zafi rau a hankali ta dinga shafa mata jiki har ta farka wani irin nauyi taji jikinta yayi mata ta Kasa motsa jikinta ,da kyar da taimakon mumy ta mike ta rakata har bayi ta hada mata ruwa wanka sannan ta fito ta tsaya jiran fitowarta cikin kankani lokaci ta fito ta shirya
Yayinda mumy ta jawota zuwa falo ta shiga kitchen da kanta ta daura mata ruwa zafi ta kawo mata ta zauna a gefenta tana mata sannu bayan ta sha ruwan lip ton ta numfasa tace "mumy wallahi bani da karfi juya juya nake gani "to ai kece ki tsaya a duba lafiyarki a hospital kinki kika matsa lallai sai kin fito ai ga irinta Nan "wallahi mumy naji jiki jiya da daddare banyi bacci ba kwana nayi ciwon ciki "shine dan wauta baki bari mun sani ba yanzu da wani abu ya faru dake fa ?" karki Kara min irin wannan ganganci gashin nan har wata katuwar rama kika yi Ina fatan dai yanzu bakya Jin komai "?
Ta gyada mata Kai alamun "eh .
Mumy ta sake tashi ta kawo mata abinci da kyar ta tura tana kammalawa lokacin mumy ta mike tana fad'in "ki tashi kije kiyi sallah ta amsa da "to" ta wuce d'akinta mumy ta kwashe kayan ta maida kitchen bata tsaya jiran masu aiki ba sannan ta nufi d'akinta dan tayi sallah itama ."
Bayan tanwer ta Idar da Sallah wayarta ta janyo daga inda tayi sallahr ta shiga turawa jaguwa Sako.
_Idan ma Wani aiki ne ya rikeka why not ka kirani ka fada min zuciyata ta Samu natsuwa ,Ina da kwarin gwiwa cewa lallai kana sona me yasa ka juya min baya ta hanyar sakani cikin damuwa, ba sai na kai karanka gurin Allah ba but ka Natsu sosai kayiwa kanka hisabi akan abinda kake Shirin aikatawa_
Shiru tayi bayan ta tura sakon hawaye na zubo mata akan quncinta wanda take jin zafinsu yau ita soyayya tayi wa Kamun kazar kuku ?" hakika soyayya bata kyauta mata ba tana son wanda bai damu daita ba ..."
Tun daga wannan lokaci al'amura suka sake kwance ma tanwer ta rasa kanta ta rasa meke damunta na rashin son kamshin d'akinta da rashin son cin abinci ,hatta turaren d'akinta wari yake mata bata son kamshinsa ga yawon tashin zuciya ga wani ciwon ciki safe da Jiri wani lokaci jikinta yayi zafi dan kanshi Kuma ya sauka batare data sha magani ba duk ba wannan bace matsalarta "me yasa jaguwa yaki d'aukar kiranta duk da ta tura masa sakoni Kashi cewar itace ya d'auka Ko yayi reply dinta , me yake nufi daita ?, shikenan ita dashi sunyi hannun riga ?" shikenan ya mantata arayuwarsa bayan ya rabata da budurcinta ?
Kai! kai !! karya ne ba shikenan ba dan dole zai nemeta ko ba yanzu ba domin jikinta na bata zai dawo gareta akwai tarin qaunarta acikin zuciya da gangar jikinsa "wayyo Allah na zan mutu Adnan idanuwana da zuciyata sun gaza jurewa rashinka na yanwanki biyu danayi babu Kai. tunda ta dawo gida take kunshe kanta a d'aki mumy da dad sun rasa gane kanta mussaman rashin fitowarta da walwalarta ko neman abinda zataci batayi nan fa hankalinsu ya tashi suka tasata gaba suna mata kuka "ki fad'a mana maye damuwarki tanweer mu iyayenki ne zamu fahimceki baki da wad'an da suka fi tunda kika dawo baki da walwala baki cin abinci baki komai da kika Saba please ki tausayawa rayuwarmu mumy ta fad'a tana rike yatsun hannunta .
dady ma kusan yafi mumy shiga damuwa sai dai shi ya kasa cewa komai domin dai idan ya bud'e baki to Shima kukan zaiyi mata ".
