Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Tabbata Bai tanka Ba Ya Kirga Dubu Goman Ya Zubemata Kan Durowa Ya Kwashi Lesunan Yafice Sannan Ta Kwashi Kudin Tajefa Ajaka Ta Kulle Gidan Ta Fice Sai Gidan Wata Kawar Mominta Hajiyar Dubai Da China Ta Kwaso Lesunan Bashi Ta Wuce Gurin Dinki Ta Bayar Da Dubu Goman Yushau A Kudin Dinkin, gidan Abokinsa Mai Kudi Ya Nufa Inda Matar Sa Tasha Fada Masa Matsalar Sikila Da Bukatar Su Ayanzu Kam Yanade Hannu Zaitafi Neman Iliminsa Kaga Na Jaruma Sumayya Mai Zizar Sunan Sumoli,kaga Mutum Na Musamman Wanda Kiyayyar Ruwa Kesashi Kiba Soyayyar Sumoli Ke Sanyashi Rama,, irin Wannan Kirarin Maikudi Abokinsa Kemasa Yushau Kam Kasa Magana yayi. Haka Dai Tazage Tana Bashi Bayanin Masu Ciwan Sikila Saboda Sunadasu A Danginsu Inda Duk Wata Alama Yushau Yaji Tafada Yanaganinsa Ga Ruma Hartagama Yatafi Abinsa Tare Da Yunkurin Komai Zai Daidaita Tunda Yagano Bakin Zaren, ********* garin Rana Sosai Ruma Damai Adaidaita Sahunta Keke Napep Suka Hau Titin Layin Gidan Atika A Unguwar Hotoro Ruma Na Cike Da Dokin Akarasa Gidan taga Dangi Taga Kuma Sabuwar Bakuwar Dasuka Samu,dahaka Tadinga Binne Mahaukacin Masoyi Da Matsalar Sa Koda Na Wuni Dayane Tall,wato Taje Tadawo,basui Nisa Da Hawa Titinba Sai Ga Adaidaita Sahun Ya Mutu A Titin,subhan Allahi Kabiru Meyafaru?? Karfen Nan Yagaji Dani Hajiya Shekaran Jiya Fa na Karboshi Daga Gurin Mai Gyara Inda Yacimin Naira Dubu Ashirin Da Takwas Amma Tunjiya Yafara Yimin Mahangurba,ruma Tadan Yi Dariya Kalmarsata Karshe,ta Duba Agogo Taleko Kai Tana Kokarin Hango Kabiru Wanda Yadawo Ya Shi Ga Turata Gefen Hanya Inda Ya Tsayar Da Shi Gefen Wani Mota B,M,W, Series 5 Wadda Ke Kafe Gurin Tun Kafin Keke Napep Dinsu Takaraso Nan Dukda Akwai Dan Duhu Gilashin Motar Ana Iya Gane Matashin Direban Dake Kwance,mazauninsa Yana Sauraren Wakar The Power Love,maitashi Kasa Kasa Daga Bakin Celine Dion,sama Da Mintuna Goma Ruma Na Cikin Adaidita Sahu Zafi Da Ciwon Jira Na Dimarta Har Ta Kosa Tafito Ta Tsaya Akan Kabiru Wanda Yake Tabe Tabe A Injin BaBurdin,haryanzu Dai Kabiru?Wallahi Kuwa Tundazu Nake Faman Taremaki Adaidaita Din Dazai Karasa Dake Amma Kinga Duk A Cike Suke Zuwa,ikon Allah Tabi Titin Da Kallo Tana Rayawa Aranta Inama Zata Iya Data Karasa A Kafa Ta Huta Da Tsayuwar Ta Dora Da Zolayar Sa To In Hakane Kuwa Zanbaka Hutu Tunda Ga Ya Shirya Hadamu Yayimana Mahangurbar Tare Yau Wannan Zafinda Ake Kwadawa Idan Ya Rikide Yazama Hadari Yazubda Ruwa Fa? Kabir Yafara Yunkurin Tare Wani Adaidaita Dayashigo Layin Yana Amsamata Nima Haka Nafara Tunani Ai Karshen Watan Nan Ma In Allah Yaso Zan Sauya Yana karasowa Sukaga Ai Cike Yake Da Mutane Ruma Ta Rungume Hannu Ta Ce Bar tarewa Ka Koma Ka Lallaba Ko Zai Hakura Ya Bari Ka Karasa Dani, Dukansu Sukai Dariya YakoMa Yana Tabata Mintuna Biyar Tsakani Matashin Nan Ya Bude Motar Sa Yafito Ya Riski Kabiru Baidamu Da Kallon Rumasau Ba Sam,kamar Yadda Itama Bata Mayar Da Hankali Akansa,saida Maganar Sa Taja Hankalinta Ranka Yadade Meyasami Keken Naka Dazaka Shanyata Arana Haka? Abinda Kabiru Ya Kaddara Shine Ruma Tasan Matashin Danhaka Ya Amsa Da Kar Sashi,tsautsayine Yallabai Kuma Muna Ta Kokarin Tare Wanda Zaikarasa Da Ita Bamu samuba,ya Dago Suka Gaisa Yacigaba Da Duba Injin Din,sai Ya Bar Ruma Da Tunanin Ina Tasan Matashin Saurayin Baki Mai Dogon Hanci Da Fararen Idanu,? Bata Canka Ba,takuma Kasa Kojin Kunyar Kallon da take Masa Bare Ta Hakura Cikin Faduwar Gaba Da Raunin Zuciya