har alhj tahir .”
gbdy alhj tahir ya rasa inda zai saka Kansa dan kunya yayi bakinciki da wannan rana "ka kula da kyau ka dauki maganarmu da mahimmanci babu Kai babu shi kowa yayi harkar gabansa idan ka ...."shiru yayi batare daya k'arasa maganarsa ba sakamakon ruwan da jaguwa ya sake watso masa ya waigo ya sake kallonsa gbdy ya fahimci hankalinsa bai garesu ana ma kawai ya yarda yana son tanweer ,soyayyar ma bazata misaltatu ba gbdy daga anas har su Kamal da jubi da sauransu kallon jaguwa suke ..
Mmm sudais
💗💗💗💗💗💗
KUSKUREN BAYA
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
PAID BOOK
WRITING BY
AYSHA .A BAGUDO
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukata karanta shi ya tura 500 ta wannan account number din 1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an tura sai a turawa wannan number+234 703 534 8686alert domin tabbatar da an tura ko wadan nan number's din 09136918331 or 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi sai a tura ta wannan number 09136918331 domin sauraran littafaina a tuntubi Channel dina ta Hausa bakwai.
🅿️37
........"Ke aganinki har yanzu na dace dake ?me yasa bazaki fahimci illar abinda kike son yiwa rayuwarki ba ?yayi mata tambayar kamar bai ji dadin maganar data fada masa ba ,ya lumshe rikitattun idanunshi tamkar tana gabansa saboda sanyin dadin dake kai kawo a sansar jikinsa ,yayinda har lokacin hannunsa ke aikin shafa faffadan qirjinsa "eh kai kadai ne ka dace dani adnan shiyasa ,kai ne zabina , na baka yardata da amincewata da kai kawai zan iya rayuwa ,
Murmushin gefen baki yayi sannan ya d'an motsa lip's dinsa kamar zai yi magana sai kuma yayi shiru ya kasa furta komai ,ya cigaba da lumlumshe idanunshi yadda yake murmshin farinciki haka yaransa dake tsaye a gefensa suna dabansa suke tayasa murmushi ."
wani irin yanayi ya shiga mai wuyar misaltuwa sosai tsigar jikinsa ke mikewa ,ta kwantar da murya sosai tana fada masa zantuttuka masu sanyi da ratsa sansar jiki ,sosai ta dinga zayyane masa muraran qaunar da take masa ,a hankali ya fara jin jikinsa yana samun sauyi tamkar ana masa wanka da ruwan sanyi ,cikin mintuna da basu wuce goma ba komai nasa ya sake sauyawa maganarta ba iya gangar jikinsa kawai ta tsaya ba har kunnuwansa sun daina fahimtar maganar kowa sai nata ,suna cikin haka ya jiyo sautin muryar mahaifiyarta tana kiran sunanta "habibi I will call you back " ta fada tana katse kiran ."
ya dan lashi lip's dinsa na kasa yana mai maimaita sabon sunan data kirasa dashi a saman lip's dinsa "habibi! ta yadda babu mai ji "Oh my god tanwer allah yasa karki zautar dani ,gbdy hakurina ya kusan karewa akanki ,ya ajiye wayar hannunsa akan table din gabansa ya had'e hannunwansa guri d'aya ya tsarkesu yana sake lumshe rikitattun idanunshi anas ya sauke numfashi tare da d'auke bakin bindiga akan alhaji tahir ya kai goshinsa batare daya ce komai ba ,a natse jaguwa ya d'auki kwalban wine da d'an yatsantsa ya mike tsaye a rikice cikin tsananin tashin hankali duk suka dukar da kansu kasa kar kwalbar ta subuce a yatsansa ya samesu ,ya soma tafiya a hankali dan kar kwalbar ta subuce ta fadi ,duk suka d'ago kansu suka juya suna dubansa yana yawo acikin lambum cike da matsanancin mamakinsa dan basu ta'ba ganinsa cikin wannan yanayin mai tattare da shaukin soyayya ba ."
