tsaya ba ya nufi d'akinta ya shimfideta akan gado idanunshi
na kanta yana tsaye yana kallonta sai ga anas ya shigo d'akin cike da tashin hankali yana ganinsa ya janyo blanket ya lullu'beta yaja ya tsaya tare da rungume hannunwansa duka a qirjinsa cikin tsananin damuwa
anas ya zubawa tan Ido yana kallonta Ko cikakken minti biyar bai yi ba sai ga jabir, jubi ,kamil sun shigo .
duk suka zuba mata idanunsu suna kallonta kowa da abinda yake sakawa a cikin ransa a hankali jaguwa ya runtse idanunshi tare da Kai hannunsa daidai saitin zuciyarsa dake bugawa da sauri sauri ,anas ne yayi karfin halin tambayarsa abinda ke faruwa daita "daman itace babu Lafiya me ya sameta ?"aikin wancan tsinanniyar yarinya ce ya fad'a a tsawace "wacce yarinya kenan ?anas ya tambayesa a rud'e "wace ce banda waccen yar iskan zahra din asiri tayiwa yarinyar mutane amman na rantse da Allah sai naci ubanta inga uban daya tsaya mata acikin garin nan"take it easy jaguwa Kai ya akayi kasan tayi mata asiri ? tsaki jaguwa yaja da karfi idanunshi na kan tanweer dan yasan daman haka zai ce tunda baya ganin laifinta .
a tsanake jabir yace "Allah ya kyauta yanzu dai me ye solution dan naga kmr yarinyar bata numfashi ?ga tan nan dai tana numfashin sai dai ba sosai ba da kyar na samu numfashinta ya dan dawo wallahi muddin wani abu ya ta'ba lafiyarta zan shayar da Zahra mamaki inji cewar jaguwa ,gyada kai suka yi gbdy sannan jubi , jabir ,kamil suka juya suka fita daga d'akin dan babu me iyawa dashi idan yana cikin fushi sai anas ."
"kayi hakuri jaguwa ba lallai abinda kake zargi akan zahra ta aikata ba anas yayi mgnr yana dafashi a fusace ya buge masa hanun yana cewa "Daman nasan haka zakace tunda kafi qaunar dani "no !no !! jaguwa saboda qaunar da zahra take maka yasa nake kulata taya ma zaka had'a matsayinka daita gsky karka sake min hk banaso Kai fa jinin jikina ne ita Kuwa fa ? jaguwa yayi shiru tare da tsurawa tanweer Idanunshi wasu kwalla masu zafi suka zubo akan kuncinsa cike da takaici da nadamar abinda ya aikata mata, nadama irin wacce bata da amfani .
anas yayi matukar mamaki ganin jaguwa ya tasa tanweer gaba yana kwalla "lallai haka rayuwa take tana cike da abun mamaki "jaguwa ne yau yake kuka akan mace ? "Jaguwa !
Anas ya kira sunansa "yana jinsa yayi masa banza tamkar ba dashi yake mgn ba " kana mutuwar son yarinyar nan amman Kaki yarda da kana sonta , Kalli yadda kake zubar da hawaye akanta ,Kalli yadda tausayi mai hade da soyayya suke dawainiya da Kai ,ka yarda jaguwa kana sonta ka daina karyata zuciyarka , ka daina hasashen bazaka iya sonta ba, ita fa rayuwa kafi ni sanin rubutaccen alamari ne daga rabbi, hatta wannan Sana'ar tamu qaddara ce Killa da iyayenmu sun san zamu zo duniya mu kasance yan fashi wallahi da tuni sun kashemu da hannunsu ".yayi shiru yana dubansa "ka yarda Kuma ka amince kana sonta sai mu taru mu bar wannan rayuwar ,zamu tayaka inganta rayuwarka jaguwa domin sama maka farinciki .........."
