Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels Sanadin Boko 1 01 Posted by ANaM Dorayi on 09:25 AM, 10-Sep-15 Under: SANADIN BOKO Na Maryam Abdullah K.Mashi Ina sauraren duk hirar da kowaccen su ke yi, motar ta kacame da surutu. Wasu na murnar ganin Iyayensu, wasu kuma suna zancen auren su. Mafi yawa daga ciki kuma suna fadin makarantun da za su ci gaba, wasu su ce poly wasu Jami'a, wasu Nursing school. Sa'adatu da ke kusa da ni ta ce, "Hafsy don Allah kema ki shigo (A.B.U Zariya) mu hadu mana." Nayi dan murmushin takaici. "Samun (A.B.U) fa ba kamar shiga Bakori ba ne, saboda in ma zan samun bani da wani tabbas akan za a barni." Ta zaro ido. "Kada kice min kina cikin wadanda za'a dakile a kai gidan miji? Na sake ajiyar zuciya. "Ke dai Sa'a taya ni da addu'a, Allah Yasa ina da rabo, dan kuwa ina son in ga karshen boko." Jamila ta dube ni, "Hafsy ko yaushe kina bani mamaki in kina cewa za ki ga karshen boko. To bari kiji, sai dai boko yaga karshen ki. Ance miki wannan lokacin yana jira ne? Na ce, "To Malama, ban saka bakin ki ba, ina ruwanki. Ke ba kince aure ba?" Jamila ta ce, "Aure kuwa insha Allahu ba ya hana karatu, zan yi aurena na ci gaba da karatuna. Sa'a ta ce, "Wahala ai daya za ki zaba, don da kin yi ciki za ki watsar da batun karatu. Na ce, "Dubu nawa akayi? Ai ni boko yanzu muka sa dan ba." Ta ce, "Shikenan, Allah Ya taimaki kowa kan niyyarshi ta aikhairi". Na ce, "Ga magana da za ki yi kawai, Amin". Da tafiya tayi tafiya, sai ka ji kowa shiru. Ni kam fargabar Babana nake yi, nasan inba wani ikon Allah ba, da wuya naje wata Makarantar. An sauke *yan zariya, sannan mu *yan Kaduna muka nausa hanya, motar makaranta da ke Bakori Katsina, ita ce ta debo mu zuwa gidajenmu, bayan mun yi bankwana da makarantar wato mun kammala. Gidanmu ya kaure da sowa, yara na ta murna "Ga Hafsat ga Hafsat". Innarmu ta fito da gudu ta rungume ni, ina ta dariya. Almajiran da suka dauko min kaya suka sauke, na ce, "Innarmu ba su hamsin". Ta kwance habar zani ta mika musu. Yaran gida suka taya ni da kaya zuwa cikin daki, matan gidanmu kowa sai sannu da zuwa suke min ina amsawa. Inna ta aje min kwano tare da cewa, "Alalar har ta huce". Ta dire min kofin ruwa na ce, "Har yanzu bata kare ba ne?" Ta ce, "Ta kare mana, ai tun kwanaki da Kawunku Bako yazo ya ce min cikin kwanakin nan za ku kammala, kullum sai na aje alalar sai dai in naga magariba tayi ne sannan in ba yara. Nayi dariya tare da cewa, "Innarmu kenan! Ina Yaya Ummar?" Ta ce, "Tun safe bai dawo ba, kin san nasai mashin da aka yi mana rabon gadon nan, Kawun ku Bako na kawo min kudin na ce a sai mishi mashin wannan yaran, tunda zaman banza yake, aikin gyaran wutar nan ba ko yaushe ake samu ba. Ina fama da kannan shi ina fama da shi. Na ce, "Kinyi dabara Innarmu, in yayi Achabar sai a rufa asiri". Ta ce "Kwarai kuwa. Ummi ta zo ta zauna kusa da ni, na ce "Ummi da ba ina ta kiranki kin ki zuwa ba? Inna ta ce, "Kullum sai ta ce Innarmu ina Auntyna?" Na rungumota a jikina ina cewa, "Gani na dawo". Ta rufe fuskarta, ita dole taji kunya. Cin alalata nake ina jin dadi ga ni ga Innata, ta ce "Kin zo a daidai bikin su Hajara da Sakina ya kusa". Na rike baki, "Inna har da Sakina?" Ta ce, "Eh! Na ce, "Uhm! Ni da so samu ne in ci gaba da karatuna ma". Innarmu ta ce, "Malam ne matsala, amma ko Nas din nan da 'ya'yan Kawunki