itama kukan take saboda jikinta na bata diyarta na cikin damuwa ,ta mike daga zaune da take ta shiga zagaye d'akinta zuwa babban parlou'n gidan ta wuce matar danuwan mijinta da suka kawo musu ziyara tare da yarinyar su zuwa haraban gidan tana baza idanunta gani take kamar zata ga diyarta daga sama matar danuwan Alh Abubakar da suke uwa daya uba daya ta biyo bayanta ta rungumeta ajikinta "kiyi hakuri inshallahu za'a ganta "jikina na bani tanweer tana cikin damuwa Allah kasa basu ma yarinyata wani abu me suke bukata daga garemu su kira mu su tambayi duk abinda suke so wallahi a shirye nake zan mallaka musu duk abinda nake dashi muddin zasu dawo min da farincikina ..."
Tunda Hajiya zainab ta fito hankalin minister ya rabu gida biyu wani bangaren ya koma gurinta yayinda wani bangaren ke gurin d'an'uwansa da suke tare "Haba Abubakar taya irin wannan babban abun zaifaru ace bazaku sanar damu ba 'yan uwa? Wannan wace irin rayuwace ta rashin zumunci kuka zab'a kai da zainab ?". Matashin Dattijon yayi maganar cike da b'acin rai yana binsu da kallo,
kallo d'aya zaka ma dattijon matashin kaga kamanni sosai da suke da Alh.Abubakar sai dai Ko a fuska zaka fahimci ya girmemishi.
"Kayi hakuri yaya Walh tallahi kaga dagani har zainab bama cikin hayyacinmu tunda wannan tashi hankalin ya faru, gaba d'aya Zainab bataci baresha ni kaina Walh bazan iya cema when last nasa abu a cikin nan nawa ba" Alh.Abubakar yayi maganar cike da damuwa wacce kallo d'aya zaka fahimci damuwa a kan fuskarshi me tsanani dan duk yayi baki ya rame kamar ba Minister of Health ba.
"Allah sarki Ubangiji Allah ya fito mana da ita lafiya dan walh tashin hankali ya zama dole. To wai basu Kuma kiranku Ko suna buk'atar k'arin kud'iba?". Yayi maganar cike da tausayin d'an uwansa.
Girgiza mishi kai Alh.Abubakar yayi. "Kod'aya walh! Ni da zasu kira Ko duka dukiyata ce saina had'a daita su dawo da munda Tanweer". Ya k'arasa maganar cikin rawar murya wacce ke k'ara fitar da damuwar shi. "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un". Alh.Usman yayi maganar cike da tausayawa nan ya shiga lallashin Kanin nasa tilo musamman ya jima bai ganshi ba kasancewar shi a Arewa yake da zama kaduna State da iyalansa hakan yasa bai sama labari ba sai da aka kwana biyu, yaji ciwo amma yanzu jin zantukan d'an uwansa yasa yaji jikinsa ya mai sanyi gaba d'aya a tare suka koma cikin parlou'n inda diyar Alh Usman rukkaya ke kwance akan kujera mai zaman mutun uku .
Numfashi jaguwa ya furzar ya mike tsaye zai bar daki "ka maidani gidanmu plz yaji sautin muryarta cikin sanyi ya doki dodon kunnenshi "nasan ka taimaka min ,ka karasa taimakon ta hanyar maidani ga iyayena "idan kina bukatar zuwa gida ki ci abinci kina gama ci ko second biyu ba zaki kara a cikin gidan nan ba zan maidake gaban iyayenki "yana gama fadar haka yaga ta matso da kujera da take zaune ta bude kwanon abinci daya fara yin sanyi ta soma tsukura ...." wayarsa ce ta dauki qara sauti ya ciro wayar daga cikin aljihunsa yana duba screen din wayar sunan Alh Tahir ya gani yana yawo ya lumshe idanunshi sannan ya dauka batare da yayi magana ba "cike da in inna alh Tahir ya soma magana "har yanzu baka dawo da yarinyar nan ba gashi akwai next taget dina akanta ya kamata zuwa yanzu kasan yadda zakayi ka dawo daita plz "doka ce ko iko kake son min ? ya furta masa haka a natse wanda zaka ɗauka maganar ba daga bakinsa ya fito ba sai agurin alhaji Tahir kamar saukar aradu yaji maganar .
