Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fito ba "ki fita mana kina bata min lokaci, ta kallesa kmr zatayi kuka dan har hawaye sun cika mata Ido ta yunkura da kyar zata tashi ya fixgota jikinsa ya rungumeta tsam  kuka ta fashe masa dashi.
a hankali ya shiga shafa kanta zuwa  bayanta "is okay ki  kukan please  ya Isa haka  ke da zakiyi farinciki zaki kwana a gida tare da iyayenki da dinbin masoya shine zaki dinga hasarar hawayenki dan zaki rabu dan fashi  " girgiza masa Kai ta shiga yi tana sheshekar kuka  ya d'ago habarta  Yana kallon  kwayar idanunta da fuskarta  dake kwance shabe shabe da ruwan  hawaye.
tsadadden murmushinsa ya sakar mata "why tanweer ?ya zaki min hk?idan kina son na dinga tunaki a duk bayan second biyu ki daina kukan nan .
da sauri ta shiga goge hawayenta ya Kai bakinsa yayi mata light kiss "oya kije ga dad dinki can ya matsu bai d'aura idanunshi akanki ba ya saketa ta bud'e kofa zata fita yace "karki manta da alkwarinki " ta dawo kadan tana dubansa kwayar idanunta d'auke da tmby "na zaki sa akamani mana dan naga kin saci numbeta"  dukan wasa ta Kai wa  qirjinsa "Kai ko Allah shiryeka "Ameen na gode da addua ",Ki kula da kanki  sosai ki daina tsiwa da rashin kunya dan akwai  irinmu dayawa acikin garin nan "Kaima ka kular min  da kanka akan wannan sa'anartaka banason ka fad'a hannun  police "   Faduwa  da nasara  duk daya ne agurina duk wasu  kwalaye dake dakona bazasu iya komai  ba har sai  idan na tare dani ne suka bada hasken cutar dani."

"karfin zuciyarka na burgeni ta Kalli yatsun hannunta  ta  ciro zoben  silver  me shegen kyau   wanda kakarta wacce ta  haifi mahaiyar ce ta bata zoben, ta kamo yatsun hannunsa   ta zira a karamin dan yatsansa dan anan kawai zai zauna "Ina sonka adnan !"
ta fad'a tana lumshe masa idanunta bai ce mata Komai ba bare tayi tunanin  zai bata amsa.
  Jin yayi shiru yana kallon zoben da tasa masa  tace  " muje  ka  rakani   bansan gurin nan ba ", numfashi ya sauke yace " muje anything for you ta sake yunkurawa ta fito Shima ya bud'e bangaren da yake ya fito .
tafiya kad'ai suka yi ya juya yana cewa  "iya nan zan tsaya " tayi saurin juyowa da sauri  ta  kamosa tare da  nuna masa gefen kumatunta da hannunta alamar yayi kissing dinta  " kiss  yayi mata  ya juya  ta sake biyosa ta nuna masa d'ayan gefe "oh my goodness tanweer lokaci na tafiya fa kar  dad dinki  ya wuce ya d'auka karya nake masa ".
"sorry! sorry!!  daga wannan shikenan ya furzar da iska sannan yayi mata har   zai sake juyawa  ta sake riko sa "wai meye haka ne ? Yayi mgnr a fusace  ",ai Kaine Kaki  yin aikinka da kyau  saura me mahimmancin tayi mgnr cike da shagwaba tana  nuna masa bakinta daidai lips dinta .
Numfashi ya sauke da karfi  ya janyota gbdy ya rungumeta tsam ajikinsa  ya hade bakinsu guri d'aya ya  fara  tsotsan bakinta nan  idanun mutane sukayi musu  chaaa  tun da suka fara dramar soyayyarsu mutane  suke biye dasu jiki a sanyaye ya zare bakinsa  ",bye tanweer ya fad'a yana juyawa ta tsaya shiru tana kallon bayansa  bai juyo ba duk da jikinsa ya bashi bata wuce ba .
jikinta a sanyaye ta juya ta soma taku a hankali adaidai lokacin da jaguwa ya juyo a  natse  ya tsurawa  bayanta Ido yana kallon yadda take taku a hankali tana rausaya  har ta Iso gurin mahaifinta ,tana gama k'arasawa gurin mahaifinta ta zube ajikinsa .
Jaguwa ya  lumshe idanunshi ya sake  juyawa ya karasa Inda motarsa take pake  ya shiga ya tayar sai dai hakan  nan yaji ya kasa control din motar ya daura duka hannuwansa akan stearing  ...."

