Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
sai dai ki yafe mana, Allah ya baki hakuri." Ni dai nayi daki. Na koma Kano naci gaba da zuwa Makaranta, wata uku jal ya rage min in kammala HND dina, tun tafiyar abubakar bamuyi waya ba sai dai text yake turo min. Cewar inyi hakuri wai abubuwa sunyi masa yawa shi yasa, amma zai kira ni ina ranshi. Cikin bacci naji karar wayata da faduwar gaba na tashi, sai da na kalli agogo karfe 2 da minti 40 sannan na dauki wayar na duba sadeek dina na furta a hankali sannan na daga wayar a hankali na furta "Amincin Allah a gareka" ya amsa da cewa " Ameen kema amincin a tare dake, na tashe ki a bacci ko? Nayi rigingine tare da matse filon a kirjina, nace ka isa kayi fiye da hakan" Ina jiyo sautin mumurshinsa ya ce tunaninki ya hana ni bacci,kewar muryarki ta dame ni shi yasa na yanke shawarar kiranki. Na ce Nima kewar ganinka nake yi yaushe za ka dawo? ya ce, da gaske kin kosa ki ganni? na ce um, ai ganinka ya fiye min komai a rayuwa Sadeek dina. Ya numfasa"Me ki ka tanadar min kafin nazo? Me ka ke so mijina? Ya ce, ke kadai nake so. Na sake tausasa murya,Ni taka ce mijina,zan zama mai binka a kowane lkc. Ya ce Na gode Hafsat,zan nuna miki kalar soyayyata,za ki sha mamakina. Na katse shi,"Wace iri ce ka fada min. ya ce a"a sai in nazo za ki ga zahiri,yanzun zan sunbace ki in kin amince. Na ce Bismillah. Sai kawai naji sumbarshi a cikin dodon kunnena har cikin karamin yatsana, ya ce kiyi bacci da mafarkina mai dadi. Na ce ba zan iya ci gaba da bacci ba, zan tashe ne in nuna murnata ga Allah,tare da yin addu'a ya tsare min kai, ya baka duk abn da kaje nema,ya kuma dawo min da kai lfy. Da sauri ya ce, Amin-amn sweet heart . Na ce Wannan Sunan Fadima ne, zan fi so nima kasa min nawa. Ya ce, To shi kenan. Kusan sakon hudu sannan ya ce, ki kashe wayar,na ce kai ne babba kai ya kamata ka kashe,ya ce na gode. Abin tamkar cikin mafarki, wai ni ce matsalolina ke ta kwakkwancewa a hankali. Na tashi cikin farin ciki nayo alwala nazo na zube gabn Ubangijina, addu'o'i nake tare da nuna godiyata ga Allah. Na kuma yi wa mijina shima, Allah ya dawo da shi lfy,ya biya mishi dukkan bukatarshi na alkhairi,tare da dukkan Musulmi baki daya. Ta gidan Rahma na biya na ce Lissafo min abubuwan nan da ki ka ce ya dace in yi amfani dasu. Ta dubi ne, Wane abu kenan? na ce, Na Amare.. -Ta sheke da dariya, sannan ta ce, "Dadina da gobe saurin zuwa, yau ke ce kika zo neman abin da nayi ta binki da shi kina gwasale ni?" Nima 'yar dariya nayi sannan na ce, "Fada min." Na fito da memo da kuma biro daga jakata. Ta ce, "Da gaske ki ke yi? To ai gara kam ki rubuta don ba zan baki hadadde ba, zan fada miki abubuwan da ya kamata ki dinga ci." Na ce to. (Fruits ne ta yi mata listing including Nono, zuma, madarar shanu, nonon rakum, kokumba da gurji) Ta ce, "Kin rubuta?" Na ce, "Eh! Amma zan ta cin su ne haka ko yaya abin ya ke?" Rahma ta ce, "Kina iya cin su ko ki hada wannan da wancan. Na barki kije ki gwada basirarki." Na natsu ina kara kallon abubuwan, sannan na mike tare da cewa, "Bari in tafi kada Shadad ya dawo ya same ni, amma zan baki mamaki. Sai kin zo gurina rokon in fada