Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
akwai masu pada da gasken kuma suyi a aikace amma daga matar har mijin basu kula da hatsarin da suke ciki na gaza sauke hakkokin juna lokacin da suka ki daukar mataki akan kalmar ba da yake tapi ganin laipin matar , ta tashi nata sharhin sai tace. ' mata pa akwai kwakwazon korapi, tare da gaza hakuri in an kwatanta musu irin sa na tabbatar duk matar da mijinta yace mata don 'yayana nake zaune dake. Mawuyacin abu ne wannan auren nasu ya dore saboda yadda zata tattara kauna ta yanke masa. Ta pito ta cigaba da bun ragowar labarun da marubuta suka aiko, tayi tsokaci (comment) a wanda take muradi tayi jinjina (like) a wadanda suka burgeta. Ranta ya para haske kirjinta ya dan samu sarari dama zan kapin mahaukacin masori ba karamin kaye da sanda nishadi duniar marubuta ke bata ba. Ta bar nan ta tapi dandalin masorya jaridar Aminiya, zababbiyar jaridarta kenan tun kapin ta zama marubuyarsu saboda haka ita ma wata ginshikice a padada mata zucia, jakar sakonninta (inbox) ya rika kuka ta duba akwai wulgawar sakonni kusan goma a ciki. Kamar zata share su ba tare data duba ko daya ba kasanwewarta marubucia bugu da kari kuma mace wada bata tsallake neman maganar maza marasa mapadi a fb, amma da ta tuna kila akwai wadanda zasu iya dangantarta a masu sakon yan uwa ko abokan aiki da kawaye sai ta tapi inboz din kamar yadda tayi tsammani ta tarar sakon yayarta Balaraba, wadda ke paman yi mata mitar taje Abuja taki zuwa gidan ta kuma ta tsiri wata muguwar dabi'a ta kashe wayoyi , ta amsa mata da ban hakuri da alkwararin share mata hawaye, tana barin Balaraba taci karo da sabon sakon Mahaukacin masoyi Username dinsa kenan Mahaukacin masoyi. Zuciyarta ta para bugawa pat-pat amma da karpin hali ko karanta sakon batayi ba ta tapi bincike bangonsa (wall) abun da ta tarar bazai mata ampanin komai ba sabon acct ne haihuwar shekaran jiya, babu komai a cikinsa na dorarwa, adireshin ma banda suna babu komai bude, bata tsawaita wani tunani ba ta toshe shi yadda bazai sake sa ido a kanta a fb ba cikin jin karpin gwuiwar abun da tayi taci gaba da harkokinta tsawan awa daya. Tana shirin sauka saboda lokacin baccinta yayi ta koma inbox saboda tunanin kar ta bar sakon da suka kamata sai kuwa taci karo da sabon mahaukacin masoyi mai karin I a karshe, wato mahaukacin masoyii shaidar ya harbo jirginta ya kuma dana mata wani tarkon, na para mamakin yadda kike son bude kwanji ki guje min duk da ban bude nawa na para sonki da yanke kaunar rabuwa dake ta dalilin wani abu ne mai sauki na. Idona a kanki yake Rumaisau ki daina wahalar da kanki da tsammanin zaki iya kubce min, wannan wani irin zalunci ne don Allah? Kin kashe wayoyi saboda ni, na share wannan takaicin kin shigo dandalin sada zumunta na cika da doki na biyo ki amma kawai dan rashin adalci sai ki kulle tsakanina dake? Ki daina tsammanin zan yarda da wannan.. Bata ko karasa karanta sakon ba tayi baya a guje ta pice daga fb din sannan ta kashe na'urar gaba daya ta bige da rapka tagumi. Ta tabbatar da kanta in ta kai karshen sakon kila mahaukacin masoyi ya pada mata kalar kayan da ke jikinta da irin yanayin zaman ta nan rudanin a yanzu ne ta para ji a ranta ya kamata ta san waye mahaukacin masoyi. 