saurin girgiza kai Alh Tahir yayi kamar yana gabansa "no babu ko daya naga dai ya kamata ne a dawo daita haka nan "to baza'a dawo daita ba kayi duk abinda zakayi ya ja tsaki yayi disconneting din kiran ya maida wayar cikin aljihunsa tare da zura hannunwansa ciki ya juya "ki tabbatar da kin ciye abinci nan tass kin shanye driks da ruwa ke everything dake gurin make sure kin gama dashi idan kina son barin gidan nan ", Allah bazan iya cinyewa ba yanzu ma da kyar nake tura wa ",Karki yi kiga abinda zai faru "ya karasa maganar yana barin dakin kai tsaye bangaren daya tanada domin shakatawa ya nufa a can ya iske abokansa da yaransa suna shaye shaye , masu shan wiwi nayi masu shan win nayi, duk sun cika gurin da hayaniya da hayaki suna ganinsa suka hau sara masa suna masa kirari gutun wiwin dake rike a hannun jubi ya amsa ya ɗan zuka yana fitar da hayaki ta hancinsa da bakinsa sannan ya fita ta kofar baya yana tunanin mugun hali irin na Alh Tahir ko me zai yiwa ƙaramar yarinya kamar wannan gashi kuma shi din aminin mahaifinta ne?
Kusan minti goma yana tunanin agurin "
*****
"Wai Ibrahim kana so ka kashe kanka ne akan mace". Momynsa tayi maganar cike b'acin rai wanda ke had'e da tsantsar damuwar halin da d'anta ke ciki. "Momy I can't live without Tan, ta riga ta zama rayuwa ta, inda abunda nakeso bai wuce Tanweer ba Mo...". "Dakata!". Ta katse shi ta hanyar daga masa hannu da tare da mai tsawa. "Ibrahim bazan taba son ka rasa ranka akanta ba duk da nima ina matukar kaunarta saboda irin son da kake mata ,but at least ka duba lamarina kai kad'ane d'ana taya zanso akan wata 'ya mace wani abu ya sameka ?".
Tayi maganar tana kallon Ibrahim wanda tunda ta soma maganar idanunsa ke runtse.
"Ibrahim!". Ta kira sunansa cikin wani irin yanayi wanda bai taba saninta dashi a rayuwarsa ba" gaba daya Inaso kayi hakuri da Tanweer!". Ta karashe maganar cikin dakiya tana kallonsa ganin yadda har ya samu courage d'in tashi zaune shida tun b'atan Tanweer bata ganshi a zaune ba.
"Mom!". Ya fada cikin daga murya tare da gyara zamansa yana binta da wani irin kallo idanunsa ko kiftawa ba yayi, already ya gama zazzarosu waje gaba daya what !". Yayi maganar yana kallonta kamar bai fahimci abunda yake faruwa ba musamman furucinta. "Mom!". Ya Kuma fad'a yana kallonta cike da mamakin furucinta."Haba Momy, taya zakiyi wannan furucin na rabu da Tanweer bacin kinfi kowa sanin irin son da nake mata? How could you utter such words uhm?!". Ya jero mata tambayoyin cike da damuwa lumshe idanu tayi tare da fadad'a murmushinta tana shafa sumar kanshi.
