Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
bayan na cika zuciyata dafatan zaku zamewa juna alkhairi kuma idan ina da hakki akanka abinda na zabarmaka kenan amma idan kaki sai inSaka maka ido shikenan alhji ALLAH ya tabbatar mana da mafi alkhairi badan ransa yaso ba.. awashegarin ranar ne kiran alhji ya risketa hankalinta kwance dan a tunaninta zaimata nasi hane kamar yanda yasa ba kila kuma ta bankwana.amma bayansun gaisa sai yana ta tattalinta tare da kutsamata maganar yusha u cikin da bara irin tasa ta manya. Abba ya ce mata rumaisau yushau ne yazo mana da wata magana yanaso ya maye gurbin auwal.ayadda ya cemin ya jima yanasanki ganin kinkarbi auwal yasa ya hakura.nima kuma dama inada muradin hakan kimanta da wata ibtila i dakika sami kanki aciki. rumaisau kizama mai godiya ga ubangiji.ki amince ayi auran nan kamar yadda aka sanya da mari gayi.idan rumaisau karkaf abushe take kallon alhji to mizataima kuka ko tashin hankali.duk wata damuwa ko abinsanya kuka dazata ci karo dashi a duniyarta mutuwar auwal ya isa akira shi matakin kar she.idan kuwa wannan bakincikin baikasheta ba yakamata kowani tashin hankali ya zamar mata gada ta ce masa alhji badan ka bayar da goyo n bayanka a maganar nan ba alhji dana nemi hanzari.ya ce ina jinki ruma ta ce masa alhji da baka goyi bayansa ba harshensa ne yaimazuciyar sa karya takowani bangare nasan yaya yushau baida tsarin auran irina.baikamata mutum lafiyayye kamar sa yakare a auran nakasasshiya irina ba nanda ruma ta bi duk wata hanya tagama aibanta abinda aka gani ake son hada auranta da yushau.. alhji ya ce mata duk wata lalurarki ta sikila idan har bata hanaki auran auwal to bazata hanaki auran yushau ba.yadade yanai mata nuni da abubuwa dasuka sanya yakesan ayi auranta da yushau yanzu kam Ruma tana tunanin KARA,KAWAICI, SADAUKARWA, yakamatne tsakaninta d.a alhji da hajiya wadanda suke karramata daidai da mahaifanta..ko sudasu zata iya dogara ta dubi yushau matsayin mijin aure Shirye shiryen biki ya kankama innar ruma ta iso ana sauran kwana biyu amma kafinhakan tunda alhji yajizatazo ya tura su yushau rogo saboda bayaso umman ruma ta fahimcin rashin jituwar dake tsakaninsuhaka yushau yayarda sukatafi badan yaso ba ahanyarsu ta tafiya rogo bawanda yaimagana acikinsu.saidai ruma ta karbi sakonninda take ta suka sata hawaye idan ta shiga motar auwal sai ya zuge glassai tsab ya rufe, yakuma kashe A.C sannan a motar sa baya rabo da CAR HEATER saboda ita,ga tuki cikin natsuwa,ko da a hanyar da bata da kyau ne saboda kar tajigata,bugu da kari yakan umarcetatada fito da hijab a jakarta tasa idan da mayafi ta shiga motar.... . Dan Aunty. GORAN DUMA (P 24) . . duk wadannan gatancin sun kufcemata ko kallo bata ishi yushau ba bare ayi maganar tattali danhaka taiyi ma kanta gatadakanta ta rufe gilasan.shiko sai zuba gudu yake a hanya ya cika mata kune da wakar ala wanda idan ta rantse saurare kawai yake amma baya duba maanar wakar. sunkusa karaye aka bugo mata waya wannam karan ya rage karar wakar ta daga wayar ta sada zumuncine da gaisuwa daga TAHIR wani member ne a kungiyar su ta masu sickle cell. yaimata gaisuwar auwal