miki irin nawa sirrin." Ta ce, "Zamu gani." Na tafi ina dariya. Na cema dan adaidaita don Allah ya kaini kasuwa. Ya ce, Ba komai." Duk abin da na rubuta sai da na siyo su. Ta kan kankana na fara na fere bayan na markade ta har 'ya'yanta cikin blender, na dauko kwakwar da na yanka kanana itama na nika, na daka raken da na yanka kanana. Na fidda ruwan shi na hada su guri daya ban ko tace ba na fasa madara peak na zuba zuma na fasa kankara na jefa, ranar shi ne abincin dare na. Da safe kuma ina da garin alkama, na dama shi da madara na zuba zuma, bayan na dama shi ya zama kunu na sha. Da na dawo makaranta na dafa zogale na yanka gurji a ciki kanana, na kwada da kuli na zuba tumatir. Nan na zauna na ci na koshi, sannan na kora da kunun aya da dabino da kwakwa da madara da zuma yayi kauri na sha na yi kat. Da daren ranar kuma farfesun kaza na yi ruwa-ruwa na lankwashe na sha romon sosai. na yi kat, na zauna ina cin apple (Hhhhhh, lallai Hafsa da gaske take yi 'yan uwa, shan romo har da lankwashe kafa? Washegari hadin kazar amare na yi ta tamkar yanda na taba ji. Tun daga ranar ruwan 'ya'yan itace shi ne ruwan sha na, dukkan abubuwan da Rahma ta lissafo min na maidasu abincina, abin sha na. Kafin sati daya ni da kaina na yarda cewa na hadu, kai ina mamakin kaina idan na tuno irin kalaman da nayi ma Abubakar idan ya kira ni. Shi kan shi Abubakar din baya iya daukar awa 3 ba tare da ya kira ni ba, lallai na amince iya yin lafazi mai kyau ga miji yana sa mace ta mallake mijinta, nuna damuwa ga damuwar miji tana sa miji ya kara son ki. Ana gobe za su dawo na shiga kasuwa na yo cefane, duk da bani da tabbacin cewa Kano zai sauka, Na damu ya zo don shirina da nayi ya soma damuna. Ina kwance bayan la'asar na kira layinshi ya daga, cikin sauri ya ce, "D only! Yaya ne?" Na ce, "Hayate don Allah ta nan zaka biyo?" Na yi maganar cikin sigar shagwaba. Ya ce, "Muna tare da Abba yanzun, zan kira ki in mun rabu dashi kin ji?" Na ce, "Toh." Ba'a fi koh minti 10 ba ya sake kirana. "D only kina jina?" Na ce, "Eh!" Ya ce, "Muna tare da Abba ne kin ga ba dama mu rabu ko? Kuma Fadina tana sa ran zuwana." Na ce, "Kai Hayate (cikin shagwaba nake maganar) Ba fa nan ka tashi ba, don Allah ka min adalci in ganka kawai ka wuce, ko ba ka zauna ba." Zai yi magana na ce, "Please Mr Cool, bana jin zan iya kwana 2 ban ganka ba, sorry pls." Sai naji yayi ajiyar zuciya tare da cewa, "To yanzu yaya zan yi da Abba?" Na ce, "Ya san kana da ni fa a Kano, in kace zaka zo ai bana zaton cewa zai yi fada." Ya ce, "Bana son ayi zargin cewa nafi sonki amma zan dan yi dabara in zo din ko ban kwana ba, muka ga juna sai na wuce." Na ce, "To na gode Mr cool. Sai na ganka." Hmm! Ranar da zai dawo ko Makaranta ban je ba, tun safe na ke hada mishi sinasir da miyar alayyahu, simmer fish, meat bolls, meat into potatoe da peppered chicken. Na yi fruit salad na yi coslow, jus din cocumber, sai kuma na yi masa coconut drink. Nan na shiga jera masa duk abubuwan da na tanadar masa. Jus din na soma zuba masa ya sha sannan na bude masa dukkan abubuwan da na girka na ce, "Wanne zan soma zubawa?" Sai da ya hadiyi miyau sannan ya ce, "Kowanne kadan." Tun