suke yi ai zan so kiyi." Na ce, "Wane Nurse? Ni fa Jami'a nake so, burina in zama 'yar Media". Ta ce, "Me kenan? Na kafa kofin ruwa na daddaka, sannan na ajiye tare da cewa, " 'yar jarida mana! Sai dai matsalar kudi ne". Kai lomar alala da nayi baki, ta zo daidai da sallamar Baba, nan take naji wani daci tamkar na tauna madaci. Innarmu ta mishi sannu da shigowa, tare da shimfida mishi tabarma. Cikin fargaba na soma gaida shi, ga mamakina yau fuskar shi sake ya amsa, har da ce min "An dawo lafiya?" Na ce, "Lafiya lau". Innarmu ta ce, "Allah cikin ikonSa Malam yau dai su Hafsat karatun Sakandire ya kammala." Ya ce, "To dama tunda da mai sonta sai ta yi masa magana ya fito in hada su da Sakina in huta". Inna ta ce, "Anya kuwa? Ina ga daurewa da zaka sake yi ta tafi makarantar gaba da..." Wani kallo da ya mata shi ne ya dakatar da ita. Ya mike tsaye ransa a bace. "Na gaji da wasa da hankalina da ku ke yi, ba zan iya ganin Hafsa gandandan cikin gidan nan ba, duk wanda ya shigo ba zai bambance ta da matan gida ba, duk wata tana zubar da jini, ta zama Uwar mata. Wannan karon zamu yi tsiya da ku yanda bakwa zato. Wai menene cikin wannan bokon da ku ka nace mawa? Ina ce karatun gidan duniya ne?" Inna ta kufulo itama, ta ce, "To dama ka saba ka min tijara cikin gida gaban kowa akan Hafsa, tun da babu sisinka kasa ido, kuma karatu ba fashi. Ya ce, "To zan ga wanda ke auren wani, tsakanin ni da ke". Ya fita. Na dago ido da hawaye, takaicina ace kullum Iyayena basa rigima sai a kaina, bari Munnir yazo anjima, zan ce masa kawai ya turo manyansa ayi magana, ko ina dakin nasa zanyi karatuna. Ban dai fadi ma Innarmu kudurina ba. Na mike ina tattara kwanukan gabana, Inna kuma sai mita take, na ce "Innarmu ki bar batun haka, kinsan gidan nan da gulma, yanzu kowa ya baza kunnuwa yana sauraro". Ta ce, "Suyi ta sauraro din, ina ruwana. Iyaka dai mace tayi da ni naji mu kwashi 'yan kallo ni da ita". Na idar da sallar isha'i, ina zaune a gurin ina istigfari, wani yaron gidanmu yayi sallama, bai jira amsa ba ya ce "Innarsu Ummi wai ana kiran Hafsa a waje". Ta ce, "To". Na mike, nasan Munnir ne, don na aika masa da letter cewa na dawo. Na bude jakata na ciro turarena forever na fesa, sannan na sabi gyalena na fita. Tun kafin na karaso na jiyo kamshin turarensa. Yana zaune saman motarsa kirar (Toyota camry), baka wuluk, sanye yake da wando jean baki, rigarsa fara. Cikin farin ciki na isa gabansa, nayi masa sallama ya dago da kanshi daga wayar da ke hannunsa yana latsawa. "Babyna". Sunan da yake kirana kenan. Na ce, Na'am". Ya diro "Zo muje cikin mota." Na ce, "A'a mu zauna can". Na nuna mishi dakalin kofar gidanmu. Ya dan gyara tsaiwa, "Kin ce fa baki son Baba ya dinga ganina da kananan kaya, kin san dai in muna can zai ganni dole ko?" Na dan yi jim ina nazari. Hakika Baba na fada cewa Munnir ba dan mutunci ba ne, ya gane haka ne tun daga suturar da yake sakawa. Amma bana son shiga motarsa saboda ya cika son taba jikina.. Ya katsemin tunani da cewa. "Zo muje, na zo da muhimmiyar magana". Na ce masa, "Nima ina da nawa muhimmin zancen". Baya ya bude ya shiga, nima na shiga dayan gefen, sai dai ban rufe ba. Ya ce "Rufo kofar mana". Na ce, "Ka barshi haka ma ya yi. Ya kunna wutar motar, haske ya bayyana, ni da shi muka kalli juna cikin ido. Nayi saurin janye nawa idanun, domin wani abu da