Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Afuwa tun Kafin Katuna Min Laifin Yai Murmushi Ainazaci Ninai Laifin Ake Hukuntani Da Boyemin Abinda Yakamata Nasani Tashi Ga Cikin Dimuwa Menake Boyemaka? Ko Menene Banyi Da Gayya вa,a, "Da Gaske?" Aiko Da Mamaki Ace Bakida Dalilin Sanar Dani Kina Da Ciki Har Sai Likita Daga Waje Yafadamin Nandanan Tai Fuska Oh!Wallahi Nazaci Kasani Nasani? A Ina Zansani? Ta Dubeshi Ido Cikin Ido Aina Kake Sanin Abubuwan Danake Yi Lokacinda Bamatare? Yadanyi Kasake Saikuma Yamike Cikin Kuzari Yana Kai Komo A Falon Itakuma Tai Tagumi Kawai Tana Kallonsa Da Sauri Ya Nunata Da Yatsa Wannane Dalilinda Yasa Kika Boyemin Kina Da Ciki? Bare Har Na Rubanya Miki Tattalina Kukasance Cikin Koshin Lfya Keda Bebin? Cikin Dakewa Ta Kada Masa Kai Yajima Yana Kallanta Fuskarsa Ba Yabo Ba Fallasa Yanufi Daki Yana Cewa Ina Zuwa Ta Bishi Da Kallo Cikin Fargaba Tana Hasashen Abinda Zaiyi *** **** *** Yana Dogare Da Kofar Dakin Yawatsa Wa Somoli Takarda Yana Huci Idonsa Akan Mominta Ya Ce Ina Fata Zaku Hada Kare Yanzu Kubarmin Gida A Tafi A Babbakamin Gidan Wani Nidai Allah Ya Kubutar Danawa Dan haka Kudin Da Kuka Dauka Saiku Yi Hidimar Haihuwar Dasu Dama Abinda Zanyi Dasu Kenan Ya Fice Abinsa Cikin razana Musamman Da Suka Ga Saki Uku Momi Ta Dora Mayafi Aka Jikinta Sai Karkarwa Yake Kinga Kwantar Da Hankalinki Kiyi Zamanki Zanje In Sami Boka Tafice A Gaggauce Tabar Sumoli Cikin Mawuyacin Hali Da Nadama Kaitsaye Yushau Gidansu Ya Zarce Ya Kwashe Komai Yagayawa Hajiyarsa Dukda Cewa Ta Razana Dajin Hakan Ta Ce Kaikuma Haka Allah Ya Jarrabeka Da Sakin Mata Kuma Da Ciki Musamman Ma Wadda Take Gargarar Haihuwa ? Cike Damamaki Yake Kallonta Kodayake Mai Daki Shiyasan Inda Yakemasa Yoyo Amma Sumayya Ko Cikin 'yan Dari Take Dashi Ya Cancanta Yaimata Saki Uku Karfe Sha Biyun Dare Yakoma Gidansa Idonsa Akan Dakin Sumoli Yaga Alamar Tanan Cikin Tafasar Zuciya Yanufi Dakin Yakwankwasa Babu Jimawa Ta Zo Ta Bude Kofar Yajima Yanamata Kallon Mamaki Ke Kinsan Allah? Ko Kwalam Ta Koki Ce Ta Kawoki Duniya Saikin Bar Gidannan!Wallahi Sai Kinbar Shi Zama Dakena Haramtawa Kai Har Abada Saboda Haka Nayi Miki Alfarmar Safiya Ki Hada Tsiyarki Kifita Daga Rayuwata Jafa'inki Yafi Karfina Sumoli Ta Daga Kafa Da Kyar A Kokarinta Na Komawa Dakι Sakamakon Wani Matsanancin Ciwon Ciki Dataji Ya Soketa Lokacinda Yushau Ya Bar Gurin Wasa Wasa Ya Zarce Ciwon Mara Batasan Sanda Ta Rarrafa Kofar Dakin Yushau Ba Tana Bugawa Yushau Yadinga Tsaki Yana Juyi A Gado Yanajin Nishin Sumoli Har Na Tsawon Fiye Da Minti Ashirin Yana Kwance Sai Nasihar Mahaifinsa Ta Fado Masa Ka Kyautatawa Kanka Ta Hanyar Bin Umarnin Ubangijinka Bisa Kyautata Mu,amala Tsakaninka Da Matan Daka saki Hakanyasa Ya