sun sha jin ana's na fad'a masa cewar ya fad'a soyayyarta amman sai ya karyata hakan ,yau dai ga zahiri sun gani da idanuwansu bai kuma isa ya karyata hakan ba,ahankali ya juyo still da kwalbar a d'an yatsan hannunsa yana gama juyowa kwalbar ta fad'i akan table dake tsakiyarsu gabadayansu suka ja da baya da sauri sukayi ta kansu shi kuwa dafe goshinsa yayi yana runtse idanunshi ya koma mazauninsa ya zauna dafe da keyarsa da hannunwansa duka yana fesar da numfashi bai ma lura da halin da suke ciki ba ,anas ya cire bindiga a goshinsa dan tun daya dafe goshinsa da bindiga bai cire ya kalli jaguwa daga diramar soyayyarsa ba sai yanzu ,ya waigo inda yake zaune yana murmushi yayi masa kallon tsaf gbdy baya cikin haiyacinsa,
suka shiga kallon juna ,gano yanayin baya cikin haiyacinsa yasa suka sake tattara hankalinsu garesa suna kallonsa har nazifi ."
ganin yadda gbdy jaguwa ya susuce tare da lulawa duniyar tunanin soyayya yasa anas ya maida hankalinsa sosai a kan nazifi "za,a d'aukeka yanzu a fitar da kai yau daga gidan nan ,zaka koma gidanka ka cigaba rayuwarka da lamuran gabanka kamar yadda ka saba ,kasa aranka cewar babu wani baraza da za'a sake yi maka ko kawowa zuciyarka farmakin boye an gama da wannan matsalar "ya karasa maganar yana kiran sunan eku !.
"Yes boss ya amsa masa cike da girmamawa da yake da haka suke kiran gbdynsu ,"ka tasa keyar wannan mutumin ka mai dashi inda ka d,aukosa har zuwa lokacin da shi wannan zai dawo haiyacinsa asan yadda za'a yi dashi anas yayi maganar yana nuna alhj tahir dake rakube wanda ruwan sama dake sauka ahankali ya gama jika masa kayansa da jaguwa wanda bai san a duniyar da yake ciki ba ,
Batare da bata lokaci ba eku ya tasa keyar alhji tahir gaba suka nufi bangaren bq ya bude dakin daya kasance nashi né shi kadai ya turasa ya janyo kofar ya rufe sannan ya kulle kofar da mukulli ya juya . "
Nazifi ya dube anas fuskarsa cike da matsanancin farinciki yace "na gode sosai ranka ya dade allah yasa ku gama da duniya lafiya ,allah kuma ya jikan iyayenku idan sun riga mu gidan gsky idan kuma suna raye ,allah ya kara musu lafiya mai amfani "Ameen suka had'a baki gbdy ,amman ranka ya dade wayata dake dauke da sheidu akan dady fa ?"Karka damu a yanzu zamu kwashe komai dake ciki mu baka wayarka ,sheidu zai cigaba da kasancewa agurinmu ne kawai , gyada kai nazifi yayi dan ya yarda dasu dari bisa dari a dan zaman da yayi tare dasu ya amince bazasu yaudaresa ba tunda ga kamanin alhji tahir nan ya canza ba sai an fada masa ba a inda aka ajiyesa muguwar wahala yake sha ."wanda shi bai sani ba ba iya alhj tahir ne kawai ke cikin wannan halin baka'i zaune acikin gidan ba suna dayawa ."
a hankali ya dan juya yana satar kallon jaguwa da shaukin soyayya ke dibarsa yana son yayi masa sallama da karin godiya akan taimakon da yayi masa mman babu halin yin haka , ya juyo da hankalinsa ya fuskanci ana's yana cewa "ranka ya dade ina da wata yar tambaya da zanyi maka idan bazaka damu ba ?karka damu kayi tambayarka Ana's ya fada yana bawa sky umarnin ya kwashe komai daya danganci sheida akan alhj tahir acikin wayar nazifi ya kawowa nazifi wayar ,ya juya da sauri ya bar gurin domin aiwatar da abinda aka sakashi."