Mmn sudais


💗💗💗💗💗💗
KUSKUREN BAYA
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

PAID BOOK
LAST FREE PAGE
Za'a iya biyan kudinsa yanzu

WRITING BY
AYSHA .A BAGUDO

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

Wannan littafin na kudi ne mai bukata karanta shi ya tura 500 ta wannan account number din 1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an tura sai a turawa wannan number
+234 703 534 8686
alert domin tabbatar da an tura ko wannan number 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi sai a tura ta wannan number 08059623096 kada ayi vtu a number MTN ,
domin sauraran littafaina a tuntubi Channel dina ta Hausa bakwai.

🅿️22

"Shiru yayi yana cigaba da dubansu cikin wani irin yanayi mai wuyar misaltuwa, gbdy zuciyarsa ta karye sosai , tsananin tausayinsu ne ya lullu'be zuciyarsa dama gangar jikinsa . "hakika ya cutar da zukantasu na tsawon lokaci tunda ya nesantasu da sanyin idaniyarsu ,"ko yaya mahaifiyarta zataji idan ta d'aura kwayar idanunta akanta"? .
A hankali minister ya Kai bakinsa daidai saitin kunnen tanweer ya furta sunanta cikin wani irin yanayi na farinciki da tausayawa "tan my baby !
"Yes dad ta amsa cikin tsananin farinciki da fad'uwar gaba dan jikinta ya bata har lokacin jaguwa na nan atare daita bai tafi ba.
a natse ya zare bakinsa sannan ya dafa kafad'unta yana kare mata kallon tsab , ji yayi hawaye masu zafi sun zubo masa , itama hawaye ne suka samu nasarar zubowa akan quncinta sai dai ita nata hawayen na abu biyu ne suka gangaro mata ,hawayen
rabuwa da burin ranta da Kuma na farinciki dawowarta gurin iyayenta . "Sai dai azahirin gsky wacan damuwar tafi ta dawowarta gurin iyayenta cin ranta da quntata zuciyarta , iyayenta nata ne na har abada ,
amman rabuwa da Adnan fa "? Abu ne mai ciwo da wahala agareta wata Killa ma shikenan ita da shi har abada ..."
Wasu sabbin hawaye ne masu radadi suka sake silalo mata "I will miss you my Adnan ....."
ta fad'a akasan ranta tana mai lumshe tsumammun idanunta sannan ta juya a hankali ta tsurawa hanyar data ga yabi Ido tana kallo tana jin kamar karta bi mahaifinta "Ina ma zata iya hakura dasu wallahi da ta koma garesa ta k'arasa rayuwarta dashi ".
cikin mugun tashin hankali ta dawo haiyacinta alokacin da mahaifinta ya dafa kafad'anta yana cewa "yaya dai tan "? ya tambayeta ganin ta kafe guri daya ko kwakkwaran motsi batayi ,wani yanayi yake gani atattare daita wanda bai san ko na meye ba .
Gbdy ta kasa danne kukanta hawayenta suka zubo sharri ...."
nan take hankalin minister yayi kololuwar tashi "menene tan "? ya sake tambayarta cikin tsananin damuwa kallonsa kawai tayi tare da ciza lip's dinta na kasa da karfi  sosai taji zuciyarta na bugawa amman tayi saurin sanyawa jikinta jarumta tace "babu komai dad muje gida Ina tsananin son ganin mumy nasan itama tana can tana jiran qarasowata ". cikin sauri ya riko tsintsiyar hannunta cikin nasa suka fara takawa yana cewa "sosai ma kuwa yau ban san irin farinciki da zainab zatayi ba idan ta d'aura kwayar idanunta akanki , surprise zan mata sai dai kawai ta ganki daga sama ".
"Kai dad ba dai mumy batasan da dawowata yau ba ? tayi maganar tana waigen bayanta ko zata sake ganin Adnan  dinta sai dai ina batai  nasarar hangosa ba .zuciyarsa ta sake tsinkewa ta shiga karkarwa da shiga tashin hankali , "gsky bata sani ba saboda dan fashin da yayi kidnapping dinki yace kar na kuskura na bar kowa ya sani muddin Ina bukatar diyata araye ."
shiru tayi tana sauraren dad dinta zuciyarta na wani irin bugawa da karfin gaske wanda adaidai wannan lokacin Shima gaban jaguwa banda bugawa da karfi babu abinda yake.
a hankali ya dinga jin kamar rayuwarsa tana rabuwa dashi ne , tafiyarta tafi muryarta burgewa  yana zaune yana kallonsu suna takawa da mahaifinta har sanda minister ya bud'e mata gidan gaba ya sanya ta shiga ciki ta zauna ya maida kofar ya rufe sannan ya zagayo da sauri yana waige waige ya bud'e bangaren direba ya shiga ya zauna ya tada motar tare da riko yatsun hannunta ya damke gam cikin nashi kamar wacce za'a sake kwace masa ita ."