Fito Kilama Haihuwa Ce Amma Me? Yana Bude Kofar Yaci Karo Da Ita Kwance Cikin Jini Da Alama Ta Mutu! *** ***** Idon Ruma Nakan Hanya Nazifi Yafito Dakin Hannunsa Dauke Da Wayoyi Biyu Yazauna Kusa Da Ita Ta Fahimci Wayartace Da Tasa Wayar Cikin Dukan Zuciya Daitake Binsa Da Kallo Tana Canki Cankar Meyake Nufi Iyakar Zamanta Dashi Bata Taba Ganin Wayarta A Hannunsa Ba Yadago Wayarta Yana Karemata Kallo A Hankali Ya Ce BB PORSCHE Ya Dago Ya Dubeta A Ina Kika Sai Wayar Nan? A Rude Take Ta Ce Milkyway Mana Ai Tunda Kuka Tsafeni Ko katin Waya In ba na Can ba Sai Inga Bashi Da Auki... ᴬˢᴹᵞᴳᵞᴳᴳ Dan Aunty GORAN DUMA (P 66) . . Nawa Kika Siya Ina Tsammanin Ko Dubu Tamanin Ne Ko Saba'in Ne Mts Na Manta Dai Zaki Iya Tuna Ranar Dakika Sai Wayar? Ban Mance Ranar Dana Siya Ba Ranar Sha Biyar Ga Watan Nuwambar Shekarar Dubu Biyu Da Sha Biyune Na Rike Ranarne Lokacindana Shiga Tarkonka Na Bincika Kuma Na Tarar Kaine Nazifin Dana Fara Haduwa Dakai Ranar Danaje Siyen Wayar Kinsan Gaskiyar Kudin Wayarnan? Ta Zuramasa Ido Tana Dawani Farashine Bayan Wanda Na Siya? Kudin Wannan Wayar Yana Kamawa Daga Dubu Dari Uku Zuwa Sama,ruma Ta Saki Baki Kawai Tana Kallonsa Har Tsawon Dayagama Danne Dannensa A Wayar Ya Dago Suka Hada Ido Yasakar Mata Murmushi Itakuma Ta Basar Ta Kawar Dakai Amma Yasanya Ta Dawo Dakan Ta Dubeshi Lokacinda Ya Cemata Inasonki Rumasai Muryarta Na Sarkewa Ta Ce Game Din Bai Kare Ba Kenan? Yadan Kai Mata Dukan Wasa Cikin Raha Wato Game ne? Kai Ka Kirashi Da Haka Ta Fada Yanisa Hakane Ubangiji Mai Cewa Kasance Kuma Ya Kasance Shi Yajefamin Kaunarki Farat Daya A Ganin Farko Danayi Miki A Harabar Milkyway Ranar Sha Biyar Ga Watan, Nasan Zaki Tuna Yadda Naso Nuna Kaina A Wajenki Kika Ki Bani Hadinkai Inda Har Na Kai Ga Yimiki Karya Na Karanta Jarida A Jami'ar Bayero Na Kuma Dace Na Fada Daidai Alhalin Ban Taba Karatu A Kanoba Ta Daga Masa Hannu Alamar Jinjina Tana Murmushi Daga Nan Saime? Yakama Hannunta Yahada Da Nasa Shirine Ni Da Masud Wato Manajana A Karbi Wayarki Da Zummar Za A Sanya Miki Credit Anan Muka Dauki Lambobin Wayarki Ta Zaro Ido Cikin Mamaki Eye!Ai Tukunna Ya Fada Yana Dariya Ta Sauke Ajiyar Zuciya Sannan Ta Zame Hannunta Daga Nasa Ta Mayar Da Tagumi To Cigaba Yakarbi Wayarta Yana Dubawa Wannan Wayartaki Ko Sati Daya Banyi Da Mallakarta Ba Na Siye Ta A Japan Sannan Wani Abokin Karatuna Kuma Kwararre A Fannin Kerekere Yayi Aikin Sanya Mata Wata Software Mai Suna "droid Air Ya Ajiye Wayar Tata Sannan Ya Dauko Tasa Ya Shiga Matso Hotuna Kana Ya Ci Gaba Kinsan Ko Wacce BB Tana Da Blackberry Id Wannan Ne Yake Bayar Da Damarko Ansace Ta Ake Iya Ganota Ta Wannan Hanyar Kuma Ana Iya Ganin Abinda Ke Gudana A Wayar Kamar Aikawa Da Sakonni Kira Da Shiga Internet a