alwala nayi sallah wanda ita kadai ce mai mun magani damuwa. ***** ***** ******** Munnir yashiga gdansu cike da tunanin ta ina zai fara yiwa iyayensa bayani, yace mum, tadubeshi cike da tausayi, don tunda yaci karo da ciwon nan suke tausaya masa, tace lfy munnir meya faru? Yace mom eh....daman...wataran....sai yai shiru, tace kayi mgn mana menene yafaru? Yarike kai, tace ciwo yakeyi? Tazo gabanshi a rude, yace mum wani yaro nagani kuma muna matukar kama, kuma ada maman yaron budurwatace, IYE!!! Mekace? Tazauna gabanshi a kasa, tace yimin bayani yadda zan fahimta, tace inba wani abu yashiga tsakaninkuba toya daga ganin yaro dan yayi kama dakai sai kace abaka? Yace mum shekarun baya zaki tuna wata yarinya datazo gdan nan tace tanada ciki? Tayi shiru tanason tanawa shikuma yayita mata kwatance har saida tagane, yace to itace mum, kuma nasan cikinane tunda nina mata ta karfin tsiya, (oh kuji rashin ta ido) mum tace inane gdansu? yace nan abj road ne, tace to bari dadynku yadawo saina masa bayani. Da dady yazo tafada masa, nan da nan sai yau murna tare da shan alwashin in zai karar da duk abinda ya mallaka saiya amsa jikanshi da namiji, munnir cikin murna yace, dady itace wadda yan yola sukazo daurin auranta yau din nan, cikin mamaki dady yace, kana nufin daurin auren damukaje? Munnir yace eh dady, yayi shiru yana tunani, mom tace, ina ruwanmu don dan abokinka ya aureta? Allah yakaimu gobe, nida kaina zamuje gdan, hakan kuwa ta faru, misalin karfe 10 na safe munnir da dadynshi sukayi sallama kofar gdan baban hafsa. Daman baba yana zaune inda yayi sallar walaha bai tashiba........ Zaharaddeen Shomar whatsapp 08168575100 Sanadin Boko 4-02 Posted by ANaM Dorayi on 06:37 PM, 28-Sep-15 Under: SANADIN BOKO Ya daddogara yafito, bayan sun gaisa, sai yace dama yazone da batun yaro, wanda 'yarshi ta haifa, baba yace banganeba? Munnir yace, baba baka ganeniba? Ninefa munnir saurayin hafsa, kuma dan data haifa nawane, shine na ganshi gurin bikin nan. Dady Yace, duk abinda aka kashe zan biya, munzone mu sulhunta abamu yaron,ran baba ya baci,ckn xuciyarsa kuma yaqi yadda da yadda suke so.Tun farko matsalar me yana kawo cuta da cin xali don suna takama da kudi shine xasu daurewa dansu gindi yayi wa yarinya mugunta?Baba yace gaskiya ni bansan da wannan xancen ba "yata kuma ba a nan take ba a kano take sannan dan da kake magana yana da ubanshi.Daddy ya kalli munnir toh kaji?Munnir fa daddy yaron yayi kama dani sosai.baba yace itace hujjark kawai?nan gaba wannan ba hujja bace don nasha ganin masu kama dani da sai in bisu ince yayana ne? Daddy yace to wai yanxu ina yaron yake?baba yace sun tafi gidansu sai anjima.ya nufi gida daddy ya hau munnir da fada wai ya musu karya.suka shiga mota suka tafi ,shidai munnir ya tabbata danshi ne kuma xai ta bin diddigi sai ya amshi dansa.ya lumshe ido ya tuna kyakyawan fuskar yaron mai kama dashi mai cike da wayo da dabara gami da lfy.Mom tayi jigum dajin cewa xancen ba gaske bane.tace ina ce son yara ne yasaka yin haka toh ai shi kenan.Munnir yace nidai nasan dana ne kuma xan ta bin diddigi har sai na samo shi.Daddy yace in kaje ka janyo rigima kaga dan wani kace naka ne kai xaka kwana ci.mom tace kai dai ka barshi ya san nashine ta kalli munnir kabi diddigi xamu dauko lauyoyi.Munnir yace yauwa mom danAllah ki sayamin donko nasan cewa yaron nan nawa ne.tace kada ka damu kaidai