Wani irin tsalle had'e bugawa zuciyar jaguwa dake zaune agurin yayi wanda har sai da numfashinsa ya d'an tsaya na wani lokaci hatta bugun zuciyarsa sai daya tsaya wanda yake daidai da barazanar da tarwatsa kwakwaluwarsa da zuciyarsa yana zaune har sai da ya ga tashin motarsu sannan ya samu kuzarin soma k'okarin barin gurin zuciyarsa cike fal da matsanacin firgici da fargaba ya nufi hanyar gidansa .
Yana tafiya zuciyarsa na cike da fargaba da alhinin rabuwa da tanweer yarinyar da kullum yake ikirarin baya sonta zallar tausayi ne kawai .
A hankali zuciyarsa ke sake raunana da narkewa akanta yana tuno abubuwanta da abinda ya faru a yanzu kafin rabuwarsu, ta nuna masa so iya so mai tsayawa a rai  , ya lumshe idanunshi a lokacin da zuciyarsa ta hasko masa gefe da gefen quncinta Inda ta bukaci ya sumbaceta a mintunan da suka gabata har a karshe sai da tasa yayi kissing dinta mouth to mouth "bye tan ! ya furta a lokacin daya kawo karshen rabuwarsu yayinda ita Kuma tayi shiru tana kallonsa ."

