da kasa. kamota yayi ya rungumeta yana shafa bayanta"is okay zainab babu abinda zai samu tanweer dinmu da izinin allah lafiya zata dawo garemu . yayinda ita Kuwa hjy zainab babu abinda take cewa sai "ka kira commissioner ."
Can bangaren jami'n tsaro kuwa suna Isa 1829 plaza dake gaban isalo a matukar harzuke suka firfito suka shiga ciki kmr d'azu wasu suka tsaya a waje Wanda suka shiga suka fara tambayar manager gurin, Kai tsaye aka nuna musu Inda yake nan da nan suka fara aika masa tambayoyi akan mutane da suka shigo plaza din a wanni da suka gabata "ai mutane dayawa sun shigo a yau din nan yalla'bai "ko zaka iya gane fuskokin wanda da suka shigo ya fad'a tare da nuna masa hoton jaguwa ?" gsky bazan iya ba amman tunda ga hoto bari mu qunna cctv camera mu duba " take yayi rewarning cctv suka tsurawa tv din dake gurin kusa guda biyar idanunsu , idanun manager ne ya Kai kan motar jaguwa "yalla'bai ga wata mota nan ta tsaya a haraban plaza a awa biyu data gabata nan dukkaninsu suka bada attention dinsu suna duban motar suna sauraronsa " mutun d'aya ne ya fito daga cikin motar fuskarsa rufe da face mask nima Kuma a wannan lokacin na fita Kuma tabbas naga wannan motar mai number 2548 bayan ya shigo nima na dawo Ina kallonsa yana daukar dogayen riguna na mata haka kawai naji hankalina bai kwanta dashi ba idanuna na kanshi har sanda ya biya kudin kayan ya wuce duk yadda akayi wannan mutumin ne duk da fuskarsa bata bayyana ba kamar yadda hotonsa yake suna tsaka da sauraronsa kiran commissioner ya shigo wayar dcp, ya d'auka cikin sauri yana cewa "hello sir "kuyi maza ku dawo akwai matsala "matsala Kuma sir ?
"Eh babba kuwa domin rayuwar yarinyar na cikin hatsari idan aka cigaba da bibiyarsu ga dukkanin alamun akwai wanda yake yiwa hukuma zagon kasa". aikuwa yayi babban kuskure ya cuci alluma har ma da zaqaqarun yansanda masu k'okarin ganin an kawar da ta'addanci a kasa inji cewar dcp batare da bata lokaci ba dcp ya juya yana bawa yaransa umarni ."Tafiya kawai dcp yake baya ko gamin gabansa saboda takaici da bakinciki wai sai yaushe ne zasu yi nasara akan jaguwa ?sai yaushe zasu yi nasara akan shi Kawar dashi daga doron duniya da wannan tunani ya Isa gidansa.
Jaguwa ya dade tsaye a lambun gidansa byn ya gama waya da mahaifiyar tanweer yana shawagi agurin tare da tunani kala dabam dabam cikin haka wayarsa ta soma ringing ya d'auka ya manna a kunne ya tura hannunsa cikin aljihun wandonsa maganar minti biyar kacal sukayi ya katse Kiran ya cigaba da shawagi sai gasu anas kowannensu hannunsa rike da tabar wiwi yayinda anas ke rike da biyu ya mikawa jaguwa d'aya, ya amsa ya kai bakinsa ya fara zuka sannan gabad'ayansu suka samu guri suka zauna suna magana akan mata "ya kamata mu dan fita yau ko Kuma muyi invent dinsu zuwa gidan nan ?"ai rayuwa babu mace quntatawa ne kasamu mace lafiyiyayya Kuma me shaye shaye ka sauke gajiyarka akanta inji cewar jubi murmushi jabir yayi "wallahi kamar kuwa kasani mace me shaye shaye tafi dadin muamula ga juriya saboda bata haiyacinta haka dai sukayita hirarsu akan mata
yayinda jaguwa ya lula duniyar tunanin wanda tunanin kusan duk na tanweer ne .yana jin kamar ya shareta amman zuciyarsa ya kasa aiwatar da hakan ko babu komai tana bukatar kulawarsa tunda bata da lafiya kuma idan bata ci abinci ba taya za'a yi ta sha magungunanta ?
