Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Munnir, wai ya taimakeni ne don bukatarshi, dama haka halin maza ya ke? Dama Munnir mayaudarin 'yan mata ne? Tafiya nake amma sam ban dauki hanyar gida ba ko cikin mafarki ai ba zanje gida ba. Zuciyata ta bushe na share hawaye na na nufi Babban titi. Kwatsam! Sai ga Yayana Umar ya sauke wani a mashin, cak na tsaya don mun riga mun hada ido. Cikin mamaki ya ce, "Hafsa daga ina haka?" Gabana ya fadi matuka, amma sai na kanne banda wata damuwa na ce, "Na zo ne yau ko gidama ban karasa ba, gidan su wata na zo." Ya ce, "Wacce watan?" Na 'kirkiro 'yar dariya, "Yar ajinmu ce ta yo mana gaba da kaya to na zo kuma bata karaso ba." A take karyar tazo min, ya ce, "Hau na kaiki gida." Muna cikin tafiya ina tunanin ban so na hadu da Yaya Umar ba, sai ya jeho min tambaya, "Hafsa sai na ganki duk a hargitse, fuska a kumbure kamar kin sha kuka." Gabana ya yi mummunar faduwa amma don kada ya ganoni na ce, "Kukan lafiya? Ka sam zaman mota, kuma baccina na sha har na gaji." Ya ce, "Irinku ne ake sace wa, nan da Kano kin hangame baki kina bacci,." Na ce, "Cikin kwanakin nan ne bamu samu bacci ba saboda karatu." Ko Inna abinda ta soma tambaya ta shine lafiya? Cikin dariyar da bata kai zuci ba na ce, "Lafiya Innarmu." Na shige daki na kwanta kan gado.Jim kadan Ummi kanwata ta shigo da kwanon alala ta ce, "Anty gashi." Na amsa na aje. Ummi ta tsaya tana kallona, ina zaton dan wasan da na saba yi mata ne taga ban mata ba. Inna ta shigo, "Wai Hafsa lafiya na ganki kwatsam! Kuma kina zuwa kin zube a gado?" Ban san yadda aka yi maganar ta zo min ba, sai dai kawai naji ina bata amsa, "Innarmu gajiyar mota ce, kuma dama bani da lafiya ne. Can ma muna ta sintirin asibiti shine aka ce in zo gida in nemi na hausa." Cikin fargaba da Tausayi ta ce, "Ashsha, me ke damunki?" Sai kurum na ji bakina ya ce, "Shawara da Basiri." Ta jinjina kai, "Sannu, Allah ya sauwake, jiki da jini haka ne. Ta ce ci alalar." Ta daga murya, "Ummi! Ummi!!" Yarinyar ta shigo da gudu. Inna ta ce, "Kira min Baban gida in aike sh dattawa ya hadowa Hafsa maganin basir da shawara." Ta kwance habar zaninta ta ciro kudi naira dari 3 da ashirin ta ce, "Ungo ka hau mota ka je layin dattawa gurin masu magungunan gargajiya ka siyo mata maganin shawara da na basir." Ya ce, "To." Ya amsa ya fita. Bani da damar in ki sha domin Inna tsareni take, a cewarta tun ina karama bana son magani. Duk lokacin da zan sha ina sha da niyyar cewar Allah ya sa cikin nan ya fita amma shiru, sai ma tsananin amai da ya karu gareni da kuma kasala. Tausayin Inna yana sani kuka, in naga irin fadi-tashin da take yi gurin neman min magani.Wata rana ina kwance dakin Baabah amai ya sarkeni na tashi da sauri kafin na bude kofa na soma sheka shi. Baabah ita ce ta taimaka min na gyara jikina ta kuma kwashe aman. Har na kwanta ta ce, "Hafsa!" Na ce, "Na'am." Na tashi zaune, ta ce, "Zo nan." Na mike na bita can kuryar daki ta ce, "Hafsa ki fada min tsakaninki da Allah me ke damunku?" Gabana ya yi mummunar faduwa, zufa ta keto min na ce, "Me,,,,,me kika gani?" Ta ce, "Hafsa na ga wasu alamu da suke nuna kina da ciki, menene gaskiyar hasashena?" "A'a bani da