"to yanzu kana ganin idan an canza masa za'a samu me karfin na farko ?"sosai kuwa za'a samu zan duba me karfi wanda yafi na farko zuwa gobe sai nazo dashi "to shikenan na gode son Allah yayi maka albarka ya Kai hannu ya zagaye kafad'an nazifi yana tafiya dashi acikin falonsa" ka cigaba da bin umarninna ni Kuma bazan gaji da tura maka sakona ba "nazifi ya gyada masa Kai tare cewa "babu komai dady ai ko baka biyani ba ya zama dole nabi duk wani umarninka nasan kana da wata munafa me kyau akan ib shiyasa kake bukatar ganinsa akwance ?".
"yauwa nazifi a she kana da fahimta ?" shi yasa kullum kake kara burgeni saboda kaifin baseerarka" cike da girmamawa nazifi yayi sallama da alhj Tahir ya fito zuwa babban falon gidan Inda ya iske hajiya baseera zaune kusa da Ibrahim dake zaune akan wheelchair tana bashi abinci a baki tausayinta dana Ibrahim ya kamashi ,mace har mace me tausayi da biyayya amman batayi sa'ar miji ba "har ka fito nazifi ? "eh mumy na fito "to sannu da kokari Allah yayi muku albarka gbdy , yadda kake kula da abokinka baka gajiya Allah ya kula da lamarinka "Ameen mumy ai kula da ib ya zama dole , Ibrahim ya dubesa wuyansa a karye magana yake son yiwa amininsa amman ya kasa furta Komai so yake ya sheida masa Kiran daya samu daga bakin alqali a kwanakin da suka gabata .
sai da nazifi ya sake duba jikin Ibrahim sannan ya fito zuwa haraban gidan ya shiga motarsa ya zauna ya bata wuta, tafiya kad'an yayi ya gangara gefen titi yayi parking ya Kasa cire hannunwansa akan stearing motar ya shiga kogin tunani ta yarda alhj Tahir yake wa dan lelensa wanda shi kad'ai ya haifa a duniya mugunta.ji yake kamar ya tattara ib da komai nashi ya turasa zuwa kasar england domin ya samu kulawa daga manya likitoci , dan allurar da mahaifinsa yake sa shi yayi masa bata da maraba da poising me karya garkuwar jiki gashi sanadiyyar haka an tsaida komai nashi bayan shi din mutum ne mai qulafucin akan aikinsa"gbdy zuwa yanzu ya soma zargin manufar alhj Tahir akan d'ansa Ibrahim, idan kuwa haka ne babu shakka akwai lauje cikin nadi wato akwai saka hannun alhj Tahir cikin kidnappin din tanweer da yan fashi suka yi .
"haka ne ma zuciyarsa ta tabbatar masa da hakan , wannan dalilin yasa alhj Tahir baya son Ibrahim ya tashi bisa kafafunsa ya nemi tanweer da karfin da iKon da Allah ya bashi, tabbas Ibrahim nada gogewa da jajircewa da qulafici akan aikinsa da duk wasu masu laifi a kasar nan.
" idan ya gangara ta bangaren aikin sirri shine kan gaba saboda kwarewarsa ya iya binciken sirri tamkar aljani tare da abokan aikinsa har su gano me laifi yanzu abinda zai yi zai cigaba da boyewa alhj tahir tare da biye masa har sanda zai kammala komai akan abinda yake zarginsa akanshi tare da nemo sheidu masu karfi ta yadda za'a samu nasarar kamashi a sikwane , yana da tabbacin muddin aka kamashi za'a kama ragowar abokan sana'ar tasa dukkaninsu su girbi abunda suka shuka ya kusan awa d'aya agurin yana saka da warwara har hawayen tausayin Ibrahim ya zubar saboda rashin dacen mahaifi da yayi sannan ya tada motarsa zuwa office dinsa har ya Isa office tunanin aminisa yake .."