da ya soma yake fadin, "Alhamdulillah Masha Allah, na yi dace kam." Dadi nake ji tamkar in yi tsalle sai sake zuba mishi na ke, ya ce, "Bar shi kada in kasa bacci." Na sirka mashi ruwan wanka, ya ce da na sanyi zai yi na ce, "A gajiye ka ke zaka fi jin dadin wanka da na dumi." Ya ce, "To." Daki ya shiga ina daga waje ya bude jakarshi ya canza kaya, sannan ya ce, "Zo ki raka ni in kama masauki." Na ce, "Nan gidan ba za'a iya bacci ba?" Ya yi dan murmushi, "Zo dai mu je mu dawo." Shahararren masaukin bakin nan muka je ya kama daki, na bata rai. Bayan mun zauna bakin gado ya ce, "Yi min dan murmushin nan mana." Na dan harare shi da wasa, "Ba ka 'ki kwana gidana ba." Ya ce, "To ni nan zaki taya ni kwana." Na zaro ido, "In taya ka me? Tab! Tunda dai na rako ka maidani gidana." Ya ce, "Tsoro nike ji, dakin yayi min girma." Na harare shi tare da cewa, "Da can ba kai daya kake kwana ba?" Ya ce, "To ai yau na soma jin tsoron, ba kin ce kin min tanadi ba?" Na ce, "To ba na baka ka ci ba?" Ya ce, "Daman wai tanadin abinci ne?" Na ce, "Eh mana." Ya ce, "Ammafa ba haka muka yi da ke ba." Na ce, "To yaya muka yi?" Ya mike ya dauko jakarshi, "Zo ki gani." Ya fitar da duk kayan jakar, can kasa ya fito da wasu kaya, kayan baccine 'yan India masu shegen kyau, baki da pink ne. Ya fito da pink din ya ce, "Gwada wannan in gani." Na amsa na daga ina kallo, akwai kyau amma zai fi dacewa da sunan Fandarinki tsirara. Na yi tsaye ina kallonshi yana mai da kayan, ya mike, "Kawo in gwada miki." Na ce, "Zan iya." Na fada toilet na saka, na dubi kai na, zan iya fita kuwa? Na yi ta maza na kama kofa zan bude, sai kurum na ga ya bude ya shigo. Na runtse idona shi kuma ya ce, "Kai cancadi! Zo mu je in miki hoto." Ya rikeni muka fito. Ya zauna bakin gado tare da dorani kan cinyarshi, Kai Subhanallah!!! Abubakar ya fara shafani tun daga wuyana har ya sauko kirjina wanda ba kace na shayar da Shadad ba, ya rude ya shiga kissing dina, anan dai ya dinga yaba min irin goyon bayan da na bashi tare da tanadin da nayi masa, ya dinga min surutai wanda bana gane mai yake cewa, sai dai numfashinsa kawai nake ji, kai ba zan manta da wannan rana ba, son Abubakar da kaunarshi gami da kishinsa sun karu gareni, kai na so in cuci kaina, kuma na yarda cewar soyayyarshi mai tsada ce, amma na kula shima ya yaba da ni matuka. Nan muka yi Magriba da Isha'i munata tarairayar juna, ian kallonshi ya kashe dukkan wayoyinshi, a takaice dai nan muka kwana muna faranta ran juna cikin farin ciki, ko kuda baya son yaji a jikina. Misalin Goma na safe muka dawo don 12 zai nufi Yola, amma sai muka bude sabon shafin soyayya anan gida na, ya dinga lugwiguita ni yana zantuka iri-iri masu wuyar ambato, Abubakar ya dinga santi tare da yabon Hafsa cikin kalamai masu dadi, nan muka kwashe lokuta da dama dan bamu san lokaci ya tafi ba, har ya so ya makara. Ni kam da zai tafi har da kukana, ya lallashe ni da cewa jibi zai zo mu wuce Kaduna don karkare shari'ar nan, da kyar ya lallasheni sannan ya tafi. Kwana daya jal da muka yi ya sani na manta duk wata damuwa da ke raina, lallai Abubakar shine irin mijin da mata ke so, wanda zai shagwabaka, ya so ka kuma