Iri Iri,can Yajuyo Yadubeta Duban Da Bai Nuna Mamaki Ko Tuhumar Kallan Datake Masa Ba Yadago Ya Dubeta Aransa Yana Mamakin Kota san shine Takemasa Kallo Haka Yanuna Motar Sa Kinga Muje Inkarasa Dake, Tajima Mamaki Yadda Yake Kokarin Bata Umarni Irin Na Yaya Da Kanwa Amma Hakan Bai Hana Ta Daure Gira Ta Cemasa Bisa Wace Hujjar,,? Ragowar Maganar Tamakale A Makoshinta Bayan Tagane Motar Data Dan Gifta Su Kadan Yanzu Ta Yushau Ce Kuma Da Alamu Ya Ganta Dan Gashi Can Yana Kokarin Samun Guri Ya Tsaya Nantake Taji Haushi Da Kyashin Ya Ce Tazo Yakaita Kuma Itama Ta Bishi Suje Gidan Mutane Da Kowa Yagansu Tare Zai Ga Bakinta Arashin Zuciya Kawai Saita Zabi Bin Matashin Nan Wanda Zuciyarta Ta Darsa Mata Kila Irin Kannen Mijin Anti Atikane,tunda Gashi Yasan Ta Ita Kuma Tanai Masa Kallon Sani,to Nagode Tasami Kanta Da Fada Tare Da Kada Kai Alamar Amincewa Ta Dubi Kabiru Ka Kyale Shi Kaje Ka Nemo Mai Gyara Idan Na Dawo Da Yamma Kazo Kasameni Da Sauri Ta Bi Bayan Saurin A Zuwan Bataga Yushau Wanda Ya Bude Mota Ba,da Alama Shima Matashin Kamar Yagane Abinda take Gudu Cikin Zafin Nama Yadaga Motar Suka Bude Yushau Da Kura,daidai Lokacin Dayake Daga Musu Hannu, matashin Ya Figi Motar Kamar Mai Shirin Tashi Sama Fuska Ba Yabo Ba Fallasa Idansa Ga Titi,hakan Kuwa Ya Kada Hantar Ruma Tafara Zargin Kanta Da Gangancin Kaikanta Makasa, Har Suka Kusa Gidan Anti Atika Ba Wanda Yai Motsin Ha,inci Atare Dashi Bai Dubeta, Ba Illa Yanata Hidimar Tukin Motar Sa Yanabin Wakar Sa,can Yajuyo Yana Rage Karar Sautin Au Namanta,ruma Yayajiki,nauyin Da Zuciyarta Tai Wajen Kokarin Ta Gano Inda Tasanshi Kokuma Tasan Muryarsa Ya Sanya Ta jinkirin Amsa Masa,da Sauki,dafatan Iyali Da Kowa Lfya,ta Kara Da Cewa Muryarta Na Rawa,akwai Alamun Ya Shanye Mamaki Lokacin Dayake Amsamata Kowa Lfyar Su Lau,kayi Hakuri Banfa Ganeka Ba Wallahi,, murmushi Kawai Yai Ya Basar Har Suka Karaso Batare Datamasa Iziniba Yanemi Guri Ya Tsaya Da Mota,adan Zuciye Zatafita Bakiji ba? Da Sauri Ta Tsaya Bayan Tafitarda Kafarta Na Farko,yanawasa Da Key Holder Inkinshiga Dan Allah Ki Gaidamin Mai Jegon,takarasa Ficewa Cikin Fusatarta Wadda Kuzarin Gangar Jikinta Ce Kawai Kenunawa Ta Rufemasa Motar Nagode Wazance Yanamata Barkar? Idanta Akan Makullin Motar Dayake Kadawa Cikin Sakanni Kadan Hantar Cikinta Yai Mugun Kadawa Sukadinga Lugude Abubuwa Biyune,wani Irin Kallo Dayake Mata,sannan Da Da Tambarin Milkyway Datagani Manne A Key Holder Sa,batagama Rudewa Ba Bare Tanemi Mafita Ya Tashi Motar Yafara Ja Sannu Yana Amsamata Cikin Murmushi MAHAUKACIN MASOYI Da Sauri ta Janye Jiki Tare Da Kokarin Tantance Shi Duk Da yaja Motar Aguje Haryana Neman Bugeta Ita Ma Kamar Zubin Haukar Bana Ta Diba A Guje Cikin Gida Daidai Lokacinda Yushau Ya Tsayar Da Motar Sa Inda Mahaukacin Masoyi Yadaga A Kidime Tafada Falon Atika Wanda Ke Cike Da Dangi,asiya MAIMUNA HAFSAT,DA YA'YAN KANWAR HAJIYAR SU HASANA DA HUSAINA,jiyo Sallamar Ta Kafinta Shigo Falon Ya Sanya Kowa Yadau Murna musamman Hafsat Wadda Tatashi Yiwa Ruma Oyoyo,amma Ina Ruma A Birkicetake,tana Zuwa Ta Suri Wayar Asiya Komai nata Rawa Sai Gashi Takarde Dakin Da Muryar Abdullahi Madarut Acikin Suratul Bakara Ta Ajiye Akan Kujera Taja Jiki Gefe A Hankali Ta Zauna,,falon Yai Tsit Cikin Alamar Tambaya Kuma Danta Gajarta Musu Aiki Saita Hada Tambayoyin duk Ta Amsa A Kalmomi Kadan,motar Aljani Na Hau Shiyakowani Har Kofar Gida Suka Dinga Duban Juna Anrasa Wanda zai yi magana..... . Dan Aunty GORAN DUMA (P.56) . . Hafsat Ta Ce Shine Wannan Ya Shigo Ta Girgiza Kai Toyaya Akai?Kowa Saitambayarta Yake Sai Ga Yushau Da Kyar Suka Kori Rudu Aka Gaisa Idan Aka Cire Ruma Wadda Take Takure Tana Karkarwa Yushau Yakore Kunya Da Nauyi Cikin Kishi Da Fargaba Da So,cikin Rada Hafsat Ta Matsa Kusa Da Ruma Ko Yaya Yushau Ne Aljanin? Ruma Ta Girgiza Kai ,to Ku Kashe Karatun Mana Kunata Faman Sheka Surutu Kuma Kun Ware Kuna Sheka Kuka Suka Kashe,,,kekuma Kalau?Yanzufa Naganki Lfya Harkina Shuka Min Wulakanci Ki Barni Tsaye Yanzu kuma Gaki A Burkice,duk datana Cikin Rikita Bata fasa Jin Haushin Son Nuna Mata Iko Da Yushau Yakeba Waita Wulakan tashi? Dan kawai Ta Guji Hawa Motar Sa Ta Ce Kai Yaya Yushau Kadaina Mayar Da Allura Garma Wulakancin Mena Shuka Maka? Amma Nasanar Dake Takanas Yau Zan Zo Gidan Nan Donke Daidaine Acce Kin Ganni Kin Shareni? Saima Budeni Da Kurar Dakikayi?Bisa Wani Dalili Zakazo Gidan Nan Domin Ni? Cikin Dacin Murya,kowa Kallansa Kawai Yake Yakore Kunya Kan Tsinkawar Da Ruma Taimasa Gaban Kannansa Inkin Kwantar Hankali Tunda Nazo Ai zan Fadamaki Dalili,, cikin Ci Da Zuci Ta Ce Saidai Wani Lokaci,ni Wallahi Yanzu Banda Sukuni, ran Yushau Ya Baci Sosai,amma Dole Yashanye Yana Nazarin Ruma Saikawai Ya Kaddara Aljanarta Ce Ta Bijiro Take Masa Rashin Kunya A Fahimtar Dayaima Matar Maikudi Amininsa Kenan Amma Tuniya Kwana Da Sanin Ruma Ba Halinta Ba,amma Dai Makakin Kishin Saurayin Ruma Ta Hawo Motar Sa Ya Gallabi Zuciyar Sa Ya Ce Wanne Shegen Ne kika Hawo Motar Sa Ya Badamin Kura? Ta Dauki Lokaci Bata Amsa Ba Kowa Yai Tsit Inka Cire Hafsa Wanda Dukkan Alamunta Kenuna Ita Idan An Bar Ta Zata Iya Bada Amsar, Kamar Aiken Amsar Daga Mahaukacin Masoyi Sai Ga Sakon Tex Dinsa Yafado Wayar Zuciyarta Tadinga Azalzalawa Ta Karanta Kozata Ga Abinda Zai Bata Tabbacin Kasantuwar Sa Jinsin Aljanu,INA MAIYIMIKI RANTSUWA DA ALLAH NI NAFI KOWA CANCANTAR ZAMOWA JAGORANKI,BA A SO KAWAI BA HAR DA BARAZANAR KAMUWA DA CIWAN ZUCIYA IDAN AN SOKEKI KO A TUKUICINE KAWAI BATARE DA SO BA,KI TAIMAKA AKARE NAWA MUTUNCIN KAR KI BARI A AIBATA MIKI NI. NAKI MAHAUKACIN MASOYI BA SHEGE BANE DAN HALAK NE! Tasami Kanta Da Kallon Tsakiyar Idansa Cikin Kuka Ta Ambata,a Maimakon Tasanar Dashi Cewa Aljani Ya Dauko Ta Bayan Ta Ga Tabbacin Aljanancinsa A Sakonsa,amma Aljanin Baiyi Tasirin Komai A Zuciyarta Da Fargabarta Ba,illa Zuciyarta Data Yi Mugun Raunin An Ce Masa Shege Bata Hana Ba,wani Mugun Kishi Ya Turnuke Yushau Yanata Kallanta Kallan Dake Son Dawo Da Ita Hayyacinta Tagane Cewa Ta,addanci Fatakewa Zuciyar Sa A Kokarinta Nafifita Wani A Kansa,amma Maimakon Haka Sai Ruma Takara Wani Taddancin Cikin Kuka Ta Maimaita Kalma Daya WALLAHI BA SHEGE BANE, yushau Dayaji Ashar Naneman Kwace Masa Saiya Fice Daga Falon ,falon Yai Tsit Illah Sheshekar Kukar Ruma Sai Can Hassana Tafasa Shirun Cikin Yanayi Na Zolaya Da Nuna Tausayi, ABIN TAUSAYI WALLAHI,YAYA YUSHAU YA FARKA DAHDAI LOKACIN YAKUSA MAKARA YASAMI WANI MAI KWANJI YAYI FASHIN ZUCIYAR, Hakan Yasa Kowa A Falon Yah Dariya Ruma Kuma Ta Tsagaita Da Kuka Takoma Hidimar Goge Hawaye,dan Allah Wai Yaya Akaine? Kin Barmu Cikin Duhu.Da Gaske Aljanine Yakawoki Kuma Shi Kika Zaba Kikabar Yaya Yushau? Maimuna Ta Cehaka ,hafsat Ta Zabga Mata Harara,a Kayan Miya Meyeshi Yaya Yushau Da Baza A Barshi Azabi Waniba? Zuciyar Ruma Kam Arude Take, Tamike Ta Isa Ga Usaina Ta Amsa Jaririn Tana Amsa Tambayar Maimuna A SURA KYAWAWAN DABIU DA SHIRYA KALAMAI MUTUM NE BA ALJANBA,AMMA A WASU