Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fa ?xuciyarsu cike take da mugunta ni idan ma mutuwar ce gara ni na tafi, dan idan wani abu ya sameka gbdy babu wanda zai tsira dagamu har ahlinka "tô sai me ya gwada mana idan zai iya ."
anas ya girgiza kai dan shi bai taba jin wani abu zai faru dasu ba sai a wannann lokacin .”

jaguwa ya kira sunansa anas ka shiga ciki gurin matarka ka kwanta karka manta gidan gbdy a tsare yake da matakan tsaro tun daga get din gidan nan  har zuwa katangar gidan to me zai tsorata?
" Kai fa idan wani abu ya sameka yaya kake son muyi babu abinda zai sameni kaima babu abinda zai sameka kamr yadda kayi auren haka nima zanyi ,
kalleni kaga ,anas ya dago ya kallesa nan da wata biyu zanyi aure inshaallahu ."
"What ?
“Abinda kaji na fada haka ne ,Ai ansa bai san lokacin da murmushin farinciki ya subuce masa ba ya rungume sa ajikinsa yana shafa bayansa " kai amman ka faranta min rai "saboda kai ne anas amman ban so nayi aure  a yanzu ba ya fada yana zaresa ajikinsa yana cewa "sai dai safe ya juya ya fita anas ya kulle koina ya nufi dakin matarsa .
Koda jaguwa ya isa gida ya kwanta a gadonsa flat yana tunani maganar nabel bai yi zurfi cikin tunaninsa ba tunanin da yafi kowani tunani tasiri ya kawo masa ziyara daga nan bai san sanda bacci barawo ya sacesa ba .


*********
Washegari da yammaci ya isa asibitinta yayi parking ya kira layinta cikin kankanin lokaci ta fito sanye da doguwar riga zuciyarta cike da mamaki take takowa zuwa haraban hospital ta iske shi jikin motarsa tsaye fuskarsa a hade yayi mata alamar ta shiga mota tayi shiru tana kallonsa fuskarta dauke da alamr tambaya ,"shiga ina son magana dake "jiki a sanyaye  ta bude gaban mota ta shiga ta zauna zuciyarta na rawa dan bata san da me yazo mata ba allhairi ko akasin haka ya zagaya ya bud'e bangaren direba ya shiga ya zauna ya tada motar "ya naga kana kokarin tafiya dani ina zaka kai ni byn mgn kace zamuyi ?
Tayi mgnr a matukar tsorace .

“zanje na cinyeki ne bata sake yin mgn ba shima haka bai tsaya  akoina ba sai bakin maria beach byn yayi parking ya fito itama ta fito tana sauke numfashi dan sai yanzu hankalinta ya kwanata tana kallonsa ya jingina bayansa da mota itama tayi kamar yadda yayi bayan wasu mintuna ya juyo ya tsura mata idanunshi "Kinsan abinda yasa na kawoki nan gurin "?ban sani ba amman nasan ba dan saboda sumbata bane ,ke abinda ya fara zuwa zuciyarki kenan sumbata yayi taku daya biyu zuwa uku ya tsaya yana kallonta mace a rayuwarta sumbata , kywun jiki me kyau ,tsayu da kuma fadi qirji shi suke kira soyayya ,magana akan jiki tsayi ta wan bangare kenan gbdy a haka kake kallon qaunar da nake maka ?

Ya matso kusa daita sosai har suna iya jiyo bugun zuciyarsu da saukar numfashinsa "sam ba haka bane "to me kake nufi da lissafosu "?Ya rungume hannuwansa duka a faffadan qirjinsa yana kallonta itama cikin kwayar idanunsa take kallo "nasan zaki iya fadar abu bayan idona sannnan idan ina nan zaki iya fadar sa koma menene amman ni bazan taba canzawa ba naunayen ajiyar zuciya ta sauke taya akayi ka canza da sauri haka adnan ?”.