"Tambayata shine ku din su waye domin ya kamata nasanin kafin na bar gidan nan dan ina komawa gida dole yan'uwa da abokan arzikina zasu so suji komai daya faru dani ,sannan zasu so suji su wadan ni mutane ne suka taimaka min jami'an tsaro ne ko kuwa akasin haka?"kada kayi mafarkin fad'awa kowa komai daya faru da kai dan bama son asani shiyasa ma muka rabaka da sheidar hannunka, bama bukatar kowa yasan su wayemu dan duk aikin da zakayi dan allah bai dace wasu su sani ba .
nazifi yayi shiru yana sauraransa yana nazarin maganarsa só yake ya gano gaskiyar su din su waye ga bindigu kala dabam dabam agabansu kamar jami'an tsaro kamar kuma yan fashi da makami a shigowarsa gida yaga abubuwa dabam dabam duk da a killace yake amman ya kan leka ta window dakin daaka masa masauki idan yaji motsi, mutane dabam dabam suna shigowa gidan idan kuma dare yayi yana jin Ihun mutane suna kuka da neman dauki wanda ya rasa dalilin haka ,sannan yanzu haka gashi agabansu amman bashi da dalilin sake antaya masa wata tambayar yaja bakinsa ."
yayi shiru yana kallon cikin lambun yana saka da war wara acikin zuciyarsa gargadin da anas yayiwa alhj tahir ne dazu ya shiga dawo masa daya bayan daya yana samun kyakkyawan mazauni acikin kwakwaluwarsa "lallai su din sunfi kama da yan fashi da makami abinda ma zuciyarsa yafi yarda dashi kenan sune sukayiwa mahaifin tanwer fashi sannan suka wuce daita na tsawonlokaci , idan ba haka bane a ina suka san alhji tahir ? me ye kuma hujjarsu nayi masa gargadi akansa? tambayar da yayiwa kansa kenan wanda bashi da mai basu amsarta .shiru ya cigaba dayi agurin yana sake yiwa tunaninsa dalla dalla lallai so yake ya gano wani abu a tattare dasu da zai bayyana masa gaskiya sai dai duk dogon tunaninsa da nazarinsa bai hango abinda zuciyarsa ke zarginsu akai ba dan kuwa babu ta inda sukayi kama da yan fashi ,idan kuma sun tabbata yan fashi ne to kuwa nasu fashin mai kyau ne da adalci "to ma ina tanwer din take ?tambayar da zuciyarsa ta sake aikawa kwakwaluwarsa kenan har ya bude baki da niyyar yi magana sai kuma ya fasa yaji kamar an saka superglue ya manne masa baki ne ."
cikin kankanin lokaci sky ya dawo hannunsa rike da wayar nazifi ya mikowa anas shi kuma yace ya mikawa nazifi ,ya karba yana sake yin godiya sannan anas ya bawa scorpion umarnin ya kai shi gida atare suka mike suka soma tafiya ,yayinda gbdynsu suka tsura wa jaguwa idanunsu suka cigaba da kallonsa eku sky suka kallesu sannan suka kalli jaguwa tare da kwashewa da wata dariya garin subawa juna hannu dan su kashe suka bugi table din gabansa nan take glas cup's din dake ajiye akai suka tarwatse ,bugun table din ne ya dawo da hankalin jaguwa jikinsa ya kuma ankarar dashi halin da yake ciki "Am ranka ya dade daman haka idanunka suke ?" "Sosai ya sake dawo wa haiyacinsa yana dubansu fuskarsa tattare da alamun tambaya "lallai wannna soyayya hakika ta tabbata sosai jabir ya fad'a yana murmushin tsokana" da wa kenna?jaguwa ya tambayesa ya dan kallonsa idanushi still a lumshe tamkar wani mashayi "da kai mana idan ma ba kai ba wa za'a nunawa irin wannan soyayyar ? "uhm ka duba dan allah sai kace ita din ba diyar minister ba, idan tana yin wasu abubuwa sai ka dauka ita din ba diyar babban mutun bace ,amman kowa ya ganta yasan yar gidan manya ce jubi ya fad'a yana kwashewa da dariya."
