fad'a kenan ya cigaba da tafiya bai tsaya akoina ba sai a d'akinsa ya zaunar daita tana wani irin kuka me ta'ba zuciya ."
camerar part dinsa ya kunna yayi rewarning d'aga Inda ta shigo masa ya juyo da tv Inda take "ki bud'e idanunki da kyau ki Kalli komai daya faru "shiru tayi tare da tsaida kukanta shi kuma ya koma jikin bangon d'akin ya tsaya rungume da hannunwansa duka a saman faffadan qirjinsa sai dai gbdy hankalinsa da Idanunsa sun tattara ne akanta .
a hankali ta fara ganin komai tun daga shigowarta d'akin da yadda ta kunna wutar d'akin ta Isa Inda yake kwance tana shafa jijiyarsa har zuwa sanda ta d'auki bindigarsa da yadda ya amince mata ya kusanceta suman zaune tayi agurin , lokacin data ga yadda ya dinga sarrafa dukiyar fulaninta da yadda ya dinga tumurmusanta bata san sanda ta zamo kasa a gigice ba tana furta kalmar "inna lillahi wa inna ilaihi rajiun " me ya sameni haka ?"me ya shiga cikin tunanina ?"wallahi ban san na aikata haka ba, bansan abinda ya sameni ba "inna lillahi na shiga uku shikenan na rasa budurcina ?" wayyo Allah ni surayya ka kuwa san maseefar da ka jefani aciki ? me yasa kayi sex dani ? "yanzu me kake son nacewa mijin da zan aura ?hawayen ya zubo mata sharr ... akan quncinta take Kuma jikinta ya kama rawa "gbdy zuciyarta ta sake karyewa "me yasa baka dawo dani haiyaci ba a lokacin ?"wallahi bansan na aikata hakan ba Shima jikinsa rawa yake tausayinta ya kamashi gbdy ya manta wancan tashin hankali da dcp ya jefashi ciki ya matsota sosai yana me jimamin da nadamar abinda ya faru."
kusancin dake tsakaninsu yasa ta jiyo yadda qirjinsa ke bugawa da karfin gaske "dan Allah kiyi hakuri nasan bakya cikin haiyacinki lokacin da abun ya faru nayi k'okarin kar hakan ya faru a tsakaninmu amman saboda bakya cikin hayacinki burinki na kusanceki alokacin shiyasa nayi .
"me Ka bani wanda ya gusar min da hankalina ? girgiza mata Kai yayi alamun "Babu " Karya ne ka bani wani mugun abu idan ba haka banga dalilin da zai sa na kawo maka kaina ba kayi yadda kaga dama ba ta k'arasa maganar tare da fixgo numfashi da karfi ta fesar kmr me cutar asthma tayi shiru hawaye na xubo mata "kenan shiyasa a wacan ranar yayita matsa mata lallai sai tayi wankan tsarki ? ashe yasan mugun Abu da yayi mata ta zabura zata mike ya rikota gam ya makaleta ajikinsa yana shafa kanta zuwa bayanta yana jin kmr ya mutu , yana son ya fad'a mata cewar asiri akayi mata a waccen ranar yasa komai ya faru yana jin tsoron wani sabon tashin hankalin da za'a yi idan tasan da hakan.
"kiyi hakuri da abinda nayi miki nayi k'okarin gujewa hakan nasan illar abinda nayi miki tunda an ta'ba yiwa yar'uwarta
a lokacin ji nayi kamar na mutu duk yadda mutane ke bani hakuri akan nayi hakuri kasawa nayi har sai dana d'auki fansa da hannuna sannan ruhina ya samu salama " iya radadi naji a wannan lokacin ,qunar abinda na miki ya tsaya min a zuciya kullum dashi nake kwana nake tashi na zubar da hawaye sosai naji kamar na kashe kaina a ranar ,ki ya femin tanweer domin kece mace ta farko dana amshi budurcinta , bana sonki amman budurcinki shine abinda yafi komai tsaya min arai har na mutu bazan manta cewar ni ne mutumin dana amshi budurcin tanweer ba, kuma bazan daina ganin kima da martabarki ba ."