ya riritaka, har ka mance a duniyar da kake. (Ohh! Su Hafsah sai sambatu ake) Ya san so yasan sirrin so, ya san yanda ake zama da mace. Haka ya tafi ya barni da kewarsa duk na rikice. Da dare ina kwance tamkar in kirashi amma sai na tuno can mafa yana tare da matarshi, kishi ya isheni, yanzun duk irin kulawar nan da ya bani haka zai bata? Sai hawaye masu dumi suka soma sakko min, can dai na dauko wayata ina kallon hotunan da muka dauka ni da shi cikin soyayya da kauna irinta masoya, lokacin muna cin abinci cikin soyayya da tsokanar juna a masaukinsa, kawai sai na samu kaina da rubuta masa I LOVE U na tura masa. Can har na fara rubuta dogon text na soyayya, sai kuma na fasa na ce abinda baka so a maka kai ma kada kayi ma wani, don haka sai na danne. Kusan 12 sai ga kiranshi, da sauri na daga, a hankali yake magana ina zaton ko Matarshi ta yi bacci ko kuma ta dan fita oho, ya ce, "The only kina jina?" Na ce, "Eh." Ya ce, "Na ga sakonki, ina sonki sosai, ba zan manta irin kaunar da na sha a gareki ba, kin jiyar da ni dadi matuka, inata tunanin kasancewa tare da ke, kiyi bacci kinji?" Cikin Marairaita na ce, "Ba zan iya ba Cool, yaushe zaka zo?" Ya ce, "Zan kira ki anjima kin ji?" Na ce to. Ya ce, "To in kin kasa bacci tashi kiyi mana addu'a Allah yasa mun samu Baby." Na ce, "To Cool, miss U." (Hhhhhh, Su Hafsah an hau duniyar sama an gaza saukowa) Hakan kuwa na yi, da nayi alwala na dauki Al-kur'ani na soma karatu, sai na samu nutsuwa. Kusan 2 na dare ya kirani, "Me ya hana ki bacci d only?" Na ce, "Tunaninka mana." Ya ce, "Nima kina raina Hafsah, da ban same ki ba da nayi asara." Na ce, "Wai! Ni ce zan ce da nayi asara don irinka akwai wuyar samu." Ya ce, "Maza da yawa ba zasu gane ba sun fi kallon kyan fuska, Hakika suna zaban tumun dare." Na yi dariya sannan na ce, "Ka kwanta don Aunty Fadima ma baza ta so muna yin doguwar hira lokutan kwanan ta ba. Sai da safe." Ya ce, "To." Na sake alwala na zo ina Nafila dan wannan sallar tana da Muhimmanci gurinmu, in har zaki yarfe bacci ki tashi daidai wannan lokacin ki fadama Allah, to kuwa duk wata matsala taki zata yaye. Ubangiji da kanshi yake cewa da mai bukata ya tambaye shi Shi kuma ya biya mana, wannan kadai na tsare, ba boka ba mallam ga matsalolina a hankali duk sun warware. Allah ka yaye mana dukkan matsalolinmu Ameen. Ranar Lahadi kuwa ranar da zai zo cewa yayi in masa tuwon semo, sai kuma in masa jus din Shinkafa din nan. Miyar danyar kubewa na yi masa, ta ji bushashshen kifi da nama, na masa jus din shinkafa, sai irin kunun ayan da nike sha mai dabino da kwakwa da zuma. Wando da riga na ci sabbi ne na siyo su, da ina zaton ba zan iya saka wando ba amma daga baya sai na ce kiji kana cewa baka iya kukan mutuwa ba Uwarka ce mata mutu ba. Da kadan ya wuce gwiwata, rigar ma ta dame ni. Kallona yayi ta yi tunda ya shigo na masa oyoyo, da kyar na bambare daga jikinsa don yi masa shimfida, ya ce, "Ya ya aka yi kika san ina son shigar English wears?" Na ce, "Duk abinda ka ke so a kwayar idonka nake karanta, ai ba kallon kawai nake maka ba." Ranar dai mun ciyar da juna abinci, sannan muka shiga wani shafin, daga baya muka yi wanka muka