kabi komai a sannu.ya mike ya fita daddy na kara jaddda musu cewa shi fa ba ruwansa. Kasan cewar ban samu bacci ba sai ya xamana na makara, nayi sallah tare da shirya shadad. kaxar jiya na bashi da milk din yaci.sai ga yayan su Rahma yayi sallama na saka hijabi na fita muka gaisa,yace shadad ya fito xai kai su makaranta shi da yayan sa dama mama tace min shi ke kaisu,duk da cewa ba makarantar su dayaba.muka gaisa suka tafi na shigo na gama yan gyare gyare na nayi wanka.ankon bikin rahma nasa ya shigo da sallamarshi hannuwansa dauke da ledoji farrera guda biyu.na fito da sauri na amshi tare da cewa sannu xuwa yace yauwa sai ya sake fita dauke da buhun shinkafa ya shigo.haka ya dinga shigo da kaya ina ta masa sannu da xuwa har ya gama.na shimfida mishi tabarma a ciki ya xauna na gaishe shi ya amsa.ya amsa ba yabo ba fallasa nace mai xaka ci in maka ya dubeni ido cikin ido yace am ok.ya kalli agogo yace jirgin karfe goma xan bi xuwa yola,na kalli agogon bango karfe 8.na dubeshi wani sonshi ke fisgata kamar in sa kaina a jikinsa.kamshinsa mai sanyin dadi ya karade ko ina acikin dakin, muryarshi ta kaseni.""ki duba abubuwan dana kawo in akwai abinda kike bukata babu sai ki gayamin.Bansan me yasa muryata ta dishe ba nace ko ban duba nasan abundaka siyo sunyi.Allah ya kara budi nagode.yasa hannu cikin aljihu ya kirga kudi naira dubu 10 ya bani.ki riqe wannan bani no mai adaidaitar da yake kaiku makaranta na dauko wayata na dauki lambar tare da mika mishi harda wayar ya amsa tare da dubawa.ya kirashi ya amsa .ce masa yayi yana jiransa an nan gidana yace toh.na sake cewa kodai indomie xan dafa ma yace a'aah.ya fito da wayarshi daga aljihusa tana ruri tare da karawa a kunne yace sweet honey. gabana das ya fadi tabbas fadi ce na mike na fita raina daure naje in kwashe kayan daya xubamin.dana gama na xauna waje kan kujera ina son in tuno abin da abubakar yayi min me yake nufi dani? tamkar in bar gidan saboda bakin ciki yanda suke hira da daria.duk da cewa yarensu suke yi sai turanci jifa jifa sunkusa minti ashirin sannan suka yi sallama.wayata dana baro a dakin sai ta shiga ruri ya dauka ashe dan mai adaidaita sahun ne ya iso don haka ya mike yace yana xuwa.ta gabana ya fice,kusan mintin 5 sannan yace ni xan wuce.na ce saboda anagutsirrkah dole kace xaka tafi ,ko kuma ince ka kosa xaka tafi daga wurin maqiyarka.yayi dan murmushi hakan ne"ya cigaba da cewa ni xan tafi kamar yanda nace kuma ba xan cemiki ga randa xan dawo bah sai san da na samu sukuni.haka nan kuma bayan mkrnt ban laminta aje ko ina ba sai an nemi ixini in sani.maganarshita fako ta kona mun rai wai hakan ne kenan ni makiyarsa ce,na dago na dubeshi "wai mai nayi maka ne kake son kuntata wa rayuwata?tun daga ranar dana sake ganin kah na rasa sukunina,meye nufinka dani? :kuka ya subuce min yace "au da ke baki san kinyi wani abu ba ?to duk ba wannan ba ni me na miki.kince mkrnt na dawo dake na baki abinci na baki kudin cefane, na daukin nauyin dake a kanki na dawo dake.me kike so bayan haka?ya sake matsowa kusa dani tare da sausauta murya "fadamin in kina da wata mastalar?nayi shiru ina son tuna me xance?sai ince baka sakar min fuska kuma baka saurarena ?kai gaskiya in nayi haka ba da kai ne...ya katseni dake nake nace akwai sauran matsala?na dube shi ka fini sani.ya sake matsowa ya ce kuntatawar da nake miki ?nace da ban hadu da kai ba hankalina