tafiya yake sai dai tuninta yaki barin zuciyarsa ta huta gabansa sai faduwa yake yana Jin kamar ana buga masa guduma ne sai dai shi anashi kokari yake yaga ya manta daita arayuwarsa tun akan hanya Amman Ina Hakan ya citura yana yakiceta a zuciyarsa tana sake makalewa zuciyarsa da rayuwarsa ma gbdy . a hankali yaja dogon tsaki tare da dukan stearing motar kana ya kamo lip's dinsa na kasa ya ciza da karfin gaske yana furta "why tan ? " kar muyi haka dake . dan Allah ki bar zuciyata ta huta "ta yaya zuciyarka zata huta ai yanzu ma ka fara tunaninta"? zuciyarsa ta bashi amsa da  haka .
"zuciyata ki shiga hankalinki ki dawo daidai kamar yadda kike before , bari kiji duk nacinki da son karki manta da tan acikinki dole sai kin mantata tun da ba tare kukazo duniya ba dan dole sai na yakiceta sai na mantata don ni nake dake bake kike dani ba, nine zan juyaki ba kece zaki juyani ba ya fad'a yana sake dukan stearing motar tare da falfala gudu akan titi sam yaki goyawa zuciyarsa baya akan kamuwa da son tanweer .
haka nan Kuma ya dinga jin ransa na mugun baci dan haka ya dinga sharara gudu akan titi batare daya san Ina zai dosa ba dan baya jin zai koma gida a lokacin tsaki yake ta faman aikin ja yana furzar da iska mai zafi daga bakinsa a hankali ya lumshe idanunshi dake kallon titi na second daya sannan ya bud'esu a natse yana tunanin Inda ya kamata yaje domin dawo da zuciyarsa daidai .."
yana k'okarin d'aukar hanyar zuwa shurem gidan rawar fela wayarsa ta d'auki ruri ,a natse ya Kai idanunshin kan wayar dake qara sunan anas ya gani yana yawo da kamar bazai d'auka ba sai Kuma ya kasa aikata hakan ,anas na dabam ne agurinsa duk runtsi duk tashin hankali bazai iya kin d'aukar wayarsa ba jiki a sanyaye kamar wanda akayiwa mutuwa ya d'auka yana cewa "anas ya'akayi ne ? "Normal jaguwa kana Ina ne ?
" Ina kan hanyar zuwa shurem !
"Kayi me Kuma acan ? Amman dai ka mayarda yarinyar nan ko ? "eh na had'ata da mahaifinta har ma sun kama hanyar zuwa gida ".
"shine Kai Kuma damuwar rabuwa daita zatasa kaje shurem ba "?.
shiru jaguwa yayi yana sausauta gudun da yake akan titi "karka min haka aminina Ina tsananin bukatarka, Ina sonka fiyye da tunaninka banason damuwarka ,haka zalika bana son na rasaka dana rasaka gara na rasa raina raina fansa ne agareka dan Allah ka dawo gida a yanzu, Idan Kuma bazaka dawo ba nima zan biyoka yanzu mu had'u idan ma damuwar ce muyita tare".
sai lokacin jaguwa ya sauke naunayen numfashi tare da cewa "no kayi zamanka anas banason tafiyarka Kai kad'ai Kai ganin nan ma dawowa gida yanzu ya fad'a tare da karya kwana ya d'auki hanyar zuwa gida Cikin kankanin lokaci ya Kara so gidan saboda mugun gudun da yayi a haraban gidan ya iske anas zaune shi kad'ai ya had'e hannuwansa duka a qirjinsa yana jiran qarasowarsa . naunayen ajiyar zuciya jaguwa ya sauke yana jinjina girman qaunar da anas yake masa baya samu kwanciyar hankali muddin baya tare dashi ,baya iya runtsawa muddin bai ga ya runtsa ba ,baya samun natsuwa muddin yana cikin damuwa , numfashi ya fesar ya cigaba da tafiya a natse batare daya ce masa komai ba .
anas na ganin haka ya mike ya biyo bayansa, kai tsaye jaguwa d'akinsa ya shiga ya janyo kujera tsood ya zauna ya tsurawa mirrow Ido yana kallon Kansa yayinda anas ya tsaya ya jingina bayansa da bangon d'akin yana kallonsa  cike da tausayawa dan  ya rigada ya afka son tanweer  sai wani iKon allah."
a hankali jaguwa ya sauke naunayen ajiyar zuciya , lokaci d'aya idanunshi ya sauka akan zoben da tan ta saka masa , shiru yayi yana kallon zoben yana Jin kamar ya cire ya yar dan sake nisanta kanshi daita , sai kuma ya kasa yana cewa zuciyarsa"Me yasa zaka yar "?.
"Saboda  zoben zai sa ka damu kanka akanta ? ya bawa zuciyarsa amsa da hakan " damuwa daita ai ba lallai ne kana sonta ba ,sabo ne , shi Kuma daman sabo haka yake ,ka rigada ka saba daita ne shiyasa , har yanzu Kuma akwai wannan sabon da sannu zaka manta daita ne a rayuwarka ."