Sannan Kuma Ana Iya Gane Inda Take Ruma Tadinga Kallon Wayar Cike Da Doki Bayan Haka Ita Wannan BB Porsche Din Tana Iya Daukar Hoto Mai Ita Ta Tura Wani Guri Daban Idan An Saita Ta Yamika Mata Daftarin Wasu Hotuna Daya Budo A Wayar Sa Hannunta Na Karkarwa Ta Karba Cikin Baza Ido Dantun Kafin Wayar Tazo Hannunta Ta Gane Hotunanta Ne Cikin Rawar Ido Da Jiki Tafara Duban Hotunan Daya Bayan Daya A Abujane A Kano Ne A Motane A Rano Ne A Kan Dutsene Gasunandai Dayawa Yamiko Hannu Ta Bashi Wayar Amma Takasa Kawai Sai Ta Dago Ta Zuba Masa Ido Numfashinta Na Bugawa Da Sauri Da Sauri Ya Boye Damuwar Rikitar Yaci Gaba Dayimata Bayani Waccan Software Da Abokina Yasanya Min Ana Samunta Ne A Irin Wannan Android Din Yanuna Mata Wayar Sa Dake Hannunta Idan Aka Saita Wayoyi Biyu Masu Wannan Software Duk Nisan Dake Tsakaninmu Ko Da Inanan Nigeria Kina China Zaniya Sarrafa Wayarki Yaddanaso,zaniy a Gano Indakike Zaniya Daukar Hoto Zaniya Nado Sauti Zan iya Shiga Mesgs Dinki Hakadai Ya Ci Gaba Da Nunamata Ita Kuma Taita Godiya Ga Allah Dayasanya Bawani Abin Asshan Take Aikatawa Ba A Boye Lokacin da Kike Tsaye A Harabar Milkyway Muna Tsaye Nida Masud Muna Kallonki Tare Da Kulla Yadda Zamu Bullowa Lamarinki Har Lokacinda Kawarki Ta Shigo Kuka Shigo Tare Kawai Sai Ga Sani Ya Rugo Fadamana Ai Ipad Kikazo Siya To Anan Ne Ba Tare Da Dogon Nazari Ba Masud Ya Kawo Shawarar A Siyar Miki Da Wannan Wayar Ruma Ta Rasa Bakin Magana Sai Kallonsa Kawai Take Babu Kiftawa Cikin dariya Ya Hura Mata Iska Ta Wadannan Hanyoyin Nai Tracking Din Ayyukanki Ta Haka Nasan Ke 'yar Jarida Ce Har Nagano Jaridardakike Da Wa Aiki Wanda Hakan Ya Saukakamin Gano Muhallinki Ta Haka Nasanke Sikila Ce Ta Haka Nasankin Taba Aure Har Nasanwa Kika Aura Nasan Kintaba Son Wani Auwal Amma Ya Rasu Nasan Ranar Birthday Dinki Saidai Nasan Ki Da Kyau Daga Nanan Gidanku Abuja Har Mazauninki Na Kano Kafin Nan Tunda Nasan Ke Sikila Ce Na Shiga Neman Sani Akan Sikle Cell Naziyarci Kwararren Likitan Da Ya Shawarceni Tare Da Gwaje Gwajen Har Na Dace Da Cewa Zan Iya Aurenki 'ya'yanmu Su Tsira Saida Duk Na Gama Danan Sannan Na Dauki Hanyar Kano Dan Haduwa Dake Nana Kum Nayi Katarin Haduwa Da Sani A Matsayinsa Na Abokin Abokina Shi Kenan Yaimin Tsanin Haduwa Da Alhji Wadda Nan Ma Na Sake Katarin Ashe Yasan Mahaifina Wannan Katarin Ma Yakara Saukaka Min Samin Aurenki Musamman Ta Bangaren Mahaifiyata Waddata Kyamaci In Auri Bazawara Amma Mahaifina Na Jero Mata Lissafin Daga Gidan Dakika Fito Saita Saki Ya Tayar Da Kallo Akanta Cikin Dage Gira Wannan A Takaice Kenan Kin Gamsu? Jiki A Sanyaye Da Kuzarin Karfin Hali Ta Girgiza Kai Sannan Ta Shiga Cikin Wayarta Ranar Sha Daya Ga Watan Sha Biyune Naje Abuja Dan Tsira Daga Basajarka Ta Kano Nakuma