a duk sanda suke tare.. ..
"Ni ka yiwa gargadi sai gashi kai ne ka aikata hakan, jin haka yasa Jaguwa mikewa ya sauko yana gyara zaman gajeren wandonsa dinsa daya dan zamo daga kugunsa ya nufi kofar fita "bai dace ba gaskiya ,abinda mukeyi ne fa kana mana faɗa me yasa zaka yi ...?saurin dakatar dashi yayi "ni din ma ba da wata manufa na d'aukota ba ,na d'aukota ne da niyyar azabtar daita, na gana mata azaba na nuna mata kuskurenta akan abinda ta min sai....
Yayi shiru ya kasa karasa maganar "sai kuma ka bige da .......
dakata dan Allah malam ni babu abinda nayi daita "to me amfanin rike musu yarinya da kayi ? "Ka ....
kit ya katse kiran yana dafe goshinsa tare da rike kugunsa da daya hannunsa wani kiran ne ya shigo ya sake katsewa ya kashe wayar gaba-daya ya koma d'akin yana Kallonta idanunta a lumshe alamun tana jin bacci rabawa yayi jikinta ya kwanta tare da matseta ganin haka yasanya shi gaggawar birkitota suka fuskanci juna eye's dinsu suka haɗu zuciyarsu yayi mummunar bugawa a tare laulausan tafin hannunsa taji yana yawo ajikinta tun tana jin abinda yake har bacci yayi nasarar d'aukarta amman stil tana jinsa , gabad'aya ya gigice irin gigicewar da bai taba yi akan kowace mace ba, duk tunaninsa ya kau burinsa kawai ya samu biyan bukata sai dai bazai iya aikata komai daita ba.......
sama da awa biyu ya ɗauka yana romacing din jikinta daren da yake jin kasancewarsa na musamman gareshi dan kuwa ji yake tamkar yana tare da matarsa ce ina ma zai iya daya yaki zuciyarsa ya aureta kamar yadda ta bukata dan yasan zai samu dukkanin wani kulawa daga gareta ,zata shayar dashi soyayya ,a hankali har ya samu natsuwa ya kwantar daita a saman faffadan kirjinsa yana sauke numfashi ...
hannunsa ya daura saman gashinta yana shafawa zuwa gadon bayanta haɗe da kissing foring head d'inta "acikin zuciyar tanweer kuwa addu'a take da Allah ya tsaida shi iya haka batare da ya kusanceta ba , Allah kasa wannan bawa naka ya aureni dan zan sha soyayya shi din na daban ne i love you adnan ta furta haka acikin ranta , rufe musu jiki yayi yana sake lumshe kyawawan idanunshi har bacci yayi nasarar daukarsa.....
*****
A hankali ya bude kyawawan idanunshi ya daura akan ƙaramin agogon dake ajiye akan abun gado, karfe takwas ya gani har ta wuce da wasu yan mintuna tsaki yaja saboda ya makara idan akwai abinda ya tsana bai wuce makara gurin sallah ba , ya kwantar daita tare da lullu'beta da bargo ya mirgina ya sauko ya janyo towel ya d'aura ajikinsa cike da natsuwa ya shiga bathorrom , bathtube ya shiga ya tsaya ya soma sakarwa jikinsa ruwa, wankar tsarki yayi tukuna domin tsaftace jikinsa sannan yayi wanka soso da sabulu bai dade ba ya fito yana goge jikinsa yana kallon fuskarta da gashin kanta mai tsantse da sheki komai nata mai kyau ya furta hakan a kasan ranshi ..