Ya mike tsaye ya goya hannuwansa duka a bayansa ya soma zariya acikin d'akin yana zurfafa tunaninsa " yanzu ba lokacin tunanin wata tanweer bace , kamata yayi ka tsaya kayi tunanin akan yadda dcp ya samu number wayarka Kai tsaye , hannuwansa dake goye abayansa ya cire ya zura cikin ajihun wandonsa yana cigaba da taku kafin daga bisani ya soma cire rigar jikinsa ya Saura daga shi sai far singlet da dogon wando a hankali ya kira sunan anas "anas...!
ya amsa da na'am yana dubansa "had'omin kan mutanen gidan nan  gbdy Ina da magana dasu ." Yana gama fadar hk ya shige bayi shi Kuma anas ya nufi kofa fitar da sauri zuwa falon baya inda ya iske su jubi zaune suna shan tabar wiwi kowannensu idanunsu yayi jajur sannan d'aya byn d'aya ya tattara kowa ya sanar dasu sakon jaguwa . "

A babban parlour jaguwa suka had'u Suka zauna zaman jiran karasowarsa ya fito yana taku a hankali yana shafa qirjinsa yana kare masu kallo d'aya byn d'aya yana masu kallo mai cike da tunhuma tunda suka ga yanayinsa kowannensu ya sha jinin jikinsa bare jamin sirrin dake tare dasu Wanda yafi kowa shiga tashin hankali da fargaba sai dai yayi k'okarin daidaita natsuwarsa dan karsu ganoshi .
a diririce yake amman ba lallai ka fahimci hakan ba sai kwararen ma'aikaci irinsa ne kawai zai iya ganosa .
sosai jaguwa ya had'e girar sama data kasa kafin daga baya a hankali muryarsa ta fito amman cike da tsawa "wa nene acikinku ya siyar da number wayata "?.
Shiru sukayi gbdynsu suna kallon junansu har sai daya sake maimaitawa sannan jikinsu na rawa duk sukace basu bane.
a tsawace ya dakatar dasu da hannunsa "karya kuke anas koma can ya fad'a yana nunawa anas gefensa "wannan kawai zuciyata zata iya cirewa acikinku Amman gbdynku ban yarda daku ba dan haka a fad'a min gsky kafin nayi kwakkwaran bincike na gano Wanda keda hannu cikin wannan aika aikan na aikashi lahira ".
"Haba jaguwa mu da Kai da anas fa duk Abu daya me yasa zaka dinga ware anas acikinmu idan Kuma ya zamo anas din ne ya bada numberka fa?"
"Impossible anas can't do that to me bazai ta'ba min haka ba" kana da dalilin da yasa ka tunhumemu ne ? Ko kuwa mun ta'ba cin amanarka ne dayasa ka ware anas ka barmu?inji cewar jubi da ransa yafi na kowa dungunzuma.
Shiru jaguwa yayi dan bashi da wani dalilin dayasa ya tunhumesu ban da anas .
Sai daya furzar da iska mai zafi sannan yace bani da wani dalili amman muddin na sameku da haintata wallahi sai na kasheku daya bayan daya na binneku acikin gidan nan ya k'arasa maganar yana tsaida idanunshi akan mai gadinsa da sauri yayi kasa da Kansa dan bazai juri kallon jaguwa ba duk da shi din ba wai mai laifi bane .
parlour ya d'auki shiru yana cigaba da dubansa yana nazarin wasu abubuwa sai dai nan take gabansa ya cigaba da fad'uwar da yake anas ya matso kusa dashi ya riko tsintsiyar hannunsa cikin nashi sannan ya zaunar dashi akan d'aya daga cikin kujerun falon yana cewa "ka daina zargin su dan Allah , kamata yayi kayi tunanin mai zurfi akan lamarin , "mai ma yasa baka fad'a min ba tun a d'aki domin muyi tunani a tare domin mu san ta inda matsalar take ? " Sam banji dadin abinda kayi ba dan bana zarginsu da aikata hakan ya k'arasa maganar tare da karasawa ya bud'e fridge ya d'auko kwalban wine mai sanyi ya balle ya siyaya a glass cup ya Mika masa" ungo ka Sha kaji sanyi sarkin rigima kawai idan baka d'aga hankalin mutane ba baka samun natsuwa".
jiki a sanyaye jaguwa ya amsa cup din ya rike sai dai ya kasa sha sakamako kwakwaluwarsa data Lula duniyar tunani .
Anas ya juya ya fuskance su jubi "dan Allah Kuyi hakuri karkuyi fushi dashi Kun rigada kunsan halinsa idan ransa ya baci babu abinda bayayi dan yaga ya huce akan mutane ni daku duk abu d'aya ne agurinsa babu wani bambamci .
wani irin mugun kallo suka masa mai tattare da tsananin bacin rai suna jin kamar su shake masa wuya agurin su aika sa lahira, babu wanda yace uffan acikinsu illa juyawa da sukayi suka bar falon cikin tsananin damuwa."
anas ya dafa goshi yana furzar da numfashi sannan ya dawo Inda jaguwa yake zaune "Adnan dan Allah ka daina nuna Kafi qaunata akan sauran abokanmu , tsakani da Allah ni banga abun wariya aciki ba tunda kana zargine kamata yayi kayi zargin har dani ,kawai giyar soyayya na dibarka kazo kana wa mutane shirmen banza " tunda anas ya fara magana yake ta jan tsaki aransa kafin daga baya ya mike yace "Kamin shiru anas karka dameni da hauka idan ba haka ba zan fasa maka Kai yanzu ya fad'a yana zaro bindiga pesto a bayan wandonsa ya saita Kansa yana huci ."ka harbeni mana". anas ya fad'a yana dubansa cike da fushi, jaguwa ya turesa kan kujera ya ijiye bindigar hannunsa ya fito yana tsuma kamar wani mayuncin zaki Kai tsaye gurin shakatawa ya nufa Yana sake shiga duniya tunani Dan dole so yake sai gano inda dcp ya samu numbersa ."