Zarce Milkyway Da Zummar Tura Wasu Ayyuka Ta Yanar Gizo Tunda Na Sauka Abuja Na Fahimci Mutane Na Binada Kallo Haka Ma A Milkyway Din Kowa Yasamin Ido Miyasa? Mutanen Gari Dake Kallonki Tsarguwa Kawai Kikayi Jama,ar Milkyway Kuwa Duk Sunsan Da Zamanki A Zuciyata Harma Masud Ya Basu Umarni Duk Lokacinda Suka Ganki Su Sanar Masa Ta Kada Kai Alamar Nuna Gamsuwa Sannan Tajefo Wata Tambayar Yaya Akai Kasan Zanyi Rubutu Akan 'yan Maye Ko Zuwana Gidan Hafsa? Na Nadi Sautinku Lokacinda Kuke Hira A Mota Da Mubarak Tare Da Abokinsa Haka Zalika Na Nadi Sautin Farkon Hirarku Da Hafsat Ruma Tajima Cikin Kada Kai Da Tunani Sannan Ta Furzar Anji Amma Tayaya Kake Gane Abubuwan Da Nake Rayawa A Zuciyata? Cikin Zaro Ido Ya Ce Kai Haba!Saika Ce Wani Maye? Sukayi Dariya Su Duka Sannan Tazarce Da Magana Misali Ranar 16th Ga Watan Biyu Dubu Biyu Da Sha Uku 16-2-2013 Ranar Naje Rogo Kuma Na Hau Dutse Sakonka Na Daidai Lokacin Tamkar Kalubalanta Ne Ga Radadin Da Zuciyata Take Dalilin Hasashen Da Kaicon Daya cikata Tana Sauke Numfashi Ya Amsa Mata Idan Ina Son Abu Ko Wane Irine Ina Da Juriyar Nunawa Allah Shi Na Tsananta Addua Akanki Fiye Da Yadda Kike Tsammani A Tsawon Dararena Dan Haka Karkiyi Mamaki Idan Na Dinga Aikin Da Zai Dinga Dacewa Da Abinda Uwar Dakin Zuciyarki Ke Kimsawa Abuna Gaba Kuma Daya Kamata Kituna Digirina Na Farko Halayyar Dan Adam Na Karanta Babu Laifi Ina Iya Karantar Mutane A Yayin Furucinsu Ko Kallonsu Lokacinda Suke Wani Aiki Kamar Dai Yadda Na Kalli Fuskarki Akan Dutse Sanin Kankine Duk Wanda Zai Nufi Daji Ya Kurawa Horizon Ido Cikin Aihini Tabbas Sai An Tarar Yana Jinjinawa Makagin Sammai Da Kassai In Kuma Zai Zurfafa Tunaninsa Sai Ya Dangana Da Mutuwa Ruma Ta Sake Rafka Tagumi Tana Kallonsa Cikin Murmushi Can Ta Sauke Wata Wawuyar Ajiyar Zuciya Wato Abinda Kaimin Kenan,? Kwarai Da Gaske Kyautatawa Nayi Ko Laifi? . Idan an samu isashshen commnts zamuyi post din karshe anjima.... . Dan Aunty GORAN DUMA KARSHE... NA MAIMUNA BELI TARE DA ABBAS ABDULKADIR HADA HADA . . Eh To Uhum Ka Kyauta Din Kenan Kila Ba Dan Kayi Haka Bada Yanzu Bansami Maijin Kaina Nida 'ya'yana Ba Cike Dajin Dadi Yace Ko Banyi Haka Ba Dole Zamu Hadu Allah Ya Hukunto Tuni Cewa Sai Mun Auri Juna Saboda Haka Dole Mu Hadu In Baki Wannan Bebin Tare Da Kannensa Masu Zuwa Ya Shafi Mararta Ko? Tafada Cikin Kunya Da Dariya Toke Yaya Kika Gani? Yatareta Cikin Dole Dan Karta Ci Gaba Da Sharewa Takada Kai Hakane Yadanyi Shuru Zuwa Wani Lokaci Sannan Ya Ce Idan Nasami Lokaci Mai Kyau Zan, Samu In Wargaza Saitin. Ya ShiGa Duban Agogo Sannan Yasake Dubanta Lokacinkine Yanzu Kin Kuma Cinye Shi Da TuhumeTuhume Karka Damu Duk A Ni Din Ne Yakura Mata Ido Har Saidata Tsargu Tanemi Baasi Da Ido Ya Ce Wai Da