tare da jajantawa yushau ya ce mata wanene kukai waya da shi? tajima kafin ta ce sunansa TAHIR TAFIDA MUHAMMAD tana rufe baki ya watso mata wata tambayar yakuke dashi? memberne a kungiyarmu ta sickle cell acan muka san juna muke zumunci. ammadai kina da kudurin idan munyi aure zaki bar kungiyar? dayake na kwana sanin aurena ba zai rabani da sikila ba,sai ban ta ba tunanin zan bar kungiyar ba. amma nasan kin san duk lalacewa kinsan cewa mijinki yana da ikon hanaki duk wata muamala da yake da shakkunta ko? duk yadda kike jin wayewa nasan kinsan mijinki yana da karfi akanki. ruma tajima kwarai maganganunsa nayi mata ihu aka.saidai tayi jarumtaR boye kaico da hawaye,saboda haka ta shirya magana ma sai ta kori rauni a zuciyarta wata sha afa da mukai kenan nida kai da iyayen mu a kaida duk wanda zai auri mai sickle cel ya kamata a zauna a tattauna dashi bayan gwaji yaji matsalolinsu yaga abin juriya akai in zai jure din, yushau ya ce dan na ce ki bar kungiya idan kinyi aure? ko ruhin ciwon naki makale yake da kungiyar da idan an hanaki ya tsinke Ranki duk dai taji zafin maganar amma a sanyaye ta girgiza kai shikuma ya sami damar dorawa cikin zafin rai kiyi kokari ki fahimceni karki dinga sauya min magana kina hada min ita da ciwo.yanzu dai naji kina waya da wani wanda ba muharraminki bane... a raunane ta amsa da cewa ban dauki fadan hakan laifi bane sannan ban shirya karya ta shi ga tsakanina dakai ba Idan hakane sai ki yanke hulda da abinda kikasan banaso,dankar kifada min gaskiya inki fahimtarki kiji ciwo.inkuma karyar kike yimin ALLAH ne shaidata,kamar yanzu dakika cemin dan kungiyarkune ai bansan gaibuba,in bayan dangatakarku ta kungiyancin akwai wata dangatakar yaya zansani kaitsaye ta amsa tana duban titi. kobaka sanidinba rashin sanin ba zai cutar dakai ba,ko da cutarwar ta fargaba ce tunda kasan ciwon sikila ba kanjamau bane da ake bukatar mai shi ya auri dan uwansa mai shi shi sikila so ake ya nemo lafiyayye ya aura dan dorewar haihuwar yayansu masu lafiya.saboda haka karkadamu kanka da dangantakata da wani sickler ko kuma ka saka mana zargin dangantakar soyayya afusa ce ya juyo ya dubeta idan na fahimceki umarni kike minko?kawai saitasami kanta da tuntsi rewa da dariya tana kare masa kallo kaitsaye ta ce. "Haba dai, yaushe zan maka umarni? Na ga dai kamar bai kamata mu dore a gizago da biyayyar babu ji babu gani ba. Ya wajaba mu tattauna matsalar ciwona da kai a yanzu kafin nan gaba ka ce an baka a rufe". Karkacewar da bakinta ya yi wajen dariyar da take, yasa tausayinta ya danne takaicin dariya da ma'anar maganar da ta yi masa. Ya kawar da kai ya bi titi da kallo, sannan murya 'kasa-'asa ya ce. "Tunda ba fasa auren za a yi ba idan na ji abin da bai yi min ba cikin abin da za mu tattauna din ai barin tattaunawar ya fi..." Ta tari numfashinsa da fadin. "Me yasa za a kasa fasawa in kuma ka ga ba ka muradi? Duk sickler ya san a saka aurensa a fasa ba wani ba'kon abu ba ne, saboda haka babu abin da zai fari dan ka fasa". Ya jima kwarai yana sa'ka maganar da zata fito bakinsa kafin ya barta ta fito. "Da zaki ajiye bokonki waje guda, in sami kawwamammen matsayi