"Zaka cigaba da ganin kima da martabata ? ya gyada mata kanshi "amman kace bani da tarbiya ? shiru yayi kawai dan rasa abinda zai fada mata "haka kayita maimaitawa abokinka cewar ni mara tarbiya ce kuma nasan shima zai tsaya maka arai baza ka ta'ba ganina da wannan darajar ba ? " no karki ce haka ,kiyi hakuri da furucina na d'azu am really sorry bazan sake ba ya rike kunnuwansa da hannunwansa , "babu ruwana da nadamarka ka biyani budurcina kawai dan wallahi bazan yarda ya tafi a banza ba".
shiru yayi yana kallonta maganarta tayi matukar bashi dariya amman ya hadiye ,
yarinyata ne zalla atattare daita bancin haka taya zai biyata budurcinta daya amsa ?
Numfashi ya fesar kafin a hankali ya mike ya Isa gaban wani katon akwatin me ratsin baki da ja ya janyo akwatin zuwa gabanta ya bud'e dalolin kudin american ne cike dashi "bani da abinda zan biyaki dashi sai dai ..... "dakata ai kasan ni ba bakuwarsu bace dan zan iya baka ninkinsu abinda nafi bukata ka dawo min da budurcina na koma yadda nake Kuma a yanzu ".
tsura mata tsumammun idanunshi yayi kawai yana kallon karamin bakinta ,ya furzar da numfashi wanda hucinsa ya doki fuskarta ,a natse ya d'auke idanunshi akanta zuciyarsa na tafarfasa "yau tazo masa da abubuwa a cukurkud'e "Ina dcp ya samu numbersa da har ya kirasa yana masa barazana ? sannan da wannan tashin hankalin da furucin bakinsa yayi nasarar jefashi ciki ,taku biyu yayi ya tsaya jikin window d'akin tare da juya mata baya ,bayansa tabi da kallo batare tace uffan ba illa sheshekar kukan da take zuciyarta na hasko mata yadda ya dinga juyata .
A natse ta soma jiyo sautin muryarsa na shiga kunnuwanta "ki shirya gobe zan mayar dake gidanku nasan zakiyi farinciki da jin hakan sannan dashi kawai zan iya biyanki budurcinki dana amsa ya k'arasa maganar tare da juyo ya kafeta da Idanunshi yana ciza lip's dinsa na kasa da karfi ".
Wani sanyayyayen farinciki ne ya lullu'beta alokacin d'aya , duk cikin kalamansa babu wanda yayi mata dadi ya sanyaya zuciyarta kamar wannan "zani gida kace ?ta fad'a tana tsareshi da idanunta ya gyada mata Kai alamun "eh! gbdy taji raunin da yayiwa zuciyarta ya Kau hawaye ya gangaro mata amman wannan lokacin na farinciki ne, sosai take kuka wanda ya rasa dalili a tunaninsa murna da farinciki har ma da tsalle zatayi na barin gidan .
ta tsugunna kasa ta cusa kanta a tsakankanin cinyoyinta hawaye na cigaba da gangaro mata ya rasa ya zai yi daita abubuwa dayawa suka zo masa kukanta da rabuwar da zai yi daita rarrafowa yayi ya dawo gabanta ya kafeta da tsumammun idanunshi masu kashe mata jiki tun ba'aje koina ba ya soma Jin babu dadi a ransa ,ya bud'e baki da niyyar yin magana kenan kira ya shigo wayarsa ya janye jikinsa ya mike ya karasa Inda wayoyinsa suke ya d'auki wacce ke ruri ya duba sunan amminsa ne ke yawo a screen din wayar dan haka da hanzari ya danna Koren madanni tare da manna wayar a kunnensa ya soma tafiya yana Kiran sunanta "ammi!
bata daga Kai ta kallesa ba har ya bar d'akin kusan minti biyar da barinsa d'akin ta d'ago kanta ta bin hawayen dake zuba akan tafukan hannunta da Kallo.