Jallabiya ya ciro wani design din yasa ya karasa kibabben gurin sallarsa ya soma gabatar da sallah gabansa na faduwa , yana matukar fargaba da tsoron mahalincisa a duk sanda zai yi sallah sai yaji gaba-daya komai ya kwance masa ,yasan abinda yake aikatawa bai da kyau har yana jin tamkar ibadar da yake ma ba'a amsa ,yayinda take zuciyarsa ta kawar masa da wasi wasin data shiga ya dinga yi mata naci da karfafa gwiwar da ana amsa har ya idar zuciyarsa rawa take ya mike ya dawo inda take kwance tana sauke numfashi hannuwansa duka ya kai jikinta ya d'agota ta zube jikinsa ta lafe tare da turo masa karamin bakinta gaba , bakinsa ya kai cikin kunneta "ki tashi kiyi sallah lokaci ya tafi mika tayi ajikinsa wanda ya haddasa masa jin wani irin shock , "uhm zanyi zuwa anjima bacci nake ji jikina duk ciwo yake min ,gefen kunneta ya ciza da dan karfi ta saki qara tana sake shigewa jikinsa "dole ki tashi kiyi sallah me kika yi da kika gaji ya k'arasa maganar yana busa mata iskan bakinsa take tsigar jikinta suka mike sake turo masa bakinta tayi tana kokarin buɗe bakinta taji yayi sama daita ya shige bathorrom daita ya sakata a bathtube "ba'a lattin sallah a gidana oya kiyi alwala ya juya ya koma d'aki bayan kamar minti uku ya dawo hannunsa rike da jallabiya ya ajiye mata ya sake fita ..
Jiki a mace ta fito tana kallon inda yake zaune rigingine da gado ta isa inda taga dadduma ta tada sallah bayan ta idar ta koma dayan bangaren da yake ta zauna "good morning ?"morning ya faɗa atakaice batare daya kalleta ba "ya kamata na koma gida ina so..
"zaki tafi nan da wasu awani dan zamanki bashi da wani amfani , ya fada yana mik'ewa akan katifa bata sake cewa komai ba ta zame ta kwanta tana runtse idanunta "komai cikin gadara da isa da nuna rashin kulawa ta fadi haka a kasan ranta .......
ya mike ya fita daga dakin zuwa wani dakin , yayi shirin fita operation dinsa tsaf ya shirya cikin bakaken kaya riga da wonda na suit ya ɗauki bindigarsa pistor guda har guda biyu ya soke ajikinsa yabi jikinsa da turare mai sanyi kamshi sannan ya fito zuwa babban parlou'n gidan yana d'aura agogo a tsintsiyar hannunsa turus yayi ganin jabir kamil jubi da Anas zaune suna tautaunawa akansa ganinsa yasa suka mike suna kallonsa , kallonsu shima yayi daya bayan daya yana tabe baki sannan yace "ku kuma fa ? "a tare suka bude baki mun zo ne akan wannan fitartaka bama son ka fita aikin nan dan Allah ka hakura ,"me yasa bakwa gajiya da magana ɗaya nifa wannan ba sabon abu bane agurina,",Koda yaushe kana jayayya damu akan ra'ayinka amman akan wannan dole mu fi karfin ka "karfin wa ? ya furta yana musu wani irin kallon kasan ido
"Duk ma abinda zakuce kuce but I must face tanko gote zasu sake magana ya dakatarsu har zai fita yaji jikinsa yayi masa wani iri a hankali ya juya ya koma ciki ,kai tsaye d'akin da tanweer take ya shiga ya hawo har saman gado ya shige jikinta yana kissing din bayan wuyanta jinta yake kamar matarsa ya zira harshensa cikin kunneta sannan ya kamo hannunta cikin nashi "zani wani aiki mai mahimmanci da zarar na dawo zan kai ki gidanku ajiyar zuciya ta sauke tana juyo ta zuba masa ido batare da tace komai ba shima bai sake furta komai ba wani iri suka ji ajikinsu a lokacin da kwayar idanunsu suka tsarke cikin juna ,bai sake cewa komai ba ya fice tabi bayansa da kallo kamar ta hanashi fitar duk da batasan inda zashi ba , har lokacin su Anas suna tsaye ya nufi haraban gidan suka biyo bayansa suna masa magana amman ko tari bai yi bare su saka rai zai amsa musu , kai tsaye dakin ajiye makamansa ya nufa ya dibi harsashi da kudi masu yawa ya ɗauki keyn motarsa city ya fito still suna biye dashi ya karasa inda aka tanada domin ajiye motocinsa ya danna key din hannunsa ya bude kofa mazaunin direba ya shiga ya tayar mai gadi na ganin hancin motarsa ya bude masa, ya cilla motarsa waje .