Numfasawa tayi tare da sanyawa jikinta jarumta tace "babu komai fa ,atare suka girgiza mata kansu alamun basu yarda ba "Allah mumy idan akwai abinda ke damuna zan fad'a muku kawai dai bana Jin dadin jikina ne yanzu haka Ina treat din kaina da magani malaria ne , inshallahu nan da wasu kwanaki zan dawo daidai ".
atare suka sauke naunayen ajiyar zuciya maganarta ta shigesu tunda sun san ba lallai agurin Mai kyau yanfashin suka ajiyeta ba.
Ta tsurawa iyayenta Ido tana Jin kamar ta fad'a musu gaskiyar halin da take ciki na soyayyarta da jaguwa amman tana Jin tsoro dan bata san yadda zasu d'auki abun ba, ta dai San duk yadda suka Kai ga qaunarta bazasu ta'ba barin tayi soyayya da dan fashi ba bare har su bashi aurenta , idan ma fa yana sonta Kenan mutumin da bai qaunarta ," kaico dina ni tanwer , ita kanta bata hangowa kanta dacewarsu ba Amman ya ta iya da sharrin soyayya abincin wani gubar wani ita kuma nata qaddarar Kenan soyayya da dan fashi , Allah ka rabamu da muguwar qaddara. "Ameen "taji iyayenta sun furta a lokaci daya sai lokacin ta fahimci a fili tayi maganar Basu kawo wa ransu komai ba dan a tunaninsu saboda rasa budurcinta datayi yasa ta fadi haka sun dade tare daita kafin daga baya duk suka fita suka barta da rukayya ."
*******
A yau asabar gidan shiru ba kamar da ba da gidan ke cika makil da mutane dabam dabam Kuma kowanne zaka Kalla fuskarsa cike take da farinciki da annushuwa a baje a falo aci wannan asha duk abinda ake so a daura wannan a sauke daga safe har dare basu da Hutu daga ita har masu aikin gidan a tsaye suke yini saboda hidimar mai gidan da abokansa.
a falo ta wuce wasu abokan minister daka zo tun awa uku data wuce ta shiga zuwa dakin minister ,dad na zaune a d'akinsa Shi kadai shiru zuciyarsa nayi masa Saka kala kala tunda yasan anyi wa tanweer fyade ya tattara komai ya watsar,hatta nombobin agent dinsa masu kawo masa mata tuni ya gogesu a wayarsa , mumy ta karaso kusa dashi ta samesa zaune shiru ya rafka tagumi tace "ya ka zauna shiru baka shiga wanka bare ka samu damar fitowa ga jamarka can sun hallara yayi dan gajeren tsaki yace "rabani dasu duk gayawar tsiya ne suzo su cika mutane da surutu marasa amfani ta numfasa tace "yaushe ka fuskanci surutu suke damun mutane dashi "? Yayi shiru "na godewa Allah da ka fahimta hakan dan ada ka makance akansu bakaji baka gani kowa sai su numfashi ya fesar batare dayace komai ba.
Ta cigaba da magana to dai ka d'aure ka fito ko dan hira kuyi dasu tunda an rigada an Saba "to shikenan naji jeki kira min tanweer kice ta biyo ta kofar baya saboda su ta mike ta nufi dakin tanweer ta tura kofar alokacin kakarin amai ya fara dibar hankalinta cikin fargaba ta nufi kofar bayi ta Murda ta Bude "tanweer !.