a kwance.yace saboda ba ki sona koh?haushi ya sake cika ni ,son shi ya cika ni ya hanani sakat sannan ga abubuwan da suke biyo baya,amma xai ce wani bana son shi.bansan sanda nace eh!ai tuni nace bana sonka mai yasa ka tursasamin har sai da ka aureni.ya xura min ido.nayi laifi dana raba ki da rayuwar kangi da gantalin bin maxan d akike yi?na mike tsaye ni kada kamin sharri baka ganin a dandi ba.yayi yar daria yace yaro yaro ne koh ba da kanki kika fadamin cewa ke karuwace a nan gidan ba a wurin nan bah.kila ma dan gidan baya magana ne daya shaideni,nalumshe ido ckn takaici na ce magan xarar bunu na nufi daki shikuma in jin fitarshi.nayi kuka mai isata sannan nace laifina nake nina kashe kaina.shi kuma a cikin jirgi yayi jugum gani yake ya xalunce ta, bai dace ya ringa jefa mata magana ba in yai la'akari da ya fa aureta. :Saidai har yanxu yana takaicin kasancewarta karuwa ce ada bai san adadin maxan da ta kwana dasu ba.Don haka kyankyaminta yake yi in ya ganta sai ya tuna lkcn da take gayamasa ita karuwa ce.sai yaji haushin ta.sai dai duk wannan bai hana sonta yayi anbaliya a cikin xuciyarsa ba.ni kam haka nayini da takaici,washegari haka na bufi makrnt tare da yi wa Sa'adatu suleiman godia.na samu duk tayi min test dina.nan suka yi tamin tsokana wai daga xuwa daurin aure sai na bi miji yola nabarsu da katin walima.daria kawai nayi tare da basu hkr.sam bana xuwa ko ina sai mkrnt.daidai da gidan su rahma bana shiga sai dai in aika shadad yace in gaishe da maama.in nayi abincin marmari sai in aika mata koh in ina dawowa daga makarnt sai in siya mata goro in aikamata dashi :Rahma ma ta gaji da tambayata yaushe xanxo sai gata rannar wata lahadi.itace ma na ba wa dinkunana na ce taje dasu ayi min, tace inxo muyi mgn da telan, nace rahma Abubakar ya hanani xuwa ko ina inba mkrnt ba.ta ce toh"xamuyi magana ta waya in yaso sai in baki no telan nace toh!!nagode.tunda ya tafi sai daya kwana biyu sannan ya kirani ,gaisawa kawai muka yi yace in bashi shadad su gaisa na bashi suka yi ta surutun su hardai na tashi naje nayi sallar isha'i sannan suka yi sallama.shadad ya dube ni Anty kinsan me?nace a'aa yace Uncle yace wai da ina da ina kike xuwa bayan mkrnt nace babu koh gidan su maman rahma ma kin dena xuwa.sai yace ki ringa xuwa kina gaisheta.wai kuma ince miki sai da safe ,kuma in muna son wani abu ki fada mashi ta txt.nace shadad tashi kasa kayan bacci,ka kwanta "cikin xuciyata kuwa nace koda xaya kirani ba xan cemi shi bamu da komai bah koda ba mu dashi.:Kullum xai kirani daidai wannan lkc wato bayan sallar isha kenan,tsakaninmu gaisuwa.kuma xai ce in bashi shadad suyi mgn a waya ,wani lkcn ma kwanciyata nake yi in sharesu inyi bacci na.kwatsam ranar wata juma'a a lkcn muna tsakiyar jarabawa na dawo a gajiye ga tarin gajiya don kullum karatun dare nakeyi.na watsa ruwan sanyi,bacci nake ji baxan iya girki ba don haka gari na jikawa shadad da madara na rufe gida na kwanta.banyi nisa cikin bacci ba anji shadad yana jijjigani .Anty a buga gida inje in bude?Anty? da kyar na amsa.shadad danAllah ka barni inyi bacci.Anty ana fa buga gida inje in buda.nace jeka shadad.naci gaba da baccina.ya taka kujera yaje ya bude nan take ya dane Uncle dinshi suka shigo tare.nayi dai-dai kan katifa na dura kaina kan filo tsakiyar kafa funa na saka filo a tsakiya.sanya nake da farar singlet sai wani siket dina mai fadi ,tsawon