“nayi tsamanin kazo ka sake haukatani ne ."

“kiyi min shiru da wata magana shiru din tayi tana sauke numfashi." a wannnan zamanin mata suna daukar maza a wani abu da zarar sun samu wani abu daga gurinsu sai suyi murna da zarar kuma yayi masu abinda suke bukata sai suyi farinciki ,tsuke bakinta tayi sannan ta motsa lip's dinta sunayin haka ne ga wanda suke so ni ko galashinka na kalla farinciki nake sosai bare ka bani na gani shiru yayi yana cizan lip's dinsa na kasa yayinda idanunshi na kanta” idan wanda kike só aka wayi gari kinyita kiransa bai shiga ba ko kuma bai samu ya daga ba ballantana ma ya kiraki me ye abinda zai faru ?

"Bani da matsala komai daidai a soyayya cike da tashin hankali yace "me kike so agurina tanwer?ta kalli yatsun hannunta sannan ta dago ta kallesa idanunta cike da hawaye "ina son na kare gabadaya rayuwata da kai adnan kasancewa ta tare da kai zai sani farinciki damun rayuwarka da abubuwa dayawa sa kaina akafadarka ba wai saboda kuka ba soyayyarka ce tasa na kasance a halin da nake ciki yau gbdy muryarta ta sauya alamun kuka hakan yasa ta tsaida maganarta ta sunkuyar da kanta a lokacin da hawayen dake makale da idanunta suka samu nasarar zubowa tasa dan yatsan hannunta ta dauke tana sanyawa jikinta jarumta sannan ta cigaba da magana ."

"Kamar sauran mata nima ina son abubuwa dayawa ina son na cigaba da sonka adnan ,ina son a kowace rana na dinga kallon idanunka sannan a rana daya idan na rufe idanuwana na mutu a hannunka nayi mutuwa cikin salama shine abinda nake bukata ta karasa maganar tana dago idanunta dake tsiyayar ruwan hawaye,tsawon mintuna shabiyar suna tsaye babu wanda ya furta uffan hakan yasa ta sake maida kanta kasa sannan taji sautin muryarsa cikin wani irin yanayi mai gigitarwa "ina sonki surayya...."
Da wani irin sauri ta dago Kanta tana dubansa hawaye na turereniyar zubowa "ina sonki kuma akoda yaushe tun daga sanda na fara daura kwayar idanuna akanki alokacin da kika kusan bigeni amman karya nakewa zuciyata da kuma ke haka ne yasa banason na fada miki ."

Tunda ya soma magana jikinta da zuciyarta ke karkarwa at the same time tana sheshekan kuka maganarsa ta rikitata bata taba tsananin zataji wannan kalmar a bakinsa ba runtse idanunta tayi da mugun karfi tana ciza gefen lips dinta da karfi domin ta tabbarwa kanta gaske ne ko kuwa mafarki ne "zaki aureni surayya? "wani sabon gigita ya mamaye jikinta nan take jikinta ya kama rawa ya matso sosai kusa daita ya kai hannunsa ya dago habarta yana kallon cikin idanunta da suke arikice "ki bani amsa kina nan akan raayinki zaki auri gagarumin barawo kiyi rayuwa dashi "?Ajiyar zuciya ta sauke da karfi tare da cire hannunsa dake rike da habarta ta rungumeshi tsam tsam ajikinta tamkar zata rabashi gida biyu ya daura kanshi akanta yana jin soyayyarta me zafi kissing din kanta yayi sannan ya kai bakinsa kunnenta “ki aureni da sana’ata surayya .”
a hankali ta soma girgiza masa kanta tana kokarin zare jikinta tace "a'a bazan aureka da wannan sana’ar ba ta fad’a tana sheshekan kuka ta juya da sauri ta soma daga kafafunta......."