Gaske Zaki Haifo Min Ya'yan Dazasu Janyo Na Kara Sonki? Kuma Nima Idan Na Haifo 'ya'yan Nasan Tawa Zuciyar Zata Iya Tarar Da taka Zuciyar Wadda Ta Shahara A Sona Ya Kame Kafadarta Da Sauri Tokice In Kara Murna Haihuwarki Nafada Ka Kara Murnar Suka Tuntsire Da Dariya Su Duka ********* *** Duk Da Yushau Ya Yanke Kaunar Kawai Sumoli Ta Mutu Bai Kasa Kwasarta Cikin Tashin Hankali Yanufi Asibiti Ba Ananne Aka Tabbatar Masa Da Bukatar Jini Bayan Ta Farko Daga Dogon Sumanta Lokacin Dake Gwada Jininsa Dan Neman Dacewa Da Nata Saida Ya Kawar Dakai Cikin Hawaye Ga Ruma Can Wadda Ta Cancanci A Bata Abinda Yafijini Tana Can Tana Rayuwa Da Jininsa Amma Ba A Matsayinsa Ba Wannan Asarar Da Kyar Zai Iya Mayar Da Gurbinta Jinin Sumoline Ya Hau Abinda Ya Sabbaba Mata Barin Jini Kenan Ta Galabaita sosai, Aka Fara Yimata Karin Jini Da Jiran Cikar Waadi Da Idan Bata Haihu Ba Sai Ayimata Aiki Cikin Ikon Allah Kafin Sfya Ta Haifi Santalelen Danta Namiji Bayan Yai Waya Gidansu Ya Sanar Da Hajiyar Su Haihuwar Saiya Mikawa Sumoli Wayar Wadda Ke Kashangare Tana Kallansa Bakin Cikin Sakin Dayai Mata Ya Hanata Farin Cikin Karuwar Data Samu Ungo Ki Kira Mutanen Gidanku Ki Sanar Dasu Kin Haihu Kai Bazaka Sanar Dasuba? Ta Tambaya Ya Kawar Dakai Yana Kara Bata Rai Idan Kina So Su Sani Kawai Ki Sanar Dasu Kaitsaye Ta Amsa Cikin Kuramasa Ido To Banaso Su Sani Dan Allah Ka Daukeni Mu Koma Gida Na Rantse Zan Rayu Dakai Kai Kadai Batare Da Kowa Ba Kuma Nai Alkawari Zanzame Maka Zallar Farinciki Har Mutuwa Ya Gwasaleta Ya Ce Allah Sarki Bakin Alkalami Aiya Bushe Sukai Shuru Har Tsawon Wani Lokaci Saida Sumoli Ta Ga Babu Sarki Sai Allah Sannan Taiwa Mominta Waya Ta Sanarmata Yushau Na Harabar Asibitin Mahaifan Sumoli Sukazo Tare Dawasu Yayyenta Yana Sane Ya Boye Musu Suka Shige Har Saida Yagano Nasa Mahaifin Sannan Yataro Su, Tunkafin Su Shiga Dakin Suke Jiyo Bambamin Fadan Mahaifin Sumayya Wanda Ya Saci Jin Hirar Anyiwa Sumayya Saki Uku A Dalilin Satar Kudi Tsakanin Momin Da Yayyenta Masifar Dayake Batawasa Ba Ce Yana Nuna Tsananin Bakincikinsa Da Auren Momi Wadda Ta Tarwatsa Masa Rayuwar 'ya'ya Yanzu Zawarawanta Hudu A Gaba Allah Ya Kubutardani Abinda Yushau Ke Maimaitawa Cikin Ransa Kenan Ganin Su Yasanya Mahaifin Sumoli Yin Shuru Saida Aka Gaggaisa Tare Dayiwa Juna Barka Sannan Mahaifin Sumoli Yanemi Komawa Fadansa Alhjin Yushau Yatareshi Ai Alhji Duk Hakuri Za Ai Kai Yushau Daure Ka Mayar Da Matarka Cike Da Karsashi Yushau Ya Ce Ai Saki Uku Ne Alhji Kayi Wauta Yushau Alhji Yadinga Maimaita Cikin Alhini Yushau Kuma Yai Sagare Yana Kallan Alhji Sannan Ya Dubi Sumoli Wannan Kadai Yaisa Tabbatar Da Nufinsa Na Sumoli Tafi Karfin Hakuri Duniya Mahada Duniya Maraba Inji Wani Mawaki Anan Dangi Biyu Suka