*******
Tanweer bata farka ba sai gurin karfe d'aya na rana ta farka cike da matsanacin azaban ciwo dan ta sha wahala sosai jikinta na rawa koina ciwo yake mata sai numfashin wahala take fitarwa , wani abu ya hadiye sannan ya matso kusa daita sosai ta bud'e idanunta da suka mata nauyi ta ga shine zaune a kusa daita wani marayan kuka ta fashe dashi tana shesheka, muryarsa a kasalance yace "lafiya kike kuka me ya sameki ? ya fad'i haka ne dan ya sake tabbatar da tana sane da abinda ya faru a daren jiya duk da baya doubt akan gaskiyar abinda baba ya fad'a masa .ta fashe da wani sabon kuka tana cewa "nima bansani ba amman duk ilahirin jikina ciwo yake min tunda nake ban ta'ba Jin irin wannan ciwon ba dan Allah ka taimakeni ka maidani gida ....." ta k'arasa maganar tana sheshekar kuka bai sake yin magana ba ya ɗauketa cak ya nufi bayi daita ya had'a mata ruwan zafi ya Kai hannu zai riko hannunta ta goce ya bita da wani kallo.
ta zabga masa harara tana hura masa hanci ,shiru yayi yana cigaba da kallonta yayinda kukanta yaki tsayawa ganin ko ya rarrasheta 'bata bakinsa zai yi yasa a hankali ya Isa Inda take jingine acikin bayin ,batayi expecting ba taji ya rungumeta ajikinsa tsam , ajiyar zuciya ta saki ta had'e rai sosai .
rarrashinta yake son yi amman yasan halinta ba lallai ta bashi had'in Kai ba zata iya butsare masa "tanweer ! ya kira sunanta muryarsa a sanyaye tana jinsa taki amsawa ta cigaba da kukanta "tanweer !" ya sake kiranta cike da rauni Yana shafa sumar kanta zuwa gadon bayanta " Kince jikinki na ciwo ? ta gyada masa Kai kawai " ki d'aure please ki shiga ruwan zafi zaki daina jin ciwon kinji "tayi masa banza tamkar ba da ita yake ba bare ta nuna alamun zata yi abinda ya bukata ,a hankali ta soma k'okarin kwace kanta daga jikinsa har ta zare ta tsura masa idanunta fuskarta babu annuri a kallon da take masa taga goshinsa ya dan kubura ta Kai hannunta ta shafa gurin batare da tace masa Komai ba duk da tmbyrsa bakinta yake son yi amman ta kasa sarrafa harshenta , hannunta ya kamo cikin nashi ya matse gam "ki shiga ruwan zafi zan gasa miki jiki ta yadda zaki daina jin ciwon komai ajikinki" girgiza masa kai tayi sannan ta motsa labbanta " ka fita kawai zanyi da kaina ba sai ka tsaya ba dan bazan iya tubewa agaban wani katon banza ba ta fad'a Kai tsaye taja ka'fafunta ta jingina jikinta da bango bayin ."
yayi shiru kawai yana kallonta maganarta ta sosa masa rai sosai azahiri ake iya hango hakan "idan Kuma bazaka fita ba bari ni na fita ta juya tana d'aga ka'fafunta da kyar ya nad'e hannun rigarsa ya kamo kafadarta bai tsaya wata wata ba ya d'auketa ya dannata cikin ruwan zafi wani qara ta saki mai sauti ta zabura zata mike ya sake dannata ta zaro idanuwanta gbdy hawaye na zubo mata , kallon juna suke wanda ita nata kallon na fita haiyaci ne shi kuwa na mugunta ne "muryarta a tsarke tace "Allah ya Isa ban yafe ba mugu azalumin kawai Allah ya Saka min nace maka zan gasa jikina dole ne da zaka wani sundumani cikin ruwan zafi dan mu...." ? bata k'arasa mgnrta ba ya dalle mata baki da yatsansa "har yaushe zaki daina yiwa mutane rashin kunya ?ya fad'a yana sake dannata cikin ruwan zafi har sai da ta sake sakin qara me sauti tana cewa " har sanda mahdi zai bayyana ta bashi amsa da haka tana marairaice fuska .