Har dana Monday 🤪


Mmm sudais



💗💗💗💗💗💗
KUSKUREN BAYA
     💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

PAID BOOK

WRITING BY
AYSHA .A BAGUDO


WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

Wannan  littafin na kudi ne  mai bukata karanta shi  ya tura 500 ta wannan  account number din  1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an tura sai a turawa wannan number+234 703 534 8686alert  domin tabbatar da an tura ko wadan nan number's din 09136918331 or 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi  sai a tura ta wannan number 09136918331 domin sauraran littafaina a tuntubi Channel dina ta Hausa bakwai.

🅿️41


……a matukar kidime ya biyota yana kiran sunanta “tanwer ina zakije ki barni ki tsaya mu qarasa maganarmu mana ? sai dai ina bata tsaya ba ta cigaba da tafiya cikin sauri tana kuka mai tsanani tunda ya furta mata kalmar yana sonta taji kamar an yaye mata dukkanin damuwarta akanshi ne”
“oh my goodness wai me ye haka ne ki tsaya mana ya fad’a yana cigaba da binta a baya “nace ki dakata tanwer ki bani amsar tambayata “?ya qarasa maganar yana qara sauri cikin zafin nama ya shan gabanta ya rike tsintsiyar hannunta cikin nashi dayan hannunsa kuma ya riko kugunta dashi .”
tayi sauri kawar da fuskarta gefe tana sheshekan kuka ya juyo daita gbdy suna kallon juna , cikin tsananin tashin hankali yake kallon kyakkyawar fuskarta zuciyarsa na sake narkewa akanta ,wani irin sonta ne ke ratsa tsantsar jikinsa yana yawo acikin jininsa ,ya matsota sosai sunyi mugun daf da juna wanda da zai qara taku daya zai iya masauki a jikinta .”

ya kai hannunsa gefen fuskarta yana shafawa a hankali ahankali yana cigaba da kallonta “bai ta’ba d’aukar idan ya furta mata kalmar yana sonta zai aureta zata nuna damuwarta bare ma taki amincewa ba “ why tanwer ina zaki tafi ki barni alhalin baki bani amsar tambayar dana yi miki ? bata bashi amsa ba ta cigaba da sheshekan kuka “Why’re you crying tanwer?” please ki daina kukan nan haka yana touching heart dina ya zaro hanky a aljihunsa yana goge mata hawayen dake gangarowa akan kuncinta yana cewa “I don’t won’t see your tears just tell me zaki aureni ?ya sake tambayarta abinda ke d’aga mata hankali da dagula mata lissafi cike da raunin zuciya ta girgiza masa kai alamun “a’a!


“daman karya kike ma zuciyata tanwer?.“Me yasa kika min karya ?“ wannan karya haka tanwer?“kenan karya kika fada min cewar kina sona zaki aureni ?a she karya kika min na cewar baki son kowa a duniya sai ni a she bani kike so ba .”? Yayi mata tamabayr cikin wani irin salo da bata ta’ba ji daga bakinsa ba hucin numfashinsa na dukan wuyanta wanda ya haddasawa tsigar jikinta mikewa sannan bugun zuciyarta da tausayinsa ya qaru .”
kafin kace me wasu daga cikin mutanen dake gurin domin shakatawa suka zagaye su suna dubansu bai damu da mutane dake tsaye suna kallonsu ba ya had’e fuskarsu guri d’aya ta yadda zasu iya shakar numfashi juna ,anyi sa’ar faruwa hakan domin kuwa nan take suka dinga exchanging din numfashi junansu ta lumshe idanunta tana cewa “Kaga ka sakar min jiki mutane na kallon mu fa “.