komai." Tayi-tayi da ni in fada mata gaskiya amma na dage kan cewa bani da komai, don haka ta kyaleni tare da cewa, "Shike nan. Dama ke nake tunanin zaki bani hadin kai domin Innarku ba zata fahimce ni ba na sani shi yasa na miki magana." Na ce, "Ni fa kalau na nake." Don haka sai ta rabu da ni. Kafin sati 2 duk 'yan gidanmu sun gane halin da ake ciki, amma banda Innarmu sam bata lura ba bata zata ba, ba kuma ta tsammanin haka zata faru ba, 'yan tsegumi har cewa suke mata, "Yaya 'yar boko da jiki?" Haka ta ce, "Da sauki." Tana washe baki ita a dole an gaishe ni. Sannu a hankali zance ya soma fita makota sai gashi ana shigowa dubani, niko ko yaushe ina cikin Hijabi. Baabah Maimuna ita ce ta shigo dubani yau kawar Innarmu ce kut da kut ta kalli Innarmu, "Kin san zancen da yake yawo unguwar nan?" Ta ce, "A'a." "To 'yan gidanku sun fita suna yada cewa Hafsa ciki ta yo." Inna ta mike cikin tsananin tashin hankali, "Wane dan sharrin ne? Wallahi zan iya maka mutum a kotu." Maimuna ta ce, "Saurara kiji, kafin ki fita kiyi wata magana soma tuhumar ta tukunna." Innarmu ta ce, "Haba Maimuna, sanin kanki ne Hafsa bata da rawar kai irin na 'yan iska, sharrine kawai za'a mata. Kin san bani da hakuril dole sai ba ni ba'asni wanda ya mata wannan sharrin." Maimuna ta ce, "Don Allah ki bar zancen nan." Amma Inna bata saurareta ba ta fita tana fada, wai yaya za'a yi ta bar wannan zancen ana kallon 'yarta a matsayin 'yar iska! Kai tsaye sashen su Asabe ta nufa tana fadin, "To munafukai magulmata masu zuwa lahira da kokon dambu! Za kuce 'yata cikine da ita, to aniyarku ta biku. Kuma Insha Allahu 'ya'yanku ne zasu yi ba tawa ba. Kanta aka fara ciwo da za'a mata sharri?"Kuma in sha Allahu yayanku ne zasuyi ba tawa ba kanta aka fara ciwo za a mata shairi? Asabe tace aina kika ji? Mu nan dai ba wanda ya san haka inna tace rufe min baki munafukai, to nazone in muku gar gadi zan maka mutun a kotu, sai ta fito mun da wanda ya fada mata. Ade tace maganar gaskiya ki bin ciki yarki dan muma a makota mukaji. Inna tace ahaf na san duk inda aka zaga aka zago kune zaku fadi wanan maganar, kuma zaku amsa kiran alkali,gida ya hautsine baba ya shugo yana tambayan ba asi, babah tace a a yar rigimar yara ce ba sai kaji ba. Nufinta kada yaji don tasan in yaji sai yabi duddugi amma jin zantukan sun cika gidan har makota sun soma zagayowa, ya fito dan jin ba‘asin tun bai karasaba ya soma jin muryarsu Ade na cewa an dai fada maki kije ki tuhimi yarki, ba kizo ki tasamu kina zagi ba. Ki dau mataki tun kafin lokaci ya kure miki, in shairi a ka mata sai kiji dadin kaiwa kotun. Asabe ta kara da cewa, inko kin tafi yanzun kya iya zuwa kiji kunya. Ya iso gurin yace zo, babah ta malam na kiranki don Allah kiyi hakuri ki bar zancen nan, wanda ya fada ba don kansa ba. Ta nufo daki inda baba ke kiranta, ina kuryar gado tare da fatan Allah ya dauki raina yanzunnan. Baba ya dubeta, to in kin gama fadan kira min yar bokon yar taki inna tace saboda Allah malam daga ciwo sai ayi mata sharri? Ca wa fa sukayi tana da ciki yace ai ba abin mamaki bane kira min ita. Hafsa zonan, na fito kishirya mutafi asibiti inna tace malam asibiti suna bada maganin basir ne? Acan makarantarsu