a hankali ta soma share hawayenta zuciyarta na tsinkewa , ta tsaya shiru tana kallon d'akin har zuwa kan bed dinsa da komai ya faru sosai take tunani matsayar rayuwarta , kwakwaluwarta ta shiga tunani "shikenan ya amshi budurcinta zai barta ? " bana sonki amman budurcinki shine abinda yafi komai tsaya min arai har na mutu bazan manta da ni ne na amshi budurcin tanweer ba" kwakwaluwarta ta dawo mata da maganarsa "Adnan ka cuceni amman Kuma ka sake mamaye zuciyata da komai nawa , ka sake samun gurbi acikin zuciyata ,ka amshi abu me daraja da tsadarsa ya wuce komai acikin fad'in duniyar nan to me yasa har yanzu zuciyarka ta kasa amsar soyayyata ?why! why !! adnan kwalkwaluwarta ta toshe kanta ya cunkushe duk abinda ya fad'a rashin sonta daya furta shi yafi komai d'aga mata hankali "nima bazan manta da Kai ba har karshen numfashina ,Kuma har yanzu ban ji na tsaneka Ina tsananin sonka adnan nasan Allah yana da kyakkyawan nufi akan ni da Kai yasa ya had'amu , yadda nake sonka haka zalika Kai ma kana Sona duk da cewar kana boyewa , amman soyayyata ta gama fallasa kanta ajikinka tunda har abokanka suka san dashi , zan tafi na barka da dunbin qaunata daskare a zuciyarka , ba zaka gane hakan ba sai bayan bama tare idan Kuma hasashena dana abokanka bai zamo gaskiya ba " ya Allah ka jarabi adnan da mutuwar sona , yaji idan bai dora idanunshi akaina ba bazai iya rayuwa ba ,
ya kasa samun natsuwa ,ya kasa hutawa ,ya kasa tsaye ya kasa zaune har sai ya tunkareni da batu na soyayya , Allah kasa na zamo silar shiryuwarsa ya dawo mutumin kirki ...." ta k'arasa maganar tana mai runtse idanunta tare da jingina bayanta da abun gado tana sake zurfafa tunaninta tun daga farkon haduwarta dashi har zuwa wattanin da tayi a hannunsa ta fahimci abubuwa da dama akansa illarsa dai shan wiwi da sanar satar da yake bancin hk bashi da wata makusa ,yana qaunar ahlinsa da taimakon mutane gari yana kyautatawa duk wanda yake tare dashi gashi shi din me basera ne ta kowani bangare yana da matukar da basera akan komai ."
******
Bangaren hjy baseera kuwa tunda nazifi ya bar gidan alhj Tahir take cikin furgici da tashin hankali ta rasa samun natsuwar zuciya da kwanciyar hankali" tabbas allura na shirin tono garma domin kuwa bazata rungumi son ran alhj Tahir akan tilon d'anta ba ,bazata d'auka ba ,sam bazata zabi halin da yake k'okarin saka ita da d'anta ba akan cikar burinsa .
shiru tayi tana kallon celling falon tana nazari , tunanin abubuwa da dama suka dawo mata tana jin kamar karta amince da shawarar nazifi na guduwa da Ib zuwa wata kasa gara tayi komai ta ku'butar da rayuwar d'anta idan ma ta kama ta fito tayi gaba da gaba da alhj Tahir ta nuna masa tasan komai da yake ciki , amman tasan ko taki amincewa da shawarar nazafi me hali bazai fasa halinsa ba dan ba lallai idan ta fuskancesa ya fahimceta ba gashi har mugun halinsa yasa nazifi zarginsa akan bashi ne ya kawo Ibrahim duniya ba, da'ace shine ya kawo shi duniya tabbas duk son kudi irinsa nasa dole ya hakura ya rungumi rayuwar d'ansa dan bazai cutar da gudan jininsa ba wannan shine tmbyr da nazifi ya sha yi mata a tun sanda Ibrahim ya fara rashin lafiya ."