"ka daina fad'a min haka anas banaso ji wannan kalmar daga bakinka sau nawa zan fada maka tausayi ne ba so ba ?"yayi saurin karyata amininsa taya ma zai sota byn tanweer tafi karfinsa a aure, waye shi ,? waye yan'uwansa a fad'in kasar nan ?
duk da a yanzu ya taka matsayin da kudi ba matsalarsa bane amman yasan aurenta zai masa wahala, ya sake fuskantarta sosai yana Jin kamar yayi mata numfashi ,sosai ya fad'a kogin tunani hankalinsa ya bar duniyar da yake ciki ya Lula wata duniyar dabam ."
"Bamu saba boyewa kanmu komai Daya shafi rayuwarmu ba ,jabir, jubi kamil ,duk tare suka ganmu kana fada min gaskiyar dake cikin zuciyarka akan komai amman akan wannan yarinyar ne kawai ka kasa fad'a min matsayinta a zuciyarka ,kana tunanin zan hanaka soyayya ne da ita ko me?wallahi kamar yadda kaji na fada maka ni me rungumar komai ne akanka Koda kuwa mutuwa ce, Ina maka soyayyar da zan iya sadaukar da rayuwata akanka, karka manta mu din masoyan juna ne da muka yarda da juna Kuma muke son juna saboda Allah, zuciyata ta yarda ta amince kana son yarinyar nan so me tsanani ko dan tana diyar minister yasa kake gudun fallasa sirrin soyayyarka ?
"ko d'aya bana dai sonta ne " kama saukakawa kanka nan kusa ma ammi zata min mata ka san kuwa zuciyata bata da wani zabi daya wuce nata dan haka ka cire wannan tunanin a ranka ya k'arasa maganar still idanunshi na kanta " yana dasa Aya anas ya juya a hankali ransa a matukar bace.
"ta yaya gashi yana kallon tsagwaron qaunar yarinyar a idanunshi amman yake ja inja dashi ? ranar ce rana ta farko da jaguwa yayi masa abinda har yaji ya tsaya masa arai , Jin motsin Bude kofar d'akin ya sa jaguwa ya waigo da Kansa anas ya gani zai fita daga d'akin shima kmr ya bar d'akin sai ya tsinci Kansa da kasa aiwatar da hakan yaji bazai iya barinta ita kad'ai ba dan haka ya hau gadon ya janyota ya d'aurata a saman faffadan qirjinsa, a hankali yana shafa bayanta, ajiyar zuciya ta fara jerawa tamkar wacce ta sha gudu tsira ,qara makaleta jaguwa yayi tamkar wani zai kwaceta a hannunsa "Anya kuwa adnan baka fara son yarinyar nan ba ?" ya tambayi kanshi yana shinshina wuyanta" ka fara sonta mana tunda kana tsananin qaunar kasancewa daita zuciyarsa ta bashi amsa da hakan "Ina ba haka bane tausayi ne kawai babu wannan a tsakanina daita ,gyara mata kwanciya yayi sosai ta yadda bazata takura ba ya sauko daga kan gadon zai fita yaji ta riko hannunsa waiwayota yayi zuciyarsa na dokawa da matsanacin karfi ya kalleta sosai bacci take da alamun ma bata san ta aikata hakan ba , ya fito daga d'akin zuwa bedroom dinsa kana ganinsa kasan baya cikin haiyacinsa zama yayi yana neman layin sadiq ya kira sakamakon ganin missed calls dinsa ya d'auka yana d'auka yace "father komai normal dai ko ka Isa gida lfy ? "Normal sadiq komai daidai na gode da kulawarka dan uwana , sukai sallama kmr ya nemi layin zahra dan yasan adaidai wannan lokacin idanunta biyu Killa ma tana can yawon ta zubar amman ya share yana zaune zata zo ta samesa .."