AYYUKA YANAKAMA DANA ALJAN,NASHIGA WANI HALI,WANDA YASANYA NIKAINA NAKE MAMAKIN ZUCIYATADA IDAN BANYI KARYA BA ZAN FADI TA FADA TARKON SON ABINDA BATASANI BA,KO ALJANINE WALLAHI NAFADA TARKON SONSA,CIKIN TSANANIN RAUNI TAKARASA MAGANAR Duk Suka Tsagaita Da Alama Bada Wasa take Ba Hafsa Ta Ce Waiwanene? Mahaukacin Masoyi,lahaula Wala Kuwata Illah Billah,kinganshi Da Idanki? Shiya Daukoni Yakawoni Nan, Bayan Ta Zayyanamasu Yadda Haduwar Su Takaya Tare Kuma Da Cewa Tariski Sakonsa Akancewa Na Yana Dab Da Bayyana Mata Kansa,kun Barmu A Duhu Ku Warware mana? Inji Asiya, hafsat Takalli Ruma Kallan Neman Izini,ruma Tamike Tadauki Jariri Tana Ce Kisanar Dasu, Ta Wuce Kaitsaye Dakin Barcin Atika Kozata Samu Damar Wassafo Surar Mahaukacin Masoyi, Amma Tana Sauraran Hafsa Datake Basu Labarin Mahaukacin Masoyi Da Nuna Musu Tex Din Sa A Wayarta Bayan ta gama Kowa Ya Jinjina,wasu Suka Shiga Rudu,amma Abu Daya Ya Karfafamata Guiwa Maganganun Da Hafsa Take Kuma Cikin Yakini Da Gasgata Kai,na Bawa Kaina Sati Biyu Da Izinin Allah Sainabinciko Mutuminnan Haka,kawai Bazai Zautamin Yaruwa Ba Wallahi,ta Wace Hanyar? Atika Ta Tambaya Kin Manta Mijina Dan sandan Cikine? Lambobin Wayar Sa Nadauka Sun Isa Nagano Indayake, ********** Bayan Wuni Cikin Sake Sake Yushau Ya Yanke Shawarar Daukan Kwaryar Ban Hakuri Zuwa Ga Alhajinsa Bisa Abinda Yafaru A Baya Da Kokon Barar A Mayar Masa Da Ruma Yagyara Aurensa,yagama Shakulacin Bangaransa Wajen Hajiya,haryakai Ga Isa Ga Alhji Wanda Yasanyashi A Kwandan Shara,yajuyo Ya Fuskantanceshi,NASO NA TUNA WANNAN FUSKARKUWA? YALLABAI DAGA INA? Duk Dakuwa Wutar Dake Zuciyar Sa Tana Raya masa Kuka Yakamata Yayi Danhakan Kadai Ya Isa Nuna masa Saiya Wahala Malam Banfa Ganeka Ba Daga Ina?Kawai Sai Yushau Yasami Kansa Da Fashewa Da Dariya Yana Kallon Alhji Wanda Ko Kadan Dariyar Batasa Shi Ya Sassauta Damarar Dayai Wa Fuskarsa Ba,saima Yakawar Dakai Yaitsaki,hakan Ne Yasanya Yushau Yadan Shiga Taitayinsa,yadinga Kokawar Gyara Zama Yafara Bada Hakuri Na Tsawan Minti Gowa Sha Biyar,alhji Na Saurarensa Har Saida Takaici Ya Sanya Shi Tare Yushau Cikin Sarkewar Murya Dan Allah Malam Bari Batawa Kanka Lokaci,wai Hakuri Kadaine Kawai Yakamata A Rayuwa? Bashi Kadai Nara Sa Ba,abubuwa Da Yawa Wadanda Na Sasa A Bangarenka Wadanda Sukafi Su Muhimmanci Suna Fi Bukata,,,cikin Zumudi Yushau Yatare Shi Saboda Yana Zaton Alhji Zaice Ya Mayarda Auren Ruma Amma Sabanin Haka Kaitsaye Cikin Muryar Tura Haushi Alhji Ya Amsa,biya Na Kudaden Dasuke Wuyanka Mana,wadanda Nadinga Hidimar Iyalinka Dasu Tun Bayanda Ka Saki Uwar Su ,saima Ka Daukemin Kafa Da Aljihu Ka Barni Da Nauyi Danka Tabbatar Lallai Bazan Iya Kaisu Bola Na Zubarba! Ka Yi Ta Banzar Yushau Domin Komai Na Nan Arubuce Na Na Adana Ko Mutuwa Nai Na Sanar Da Magada Sunemi Hakkinsu A Wajenka,,, cike Da Rauni Yushau Yatare Shi,,kayi Hakuri Zan Biya Alhji,a Bani Adadi Sainafara Biya Daga Wannan Watan, daka Kyauta Wa Kanka,cikin Ko Inkula Alhji Yafada,falon Yai Tsit Inbanda Bugawar Zuciyar Yushau Wadda Ke Tattara Dukan Kafofin Da Zata Sauke Karfin Halin Data Wanko,akarshe Dai Da Ya Hattama Sai Bakinsa Ya Karbi Karfin Halin Yafurta Cikin Sarkewar Harshe,idan Rabuwa Da Ruma Ne Ya Nisanta Ni Daku? Kuma Har Shine Yaisa Abin Sanyawa Ka Manta Kamannina Alhji Ina Neman Alfarma Kadawo Dani Kusa Daku,,ku Mayar Da Diyancina Dan Haka Inaso Ka Sanya Albarkarka Ka Bani Dama Na Mayar Da Aurena Da Ruma... tunkafin Ya Dire Akwatin Tara Fushin Alhji Ta Cika,ya