"Nata kuke gani shi fa ?gbdy ya canza tamkar ba jaguwa ba ,yau dai kowannenmu ya gano wani sirri atattare dai kai ba kuma ka isa ka mutsa mana ba ,mu dai zamu maka fatan alkhairi dan gaskiya jaguwa ka dace kaji dadi wallahi karka tsaya sanya ka duba yarinya irin wannan haka amman ta makale sai kai congratulations kamil ya fada yana mika masa hannu yana sakar masa murmushi amman kememe jaguwa yaki bashi hannu dan wani mugun haushinsu da haushin kansa yaji ."
"yanzu dai ku me kuke tunanin abun zai kasance ? jaguwa ya mike tsaye cike da jin haushi "kai dan allah kuyi min shiru karku dame ni da wata magnr soyayya" ya soma tafiya anas yabi bayansa da ido cikin jimami kawai yana kallonsa ko har sai yaushe zai fahimci halin da yake ciki ?yana gudar masa randa soyayya zata wujijigashi tayi waccajali dashi ,
yaso yadda ya samu damar nan yayi amfani daita "kaji abinda yace Ana's wai kar mu damesa a zuwan ba gskiya bane ?"Haka zai ta nuna mana anas ya fada tare da kokarin mikewa tsaye "ina ma zanga wannan yarinyar dana fada mata ta rabu dashi da fita rayuwarsa wallahi zai fito da abinda ke ransa "bazata iya ba domin ba irinsu jaguwa mace
kewa irin wannan wasan ba , ko kun manta cewar shi din dokin tsare ne ya fada yana cigaba da tafiya ya nufi hanyar fita daga cikin lambum."
kai tsaye jaguwa hanyar dakinsa ya nufa yana gyara kwalar rigarsa yayinda hoton fuskar tanwer ya shiga masa gezo acikin kwayar idanunshi ,tun daga kwayar idanunta karamin bakinta hip's dinta har zuwa qirjinta dake cike bammm a nan ya tsaya yana kare musu kallo tamkar a zahiri , nan kuwa tunaninsa ne kawai ,a hankalin ya fara juyi acikin dakin tare da zaro tsarkar gold dake makale a wuyansa boye cikin rigarsa yana juyawa a hankali tamkar yadda yake zagaye dakin fuskarsa kunshe da murmushin farinciki yana sake zurfi acikin tunaninta."
a natse ya daga kansa saman dakin yana kallon celling dakin "ina sonka adnan dina ban samu damar yin soyayya da kowa ba sai da kai ,dan allah kace kana sona ,ka canza sana'a zanyi confused din iyayena su bari na aureka sannan zan nemo maka sana'a bazan barka haka ba kalamanta suka dinga dawo masa daki daki suna haskaka zuciyarsa ,
a hankali ya jingina bayansa da bangon dakin tare da tokare kafarsa daya "bayan kamar minti goma ya sauke kafarsa yasa dan yatsantsa jikin bangon takin yana tafiya yana bin bango da yatsansa har lokacin murmshi ne kwance a fuskarsa ,yau yana cikin farincki mara misaltuwa ,na kiran da tanwer tayi masa ne ko kuwa naji albishirin dinta ne shi dai bai sani ba amman dai yana cikin farinciki da bai san dame zai misaltashi ba ."