Cikin tsananin damuwa tace " wallahi shine mahaifinsa shine silar zuwansa duniya kawai dai haka rayuwarsa take yafi son kanshi akan kowa da komai, ta mike jiki a sanyaye ta shiga d'akinta a rikice Inda ta bar ib anan ta samesa kwance yayi shiru yana kallon sama d'akin tunanin tanweer yake yasan da lafiyarsa lau babu abinda zai zaunar dashi dole ta kowani hali ya dawo daita sai ga yadda Allah yayi dashi tashi ma baya iyawa bare akai ga magana duk wani kuzarinsa babu zuwa yanzu ya sadaukar da rayuwarsa adduar mutuwa yakewa Kansa ya huta da wannan rayuwar da yake ".
jin motsin shigowa d'akin yasa shi sauke idanunshi ya zubawa mata Idanunsa da suka rikid'e sukayi jazur , a kallon da yake mata ya fahimci bata cikin hankalinta da natsuwarta, ya cigaba da kallonta yana jiran yaji sautin muryarta ,itama kallonsa tayi dukkanin alamun sun nuna mata maganarta yake bukata ji, idanunta suka ciko da ruwan hawayen tausayinta dana yaronta ,ta zauna kusa dashi a bakin gado ta riko tafin hannunsa cikin nata hawayenta na diga .take hankalinsa ya sake tashi jikinsa ya kama rawa kamar mazari ya soma motsi da bakinsa alamun yana cewa wani abu amman babu hali .
a hankali ta fashe da matsanacin kuka tana kallonsa "na cuceka d'ana ,hakika ban maka adalci ba ,me yasa na auri mahaifinka gashi da kaina na zamo silar cutar da rayuwar d'ana ? na boye maka Mugayen halaiyan mahaifinka amman lokaci yayi da zan fayyace maka waye shi " duk wannan maganar da take acikin ranta take shima hawaye ne ke gangaro masa yana jin zafi da radadin halin da yake ciki da zubar hawayen mahaifiyarsa sai da tayi kukanta me isarta sannan ta zare hannunta cikin nashi tana shafa sumar kanshi "bari na gyara maka kwanciya ka kwanta kayi bacci inshallahu jibi duk yadda zanyi sai na bar gidan nan da Kai, bazan zuba Ido rayuwarka ta tagyayara ba, ta gyara masa kwanciya ta lullu'besa da bargo ta shiga bayi bayan minti biyar ta fito yana kallonta ta d'auki hijab dinta ta saka ta tsaya akan daddumar sallarta tare da tayar da sallah isha'i . "
bayan ta idar ta tashi ta fita zuwa kitchen babu kowa aciki kai tsaye ta shiga store din da kayan abinci yake , anan ta kira layin nazifi kira d'aya ya d'auka, ta fashe masa da kuka tana cewa"nazifi ka taimakeni tunda ka bar gidan nan na kasa samun natsuwa ,hankalina yaki kwanciya Ina ji ne kamar zan rasa Ibrahim dan Allah kasan yadda zamu bar gidan nan da Ibrahim daga gobe jibin da kace yayi min nisa dan bana son a bata lokaci dan a halin yanzu hankali yayi matukar tashi Ina ji ajikina kmr zan rasashi ne ,idan na rasa Ibrahim nima rayuwata tazo karshe zaka rasani ta k'arasa maganar tana kuka ".
" ki kwantar da hankalinki umma duk yadda kika ce haka za'a yi amman tafiya a goben akwai matsala saboda gbdy Shirin na jibi ne yanzu abinda za'a yi ki shiga d'akin ib ki soma had'a masa duk abinda kika san nashi ne me amfani inshallahu jibi zan zo da zarar dady ya bar gidan ,gobe idan zanzo zanzo da maganin bacci Koda zai zamo yana gida a jibi sai kiyi masa amfani dashi , bama anan zamu bar Ibrahim ba kasar ma gbdy zai bari na gama shirya komai tunda daman passport dinsa da naki zaku iya fita a duk sanda tafiya ta taso ".