tausayinta yaji yana yawo a sansar jikinsa shiyasa ya rabu daita dan inya biyewa rashin kunyarta komai zai iya faruwa a tsakaninsu "ni ka barni haka zafi na ratsani dayawa "ta fada tana kallonsa "abinda kika fad'a nayi aiki dashi "to ni me na fada ?ta tambayesa muryarta cike da shagwa'ba tana turo masa karamin bakinta "muryarsa can kasa yace "kince jikinki na ciwo har kasanki ko ba haka ba ?tai masa banza tana bata fuska tare da d'aga kanta sama alamun tunanin tana son ta tuna lokacin da tace masa har da kasanta ke mata ciwo ita dai tasan tace masa jikinta "ko zan iya sanin abinda yasa kike jin ciwon jiki da kasanki? ya tambayeta yana k'okarin zare rigar jikinta , idanunta ta tsura masa tana kallonsa cike da mamaki hannunsa ya Kai yana shafa bakinta kafin daga baya ya maida bakinsa ya fara kissing dinta in a romantic way tun tana turjewa har dai ta hakura ta barshi bayan ya gama romancing dinta ya zare hannuwansa yana cewa "kiyi wanka ki had'a dana tsarki ".
zaro Ido tayi waje cike da mamaki tana maimaita abinda yace a zuciyarta " ki maida wadan nan idanun naki kiyi abinda nace yana gama fad'ar haka ya juya zai fita ya jiyo sautin muryarta tana cewa "akan wani dalili zan had'a da wankan tsarki ni ba janaba ba ?"ya juyo a natse yana kallonta tai saurin kare qirjinta da hannuwanta , ya kwa'be baki yana kashe idonsa d'aya a ransa yace" abinda na kwashe rabin dare Ina sarrafasu shine dan manufarci kike wani boyewa ,numfashi ya furzar ya sake juyawa yana cewa"kiyi k'okari kiyi wankan dana tsarki idan Kuma kin Isa karki yi zan gane "baza'a yi ba , babu janaba ajikina dan hk babu wani wankan tsarkin da zan yi daf da zai bar d'akin yaji ta fad'i haka "kwa'be fuska yayi " yarinyar nan da alamun sai na baki tarbiya kafin na maidake gidan ubanki dan kanki na mugun rawa."
d'akinsa ya koma ya shiga wanka sai daya d'auki minti ashirin yana bayi sannan ya fito yana goge jikinsa da karamin towel fari tasss yana tunanin tanweer, hakan nan yake qara Jin qaunar yarinyar na mamaye ilahirin jikinsa sai dai yayi ta k'okarin yakice hakan yana karyatawa , ya shirya kanshi cikin wasu Kanana kaya wando da riga farare sol ya feshe ilahirin jikinsa da turare , ya zauna a bakin gadansa ya d'auki d'aya daga cikin wayoyinsa ya kira number aliyu number bai shiga ba da alamun akwai matsalar network ya mike tsaye ya fito yana neman layin eku kira d'aya ya d'auka tare da cewa "boss Ina yini ?"Lafiya ya fad'a atakaice , yana tafiya yana bashi umarnin ya d'auki kudi yaje adidas ya siyo masa abinci ya k'arasa maganar yana tura kofar d'akin da tanweer take ,Koda ya shiga d'akin tana kwance ta lullu'be jikinta da blanket kanta ne kawai a waje tana rawa sanyi .
gashin kanta yabi da Kallo bai ga alamun ruwa ba ya had'e fuska sosai ya k'arasa ya Kai hannunsa cikin sumar kanta ya cusa har yana ta'ba fatan kanta bai ji alamun ruwa ba ya cire hannunsa yana cewa "ke........" !