mutanen dake tsaye jiran fitowarsa suka mike tsaye ,kamar ba zai tsaya ba sai kuma ya tsaya batare daya kashe motar ba ,yayi warning glass din motar ya ciro bandir din kudi yan dubu day day ya soma raba musu kamar yadda ya saba suka dinga amsa suna zuba masa ruwan addu'a da samun nasara yana kada kai ,sai daya sallamesu sannan ya dauki hanyar zuwa donping estate ..
"Taurin kai taurin kai mutun kamar mutanen farko duk abinda kaji ance ka barshi barinsa shine alkhairi duk kuma abinda zaka samu a duniya zaka bar shi jubi ya faɗa cike da taikaici da bakinciki taurin kan Jaguwa "wayyohlly Allah wallahi har na fara tausayawa yan'uwansa da halin da zasu shiga idan wani abu ya faru dashi kamil ya fada yana marairaice fuska , jabir yace " wallahi tunda ya soma shirin aikin nan naji ajikina babu nasara "muyi masa addu'a kawai Allah ya dawo dashi lafiya domin shine karfin gwiwarmu bamu taba samun saɓanin ra'ayi ba sai a wannan lokacin inji cewar anas daya fi kowa shiga damuwa " ameen suka had'a baki gurin fadar haka..
A hankali yake murza stearing yana tunanin yadda abubuwan zasu kasance gaba-daya ya gama tsara komai da yadda zai shiga ya fito har ya dauki titin da zai kai shi estate din ya karaso bakin get din estate din yayi parking ya ɗan dade sannan ya fito daga cikin motarsa yana gyara zaman suit d'insa kai tsaye gurin securitys din bakin get ya nufa suka gaisa a mutunce bazakace masa dan fashi ba bayan sun gaisa yace "ina son ganin Alhaji tanko gote ..
Daya daga cikin securitys ya leko daga cikin wani karamin daki yana dubansa ganinsa cikin shiga ta kamala ya koma ya zauna dayan yace "me ye sunanka na duba ko kana cikin list din masu son ganinsa ? Shiru yayi ya kasa magana yana ciza lip's d'insa na kasa security ya sake kallonsa yana tambayarsa "uhm don't worry bari na kirasa "better dan ba'a bawa Kowa damar shiga sai da izininsa wayarsa ya ciro kamar zai yi kira ya koma cikin motarsa ya zauna yana tunanin yadda zai shiga cikin sauki .
" Anas........"
jabir ya kira sunansa yana zama a gefensa "na'am jabir Anas ya amsa jiki a sanyaye" everything will be fine naga duk ka damu tunda jaguwa ya bar gidan nan "dole na damu jabir ina jinsa tamkar danuwana bana son wani abu ya sameshi bana son na rasashi yayi mgnr kamar zai zubar da kwalla "jaguwa ba kamar sauran mutane bane , gabad'aya alamuransa akwai lisssfi ,yana da kaifin kwakwaluwa bazai bari mu rasa shi ba saboda yasan muna son shi "jabir nasan da haka nasan yana son mu duk duniya bashi da aminan da suka kai mu but bansan me yasa yayi irin wannan taurin kan ba ,nayi kokari fahimtar dashi nayi komai akan ya bar wannan aikin amman yaki ya kasa fahimtata jabir zuciyata na cike da tsoro yanzu idan wani abu ya sameshi adalilin tango gote ya zanyi da rayuwata ? "Anas kana tsoro da tausayinsa with reason nima zuciyata tana cikin damuwa amman abinda na lura dashi yana sane so yake mu rasa shi inji cewar kamil wallahi idan wani abu ya sameshi bazan taba yafe masa ba yayi maganar yana goge hawaye "ba haka bane kamil Anas ya fada shima hawaye ne cike da idanunshi "zai dawo zai dawo anas ya dinga maimaitawa zai dawo da kafafunsa domin shi din ba mutun bane kamar sauran mutane mutun ne mai matukar amfani ga rayuwar mutane yayi handling din matsaloli a rayuwar data gabata ina da tabbacin zai dawo da kafafunsa suka rungume juna suna kuka ..