Yunkuro Da Fushi Yatareshi,,,wallahi Tallahi Danasan Maganar Dazakai Minkenan Na Rantse Da Allah Da Samsam Ban Saurareka Ka Sarayar Min Da Lokaci Ba,saboda Haka Idan Ba Son In Sassaba Maka Kamannin Ka Ba,to Ka Digawa Wannan Maganar Aya, yushau Yai Tsita Cike Da Fargabar Ta Inda Zai Billowa Alhjin.. Dan Girman Allah Alhji Ka Bani Dama Na Fahimtar Dakai Akasin Da Aka Samu Cike Da Takaici Alhji Yake Kallon Yushau Cikin Yanayi Nata Gina-ba-ta-shiga Ba Ya Cemasa Ahau!Inajinka Yushau Ya Gyara Zama Jiki Na Bari Ina Son Ruma Alhji Duk Wata Mace a Duniya Bayanta Zata Bi A Zuciyata,ban Fahimci Hakan Ba Sai Bayan Rabuwarmu Amma Fushin Da Kuke Ciki Ya Dinga Tsoratani Yana Hanani Kawo Kaina..... . Dan Anti. . . Sannan Sai Gurguwar Fahimtar Dana Yiwa Ciwonta Wanda Shine Kashi Casa'in Na Rashin Jituwarmu,ayanzu Kuwa na Nemo Iliminsa Na Tabbatar Matsala A Dalilinsa Takare Kuma Idan An Bani Dama Na Ci Alwashin Sai Ruma Ta Rabu Da Ciwon Nan Haihata Haihata Cikin Izinin Allah, oh Kana Da Kudin Daza a Canza ,mata Bargo Ko? Alhji Yakatse Shi A Shashance Cike Da Ladabi Yushau Ya Amsa A Iyakar Gaskiyarsa,a Binciken Danayi Nagano Shafar Jinnu Ce Naci Alwashin Daganan Har Saudiya Zandauki Nauyinsa Ayimata Rukiya, alhji Yafara Yiwa Yushau Duban Mahaukaci,da Kyar Ya Hadiye Wani Yawu Daya Cikamasa Makogwaro,yanunawa Yushau Kofa,tashi Ka Barmin Gida,,,,,,,,!,, Nima Ina Da Malaminda Zan Nemo Yaimaka Rukiyar Dankafi Ta Bukatar Rukiya,,, yushau Yai Funfurus Yakitashi Sai Shi Alhjin Yamike To Ni Barina Barmaka Dakin Kafin Yushau Yai Magana Tuni Ya Fice Danshima Ya Mike Jiki A Sanyaye Yana Kokarin Ficewa Zuciyar Sa Na Karkatar Dashi Cewa Kawai Yadage Ya Nemo Kan Ruma Dakanta Inta Kawo Wa Alhji Maganar Komen Ai Bazai kiba, *********** Kwanaki Uku Da Suka Biyo Baya Mahaukacin Masoyi Ya Bace A Rayuwar Ruma Ta Zahiri,wato Ba Bushi A Sakonninsa Kuma Ba Bu Shi A Zahiri Kamar Yadda Ya Billo A Matsayin Direban,dayakai Ta Gidan Atika Amma A Badininta Yananan Yana Ninkaya,wuni Da Kwana Yana Shige Da Fice A Zuciyarta Mai Wassafa Kamaninsa Tanakara Kawata Wa kanta Shi,abuna Biyu Kuma Tana Canke,canken Mutum Ne Shiko Aljan Sai Abu Na Uku Tana Tunanin Koma Waneneshi Wato Mutum Din Dai Ko Aljan Dinshine Wannan Nazifi Muhammad Daga Milkyway,sai Abu Na Karshe Shine,tanason Ganinsa A Fili Rayuwarta Ba Irin Yanzu Daya Ke Kan Katangarta Ba,kowace Irin Rawa Zaitaka A Fili Saita Cika Kanta Tsakar Dare Ana Gobe Sunan Jaririn Atika,bacci Ya Kaurace Mata Fau-fau Bayan ta gama Laluben Mahaukacin Masoyi A Dukkan Kafar Daya Taba Lalubota Bata riskeshi Ba,kama Daga Kiran Waya Akwatin Tura Sako,social Network Da Sauransu Amma Shiru Ba Bu Alamar Shi,da Bacci Ya Kaura Cewa Idanta Sai Gata A Zaune Tanakaranta Wasikar Jaki,kamar Daga Sama Wayarta Tayi Tsuwwa Cikin Razana Da Barin Jiki Ta Wawurota Amma Sai Taga Hafsat Damamaki Ta Daga Da Sauri Ko Sallama Batai Ba Hafsat Lfya? Cikin Doki Ta Ce Lfya Kalau Nakasa Jiran Wayewar Gari Da Tsegumina Meyafaru? Ruma Tatare Ta Cikin Doki Hafsat Ta Ce Sani Munafikine Yasan Abubuwa Dayawa Dangane Da Mutuminnan, Wanne Mutumin? Hafsat Ta Ce Harkin Manta? Mahaukacin Masoyi Mana Sai Ga Ruma A Tsaye Cikin Tsananin Rudani Ta Ambata Da Gaske? Yanzu Dama Canda Sa Hannun Sani Abinda Mutumin Nan Kemin? Hafsa Tatare Ta Cikin Sauri Ko Daya Satin daya Gabata Shima Yasani Ruma Ta Sauke Kakkarfar Ajhyar Zuciya Innalillahi Wa Inna Ilai Hirajiun To Mutum Ne Ko Aljani?Kuma Meye Takamar Sa? Hafsat Na Shirin Amsamata