fa sunyi na asibitin sun gaji shinefa sukace ta taho gida ayi na hausa. Yace to ai ba matsala bace wanan, matsalata in tabatar da zargin da ake yi mata inna tace ai! Malam kaima ka yarda za ta iya? Yace kwarai kuwa, yace ita ba mutum bace? Ya ba kanshi amsa yacemutum ce kuma baliga mai lafiya, don haka yanzu da bayanin likita zan yarda da duk abinda zakuce. Nan take tsoro ya kamani hankalina yafi da tashi. Inna tace je kushirya kutafi asibitin inma har har danine sai muje. Yafita tare da cewa ina jiranku waje. Nace inna kice masa don Allah mu bar zuwa asibitin nan kinji? Tace a a ki shirya kindai san halin babanki, in ba‘aje likita ya wankekiba bamu da zaman lafiya, nace inna mudai mu hakura ba sai mu barsu da Allah ba, masu cewa inada cikin? Tace shin hafsat kodai kina da cikin ne?nazaro ido nace a a ni bani da komai tace to shirya muje, garuwa ki daureye jiki nace to a ban daki tamkar in haure yar gajeruwar katangar mu in gudu, domin na san yau idan mukaje asibiti asiri na yagama tonuwa. Yau auren iyayena zai rabu na shiga 3! Nan wata zuciyar ta fada mun ba laifina bane, in bisu inje asibitin inyaso duk yanda Allah yaga daman zai faru dani shikenan, sai in rungimi kaddara. Afili nace Allah ya isa munnir asibitin dutse muka je, baba shine ya yankar min kati suka tura mu gurin da zamu ga likitan mata. Duk da halin da nake ceki sai da nayi Allah wadai da shugabannin da muke dasu. Asibiti ka mar wannan ace likitoci mata basufi uku ba, ga mata nan sun kusa 100, wata mata dake kusa dani tace min tun asubahi suka zo nan tayi sallah. Amma har yanzu ba‘a zo kanta ba. Ina ganin rashin kula da ba ayi da likitocin shine dalili da yasa basu zuwa aiki. Haka muka yini a gurin, amma baba ya dage sai munga likita. Muna shiga ya bashi kati likita ya tambayi meke damuna?Kafin nayi magana baba yace yata ce, munzo ne ayi mata gwaji kotana da juna biyu. Likita yace bari yaji ta bakina, ya tambayeni meke damuna? Nace basir da shawara, yace yaya kikeji a jikinki? Nace amai da zazzabi. Kama hannuna yayi ya duba, nan take ya bamu wata takarda wai muje amin gwaji nayi fitsari na kawo. Nan take sakamako ya fito baro baro ina da ciki nurse bata fada muna ba, ta dai bamu sakamakon mu kaiwa likita. Lokacin zuciyata ta gama bushewa, na mekawa Allah komai. Mun shiga yana rubuta muna wani magani, sai da ya gama sanan ya duba. Ya kali baba, tana da miji? Baba yace a a likita yasake kalona, amma ke kinsan kina da ciki? Wata muguwar faduwar gaba naji, tamkar yau nasoma jin cewa inada cikin. Baba yace tanada ciki ko? Yacigaba da rubuta wata ta karda yana cigaba da cewa tana dauke da ciki. Abinda sakamako ya nuna kenan. Amma kuje ayimata (scan) don kusan ko wata nawa ne inna kawai na kallah wada ta kafa min idanu sun kada sunyi jajajir,Baba ya ce a"a bama bukatar sai tayi hoto,dama tabbacin cewa akwai cikin muke son sani, tunda akwai shi kenan. Ya kalli Innarmu,bana bukatar sai na sake tuna miki komai daga ke har ita. Ya fita abinshi. Inna cikin kuka ta ce, Hafsa haka zaki min? Hafsa na dace da wannan sakamakon? kin min adalci kenan? cikin kuka nima na ce kiyi hakuri Inna, wlh fyade Munnir ya min. Ta ce, karya ne, ki min shiru. Ta dubi Likitan