"na gode! na gode !! nazifi Allah yayiwa rayuwarka albarka , yadda ka tsaya min kaima Allah ya tsaya maka bazan ta'ba manta hallacinka ba na gode sosai ".babu komai umma ai "yiwa Kai ne ban d'auki ib a matsayin amini ba kamar dan'uwa na d'aukesa Kuma wanda nake jinsa har cikin raina, Ina qunar ib Kuma zan iya masa komai idan ta kama zan iya sadaukar masa da rayuwata Allah dai ya bamu sa'a ."Ameen nazifi sun d'auki sama da awa suna tautaunawa Kiran alhj Tahir ne ya shigo har sau biyu yasa tayi masa sallama tana cewa "ka katse Kiran dady'nku na kirana ",to umma sai goben kenan , ya fad'a tare da katse Kiran ta d'auki Kiran alhj Tahir.
yana jin sautinta ya soma magana cikin fushi da zafin zuciya "kina Ina ne? sannan dawa kike waya haka tun dazu Ina kira busy busy ? "nida hjy zainab ne ,ta bashi amsa da hakan dan ta rasa me zata ce masa, ta godewa Allah ma da sunan yazo bakinta , naunayen ajiyar zuciya ya sauke "to ki fito ina falo "tace to gani nan zuwa .
Ta fito ta iske shi hakince akan d'aya daga cikin kujerun falon ta zauna akan kujerar dake fuskarta shi "me kuka tautauna da zainab din haka ? sai data zauna sannan ta fara magana "akan dai tanweer ne "
shiru yayi sannan ya gyara zama yana cewa " ko ta fad'a miki halin da'ake game da ma'aikatan nan dan yanzu na rasa gane kan lamarin nasu ?"eh to tace dai tanweer din ta kirasu cikin tashi hankali" a matukar firgice ya tashi daga rigin ginen da yayi ya zauna sosai yana dubanta a tsorace "uhm Ina jinki cigaba da bani labari sai data numfasa sannan ta cigaba" daga baya shima dan fashin ya kirasu tare da yi musu gargadi me karfi akan jami'an tsaro dake bibiyarsa idan suka cigaba da binsa zai kashe tanweer ta k'arasa maganar tana yin shiru.
"uhm to ita zainab din me tace ? Me kuwa zata ce ai tafi bukatar rayuwar diyarta nan dai tayita masa bayani kamar yadda hjy zainab tayi mata a wayarsu ta shekaran jiya ,jinjina Kai yayi kawai yana kallonta "Suma dai yanfashi nan da wasu kudin suka tambaya suka dawo musu da yarinyarsu cikin girma da arziki dan riketa da sukayi bashi da wani amfani hjy baseera tace" uhm " yace "eh mana to meye amfanin riketa da sukayi ?
duk abinda yace daga" eh! sai uhmmm take cewa a karshe ta tashi zata barsa "bari naje na kwanta. "tun yanzu ? ya fad'a yana duba agogon dake manne a falon. yanzu ne karfe goma tayi "eh yau duk ban zauna ba saboda masu shigowa duba jikin Ibrahim ko baccin ranar da nake dan yi yau ban samu nayi ba , ko akwai abinda kake bukata ne? "eh idan zan samu bakin shayi nake so "me zai hana zaka samu mana. mikewa tayi ta shiga kitchen ,cikin kankanin lokaci ta had'a masa har zata fito wani tunani yazo mata ta fito ta shiga dakinta ta d'auki kwayar tablet din da yake sa nazifi yana bawa Ibrahim ,ta fito ta markada ta zuba masa aciki shayinsa ta soma juya wa a hankali yadda bazai nuna ba "Kai ma kaji azabar da d'ana yake ji inshallahu kafin mu bar kasar Nan sai karfin jikinka ya ragu mugu kawai azalumi "
ta fito ta ajiye masa akan center table ta janyo gabansa alokacin yana kallon labarai ya d'auka ya kur'bi kad'an ya ajiye .