a wajenki irin wanda nagartattun iyayenmu mata ke ba wa mzajensu, to ina jin zan zama mai hakuri da tuntuninki ga Auwal. Dan haka ba kya bukatar 6ata lokacinki wajen yi min umarnin in aure ki ko in fasa tare da sanin fasawar tawa ba zata rage ki ba, ko ta amfane ki, tunda wani za ki aure ba Auwalu ba". Ta yi shiru kawai tana juyawa maganganunsa, kaasa fahimtarsu sosai ya sa martaninta ya bi ruwa. Shi da ya damu da jin ta bakinta sai ya tuna mata yana mai kallonta. "Ba zaki ce komai ba?" A sanyaye ta amsa masa. "Ga6o6in maganganun naka ne da yawa, yadda kowace na karya za tashi guda in kuma jata ta yi tsawo, saboda haka kar ka zaci muhimmin abin da kake son jin bakina a kansa." Kai tsaye ya amsa mata. "Kar ki dauki kanki wata tsiyar saboda kin yi zurfin karatu, ki zauna da ni zaman bauta kwatankwacin yadda kika ga iyayenmu na yi. In kika yi hakan shine kika ba ni karramammen matsayi wanda zai wanke min dukkan tsatsa a raina na auren mai zurfin ilimi da ban ta6a shiryawa rayuwata ba". Ta dinga jan numfashi kafin ta amsa masa cikin dakewa. "Ina jin da taka karramawar zaka sai wancan matsayin da kake ambatawa, in kuma ka cire zacezace da zarge-zarge ka kuma cire garaje cikin mallakar matsayin da 'karanta rainuw da kuma sau'kaka fahimta, wannan shi ne". Ya yi dif kamar ruwa ya cinye shi da harshensa ya yi niyyar fada mata abin da zuciyarsa ta fahimta a maganarsa. To abin da zai gaya mata shi ne bokon da yake gudu ta yi masa. Bashi da za6i, dole ya yi shiru ya kyale ta, ai a kan sharafinta take tunda tana da Alhaji me tsaya mata. Har suka shiga cikin garin Rogo babu wanda ya tanka wani, suka sauka a gidan kakaninnsu, duk da tuni kakannin sun 'kar, sai 'ya'ya da jikoki. Haka kowa ya dinga sanya musu albarka, Yusha'u na shan albarkar yarda da ya yi ya auri Rumaisa'u da nakasarta, Rumasa'u na shan albarkar ajiye jimamin rasuwar Auwal da ta yi a gefe ta yarda ta kar6i dan uwanta. Sun wuni a nan gidan, sai dab da la'asar suka nufi gidan Goggo. A gidanta Yusha'u ya yi mafi rinjayen zamansa saboda sha'kuwarsa da 'kaunar da 'yan uwa da Allah Ya zuba mata. 'ya'yan wa da 'kani da mahaifinsu. Son danginta neyasa duk sa'adda ta kwashi Auwal suka je Rogo, to a gidan Goggo zata sauke shi, su yi hira su yi barkanci tare da Goggo. Wannan dalilin yasa suna shiga gidan yanzu gaba daya jikinta ya yi la'asar, musamman da Goggo ta baza musu tabarma wajen da ta saba shimfida musu in ta zo da Auwal, sai ta kasa zaman kan tabarma ta koma kan 'karamar kujera ta zauna tana kokarin hadiye kwallarta. A haka suka gaisa duk tana rikice, a karshe dauriyarta ta kai 'karshe lokacin da wasu rukunin zabbi suka gifta, ta tuno lokacin da suka zo da Auwal an kyankyaso jariran zabbi fiye da ashirin reras abin sha'awa, ya daga kai ya dubeta ya ce. "Don Allah zabbin nan ba su burge ki ba Rumaisa'u?" Ta bi zabbin da kallo tana murmushi, sannan ta ce...... . Dan Aunty. GORAN DUMA (P 25) . . "Ba na jin sun burge nikamar yadda suka burgke ka, tun dazu fa na ankara kana ta faman satar kallonsu..." Ya tare ta cikin dariya yana kallon Gaggo. "Satar kallo kuma? In zan kalli zabbi sai na saci kallonsu kamar ke zan