Can bangaren IPO kuwa yana ganin dawowar jaguwa yasan sun yi missing dinsa wayarsa ya ciro ya shiga neman number dcp baba abare yana d'auka yace "sir Kuna Ina ne ? daga can bangaren dcp yace muna kan titi har yanzu bamu ga dawowarsa ba "gsky kunyi missing dinsa dan ya dawo gida "shit ...." dcp ya furta a fusace sannan ya cigaba da magana "amman a juri zuwa rafi wata rana tulun zai fashe "wannan haka ne sir idan kere na yawo zabo na yawo wata rana zasu had'u ne ",ai kuwa haduwarmu bazata yi kyau ba dan bazan Kai shi ga office din hukuma ba bare a samu damar bada belinsa tarwatsa masa Kai zanyi kowa ya huta yana gama fad'ar haka ya katse Kiran a fusace yana bawa yaransa umarni ."
*****
Washegari da misalin karfe takwas ya fito zuwa falonsa sanye cikin gajeren trouser baki da riga fara mai hula da ratsin baki ,sanye da takalmi fari mai azaban kyau yayi kyau sosai sai dai fuskar nan tashi a murtuke tamkar jinin sarauta sannan kallo d'aya zaka masa kasan zuciyarsa a dagule take jira kawai yake a tabashi ya hau mutun , ya d'auki remut ya kunna tv ya Kai chennel zuwa na labarai yana ƙoƙarin zama friends dinsa suka shigo suka zagayesa har kamil Suma cikin shiga ta alfarma atare suka had'a baki gurin cewa"ya lafiyar yarinyar nan ?Kamar bazai ce Komai ba har sun fidda rai da zai Yi mgn suka ji yace "alhamdulillah har yanzu dai tana bacci ".Shiru sukayi dukkaninsu babu wanda ya sake yin magana sai numfashi da suke fitarwa idanunsu na kan tv yayinda anas ke son yi magana akan zahra zata zo dan tun safe ya kirata ya sheida mata abinda ke faruwa sosai ta daga hankalinta ,amman yadda yaga jaguwa ya had'e rai yasa ya kama Kansa ya ciro kwandala a cikin aljihunsa ya murza akan center table din dake gabansa take ta fara juyi a karshe ta kife ya tsurawa kwadalar Ido kawai yana kallonta ."
Suna zaune sai ga zahra ta shigo cikin doguwar riga marun colour tana karairaya tana gama tsayuwa a tsakiyar falon onexpecting taji jaguwa ya mike ya ɗauketa da wani gigitacen mari da sauri ta dafe daidai Inda ya mareta tana dubansa "ki fita rayuwata Zahra , ki tsaya matsayinki" zahra tace "me yayi zafi haka Adnan ? "dazu anas ya kirani yake fad'a min abinda kake zargina akai amman ka sani ......
"wani marin ya K'ara kifa mata sai data ga taurari masu duhu "amman kasan me din ubanki ?"me zaki fad'a min na yarda dake maci Amana kawai, daga karunwaci kin koma bin bokaye saboda ke katuwar jahila ce wannan ya zamo Karonki na farko ya Kuma zamo na karshe babu ruwanki da yarinyar nan wallahi muddin wani abu ya sameta sai na kasheki da hannuna , wai ma meye hadinki daita? ni kike wa kwakwa ni Kuma nace banayi ko dole ne sai na aureki ?ya tambayeta yana sake tsare girar kasa da sama. "duk ta rud'e sai wani gumi take fitarwa cike da matsanacin firgici tace "ka yarda wallahi babu hannuna ci...ciki " ta k'arasa maganar tana in Ina gani yadda yake mata mugun kallo yasa ta soma neman hanyar guduwa dan kallon fuskarsa kad'ai ya Isa ya tsorota mutu da sa mutun ya shiga hankalinsa sam sam babu alamun wasa atare dashi kafa yasa mata sai gata ta zube kasa bisa gwiwowinta tana kallonsa cikin muryar kuka tace "ni kad'ai kake bi bare kayi tunanin nice na aikata abinda kake zargina? Ina Jin tsoron Allah Adnan bazan iya ......"shiiiiiiiii ! banason Jin komai d'aga bakin makira irinki ."