Tana durkushe cike da ciki kamar zata mutu kan mumy ya sake daurewa domin bata ta'ba ganin tana kwarara amai haka ba ,ko rashin lfy take bata amai sai dai zafin zazzabi dan haka ta nufota da sauri ta dafata "me zan gani haka tanweer har yanzu malaria ce "?
Bata iya amsa mata ba tana tsaye har ta gama kakarin ta kuskuren bakinta hade da fuska ta fito waje batare data kula mumy ba kan gado ta fad'a tana numfarfashi .
mumy ta biyota a matukar fusace tasa hannu ta birkitota "bakya Jin Ina Miki magana ne?"nace malaria ce har yanzu take damunki har kike amai haka ?idanunta jajur cike da kwalla tace cikina ke min ciwo "tun yaushe ".
"Yau kwana uku shiru tayi kafin daga bisani ta kamota zuwa byn gidansu cikin haske , gabanta na faduwa ta kamo hannayenta tana duddubawa sannan ta gwale idanunta ta duba cikinsu a matukar tsorace ta tambayeta "ke !kina yin alda kuwa ?
Tanweer tayi shiru tana zazzaro Ido sai lokaci kwakwaluwarta tashiga caji yaushe rabon data Yi alada a tunaninta wata na uku kenan idan batayi wannan watan ba.
Nan take gabanta yayi wata irin mummunar faduwa wanda yasa jikinta ya kamata rawa sai dai cike da dakiya tace "ni wata uku kenan ta k'arasa maganar tana fashewa da kuka "shine dan ubanki ake ta faman ki bari ayi Miki wanki mara kika ki kina so ki haife shege jinin tsinannu ne"?
nan fa tanweer ta kideme ta gigice tabbas ciki gareta sai yanzu tunaninta ya hasko mata hakan, koda take gidan jaguwa tana zazzabi amman bai Kai na yanzu ba mumy ta tsura mata Ido jinita na Kara hauhawa da sauri ta juya ta barta tsaye ta nufi dakin dady tana kuka tana salati "Mai akayi ?ya tambayeta cikin tsananin damuwa da tashin hankali"alhaj mun shiga uku ka d'auki tanweer ka kaita asibiti ayi mata abortion yanzu yanzu "abortion Kuma ?"eh abortion dan kuwa wallahi ciki ga tanweer ....."
tashi yayi ya mike tsaye tare da fad'in "me ?!
Hawaye suka Kara zubo mata a hankali ya koma ya zauna saboda juyan dake dibansa bakinsa na karanta salatin manzon Allah gbdynsu tsit sukayi na tsawon lokaci sai mumy dake zubar da hawaye bai yi auni ba yaga numfashinta na fita da kyar da sauri ya tarairayota zuwa jikinsa Yana Kiran sunanta "Zainab !Zainab !!Dan girman Allah karki Kara min tashin hankali akan Wanda nake ciki ya jawo Goran ruwa ya zuba a hannunsa ya yarfa mata ya cigaba da shafa mata ruw a fuskarta a hankali har ta dawo haiyacinta ta bude idanunta tana kallonsa sannan ta sake fashewa da wani sabon kuka da take Jin radadinsu har cikin zuciyarta Nan take tausayinta yasa hawayen minister suka zubo bakinciki kamar ya Kai mumy lahira "kiyi hakuri ki kwantar da hankalinki Zainab wannan jarabawa ce daga Allah Babu Wanda ya Isa ya Hana Hakan faruwa ,ban son ki cigaba da tsananta damuwa domin zata jefaki cikin mummunar matsayi ki dogara da Allah shine zai magance komai mu ma godewa Allah da qaddara ce ta fad'awa tanweer ba bin Maza take ba.
" Aranshi yace Ina ma zan iya goge *kuskuren baya* dana aikata hakika na tafka kuskuren gashi ya shafi yaruwar dilon diyata .Ta goge hawayenta tayi iya yinta ta tashi zaune ta kasa yace karki damu da sai kin tashi yanzu kiyi kwanciyarki ki huta bari na kwaso magunhunaki naga Wanda ya dace ki Sha .