kalla a gaban Goggo?" Shi ma Goggon ta tare shi da fadin. "Dan ma ita din ba satar kallon nata kake a gaban nawa ba, 'karfi da yaji kun mayar da ni kakarku". Suka tuntsire da dariya su duka. Auwal ya ce. "Kar ki sami damuwa Goggo, ko barewa a daji da danta ta ke wasa. Ina son zabbin ya ya zaki yi da ni?" Goggo ta yi murmushi ta ce masa. "Ka zo garin nan ka siya a yi maka kiwo. Ya kuma bin zabbin da kallo, sannan ya juyo ya dubi Rumaisa'u. "Har yanzu ba su fara burge ki ba Rumasa'u? Anya kuwa zabbin nan ni ma sun burge ni? Duk abin da ya burge ni fa ya kamata ya burge ki". Ta bi zabbin da kallo suka zuba musu ido tare, sai can ta juyo ta dube shi cikin murmushi ta ce. "Wallahi sun fara burge ni". Da tausasshiyar murya ya ce mata. "Haba ko mu fa". Sai suka bar Goggo da sallalami suna yi mata dariya. Yanzu da Rumaisa'u ta 'kurawa Zabbin ido cikin kwalla nan take ita ma Goggo ta tuno tunowar da ita ma ta tilasta mata kwallar, sai suka bar Yusha'u galala yana kallonsu da kwanon ruwa a hannu. A karshe kukan zucin Rumaisa'u ya ki 6oyuwa sai da ya ta fashe da kukan bayan ta sunkuya kamar zata shid'e. Da sauri Goggo ta 'karaso wajenta ita ma nata kukan ya 'ki 6oyuwa ta ru'kota duk suka rafke da kuka cikin kuka Goggo ta ke cewa. "Manta Auwalu a zuci wani abu ne da ba zai ta6a yiwuwa ba, dan cikin rayuwarsa ya guji abin tir, babu yadda zamu yi haka zamu ci gaba da daurewa muna yi masa gatan da ya fi bu'kata yanzu, wato addu'a". Ga mamakin Yusha'u sai ya ji wani matsanancin kishi ya turnu'ke masa 'kirji, ya sababba masa fusatar da ya ajiye ruwa ya tashi a fusace ya fice daga gidan. Hakan ya basu dama cin karensu babu babbaka, suka ci kukansu, Rumaisa'u na maimaita. "Kin ga yadda Allah Ya yi da ni ko Goggo, na rantse da mafarki ne abin da ke faruwa da ni idan na farka bacci ba zan 'kara bacci har abada". Sun jima cikin wannan damuwar, da koke-koken har sai da mutam gidan suka fara zagayowa kewayen Goggo dan gaishe da ba'ki, Goggo ta ari juriya ta hau yiwa Rumaisa'u ga yiwa Auwal addu'a da sadaka su ne gatan da zai iya samu daga gare ki a halin yanzu." Rumaisa'u ta yi namijin 'kokarin gyada kai da sauri cikin gintse kuka lokaci daya zuciyarta na halarto da aikatawa Auwal dukkan Wani gata da kwanjinta zai iya in dai zai taimaka wajen sada shi da rahamar Ubangiji amma ta ji a ranta mantawa da Auwal ne har abada ba zata iya ba. Ta tuna da auwal dake firar dasuke ya ta hallakane akan matsalar ruwa inda tatuna wani zuwansu rogo yake cemata abu nafarko dazansaka agaba bayan hidimar bikin mu ita ce insamu yan kudi inzo garinnan in gina rijiya ko bayan raina sai ladar ya amfaneni farad daya tafara tunanin hanyar dazata bi ta cikamasa burinsa duk zuwan dazasui da auwal indai akwai lokaci sai sunje kan dutse.saboda haka ta shirya tama gwoggo sallamar fita zuwa kan dutse duk da tasan zuwannata sai gadar mata da kunan zuciya ahaka takasance har rana tagama yinja tafara sauka a hankali tayi kuka hartakasa gajiya duk wanda yaganta a wannan halin sai ya tausayamata.bata hango yushau na zuwa ba motsinsa kawai taji tajuyo taga fuskar sa ba annuri wai anan zaki kwanane? aranta ta ce abune mai