da ya zuba musu ido,don Allah Likita ka taimake ni ka cire mata cikin nan. Da saurin Likitan ya mike tsaye cikin murya mai karfi, fita anan domin nan ba asibitin zubar da ciki ba ne. Muka fito muka nufo gida, Inna na fadin Hafsa kin cuce ni kin kuma cuci kanki. kafin mu isa gida tuni Baba yaje yayi fadan shi a tsakar gida kamar yanda ya saba, muna isowa kowa sai kallonmu yake yi. Muna shiga yazo ya ce ya va mu zuwa da safe mu fice, yanzun ma don dare ne. Mutane na ta bashi hakuri,amma ya ce to wane hakuri zai yi? Dan ya ce mata in haka ta faru a bakin aurenta, kuma ta yarda. Ranar inna kasa fadan nata tayi, duk da matan gidan da suka cika a kofar dakinmu. Ni kaina kasa min fada tayi sai kuka da take shara6awa. Mun kule can daki, can cikin sulusun dare na tashi dan bacci taya dauki Inna na fice. Bayan na kwashe duk wani abuna mai mahimmanci, Baban titi na mika ina tafiya ba tare da tsoro ba. Daf! da Asubahi naji wata mota suna cewa kano ne? na tsaida su na shiga duk da cewa ba ni da ko sisi,saboda ragowar kudina na mikawa Inna tun zuwa na, wato kudin wayata. Sai da muka dau hanya suka ce dari biyar zan ba da, bn yi mng ba, don haka sai suka zata na yarda ne. bakwai da 'yan mintuna muka isa Gyadi-Gyadi, suka ce kudina, na ce bani da kudi,don Allah su taimaka min. Nan kwandastan ya hau ni da zagi, ni dai kallon shi nake yi. Direbn ya ce, in je amma nan gaba in banda kudi in dinga magana tun kafin na hau mota, don ba kowa zai iya kyale ni ba. Na ce na gode.Sai lokacn kuma na soma tunanin ina zan je? Wata zuciyar ta ce bakina karanta littattafan su Anty Fauziya D. Sulaiman da su Anty Sadiya ba? Ai suna fadin cewa in yara sun gudu su kan je wani gidan a rike su a taimake su. To suma ai sa rike ki in kin je ki zauna da sy za su fahimce matsalarki don suna rubutu kan haka. Amma sai wata zuciyar tace, ki je gurin Likita nan, ban san lkcn da na tsaida dan mashin ba, na masa kwantace muka tafi. Ta fito kenan zata ofis sai gani, ta ce a'a Hafsa ce .da safen nan? Na ce eh, Anty ga shi ma bani da kudin da zan ba mai mashin din. Ta zuge jakarta tana cewa, nawa ne? na ce,daga Gyadi- Gyadu ne ba muyi ciniki ba, ta bashi dari biyu,naga dai ya bata canji, amma bn san ko nawa ba ne, ta ce daga ganin ki ba wata nasara amma shiga ciki. Sai da ta huta bayan ta dawo sannan na fada mata komai, tace to ke yanzun menene burinki? Na ce ni da zan samu wani dan aiki in dauki nauyin kaina ba tare da na sake neman taimakon kowane da naminji ba, zan so haka,amma da wuya tunda takardun sakandire kawai gare ni, ta ce amma bn san hikimar guje ma iyayenki da ki ka yi ba, musamman mahaifiyarki wadda ta gwada miki kauna. Da kin bita kun gudu tare ko kwa tsira tare. Na ce Aunty ina tsananin jin kunyar mahaifiyata. Ba zan iya zama da ita ba. A halin yanzun itama nasan ta dauki hanyar gidansu, da wane ido zan kalle su? Ta ce to yanzu ina son ki zauna nan mu ga yanda za"ayi. Ni da Asabe mun zama 'yan gidan Doctor Hindu, ita ke mana awo da komai, magunguna duk ita ke ba mu. Cikin haka hr muka shiga watan Haihuwarmu ko na ce haihuwar Asabe. Ta kawo min kaya jarirai yayin da Asabe aka kawo mata daga gidan su Yasir. Doctor ta ce, Kin gani kin hana mu dauki