Sani Ya Karbe Wayar Ya Ce Haba Shekara Uku Ba Bu Aure Wasane? Kin Manta Cewa Katon A Addancin Ne Ka Bugowa Amare Waya Tsakar Dare Irin Haka Ko Baki Duba Agogo bane? Su Waye Amaren Waiku? Tafada Cikin Zolaya Tare Da Jin Ciwom Yayankemata Samun Haske Akan Majanuninta Sani Ya Ce Mu Mana! Saida Safe Kafin Ka Ajiye Saika Amsamin Tambayar Danaimata Sarkin Kulle Kullue Kanaganin Ana Neman Kasheni Da Raina Amma Ashe Kaine Mai Bada Gudumawa,saiki Hau Duro Ki Fada Ya Ce Cikin Zolaya Yakashe Wayar Gabadaya,tafada Gado Tana Ambatan Allah Wato Mahaukacin Masoyh Mutum Ne Ba Aljani Kamar Yadda Tayi Tsammani Ba Indai Sani Yasanshi To Ta Tabbata A Duniyar Su Ta Mutane Yake To Amma Tayaya Yakemata Sidda Baru? Tajima Tanakokarin Amsa Tambayar Amma Takasa Saita Hakura Ta Kamo Tashar Wadda Ta Tarar Da Shiryayyun Wasu Tambayoyin Ba Bu Amsa Wato Mene Ne ManuFar Sa Akanta? Yana Da Masaniyar Cewa Ita Sikila Ce? Kamar Amsa Ga Tambayoyinta Sai Ga Wani Kira Daga Hafsa Da Sauri Ta Amsa Ta Ce Yi Saurin Amsamin Kafin Kafin Sani Yadawo,cike Da Zolaya Hafsa Ta Ce Aiyana Kusa Kwalar Rigarsa Naci Ya Sallama Na fada miki Wani Abu Daya Da Zai Kwantar Miki Da Hankali Inajinki, hafsa Tai Kasakasa Da Murya Ta Ce Mahaukacin Masoyi Wato Nazifi Muhammad Mutum Ne Kuma Da Gaske Mahaukacikine A So,yayi Nisa Fiye Da Yadda Kike Tsammani,kuma A Nawa Tsammanin Ba A Ta Ba Sonki Kamarki Haka Ba Rumaisa"u Karyakike Hafsa,ruma Tafada A Fusace Cikin Sauri Maitafe Da Kuka Mai Tuna Baya Ni Ban Taba Wani Kamar Auwal Ba,kuma Ban Yarda Za A Sami Wanda Zaiso Ni Fiye Da Shi Ba Tanason Zarcewa Da Kuka Hafsa Ta Tareta Cikin Rudani Rage Kukan Karki Janyo Hankalin Iyayenki Gobe na Sha Luguden Fada,duk Da Tuntuni Maganar Taje Kunnen Alhji,rumaisa Tanemi Dauke Numfashi Cikin Rudani Amma Kafin Ta Tanka Hafsata Ta Rigata Indai Za A Sami Mai Son Naki Zuciyarki Ta Yarda Da Haka,ba Wai Angama Samun Mai Sonkine Kwata Kwata Ba,kidan Bude Wa Wannan Dan Tahalikin Zuciyarki Kadan Yasami Guri Ina Mai Tabbatarmiki Lokaci Kadan Zai Gawurta Harki Gane Nisan Fifikonsa Da Au... Ke Tafi Can Ruma Tafada A Fusace Ta Kashe Wayar Cikin Zafin Zuciya,kwana Tai Safa Da Marwa Da Rashin Barci,saboda Damuwa Da Rikita Yajanyo Mata Wani Matsananchn Ciwon Kafa Da Misalin Karfe Takwas Na Safiyar Ranar Inda Ciwon Kafa Da Misalin Karfe Takwas Na Safiyar Ranar Inda Ciwan Yadinga Shan Sharafinsa Har Fiye Da Awa Daya Saida Kowa A Gidan Hankalinsa Yatashi Ita Ruma Mai Ciwon Kuka,mairo Mai Tausayi Kuka Hajiya Da Alhji Da Mubarak Ba Bu Wanda Hankalinsa Ke Kwance Har Saida Ciwan Ya Lafa Alhji Yatafi Da Ita Asibiti,daga Asibitin Ne Kuma Taki Yadda Amayarda Ita Gida Saidai Mubarak Yakaita Gidan Suna Kawah Duk Da Kuwa Bata gama Wartsakewa Ba Ana Dai Abinda Yafi Ciwo Ajikinta Shine Zuciyarta Dake neman Gazawa Da Lissafin Mahaukacin Masoyi,hayaniya Bata Barta Ba Dole Atika Ta Waremata Falon Mijinta Ta Kwanta Jefi Jefi Wasu Kanshi Go Su Dubata Balaraba Yayarta Ta Shigo Ta Cemata Wai Wanene Wancen Da Sani Keta Faman Nunawa Mutane A Matsayin Mijinki? Abin 'yar Hakane Ruma Kinyi Miji Ko Albishir Ba Bu? Cikin Rudani Ruma Tatashi Zaune Ban Sanshi Ba nima,balaraba Takalleta Sororo Har Nawasu Lokuta Ta Ce Dagaske? Ruma Takoma A Kasalce Ta Kwanta Balaraba Tamike Cikin Sanyin Jiki Ban So Haka Ba Gaskiya Naso Ace Kinsan Shi,kuma Kece Kika Bashi Damar Yazama Mijinkh Saboda Nutsuwar Sa Da Kalamar Sa Dakuma Abinda Bani Kadai Na Hango Ba Wato Tarin Kaunarki Atare Da Shi,duk Kwakwar Balaraba Takasa