Tafiya minister yake a hankali yana jan tanweer da hira cikin hikima yake tambayarta abubuwa da suka faru daita, ita Kuma tana bashi amsa tare da Allah Allah su k'arasa gida ta ga mumynta , shi kuwa a ransa ba gida yake da burin kaita ba hospital zai zarce daita tukun nan
domin a bincika masa lafiyarta . kafin ya karaso cikin gari tuni bacci ya d'auke tanweer sakamakon hodop din da suka tarar a hanya , a hankali ya waiga bangaren da take zaune ta d'aura kanta a saman kafad'arsa yaga bacci take da alamun ma yayi nisa ya shafa gefen fuskarta cike da matsanacin farinciki yana sauke naunayen ajiyar zuciya .
A bakin had'add'en get din ST hospital ya tsaya tare yin hon masu gadi suka Bud'e masa tafkeken get din ya sanyo hancin motarsa ciki .
yana gama daidaita parking ya cire kanta a saman kafad'arsa har lokacin bata Farka ba dan haka ya kwantar daita akan kujera ya fito ya bud'e Inda take zaune ya cirota ya sa'bata a kafad'arsa ya nufi cikin hospital din daita , yayi tunanin kawo wannan hospital din ne bai kaita nashi Wanda ya mallaka Mata ba dan rufawa kai asiri domin acan duk bincike da za'a yi ba lallai bane ace wasu daga cikin likitocin bazasu sani ba."
Duk da dare ne amman daga cikin mutane sun fahimci minister lfy ne da Ido kawai jama'a suka dinga binsa .