"nima ina sonki tanwer son da ban taba tsammanin yiwa wani mahaluki irinsa ba ,ina jinki ajinina acikin bargona da tsokar jikina bazan iya rayuwa babu ke ba but just give me time ina bukatar lokaci zanyi wani abu akai ,wani irin sanyayyen dadi ke bin lungu da sako na sansar jikinsa ,jinin jikinsa ya ninka gudu akan yadda yake yi ,a natse ya karasa gaban mirrow ya tsaya ya tokare hannunsa da jikin bango yana kallon kansa ta cikin mirrow , yatsan dayan hannunsa ya kai cikin bakinsa yana cizawa a hankali a hankali yana jin kamar yatsunta yake cizawa "ina son fararen fure ko zaka dauko min ?ina sonka adnan na yarda da kai na kuma amince da kai ,ya tuna lokacin daya kai kangon gida da bai yi tsammani zata iya rayuwa acikinsa ba amman da budar bakinta tace "me zai hana adnan ?wallahi zan zauna dan fiyye min kowani gida muddin da kai zan rayu acikinsa karka wani damu zan zauna ". ya sauke naunayen ajiyar zuciya a daidai lokacin da ana's ya turo kofar dakin ya shigo ya tsaya ya harde hannunwansa a qirji idanunsa akansa,jaguwa bai juyo ba sai ma kura masa ido da yayi ta cikin glas mirrow yana kallonsa kafin daga baya ya juyo gbdy ya fuskanci anas soyayyar tanwer na sake kanainayesa "yanzu me ka tsayar akan yarinyar nan tanwer?" I don't know what to say but is like bazan iya cigaba da rike wasu abubuwa ba zan dai yi shawara da zuciyata nan kusa zan tsaida maka
yayi mgnr hannunsa na shafa faffadan qirjinsa ,
gyada kansa kawai anas yayi tare da sauke boyayen numfashi yace "please jaguwa ka hanzarta kayi abinda ya dace ka daina barazana da rayuwar yarinyar mutane " .
Ajiyar zuciya ya sauke tare da tsura masa ido yana jin yadda zuciyarsa ke mugu mugun bugawa ya kira sunansa "anas look at me babu wasa acikin kwayar idanuna idan bazan yi wani abu akai ba kai kasan waye ne I won't lie to you ,zanyi wani abu akai amman ban sa yaushe bane , yau né gobe ko anjima né bansani ba ya karasa maganar tare da yin shiru ya cigaba da kallon anas ,dakin dakin ya dauki shiru bayan ya rungume hannunyensa duka sannan ya janyo wayarsa da yaji tayi kara alamun shigowar sako ya shiga dubawa yana gamawa ya fesar da iska mai zafi daga bakinsa sannan ya soma magana a tsanake " satin nan zamuyi aiki ma alhji bello yanzu sakonsu ya shigo da inda zaayi aikin sai dai bana jin acikin mu biyar din nan akwai wanda zashi zan tura sconpio domin aikin zai fi dacewa da mutun daya ne ,nan da 2 week kuma zamu shiga aikin akan masu safarar hodar iblis ,sannnan ina saka rai mlm mudi zai turo mana sako yau ko gobe domin musan ta yadda zamu bibiyi alhji tajudenni da duk wasu masu irin sana'arsa ."
"suna dayawa fa kana ganin zamu iya dasu gbdy ?me yasa kayi wannnan tamabyar ?bansan dalilin ba amman haka nan nake dan jin tsoro yin aikin ."shiru jaguwa yayi yana kallonsa up and down yana taba qirjinsa sannan yace "why anas? akoda yaushe ina fad'a maka ka dinga karfafa zuciyarka ka cire tsoron a ranka babu abinda zai faru damu ,please ka kwantar da hankalinka a yanzu nima na soma hango haske acikin maganarka zan yi kokari na dawo kan hanya kamar yadda kake bukata amman kafin lokacin akwai bukatar muyi komai cikin tsare....."