31/1/2013 tana zaune a gida dab da azahar mubarak autan hajia ya kirata a waya '' anti kin pita binciken da kika ce zaki? A tausashe tace A,a mubarak, wani abu ya paru ne? Ya amsa a ladabce yana daria . Babu abun da ya paru dama neman alparma zanyi ki karaso nan B.U.K ki dauke ni na bada aron mashin dina kin san kuma hana goyon nan ya janyo karancin abin hawa. Tayi yar daria tace ban pita ba amma bari nazo na dauke ka yace godia nake anti amma dai a dan gyara laipin aron babur din da na bayar. Tace masa karka damu. Cikin sauri ta debi wayoyinta da tun hantsi ta kunna take jiran sakon mahaukacin masoyi wanda tayiwa tanade tanade marasa lissapi bai kira din ba, har ta sallaci azahar ta dawo da tsakkamin zata tarar da sakon sa nan ma shiru, har zuwa lokacin da mubarak ya nemi agajinta. Hajia taimaka ki ara min mota in dauko mubarak. Ta samu hajia a palonta ta pada mata haka tana yar daria hajia tayi mata kallon tsab ta ce a.a kiyi daria da kyau. Kina pama da kanki zaki je wani dauko mubarak? Ina babur din sa? Kai tsaye ta amsa yayi paci yace min ya rasa mai liki saboda matsalar masu gyaran sannan ga kwarancin abun hawa a gari, shine sai ke zaki dauko shi? Ta wuce kan talabijin ta dauko makullun motar tana cewa to yaya za ayi hajia? Nima ina son ganin wulgawarsa a gidan tun sape bakina ke tsami ba abokin hira. Hajia tayi daria tace Allah ya bada sa'a Allah ya kiyaye hanya. Tana picewa ta amsa Aamiin hajia ta sauke kai tana girgizawa xuciyarta cike da tausayin Rumaisau tattausar mace mai kirkin gaske amma Allah Ya kaddaro rayuwarta cikin jarrabawarSa. Bata taba jin wanda ya zauna da Rumaisau ya padi rashin kirkinta ba duk kuwa wanda yace batada kirki da zarar ka dube shi zaka ga rashin kirki a puskar sa. Tun kapin ta shiga makarantar tayi kiransa a waya Mubarak karpa na shigo ka cika min mota da abokanka inba haka na karka kuma taso ni zuwa daukar ka. Yana daria ya amsa na san da haka shi yasa ma na ware gepe. Tace dashi cikin daria aha! Ka shirya na shigo. Yace amma akwai yan uwan ki mata nasan... Yaki karasawa yana daria ita ma tayi dariyar tace babu matsala. Tana shiga ta ciko mota da Mubarak da abokan karatunsa mata, sai wani nataccen abokinsa shau'aibu da ya matsa sai an dauke shi har yana cewa Rumaisau, anti in ma ba zaki dauke ni ba sai na daura dankwali kona yapa gyale, sai in ara cikin yan matan nan bazaki rasa mai spare a jaka ba. Dole Rumaisau ta yi daria tace mai yayi zapi? Shigo mu tapi. Ta hada su a gaba shi da Mubarak ta tashi motar yayinda wasu tunanuwa masu nauyi suka wulga a zuciyarta, tunanin da ke pawar sa ta kukan jini inda anayi duk da ta san akan su tana kukan da yapi jini ciwo. Haka ta tashi motar ta pice a guje tana satar kallon wurare a makarantar, wadda ta kasa hadiye wa sai da ta para zubar da hawaye, sannan ne mubarak ya tuno katon kuren da ya tapka, yayi saurin dora hannu aka ya kame baki yana satar kallon titi cike da nadama. Ba yau ya para gayyato rumaisau tazo daukarsa ba amma yana sane da yadda matsayar dalibai jiran shigowa bus a nan makarantar ke zama wani katon abun pami a raunin Rumaisau, dan haka sai ya kan yi gaba su hadu a hanya ta dauke shi su pice ko zatayi hawaye kadan ne. Saboda haka ne ita da Mubarak suka yi dip a motar, matan baya keta hiranrsu , shu'aibu da ya rasa abokin hira yake saka musu baki, Mubarakk ya rasa bakin bawa Rumaisau hakuri ita kuma ta kasa daina zubar da hawaye har suka pito makarantar suka hau babban titi. Mubarak dubo min gilas dina a jaka. Rumaisau ta pada dan tsananin kaunar ta manta abin dake sata hawaye da kunan zucia. Cikin doki mubarak ya dauko jakarta yana cewa inaga dai anti gayyatar karshe na miki ta zuwa ki dauke ni indai ranmu zai dinga baci haka ta karbi gilas din tana dariar yake tace ko baka gayyato ni ba mubarak inna surantawa kaina makarantar nan inayin abun daya pi haka, gara ma ka dinga gayyato min ina zuwa kila na saba da kallonta gwauruwar ta... Ta kasa ci gaba da magana saboda kukan da ya toshe mata makogwaro ta bige da bude gilas kawai ta saka sannan ta hadiye kukan. Motar tayi tsit har suka kawo mahadar tituna