Fahimta Abinda Ruma Ke Rayawa Aranta Balaraba Tafara Tfya Tana Cewa Nadanyi Hira Dashi Har Na Fahimce Shi Dan Hadejane,kuma Mazaunin Abuja,yaushe Kakayi Hirar Dashi? Cikin Hanzari Ruma Tafada Tana Dagowa Balaraba Hannu Alamar Dakatar Da Ita Barin Falon,saboda Kasalar Gangar Jikinta Yanzunnan Balaraba Ta Amsa ,au Ance Ma Nasanarmiki Zai Shigo Ya Dubaki,cikin Kuluwa Ruma Ta Amsa Ba Bu Laifi Ta Koma Ta Kwanta,balaraba Ta Fice Daga Falon Batare Da Ta Canka Dalilin Kuluwar Ruma Ba Duk Da Tana Tunanin Ce Wa Marigayi Auwal Ta Tuna Ruma Takasa Cankar Inda Zuciyarta Fada Dokin Gani,fargaba Kojin Kallan Mahaukacin Masoyi? Yau Kuma Yanzu? A Haka Tajiyo Takun Sawaye Tare Da Muryar Sani Yana Karadin Hirar Sa Ta Dora Idanta Kir Akan Kofa Cike Da Dokin Ganin Inta Ga Nazifi Muhammad Kar To Taga Kafar Sa Da Kofato Dan Kuwa Idanta Na Kan Inda Kafafunsa Zasu Duro,sani Ne Yafara Shigowa Cikin Yanayinsa Na Faraa Da Kuzari Kamar Koda Yaushe Nazifi Biye Da Shi Cikin Matsananciyar Kasala Mai Alamun Tasowa Daga Zuciya,ba Kamar Ko Yaushe A Ganin Dataimasa Cikin Kananun Kaya Ba,yau shiGar Manyar Kaya Yayi Na Shadda Ruwan Toka Yar Ciki Da Babbar Riga Bata Damu Da Zolayar Sani Ba Ahankali Ta Dauke Idonta Daga Kallansa Zuwa Wani Wajen ... . Dan Aunty Al-Hada Hada Hausa Book stories GORAN DUMA (P 58) . . Sani Yadubi Ruma Wannan Wace Irin Tarba Ce? Karkuma Ki Kalawa Ciwo Dan Fuskarki Tanuna Da Sauki,takalli Sani Garau Ta Shiga Gyara Mayafi Wanda Ta Lullube Kafafuwanta Dashi Tun Lokacin Dataji Takun Shigowar Su Dahaka Ta Bar Tambayar Sani Tabi Ruwa,hakan Yasa Sani Da Nazif Sukai Murmushi Nazifi Ya Ce Ankuma Ce Tun Tuni Kina Dokin Ganina Ni Ma Ban Zaci Wannan Tarbar Zansamu Daga Gareki Ba Sai Yanzu Ta Fahimci Kwakwalwarta Ta Tsaya, sani yatafi yabar Ruma da nazifi alamu yanuna a tsorace take tundaga fitar sani daga falon nazifi ya mike cikin kwarin guiwa a tsorace cikin zafin nama sai gata a zaune tana kallon kofar cikin Gyara wuyar Riga yakaraso tsakiyar falon ya zauna kan teburin dake girke a tsakiyar dakin Wanda ya basu Damar kallon juna ruma cikin tsananin so da farin cikin ganin masoyin Ruma tafara kauda kai cikin cin magani yace najima INA kaucewa haduwa dake idan kina cikin rudu ALLAH bai nufa ba amma dai nayi nasara ba wani na ya rudaki ba nida kaina na rudaki yatsayar da maganar saboda yaga bakinta na motsi alamar zatai magana amma yana rufe baki sai yaga ta hadiye yaya jiki? Nanma kallonsa kawai tayi ta kauda kai yace nasan abinda yajanyo fushinnan lokacin da kika so ganina naki ki ganni ba fushi ya dace kiyi ba Ruma kamata yai kinemi ba'asi cikin karkarwar murya tace wa yace maka inason ganinka? kaitsaye ya amsa cikin daga gira kintashi daga kano takanas zuwa abuja din kiganni cikin tilastawa kai wani fushin face duk yafarune cikin kuskure Yanzu najanye saboda haka kana iya tafiyarka idan kazone domin na ganka takaj da raunanniyar murya yace badon kiganni nazoba nine nazo don na ganki domin nikadai kesonki nakuma cika son kai Dan banbaki damar kisoni ba a tsammanina nawa son ya wadatar tace masa wannan bayanin naka sunyi hanzari domin kai yakamata nafara sani ba kalaman soyayyarka ba amma idan kagama boye boyen kenan nagama yafada da sauri shiyasa nacemiki nafiye son kai na boye mini kaina yayinda na zurfafa a sonki har nakai bigiren da raina kejin in an raba shi da sonki bazai iya cigaba da nunfasawa ba nantake kwalla tacika mata ido domin maganarsa tatuno mata da auwal babu alamun shakku ta amsa