ta d'ago kod'ad'un idanunta ta zuba masa batare data amsa ba " wasa nake dake Koni sa'anki ne ?to ni me nayi Kuma nifa wallahi bana son takura tunda Kai ba sa'ana bane ka mayar dani Inda ka d'aukoni mana "tayi maganar jikinta na karkarwa ta janyo blanket ta sake rufe jikinta har kanta a zuciye ya fixge bargon yayi filinging dashi yana jan tsaki "ki tashi kije kiyi wankan tsarkin da nace ko na 'bata miki rai yanzu "kamkame jikinta tayi guri d'aya ta lafe akan katifa bata da alamun tashi ."
wata razananniyar tsawa ya buga mata wanda yasa tayi zumbur ta mike tsaye har hantar cikinta na kad'awa ta kwa'be masa fuska tana kallonsa, da yatsansa ya nuna mata hanyar bayi simi simi ta juya tana d'aga ka'fafunta da kyar dan kwata kwata bata ga al'amun wasa atattare dashi ba a yadda take kallonsa zai iya marinta har ma ya had'a da duka yabi tafiyarta da kallo gbdy yanayin tafiyarta ta canza kallo d'aya me hankali zai mata ya fahimci halin da take ciki ,bai d'auke idanunshi ba har sai daya shiga bayi ta bugo kofar da karfi .
numfashi ya sauke ya koma bakin gado ya zauna yana neman layin amminsa suna waya ta fito d'aure da towel tana rawar sanyi ya tashi ya rungumota jikinsa ya zaunar daita a gefensa ta rakube ajikinsa tana karkarwa ya janyo blanket ya lullu'beta tare da yi mata alamar ta kama kanta waya yake sun dade suna waya da amminsa tana sauransu Kuma duk akan maganar abinda za'a yiwa baqinsu masu zuwa neman auren shafiqa ne acikin satin ...
Lokacin da suka gama wayar tuni bacci ya d'auke tan ya kwantar daita ya tashi ya d'auko mata wata rigar ya dawo har zai Saka mata ya tuna da magani dan haka ya fita ko second biyu bai yi ba ya dawo rike da roba da gayen magariya yayi adduoi aciki ya shafa mata sannan ya Saka mata kaya ya lullu'beta ya kashe ac d'akin gbdy ya fita daga d'akin zuwa nashi ya kwanta a falonsa akan doguwar kujera."
Bai jima da kwanciya ba aka soma knocking kofar falonsa , yana daga kwance ya bawa mai yin knocking ɗin izinin shigowa eku ne ya shigo cikin falon hanunsa riƙe da farar leda, cike da girmamawa ya rusunawa ogan nasa a natse Jaguwa ya mike zaune ya zura silifas ya amsa ledar yana masa godiya eku ya juya ya fice daga falon.mikewa tsaye yayi ya fito ya shiga ɗakin tan batare da yayi knocking ba kamar yadda ya saba koda yaushe zai shiga Kai tsaye ne , sai kawai ya tura ƙofar ya shiga ciki, tun sanda ya kawota gidan yake jin haushi Kansa da bautan da yake mata amman a yau din jin zuciyarsa yake fessss akanta zai iya mata komai ciki kuwa har da zama bawanta .
Tana kwance akan gado ta kwanta ruf da ciki, bacci ta keyi har lokacin hankalinta a kwance, murmushin gefen baki yayi kamar tana ganinsa haɗe da aje ledar hannunsa" sarkin rigima da rashin kunya ya fad'a a ransa , har ya juya zai fita daga ɗakin kuma sai ya tsaya yana kallonta tun daga yatsun kafaunta har zuwa kanta komai nata abun burgewa ne , ahankali ya taka zuwa inda take kwance, tafin kafansa d'aya yasa ya ɗan shafa tsakiyar kafarta .
azabure ta farka ta zauna tana murza idanunta dan har lokacin Jan da sukayi bai baje ba , sake kallonta yayi, "Ki tashi kije kiyi wanka kiyi alwala kiyi sallah , ke fa na lura sallah bata dameki ba dan zaki iya wuni bakiyi sallah ba ki kuma kwana bakya damuwa" yayi mgnr yana mai tsareta da sexy eye's dinsa."