"Ibrahim kenan,". Ta fada tana kad'a kanta ,sannan ta tashi ta soma taku yana binta da koda'dd'un idanunsa da suka sha wahala saboda rashin ganin abincin su Tan, har ta Kai k'ofa sai Kuma ta juyo tayi murmushi me sauti tana kallonsa lokaci guda Kuma fara'a dake tattare da fuskarta ya d'auke nan take bacin rai ya maye gurbinshi."Hmm! Yaro yarone nan gaba zaka gane da kanka nasan dalilin da yasa nace ka hakura da yarinyar nan ". Tana fad'in haka ta fice ta barshi zaune zuciyarsa cike da tunanin zantukan ta musamman bacin rai daya hango cikin idannun Momyn nasa wanda kusan ya jima baiga hakan tattare da fuskarta ba. Wayarsa da ta soma ruri ne ya katse mishi tunanin daya shiga ya soma zurfi, hannunsa na rawa ya kai hannunsa ganin me kiran, da sauri ya manna wayar a kunnensa banajin me ake fada masa a can d'aya bangaren naga ya tashi da sauri. "What?!". Ya furta da d'an k'arfi tare da runtse jajayen idanunsa ya bude su tuni suka k'ara rinewa tare da k'ara tiruwa zuwa ja sosai kamar jan gauta. "Alright I am coming". Ya fad'a da sauri tare da wullar da wayar kan bed d'insa.
Yunku'rin k'arasawa wardrobe yayi amma me wani irin jirine ya kwasheshi da sauri yasa hannayensa akansa saboda wani irin nauyi da rada'dd'i da suke masa, yana ciza pink lips d'insa kanana wanda suka sauya colour saboda azabar ciwo a d'an bushe "Ya Salam I.B!". Dadynsa ya furta wanda ya bud'e ko'farsa kenan a daidai lokacin da I.B ke ko'k'arin k'arasawa k'as, cike da matsanancin tashin hankali Alh.Tahir ya k'arasa ya tallafoshi zuwa jikinsa inda yak'arasa sauke su kan bed d'in. "Ta...Ta...Tan! Da....". Karasa kulle idanunsa yayi hankalin Alh.Tahir ya tashi a wannan lokacin banda ihun kiran sunan matarsa cikin tashin hankali babu abinda yake dan ya fara tsorata da yanayin dan nasa .."
Darling's
💗💗💗💗💗💗
KUSKUREN BAYA
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
PAID BOOK
WRITING BY
AYSHA .A BAGUDO
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukata karanta shi ya tura 500 ta wannan account number din 1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan a tura sai a turawa wannan number+234 703 534 8686
alert domin tabbatar da an tura ko wannan number 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi sai a tura ta wannan number 08059623096 kada ayi vtu a number MTN ,domin sauraran littafaina a tuntubi Channel dina ta Hausa bakwai.
🅿️12
......Cike da dakiyar zuciya alqali ya cigaba da bin bayan motar jaguwa land cruiser prador yana sake neman layin IB domin bashi direction din Inda yake a daidai wannan lokacin sai dai Kiran na shiga ba'a d'auka ,ya kira ya kai sau goma bai d'auka ba wanda a wannan lokacin nazifi da alhj Tahir da hjy baseera ne tsaye a kanshi nazifi na qakokarin bashi taimakon gaugauwa , haushi ya kama alqali ya ciza gefen lips dinsa yana dukan sitiyarin motarsa "oh my goodness ko me yasa yaki d'aukar Kiran yanzu bayan bamu gama wayar ba ya ajiye ? yayiwa kanshi tambaya yana d'an rage gudun motarsa dan kar jaguwa ya fahimci su yake bi ."
yayinda a hankali motar jaguwa ke sharara gudu akan titin onipan a natse ya d'an juyo gefen da tanweer ke zaune shiru sanye da doguwar riga pinky colour ta yane kanta da mayafi baki haka ka'fafunta sanye suke cikin baby shoe baki masu matukar kyau tsintsiyar hannunta d'aure da agogo fata baki duk jaguwa ne ya bata su a wannin da suka gaba tare da yi mata albishir din maidata gidan iyayenta , kayan sun amshi jikinta sosai kamar dan ita aka yisu .