Ya mike da sauri wani duhu ya rufe idanunshi baya ganin komai sai wasu taurari dole tasa ya dawo ya zauna Yana furta hasbinallahu wa ni'imal wakil yayi ta maza ya sake mikewa mumy tace "ka zauna karkaje ka fadi ka nakasa bai kulata ba ya fice dan yafi bukatar rayuwarta akan tashi .
bai dade ba ya dawo d'akin da kwadon magungunanta ya zauna yana bincikawa jikinsa na rawa
Saboda bacin rai Amman haka ya daure ya d'auki kanta ya d'aura saman cinyarsa yana mata sannu ya goge mata kwalla sai daya kwantar mata da hankalin sannan ya mike ya nufi dakin tanweer cikin tsananin tashin hankali.
tana kwance tayi ruf da ciki ya tsurawa bayanta Ido daman wannan shine karshen masu halin munafurci irin nasa, karshen mai son zuciya kenan, Kuma duk Wanda yaci bashin Allah sai ga karshensa tun anan gidan duniya ,sannan karshen mai irin halinsa kenan dansani.
a yanzu ya gane kuskurensa da yayi tsawon shekaru yana aikatawa a boye ,ya goge kwallan data zubo masa ya kirasa sunanta "tan!
Ta juyo a natse tana fuskantashin "Tashi ki shirya muje hospital a cire miki cikin " da sauri ta shiga girgiza masa kai alamun bazata zubar .Wani irin juya ne ya soma dibarsa nan kuma ya shiga furta Kalmar Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun yana maimaitawa cikin haka mumy ta rarrafo ta shigo d'akin adaidaita lokacin da dady yake sake bawa tan umarni "ni dady Abar min abuna ina so ..."
"Kina son me dan ubanki ?"me zakiyi dashi ? kina hauka ne Ko kin fara Shaye shaye ne ?"tayi mata tmbyr ajere juya na sake dibarta kafin kace me tuni ta soma yin kasa da sauri tanwer ta sauko daga kan gado suka hadu da dady a lokacin da take kokarin kaiwa Kasa da kyar take fidda numfashi bakinta na rawa tace "tan..! tan !! ki amince a cire cikin ...."
Assalamu alaikum yan'uwa barkanmu da wannan lokacin jama'a , ku taimakawa wannan baiwar Allah Mai suna rukayya wacce ta kasance budurwa ce tana fama da ciwon no-no tsawon shekara daya Kenna saboda iyayenta basu da halin da zasu dauki nauyinta yasa brest dinta d'aya fara lalacewa , rukayya tana zaune ne a garin Kaduna a unguwar kanawa tare da iyayenta dan Allah ku taimaka mata saboda Allah da darajan fiyayyen halitta annabi Muhammadu sallallahu alaihi wa sallam ga masu bukatar taimakawa ga account number nan 1438775094 Aishat Abdullahi access bank .Domin Jin qarin bayani a tuntubi wadan nan numbobin
07039569430
07037450698
08059623096
Allah ya bada iKon taimakawa .
Mmn sudais
💗💗💗💗💗💗
KUSKUREN BAYA
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
PAID BOOK
WRITING BY
AYSHA .A BAGUDO
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukata karanta shi ya tura 500 ta wannan account number din 1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an tura sai a turawa wannan number+234 703 534 8686alert domin tabbatar da an tura ko wannan number 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi sai a tura ta wannan number 08059623096 kada ayi vtu a number MTN ,domin sauraran littafaina a tuntubi Channel dina ta Hausa bakwai.
🅿️25
zama jaguwa ya cigaba da yi rike da waya zuciyarsa na zafi da farfasa a qalla ya kusan minti goma yana tunanin maganganunta," bai san me yasa zai damu kansa akan cikin ba , cikin ma da bashi da tabbacin tana d'auke dashi .
wani dogon tsaki yaja yana sake kiran layinta , babu 'bata lokaci ta d'auka qirjinta na bugawa fat fat "Ke ni zakiwa wulakacin ? "
shiru tayi taki ce masa komai sai dai zuciyarta ke wani irin bugawa da sauri sauri .