Tsura masa idanunta tayi tana kallonsa tana Jin haushin abinda yake mata sai ya fad'awa mutun mgn yayi kmr bashi yayi maganar ba, saboda yanda yake fizgo mgnr da kyar Kallon agogon d'akin tayi yanzu ne ma hud'u ta wuce muryarta a raunane tace "gara ni ko banyi sallahr akan lokaci ba zan rama Kai fa ?meye amfanin sallahrka akan lokacin tunda kana aikata aikin haram, wad'amuhu haramun ,washarabahu haramun wa guziya bil haramun wa'anna ....."ki min shiru anan stupid " ya fad'a a tsawace , ana tausayinki bakya tausayawa kanki "nace ka tausaya min ne? ko nace ka cigaba da rikeni dole ? Ko nace dole sai ka zau....."Idan kin sake furta wata kalma anan sai na tattakaki idan km kin mutsa bismillah kiyi " yana gama faɗan haka ya fice daga cikin ɗakin ransa a bace, gsky yayi mugun sakewa yarinyar dayawa shiyasa ta rainashi .
Saukowa tayi ta shiga bayi tai alwala ta fito tayi sallah tana idarwa ta mike ta Isa gaban mirrow ledan da ya aje mata ta ɗauka haɗe da buɗewa, robobin take away ne acikin har guda uku, ɗaukan ɗaya tayi haɗe da buɗewa ta soma ci, kad'an taci dan zazzzabi take ji sosai bata jin dadin bakinta ta sha ruwa kad'an .
kamar ta koma ta kwanta ta tsinci kanta da fitowa, kanta babu dankwali ta fito zuwa falo da kyar take taka ka'fafunta , yana tsaye agaban tv ya bawa cikin falon baya yana ƙoƙarin danna code din bude wayarsa , jin motsin mutun a falon yasa batare da ya juyoba yace. "waye ? "Waye byn wacce ka sato ka ajiye a gidanka ita ce ta fito ta sha iska tayi mgnr da kyar tana kokarin zama akan kujera "shekaru sun ja wallahi ya kamata ka tuba ka daina harkar fashi ,nasan da mahaifiyarka tasan wannan aikin kake yi da bata yi alfahari da Kai ba a karshe kashe kanta zatayi dan bakinciki ."
A matukar fusace ya nufo Inda take tamkar wani mayunwanci zaki ya damki wuyanta yana Shirin danne makoshinta ya fasa saboda zafin daya ratsa tafin hannunsa ya tsura mata Ido kawai yana kallonta "ka shaki ne mana ai ni yanzu a shirye nake da mutuwa gara min mutuwa akan cigaba da zama da Kai ,a farkon had'uwa ta da Kai naji duk duniya Kai mutumin kirki ne ,Kai ne mutumin da zuciya da gangar jikina suka mace akansa saboda a tunanin zuciyarka me kyau ce a she ba haka bane mugun ciwo ne daskare a zuciyarka wannan mummunar sana'artaka yafi min komai zafi acikin zuciyata wanda adalilin haka yanzu babu kyakkyawan zaton da soyayyarka acikin zuciyata sai zallar tsana ,na tsaneka tsanar da zan iya ganin bayanka ka rubuta ka ajiye muddin na bar gidan nan sai nasa ka shiga ha......."