a hankali itama ta juyo cike da natsuwa fuskarta d'auke da murmushin jin dadi zata gida taga iyayenta cikin sa'a shima ya Kalli Inda take idanunsu ya tsarke cikin juna wani irin bugawa qirjinsu yayi , alokaci d'aya sukai shiru tare da tsurawa juna idanu gbdy suka kasa d'auke idanunsu .
a cikin zuciyarsa yake yabawa kyawunta "hakika tsarki ya tabbata ga ubangiji daya halicci wannan yarinyar , kallo d'aya zaka mata kasan kyakkyawa ce ajin farko ."
a natse ya d'auke kyawawan idanunshi acikin nata sakamakon ganin yadda ta kafe shi da nata idanunta da suka wadatu da zararan gashi Ido gashi ko kifta su bata yi shi kuma mutun ne da bai fiyye son kallo ba bare kallo irin nata dake saukar masa da kasala tare da sha'awa me tsayawa arai , dan nan take kallonta kesa yanayin mutun ya sauya batare daya shiryawa hakan ba." kasa d'auke idanunta tayi daga kallonsa saboda baiwar kyau da Allah yayi masa ta sha jin mutane na yabawa kyawunta haka zalika idan ta Kalli kanta a mirrow tana tabbatar da abinda mutane ke yawon fad'a akan tsarin jiki da kyawunta sai dai ko kusa bata kai shi komai ba , dan idan tana gabansa raina komai nata take domin gani take ya fita komai bama za'a a had'a ba .
muryarsa a kasalance ta fito kmr baya son yin magana "ki daina yiwa namiji irin wannan kallon domin duk macen dake kallon nmj haka yana nuna alamun bata da cikakken tarbiya ,mace da kunya da kauda Kai aka santa " ya qarasa maganar yana jan dogon tsaki dake 'batawa duk wanda akayi dominsa rai , runtse idanunta tayi gam tana zance zuci "nice mara tarbiya sannan mara kunya ?"tayiwa kanta tambayar ranta na quna da tuttukin bakincikin daya maye gurbin farincikin dake kwance a fuskarta , idan akwai abinda ta tsana a rayuwarta bai wuce wulakanci irin wannan ba , kusan second biyu tayi idanunta na runtse kamar bataji abinda yace ba , cikin natsuwa taje d'aura laulausan tafin hannunta saman kushin din kujera domin gyara zamanta taji ya sauka akan laulausan hannunshi nan take yaji qirjinsa ya cigaba da bugawar da yake , itama qirjinta ya shiga dukan uku uku dan wani irin zirrrrrrrrr taji lokacin da hannunta ya sauka a nasa .
ya sauke wani zazzafan ajiyar zuciya da numfashi alokaci d'aya ,
a hankali tayi karfin halin d'auke hannunta dake saman nashi a dalilin jikinta dake kyarma ta soma magana cikin fushi da bacin rai "karka sake furta min wannan kalmar domin kuwa kallon nmj bashi ke nuna rashin tarbiya ko rashin kunya ba dan haka bana son sake jin kalmar gareni domin ni din macece me tarbiya da kima idan Kai baka ganin kimata akwai dayawa masu gani ta k'arasa maganar hawaye na gangarowa akan quncinta ,ta sake kawar da idanunta sosai tana goge hawayenta dake tsiyaya "wani kallon banza ya watsa mata mai hade da harara " lallai yarinyar nan ma ta sameshi yadda ya kamata ,shi take maidawa magana ?ai duk laifinka ne da baka gyara mata zama ba ka tsaya kana tattalinta, yarinyar da yaka mata ka wulakantata ta hanyar keta mata haddi tunda abinda yasa ka d'aukota kenan " zuciyarsa ta fad'a masa
haka numfashi ya fesar yana jin zafin acikin zuciyarsa , sam bai ji d'acin Kalmar daya fad'a mata ba, dan haka yayi tunani sake musguna mata jikinsa a sanyaye ya Kai bakinsa daidai saitin kunnenta yana sake watsa mata kallon bazan tayi saurin gocewa tana furzar da numfashi tare da hura hanci sannan taki waigowa ta Kalli Inda yake bare taga kallon banzar da yake mata zafin da zuciyar ke yi yasa wasu hawaye masu zafi da ciwon sake zubo mata ita daya kamata ya farantawa adalilin zata tafi ta barshi tafiyar da ba lallai su Kara haduwa ba kamar yadda ya sha fad'a mata ."