na ji yana bin jijiyoyin jikina. Ya ce, "Ina sonki Hafsy, ban san irin son da nake miki ba." Ya kama hannuna na kwace, tare da mai da su baya na ce, "Don Allah Munnir ka daina son taba jikina, haramunne fa". Ya ce, "Zamu fara ko? Haba Hafsy, ni ne fa zan aure ki. Ko yaushe ina son in gwada miki so sai ki yi ta ki, yaya ki ke yi tamkar wacce bata je makaranta ba? Sai ka ce ba *yar boko ba? Ni fa kullum ina fada miki ba zan auri mata muje kina min wani kunshe-kunshen jiki ba. Na bata rai, ya shafi kumatuna. "Small beby, dan yi murmushi. Ba kya yin kyau in kin daure fuska". Shikenan, ban san lokacin da murmushin ya subuce min ba, matsalar ina mutuwar son Munnir. Ya ce, "To fada min maganar kafin kiji tawa, don tawa in kinji saikin bani goron albishir. Na ce, "To ni dai dama ina son ne in ce maka ya dace yanzun muyi aure, don wallahi da kyar Baba ya bari na gama karatun nan. Sam shi ba ruwan shi da da boko, ka dai sani". Ya ce, "Haba Baby, aure fa ki ka ce? Kin manta alkawarin da muka yi ni da ke?" Na ce, "Ban manta ba". Ya ce, "To ki kyale fadan Baba kawai, ba nine ke biyan komai na karatunki ba? Come on aje wannan topic din. Na shirya miki gagarumin party ne saboda murnar gama karatunki, don haka yaushe zamu je kasuwa musai kayan sawa? Takaici ya cika ni, don haka ban tanka ba. Ya sake matsowa in banyi magana ba nasan zai iya cewa zai rungume ni. Da sauri na ce, "Duk lokacin da ka shirya". Ya ce, "Gobe yayi? Dan ranar sati ne party din." Na ce, "Um". Ya ce, "Wai ba ki murna ne angel dina? Kada ki damu, kwanan nan za ki zana (JAMB), sai kin zama *yar media insha Allah. Na dube shi, "Yanzu sai zuwa yaushe zamu yi aure?" Ya ce, "Mun kusa, ai shekara hudu ya rage min na hada master dina, before time din kin zama *yar media ko? Nayi shiru. Ya sake matsowa har muna jin numfashin juna, bakinshi daidai kunnena ya ce, "Kin san ina son aure nima tuntuni damuwa daya Dad dinmu shi ne yaki. Yayyena guda uku suna nan harda mace, kin sani dai ya ce duk sai sunyi master sun fara aiki balle ni. Na ce, "To sai yanda Innarmu ta ce". Ya ce, "Bana jin Inna, zata yarda". Ya sake yin kasa da murya "In dan yi kissing din kunnenki?" Naja baya tare da cwa, "A'a". Ya ce, "To bari na tafi". Yana magana yana kallon agogon hannunshi, "Zan kalli wasan Arsenal yau." Na ce, "Kai kam har yanzu kana nan da kallon kwallon nan." Ya ce, "Kema za ki koya in kinzo gidanmu". Nayi dan murmushi. Ina son Munnir, shi yasa zan jure na jira shi, amma Allah Ya sani ina son aure, don ina zaton ina cikin mata masu bukata.... Ya katse tunanina da cewa, "Ko kada in tafi ne?" na ce, "A'a kaje sai gobe". Ya ce, "Shikenan." Ya miko min wata farar leda. ""Gashi kisha, ice cream ne da fresh milk." Na ce na gode, amma don Allah ka daina yimin irin wannan dawainiyar. Innarmu ta dubi ledar bayan na ciro kayan ciki, ashe har da kayan tea. Ta ce, "Kai yaron nan baya gajiya da dawainiya. Ni da zai fito ayi auren nan tunda yana zon karatun kyayi can a dakin shi. "Inna nayi mishi wannan zancen ya ce min in kara hakuri." Kamar na fadawa Inna zancen party din gobe, sai na fasa don nayi imani ba zata barni ba, duk da tana son abinda nike so. Yau Baba dakinmu yake, don haka dakin Babah kishiyar Innarmu zamu kwana. Ina kwance kan yaloluwar katifata mu da Sakina, can kasa sauran kannena da aka musu shimfida. Ko wannan cakudin na