Har karfe goma sha biyu saura na dare hjy Zainab bata ga shigowar minister ba zuciyarta cike da mamakin Inda ya tafi a daidai wannan lokacin dan rabon da yayi nisan kiwo irin haka har ta manta tun kafin a d'auke tanweer.
ta kira dukkanin layukansa basa shiga abu daya ake fad'a mata switch off gashi bazata iya runtsawa batare datasan halin da yake ciki ba.
tana cikin wannan halin sai ga wayarta ta soma ringing cike da tsinkewar zuciya ta Kai hannu kan bedside dinta Inda wayar take ajiye ta d'auka tana duba screen din wayar sunan minister ta gani yana yawo da sauri ta d'auka tare da Jan Koren madanni ta manna wayar a kunnenta tana furta "Assalamu alaikum". bai tsaya amsa mata sallamarta ba yace "ki shirya yanzu dolapo zaizo ya daukeki ya kawoki ST hospital". "Hospital Kuma"? "Lafiya ?
"waye bashi da Lafiya? ta furta a lokaci daya muryarta na rawa. "karki damu idan kinzo zakiga ko waye bashi da Lafiya "a'a dan Allah ka fad'a min wallahi gbdy ka d'aga min hankali gabana banda faduwa babu abinda yake a yanzu . "Kai Zainab matsalata dake kenan saurin d'aukar abu da zafi kiyi abinda nace dolapo zai zo ya daukeki. "banason irin haka fa kasan a yanzu komai na iya faruwa dani, ni dai ka fad'a min nasani tun kafin nazo "nima banason yadda kike d'aga min hankalinki ki karaso zaki ga komai yana gama fadar haka yayi disconnecting din Kiran hankalinta a matukar tashe ta mike ta soma shiri, tun kafin dolapo ya karaso har ta gama ta fito suka d'auki hanya cikin kankanin lokaci suka karaso hospital dolapo na gaba tana biye dashi Allah Allah take takaraso taga waye bashi da Lafiya.
dolapo bai tsaya a koina ba sai a bakin kofar d'akin da minister yayi masa kwatance yasa hannu ya kwankwasa kofar daga cikin d'akin aka bada umarmin shigowa ya tura kofar batare daya shiga ba sai hjy Zainab ce ta sa Kai ciki d'akin tana shiga dakin idanunta suka sauka akan tilon diyar kwance Kamar a mafarki kusan mutuwar tsaye tayi kafin daga bisani ta dafe bangon d'akin ta manne sosai tana murza idanunta da hannunwata duka " .

a hankali minister ya k'arasa Inda take ya rikota "dan Allah ka barni karka tasheni a mafarkina "cool down Zainab wannan ba mafarki kike yi ba it really gaske ne tanweer diyarmu ce kwance a gabanki tana jin abinda ya fad'a ta gyara tsayuwarta sosai ta tsaya bisa kafafunta tana maida hankalinta sosai akan tilon diyarta da sauri ta shiga daga kafafunta tana mai zubar da hawaye Wanda take Jin radadinsu har cikin ranta ta k'arasa Inda take kwance ta d'aura hannunta akan sumar kanta mai tsantsi ,ta dinga binta da Kallo "mai ya sameta na ganta haka ?sun cutar min da yarinya ko ?"sun lalata min rayuwar yarinyata ko? tayi masa tambayar ajere hawaye masu zafi da ciwo na sake zubo mata akan quncinta "ki kwantar da hankalinki tukun nan ba'a dubata ba tana dai hutawa ne ".
"Allah kasa basu cutar min da yarinyata ba ta k'arasa maganar tana sheshekan kuka tare da tsurawa tanweer idanunta , qauna da tausayin diyarta suka lullu'beta gbdy ta kasa d'auke idanunta akanta ,yarinyata tayi kyau sosai tamkar ba daga hannun yan'ta'adda ta fito ba skin dinta sai wani sheki yake ."naunayen ajiyar zuciya hjy zainab ta sauke tana cewa"Kasan san Allah zuciyata rawa take sosai akan tanweer jikina na bani an ta'ba min yarinya. "ki kwantar da hankalinki sannan ki sawa ranki komai ya faru damu daga Allah ne mu ma godewa Allah da muka ganta a raye Kuma cikin koshin lfy ...."inshallahu ma babu wani abu nasan Kai din mutumin kirki ne da yarda Allah kamewarka da jin tsoron Allah'nka bazai sa wani abu ya samu tilon diyarmu ba tana gama fadar haka ta mike rike da wayarta tana kokarin neman layin hjy baseera "
da sauri Minister ya rike mata hannu "wazaki kira a daidai wannan lokacin"? " hjy baseera ta bashi amsa da haka "karki fara Kiran kowa tukun nan mubari musan matsayin da diyarmu take ciki, yanzu ma gida zamu wuce mu Barta har zuwa gobe idan Allah ya Kai mu sai dawo.
"Da wani kallo tabishi dashi sannan tace "kana tunanin zan iya barin

Please Login or Register in order to submit comment