matukar wuya ta taRe da giRman ciwo a ce tarasa mai tattali da fara a kamar gonar auduga ace ta bige da auran mai kyaliya da gizago kamar zaki. ta tashe ta bi bayansa tana mai share hawayenta..har suka iso kano tara saura babu wanda ya tanka acikinsu Suna faka mota tafara kicikicin bude motar amma a kulle danhaka saitai shuru dan bazata iya dubansa ba balle ta nemi dalilin yin hakan.yajima yana huci san nan ya sauke cikin gyaran murya Sannan ya ce bawai gudun laifinake ba illa gudun daukaR bakuna,in ma laifine yakamata a tuhumeni da wanda nake da ruwa da tsakinsa,ba lallai agida su san haka ba,kiyi kokarin gyara wannan hawayen wofin dakike zubdawa dan karki janyo a dora min alhakinsa bata tankamasa ba tagoge hawayenta tsab ta rabka tagumi.ki kwance jaka ki shafa hoda ta cemasa dazan fito ma ban shafa hoda ba ta muskuta cikin tsananin kuncin zuciya ta cemasa shafa hoda tana nufin farinciki ko jin zakin rayuwa,nikuwa duk nayi bankwana dasu.a fusa ce ya fice daga motar yana cewa au na shafa cewa a cikin takaba kike wanda baikamata na manta hakanba itama ta fito ta wuce dan tuna cewa yaufa mominta zatazo tana isa ta ga innarta ga kuma balaraba yayarta harda kari ma wato da innar auwal. Maimakon ruma taiwajen innarta saita nufi innar auwal tafada cinyarta tafara rera wani irin kuka mai tsuma zuciya.inna data gama wani kukan sai ga zuwan ruma.inna nanata kukan ruma na nata kukan mai keta zuciya ke akaima rasuwa ruma kekikai rashin auwal.Allah ya baki hakuri da dangana Allah yajikansa kekuma ya baki wanda ya fishi.wadan nan kalaman nata ne suka kara kular da yushau.da ya shigo yanzu,yakada kai yai waje baitsaya.ba balle ya gaida bakin a can falon alhji wani takai cin yatararmmahaifin auwaldin yatarar tare da alhji suna hira.hirar kuma ta auwal da ruma game da yan matsalalolinda suka taso gab da auren.akar she hirar ya rufe da cewa dake shi ALLAH babu ruwansa sai ya saukar da ayar sa gareni.ya karbi auwal mai lfyar alhalin shikadai na haifa.yayanke min hanzarin 'ya'yan dana tara burika akansu.nake kuma tafaman hura hanci akansu.alhali bani da sani akan Samuwar su ko rashin samuwar su. hakadai har yushau yadaure yagaida su tare da alhji.danhaka alhji yanuna yushau ga mahaifin auwal tare da cewa ga wanda ze maye gurbin auwal. ya ce masha ALLAH karike ta da kyau yarinyar tsakani da ALLAH yaimasa nasiha kwarai.... . Daga uhum sai uhum baki na dai har yau a kulle yake.. Dan AuntyGORAN DUMA (P 26) . . RUMAISAU DA MOMINTA CIKIN DARE. har sha biyun dare ruma,hafsat tare da balaraba da momin ruma da barci ya ciyo idan hafsat,kuma taga alamun nuna tausayinta ga ruma kuma kamar tanasan kebewa da yartata.saboda haka taimusu sallama ko minti biyar bataida fita ba momi tadubi Ruma da kyau ta ce.inafata ba matsa ma kanki da zuciyarki kikai ba kika aminta da auran yushau.? ruma tajinjina kai tare da murmushin yake ta ce bazan iya zabar mijiba momi dantagama zancenta yaya yushau zai shi go rayuwartane dan rashin zabina bai zama karewar numfashina ba baikuma kankare aure daga cikin ayyukan da aka rubuto a allon abinda zanyi a duniya ba,rashin auwal ne matsala a rayuwata ba auran waninsaba.momi