"ba tsoro bane adnan wallahi bana son hally ta rasani ne adalilin akin nan ni kaina yanzu na fara jin dadin iyalina ka fahimceni kai kanka kasan aikinmu akwai hatsari, ada rayuwarmu kawai muke ko mutu ko mu rayu amman yanzu fa?"ina da hally acikin rayuwata kai ma kuma ina fatan nan kusa ka ajiye tanwer a gidanka for how long zamu d'au...."qarar bude kofar dakin da suka ji ne ya katsesa sky ne ya shigo hannnsa rike da farar takarda guda uku "boss ga sakon bayanai nan mlm mudi ya turo ta system gashi har na yi prit dinsa out ,okay sky ja ajiye a can ya ajiye akan table ya juya."
"Am sky yayi saurin juyowa da sauri cike da respect ,
ka kawo min bakin shayi yanzu "okay boss ya fada tare da juyawa ya fice daga dakin .
Anas ya dan yi murmushi ya cigaba da magana "rayuwar yanzu data da ba daya bace agurina ina matukar son halima kamar yadda kasani banason na bar rayuwarta cikin kuncin da matsalolin rayuwa , cikin haka sky ya sake yin knowking ya shigo hannunsa rike da farin glass cup mai dauke da ruwan coffee mai zafi ya ajiye ya juya ,jaguwa na kokarin daukar cup din coffee wayar anas ta soma ringing dan haka ya dakata yana son sauraron yaji daga ina wayar tace .
Ana's ya zaro wayar daga cikin aljihun gaban rigarsa yana kallon screen din wayar my princess wife ya gani yana yawo daman da sunan da yayi saving kenan ,ya lumshe idanunshi yana jin sanyi na ratsa sansar jikinsa ya dauka tare da rage sautin muryarsa "my princess ya kike ya jikin naki hope kin dan samu relief ?okay to shikenan my princess wife ki kular min da kanki gani nan dawo wa yanzu ,
jaguwa ya maida hankalinsa sosai akansa "ina sonki sosai my princess wife bazan jima ba muradin raina da wannan kalmar ya kawo karshen maganarsu ya katse wayar da murmushi akan fuskarsa."
"muradin ranka anas a kuma gabana ko kunyata bakaji ba kamar ni ba surukinka bane ?wani kunya kuma adnan a zaune kalau ?ai maganar wata kunya ta kare kaga bari na wuce gida my princess wife bata da lafiya gashi har uku saura ya juya , har ya kusan bakin kofa ya tsaya sakamakon jiyo sautin muryar jaguwa data fito a hankali ,"gbdy maganganunka kunya suke bani anas,Karsu baka kunya adnan ka dai yi kokari Kaima ka mallaki muradin ranka zai fiyye maka ya sa kai zai fice daga dakin yana murmushin tsokana shima jaguwa yayi murmushi yana shafa sumar kansa yace "ka shigo gobe da wuri please mu fara tsara abubuwa "okay ya fada tare da karasa ficewa.
Numfashi jaguwa ya sauke yana jin dadin yadda anas ke kulawa da kanwarsa gbdy rayuwarsa ma ta sauya ya daina shan giya yanzu iyakarsa sigari shima sai idan yaga yana sha ne .a hankali ya karasa ya dauki farar takardar da sky ya ajiye yana dubawa a tsanake yana kurban coffee at the same time kuma yana cizan lip's dinsa na kasa yana jin faduwar gaba akan tanwer duk sanda ta fado masa sai yaji gabansa yayi mummunar faduwa gashi yanzu duk bayan sakonni take fado masa yaji kamar yaje gidansu ya ganta amman bazai iya ba .
Hally kuwa tunda anas ya fada mata kalamansa masu sanyi taji ta sake nitso acikin soyayyarsa "kece muradin raina ta maimaita tana lunshe ido "nima kai ne muradina ,karfe hudu na yamma tai wanka tai kwaliyya kamar jiya sai dai kayan datasa ba irin na jiya bane dinki atamfa ne sai dai su din ma sun dan matseta daga kirji ta canza tasha zuwa zeeworld alokacin ana wani film din india mai kyau kuma na soyayya (sanam teri kasam ) daman itama mayar son kallon film din india ce karfe biyar yayi sallama taji matukar dadin dawowarsa ji tayi kamar ta tashi ta rungumeshi ajikinta bai shigo ba ya tsaya a bakin kofa .