"karya ne " ya fad'a a tsawace yana nuna ta da yatsansa "karya ne baki Isa ba , baki Isa kisa akamani ba how could you tell someone tanweer ?" you can't do that , bazaki iya ba sannan jaguwa ba zai kamu ba cikin sauki ba sai dai wani mutun dabam, da zan kamu da ban Kai iyanzu ba" yayi mgnr yana furza mata iska a fuskarta tayi saurin runtse idanunta gabanta na faduwa , ya juya mata baya tare da rike kugunsa da hannu d'aya ya fara zagaye falon zuciyarsa na tafarfasa can ya juyo a matukar fusace "and kikace me byn zaki sa na shiga hannu ?" Kin tsaneni tsanar da zaki iya ganin bayana Shima karya ne zuciyarki bazata iya rabuwa da soyayyata ba yadda kika furta cewar kina sona haka zaki tabbata da sona a karshe ciwon sona ne zai kasheki saboda Ina ranki ,na shigeki shigar da bazaki iya cireni a ranki ba ,zaki je gidan wani da tarin soyayyata gangar jikinki za'a Kai gidan wani zuciyarki kuwa tana nan ....."ya nuna qirjinta daidai saitin zuciyarta .
wani irin sarawa kanta ya dinga yi da karfi kmr zai ra'be gida biyu tayi matukar firgita da Jin mgnr shi , ta d'auka zai tsorata da maganarta sai dai taga sa'banin haka atattare dashi sam shi din ba matsoraci bane zuciyarsa a dake take ,kallonsa tayi tare da ciza lips dinta batare data sake yunkurin cewa komai ba "ki tashi ki 'bace min da gani banason ganin wannan banzar fuskarki, karki qara kuskuren zuwa Inda nake sannan duk abinda kikaga Ina yi miki karki d'auka so ne , ba so bane tanweer dan ko digo d'aya na sonki babu shi acikin zuciyata bakya cikin irin tsarin matan da zan so , idan Kuma kin koma gaban iyayenki dan Allah karki fasa idar da nufinki akaina kiyi Ina jiranki wani irin zafi da ciwo kai ne me karfi yayi mata diran makiya gbdy jikinta ya sake d'aukar zafi tayi karfin halin dafe kanta cike da sanyi jiki ta mike ta nufi hanyar komawa d'aki sai da tayi da tasanin fitowarta ."
da kyar ta dinga d'aga ka'fafunta da
idanu ya bi bayanta yana kallonta rai a 'bace har ta bace wa ganinsa sannan ya d'auke idanunshi yana fesar da iska zuciyarsa ban da zafi babu abinda take sai faman tsaki yake ja da karfi ya fad'a kan kujera ya runtse idanunshi tare dafe goshinsa cikin haka abokansa suka shigo suka samu guri suka zauna ganinsa haka yasa suka fara tmbyrsa abinda ke damunsa shiru yayi yaki cewa komai sai tsaki yake ja anas ya dafa kafadarsa "meye damuwarka Kuma ? Still shiru yayi yana ciza lip's dinsa jabir da jubi suka tashi suka fita dan sun San tunda yayi haka ba magana zai yi ba "ya kamata ka rage damuwar nan jaguwa nasan duk damuwarka bata wuce akan yarinyar nan ba "Ina matukar tausayin yarinyar nan anas amman ita burinta bai wuce taga bayana ba
yayi mgnr a fusace idanunshi sun yi jajur "kayi hakuri nasan da haka nasan kana tausayinta da qau...." wani irin kallo yayi masa wanda yasa anas ya hadiye abinda zai fad'a "na sha fad'a maka ka daina cewa Ina son yarinyar nan amman tunda haka kake tunani ka zuba Ido zan baka mamaki"
"yauwa haka nake so Ji abokina Ka bani mamaki ka rabu daita mu hutu tunda baka sonta banga amfanin zamanta damu ba dan kasancewarta damu matsala ne mu sallameta kawai anas ya fad'a yana cigaba da bashi shawara akan tanweer ..."