dunguma gidan su Rahma. Shadad kuwa sai tsalle da ya ganmu, da zamu tafi ya so binmu, har zan ce mu tafi da shi sai Abubakar ya ce, "Shadad unguwa zamu, amma gobe zaku taho da Uncle dinka na nan gidan." Ya ce, "To." Muka dawo nan gidan muka kwana. Gaskiya duk macen da ta samu miji kwatankwacin Abubakar, to ta gode ma Allah, mamaki na daya, yanda ya iya kula da mace ta kowanne fanni...... Zaharaddeen Shomar whatsapp 08168575100 Sanadin Boko 4-05 Posted by ANaM Dorayi on 05:17 AM, 29-Sep-15 Under: SANADIN BOKO Asubanci muka yi tare da su Sagir, Sagir ke tuki shi da Abubakar, ni da Rahma da Shadad muna baya. Sagir na zuba mana hira don shi Abubakar mutum ne bame yawan surutu ba, sai dai mun ta hada ido da shi ta madubi sai ya kashe min ido daya mu yi murmushi, har Rahma ta gane mu ta ce, "Kai ku dai wanna soyayya ko ina sai kun nuna ta?" Na ce, "Kuma ku nuna mana." Kotu ta cika lokacin hankalina na tashe, gani nake shi kenan za'a kwace min da. Bayan gabatarwa Alkali ya bukace mu muka fito ya ce, "Ina yaro?" Aka fito da shi ya ce, "To a musulunce za'a yanke hukunci tunda mu Musulmi ne." Duk muka amince. Alkali ya yanke cewa, "Duk da cewa fyade aka yi mata ta samu ciki, to dan ba dan Sunna ba ne, ma'ana ba ta hanyar aure aka haife shi ba. Don haka in ma ace tayi cikin shege dan nata ne ba a danganta shi da namijin saboda sai da yardarta, don haka wannan ma nata ne, sai dai shawarar da zamu iya bata ita ce ta bawa wannan mutum dan saboda zata fi mutunci, haka nan shi dan ko kuma a ba yaron zabi zai bi Uban nasa shikenan. Sannan hukuncin fyade tunda an ce bai taba aure ba, to za a yi masa bulala dari." Nan fa suka soma kuka, Mom ta zo tana kuka tana rokona wai in basu shi, na ce "Gaskiya ba zan iya bada dana ba." Shi kuma Dad dinsu ya samu alkalin suka kiramu suna ta rokonmu wai tunda gashi shi za'a dake shi, gashi bashi da koshin lafiya. Abubakar ya ce, "In dai yayi hutu za'a ringa kawo shi saboda ya san Ubanshi da danginshi." Suka yi ta godiya muka kame kanmu. Kano muka wuce bayan mun je gidanmu kowa na taya ni murnar cin nasara, daga nan muka koma Kano. Na gama jarabawata ta fita, murna ba a magana yanzun saura service Washegari da gaggawa Abubakar ya zo ya tafi dani Yola. Shadad kuma dama Sagir ya kai shi Kaduna gidan Babanshi suna ta murna. Shi kam da kyar ya lallasu daga kukan da yake sai da Sagir din ya kira ni ya ce in mishi magana. Na ce, "Shadad." Ya ce, "An'am Aunty, ni zan dawo ne ki fada ma Uncle ya dawo da ni." Tausayinshi ya kama ni na ce, "Gidanku ne ai, gidan Babanka da kake ta damuna da zancenshi." Ya ce, "Aunty ban san su ba." Na ce, "Zaka san su kayi hakuri kaji ko?" Ya ce, "To." Munir ya ce ma Mom ta amshi lambata in ya so sai su dinga kira mishi ni. Sagir ya bada lambar sannan ya tafi. Ikon Allah Shadad na ganin gata, tamkar a cinye shi don tarairaya, har an sai mishi waya don ya dinga kirana, ni kam cewa na yi kada su bata min tarbiyyar yaro, saboda su ba su da tarbiyya. Mahaifin Munir ya yiwa Shadad kyautar gidanshi da ke Kabalar road, tunda wai an ce bashi da gadon Ubanshi. Suka bude mishi account ni kam ina can Yola gidan mijina mai sona da gaske. Yau gidan Fadima