shi daidai gwiwata,ya tsura min ido lallai hafsat nada durin jiki mai kyau ,kuma daga ganin fatarta xaiyi laushi.shadad ya soma girgixa kafata Anty tashi ga Uncle anty,a firgice natshi don har ckn kaina naji kiran.idanuna jajir nake kallon shadad "menene?ba nace ka daina tashi na ba ya nunamin Abubakar dake tsaye ya kafe ni da ido.da sauri naja hijabina na rufe jikina sannan nace sannu daxuwa "ya lumshe ido tare da amsawa a ckn wata sarkarkiyyar murya.naja xani na daura sannan na shimfida mashi tabarma na dauki hulata na saka na nufi kitchen.dama naxo da kankarar pure water saboda xafin kano kullum nakan xo da kankara in saka cikin kula.da dauko nikarkiyar shinkafa ta wanda na samata kayn kamshi,na tace na saka mata flavour mai kamshin kwakwa naje fa kankara ckn jug.na dora kan tire da kofi naxo na dire a gabanshi.:na tsiyaya masa ckn cup na aje masa,sannan nace "me xa'a dafa maka?ya dube ni ki barshi.Ban san dalilli ba, sai kurrum naga hawaye sun cika idona, idanuna suna kallon cikin nashi nace in maka fruit?ya cigaba da kallon idona, nima ban dauke nawa idon ba.hawayen idona suna sauka a hnkl.Shadad ya katse mu Anty kiyi mishi fruit Uncle da dadi nima xan sha.yayi yar ajiyar xuciya, sannan ya dauke idonshi daga kaina ya maida gun shadad, yace xaka sha da gaske? Shadad ckn xumudi yace xan sha nayi murmushi kadan sannan ya dauki kofin jus din kunun shinkafar ya kurba.sai naga ya hade rai, ya hadiye jus din da kyar.sannan yace wannan fa?haka yake ba sugar.kinsan bakina yasa ba da xaki.nan da nan sai na tuna ashe sabar sauri ne yasa ni ban saka sugar,lemon tsami ba,don haka sai na saka tare da suga da na zuba masa sai naga ya hau sha. Na kira Shadad na aike shi siyan fanta gidan Maman Yusra. Na yanka abarba, gwanda da kankana, bayan na wanke su na 6are ayaba sai na yanka dabn saboda kada tayi baki, in taji sanyi. Na matsa lemun zaki,shadad ya kawo min fanta mai sanyi na zuba mishi a plate mai zurfi tare da cokali. Sannan na kawo ayabar na zuba,shadad ma na zuba mishi. Nasha mmk, kafin wani lkc ya gama da shi, Sai naji sanyi a zuciyata, farin ciki ya cika ta, dama haka mace ke ji a duk lkcn da mijinta yaci duk wani abu da ta sarrafa? Lallai kuwa zan dinga kirkirar abubuwa don na birge shi dasu. Ya katse min tunani da cewa, Zan iya shiga bayanki? Ina son yin sallah,don bn sami Jumma'a ba. Na dube shi a raunane, Me zai hana? sai dai ko in kana kyama, don namu na talakawa ne. Ya mike ba tare da ya ce kala ba, ya nufi bayina,duk da cewa bayin na gargajiya ne, amma wanke yake tsaf, ba zarni ko karni ko ko wari. Khamshin sabulun wabka ne kawai sai ko na omon wankin bayi. Ya fito yayi alwala. Tuni na shimfida masa darduma, don haka ya tada sallah, ni kuma na fada wanka ko da na zo ya idar. Shadad ya kwaso masa takardun mkrntrsa yana dubuwa, na dire tsakiyar katifa ban cire hijabin ba na murtsuka mai bayan na basu baya. Da zan sa kaya sai na diba na fita waje ya bini da ido har na fita,sai da na saka kayan na zauna kan kujera ina daura dankwali. Na kalli madubi,masha Allah! Nayi kyau, daya ne daga cikin dinkunan da na bawa Rahma na saka, riga ne da siket na leshi mai ruwan dorawa da ratsin baki. Na koma kan katifar ina saka turare, na kalle shi shima ni yake kallo. A duk lkcn da idanunmu suka sarke basa son daukewa daga barin kallon juna. Yanzun haka mun kasa ko kiftawa,shadad ya kalle

Chapter 18 of 22