Hakurkurtar Da Juna Tare Da Alkawarin Kin Yasar Da Zumunci Daganan Kowa Ya Kwashi Nasa Iyalin Akai Gida Dukda Yushau Yadinga yi yana Ta Satar Kallon Dansa A Goye Bayan Sumoli Zuciyar Sa Cike Da Dokin Ya Cika Shekaru Biyu Ya Dauko Abinsa Ba Tare Daya Tashi Gidan Da Ake Rowar Tarbiya Ba. Wani Lokaci Ciwon Ruma Yatashi Yadda Take Murkususun Ciwo Cikin Kuka Haka Nazifi Ke Murkususun Ciwon Zuciyar Tausayinta Cikin Hawaye Sai Bayan Allura Tafara Ratsa Ta Harta Sami Bacci Sannan Ya Kwashi Sanyayyar Gwiwarsa Ya Bar Dakin Da Aka Kwantar Da Ita Ya Cimma Likita A Ofishinsa Likita Wane Aikine Ka Ce Ana Yiwa Sikila A Rabasu Da Ciwon? Likita Wane Aikine Kace Anayiwa Sikila A Rabasu Da Ciwon? Likita Yadan Dubeshi A Razane Baki Na Rawa Ya Amsa "'Bone Marrow Transplant"" Wato Dashen Bargo Kasancewar Ciwon A Ainihin Jininsune Kuma Bargo Ke Samar Dajini Dan Haka Saidai A Canja Shi Da Wanda Zai Samar Dajini Mara Wannan Kantararrun Sel Din To Ina So Ayi Wa Matata Likita Ya Dubi Nazifi Da Kyau Saiya gane Sam Ba Cikin Hayyacinsa Ma Yakeba Saboda Haka Ya Bar Kujerarsa Yadawo Kusa Dashi Yadinga Rarrashinsa Tsawon Lokaci Har Ya Fahimta, " Ka Manta Ne?" Amma Tun Zaman Farko Damukayi Na Sanar Dakai Cewa A Nigeria Ba A Taba Wannan Aikinba Sai A Kasashen Turai Acandin Ma Saiwane Da Wane Akewa Saboda Yana Lasar Miliyoyin Kudi Nazifi Ya Katsi Numfashinsa Nawane Kudin Farashin Yana Canzawa Daga Wannan Kasa Zuwa Wannan Amma Dai Yana Lasar Makudan Daloli Likita Ya Amsa Nazifi Yamike Dafe Dakai Yana Ambatan Innalillahi Wa Inna Ilaihirajiun Sannan Yanuna Alamun Fadawa Tunani Mai Nuna Kwantar Da Hankali Yadinga Safa Da Marwa A Ofishin Cikin Dukan Zuciya Likita Na Kallansa Cike Da Tausayi Sai Can Yaga Nazifi Ya Daga Hannaye Sama Cikin Hawaye Fuskar Sa A Sakeya Ce Ya Ubangiji Ina Rokonka Da Iliminka Nashaida Kaine Ubangiji BaBu Wani Bayan Kai Makadaici Wanda Bai Haifa Ba Kuma Ba A Haifeshi Ba Ubangiji Kaika Ce Duk Wanda Yarokeka Zaka Amsa Masa Ina Rokonka Ka Hore Min Halak Dinda Zan Biya Kudaden Daza Aiwa Matata Ruma Da 'yarta Hamida Aiki Sannan Ka Saukaka Musu Su Da Sauran Sikila Irinsu Tare Da Dukkan Marasa Lfya Allah Ka Sanya Wannan Ciwon Yaimusu sauki, Kasa Yai Sanadin Shi Ga Aljanna In Har Sun Bayar Da Gaskiya Dakai Kuma Ka Bawa Jagororinsu Juriyar Kula Dasu Amin Likitaketa Faman Amsa Masa Cike Da Jintausayi Yana Kallan Nazifi Wanda Ya Goge Kwalla Sannan Ya Juyo Yai Masa Murmushi Yana Daga Masa Hannu Har Yafice Likita Yakoma Mazauninsa Jiki A Sanyaye Cike Dajin Wani Irin Kaye A Zuci Dama Dai Duk Sikila Suna Samun Irin Wannan Gatan Daga Mazaje Ko Iyayensu Dama Hakan Takasance Rayuwa Yacigaba Da Wanzuwa Cike Dajin Dadi Da Kulawar Nazifi Har Allah Ya Sauki Ruma Lfya Tasamu Danta Kyakyawa Maikama Da