“baza’a saka ba kuma har abada wannan jikin nawa ne dake Karan kanki ,dan baki isa ba ,baki isa ki barni ba tanwer dole ki kar’beni a yadda nake tunda da halina kika ganni kika nace ,kika koyar dani yadda zan bayyana son da nake miki ,”alhamdulillah gashi na furta miki ina sonki idan hakan bai miki bane ki fad’a min yadda zanyi .”?

muryarta cike da in inna tace “ni… ni fa ba wai bana sonka bane,ba kuma karya nake maka ba ,dan so ina sonka har yanzu adnan, burina ka zamo uban ya’yana amman bazan ta’ba auranka da wannan sana’ar ba, idan kana son muyi aure lallai adnan ka rabu da wannan aiki , sannan ka tuba zuwa ga allah abinda kasamu acikin sana’ar ka kyautar dashi gabadaya sannan Kazo muyi maganar aure .”
Kamar mai rad’a yace “kinga nayi miki kama da irin nmjn da za’a bawa umarni yabi ? tanwer ni ba irin wad’an nan mazan da mace ke iya juyawa bane ,ki tsaya a yadda nake so shine zaman lafiyarmu da kwanciyar hankalinmu , ina sonki kuma zan aureki haka zalika ina son aikina kuma bazan iya rabuwa dashi ba ,kema kuma dole ki amince da abinda nazo dashi sannan ki so aikina “.yana gama fad’ar haka ya soma tafiya daita da kallo tabi bayansa tana d’aga kafafunta da kyar har suka qaraso inda motarsa yake idanunt dana mutane na kansu sosai suka burge mutane duk da basu san akan me suke jayayya ba .”

ya bud’e mata murfin bangaren da zata zauna jiki a sanyaye ta shiga ta zauna tana sauke naunayen ajiyar zuciya,ya maida murfin kofar motar ya rufe ya zagaya ya shiga bangaren direba ya zauna ya bawa motar wuta har suka hau babban titin jakonde babu wanda yayiwa dan’uwansa magana ya cire hannunsa daya akan stearing ya daura akan hannunta dake kife akan cinyarta batare daya kalli inda take zaune ba .”waigowa tayi ta tsura masa ido yana murza stearing da hannu d’aya yayinda dayan hannun ke fama shafa hannunt sanye ac na ratsa jikinsu da zuciyoyinsu .”halayensa bazai sa taki morewa kallonsa ba dan kallonsa ba karamin jefata cikin nishadi yake ba, tafiyar mintuna talatin ta kawosu asibitinta yayi parking batare daya kashe motar ba yana jiran da zarar ta fita yaja motarsa yayi gaba ,
ita kuwa zuciyarta da jikinta rawa suke tana jin tsoron ya juya mata baya ,a hankali ta dinga jin kamar ta amince masa kawai suyi aurensu a haka “a’a surayya karki soma wannan ganganci dama ce ta sameki ,kiyi iyakar kokarinki ya canza karki sake ki biyewa son zuciyarki ki auri dan fashi da makami “
wannan karfin gwiwar da wankakkiyar zuciyarta ta bata yasa taji zata iya komai ciki kuwa har da juya masa baya ta cigaba da rayuwarta babu shi murmushin jin dadi ya bayyana akan fuskarsa
ganin bata fita da sauri ba kamr yadda yayi tsammani suna gama qarasowa zata fice ta barshi dan haka tunaninsa ya bashi hakuri zata bashi .”

Bai Ankara ba yaga ta soma kokarin yunkurawa tare da kai hannunta jikin murfin mota ta bude ta fara fitar da kafafunta sannan gangar jikinta, ya bita da wani irin kallo yayinda ransa yayi matukar baci zuciyarsa ta soma tafarfasa kamar ya kama da wuta,
Amman dake shi din namiji gaske kuma dauriya da jajurcewa ajininsa suke bazaka ta’ba fahimtar hakan ba atattare dashi ba , abun takaici da bakinciki agareta bai wuce murmushi daya sakar mata byn ficewarta a motar ba gabadaya batare da wata damuwa akan fuskarsa ba ya daga mata hannu alamun” bye bye wanda hakn ya kusan tarwatsa zuciyarta amamn tayi kokarin ta danne damuwarta tayi itama ta daga masa hannunta ta juya ta fara tafiya a natse cikin sanyin jiki ,Shima jikinsa a sanyaye yaja motarsa .”