daga cikin abin da yasa nake son in ganni a dakin kaina. Washe gari tun safe muka soma aikin alalar siyarwa da Innarmu ke yi. Misalin uku saura Nazifi ya shigo yana cewa, "Hafsa ga saurayinki a waje. Ko da bai ce na kira ki ba, nasan gurin ki ya zo. Dama tuni nayi wankana, ina sanye da riga da siket na atamfar (Java), gyale na sura na ce "Inna Munnir na kirana." Ta ce, "To." Na nufi waje kai tsaye. Yana sanye da kananan kaya kamar ko yaushe, ina isa ya budemin gaban motar na shiga, sannan shima ya shigo. Na gaida shi ya amsa tare da yiwa motar key, na ce, "Muyi sauri ban ce zamu fita ba." Ya ce, "To". Wani (Boutique) muka je, duk tsinannun kaya ne a gurin, shi dai ya zabi nashi, amma ni nace ban ga wanda ya yi min ba. Nan ya shiga jidar min, na bata rai tare da nuna mishi sunyi yawa. Ya ce, "To zabi wanda ki ke so." Na daga duka babu na arziki, siraran wanduna ne da *yan riguna, sai doguwar riga wadda in nasa da kyar zata wuce gwiwata. Na aje su gefe, na dube shi. "Duk ba su yi min ba". Ya bata rai sosai, "Tashi muje". Na kafa mishi ido. Ya ce, "Tashi mana". Cikin daga sauti na ce, "To, to naji zan amsa, amma ni na gane kamar zasu yimin kadan." Ya dan sassauto "Muje gidanmu ki gwada." Da sauri nace, "A'a zasu yi min." Yayi murmushi, sannan muka je ya biya muka shiga motarshi. Ya ce, "Muje mu dan sha Ice cream". Na ce, "A'a kai ni gida, Innarmu bata san na fita ba, kuma nasan zata sa a leka ni, fada kuma zata yi min". Ya ce, "To naji sarkin tsoro, ke dai kawai kina tsoro ne kada na cinye ki." Gabana yayi muguwar faduwa ganin Baba zaune a dakalin kofar gidanmu, na ce na shiga uku, ga Babana, ya ce "To menene? Ina jin mamakin ki wallahi. Shi yasa Dad din mu yake matukar burge ni, baya takura mana, shi dai in dai zamuyi karatun boko to duk abin da muka ga dama muyi. Kuma zai kashe mana the last kudin shi don muyi karatu. Na ce, "Uhm, don Allah ka tafi da kayan, na karba, amma ka fito ku gaisa. Tare muka fito daga motar, jikina har bari yake. Na nufi cikin gida, Munnir yayi gurinshi. Ina isa Inna ta ce, "Daga ina ki ke Malam ya shigo yana ta fada yaga lokacin da ki ka shiga mota? Na ce, "Um asibiti muka je dubo kanwarshi". Ta ce, "Shi ne ba za ki fada ba? Kin san fadan Malam, don Allah ki rufamin asiri kada ki ja min surutu sanadin bokon nan." Na ce, "Kiyi hakuri Inna." Ina rufe baki Babanmu yana shigowa, tun kafin ya karaso na jiyo muryarshi yana cewa. "Na fada maka kenan, in da gaske ka ke yi ka turo min manyanka. Shekara nawa ina ganinka a kofar gidan nan wai ku *yan boko, zaku ce min sai kun gama boko, to ban laminci wannan ba." Hanyar uwar daka nayi, don nasan yanzun ya make ni, ya ce "Ke *yar boko kinbi saurayi kasuwa ko? Inna ta ce, "A'a Malam asibiti fa suka je." Ya zaburo tamkar zai kai ma Inna duka, ya ce, "In ji wa? Wa ya fada miki?" Inna ta ce, "Ga ta nan." Ya ce, "Makaryaciya, to shi abokin yawon nata ya ce min daga kasuwa suke, duk ya rasa wanda zai ce ya raka shi kasuwa sai ke?" Inna ta tsare ni da ido, "Kasuwa Hafsa?" Nace, "Kuyi hakuri, ba zan kara zuwa ba." Tayi kwafa tare da ci gaba da yin aikinta. Baba ya ce "To wallahi ba zan yarda da gantali ba, wai ku *yan boko." Inna ta dube ni, "Ai gara ki saka min da haka. Tunda ni na jajirce ki samu karatun boko." Na ce, "Don Allah Innarmu kiyi hakuri, wallahi ba zan sake ba". Ta ce, "To me yasa ki ka min