ya matso kusa daita Sosai yana busa mata iskar bakinsa , bakinciki da takaici yasa tayi saurin janye jikinta daga nashi tana kallon gefen titi ,shiru yayi yana kallon gefen fuskarta numfashi ma da kyar take fesarwa bai san yadda akayi ba ya sake matsowa sosai ya d'aura kanshi a saman kafad'arta ,shiru tayi taki motsi sannan taki waigowa, jin shiru taki motsawa ya tabbatar masa da lallai fushi tayi dashi tsintar Kansa yayi da rashin jin dadin yanayinta can Kuma ya furzar da iska had'e da jan dogon tsaki "me yasa zan ji babu dadi araina dan tayi fushi dani ?ya jefawa kwakwaluwarsa tambayar " Kiran daya shigo wayarsa ya katse masa zance zucin da yake bare ya samu amsa daga wankakkiyar zuciyarsa , ya lalu'bo wayarsa daga cikin aljihun wandonsa ya mannata a kunnensa batare daya duba me Kiran ba.
jin sautin muryar amminsa ce yasa shi barin jikinta da hanzarinsa dan yana expecting jin dadd'adan labari daga bakinta dan jiya da sukayi waya yake sheida mata ya kamata ace yaron dake son shefiqa ya turo iyayensa ayi maganar aure ,a lokacin ammi ta tabbatar masa da zatayiwa shafiqa din magana , ai kuwa abinda yake expecting ji shi ta fara fad'a masa yasa wayar a hands free ya d'aura wayar a kafad'arsa ya jingina jikinsa sosai a kujera."
"yaron nan gali wai zai turo iyayensa ranar lahadi tare da saka rana gbdy " murmushi jaguwa ya saki na farinciki yana cewa " Allah ya nuna mana ranar lafiya so nake na aurar dasu gbdy kafin nawa auren . "a'a ban yarda da wannan tsarin ba ,idan ma son samu ne a had'a auren da naka ba qaramin farinciki zanyi ba "shinkenan ammina yadda kikace haka za'a yi bani da za'bin da ya wuce naki zanyi k'okari naga anyi auren da nawa sai dai ki qara addua akan wanda kike min Allah yasa na samu me sona tsakani da Allah "zaka samu da iKon allah dan baka da makusar da wata diya mace zata kika ni dai fatana kayi kokari ka cika min alkawarina Ina son kyakkyawar suruka me nagarta idan son samu ne wacce ta fika kyau". wani narkakken murmushi ya saki kamar yana gabanta kana yace "kin samu kin gama ammina dan sai na kawo miki irin matan hurul'ain dan irinta kike bukata ta zama surukarki ya k'arasa maganar yana dariya tare da matsowa ya kamo yatsun hannun tanweer ya rike gam cikin nashi yana massaging a hankali , itama ammi dariya take sosai tana sake tabbatar masa da hakan take so , ita Kuwa tanweer gbdy ranta a dagule yake sbd haushin abinda yayi mata da Kuma haushin maganarsa da mahaifiyarsa dan duk tana ji abinda mahaifiyarsa ke fada masa sannan tana Jin amsar da yake Bata cike da fushi ta soma k'okarin zare hannunta cikin nashi tana sauke wahalalle numfashi sai dai ta kasa kwatar hannunta dan haka tayita jan tsaki babu kaukautawa ganin hk yasa yayi sallama da ammi tun kafin ta tunhumeshi ,ya katse Kiran yana cewa "ki daina wahalar da kanki bake ba ko namiji dan'uwana na rike bai Isa ya kwace ba bare ke " ko kina tunani ni din irin lusaran samarinkanki ne da zaki gwada karfi dani ..?"ya karasa tmyr yana furzar da iska mai zafi daga bakinsa."