ta juyo a hankali taga motarsa har ta fice da gudu ta kai hannunta daidai saitin zuciyarta dake beating very fast “allah karka bar zuciyar adnan ta samu sukuni daga wannan lokacin daya furta yana sona da bakinsa ya allah karka bar zuciyrasa ta zauna lafiya ka sake jarabftarsa da matsanancin soyayyata har sai ya amince da tsarina , tayi hanzarin barin gurin ta isa office dinta ta soma hada kayayyakinta masu mahimmanci tana kiran layin direbanta cikin kankanin lokaci ya qaraso ta dauki hand bag dinta ta rataya akafadarta ta fito zuwa haraban hospital din ta shiga bayan mota ta zauna bata san yaakayi taji digar hawaye na gangaro mata a kuncinta dirba yaja suka dauki hanyar gida.”

Direba na gama parking ta fito jiki a sanyaye batare data rufe murfin motar ba ,da kyar take daga kafafunta tamkar wacce bata da laka ajikinta har ta sanya jikinta cikin hadadden parlour’n nasu ta bude baki da kyar tayi sallama, mumy dake zaune a falon ta amsa mata cike da kulawa sai dai kallo daya tayi mata ta fahimci tana cikin damuwa “sannu da gida mumy. “sannu da zuwa tanwer ya fama da jamaa ?
ta amsa sannan ta zauna kusa da mumy tana cewa “mumy yau dai adnan ya amince da zai aureni amman ya tabbatar min sai dai na auresa da aikinsa,ni kuma ko ba d’an alkawarin dana daukar miki ba mumy ba bazan iya rayuwa aure dashi da wannan sanar ba me zanyi mumy na raba zuciyata da soyayyarsa ?”wallahi mumy na gaji da wannan azababbiyar soyayyar ,nayi tunanin zuwa yanzu zai yi tunanin canza rayuwarsa amman sai ya nuna min lallai sai dai muyi aure a haka kuma dole na auresa da aikinsa ko ina só ko bana só ta karasa maganar tana zubar da hawaye .”


“Ya isa bana son wannan kukan mumy ta tsaida
ita daga kukan da take ba musu tabi umarnin mahaifiyarta “ni kaina mahaifiyarki ina jin zafi da ciwon irin son da kikewa yaron nan daga ni har masu qaunarki babu wanda zai so kiyi rayuwa da mutun irinsa domin gibi ne rayuwarki sai dai akwai wasu abubuwa da nayi nazarinsu cikin takaitacen lokaci akansa yasa kika ga ni kaina na amince daki auresa bugu da qari idan adnan ya shiryu adalilinki bakaramin jahadi kikayi ba.”
“ yanzu abu na farko da zakiyi shine “ta fada tana daga mata dan yatsanta daya .“ tunda ya furta miki yana sonki da bakinsa kuma zai aureki ki nuna masa lallai sai dai ya zabi daya aikinsa ko aurenki zanso adnan ya shiru kafin kuyi aure tanwer“.shiru tayi tana kallon mumy kafin ta cigaba da magana “abu na biyu idan bai zabi daya acikin ba ki nuna masa zaki iya cigaba da rayuwa babu shi .”
“Abu na biyu ki rage ko ki koyi boye wannan son
da kike masa ,ki nuna masa kawai idan bazai iya canzawa ba babu shi babu ke idan har lallai yana sonki zaki karya isa da qarfin izzar da ikon da yake ji dashi sannan ki hada da addua wannan itace kawai hanyar da zaki mallakesa ki mallaki zuciyarsa a wasu lokuta dayawa nuna wa nmj zazzafan só irin wanda kike masa babu abinda yake jawowa sai nadama kima godewa allah da ya jarabi adnan da soyayyarki da baki ga katin gayyayar aurensa da wata ba .”
“d’an haka ki kwantar da hankalinki karki sake damuwa akanshi ,ki saki jikinki kiyi lamuran gabanki idan yaga kin fita rayuwarsa gbdy shine zai dawo gareki yana rokonki mumy ta qarashe maganarta tana sakar mata murmushi “wannan shawara ce da umarni idan kika bi zaki ga yadda adnan zai haukace miki wallahi sai ya dawo yana baki tausayi sai ya dawo yana bin duk abinda kike so da duk wasu shawarwarinki ,kiyi kokarin danne soyayyarsa baya ga haka babu abinda zai sauya acikin zuciyarsa kullum kece zaki qare a wahala.”
“Ki saki ranki bari akawo miki abinci kici kinji mamana mumy ta fad’a tana shafa fuskarta.”