na kabugam yanzu ta hakura da kukan duk da karpin hatsi tasa masa amma dai yabi umarninta ne da taimakon hango wasu mata biyu datayi suna bara a tsakanin motoci. Matan ba wai tsoppin almajirai da ido ya saba gani ba, a'a matasan mata yan shekaru ashirin da biyar zuwa talatin kuma abun da yapi shayar da takaici shine da yanayi irin na mazan da sukayi kaurin suna wajen hawa gajimare ( shaye-shaye) bata magana cika jakar mamaki da alhininta ba sai ga su gabanta dayar zuro hannu ta rike sitiyari tana layi, Hajia ki taimake ni kamar yadda Ubangiji Ya miki sutura ki bani na siye abinci da dan hayaki... Dayar kuma ta cape da cewa bata wulga ta kantaba... Kina hada mutum da Allah baya nupin an rasa yadda za ayi in motar nan cancakar naso sacewa na rantse yanzu zan muku rupa ido in dauke shi.. Ko ba haka ba? Suka dubi juna ita sa su Mubarak zai yi magana ta hana shi dayi masa inkiyar ya bude mata jaka amma sai ya kankame jakar ya juya keya ta pahimci manuparsa saboda jaka tayi yar daria ta dube su da kyau tace aini ma da na ganku murna nayi da Allah ko yar naira shirin ce ku bani goro zanci. Nan da nan kamar walkiya suka bace daga gare ta, duk motar kowa ya rude da daria lokacin da suka sami hannu suka wuce. Shu'aibu yace anti yaya akayi kika san mashayan nan ba sa son a roke su kudi? Tana daria tace ko daya, na san wanzami baya son jarpa, amma dai nayi mamaki in labari aka bani shayeshayen mata ya kai matakin pito da su kwararo da dabi'u irin na yan daba, Wallahi karyatawa zanyi.. Amma sai idona yaga zahiri.. Shu'aibu ya tareta da padin anti ai gara wadannan da ganinsu kin san dama sun gagari iyayen su ne akwai wata budurwa a anguwar mu bazan iya kirga sau nawa na ganta a make ba, na sha kamata na kai ta gidan yayata a tsare ta yapi a kirga, ina mata gudun batagari su cimma wata mummunar manuparsu akanta. '' Innalillahi wa innan ilaihi raji'un. Rumaisau ta pada cikin kololuwan bayyana takaici da alhininta sannan ta dubu mubarak tace mubarak ko akan shaye shayen mata zanyi batuna a wannan watan ne.? Good! Wannan zai kayatar kuma zai padakar. Zaka taimakeni da bincike kenan? Ya amsa mata da karpapawa, babu matsala yau zuwa gobe ina cikin yanci. Ko baka cikin yanci ma naga ai kana dagawa kayi aikina. Ta pada ba tare da ta dube shiba da yayi dan nazarinta sai yayi daria yace Allah ya sa ban kauce hanya nayi kuskure a magana ta ba. Tayi daria kawai, shuaibu yace ka kawota gidanmu taga yarinyar danayi maka maganarta idan tana da bukata. Cikin sauri Rumaisau tace mai zai hana? Idan babu damuwa muje gida kuci abinci sai mu pito tare. Ok babu matsala inji shuaibu, mubarak ya dora da cewa sai kuma ina? Tace da sape ka raka ni freedom nayi cigiyar hajia Maryam (Maryam Babban suna, ina gaida duk mai suwa Maryam , (Dan Aunty) ) 1/2/2013 ta wayi garin ranar yau da kumajin datajima bata tabadarwa kanta shi ba har ga Allah tanaji a ranta sunyi hannun riga da Mahaukacin masoryi tunda dai gashi kwana 2 kenan babu sakonsa a waya saboda shi ma ta kara lokutan hawa fb amma ya bacewa ganinta wannan ba karamin dadi ya yiwa ranta ba ta shirya karasa watsar da shi da tunanin yadda zata gungura rogowar tsumman rayuwarta data ke wa take gawa taki rami . Ba kamar yadda ta so ba wato zuwa freedom tare da mubarak sai Alhj ya bashi wani aiki na wakiltarsa daurin aure garin katsina, a ranar juma'ar da jiran bikin nadin sarauta a washegari asabar, wannan yasa ita kadai taje freedom bayan an sauko masallaci. Bata sami ganin hajia Maryam ba kan abin da yakai ta, sai dai ta samu garantin ranar samunta, bata dawo haka ba sai da ta shiga sashin labarai neman ji daga wanda ya kawo wani rahoto game da yadda wata yar maye ta dabawa