Ubansa Cike Da Koshin Lfya Batare Da Sikila Ajikinsaba Inda Suka samasa Sunan Mahaifin Yushau Sunakiransa Da Irfan Dan Ruma Tana Alfahari Da Alhji Yajajirce Kwarai Akanta Da Lfyarta Wanda Tai Amanna Koda Mahaifantane Iyakar Abinda Zasui Matakenan. . ALHAMDULILLAH KARSHE Marubucia MAIMUNA IDRIS SANI BELI. . Naso ace an iso wajen da Ruma zata samu lapia , ace koda a cikin dangi ne an hada kudin da za a mata aiki da erta Hamida, ciwon bashi da dadi ko kadan, nasan ciwon, shine sanadin tafiyar kanwata mai bina, yanzu haka karamin kani na yana dauke da kwayan ciwon. Likitoci sun tabbatar ba cuta bace, halittace abun kamar yadda kuka ji a cikin littapin, mace da na miji su suke haipar da irin kwayar cutar a jikin d'an da zasu haipa. Shi yasa yanzu likitoci suke bada shawaran kowa yasan Genotype din sa, tun kapin soyayyar ku tayi nisa kusan makomar ku, ammana kuskure ne sai ana saura kwana 3 aure aje gwajin genotype, da dama basa barin auren su koda an same su da duka A.S , suna duba soyayyar dake tsakanin su alhali basu san illar ciwon ba, a cikin littapin nan kadan aka ambata muku game da illar ciwon , ga wanda suka sani sun sani, ciwon kaman iska, yanzu-yanzu zaku zauna da mutun lapia anjima kadan ya birkice babu lapia. A binciken da akayi a dunia a Nigeria tapi yawan masu dauke da ciwon sikila, kuma arewacin Nigeria ne, saboda ba'a gwaji yayin aure shi yasa muka pi kowa dauke da masu shi ciwon, kwanaki nagani a jarida wasu en mata da aka musu dashen bargo tun suna yara, a lokacin an musu dashen bargon ne ko wacce kimanin 26m a Austrilia, A yanzu kuma kudin ya kama kimanin 100m (Miliyon dari,) a kudancin Nigeria ma wai an para, anyiwa mutun 6 an samu nasaran mutun biyu, lititocin sunce idan ana son abun ya daure dole sai gwamnati ta shiga ciki ta bada nata gudumowar da tura likitoci kara ilimi da kayan aiki. . dan Allah ina kira ga samarin gidan nan da en mata da ku ziyarci asibiti domin a muku gwajin wannan GENOTYPE din saboda koma yasan makomar sa. Ina ganin yadda mahaipiya ta take pama da ciwon, tayi jinyar kanwata, ta rasu 2015, tun tana wata 8 ake pama da jinyarta, san da takai shekara 15 ta rasu, yanzu ma haka ga kanina ana pama da jinyar sa shima tun aihuwar sa, shi da zapin ciwo yana kuka mahaipiya da hawaye.... Kusan kullun haka suke shi da ita idan ciwon ya tashi babu bacci a idon su, haka zasu ini haka zasu kwana. Mahaipiyata kullun tana hanyar asibiti tare dashi.... Ciwon babu dadi ko kadan. Ina mai Addu'ar Allah ya sawaka wa masu pama da cuta komin kankantarta Ya basu lapia Ya yaye musu, mu kuma da muke da lapia Allah Ya kara mana lapia mai albarka. Aamiin . Dan Aunty... Angon Hamida.. Ehem.. An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 21 of 21