Cikin natsuwa da rashin kuzari yake tuqinsa cikin zuciyarsa kuma yana jin tanwer bazata iya barinsa ba ,duk abinda ta fada masa matsayin wasa ya daukesa dole zata dawo garesa dan ya rigada yasan yadda karfi da tasirin qaunar da take masa wannan karfin soyayyar da take masa zai taimaka masa ya sake tsaida hankalinta kanshi amman kuma haka nan yake ji tashin hankali daga kasan zuciyarsa tare da mummunar faduwa gaba.”
wayarsa ya lalubo ya kira layin anas kira daya ya dauka “anas tanwer zan aura kamar yadda kake so ,”dan allah abokina? ya gyada masa kai kamar yana kallonsa amman …“Kai gaskiya naji dadi nasan itama zataji dadi sosai kai allah na gode maka sam yaki bari jaguwa ya karashe masa bayani halin da suke ciki dole ya katse kiran ya cigaba da tuqi Jaguwa ya shiga gida babu kowa a babban falonsa dan haka kai tsaye ya nufi dakinsa ya fad’a akan makeken gadonsa tare da dafe goshinsa da yayi wani irin rikewa ,ya kusan minti shabiyar kwance yana tunani sannan ya yunkura ya tashi ya shiga bathroom ya shiga zubawa kansa ruwa sai da yaji kan ya dan rage masa ciwo sannan ya fito jallabiya kawai ya zira tare da wucewa masjid .”

“Ranar yau anas jinsa yake dabam ,jinsa yake kamar an sake sauya shi, wani irin farinciki ke rasashi wanda ga duk wanda yasanshi yasa fuskarsa ta sake wadatuwa da farinciki fiyye da yadda fuskarsa take ,
itama hally haka nan ta tsinci kanta da farinciki dan yanzu ta maida damuwarsa nata haka farincikinsa ,
taja Karan hancinsa da take mugun so tana sakar masa murmushi ya janyota gabadaya ta zube aikinsa ya rungumeta tsam ya kai bakinsa cikin kunnenta yana sakar mata numfashi “matata yau ina cikin farinciki .”Ta juyo gbdy ta fuskancesa “naga alama nima ina tayaka farinciki amman meye abinda yasakaka farinciki haka “? murmushi yayi mata yana sake rungumeta tsam yana bata labarin soyayyar yayanta da tanwer sai dai bai bayyana mata yadda soyayyar ta samo asali ba .Ta ware masa idanunta sosai tana cewa “to ya zaiyi da aunty haseera?yayi kissing din idanunta “zaki fara ko ?”me kuma nayi daga tambaya ?a duk sanda kika bude min wadan nan idanunki ina kwadaita dake my princess
bakiji yadda naji ajikina ba yanzu dana kalli cikinsu.” ya karashe maganar yana matseta ajikinsa har tana jin yadda jijiyarsa ke zungurinta .”