wannan tunanin yasa ya kira aliyu ya aika siyo mata abinci bayan kamar awa d'aya aliyu ya dawo hannunsa rike da farar leda ya amsa ya ajiye ya cigaba da zugar wiwi , sai da yayi mankas sannan ya mike ya nufi d'akinta bakinsa d'auke da sallama hannunsa rike da farar leda yayinda gbdy jikinsa ke warin wiwi hade da turaren jikinsa .
shigowarsa ke da wuya d'akin ma ya kaure da warin wiwi dana turarensa wani irin haushi ya kamata idan akwai abinda ta tsana shine warin wiwi ko ta'ba , kallo d'aya tayi masa ta d'auke kanta ta mayar wani gefe tana wasa da yatsun hannunta .
Ya ajiye ledar hannunsa yana cewa "ga abinci nan kice ki sha magani kin ma kuwa yi sallah isha'i ? "ban yi ba Kuma bazan yi ba, wallahi idan ka sake min magana akan sallah sai na kashe kaina "Allah ya bada sa'ar tafiya dadin abun idan kin kashe kanki bazaki rataya a wuyan Adnan ba kice zaki mutu kafura ".
"Kai ne dai kafuri Kuma Kaine zaka mutu a wannan rayuwar da kake. "are you out of your sense ? ya fad'a a fusace " ni kike fad'awa haka ?" shiru tayi tana dubansa kafin idanunta ya kawo ruwa "amman Kai me yasa kullum sai kayi min magana akan sallah kamar wata kafura ? "Alama na gani na bakin son yinta " .
shiru ta sake yi kamar me nazari numfashi ya fesar ya juya zai fita
yaji sautin muryarta a raunane "kazo ka d'auke banzar abincinka dan ba zanci ba" kad'a kafad'unsa yayi yace "daidai kenan Ina son haka ,Kinga rashin cin abincinki ko rashin walwarki bazata dameni ba saboda bana sonki bakya cikin rayuwata kisan Allah ko nemanki nayi na rasa bazan damu ba dan bayan mahaifiyata da kannena ban san ciwo kowa ba, bayan darajan kannena dana sani ban San darajan kowace mace ba Kinga Kenan Kema kina cikin matan da bana ganin darajansu ,yana gama fad'ar haka ya fice daga daki ."Kuka ta rushe dashi tana Kiran tashi uku sai da tayi me isarta sannan ta janyo ledar daya ajiye mata dan yunwa take ji sosai , taci kad'an ta bar sauran ta shiga bayi tayi wanka ta fito ta sha magani tayi sallah ta kwanta lamo akan bed tana tunanin iyayenta, "Allah sarki dadynta muryarsa ta nuna yana cikin damuwa " dad dinta da bai iya cikakken awa d'aya ba tare daita ba ,ko zuwanta turai karatu baya jimawa batare daya ganta ba, kullum Kuma cikin video call suke ,ko ya dad dinta zai ji idan ya ga ta dawo garesa ? tasan rungumeta zai yi a karshe ya d'auketa sama yayita juyi daita yana cewa "my tan ta dawo I really miss you my tanweer wasu hawaye masu zafi ne suka biyo gefe da gefen idanunta.