ta ce to ALLAH yajikansa yasa aljanna ce makomar sa.kekuma ki rage yawan damuwa kinsan yanayin ciwonki.balarab kawai kallonsu take yi saboda tsabar tausayi takasa cewa komai.ruma ta shaRe hawayenta ta ce ina tilastawa kaina musamman danganin bakincikin rashin auwal ya isa ya karar da nawa numfashin.amma gani a raye ALLAH Ne kadai yasan abinda yake boye yaSa ya barni araye bataRe da auwal ba saidai ina neman wata alfarma wadda nake ganin zata taimaka min narage tuna auwal cikin kunan zuciya,illah in na tuno shi nai farinciki umma da balara ba cikin doki tare da hada baki wa ce alfarma?momi kiyimim alfarma na sayar dawasu hannun jarinda kika saimin da kudin motar da alhji ya hanaki siyamin.kikuma banidama na sayar da sarkokina ahadamine kudin da dangin auwal suka barmin ko a siyar dawasu da wasu daga cikin kayan lefan... Cikin kaguwa momi ta ce aime da kudin? Ruma ta shaida musu yadda sukai da auwal dakuma bukatar cikamasa burinsa.asanyaye balaraba ta ce amma dai zaki iya dorewa dayimasa addua samun rahamar ubangiji ruma ba saikin salwantar da dukiya mai yawa ba..momi tai saurin dakatar da ita ta ce a a balaraba ba salwantar wa ba ce,ya kamata tunanindatai auwal yafi karfin komai agurinta,ba komaikarki samu damuwa za ayi zanfadawa dadynki idan kudin basu cika bama zancikamiki. cike da farinciki ruma t.ai godiya momi taji farinciki ya cikata dan tada de bataga farincikin ruma kamar na yanzu ba tun kafin rasuwar auwal sunata hira har suka fado kan yush.u anan ne ruma tafadi wata alfarma momin su alhji sundauki yaya yushau dan gida a ciwona suna ganin kamar babu wani bukatar a tattauna matsalar ciwona dashi dan haka ba a tattauna dinba.bana son a share wannan batun kirjin momi yaf.ara lugude dan haka tai zuru tana kallon ruma ta tabbatarw kanta akwai dalilindayasa ruma wannan maganar kasancewarta mace mai zurfinciki da karanta korafi.ta ce fadamin gaskiya saboda ALLAH mekika hanga kikawo wannan maganar? A sanyaye ruma ta shaida ma ummanta yadda sukai da yushau bayanta amsa wayar tahir tafida muhammad takare da cewa bazan iya dorar da yadda yaya yushau ke karbar alamurana ba,amma ko ma menene baya karbar .alamura da sassauka fahimta yazuwa yanzu momi ta rafka tagumi sannan damuwa tattare da fuskarta momi ta ce kunya da nauyin alhjh. nake ji ruma da badan haka ba bazan bawa yushau aurenki ba cike da tawakkali ta dubeta badam nadaga miki hankali kodan in sanyawa ranki rashin natsuwa cikin aurena da yaya yushau ba.nandai suka ci gaba da tattaunawa daga karshe ruma ta ce ki kyau tata zato a aurena da yaya yushau,.. washegarin ranar alhamis kenan ya shigo gaida umman ruma..nan ya taddasu harda ummansa haryatashi zaifita umman ruma.ta ce masa idan babu damuwa kadawo kamar karfe sha biyu don ALLAH inason kakaini yankaba wajen aunty fati . Yusha'u ya hadiyi wani irin yawu wanda ya taimaka masa hadiye 'kuntata masa ran da yake jin an yi, ya dubi agogo ya ce. "Babu damuwa Momi, zan yi 'kokari in dawo din duk da akwai tarin ayyuka a gabana kasancewar jiya ban sami sararin zuwa kasuwar ba, amma dai komai runtsi zan yi 'kokarin dawowa zuwa azahar... Ko kuma na yiwa direban