mataki da kema yanzun dole su ringa yi miki komai. Na ce, Bar su kawai Anty, Ni yanzun ba n da burin da ya wuce in haihu lafiya, ina so in tsaya da kafafuna ko Allah zai taimake ni in dawo da iyayena farin cikin su. Ina tuna kannena, musamman Ummi, Nasan Baba kishiyar Innarmu bata da mugunta, zata rike su amma nasan ba za su yafe min ba, Matsawar suka ji cewa ni ce na kashe auren uwarsu da ubansu. Doctor ta ce kada ki damu, Insha Allahu za ki dawo musu da komai. Asabe ta haihu'ya mace, kyakykyawa. Duk da 'yan gidan su Yasir da shi kan shi ba su zo ba, amma sun aiko da komai hatta ragon suna. Sannan suka ce ta sa ma 'yarta sunan da take so. Doctor ce ta bada shawar a saka sunan mahaifiya Yasir wato Maryam.A cewar Likitar, zai fi girmama yarinyar duk lkcn data koma gare su. ... A ganina matsalar Asabe mai sauki ce, don mahaifiyarta har duba ta tazo sa6anin ni da ban san halin da nike ciki ba? suma ba su san in da nike ba, Mai aikin Doctor ita ce ke mata wanka., Kwanci tashi ni ma(E .D. D) na ya cika har ya gota, amma shiru ba batun nakuda bare haihuwa, Ranar Litinin tana min gwaji ko na ce awo, ta ce yaran nan naki fa yayi girma da yawa ga shi kin kasa kwantar da hankalinki jininki kullum kara hawa ya ke yi. , Yanzun ya wuce ka'ida ina miki tsoron afkawa cikin matsala, kin kasa daukan kaddara. Kuka ya kwace min Anty zan so in mutu a gurin haihuwa nan, shi ne kawai burin zcyta. Likitar ta ce dama mun saba fada, duk lkcn d zan miki awo,mugaye fatan d ki ke yiwa knki kuwa da kina da kambun baka da yanzun kin lalace., Na ce Allah isa tsakanina da Munnir Ta ce " Ameen. Amma yanzun na fi so ki kwantar d hnklnk kin ji? Na ce to. Wasa- wasa gani na kara sati 3 ta ce in na kara kwana 3 za a yi min akin. Talata Doctor ta tafi wani taro a brnin Tarayya, ranar ce kuma na soma nakudar Haihuwa. Haka na kwna na yini, mai aiki tana kula dani, bayan magriba ta shigo fada ta hau mu da shi me yasa b muje asibiti ba? Ni kam na galabaita matuka,gado aka turo aka dauke ni, zuwa cikin asibiti, amma haka na sake kwana dole ayi min aiki. dn hk Likitar tasa a min shiri a sani a dakin tiyata.Tare da taimakon wani Likitan suka yi nasarar ciro min katon yaro namiji. Hakika na matukar shan wahala, kusan kwana 3 ban sami kaina ba., Sai a rana na 4, din ranar har na tashi an jingina min filo. Likitar ta kawo min yaron. kai na kauda domin a ganina shi ne silan raba ni da iyayena. Ban ta6a ganin fushin Likitar ba a iya zamana a gidanta sai yau. Ta ce, Dauke shi ki ciro nono ki bashi . Na fashe da kuka Anty ban yi aure ba kada ki sa in ba shi nonona su fadi, ba zan ba shi ba. Ya ya za'ayi ya raba ni da iyayena, na ci gaba da kuka, ta ce ke rike shi kafin in zabga miki mari. Shi ina ruwan shi? Shi ya samar da kan shi ko samar da shi ku ka yi? Don me za ki ga laifin shi ? Da ba ku aikata abin da ku ka aikta ba da Allah bai samar da shi cikin mahaifarki ba, ganin irin kukan da nike yi yasa ta koma lallashina, bayan na dauke shi. Babansa ya juya masa bya, kada kema ki zama kin juya masa, Kina nufin ba za ki rungumi kaddara ba? da lallashi ta shawo kaina na ciro nono yana sha ina kuka. Satina daya na gargije, muka koma gida., Ba a yanka ragon suna ba, sai