"Ko waye wanda ya tura musu yan fashi ?waye wannan ? ta tambayi kanta "waye cikin family dinmu ?dangin mumcy dina ne ko dangin dad dina ne ?"dangin dad dina basa zaune a lagos tunda shi din haifafen garin Kaduna ne, mumcy dina Kuma yar d'aura ce ",ai daga koina mugu zai iya idar da nufinsa ya farmaki rayuwarka,Allah sarki mugu bashi da kama suna tare dashi Amman basu san cewar shi din makiyinsu bane "shiru tayi tana sake zurfafa tunaninta ,babu abinda ya shiga
yawo acikin kwakwaluwarta kamar hirarsu jaguwa a wacan ranar data san dan fashi ne "tabbas taji sun ambaci sunan Alhj tahir a hirarsu .
a lokacin ta zurfafa tunanin domin sanin me sunan a karshe zuciyarta ta tsayu akan mahaifin Ib shi kad'ai tasani me wannan sunan, tashi tayi zaune ta zauna "tabbas shine me sunan Ibrahim Tahir ta furta a fili "Kai ba dai shi ba bazai ta'ba aikatawa mahaifinta haka ba sai dai idan suna ne ya zamo daya , to Kuma ai maganar Adnan ta nuna Wanda ya turasu na tare dasu to meye gaskiyar lamari ? take zuciyarta ta shiga wasi wasi wata zuciyar tace shine wata zuciyarta ta karyata hakan .
wasu hawaye ne masu zafi suka
zubo akan kuncinta " tana bukatar ganin iyayenta tana son ganin dad dinta da mum dinta tana bukatar Jin dumin jikinsu kamar yadda ta saba dan girmanta bai hanata kwanciya ajikinsu ba she really miss them .".
Daren ranar kasa runtsawa tayi jikinta yayi zafi rau kamar garwashin wuta sai faman juyi kawai take akan mamaken bed din da take kwance tana tunanin mafuta kwakwaluwarta ta sake lula kogin tunani mai zurfi akan yadda zata bar gidan ta kowani hali dan dole tasan yadda zatayi ta bar gidan tun bai canza ra'ayinsa akanta ba ya fara kusantarta.
da kyar bacci barawo ya saceta washegari da safe bai shigo yaga halin da take ciki ba yayita lamuran gabansa ita Kuma hakan ya bata damar tsara yadda zata bar gidan kota halin balai, ta fito sanye da doguwar riga baka har kasa tayi rolling kanta da mayafin rigar Kai tsaye ta wucesu a falo zaune tare da abokansa har ta fito haraban gidan
ya fito ya biyota yana cewa " ke Ina zaki kika wani wuce mutane dan iskanci ?
"Bansani ba Kuma karka sake tambayata Inda zani dan ni ba diyarka bace sannan ba abar ikonka bace da zaka wani tsareni da banzar ta....." shiiiii wuce ki koma ciki" "bazan koma ba gidan nan zan bari Kuma a yanzu ta fad'a tana cigaba da tafiya taku uku yayi ya riko tsintsiyar hannunta "muje babu Inda zaki sai wadin zamanki a gidan nan ya Kai .
ta juyo a fusace ta sanya kwayar idanunta cikin nashi cike da balai tace "Kai waye da zaka hanani tafiya?.
"ni Adnan amad ".ya bata amsa yana kallon cikin idanunta fuskarsa a had'e babu alamun wasa .
"wallahi baka Isa ba who the hell are you? duk da me gadi gidan nan abun ikonka ne zanyi duk yadda zanyi na bar gidan nan Kuma a yau .
jaguwa bai saurarata ba ya jingina jikinsa ajikin motarsa ya tsura mata Ido yaga iya gudun ruwanta . tanweer ta Isa Inda taga makulan motoci rataye ajikin bangon rufar motaci ta d'auki ta camery ta rike gam zata bude moto tuni yaransa suka tareta bisa umarnin jaguwa da yayi musu umarni da Ido sai dai hannunsu bai ka ga jikinta ba suka hanata ta'ba kowacce mota a daidai lokacin su anas suka fito suka tsaya suna dubanta .
xagi ba kalar da tanweer bata musu ba da hausa da turanci Amman Babu Wanda ya kulata haushi ya isheta ta bar gurin mota ta nufi bakin get nan ma babu hali dan me gadi yaki bude mata get duk Inda tasan zata bi ta fita daga gidan babu hali ta shiga maseefa tana cewa " sai na bar gidan Kuma Babu wanda ya Isa ya hanani fita idan na bar gidan sai na sa ankamaku anyi muku hukunci me radadi,wallahi da Kun San Koni wacece a garin nan da baku tsaya bin umarnin wannan ba Kun hanani fita ba, ta juya ta Kalli Inda jaguwa yake tsaye jikin motarsa Idanunsa na kanta yana cigaba da kallon bakin tsiwa "zan nuna muku ko ni wace acikin garin nan tare da juya masa baya.