karya? Kin san dai na tsani a min karya, duk abin da ya faru nafi son gaskiya ko?" Na ce, "Na sani. Haka nayi ta bata hakuri, kun san Uwa, nan da nan ta sauka. Ta min fadan cewa kada na sake yarda na bi saurayi wani guri. Kwana daya, biyu ban ji daga Munnir ba, lallai Babane ya kore shi letter na rubuta na ba Nasirun gidanmu na ce ya kai masa. Tambayarshi nayi ko lafiya? Na jishi shiru. A bayan takardar ya rubuto cewa Babana ya kore shi, don haka shi ya hakura da ni. Na girgiza da jin wannan zancen, don ina son shi kullum burina na aure shi. Shi kadai nake jin sha'awa. Na rasa yanda zan yi ko satar jiki zan yi na je gidan su? Innarmu ta gane ina cikin damuwa, ta ce "Hafsat ba ki jin dadi ne? Na ce, "Ciwon kai ne yake damuna." Ta bayar da Naira goma a amsomin panadol." Da dare nace Innarmu zan je gidansu wata yarinya *yar makarantar mu, in amso wasu takarduna, ta ce, "Kar ki zauna, maimakon kije tun ido na ganin ido?" Na ce, "Ai dazun ciwon kai ke damuna." Ban yi wata kwalliya ba, kada ta gane, sai kawai na dan fesa turare. Na zari mayafi, gidan su Munnir da dan tafiya tsakanin mu saboda mu muna Rigasa ne Abuja Road ta kasa, su kuma suna Makarfi Road. Tun daga nesa na hango shi su da wani tsaye, ga motarshi gefe, ina zaton fita zasu yi. Sai na kara sauri. Daidai ya bude motar zai shiga na ce, "Munnir" Ya juyo da sauri, ya mai da motar ya rufe. Abokin nasa yana ciki, ya ce, "Beby lafiya?" Na jingina da motar, sannan na sauke ajiyar zuciya, domin na gaji. Sai dai kuma lokacin ne naga rashin hankalina. Yanzun ince mishi me? Na zo in bashi hakuri ko nazo biko? Ya sake cewa, "Me ya faru Baby? Na ce, "Ai ba ka ma sani ba?" Dabara tazo min, na ce "Dama nazo ne na maka godiya akan dawainiyar da kayi da ni, don ko zamu rabu bai dace mu rabu ba zumunci ba." Ya ce, "Baby kenan, don na fada kina ganin zan iya rabuwa daKe? Ni ina sonki, Babanku ne ya tozarta ni" Kafin nayi magana ya ce, "Ina zuwa." Ya leka motar yayi magana, sannan ya ce, "Zo muje ciki kiji." Na ce, "A'a. Ya bata rai, "Bana son yawan gaddamar nan, ki daina kada muyi aure mu zo muna samun matsala. Na ce, "Ina jin kunya ne, saboda Mamanku, Ya ce, "Ba za ta san kin shigo ba, zo muje. Na bishi, ya tura Gate din gidan, muka shiga. Yau ne na soma shiga gidansu, ginin zamani ne ga haske tamkar rana, me gadinsu ya ce, "A'a, ka fasa fita dinne? Ya ce, "A'a Baba, yanzun zan fita. Na gaida maigadin muka tafi ginin farko daga cikin gine-gine ukun da ke harabar gidan, ya ce, "Yau kin zo gidan mu, ba don kunya ba da na kira miki kannena su Nana. Na ce, "Barsu yanzun zan tafi, kuma bai dace su ganni cikin wannan yanayi ba, ina nufin shigar da nayi. Ya ce, "Shikenan. Katon falo ne, yana dauke da kayan more rayuwa, sai kofofi guda uku, yace in zauna kan kujera, na zauna. Ina kallon ko ina, ya nufi kofa daya daga cikin kofofin, jim kadan ya fito dauke da gwangwanin maltina da kofi ya zauna hannun kujerar da nike Zaharaddeen Shomar whatsapp 08168575100 Sanadin Boko 1 02 Posted by ANaM Dorayi on 09:42 AM, 10-Sep-15 Under: SANADIN BOKO Na Maryam Abdullahi K/Mashi Katon falo ne, yana dauke da kayan more rayuwa, sai kofofi guda uku, yace in zauna kan kujera, na zauna. Ina kallon ko ina, ya nufi kofa daya daga cikin kofofin, jim kadan ya fito dauke da gwangwanin maltina da kofi ya zauna hannun kujerar da nike. Ya balle hancin