yake, amma ya kira ni wai zaya zo cin abinci da rana. Na ce, "A'a, sai dai na yarda ka aiko a karba maka, don kada mu shiga hakkinta, Don nima ba zan so amin ba." Ya ce, "To naji." Na yi masa french dish rice serve with grill chicken, sai kuma na masa dan waken rogo da dawa, dama ina da garin, sannan na masa jus din karas, duk san da zanyi girki na kan yi da dan dama saboda mutan gidanmu suna son abinci na. Hakan nan na kan kirkira girki inyi ma Abba da Lamido da kalokin Jus na kan zauna ina kallon tashar girke- girke ina rubutawa na Chanis ko Italia ko Senegal da dai sauransu. Saboda kawai in samo girki wanda ba a saba da shi ba. Fadima ta dube shi, "Ban gane nufinka da amsa abinci gidan Hafsa ba?" Ya dube ta bayan ya dire kofin hannunsa ya cea, "Ta iya girki ga kokarin yi, bata da kuiyar dafa abincin ko kala nawa ne." Ta hade rai, "Ni ban iya ba kenan?" Ya ce, "To ke ko kin iya din ma yaushe kyuya zata bar ki? Ballantana kure girkinki shi ne shinkafa da miya ko taliya. Da zaki daure da kin je kin koyo kafin ta tafi CAMP." Ta harare shi sannan ta ce, "God Forbid in je gurinta koyon girki ka cuce ni, kuma wallahi ba zan yarda ba. A ranar girkina ace abincin ta zaka ci? In an sake kawo min nan zan zubar dashi." Ya ce, "To shi kenan, zan so ki zubar din." Cikin fushi ta shige daki. Duk ranar da yake gidana akwai wasu jus na kankana, Apple, ayaba, madarar ruwa, zuma da kuma garin ridi, in sa kayan itacen a blender in nika in zuba madarar da zumar da kuma garin ridin in sha, in kuma zuba masa ya sha, har dai wata rana ya tambayeni me nake sawa cikin wannan jus din? Don shi kan shi yana jin shi kullum yana kara lafiya da kuzari, yakan kuma ji yanayi daban da in bai sha ba. Na ce 'ya'yan itace ne. Har ma watarana a gabanshi nake hadawa. Wataran kuma in hada rake, zuma, madara peak, garin ridi. Kafin wani lokaci sai gashi na zama Malama ta hada kayan gyaran jiki, in mun yi waya da Rahma in na fada mata wasu sai tayi ta mamaki, na ce, "Dama na fada miki." Abin da yafi bani mamaki, da zan tafi CAMP a Kaduna aka tura ni har da kukan shi da hawaye don damuwa. Shi ya kai ni sannan ya biya ya taho da Shadad ya kai shi gidan Rahma a Kano. zaman sati 2 a camp ko ni na san na yi missing din gwarzon masoya, Abubakar Sadiq. Fadima ta dubi Rukayya, "Kin san Allah ni zan kai karar Hamma gurin Abba, sam baya cin abincina sai na Hafsa. Don gulma har nan zaki ga ta yo ta aiko mishi da shi, kenan ya fada mata cewa ban iya girki ba." Rukayya ta ce, "Ai Hamma ta riga ta gama da shi, ke har su Daada ma in kinji yanda suke yabonta? In ta yo abinci ta kawo ma Abba kiga su Ummi har ma Daada din sai suyi ta yabonta." Ta ce, "To gurin Lamido zanje." Rukayya ta ce, "Kin ji ma inda zaki fi jin dadin kai karanki, kuma zaya ci musu daga shi har ita. Dama ai ba son auren yake ba, kila ma yana kushe auren." Cikin zumudi Fadima ta ce, "Anjuma zan je." Ta shigo gidan da sallamarta suka gaisa da mutan gidan, tsoffin suna mata tsiyar cewa sun kwace miji. Ta shiga gurin Lamido, bayan sun gaisa ta ce dama ta kawo karan Hamma ne. Lamido ya gyara zama ya ce, "Tun kafin aje ko'ina har an soma matsala? To me ya faru?" Ta ce, "Baya