"Zahra!
ya kira sunanta muryarsa a tsarke ta zuba masa Ido tana amsawa da" Na'am "babu tsoron Allah"n daya halicceki acikin zuciyarki dan hk nasan zaki iya aikata komai akan cikar burinki ,masu kyakkyawan zuciya da tsoron Allah su suke tsoron aikata mugunta ke Kuma baki da ko daya aciki "yayi shiru yana numfasawa sannan ya cigaba da mgn "daga yau idan kika sake shiga harkata zan mugun baki mamaki kuma dan Allah karki cire hannunki akaina da duk wacce zaki ganni idan Kuma kinki yiwa kanki kiyamul lail zaki hadu da cuuttuka ,sannan zan ganar dake da yaren da zaki gane yana kaiwa nan yace " ki tashi ki bani guri bana son ganin wannnan fuskar taki ".
"naji zan tafi amman kayi hakuri kayi bincike sosai akai muddin aka tabbatar maka Ina d'aya daga cikin wad'an da suka aikata wannan laifin ka min hukuncin da yafi wannan "wani bincike zanyi bayan nasan babu me shegen naci a rayuwata kamarki ?ya matsota sosai ya cafki makoshinta idanunta suka yo waje "ki fad'a min gsky kece kikayi mata asiri ?ta shiga girgiza Kai alamun a'a "bazaki fad'a gsky ba ? girgiza masa Kai ta sake yi anas ya taso ya rikesa karka yi kisan Kai Adnan "ka rabu daita karka kashe yar mutane "kace mata ta fad'a min gsky da bakinta
"me yasa tayi wa yarinyar mutane asirin data kawo min kanta gareni na aikata abinda ban yi ra'ayi ba? ya fad'a yana filinging daita sauran kad'an kanta ya bugi bango anas yayi saurin riketa yana bawa jaguwa hakuri .wani sanyayyayen numfashi Zahra ta sauke da kyar tana jin dadi aranta burinta ya cika tunda ya kusanceta rabuwarsu tazo duk nacinsa dole su rabu ,abokansa kuwa da Ido suka bisa suna mamakin jin furuncinsa ,me yasa kika yiwa yarinyar mutane asirin da ta kawo min kanta gareni na aikata abinda ban yi ra'ayi ba? suka tambayi zukansu suna dubansa fuskokinsu d'auke da qarin bayani .
"Anas kaji abinda yake fad'a , dan jarabansa ya ciyosa ya kwana da yarinyar mutane shine zai d'aura laifina akaina , kasani babu hannuna acikin wannan aika aikan " ,jaguwa juya mata baya ya tsuke fuska alamun bai son jin komai daga bakinta muryarsa a tsawace yace "anas ka sallameta daman Kaine kake gayyatota zuwa gidan nan " da sauri anas ya riko hannunta ya nufi kofar fita daita "anas ka sakeni na fahimtar dashi gaskiya "bazai ta'ba fahimtarki ba kije kawai dan Allah nima daga yau karki sake kirana na yanke muamula dake bazan Kara kiranki ba banason na samu matsala da abokina, aminina ,farincikin rayuwata .
fixge hannunta tayi daga cikin nashi adaidai lokacin da suka fito zuwa haraban gidan ta tsaya a hassale tana dubansa "ka dade baka daina kirana ba ,bazan kiraka ba shima bazan kirasa ba Amman na rantse sai Adnan ya dawo ya nemeni da kansa ka rubuta ka ajiye a Inda bazai goge ba ..."
Mmn sudais
💗💗💗💗💗💗
KUSKUREN BAYA
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
PAID BOOK
FREE PAGE
WRITING BY
AYSHA .A BAGUDO
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukata karanta shi ya tura 500 ta wannan account number din 1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan a tura sai a turawa wannan number+234 703 534 8686
alert domin tabbatar da an tura ko wannan number 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi sai a tura ta wannan number 08059623096 kada ayi vtu a number MTN ,domin sauraran littafaina a tuntubi Channel dina ta Hausa bakwai.