gwangwanin ya cika dan kofin ya mika min, na girgiza kai tare da cewa, "Na gode. Ya ce, "Wasa ki ke yarinya, rike nan ko na dura miki. Da sauri na amsa saboda nasan halin shi sarai, zai iya. Kurbata biyu na aje, ya kama hannuna na kwace tare da mikewa. "Tunda ka huce ni zan tafi. Ya ce, "Dama ni banyi fushi ba. Na kalli fuskarshi muka hada ido, ya kashemin idonshi daya, nayi saurin kauda idona saboda yarr din da tsigar jikina tayi. Na ce, "Yaushe zaka zo? Ya ce, "Zauna to mu tsara in da zamu dinga haduwa, don Babanku ya ce in manyana ba su zo ba kada ya sake ganina. Na ce, "Fada min daidai ina ne zamu dinga tsayawa? Ya dan yi shiru, "To ni bansan yaya zamu yi ba, na ce zan hada miki phone kin ce a gida ba za a barki ba, wai ke ba ki da irin 'yar dabarar ku ta mata ne? Ki saka ta a silent. Na ce, "Barta kawai. Ya dube ni, fatin kuma fa? Na marairaice murya ina kallon shi da idanuna, da na lura yana son su. Mu bar maganar party din nan, wallahi ba Babana ba har Innarmu in ta sani zan bani, ka ji. Ya tsare ni da manyan idanunsa. "Yanzun nayi asara kenan? Ya ci gaba "Ban san me yasa gidanku ake yin haka ba, ni kinga kannena su Nana da Suhaila Mom din mu da Dad din mu sune suka shirya musu party din su last week. Amma ku sai ana hana ku. Wannan duhun kai ne, yanzu fa an waye. Na ce "Ba wani duhun kai, kowa da irin tarbiyar da yake son ya yi ma 'ya'yanshi. Ya ce "Shikenan dai, mu bar maganar, naji nayi asarar kudina, kuma ba wani gida ke ce dai ba ki ga dama ba. Wani friend dina yarinyarshi itama 'yar Geto ce, amma ta jirga Iyayenta da cewa suna biki ne tazo muka yi shagali, amma ke kin kasa. Na ce, "Ni dai kayi hakuri kawai. Ya zuba min ido, sai kin yi min kiss zan hakura. Da sauri na dauki hanyar fita, sai kawai naji ya rungume ni ta baya, jikina ya dauki rawa. Cikin rawar murya na ce, "Munnir la..la....lafiyarka? Don Allah sake ni. Da kyar na kwace, kamanninshi sun canza, da sassarfa na fito na dau hanya. Ya biyo ni da mota shi da abokinshi, wai na shiga su kaini gida, na ce, "A'a don na tsorata, dole suka bar ni. Da na zo barci na jima ina tuno abin da Munir ya min, dama an ce mace da namiji in suka kebe na ukun shaidan ne. Ba don son da nake yiwa Munir ba, da tuni na bar shi. Mun canza gurin hira, bayan layinmu yake tsayawa. Na fada ma Innarmu ta ce saboda me? Na ce, Baba ya hana shi zuwa nan. Inna ta ce, "Mallam ho! Shikenan, ki dinga zuwa da Ummi kin san mutane da sa ido, yanzun sai ace wani abin ne yasa ku ke zuwa can. Fatana ki kama kanki. Na ce, "To, nima zuwa da Ummi zai fi min, duk da Munir ganin Ummi bai hana shi son taba jikina ba. Cikin haka muka soma shirin zana (JAMB), Baba bai sani ba, Munir ne ya sai min form, sai dai tsorona daya randa Baba zai sani. Na zama cikin sa'a kamar ko yaushe, Munir ya tsaya tsayin daka har na samu gurbin karatu a (B.U.K) Kano, sai dai ya zamuyi da Baba? Haka na ce ma Innarmu, ta ce yau na yanke shawarar sanar da shi komai, tunda gobe za ku je yin rijista. Kusan goman dare, lokacin ina kwance muryar Innarmu nake ji tar daga dakin Baba, domin bangonsu daya. Tana sanar da Babanmu komai. Bai katse ta ba har ta kai karshe, ya ce, "To bokon nan ba da yawuna ba, bayan shekara shidan da na hakura tayi yanzu kuma wata zata? Wai lahira take so ko duniya? Inna ta ce, "Duka. Ya ce, "Karya ne, duniya ku ke nema, kuma

Chapter 1 of 22