"Kashi Amman na tausaya miki wannna shi ake kira da power less" juyowa tayi cikin fushi ta Kalli Inda yake idanunta ya sauka akanshi.
yana nan tsaye sai dai zuwa wannan lokacin ya harde hannuwansa a qirji yana mata murmushin mugunta fuuuu ta nufosa cikin tsananin fushi da zuciya tace "zan nuna maka wannnan power din kasa Ido ka gani"tayi mgnr tana nunashi da yatsa "me zaki iyayi ?ba abinda zaki iya yi min ,ki daina takama da wannan dan matsayin da mahaifinki yake dashi dan baki da wani power da zaki iya min koma" .
ba bata lokaci ta cukumi wuyansa "zaka ga abinda zanyi ".
Yaransa suka bishi da kallo haka ma abokansa me gadi kam saurin kawar idanunshi yayi kamar bai ga abinda ke faruwa ba ran jaguwa yayi mugun 'baci sai dai bai ce mata Komai ba har sanda ta hau fad'a da maseefa da zaginsa da fada masa bakaken maganganun ,sai da tayi mai isarta sannan ta sakar masa wuya ta dukurshe ta zube kasa ta runtse idanunta wasu hawaye masu zafi suka zubo mata .
shi kuwa ya matsa gefenta ya tsura mata Ido ransa na quna kafin daga baya ya canza kallon zuwa natsana yayi taku biyu zuwa Inda take durkushe dafe da goshinta "sorry tanweer bazaki iya komai ba sai da kiyita ihu kina kuka kina zagina
just like a baby ,the great tanweer, kyakkyawar matashiya mai ji da
kudi yanzu ta zamo abar tausayi agidan nan , gidan nan fa ba yadda kike tunani bane dan ba haka kawai yake ba ko mahaifinki da karfin masu karfin garin nan zasu zo basu Isa su shigo ba, Ina tabbatar miki muddin kika bar gidan to nine na fitar dake amman rashin kunyarki da ihunki bazasu fitar dake ba cikin sauki ba ."
wani mugun kallo take masa tabbas da zata samu bindiga a halin yanzu da zata hakura da son da take masa
ta harbesa ta huta, hakan ne ma zai zame mata sauki a rayuwarta dan tasan muddin bai duniya zata hakura dashi , "amman bari na gwada miki karfina ai kina son fita ko?tayi shiru taki cewa komai sai hawaye dake zuba "Ammar bude mata get tuni
taga get ya bude "how dare you? ta fada tare da k'arasawa gurin me gadi ta d'aukeshi da mari "Kai har ka Isa na maka mgn Kaki bin umarnina kasan kuwa waye ubana a garin nan? "ubana shine minister of health na garin nan waye shi wannan daya ajiyeku ban da tantiri ?jaguwa ya matso gabanta ya mika mata roban ruwan faro me sanyi ",Sha ruwa sanyi tanweer kiyi aiki da kwakwaluwa " me yasa mahaifinki zai d'auki mataki akansu ?"anan basu san kowa ba sai sani , babu dokar kowa da zai yi aiki sai nawa ,gidan nan gidana ne mahaifinki bashi da wani matsayin bashi da power haka kema , shi wannan matsayin ko power din ki bari sai kin koma gidanku dan anan babu Wanda zaiyi respect dinki babu Wanda zai ga girmanki sannan babu Wanda zai bi umarninki sai nawa , nawa za'a bi kin san me yasa ?Yayi kusa kusa daita "kowa yasan matsayina, dan fashi ne dake sata wa kasa da kasa the CEO of armrobber's, armrobber's din daya yi suna da girma a fad'in Africa gbdya kowa yasan jaguwa wato Adnan amad gwoza anan wa yasan matsayin tanweer har ta bada umarni abi har ta kafa doka abi a zauna ?ke ba kowa bace sai diyar common minister of health da iya garin nan da wasu tsirarun garuruwa akansansa