****
Alhaji tanko gote zaune a cikin tangamemen parlou'n sa daya ji kayan more rayuwar duniya tare da manya abokansa kowane hannunsa rike da glass cup suna kurban ruwan win yayinda gabansu table ne dake dauke da kayan itatuwa kala dabam dabam,tun daga kan ginin gidan da tsarin da'aka bi dashi za ka san mamalakin gidan attajirin ne,gidan zagaye yaje da flowers sannan yafi Kowane gida dake cikin estate din kyau da tsaruwa .
shewa ne ke tashi acikin parlou'n "mutunen da zasu ce meye namu acikin lamuran kasar nan ina tunanin mutanen sun tabbata dakikai ne , domin daga kasar nan tamu har zuwa kashen ketari sunanmu ya zagaya sannan a san da zamanmu, maga Wanda ya isa yace meye namu acikin lamarin kasar nan bayan mune gwanati "wannan haka ne inji cewar Alhaji amadu dan iya wanda ke fuskantar alhj tanko gote "muna da tarin kudi muna da tarin mutane muna da hanyoyi daban daban akwai connection me muke so acikin kasar nan da bamu samu ba da har wasu zasu dinga cewa meye namu aciki ? "babu ma wanda ya isa domin mune gwanati kuma ko ana so ko ba'a so dole a dama damu kuma muyi abinda muke so "wannan gaskiya ne ...
"waɗan kananun maganganun yasa nake gudun shiga siyasa Gara na tsaya iya haka tunda duk abinda nake nema ina samu sannan ina juya waɗan da nake so na bada umarni kuma abi inji cewar Alh Tanko gote suna cikin hirar wayar Alhaji tanko gote ya ɗauki kara ya mike sanye da bakin kaya wando da riga da hula ya ɗauki glass cup ya dauki wayarsa ya miko dogon coridor din gidansa sannan ya ɗauki wayar ya soma magana kasa kasa "ranka ya dade aka fada daga dayan bangaren na turo da kudaden yanzu haka yarona na bakin get din estste " oooooo my god me yasa baka da fahimta ni da nace a wuce akai kudi banki shine zaka turo min yaro madadin ma ka kirani na turo body guad "am sorry sir gani nayi idan na turo kudin zaka fi maida hankali "haka ne kana da fahimta dan a daidai wannan lokacin ina tare da shi wanda zai saka hannu "to kagani sai ka bashi ayi agama komai dan so nake ya fito zuwa jibi dan Allah kasa a kashe wani a madadin falsa .." shikenan a gama karkaji komai " zan bada umarnin a shigo da yaron yanzu ya fada yana canza magana "you have to understand that you should know that what someone like us can do in this land be left ,ya maida wayar zuwa dayan kunnenshi tare da shiga karamin parlou'nsa ya bude window dining area "nasani ranka ya dade nasan zaka iya komai murmushi tanko gote yayi" ka kwantar da hankalinka komai zai tafi daidai cikin haka amaryarsa ta shigo tana taku day day ta nufi inda yake tsaye ta rike hannun daya daga cikin kujerun dake zagaye da dining yana ganinta yayi saurin "cewa I will call you later uhm alright "my dear ta matso jikinsa ya cire wayar a kunneshi yana rungumota jikinsa ya manna mata kiss tayi murmushi "darling har na fara kewarka da tunanin tsawon lokacin da zaka ɗauka idan ka tafi hong Kong dan Allah kar ka dade kamar sauran lokuta karka ɗauki lokaci mai tsawo bana son ka dade ka dawo da