Alhaji maganar ya zo ya kai ki...?" Ta yi saurin tare shi da girgiza kai. "Kai nake so ka kai ni..." Hajiya ma ta yo kansa ta fada. "To wai umar me kake a kasuwar me shegen nauyi haka?" Nan da nan ya karya murya ya ce. "Babu matsala zan dawo, ku shirya zuwa sha biyun". Hajiya ta juya kai, Momi kuma ta yi saurin cewa. "To Allah Ya dawo da kai lafiya na gode". Ya amsa, "Amin." Sannan ya fice ransa na yi masa wani irin 'kuna, takurar da yake fuskanta daga mahaifansa akan wannan auren bai san dalilinta ba. Sai ka ce shi ya dau ran Auwal? Dole kafin sha biyun ta cika ma ya dawo gidan ya dauki Momi, kasancewarsa mutum mai saurin fahimtar abin da mutane ke yi, ko shirin yi yasa shi zargin akwai abin da Momi ke nufi da ya kai ta 'Yankaba tunda ya ga ita kadai ta fito. Saboda haka da suka dauki hanya bai dauki furucinta a ba-zato ba lokacin da Suna tafiya daga cikin harabar gidan t. a cemasa yushau waikuwa kunje sickle cell counselling centre kaida ruma? yushau mutum ne da bai iya karya ba danhaka kaitsaye ya ce a.a bamuje ba,jiyannan dai ruma taimin magana.nikuma inagai idandai zuwa neman shawaran bazai sauya komai na yuwuwar auren mu ko rashin yuwuwar hakanba.inaganin babu bukatar batawakai lokaci momi ta ce masa neman shawara zai iya rushe aurenku.amma idan kunso..yushau yakurawa titi fuskar sa ba ya bo ba fallassa ya ce OK. hakan yasa takauda kai ta ci gaba da bayanani tundaga matakin farko har iya idan take ganin zai fahimci komai.tadade tana masa bayani daga kar she tadaka ko zaice wani abu kafin ta dora da.... Gwajin ba ya daukar wani dogon lokaci, za a dauki jininka ne a sirijni sai shigar cikin na'ura ta musamman domin wannan aikin. Gwajin zazzabin maleriya ma ya fi gwajin sikila jimawa. Sannan komawa asibitin ko sickle cell couseling center ga me shirin auren sickler a karo na biyu, shi ma wani gingimen muhimmi ne cikin dukkan matsayin da gwaji ya nuna mutum, AS ne ko AA, in AS ne zai je neman shawara tudu biyu ne, wato matarsa da kuma 'ya'yansa ko 'ya'yanta da zata haifa ko zai haifa. Cikin shawarwarin likitoci nunawa abokin zama yadda ciwon sickle cell yake kamar yadda na fara yi maka bayani a baya alamomin tashin ciwon, kulawar da ya kamara ciwon ya samu a gida idan ya tashi da kuma abubuwan da ya kamata a kiyaye dan kar ciwon ya tashi, da kuma abin da za a yi a gida in ciwon ya suman a garzaya asibiti, juriyar zuwa asibiti duk wata, sannan da tanadin kudi saboda ciwonsu, ko mutum AA ne ya kamata ya kwana da wannan Sani..... . Dan Aunty. GORAN DUMA (P 27) . . . In kuwa AS ne zai 'kara da tanadin kudi dan hidimar ciwon sauran sickler duk da zai haifa, tunda ciwon sickler ba ciwo ne da ake warkewa ba, yadda Ubangiji ya halicci mutum ke nan haka Ya so da ganinsa ba dan yana 'kinsa ba, illa iyaka dai ya kamata mace ko miji su sani ba mutum daya ke gadar da sickle cell ba, ma'ana ba dan mace sickler ba ce kawai ta ke haihuwar sickler ko ba dan miji sickler ba ne aka haifar masa sickler ba, a'a duk su biyun mata da miji ke karo-karo su haifi sickler..." Momi ta dan dakata ko Yusha'u zai ce wani abu kafin ta dora da zayyana masa yadda sicklers ke jin ciwo a jikinsu