danne abinda taji ya tsaya mata arai tayi tana zance zuci" shi take mutuwar so amman shi burinsa kullum ya cusguna mata tare da nuna mata ita din ba kowa bace , tunda suka had'u yake kyautata mata ta hanyar bata kulawa sai dai a fahimtarta bashi da burin daya wuce ya 'bata mata rai ta hanyar fada mata baqaqen maganganu . tasan ba lallai ta zamo test dinsa ba amman at least itama tana da daidai nata kyau sama sama ta dinga fidda numfashi tana danne damuwarta "dan Allah direba ka taka motar nan da sauri Ina son d'aura kwayar idanuna akan iyayena wad'anda suka zamo min bango abun ma jingina kuma farincikina nasan suma nice farincikinsu rashina baqaramin babban tashin hankali bane garesu suna can suna mararina"
"shiiiii......." munafurcin banza kawai kina dai son kije kiga wad'an can rubabbun samarin naki barin wancan me murya gangarin da bata dadin saurara "ya Allah ta furta dan sai lokacin ta fahimci a fili tayi maganar , muryarta qasa qasa tace "kafa san irin maganar da zaka dinga fad'a min dan ni din ba motar haya bace bare kayi tunanin Ina tara kwashe kwashen samari Ko da yake yau ne final kasancewata da kai zaka mayardani gidanmu na gode da taimako ta k'arasa maganar tana murgad'a masa 'karamin bakinta "karki gode min ki godewa Allah sannan na fiki jin dadin zan rabu dake na huta da ganin wannan fuskartaki .
muryarta a raunane tace " aikin banza kawai Nima daga yau ai bazaka sake ganin ko me kama dani bane tayi mgnr tana jan dogon tsaki shiru yayi yana ciza gefen lips dinsa can kuma ya murtuke fuskarsa yace "wannan shine Karonki na farko Kuma Ina son ya zamo Karo na karshe karki yarda ki sake min tsaki a rayuwarki , ko ni sa'anki ne da zaki dinga ja min tsaki yayi tmbyr yana murd'e mata hannu qara ta saki mara sauti tare da cewa "a'a kayi hakuri hannuna zafi bai mata magana ba ya sausauta rikon da yayiwa hannun tare da bud'e tafin hannun ya tsurawa tsakiyar hannunta kyawar Idanunshi yana kallo , a hankali ya d'aura dayan hannunsa ciki ya fara mata tafiyar tsutsa wani irin tsalle hade da bugawa zuciyar tanweer yayi take tsigar jikinta suka mike kasa cewa komai tayi illa numfashin da take saukewa da kyar tare da jin wani sauyi na dabam a sansar jikinta. Shima wani irin abu yake ji yana masa yawo a gbdy ilahirin jikinsa wanda ya haddasawa qirjinsa tsananta bugawa wani tunani yayi gara ya sake musguna mata kafin su rabu ,wayarsa ya d'auka ya soma danne danne bayan kmr second biyu ya kira sunan eku remo dake tukasu ."eku ka duba wayarka na tura maka sako eku yace "noted boss ya tura wa su anas dake bayansa Sako kamar yadda ya turawa eku sannan ya koma ya jingina bayansa ya runtse idanunshi .."
motar bata tsaya a koina ba sai gaban katon get din Rita Lori hotel dake onipan , get din already a bud'e yake kamar Koda yaushe security's ne tam ciki da wajen hotel din saboda manya masu kudi da kusoshin gwanati dake zuwa da manya manyan yan fashi da makami , gurin fitowa daga ciki hotel din dabam haka zalika gurin shiga dabam , eku ya sanya hancin motarsa cikin Rita Lori, d'aya daga cikin security's din gurin ya mike da sauri ya zare karfen da sakale Wanda ke bawa mutun damar shiga, eku ya samu guri ya soma k'okarin parking adaidai lokacin da motar alqali danasu anas ya shigo
haraban hotel ne dake da bangare dabam dabam dan shakatawa sam tanweer bata fahimci Inda suke ba saboda ranta dake 'bace .