wuri duk yau sati ne fa da dawowarka "uhmmm gaskiya ne amman this time a round just 1 month zanyi na dawo nayi wata uku ban fita kowace kasa ba "really ? ya gyada mata kai "idan zan dawo zan biya ta itly "kai dan Allah tayi maganar a shagwa'be "dole na biya dan akwai abinda zai kai ni daga nan naga bilal ta soma tafiya tana farinciki yana biye daita abaya suka zauna akan farar kujera mai zaman mutun biyu har zai ajiye wayarsa ya tuna bai kira securitys ba ya soma ƙoƙarin kiransu kira ɗaya suka ɗauka "hello sir daga ɓangaren Tanko gote yayi shiru yana tsotsa keya yana ciza baki saboda bai tambayi sunan yaron da aka aiko gurinss ba iska ya furzar yaceb"akwai wani yaro yana ....
"Okay sir gashi nan ma "yauwa ku barshi ya shigo "okay sir ya katse kiran tare da janyo amaryarsa jikinsa ",zanyi missing din waɗan abubuwan ya kai hannu ya shafo qirjinta bata yi sanya a gwiwa ba ta kai hannunta ta soma wasa da sansar jikinsa kusan minti goma suna rungume da juna wayarsa ta sake ɗauka qara ya zareta ajikinsa yana ƙoƙarin d'aga wayar gabansa yayi wani irin muguwar faduwa yayi shiru rike da wayar ya kasa ɗauka babu abinda yake ji sai faduwar gaba.
Saurin mik'ewa yayi yana kallon parlou'n kansa na juyawa a matukar zabure amaryarsa ta mike "what happened ? "gabana ke fad'uwa da matsanancin karfi "gabanka ke faduwa ta maimaita tana kallonsa" ina jin kamar takun mutane "how is there tayi maganar tana kallon kofar parlou'n tayi maganar a tsorace ganin haka yasa ya riko hannunta "colm down never mind "what do You mean never mind ? tayi maganar a tsorace "don't leave the parlou "ban fahimceka ba ? " Ina zuwa yayi foring head d'inta kiss "i think I will back don't leave the parlou ya juya ta riko hannunsa da sauri "karki damu zan dawo yanzu ya sake rungumeta ya mannata mata kiss ita dai a sanyaye ta bishi da kallo "meke faruwa ne haka daga gabansa na faduwa yace na tsaya anan na jirasa zai dawo tafiya yake gabansa na faduwa ya biyo dogon coridor da zai kai mutun wata kofa data fuskanci hagu ya fito a hankali yana dube dube har inda wata motar take parke yana dubawa gabansa na faduwa wanda duk sanda yaji haka yasan akwai wani mummunar abu da zai samesa cigaba da dube dube yayi a hankali ya juyo yabi wani hanya stil bai ga kowa ba bai ga komai ba, ya tsaya yana waige waige hagu da dama sannan ya sake juyawa ya nufi kofar daya biyo "Alhaji tanko gote.........."
yaji sauti daga bayansa cak ya tsaya tare da juyowa gabansa na wani irin dokawa a hankali Jaguwa yake daga kafafunsa "waye kai ? tambaya kake ko neman sani ? "duka ya fada cike da tsoro , jaguwa yayi murmushin "colm don Tanko gote zaka san komai cikin second daya yayi mgnr haɗe da ciro bindigarsa daga maajinta ya soma gyarawa yana kusanto inda tanko gote yake tsaye a matukar tsorace yake kallonsa da bindigar hannunsa alama su shiga ciki yayi masa babu mutsu ya juya Jaguwa na biye dashi har suka shiga parlou'nsa na uku ya tsaya " ba wani abu ne ya kawoka ba illa kudin da'aka ...