da kuma matakan da ake bi wajen taimakon gaggawa, ciwon ya sauka amma sai jikinta ya yi sanyi, domin ko kadan fuskar Yusha'u ba ta sauya da tausayi ko mamaki ba, kusan ma kamar a gundure ya ce. "Allah Ya sawa'ke, kuma maganar gwaji ma ai ta wuce kamar yadda na fada, in dai zuwa gwajin ba zai tankwa6e Alhaji hana shi daura auren ba... Ni ban ma dauki ciwon Rumaisa'u wata martsala a cikin aurena da ita ba..." Momi ta jima tana kallon tagar mota cike da matukar takaici, sannan ta daure ta ce. "Yusha'u ba ka son auren nan, Alhaji ya matsa maka ko?" Ya yi girgiza kai cikin murmushin ya'ke ya ce. "Ni ba matsa min ya yi ba wallahi, bamban muka sha da ku kawai, abin da kuke kallon shi ne matsala ni a gurina ba shi ne matsalar ba". Har yanzu Momi sha'ke ta ke da takaici, sai dai wayewarta ta hadidiye takaicin, ta nisa ttace. "Yusha'u me yasa ba ka yi tunanin mun fi ka gaskiya ba tunda mun rinjaye ka". Ya jima cikin shiru kafin ya tanka. "Momi ai duk ba wasu abubuwa ne masu zafi da za yi ta tashin hankalu a kansu ba...." Fuskar Momi cike da damuwa ta girgiza kai ta tareshi. "Don Allah Yusha'u me yasa ba ka bijirewa auren Rumasa'u ba tunda akwai matsala a cikinsa abin da ba ka fahimta ba shi ne, kai ba ka kallon ciwon Rumasa'u matsala, ni kuma a duniyar nan ba ni da matsalar da ta fi shi girma, ko tattalin ciwon Rumasa'u nake, to na tabbatar ina yi masa tattalin da yake wa rayuwarta amfani dan ina kokarin kore dukkan abin da zai motsa mata ciwo saboda ina jin ciwon cikin matsalolin da ke daga hankalina. To kai ba ka dauki ciwon matsala ba ta ya ya zaka iya kare shi? Abin da kake dauka shine matsala wata'kila ni da Rumasa'u mu 'ki kula da shi, dole ne wadannan bambance-bamncen fahimtar su gadar mana da matsaloli a gaba akan wannan Yusha'u na so ace ka 'ki auren nan... Ina da juriya akan komai amma Allah Ya sani ba ni da ita akan Rumaisa'u, ina fada maka gaskiya ne dan ba zan iya fitowa in hana ka aurenta ta dalilin bambancin al'kibla ba". Nan da nan Yusha'u ya gane kato6arar da ya yi, wadda ya ke tsoron zuwanta kunnen Alhaji, dan haka ya yi sauri ya gyara muryarsa da ladabinsa. "Haba Momi ba ki fahimce ni ba ne, ko Rumasa'u ba ta aure ni ba, ai ni mai zage kwanji in kare mata abin cuta ne, balle ni in zame mata cutar, don Allah ki kwantar da hankalinki ki bi mu da addu'a... Ni fa babu wanda ya matsa min aurenta". Momi ta yi shiru kawai da alama zuciyarta ta fara sanyi, sai can jimawa ta ce. "To maganar zuwa asibiti?" Tana direwa ya amsa cikin kwantar da kai da murmushi. "A kyale maganar gwajin kawai, ko ya ya zata haifar min 'ya'ya ina son su haka zan kuma tanade su". Momi ta dan juyar da fuska ta ce. "Ko 'ya'ya zaku haifa dai ai na fada maka mutum daya ba ya haihuwar sickler". Cikin irin karya wuyan nan na to da hausawa suka ce ba ta karya wuya ya ce. "Ko 'ya'ya zamu haifa Momi, ku yi mana addu'ar Allah Ya ba mu ikon kula da su". Yanzu ta fara saukowa sosai, ta ce masa. "Amin. Amma tilas ne ka je ga mashawartan sickler dan jin irin dawairniyar dake gabanka da kuma abin da zaka yi hakuri a kai. Adddu'a ma ibada ce, amma akwai ayyuka tu'kuru kamar yadda aka

Chapter 9 of 21