Ita Kuwa tanweer tana shiga d'akin ta shiga har gitsa d'akin tamkar mahaukaciya a karshe ta fad'a kan gado hawaye na zubo mata sharrrrr akan quncinta tasan hawayenta nada halaka da bakaken maganganun daya fad'a mata , zuciyarta ta karye madadin soyayyarsa ta bar zuciyarta kamar yadda take buri sai ta dawo mata sabo fil tunda take baa ta'ba kallon idanunta aka furta ba'a sonta ba sai Adnan shine mutun na farko jikinta ya sake d'aukar zafi sosai wuni ranar bai shigo Inda take ba har dare ita Kuwa zazzabi da dacin maganarsa da ciwon gajiyar sex din jiya suka hade mata guri d'aya tayi kuka har hawayenta suka kafe bai shigo Inda take ba ya kama kanshi dan yasan koya shiga gurinta wani rashin mutunci zata masa shi Kuma bazai dauka ba ."
washegari tun karfe goma suka bar gidan batare daya lekata ba , dan har lokacin haushin abinda tayi masa bai bar zuciyarsa ba Kowani titi jami'an tsaro ne over fiyye da duk wani abun hawa, duk motar data zo wucewa sai an tsaresa an bincika ciki da wajenta tun daga nesa suka hango motar jaguwa tun kafin motar ya gama karasowa garesu suka daga ma eku hannu alamar ya tsaya a hankali motar ta rage gudu tare da k'okarin yin gefen titi ,a hankali eku yayi waning glass din motar yana mazurai ,daya daga cikin police officer ya dan leko cikin motar, cikinsa ne ya duri ruwa sakamakon ganin pesto a hannun jubi , ya ware Idanunsa sosai yaga ak 47 akan cinyar eku dake tuki ya Kai Idanunsa baya nan yaga sabon tashin hankali domin kuwa manya bindigu ya gani akan cinyar anas da jaguwa wanda ya kawar da fuskarsa gefe yana kallon titi da sauri Police office's din da suke zagaye da motar suka yi baya jiki na rawa .
daya daga cikin police yace "sorry ban San ku bane you can be on your way " a hankali glass din motar ya fara yin sama motar ta fara move police sukayi sauri suka tsaida wani me adaidaita suka duba cikin motarsa kana suka bashi hannu ya wuce direct to Ogun state suka nufa basu suka dawo gidan ba sai daf da sallar magriba wanka ya fad'a tare da alwala ya fito ya soma k'okarin gabatar da sallah byn ya idar da sallah magrib ya nufo d'akinta hannuwansa duka zube cikin aljihun wandonsa ya hangota kwance tayi ruf da ciki ko motsi kirki bata iyawa , ganin yanayinta yasa qirjinsa bugawa da sauri sai dai bai nuna hakan ba a fili tun kayan jiya ne sanye ajikinta, harara ya wurga mata sakamakon tuno abinda tayi masa a natse ya qaraso Inda take ya Kai hannunsa wuyanta nan yaji wani zafi ya ratsa tafin hannunsa kmr ta buge masa hannu sai dai bazata iya ba dan jikinta babu karfi "baki da lfy ne ?ya tambayeta banza tai masa taki motsa labbanta "raguwa banza kawai ya fad'a acikin zuciyarsa ."
"Kinyi sallah ma kuwa ?
Still shiru tayi masa bai damu ba ya cigaba da mgn "idan kinyi sallah ki canza kaya ki sameni a falon dan naga alamun tun kayan jiya ne ajikinki yana gama fad'ar hk ya juya har ya kai tsakiyar daki yaja ya tsaya yana cewa "na sanki da shegen d'aurin Kan tsiya ,minti goma kawai na baki ki sauya kaya ki fito dan Allah karkiyi abinda nace ya cigaba da tafiya ya fice daga daki .
Babu yadda ta iya ta mike ta shiga bayi alwala tayi ta fito ta tada sallah byn ta idar taki sauya kaya kmr yadda ya bukata ta fito , yana tsaye tare da friends dinsa ta fito duk suka tsura mata Ido suna kallonta maganar jaguwa ta jiya ce ta fad'o musu sosai suka qura mata Ido
suna yabawa da kyawunta .
yaji motsin fitowarta amman yaki juyawa "muje ko yace
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 18 Chapter of 62