sannan mutumin dake zaman banza
a offishinsa da suna yana aiki wa alumma mutumin da maci amana kasar ne , bai San komai ba sai shaye shaye da neman matan banza da bata rayuwar mutune wannan shine cikakken halin mahaifinki da kike takama dashi ,bari kiji da zai fito da boyayyen halinsa fili babu mutun d'aya da zai ga girmansa hatta ke kanki sai kin tsaneshi ,wallahi idan baki yi amfani da tunaninki kin kiyayeni ba kin daina zagina ba zan nuna miki asalin waye jaguwa, zan fito miki da true colour dina, zan yaga miki rashin mutunci ,zan mayar dake baiwa a gidan amadadin bautar da nake miki , sannan ki zamo daya daga cikin karuwaina nayi duk yadda nake so dake idan bukatata taso nayi ko sau nawa nake so yana gama fad'ar haka ya juya abunsa ."
ran tanweer yayi mata zafi ta dinga Jin zuciyarta kamar wuta magangunsa suka tsaya mata arai ta kasa motsi, ta bishi da Ido kawai
tana kallonsa ,lokaci na farko kenan da'aka fad'a mata bakaken maganganun da suka daga mata hankali Km akan masoyinta data fi qauna akan komai,sosai taji mgnr sun tokare mata zuciya Kuma ta kasa Koda motsi balle ta bud'e baki ta zagesa ko ta fad'a masa bakar mgn. shiru tayi tana mamakin abinda ya fad'a akan mahaifinta karyata hakan zuciyarta tayi sai dai Kuma ta rasa dalilin da zuciyarta ke wasi wasi akan maganarsa ."
Shi kanshi jaguwa yayi mamakinta Yana jiran yaji ta balbalesa da masifa da balai akan furuncinsa sai yaji shiru don haka byn ya dan yi nisa kad'an sai ya juyo yaga me takeyi, har yanzu tana zaune tana kallonsa yaga wani bacin rai atattare daita wanda bai ta'ba gani ba tayi sanyi sosai bazai iya karantar meye a kwakwaluwarta ba tuni yaji hankalinsa yayi matukar tashi Anya bai fadi magana dayawa ba kuwa akan dad dinta ? "Shi kansa yasan ya fadi abinda bai dace ya fad'a ba , jikinsa ne yayi sanyi ya Isa d'akinsa yana tunani hankalinsa ya tashi dan arayuwarsa baya qaunar ya batawa wani bare ita da yake jin duk saukar numfashinsa yana sauka da tunaninta ne ,yadda yaga yanayinta yasan ya ta'ba zuciyarta" me yasa na fadi abinda na fada "karka damu is a very good respond to her akan furucin bakinta km ya kamata tasan kadan daga cikin halin mahaifinta .
" amman Kuma karya zamo da gaske zata shirya daukar fansa akanka ? tsaki yaja dan me zakaji tsoro ko ka manta ko kai waye ? Yayi shiru na dan tsawon lokaci sannan yace "babu abinda zata iya ya kwanta akan kujerar kushin ya janyo pillow kujerar ya rungume a qirjinsa yace"tanweer you can't do anything coz na zamo wani bangare na rayuwarki ."