"har kin isa ki dinga farfad'a min magana son ranki ?"
ya sake tmbyrta tare da jan tsaki "har ma da kashe min waya ? "shiru tayi still cikin tsananin tashin hankali tana tunanin abinda zata sake fad'a masa wanda zai sake d'aga masa hankali sai dai bata kai ga tattara abinda zata fada masa ba ta tsikayi muryarsa na dukan dodon kunnenta.
"dan kinga ina lalla'baki shine zaki d'auka ko ina jin tsoron ki haifi cikin ne ? "to kar allah yasa ki cire cikin ai cikin ba ajikina yake ba idan akwai shi kenan dan haka ko ki cire ko Karki cire ruwanki sannan matsalarki ce bata Adnan .
ba Adnan za'a dinga kwatance dashi ba , sannan ba shi zai rasa mai aurensa ba . aurenki ne dai bazan yi ba kije ki nemi abokin rayuwarki dan ni tuni na amince da zabin mahaifiyata aikin banza Kawai ki jira ki gani idan zan sake nemanki".
ya k'arasa maganar yana jan dogon tsaki sannan ya katse Kiran yana fidda wani wahalallen numfashi ,yasa hannunsa d'aya ya dafe goshinsa yana jin zafi da ciwo a ransa, shiru yay na second goma qirjinsa da gangar jikinsa na rawa gbdy sai yaji kimai ya tsaya masa guri daya ya shiga tunanin abinda yayi mata a ganin zuciyarsa bai kyauta mata ba daya farfad'a mata son ranshi dan bata cancaci ya fad'a mata magangun daya fad'a mata ba ,ita din wata aba ce mai daraja da kima a rayuwarsa. amman daya tuna irin maganganun data fad'a masa da irin mugun fatan da tai masa a mintunan da suka gabata sai ya dawo haiyacinsa , komai ya dawo masa daidai, qirjinsa da gangar jikinsa da suka d'auki rawa suka daidaita yaga mai ma yayi mata ai bai mata komai ba . "
Bangaren tanwer kuwa maganganunsa sun daki Kunnuwanta sosai sannan sun wuce har cikin zuciyarta, gbdy ya kunno mata wutar damuwar da take dannewa acikin zuciyarta ,Kawai sai ji hawaye yazo idanunta ya fara zuba akan kuncinta, a hankali ta fara rare kuka mara sauti qirjinta na zafi "Allah ka gani ba wai nayi masa haka dan na wulakatanshi bane , "na yi dan na raunata zuciyarsa,na yine ko zai saduda ya zubar da makamansa ya canza rayuwarsa darajan tace bata zubar ba suyi aure ,ashe wata sabuwar maseefa ta jefa kanta ciki tayi maganar a fili tana sheshekan kuka "wayyo Allah ka d'auki raina na huta da wannan rayuwar da nake " wani zafi take a kahon zuciyarta sam ba taji kashi daya na son da take masa ya rugu sai ma qaruwa da son shi yayi acikin zuciyarta , tana sonshi muddin zai aureta zatai confuse din iyayenta akwai hanyoyi da dama da idan ta bullo dasu dolensu su hakura su rungumi nata qaddarar su aura mata shi amman shi kuji abinda yake fad'a mata har ma ya amince da zabin mahaifiyarsa ita ko oho zama tayi ta cigaba da rera kukanta tare da rafka uban tagumi cikin zullumi da rashin sanin madafa ."
tana cikin wannan halin rukayya ta shigo d'akin ganin idanun tanwer na zubar da ruwan hawaye yasa ta karasa shigowa d'akin da sauri tana cewa "lafiya tanwer menene Kuma ?"