a natse jaguwa ya fito ya zagayo bangaren da take zaune ya bud' mata kofa "fito ko ".ya fad'a yana furzar da iska mai zafi daga bakinsa
ta yunkura a hankali ta fito tana jiran ta ganta a haraban gidansu kawai ta ganta a Rita Lori hotel a hankali ta dinga bin gurin da kallo qirjinta na dokawa da matsanacin karfi tana son gano Inda take bata Ankara ba taji ya riko tsintsiyar hannunta ya fara tafiya daita zuwa cikin had'ad'd'en club din dake ciki, banda sautin kidi da waka baka Jin sautin komai "Ina ne nan ka kawoni ? tayi masa tambayar muryarta a tsarke "gurin shakatawa yayi maganar a dake yana cigaba da tafiya daita yayinda har lokacin hannunta na cikin nashi jikinta na rawa taja ta tsaya qirjinta na wani irin bugu fiyye da kaida juyowa yayi ya tsaida idanunshi a kanta take ya fahimci damuwar data shiga adalilin ganinta a Inda suke "gida mukayi da Kai zaka Kai ni me yasa zaka kawoni nan ?shiru yayi kawai yana bin qaramin bakinta da kallo yana jin kmr ya rungumota jikinsa ya hau sotsan lips dinta ." ni gaskiya gida nake son zuwa ba nan ba ka Kai gidanmu tayi maganar kamar zatayi kuka dan tuni hawaye sun gama cika mata Ido kafin kace me hawaye sun shiga turereniyar zubowa har da shesheka hankalinsa ya tashi dan hk cikin tsarkewar murya yace "Kinga dan Allah ki kwantar da hankalinki bazan cutar dake ba Kuma bazan bar kowa ya cutar dake ba domin ba haka yasa na d'aukoki ba dan haka ki natsu ki kwantar da hankalinki ya dan yi shiru dan jin me zatace itama shiru tayi saboda jin maganrsa " kennan idan ta fahimci maganarsa shine d'an fashin daya d'aukota daga gaban iyayenta ? wani irin bugu gabanta ya sake yi da karfi kafin daga bisani qirjinta ya shiga dukan uku uku da numfashinta dake k'okarin tsayawa hankalinta yayi matukar tashi ta dinga maimaita kalmarsa ta karshe daya furta ."
a hankali ta shiga girgiza Kai "no no impossible bashi bane sam bai yi kama da irin wad'an nan mutane ba dukkanin alamun sun nuna shi din mutumin kirki ne ya dai taimaketa daga hannun yan fashi ne zuciyarta ta tsayu akan haka ,cikin natsuwa ya juya ya cigaba da tafiya cikin Isa da izza ya barta tsaye adaidai lokacin da alqali ya fito daga cikin motarsa wani yawu ta hadeye tana qoqarin daidaita numfashinta da natsuwarta ta biyo hanyar da ta ga yabi tana waige waige karaf idanunta ya sauka akan alqali da hannunsa yayi mata alamar ta tsaya amman dake a tsorace take cikin sauri ta shiga d'aga ka'fafunta kmr walkiya ya nemeta ya rasa Yana nan tsaye su anas suka fito daya bayan daya suka wuce ta gabansa kowanne ya kama gabansa kasancewar kowannensu akwai bangaren da yafi so ."
*******
Tsaye tanweer tayi aguri d'aya kamar wacce aka dasa tsabar tashin hankali Inda ta tsinci kanta a yau din nan , ta rungume hannuwanta duka aqirji har loakcin sauti ne ke tashi akoina acikin Rita Lori yayinda jaguwa tuni ya
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 10 Chapter of 62