Tanweer ta koma d'akinta ta kwanta lamo akan kayan da tayi kaca kaca dashi sai dai tsabar zafin zuciya ta jima tana tunani wani lokaci hawaye ya zubo mata ta tsinci kanta cikin kewa ta dinga Jin kamar bata da kowa da komai a duniya a tattare daita haka ta yini kwance agurin ta Kulla wannan ta kwance har dare jaguwa yasa aka yi order abinci kala kala wanda yasan take so, ya nufo d'akinta Yana bud'ewa yaga wani duhu ya kunna wutar d'akin ya sameta kwance cikin yanayi mai ban tausayi ya matsa gareta ya tabata "tanweer "!
ya kira sunanta ai kamar wanda ya dana mata shoking din wuta tayi saurin mikewa ta buge masa hannunsa "ka kyaleni ka rabu dani kaji dadi burinka ya cika kasani cikin wani hali ,ka rabani da kowa nawa,kasani cikin damuwa hawaye ya zubo mata "ka rabani da masoyina ka rabani da dady ka rabani da komai hatta matsayina da mutuncina ka rabani dashi kana Jin wai Kai wani
ne shiyasa ka dauki kanka a wata tsiya to bari na fad'a maka sai dai idan ban bar gidan nan a raye ba amman wallahi sai na ......" shiiiiii ki Daina wahalar da kanki coz you can't do anything ".
dukkaninsu sukayi shiru suna kallon juna a zahirin gsky bai so ya fad'a mata abinda ya fad'a ba amman tunda ya fad'a babu abinda zai goge hakan, muryarsa can kasa yace"ga abinci kici ki km huce dan nasan baki ne babu abinda zaki iya yi ya mike ya juya yana cewa "ki tabbatar kin gyara d'akin ko ki kwana cikin datti ". kifi abincin tayi a kasa "baza'a ci abinci ba, gbdy ta zubar dashi tabisa da fad'a da tsawa bai kulata ba ya wuce ya tafi a wannan daren dukkaninsu babu wanda ya runtsa kowa da abinda ke ranshi ke sakawa jaguwa da bacci ya gagara ya tashi ya shiga d'akin anas kusan kwana sukayi suna Hira sai dai bai yarda ya Sako mgnr tanweer ba yayinda Zahra tayita Kiran wayarsa bai d'auka ba , wannan abu yayi mugu mugun d'aga hankalin zahra ta kwana da matsanacin fushi da bacin rai a zuciyarta da sake d'aukar burikan mugunta akan tanweer haka ma washegari bata hakura ba tayita kiransa bai d'auka ba shi kuwa duk kiranta yana gani amman yaki d'auka dan bai ga abinda zaiyi da kiranta ba ya cigaba da harkokin gabansa ."
A daidai wannan lokacin kuwa Zahra na can cikin tsananin tashin hankali tsaye cikin bakake kaya kunneta manne da waya cikin yanayi na tashin hankali take waya da blessing "matsalata daya yanzu arayuwa shine Adnan ."
"Na fada miki zaki samu Adnan zaki auresa ta kowani hali duk Wanda zai shiga tsakaninki dashi karshensa mutuwa ,mutuwace makomarsa dan haka ki kwantar da hankalinki mu gama da next target dinmu ki natsu karki rusa mana plan idan aikin boka yaki akwai makirci bare zai ci zan sake kaiki wani guri Ina tabbatar miki duk abinda yake takama dashi da asiri baya cinsa sai mun rusa, mun ruguza komai nashi yaji baya qaunar ganin kowa sai ke ."
"Shine abinda nafi qauna blessing ya zo da kanshi ko bai rokoeni soyayya ba ni dai yazo blessing bazan iya rayuwa babu Adnan ba "ki daina kaskanrar da kanki kina da komai da duk wani cikakken nmj zai soki akanshi kece kika fi dacewa da cancata dashi ba wacan tsinanniyar yarinyar ba, ya soki ya qaunaceki amman saboda rashin hankali da tunani me kyau irin nasa ya rasa Inda zai ajiye soyayyarsa sai gurin...." "excuse me blessing don't ever call him mad karki sake zaginsa idan kina cewa bashi da hankali da tunani ni Kuma da nake so shi fa ?don't don't try to insult him "am sorry kit Zahra ta katse Kiran batare da ta jira taji me blassing zata sake cewa ba ."