"Dakata kafin wannan kamar baka ganeni ba ?ya girgiza masa kai "Jaguwa yayi murmushin "daman mutane irinka basa iya gane mutane abinda yafi haka ma zaka iya saboda mutun azzalumi irinka ba lallai ne ya zamanto mara mantuwa ba well ba wannan ne abinda ya kawoni ba shiga ka fito dan zuwa yanzu ka fahimceni "sosai ai idan kudi ne zaka samu har sai kabari ni Dai ka barni da Raina da lafiyata "ban soma wannan aikin dan na dauki ran wani ba sai dai a rashin sani amman kai wallahi zan iya daukar naka take jikin Tanko gote ya sake ɗaukar rawa ....
" muje inda kudin suke jikinsa na rawa ya nufi wani daki suna shiga sanyi ac ya ratsasu buhu ne cike da kudade daban daban na kasar negeria da kasashen ke tare ka ɗauki duk wanda yayi maka "Jaguwa yayi murmushin yana shafa qirjinshi da hannu "ai gaba-daya zan wuce dasu dan haka ka soma ɗauka daya bayan daya "ka bari na bada umarni a kai maka su cikin motarka tana ina "ance maka ni karamin kwaro ne karka bata min lokaci ka soma abinda ya kamata kafin na fasa maka kwakwaluwa .....
Darling's
💗💗💗💗💗💗
KUSKUREN BAYA
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
WRITING BY
*BAGUDO& MIMI'S QUEEN*
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
https://my.w.tt/lcJskJdtpbb
🅿️09
.....Mamakin jin furucin Jaguwa na karshe ya cika zuciyar Alh tanko gote mutumin daya shahara a cikin fadin duniya da aikata masha'a bangaren neman mata cin amana ,makirci, son abun duniya ba dan bashi dashi ba ,daurawa mara laifi laifi domin bawa mai laifi gsky saboda abun duniya ,idan kana son ka kasance dan ta'adda mai lasisi da neman gindin zama acikin kasar nan nemi tanko gote,idan aikinka garkuwa da mutane ne fayde zama dilan kwaya da sauransu nemi tanko gote duk zai tsaya maka asirce kaci karen babu babbaka ko an kamaka zai sa a sakoka cikin kankanin lokaci .............
Duk wannan mugun aikin daya ɗauki tsawon shekaru yana aikatawa adalilin connection din da yake da acikin yan siyasa babu wani mutun ko ɗan fashin da makamin daya taɓa kawowa rayuwarsa farmaki ,
hasalima yana jin sign dinsu ajikinsa kafin su karaso gareshi yake maganinsu , sai gashi yau da ranar Allah dan fashi kwaya daya tal ya farmaki rayuwarsa har yana masa barazana da rayuwarsa , jiki a matukar sanyaye ya soma jan buhun kudi jaguwa na gefensa "idan kayi wata alama da wani zai gane halin da ake ciki wallahi zan ɗauke numfashinka daga doron kasa sai dai nima a ɗauke nawa numfashin wanda daman ni da wannan shirin na fito mutuwa ko akasin haka ..... "
"Karka damu babu wanda zai fahimci komai ya fada hannusa na karkarwa, kai tsaye bayan but din motar Jaguwa suka nufa ya jefa buhun kudin da kyar yana haki , haka suka dinga jerewa suna shiga yana dauko buhun kudi har ya kwashe tasssss ya tsaya tare da nad'e hannunwansa guri daya har lokacin zuciyarsa cike take da mamakin irin gogewa da kwarewar jaguwa .