ita Kuma ta wuce daki tana shigowa Ibrahim ya bud'e idanunshi dake lumshe , a natse ta k'arasa Inda yake kwance ta Kai bakinta daidai kunnensa "Ibrahim d'ana jibi idan Allah ya Kai mu zamu bar gidan nan da Kai zuwa kasar Egypt domin duba lafiyarka tana gama fad'ar haka ta cire bakinta ya kura mata Ido yana bukatar qarin bayani "nasan Karin bayani kake bukata zanyi maka amman sai mun bar gidan nan .idanunshi ya shiga juya mata alamun bazashi koina ba, idanunta suka ciko da ruwan hawaye "idan har ban bar gidan nan da Kai ba mahaifinka zai yi sanadiyyar ruguza rayuwarka , idan har kana son ka mike bisa kafafunka ka taimaki tanweer ta dawo garemu dole sai ka bar gidan nan kayi nisa da mahaifinka ,zan maka bayani komai kamar yadda na fada maka amman sai mu bar nan , idanunshi ya lumshe mata alamun ya gamsu daita .ranar sam hjy basera bata runtsa ba ta zauna tana shirya duk abinda tasan zasu bukata har karfe d'aya saura sannan ta koma ta kwanta akan daddumar sallarta ."
****
Jaguwa ya gyara tsayuwa yana shafa qirjinsa da hannu d'aya sannan yana jin bayani amminsa daki daki akan matar data samo masa ,"ammi ki bar maganar wata hasera a yanzu , zanyi k'okari na kawo miki wacce zan aura ".ya fadi hakan ne ba dan zai Kai mata din ba sai dan ta rabashi da batun wata hasera .
a bangaren ammi ta katse shi da sauri "lokaci ya kure maka bazan sake baka wata dama ba dan naga alamun zuciyarka bata shirya amsar soyayyar kowace mace ba ,gara ni na shirya maka ga hasera nan ita zuciyata ta zaba maka Kuma ita zaka aura muddin Ina raye idan Kuma bujirewa zabina zakayi to sai ka sanar min ? ". Shiru yayi
tare da lumshe idanunshi a tsayen da yake dan amminsa ta rigada ta gama d'aure shi da maganarta "kayi shiru ko bazaka bi zabina bane nasani ? "
"Ban Isa ba ammi ,ban Isa naki bin zabinki ba amman ki canza min da wata ban da hasera" ya fad'a yana Jin wani sabon tashin hankali ya kusanto rayuwarsa "Amman Kaine kace duk wacce na zaba maka baka da ja ?sun d'auki tsawon lokaci suna tautaunawa a karshe yace ta bar maganar idan ya shigo karshen sati zasu sake tautaunawa akai ".
Bayan ya gama waya da ammi ya boye number ya kira mahaifin tanweer magana biyu yayi masa ya katse Kiran sannan ya kira number baba yana sheida masa zai maida tanweer gobe "bana ce maka karka kuskura ka maida yarinyar nan ba ?
"wannan yarinyar da kake tare daita a gidanka karka yarda ka rabu daita ko ka yarda ta matsa a kusa da Kai kmr yadda na fad'a maka a watanni da suka gabata ,
abinda bakasani ba ajikinta akwai taurari masu haske da karfin da zasuyi maka amfani akan aikinka ka barta a karkashika karka yarda ta bar karkashinka ".
"shiru jaguwa yayi yana tunanin abinda yake ta fad'a masa kenan kafin daga baya ya soma magana a sanyaye "bazan iya cutar daita ba sannan bazan iya amfani da taurarinta ba, idan da hali na zauna a yadda nake.
na samu duk abinda nake nema batare danayi amfani da taurarin kowa ba..".
"Wannan yarinyar dabam ce km ko ba yanzu ba dole zaka bukaci me irin taurarinta sai dai ba lallai ka samu ba dan haka ka barta kayi amfani da taurarinta ." bazan iya cigaba da zama da....."