🅿️16
"Kenan da gaske kin aikata abinda yake zarginki akan shi ?" idanunta da suka rikid'e sukayi jazur ta cigaba da kallon anas wanda yake tsaye a gabanta yana huci kamar zaki dasu "eh na aikata Kuma bazan tsaya iya nan ba ta fad'a a matukar fusace " zan d'aura daga Inda na fara , zan tabbatar da na azabtar da yarinyar nan da azaba mafi muni , ba dai duk akanta ya mareni ba?" ya mareni akanta anas , ya ci mutuncina akanta ya wulakantani a rita lori akanta ,wallahi ya kwana da sanin zan fanshe duk abinda yayi min akanta 'zan mata azaban da rad'ad'insa yafi zafin dalma , zan rikirkita mata rayuwa zan....."saurin dakatar da ita yayi ta hanyar buga mata wata razananniyar tsawa yana cewa "enough !
"karki fara zahra dan bazaki ci riba ba , wad'an da ma suka fiki sunyi sun hakura sun barshi dan ba zasu iya ja dashi ba domin shi din dokin tsere ne bazaki iya karawa dashi ba ,shi guguwa ne idan ya tashi zai tashi da rayuwarki , zai juya rayuwarki daga sama zuwa kasa ki rasa gane kanki ......"ya k'arasa maganar yana nuna da yatsansa .
"Zahra !
Ya kira sunanta cikin tsananin 'bacin rai " ki tsaya daga Inda kike idan ba haka ba ki shiryawa gudun tsere da mutuwarki , dan akan ki ta'ba wannan yarinyar gara kin rungumi mutuwa da hannuwanki." Adnan yace bai sonki ya nuna azahirin bai sonki, tunda ba tare aka halliceki da soyayyarsa ba ya kamata ki hakura ki rabu dashi ki tsira da rayuwarki dan akan yarinyar nan ba zai raga miki ba zai iya destroyed din rayuwarki, ki manta da kin ta'ba muamula da Adnan a rayuwarki ". wannan shine abinda zan fad'a miki idan Kinga dama ki d'auka ki cire hannunki akan mugun nufinki ki zauna lafiya idan kinga dama ki cigaba kece zaki kare rayuwarki a nadama ".
Tunda ya soma magana zuciyarta ke bugu very fast ta kafe shi da idanunta ta cigaba da kallonsa ,a yau gbdy babu sauran burbushin tausayin data saba hangowa acikin kwayar idanunshi a duk lokacin da hargitse ya shiga tsakaninta da adnan , yau ce rana ta farko da anas yayi hannun riga daita . ka'fafunta ne suka kasa d'aukarta ta durkushe kasa bisa gwiwowinta tana wani irin kuka tana cewa "kasan kuwa yadda nake ji a zuciyata ? "maganganunka suna huda min zuciya, me yasa zaka nisantani da Adnan ? ya kalleta cike da matsanacin bakinciki dan gbdy ya fuskanci bata da niyyar saduda shi kuma a yau gbdy babu wannan tausayin da yake ji nata, da tayi silar rabashi da masoyinsa da yafi qauna akan komai a rayuwarsa gara ya yakiceta ta karfin tsiya sunyi hannun riga daita "amman kai kana ganin zan iya rabuwa da Adnan dan yace bai sona ?ko kana tunanin zan iya daina sonshi ne ? Me yasa zaka ce na manta da soyayyata ? "haba anas idan kayi min haka baka kyauta min ba ,yanzu adalci ne daka nuna kafi bukatar rabuwarmu dashi ?
ya gyada mata Kai alamar"eh! " cikin firgici da tashin hankali ta shiga girgiza masa kanta sannan ta cigaba da magana "ada tunanina kana sona da Adnan ne a she duk ba haka bane karya ne baka qaunata dashi ? to bari kaji in fad'a maka maganganunka ba zai sa na fasa duk abinda nayi niyyar aiwatarwa ba ko da kuwa zan mutu ." ta k'arasa maganar tana sheshekar kuka "karki fasa zahra bazan baki hakuri ba kije kiyi duk abinda zakiyi amman Ina tabbatar miki wahalar banza zakiyi dan ba zaki yi nasara ba hasarar kudinki da lokacinki kawai zakiyi yana gama fad'ar haka yace ki tashi ki 'bace min da gani yadda Adnan baya son ganinki nima hakan take gareni ".