Jaguwa ya manna gun a gefen brain d'insa "muje ka kaini gurin yar gaban goshinka Alh tanko gote ya kalleshi a matukar frigice zuciyarsa na dokawa da karfi "karka taɓa lafiyar iyalina idan wadan nan kudin basu isheka ba zansa akawo ninkisu yanzu
" yayi kyau shugaban fataken dare sai dai kar kwakwaluwarka tayi maka wanann banzan tunani dan nasan daraja da kimar dan adam ba irinka ba wanɗa yake danne hakin dan Adam domin son duniya , a hankali ya dinga daga kafafunsa zufa na karyo masa a gaba-daya sansar jikinsa yana tunanin "waye shi wannan ? "da dukkanin alamun yasan shi farin sani har suka shigo parlou'n zuciyarsa na cikin frigici , yayinda har zuwa wannan lokacin amaryarsa na tsaye hankalinta a matukar tashe tana ganin bindiga a gefen brain din mijinta tayi saurin durkushewa bisa gwiwowinta tana furta "na shiga uku me zan gani haka ni salma ? Alama jaguwa yayi mata da bindiga take tayi shiru jikinta ya kama kyarma ..
"kin san me yasa na bukaci wannan azalumin mijin naki ya kawoni gareki ban bukaci ya kai ni gungu mattarar tsiya ba ? tayi saurin girgiza masa kanta jikinta na rawa "saboda nasan kece tauraruwar gidansa da dokarki ake aiwatar da komai na gidan nan , sai yadda kika so za'a yi dan tanko gote mijin tace ne agurinki sai yadda kikayi dashi "ki faɗa masa kar ya kuskura ya kawo wa aikina hauka , bayan wannan ya kamata ki san ko waye wanda ke tsaye a gabanki duk da idanunki a halin yanzu a makance suke ,"sunana jaguwa akaro na farko da wani a duniya zai san wani abu daya danganceni sannan ya san sunan dan fashin daya gagarin kasa da yan sanda "
" a wasu shekaru da suka gabata anyi wani natsatsen yaro wanda ya taso cikin gata da kulawa, yana da mahaifi da mahaifiya da kane gudu hudu namiji daya mata uku , wahalar duniya tayi musu yawa naci ma da kyar suke samu sai da wannan azzalumin mijin naki yayi nasarar jefa rayuwarsa cikin gararin rayuwar da yasa ya dawo wannan mutumin dake tsaye agabanki , jaguwa ya sake tsuke muryarsa ya cigaba da magana "abinda yasa na dan baki labari ,mijinki ya cancaci na kashe shi bisa girman laifin da yayi min a shekarun da suka gabata sai dai na barshi da halinsa dan hukuncin Allah zai fi akan nawa hukunci ,sai abu na gaba " idan mijinki yayi kuskuren ko gigin sako jami'an tsaro ciki aikina domin yunkurin tona min asiri ko bincike akaina zan.....
da sauri tace" he wont involved the police farinciki ya ziyarci zuciyar jaguwa saboda ya hango firgici da matsanancin tsoro attare daita, yana gama jin abinda tace yace "shiga muje kou " Alh tanko gote yayi saurin waigowa gefensa inda Jaguwa ke tsaye fuskarsa da alamun tambaya "karka ɗauka bansan abinda nake ba ,nasan halin mutane azzalumai irinku masu bin mutane da bita da kulli ka shiga muje kawai ban gama da kai ba idan kuma mutsu zaka min yanzu na harbeka na harbe kaina muyi mutuwar kasko ,babu mutsu ya shiga gaba jaguwa na biye dashi har cikin mota ,Jaguwa ya zagaya ya shiga bangaren direba ya tayar ya nufi get ....
Suna karasowa bakin get securities suka tsaida shi warning glass din bangaren Alh tanko gote yayi suna ganinsa suka shiga rigerigen kawo gaisuwa cike da girmamawa, daya daga cikinsu ya bude tafkeken get din estate din jaguwa ya
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 7 Chapter of 62