*******
Alhj tahir dake zaune yana jiran zuwn nazifi yace "ya'akayi son Kai nake jira anyi nasarar samun alluran kuwa da kwayoyin ?"kayi hakuri karka ga kamar Ina cutar da abokinka wallahi rashin tashinsa shine zaman Lafiya da kwanciyar hankalina sai da nazifi ya zauna akan kujera sannan yace "karka ji komai dady an samu da yarda Allah Kuma zai yi aiki ajikinsa sosai fiyye dana baya dan wannan maganin bincike ya nuna idan anyiwa mutun sau goma zai iya mutuwa dady ya matso gabansa "kar dai ya mutu amman Kuma idan mutuwar zata zame min hutu Allah ya bada ikon tafiya "inna lillahi wa inna ilaihi rajiun nazifi ya furta a ransa qirjinsa na bugawa da matsanacin karfi a sukwane nazifi ya jingina bayansa da abun kujera "dady nifa Ina ganin daga wannan maganin da zan kaiwa mumy bazan sake kawo komai ba nagaji da wannan aiki zuciyata ta kasa samun natsuwa kullum zuciyata na fad'a min Ina cutar da aminina, ruhina yaki samun salama wallahi bana iya runtsawa dama nasan dalilin da yasa kake son kassara rayuwar Ib Kuma nasan cewar ba cutarwa bace a rayuwarsa wallahi zan tsaya sai Inda karfina ya kare sannan zan tsaya naga komai ya tafi daidai ."
"kai dan Allah gafara can Sha Sha dady yayi hanzarin katseshi ta hanyar fad'ar haka "Ashe baka da hankali Taya kake tunanin zan fada maka dalilina ? karfi da matsayin da Ibrahim yake dashi acikin garin nan ne farkon jegon komai , muddin na bari ya tashi bisa kafafunsa komai zai iya faruwa dani, kasani Kai ma ko ka manta matsayinsa ne?bama haka ba Ibrahim nada karfin da zai iya komai akan cikar nawa burin dan haka
nazifi bazan barshi ya tashi ba Kuma bazan fada maka dalilina ba dan ko na fad'a maka bazaka fahimta ba ka dai qara min lokaci ka cigaba da aikin nan karshensa ma yazo ".
nazifi ya furza da wani huci Yana tsinewa alhj Tahir a zuciyarsa ya mike tare da yi masa sallama har ya kusan Kaiwa bakin kofa yaji muryar alhj Tahir "karka kuskura ka fadawa kowa wannan shiri dan bazan fad'a maka abinda zai biyo baya ba sai dai kawai ka tsinci kanka cikin tsaka me wuya abinda bazan so faruwarsa ba kenan dan har yanzu kana nan a matsayin d'ana" . gyada Kai kawai nazifi yayi ya fice .
Hajiya baseera zaune akan kujera me zaman mutun uku sai ga nazifi ya shigo hannunsa rike da leda wanda da gani kasan na asibiti ne dan a zahiri ake iya ganin abinda ke ciki ,hjy baseera na ganinsa ta saki fuska duk da zuciyarta cunkushe take da damuwar rashina lfyr Ibrahim ,
sosai tayi farincikin ganinsa tana qaunarsa tamkar yadda take qaunar Ib .ya dan rusuna cike da girmamawa ya gaisheta "Ina yi mumy ?"lafiya lau son ya fama da jama'a da kokari Kuma ?
"alhamdulillah mun godewa Allah ya Ib da jiki ? alhamdulillah Lafiya na ta samuwa ta nuna masa gurin zama da hannunta "ka zauna son "ya samu guri ya zauna yana cewa daga bangaren dady nake gbdy lamarinsa babu sauki a yadda yake kokarin son kassara rayuwar Ib,wallahi mumy abun na matukar bani mamaki haka nan sai na zauna Ina tunanin Anya kuwa mahaifinsa ne da yayi silar zuwansa duniya ?"mahaifinsa ne nazifi
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 20 Chapter of 62