Batace masa komai ba ta mike da kyar ka'fafunta na rawa ta juya ta soma tafiya hawaye masu zafi da ciwo na sake zubo mata akan quncinta , zuciyarta bata ta'ba karaya ba atun sanda jaguwa yake furta mata kalma bai sonta sai a yau da anas ya sake maimaita mata , duk da ba yau ta saba jin kalmar baya sonta daga bakinsa ba amman ciwon na yau daban ne a cikin zuciyarta sannan ya mugu mugun tsaya mata arai ya d'aga mata hankali ya dagula mata lissafin tsarin rayuwarta data shirya dashi , Kuma duk runtsi duk wuya sai tayi abinda zai furta mata Kalmar so da bakinsa , sai ya dawo yayi kuka da idanunshi yana rokon ta amshi soyayyarsa, ko zatayi yawo tsirara sai ta aureshi idan Kuma hakan bai samu ba zata saka rayuwarsa ta quntata . "
anas ya yabi bayanta da kallon bakinciki ,ya rasa wani irin naci ne irin nata , mutun ya nuna miki da Ido ya nuna miki da jikinsa har ya fito ya furta miki amman ki tsaya kina hauka akanshi, tsaki yaja ya juya ya shiga ciki falon zuciyarsa cike da takaicin abinda zahra tayi . Inda ya bar jaguwa anan ya iskeshi tsaye a tsakiyar falon rungume da duka hannuwansa a qirji sai faman cika yake yana batsewa .
jikin anas a sanyaye ya samu guri ya tsaya kusa dashi ya dafa kafad'arsa, jaguwa ya juyo ya kalleshi yana cije lip's dinsa na kasa a hankali ya sake juya masa baya yana furzar numfashi kana yace "ka gama munafurcin ?wani irin bugu qirjin anas yayi da karfi " a hankali sautin muryarsa ya fito yana cewa"idan zanyi munafurcin kowa bazanyi naka ba, idan zan cuci kowa bazan cuceka ba, kama daina min irin wad'an nan abubuwan dan wallahi suna Kona min rai da mugun tayar min da hankali ".
Jaguwa ya waigo ya fuskanci anas sosai yana sake furzar da iska mai zafi daga bakinsa "muddin kana son zuciyata ta cigaba da amincewa da Kai sannan na daina fad'ar haka akanka anas ya zama dole sai kayi hannun riga da zahra bana qaunarta bana qaunar ganinku tare muddin zaka kasance dani sai dai ka za'ba ko ni ko ita ? taku daya biyu yayi ya matsa daga kusa da anas yana tafiya a hankali still yana rungume da hannunwansa.
"jaguwa !
anas ya kira sunanshi cikin yanayi na firgici da tashin hankali , idanu kawai jaguwa ya tsura masa batare daya amsa masa ba" shakka babu duk duniya nafi sonka akan kowa, Ina qaunarka fiyye da ni kaina maganar zabi ma bata taso ba dan kasan waye zabina" yayi mgnr hawaye na ciccikowa a idanunshi "Kai ne zabina Adnan Ina sonka fiyye da kowa da komai nawa " tautausan murmushi jaguwa ya sakar masa yana mai Jin sanyi acikin zuciyarsa , cike da farinciki ya mika masa hannunsa
da sauri anas ya mika masa nasa hannun suka rungume juna suna sakin numfashi atare , jabir , jubi ,kamil da suke zaune duk sukayi shiru suna dubansu dan ba wannan bane karon na farko da suke samun matsala a tsakaninsu kuma cikin kankanin lokaci suke daidaita kansu.