Ta kallesa tace "Lafiya ka tsaya anan?"
Ya dan daga kafada "bazan shigo ba sai da kulawarki tayi murmushi tana mai tsaida idanunta akanshi "kulawa kuma tame "?ai ya kamata na samu ko yar runguma ne ayi min ko ba haka ba ?Tayi kasa da idanunta ta gyara zamanta babu alamun zata tashi "da gaske fa nake idan baki taso kin rungumeni ba alamar barka da dawo wa a haka zan ta tsayuwa bazan shigo ba gashi kuma na dauko yunwa ."
Jikinta a sanyaye ta tashi ta nufi inda yake tsaye yana aiko mata da kallon love sai dataje daf dashi sannan ta tsaya "to shikenan ka rufe idunka ya kuwa rufe a hankali ta karasa ta rungunesa tsam,shima ya hadeta acikin hannuwansa ya rungumeta ajikinsa yana shafa gadon bayanta "my princess wife nayi kewarki duk abinda nake hotonki nake gani na tabbatar dana bari na kai Kmr jiya zaki sha mamaki domin zan iya ramewa."
Tayi murmushi "ramewa kuma ?"Wallahi zan iya ramewa domin kawai tunaninki nifa kin kara siyo min wata kima da daraja agareni sonki ya ninku a zuciyata fiyye da wanda banyi tsammani ba ina jinki a sahun macen da ko mutuwa idan ta rabu mu ita kanta tasan bata mana adalci ba ,ya dan zareta ajikinsa yana kallonta itama shi din take kallo da kwayar idanunta ya kai hannunsa yana shafa lip's dinta "ban taba jin bakinki ya fadi irin haka ba ina son nasan yadda kike jina acikin ranki ".Taja hannunsa zuwa kan table domin abincin rana datayi bata dauke shi ba yana cikin flak's "kace kana jin yunwa?"
"Eh ina jin yunwa amman kuma bazan ci abincin ba sai kin gaya min yadda kike jina acikin ranki "ka fiyye fitina yanzu ya anas mai yasa ne ?"saboda na damu dake ne kuma mutuwar sonki banason abinda zai nisantani dake my princess ya fada idanunshi na kanta ta danyi kasa da idanunta a hankali ta soma motsa lips dinta "ina... ina .." sai kuma kunya ta hanata furta abinda take son fada masa .
da murmushi ya sumbace kumatunta suka zauna bisa table "zanso ace muna rayuwarmu kullum atare batare dana fita zuwa koina ba amman ina hakan ba mai yuwa bane kullum cikin aiki muke ta dago ta kallesa daga zuba masa abincin da take "haka ai shine daidai ,abun haushi ma gobe akwai aikin da zamu fitar dani ta sake dagowa da murmushi a fuskarta "meye abun jin haushi aciki dan zaka fita nemo mana halal?".nan take yanayinsa ya sauya zuciyarsa ta soma rawa ,yayi shiru yana kallonta cike da tausayawa "karka damu nasan na dan kewar juna da zamuyi ne wannan kuma na dan wani lokaci ne kawai ta ajiye abun zuba abinci ta kamo hannunsa cikin nata ganin yanayinsa ya canza "haba mana ya anas ai baa acan zaka kwana ba da ka wani canza Kmr idan ka fita goben bazaka dawo ba ?"
Yayi saurin girgiza mata kai "to ko na shirya goben muje tare ne ?ya harareta cikin tsigar wasa yana dawo da natsuwarsa "allah sai muje tare,shimkenan zan muje tare amman a zuciyata zan miki kyakkyawan riko ya fada yana shirin fara cin abinci ."Sarai ta gane ba zuwa zaiyi daita ba "ai kuwa idan bakaje dani ba bazamu kwana tare ba ya dago yana dariya "ai kuwa yarinya baki isa ba ai daga yanzu kullum tare zamu dinga kwana har na
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 50 Chapter of 62