"to ka aureta domin ta kasance a karkashin ikonka abinda ake so dai ta zauna tare da Kai ".
"Aure Kuma baba ?"
Mmn sudais
💗💗💗💗💗💗
KUSKUREN BAYA
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
PAID BOOK
FREE PAGE
WRITING BY
AYSHA .A BAGUDO
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukata karanta shi ya tura 500 ta wannan account number din 1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan a tura sai a turawa wannan number+234 703 534 8686alert domin tabbatar da an tura ko wannan number 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi sai a tura ta wannan number 08059623096 kada ayi vtu a number MTN domin sauraron littafaina a tuntubi channel dina ta hausa bakwai .
🅿️ 21
"Eh ! abinda nake nufi Kenan kuma nake bukata ka aikata, muddin wannan yarinyar bazata kasance karuwarka ba to ya zama lallai ka aureta Kuma acikin tsakankanin wannan lokacin ".
Cikin tsananin firgici da tsinkewar zuciya jaguwa yace " me yasa baba ? "mai yasa baza'a bar wannan maganar ba dan Allah ? " ni dai gsky a biyo wata hanyar banda wannan, tanwer tasan koni waye , tasan sana'ata fashi ne , nayi Imani Koda na fada mata zan aurenta bazata aureni da wannan sana'ar ba ya k'arasa maganar tare da yin shiru yana tunanin zuci "shi dai gaskiya komai za'a yi bazai taba auren tanwer da wata manufar ba ko cutar daita ba domin yana jinta ajikinsa tamkar jininsa ."
Shiru ne ya biyo baya na wasu mintuna kafin daga bisani baba ya numfasa kana ya soma magana a dake "Hanya daya ce zata maye maka wannan gurbin , ka nemi mace mai irin taurarinta ka ajiyeta akarkashin ikonka Koda bazaka aureta ba ka dinga saduwa daita saduwa irin ta aure idan kayi haka shikenan komai zai cigaba da tafiyar mana yadda muke so batare da wata matsala ba ."
"shiru jaguwa yayi yana kallon zara zaran yatsun kafafunsa masu tsananin kyau da sheki yana nazarin maganar baba, nan take gumi ya shiga tsatsafo masa a dukkanin ilahirin jikinsa, kwakwaluwarsa ta toshe zuciyarsa ta cunkushe guri daya , tunanin da yake ya tsaya cak ya Kasa cigaba da tunanin komai . sai daya dauki minti biyar tsaye batare da yasan madafar dafawa ba "amincewa auren tanwer Ko nemo mai irin taurarinta ya ajiyeta akarkashin ya dinga aikata zina daita "shi da yake neman yakice zina arayuwarsa sai ga baba na kokarin maidashi ruwa tsundum.
"Ya amince ne ko kuma ya fada masa a sake nemo wata mufutar ? sautin muryar baba ne ya dawo dashi cikin hankalinsa ta Inda ya cigaba da zayyano masa hujojinsa akan bukatar auren tanwer da yake son yayi Ko kuma ya shiga gari ya nemo mace me irin taurarinta idan ba haka ba nan gaba kadan za'a yi galaba akansa " .
duk abinda baba ya fada yasan yana da huja akan hakan kuma yasan ya fada ne domin ingata rayuwarsa daga sana'ar fashin da yake but shi baya jin zai iya ajiye tanwer a matsayin karuwarsa Ko aurenta domin samun wani biyan bukata daga gareta ". ya runtse idanunshi yana mai sake gyara tsayuwarsa yana jujuya maganganun baba yana sake fadadasu yana masu filla filla , gbdy komai ya tsaya masa.
ya sake neman natsuwarsa ya rasa , ji yake Kamar zuciyarsa zata buga tsabar shiga rud'ani tunanin matsalar dcp ,tanwer ,
Amminsa , yanzu Kuma ga matsalar baba da me zai ji?
"me ya kamata yayi ya samar ma zuciyarsa
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 25 Chapter of 62