wani matsashi wuka. A ranar yau Rumaisau ta kara godewa Ubangiji da Ya jukuntota a mai son bincike dayin rubutu game da abubuwan da zasu ampani al'umma, saboda yadda take haduwa da ayoyinsa iri iri masu kara mata tsoron Allah da goge maSa, da kuma masu sanyata gudun yi maSa butulci da daukar sabonSa ba a bakin komai ba. Tana freedom radio akayi sallar la'asar dan haka kapin ta pita sai da tayi alwala ta shiga masallacin mata tayi sallah. Bayan ta idar ta bude jaka ta hau goge gogen puska da gyara daurin kallabi ta gama tana mayar da kayan jaka taken shigowar sako ya kasa a wayarta,.da karpin hali irin na dan daudun daya kamo kadangare ta capko wayar ta para duba sakon. ''Rumaisau ban kasance ma'abocin sauraron wakoki ba amma abun mamaki wata waka ce yanzu take gilmawa kunnena wadda ta motsa min dubun taki kaunar a makoshi na, kin san wakar? Itace wakar YAR MAYE. Wakar ta shige ni! Ta sani tsausayin kaina piye da tausayin matan dake je pa kansu a haln shaye-shaye, saboda na san giyar kaunarki ta make ni piye da yadda ko wanne irin kayan maye ke make ma'abotansa. Idan kin taba nazari akan yan maye ki zace ni da kalar tsausayi piye da yadda kika san su, mahaukacin masoyi. Tayi iyakar kokarinta wajen hadiye rudaninta saboda wasu mata biyu dake salla gepenta kuma wannan dakewar tata xe ta bata samar yin wani tunani na zaton duk yadda akayi mahaukacin masoyi akwai kapar da yake samun labaran halin da take ciki ya turo sakonsa a kansa in dai shi ba junnu bane. Bata tsawaita tunani ba bare ta samo abun da zai kore mata wanda ya gaskata ta para latsa wayarta ta kira Mubarak. Mubarak wa ka sanarwa cewa zanyi rubutu akan masu shayeshaye kuma waka sanarwa zuwa na freedom? Mubatar ya jima yana jan numpashi kapin ya amsa mata anya nayi maganar da wani? Kusan mapa Wallahi na manta maganar tun jiya da muka je unguwar su Shuaibu. Tayi ajiyar zucia ita ma ta jima tana jan numpashi sannan tace Ina shuaibu? Yace munyi waya dashi yau da sape yake cemin yana kwance a gida saboda ya gamu da masassara (zazzabi), wani abu ne ya paru? Muryar Rumaisau na rawa tayi saurin girgiza kai kamar yana gabanta a'a babu komai kanajin babu wanda zai iya sanina wajen shuaibu har ya bashi batun ina bincike akan mashayan mata? Nan ma Mubarak ya ja pasali sannan ya amsa anya ina tantama wai me ya paru ne? Tayi dariyar karpin hali tace ok babu komai yaya katsinan? Ina patan kana shirin ganin gari? Mubarak ba dan ransa ya so ba ya yarda da wannan ninkuwa bai bai din da tayi masa ya amsa a sake sukayi sallama suka ajiye wayoyi. Tana daukar mota ta pigeta sai Dawaki road gidan Hafsat yayar Mubarak, wadda take tsararta kuma tare ma sukayi yammatancin su . Hafsat da tsohon cikinta ta karbeta cike da mamaki . Rumaisau bata irin wannan ziyarar ta bazata to yaushe ma ta ke son zuwa gidanta duk irin shakuwar da sukayi? Suka zauna apalo Hafsat ta sa aka cikata da kayan sanyi amma ko kallon inda suke Rumaisau taki yi. Tayi nazarin agogo sannan ta sauke ganinta akan Hafsat tana padin Hapsat wata almara ke paruwa dani, shine na daukota na kawo miki mu tattauna akanta, a gaggauce saboda kin san babu lokaci. Hapsar ta gyara zama idonta akan Rumaisau sai dai bata tanka ba. Ta budo sakonnin mahaukacin masoyi tun daga parko tana mata bayani tare da yanayin da sakonnin ke samun ta, har Rumaisau ta dire wa hapsar ta dauki abin, dan daria kawai ta ke tuntsira mata sai da ta ga ranta ya baci ne ma sannan ta dawo ta saurare ta . To wai ke me kike zato? Rumaisau ta dan harare ta. Idan na zata mai zai kawo ni gidan ki? Da ba sai nayi zamana nayi hukunci da zatona ba? Hapsat na kunshe baki tace Allah Ya baki hakuri amma ni nayi zargin ko a makaranta