dai na ce ma Anty duk sunan da ya dace ta sa mishi ta ce a sa mishi SHADDAD. sunan wai yana mata dadi. Har ta kara da cewa da Allah ya nufe ta da aure ya bata da sunan da zata sa masa kenan, don haka yaro ya ci suna Shaddad. A hankali na rinka jin kaunar yaron tana shigata, sai dai kullum kamanninshi da Munnir kara bayyana take, ban ta6a ganin da mai tsanabin kama da ubansa ba irin haka. Zuwa yanzun zcyt ta dake,watanmun 3, Wata rana Doctor Hindu ta zo mana da lbr mai dadi, wai ta samu miji, tsohon ministan ilimi na kasa. Muka yi ta murna, ita kam har da Azumi 2 don nuna godiya ga Ubangiji. Sati 4 aka sa bikinta, mu ne har Katsina gidansu. 'Yan uwanta da take bamu lbr duk mun gansu,ita ce ta dinka mana ankon dinner. Ranar daurin aure da dare aka yu dinner. Sam na kasa sakewa,saboda kallon da maza ke min, duk da yaron da ke kafadata. Ni kuwa yanzu duk namiji da zai kalle ni ko da bisa rashin sani ne ai bn da makiyi kamar su. Mun sha biki,sannan muka dawo,mun samu gidan yasha gyara,an zuba komai sabo,shi yana zaune a Abuja da Iyalansa, amma ita zata zauna a gidanta saboda aiki. Ada na cika wasa da tsokana ga son raha, amma yanzu na koma miskila,masifaffiya, mara fara'a.Bugu da kari yanzu ba ni da tsoro, musamman akan namiji. Kwanci tashi hr Asabe ta yaye 'yarta, kuma tuni an kaita gidan su Yasir. Bayan hukuma ta shiga batun don kare lafiyar yarinyar. Sannan ta samu miji a can kauyensu, mun je har can bikinta garin da aka kaita ya dan fi kauyensu zama birni. Ni kam kullum cikin yiwa Likita naci nake, ta samar min aiki ko na gida ne, ta ce an gudu ba a tsira ba, dubi abin da ya faru da Asabe sanadin aikin gida. Cikin satin da muka yi wannan maganar tazo min da lbrn cewa ta samo min aiki a wani Super market, amma da nisa tsakaninsu da unguwarmu. Zaharaddeen Shomar what's app 08168575100 Sanadin Boko 1-7 Posted by ANaM Dorayi on 12:29 PM, 12-Sep-15 Under: SANADIN BOKO Cikin satin da muka yi wannan maganar tazo min da lbrn cewa ta samo min aiki a wani Super market, amma da nisa tsakaninsu da unguwarmu.Na ce ba komai zan iya, ba d jimawa ba na yaye Shadad, na ci gaba da zuwa aikina, a wata dubu goma ake biyana. Shawara ta bani, wai in bude (account) tunda bn rasa komau ba, hatta sutura tana bani nata. Dan Adaidaita ta samo min duk wata sai dai in biya shi, sauran na kai banki, Nayi-nayi ta dinga cire wani abu a cikin albashina, amma sai ta ki ta ce ita don Allah take zaune da ni,matsala daya a gurin aikinmu ita ce manajanmu ba shi da mutunci.Farkon zuwana ya yi ta shige min shi yana sona, ganin yanda na birkice mishi sai ya sama min lfy, amma akwai zuga rashin mutunci. In minti daya ka kara bisa karfe 8, to zaya iya korarka, ban ta6a kai takwas ba tare da naje ba, sbd ina matukar son aikina. Shadad yana da hkr yana zaman shi gurin mai aiki. Cikin haka muka wayi gari cikin farin ciki, Doctor ta samu juna biyu, Mijinta mu2m mai mutunci da sanin ya kamata. Yayi murna, sai dai cikin yazo mata da matsaloli masu dama, ko dn ta manyanta ne? oho. Kwanci tashi ta shiga watan haihuwarta, mijin ya ce ta shirya su tafi Abuja ta haihu a can, wani asibiti na musamman. Sun tafi ko yaushe muna waya da ita, maganarta daya kullum ita