masa rashin masoyi baya kisa dayanayi dabaka ganni a Raye ba har ka soni. nazifi ya dauke wuta dad fuskarsa da gangar jikinsa sun nuna damuwa kishi yajima cikin kallon shimfidar falon kamar yadda taciga ba da kallon talabijin zuciyarta a auwal batare da nadamar maganar dataiba said a ta hangi inuwar nazifi a tsaye tajuyo ta dubeshi lokacin yakusa kofar fita falon tagama yanke kaunar sai fice baice komaiba amma sai ya jiyo a sanyaye yace nasan ba zafafa cimma burina ne yasanya nijin cewa ALLAH ya karbi ran Auwal ya barmin me ba don nafishi cancantane.na fishi sonki na kuma fishi cancantar zama mijinki RUMAISA'U sikila..,. watakila sai lokaci yayi zaki fahimci hakan tai shuru tana kallonsa da alama kamar laluben ta inda yafi Auwal cancanta take zanwuce masaukina yanzu badon zantakura mikaba danazo gidan yau da dare gobe don inanan kano har safiyar jibi itadai kam hawaye take face masa jimana tareda karfin halin mikewa tsaye yajuyo ya kalleta tadanyi kamar xatafadi a kokarinta na gyara tsayuwa da sauri yadaga mata hannu , a, ah koma ki zauna ta koma ta xauna tace maasa kafin goben inasan sanin kai waye I na tsammanin a duniya babu abinda ya shige min gaba kamar son sanin amsar wannan tambayar akwai wani suna dazan sake amsawa ne banda MAHAUKACIN MASOYI? wannan sanin yakamata ki rike ba na tsammanin zakisami Wanda yafishi da gaske ne ni MAHAUKACIN sonkine ba wannan nake tambayaba ai tundazu akan haka muke magana tambayata anan itace ta wace hanyar kake shiga zuciyata? tawace idon kake kaina hatta a lokutan da nakasance nesa da idon kowa yakada kai yana dariya au hakanefa duk naji zarge zargen dakikemin wajen sani zargi ne wato ba gaskiya bane? ta tambaya cike da mamaki kwarai da gaske ya amsamata shikenan saika tabbatarmin da gaskiyar yanzu. ya CE a irin wannan lokaci n dakika cakuda min zuciyata da takaici ? INA girmama Auwal don darajar zuciyarki tasoshi ni kuma masoyin kine ke da komanki amma girmamawar taki shafe kishina ya fice ya var falon tunbayan fitar MAHAUKACIN MASOYI Gidan sunan yaimata zafi tatashi tashiga cikin jamaa inda ake ta kayakaya murna da daukan hotuna kozata manta amma hotunan MAHAUKACIN MASOYI a cikin zuciyarta musamman daidai lokacin da yake cewa NASAN BA ZAFAFA CIMMA BURINE YA SANYA NAJI CEWA ALLAH YA KARBI RAN Auwal YABAR MINKE BA DON NAFISHI CANCANTANE NAFISHI sonki KUMA NAFISHI CANCANTAR ZAMOWA MIJINKI RUMAISAU sickle INA GIRMAMA Auwal DON DARAJAR ZUCIYARKI TASOSHI NI KUMA MASOYINKINE KE DA KOMANKI AMMA GIRMAMAWARKI TAKI SHAFE KISHINA wadannan zantukannasa sunki bacewa daga zuciyarta da alama duminsu ne yake ta faman kyankya sar son ubangidansu wato MAHAUKACIN MASOYI a kirjinta ta yarda ya iya so tunda ya iya sonta ita da son dataiwa waninsa AUWAL kuma kishinsa ya na nan daram amma baya runtse masa I do ya ya mayar masa da sonta kiyayya ,tabbas ko yayane zai iya zama waziri a fadar so da kaunarta yayinda auwal yake sarkin sarakuna , ##**************** Dan rumaisau yushau ya isa gidan sunan da gamma da sunan wai yaje daukar sumoli wadda ta mayar da kanta amarar biki da karfi da yaji yayi katari an kwakolo rumaisau da kyar zuwa wajen daukar hotuna a harabar gidan sai gashi dayin abinda babu shi a cikin tsarinsa wato shiga sabgar bikin mata ya rungume hannu ya tsaya kusa da kanin mijin atika yana satar karewa Ruma kallo Wanda kaf Cikim matan dasukazo sunan sinfita daukan ado amma a haka it'a kadai kallon ta ke buga masa zuciya musamman

Chapter 18 of 21