cin abincina, ranar da yake gidana sai ya aika nan a karba mishi abinci fa, kuma in nayi magana sai ya ce ta fini iya girki. Shi ne ni na gaji da wannan maganar." Can ya ce, "Shikenan?" Ta ce, "Eh." Ya ce, "To yanzun ina Baban nawa?" Ta ce, "Yana cikin gari." Lamido ya kira shi a waya ya ce ya zo yana nemanshi. Kusan minti 30 sannan ya iso Lamido ya ce masa, "Daga ina?" Bai ji mamakin ganin Fadi ba. Lamido ya karanta mishi laifukan da ta fada, sannan ya tambaye shi ko haka ne? Abubakar ya ce, "Haka ne." Lamido ya ce, "Don me to baka son cin abincin nata?" Abubakar ya ce, "Don bata iya ba, kuma don na amso a gurin Hafsat wadda ta iya bana zaton na yi laifi. Saboda Manzon Rahma (S.A.W) yana amso abinci a gurin Nana Safiyya ya ci in yana dakin kowacce daga cikin matanshi. Don haka ni Sunna na yi." Ta ce, "Amma shi bai yi wulakanci ba." Lamido ya ce, "To naji yanzun dai sai kiyi kokari ki gyara." Abubakar ya ce, "Abin da in riga ta dawo wa kullum sai na fa jira ta ta dawo sannan ta min abincin. Ita kuma Hafsah ko ina zata sai tayi min abincin ta bari in dai tana gari, amma ita wannan sai son jiki." Lamido ya ce, "Ka yi hakuri tashi ka je abinka.Bayan fitar Abubakar Lamido ya ce, "Ke Fadima abin da zan fada miki, kin ga bakuwar yarinyar nan? To ta fiki hankali. Tun yaushe rabonki da gidan nan da sunan ki zo gaishe mu? Ita kuwa ko bata garin nan ta kira mu ta gaishe mu a waya. Girkinmu daban ga girmama mutane, don haka ki nutsu ki zauna lafiya. Ba zan 'kita ba don tana bare, dama ai mugun iri ake tsoro." Fadima dai ta tashi jiki babu kwari ta tafi gida, zuciyarta cike da haushin Hafsah, wato ta zo zata siye dangi? Ta ja wani Uban tsaki. Allah cikin ikonsa mun gama CAMP sai dai Abubakar ya ce zai yi duk yanda zai yi a barni a Yola, ba zan kara nisa da shi ba. Daga baya ma ya ce in na gama bazan yi aiki ba, ni dai ina jin shi ban ce komai ba. Allah ya taimaka da ya shiga ya fita sai ko aka barni a Yola, ni kaina nayi murna don bana son inyi nisa da mijina, Shadad ya dawo Yola shima Abubakar ya canza masa Makaranta mai kyau, duk da cewa Iyayenshi suna ta turo kudi wai na karatunshi. Dad har Yola ya zo kuma ya sanar da abokinshi Mai Martaba Baban su Hashim cewa Shadad jikan shi ne, don haka yaron bai da matsala ko cikin gida, gashi da farin jini. Cikin haka ne FADIMA TA SOMA LAULAYIN NAN, naga rawar kai wurin Abubakar da 'yan uwansa, ganin haka nima na soma zuwa kullum ina dubata, sai ta tsiri cewa wai turarena na sata amai, in daina zuwa. Abubakar ya ce, "Fadima ta ce bata son turarenki ki daina zuwa kawai." Allah yasan na ji haushi, amma sai na share saboda sanin halin Abubakar shi mutum ne sak babu kwane-kwane a tsarin shi, baya rufa-rufa ko kara zance, yanda aka fade ta haka yake daukenta, shi yasa na sha wahala lokacin da na ce mishi ni karuwa ce, har sai da ya zo ya ji komai da kunnanshi na samu sukuni. To yanda Fadima ta ce haka zai fada gaskiya tsagwaronta yake yi ba ruwanshi, don haka na ce, "Shi kenan, na ringa kiranta a waya muna gaisawa." Ya ce, "Hakan zai fi." Daga baya sai ta tsiro cewa ita ba zata iya bacci ba sai in yana gurinta, Ya ce to bari ya same ni. Ina

Chapter 20 of 22