ce mu sa ta addu'a, sannan ta ce min " Hafsa koda bn dawo ba kiyi kokari ke nemi mahaifanki tare da neman yafiyarsu. Mummunan lbrn da ba zamu ta6a mantawa da shi ba, musamman ni, shi ne na rasuwar Doctor Hindu, nayi kuka tamkar raina zai fita. Ta rasu bayan awa daya da haihuwarta, ta samu 'yan tagwaye mace d namiji, Innalillahi wa inna ilaihin raji'un, ko dangin Doctor basu kai ni jin mutuwarta ba, domin ni ita ce dangina uwata kuma ubana. Can Abuja a kayi jana'izarta, amma gidanmu ake zamn makoki, in da dangin ta da na shi suka zo. Tun kafin bakwai na soma tunanin gurin zuwa, don kan yanzun asirina ya tonu, gatana ya fadi., A zaton danginta ni 'yar aiki ce, amma dangin mijinta sun zaci ni 'yar uwarta ce, yaranta tubarkalla, lafiyyu ana ta ji da su. Ranar 7 kuwa subahanallah,tunda aka ce mu hada kayanmu za su rufe gidan hankalina ya tashi, mai aiki kuwa dama daga kauye take, bata samu matsala ba don ta riga ni tafiya. Ga shi gobe zan koma aiki hutun da gurin aikina suka bani a matsayin uwata ta rasu, kamar yanda na fada musu. Rahma ce ta fado min a rai, yarinyar da muke aiki shago daya da ita.Rahma tana da mutunci, bari in nemi taimakonta. Na kira lmbrta t daga, na ce Rahma don Allah ina nema wani agaji, ta ce na me? muryata ta sarke, Rahma ina son dakin haya a unguwarku, zan samu? Ta ce yau-yau din nan? Na ce eh, ta ce gskiya ba za a samu ba, sai dai in an bincika a hnkl. Na ce na shiga uku! Ta ce wai me yake faruwa? Na ce ba ni da gurin kwana, ta ce, gidanku fa,? Na ce ba gidanmu ba ne, kuma yau masu gidan zasu rufe gidansu, Ina da matsala. Ta ce ok, yanzun kina ina? Na ce ina gidan ina hada kayana, ta ce to za ki gane gidanmu? Na ce eh, ba Tukuntawa ba? Ta ce eh, Mama tana nan sai kiyi mata bayani kafin na dawo, na ce to na gode. Sun bani kayan sawa nata da yawa, na nemo dan tasi ya dauke ni zuwa Tukuntawa unguwar su Rahma, Mama da matar Yayan Rahma ne kadai a gidan. Muka gaisa, Mama ta ce daga ina? Sobada ganina da ta yi da kaya riki-riki na ce sunana Hafsat gurin aikinmu daya Rahma. Ta ce oho, yarinya da ku ka zo duba ni kwanaki ko? Na ce eh, ta ce ba Rahma ta ce min Mamanki ta rasu ba? Na ce eh ba Mamana ba ce, ta rike ni ne kuma yanzun 'yan uwanta sun zo zasu rufe gidan saboda ya zama na 'ya'yanta. To shi ne nake son ko zan samu dakin haya nan kusa da ku? Ta ce to za a cigita, sauke yaron ki shiga da kayan ki can dakin Rahma. Ina jin dadin zama da su Rahma don ina yin biyayya gare su, matar wan Rahma ce ka dai ke son min tambayar kurilla,tana yawan cewa to wai ina iyayenki? Ban ta6a amsamata ba, don ko Rahma bata san komai a kaina ba, bata san Matsayin Shadad a gurina ba, duk da ta cancanta in fada mata. Matsawar da nayi da son samun dakin shi yasa su Mama suka sa ne man dakin, amma d ta ce in yi zamana a nan gidan tun da ba ni da matsala, haka dana. Na ce, a'a ni dai na fi sobn na samu daki gidan mutunci gidan Hjy Iya aka samu dakin sai dai sun ce min sai nayi hakur, don tana da fada. Na ce, ba komai, in dai sai an tsokane ta ne zata yi to ba za ta ta6a yin fada da ni ba. Matsalar in da zan dinga kai yarona kafin ya isa shiga makaranta, ko da rainon kudi ne. Ta ce, ki dinga kawo shi nan

Chapter 6 of 22