Rukayya ta samu guri gefenta ta zauna ta riko hannuwanta duka cikin nata tana dubanta cike da tausayawa , runtse idanunta tanweer tayi sai ga wasu hawayen sharrrrrr."
"wallahi ina cikin damuwa rukayya ,ina cikin tashin hankali na rasa yadda zanyi da wannan rayuwar da nake ciki , komai ya canza min rukayya ina ma rayuwata ta baya zama dawo , "ina ma ban dawo kasar nan ba"..
Rukayya ta numfasa tace" haka ne kina cikin damuwa da jarabawar rayuwa tanwer amman kiyi hakuri da sannu komai zai daidaita ,"sannan kiyi kokari ki rage damuwar nan duk da tasan komai dake faruwa daita amman taki fitowa ta bayyana mata .
" ki kara imani da qaddara komai ya faru da bawa a rubuce yake bawa bai isa ya gujewa qaddararsa, rayuwar bawa tana tattare da qaddarori ne kawai dai Allah ya bamu Ikon cinye jarabawarmu rukayya ta fadi haka ne dan takaita maganar .
"nima ina son na rage tunanin Adnan acikin zuciyata amman na rasa dalili da tunaninsa kullum sai gaba yake , wallahi ina masa wani irin so da bansan ranar da zan daina shi ba , kuma bazan taba fidda raina akanshi ba sai ranar dana ji an shafa fatihan aurensa ta k'arasa maganar tana mai runtse idanunta."
"Aure ma zaiyi shine kika zauna kina tunaninsa "? tanweer ta gyada mata kai alamun "eh! "gskiya dai ni aganina ki manta dashi kawai ki cigaba da rayuwarki tunda ma aure zai yi ki manta shi kiyi addua sai Allah yayi miki sauyi na alkhairi .
Tanweer ta gyara zama tana kallonta "na fahimceki yar'uwarta zan cigaba da addua na gode da shawarki "to amman banason kina damuwa, tanweer ta sake yin murmushin wanda ciwonsa yafi kuka gbdy kana kallonta kaga damuwa attare daita duk ta fita haiyacinta soyayya ya canza mata rayuwarta muryarta a raunane tace "na gode rukayya inshallahu zan daina .
." Ki kwantar da hankalinki kinji dan Allah karki sake daga hankalinki akansa Ki fara nemi zabin Allah kiyi k'okari kiyi istahara domin neman zabin Allah "rukayya ko ya min wani irin adduar istaharar da zanyi".?
"zan koya miki , mu nemi zabin Allah bamu sani ba ko akwai alkhairi atsakaninku idan babu idan kinyi zaki ga komai ya tafi daidai amman Karki yarda ki bari wani yayi miki kiyi da kanki ,zaki iya yi kullum idan zaki kwanta raka biyu zaki yi sai kiyi sallama sai kiyi addaurki ta istahara inshallahu zaki ga cigaba a rayuwarki hatta wannan radadin da kike ji akanshi zaki rage jinsa ."
Jiki a sanyaye tanwer ta janyo handbag dinta ta Ciro biro da farar takarda ta mikawa rukayya.
ta amsa ta fara rubuta mata adduar "Allahumma inni astakhiruka bi ilmika,wa astaqdiruka bi kudiratika wa as'aluka min fadilikal azim,Fa innaka taqdiru Wala aqdiru,wata alamun wala ahlamu ,Wa anta allamul guyub, Allahumma in kunta tahlamu ana hazal amuru anan sai ki fadi bukatarki sannan ki cigaba,Khairulli Fi dini wama ashi wa akibati amri,Ajilihi wa ajilihi,Faqdurhuli wa yasshirhuli summa barikli Fi,Wa in kunta ta'alamu inna hazal amri sharruli Fi dini wama ashi wa akibati amri ajilihi wa ajilihi,Fasrifhu anni wasrifni anhu,Waqdurliyal khaira haisu kana summa ardini bihi."inshallahu inshallahu tanweer sai kinga komai ya daidai ki mikawa Allah alamirinki zai isar miki wallahi idan Adnan rabonki ne zai dawo da kafafunsa har ma kuyi aure "na gode rukayya inshallahu zanyi ,sun dade suna hira rukayya na deba mata kewa , bata ta'ba sanin zama da mutun guri d'aya yana kawowa rayuwar mutun sauyi ba sai data dawo gida ta iske rukayya , rukayya na k'okarin kawar mata da dukkanin damuwarta tare da bata shawarwari masu kyau ."