“Shikenan na daina amman fa akwai daru idan aunty haseera tasani ,tanwer tafita iya daru ai sai dai kawai idan taga damar barinta ko kuma ta duba dangantar dake tsakaninku “a ajiye wannan ammi fa tana matukar son yaya ya auri aunty hasera domin itace ta hada duk abinda ammi take so ga surukarta ya riko hannunta sosai cikin nashi yana murzawa cikin wani irin salo na shauki “fada min abinda ammi take so ga suruka? “tana son farar mace doguwa kyakkyawan mai shape ,me tarin Ilima addini dana boko ,me tsafta da iya girki uwa uba kula da miji ta karasa maganar tana rufe idanunta da tafukan hannuwanta duka alamun kunya .”
ya cire hannuwanta yana cewa “kalleni !.
Ta tsura masa narkakkun idanunta dake tada masa tsumin shaawarta “dan baki taba ganin tanwer bane ta hadu iya haduwa fiyye da tunaninki idan dan kyau ne da abubuwan da kika lissafa to auntynki hasera bazata tsaya a kusa daita ba iya girki ne kawai bani da tabbaci saboda ban ta’ba cin girkinta ba amman sauran abubuwan da kuka lissafa duk tana dashi “gsky zan so na ganta nice ma zan fara sheidawa
ammi “a’a ban yarda ba ki barshi yaje ya fad’a mata da bakinsa ya fada yana shafa saman dukiyar fulaninta dama kuma dibiarsa kenan muddin suna tare hannuwansa basa rabuwa da ta basu ,yana qaunarsu da hips dinta fiyye da komai ajikinta barin yanzu da lafiyayyen sex din da take samu ya qara fito dasu sosai .”

Bai barta iya haka ba yayita luguiguita mata jiki da salonsa gbdy ya kashe mata sansar jiki dan har ta fara tsiyaya, kusan mintuna talatin suna makale da juna taji ya zareta ajikinsa yana kokarin tashi ta rikosa cikin matsananciyar sha’awarsa tana cewa “ina kuma zaka ?zanje gurin yayanki bazan barsa yayi celebrate din farincikinsa shi kadai ba.”
ta karyar da wuya tana rausayar masa da kwayar idanunta “banason ka fita ka zauna tare dani .”
“Allah my princess ?ya fad’a yana kashe mata idonsa daya ta janyosa ya zubo jikinta ta kamo hannusa ta kai daidai pent dinta “taba kaji duk nayi ….”
Sai kuma tayi shiru taki qarasawa “duk kinyi me ?
Tayi shiru tana fidda numfashi sama sama “gbdy ya fahimci tana bukatarsa dan haka ya biye mata ya hade bakinsu guri daya yana tsotsan yana cigaba da shafa pent din daya jike da ruwan shaawa .”
Bai samu damar fita koina ba yana makale daita sai washegari karfe shadaya daidai a gidan jaguwa tayiwa Ana’s har cikin bedroom dinsa ya shiga yana kiran sunansa , yana zaune a gabansa system sai dai ba aiki yake ba illa idanu kawai daya zuba wa computer ,ya dago ya kallesa ya dauke kanshi yana furzar da iska dan ya dauka tun jiya daya sheida masa zai zo yaji me ake ciki amman ya wani sharesa anas yayi murmushi ya zauna kusa dashi yana mika masa hannu domin su gaisa shima hannu ya mika masa suka gaisa .”

“Abokina ya ake ciki ne? zan so naga idanun tanwer , yanzu yaushe zaa tura gidansu? ”ya ake ciki yaushe zaa tura gidansu sai yanzu kaza min wannan tmbyr ?
“tun jiya na kiraka kama tsaya kaji me ake ciki kaki bare ma kazo kaga a wani hali nake ciki ya fada a dan zafafe yana furzar numfashi “yi hakuri abokina wallahi tun jiya naso nazo “to me ya hanaka zuwan ?
“Na

Please Login or Register in order to submit comment