kuka sosai anas yake jaguwa na shafa bayansa kamar wani karamin yaro "is okay anas na sani , nasan kana qaunata da gsky kmr yadda nake qaunarka am really sorry for my active har cikin zuciyata nake jin qaunarka , Kai zinari ne acikin zuciyata Ina sonka anas "Nima Ina sonka kyakkyawan abokina had'e da qauna mai karfi , cikin kankanin lokaci komai ya daidaita a tsakaninsu suka samu guri suka zauna cikin sauran abokansa nan hira ta barke a tsakaninsu .
su jubi sun so kwarai su sake samun qarin haske akan maganar jaguwa ta d'azu akan yarinyar amman yaki bada dama amman duk da haka sai da kamil yayi magana Cike da kulawa kamil yace "anyi maka tambaya akan yarinyar nan ka wani share mutane " to me yasa meka a goshi Kuma ? ko baku lura da goshinsa ba ?ya fad'a yana kallonsu d'aya byn daya ,kun san halin miskilancinsa ai ba lallai ya fad'a ba ni tun jiya na gani sanin halinsa yasa na share inji cewar jubi .
"ku manta da wannan maganar idan akwai wacce ta fita mahimmam ku kawo muyi kawai " anas ya fad'a dan jaguwa wayarsa ya d'auka yana duba sakonin mutane , basu tashi a falon ba sai da suka tsara yadda tafiyarsu Ogun state zata kasance a gobe .
" Yadda suke tsara komai akan aikinsu haka Suma jami'an tsaro dana sirri suke shirya yadda zasu kamasu a yanzu ma Asst Commissioner of police ne ya kira layin d .c .p baba abare wato lawan numan byn ya d'auka suka gaisa ya fara magana cikin zafin rai " wannan mutumin bai kamata a barshi har zuwa wannan lokacin batare da anka mashi ba , yayi mgn tare da yin shiru "eh to haka ne amman abinda nafi bukata a Kara saka Ido sosai akan duk wani motsinsa da shiga da fitarsa bama iya rayuwarsa ta fashi ba hatta rayuwarsa ta duniya ma sai na tabbatar da ta ru'bance idan yazo hannu , sun dauki lokaci mai tsawo suna tautaunawa akan jaguwa da yaransa kafin daga bisani suka yi sallama. "
*****
"Nazifi haka mukayi da Kai ?a she baka da amana ban sani ba ? ya rufe shi da fad'a ta Inda yake shiga ba ta nan yake fita ba cike da matsanacin firgici nazifi yace "dady me nayi Maka ? bangane me kayi min ba ? ya tambayesa yana maxurai ",ni zakawa tambayar rainin hakali ? to yau duk a zaune naga Ibrahim alhalin na fad'a maka bana son ganinsa a zaune sai akwance dan lokacin tashinsa bai yi ba tukun "sai lokacin nazifi ya fahimci rashin amanar da yayi masa . ya shafa sumar Kansa yana cewa "Allah dady Ina iyakacin k'okarina Ina yin komai yadda ya kamata alluran da na saba yi masa shi nake masa haka zalika maganin da yake sha shi nake kawo wa ban canza ba ".
"wannan karya ne nazifi "da gaske dady baza yi maka haka ba ,ai duk abinda kace shi zanyi tunda ka zabi abarshi cikin wannan yanayin ni me zaisa naki?" ai ya zama dole nabi
duk wani umarninka bayan haka ma duk sati sakokan na shigowa account dina ,nafi tunanin yawon magani da allurar da ake masa ne yasa suka daina aiki ajikinsa Ina ganin me zai hana a canza masa ? ". ya fad'a yana tsine masa acikin zuciyarsa domin kuwa mutane masu hali irin na alhj Tahir sam basu ya kamata su haifi d'a irin Ibrahim ba. "to shikenan na d'auka kana cin amanata ne ?Ina ai bazan ta'ba cin amanarka ba wannan ai sirri ne a tsakaninmu " alhj Tahir yayi murmushin jin dadi yana cewa
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 17 Chapter of 62