Da misalin karfe goma na dare kowa ya shige d'akinsa tanweer ta shiga bathroom dinta tayi alwala ta fito ta sanya dogon hijab dinta tare da shimfida sallaya tayi sallahrta raka biyu sannan ta gabatar da adduar istaharar da rukayya ta rubuta mata sannan ta nemi guri ta kwanta akan katifa zuciyarta cike da tunanin Adnan kala kala a hankali wani bacci mai ni'imal ya d'auketa ."
Dare ya raba bacci yaki zama cikin kwayar idanun jaguwa saboda zafi biyu sun had'e masa takura masa akan auren hasera da amminsa take so ga Kuma takaicin kin zubar da cikin da tanwer tayi uwa uba tsakin data had'a mashi dashi har yanzu abun nayi masa zafi a zuciya idan ya tuna kalamanta ya kanji kamar ya mutu wai shi ne zai haifi magajin fashi ?"
Idanunshi suka cika da hawaye amman ya danne .
haka ya wayi gari da rashin bacci shiyasa da gari ya waye yake ta jin kasala ajikinsa.
Shigowar Anas yasa ya dan ji dama ya dan mike ya zauna rigingine dan yasan dole zai dawo dashi daidai "mutumina ina fatan dai lafiya ba wata matsalar bace ?"
naunayyen ajiyar zuciya ya sauke yace "matsaloli ne ba matsala Kawai ba, sai dai fatan samun sauki daga Allah .
"ammi ta matsa lallai sai an saka ranar aurena da haseera karshen watan nan da zara an gama bikin Shafik kenan ,ga matsalar yarinyar nan wai ni tanwer zata wa haka ina bata umarni tana wani butsarewa wai har da cewa bazata cire ciki ba zata haifa ko na kar'ba ko ta Kawo wa ammi," ni ba kaiwa ammi ne ma yafi damuna ba wai ta haifar min wanda zai gajeni a fashi ba sai nayi training yayan wasu ba ,wallahi wannan abu yayi min ciwo ko ance mata wannan sana'ar muna yinta ne dn dadin rai ?"
"Kana ji ko muyi magana ta fahimtar juna Allah kuma yasa ka saurarrni ,Jaguwa ya kara matsoshi sosai"me zai hana Anas ka fad'a komai zan saurara dan mafuta yake nema tun kafin komai ya kwabe masa ."
"Abinda kakewa yarinyar nan Sam bai da kyau , duk fa kai ka jawo abinda ta fad'a maka ba wai wulakanci tayi maka ba ,sai abu na gaba adnan Kana yiwa yarinyar nan wani so na dabam haka itama tana sonka sosai fiyye da komai irin son da zata iya rabuwa da Kowa nata dan ta rayu da kai hasalima soyayyar da take maka ne yasa ta kasa zubar da cikinka ba wai ina takura maka akan kana son yarinyar nan bane ,sai dai ina son ka sani har abada bazaka daina sonta ba , itama haka . zanyi farinciki idan ka sauke komai ka rungumeta ka aureta , nasan muddin iyayenka sukaje neman aurenta zata yarda ta zubar da cikin duk da shima zubar da cikin babban laifi ne .
Jaguwa ya numfasa tausayin kansa dana tanwer
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 30 Chapter of 62