shapinki na jarida ne wani ya boye yake wasa da hankalinki haka? Rumaisa tayi saurin girgiza kai tace kuma a lambobin wayata wadda bana hulda da kowa sai dangina salonninsa na parko pa a layina dan alkawari yayi su layin dako layika na cin amana shi dai bai kamata yaci ba, hapsat ma bata son tsawaita wannan maganar akan layi dan ta san makoma abin. Saboda haka tayi saurin tare Rumaisau da cewa anya kuwa ba Yusha'u bane? sai kawai Rumaisau tayi zuru tana kallon haprsat kamar wadda hankalinta baya jikinta tace ko a tatsunia bai kamata kiyi zaton yaya Yushau ba, me ya ani da yaya Yushau zai bata lokacinsa a kaina? Ko kin manta ne ? Ai ko a layin mutane nake zaton mai turo min sako bai kamata ki kawo yaya yshau ba. Hapasar ta rausaya kai cikin sallamawa tace haka ne wai dama da ake zargin mai wayar a cikin dangi.. A dan kupule Rumaisau tace ko mun rage mu biyu daga ni sai shi ya kamata in pita waje neman mai turo min sako. Hapsat tayi shiru saboda rashin abun cewa, kamar amsa ga abin da sukayiwa tagumi suna tantama sai ga taken shigowar sakon mahaukacin masoyi.. Rumaisau na dubawa ta gashi ne, sai ta mikawa hapsat wayar ba tare data karanta ba. Ta mike da hannu dunkule tana dukan hannun hagu tare da pareti a palon. ''Rumaisau akace mutun mutun gida ne da rabin mutun da wanda ba komai ba, wanda yake mutun shine mai yin shawara da al'amuransa, kuma mai ra ayin madaidaici wanda yake rabin mutun shine mai shawara amma bashi da madaidaicin raayi ko kuma yana da madaidaicin raayi amma ba shawara, wanda yake ba komai ba shine mara shawara, kuma mara raayi. Wani babban sahabi yace mana ''kuyi shawara da mutanen kirki na gama yi miki sanin raayi madaidaici wato tuni na san cikar rabautarki ashe ke guda ce naji a raina kina son kiyi shawara akan harkar soyayyata haka ne? Ina sauraron abunda hukunci zai yanke min, mahaukacin masoyi. A pili Hapsat ta karanto sakon, zuciyarta na harbawa , hannunta sai karkarwa yake ... . GORAN DUMA 4. . . a pili Hafasar ta karanto sakon zuciyarta na harbawa, hannunta sai karkarwa yake idon ta cikin na Rumaisau bakin ta na rawa tace da wa kikayi zancen zaki zo neman shawara a gurina? Babu tsoro a puskar Rumaisau ta kebe baki tace da harshena dai ban pitar da sautin zan nemi shawarar wani ba dazun nan a freedom na zanta da zucia ta ina pitowa kuma kai tsaye na nupo gidan ki. Mun shiga uku, hapsat ta pada tare da wurgar da wayar a dan tsorace cikin jikinta yasa da sauri Rumaisau ta isa gareta ta ruko kapadarta tana daria matsalata dake tsoro Wallahi, baki san babu abin da zai iya samun dan Adam ba sai abin da Ubangiji Ya kaddaro maka ba? Bana tsammanin wani katon Al'amari cikin sakonnin mahaukacin masoyi, kawai dai na gajia da bacin lokataina da tunanina ne wajen wassapa shi yada sakonninsa. Hapsat tayi kasake sai nan take ta dawo hakalinta ta mika hannu ta dauki wayar ta sake duba lambar, nan take ta dannan maballin kira, ta gama bincike dab da zata shiga sai ta katse, kusan sau goma tana gwadawa hakan na paruwa a karshe ta kwape lambar a wayarta ta jira nan ma hakance ta paru suka dubi juna kowacce puskarta da jarumta tace ina horonmu da addua da mayar da lamari ga Allah Rumaisau karmu raya wani mugun abu a cikin sakonnin nan mu kwantar da hankali mu kuma dauke su ba komai ba ki bani kwanaki biyu nayi wani dan bincike idan kin amince zan sanar da sani. Rumaisau tayi saurin girgiza kai ban amince sani yaji ba kin san sanida surutu maganar tana iya zuwa kunnen su hajia ba tare da mun shirya mata ba, cikin saduda hapsat tace hakane amma dai surutun sani mai maana ce ki daina suppanta shi da wani aku... Ta kare da zolaya duk kuma suka yi daria suna pitowa harabar gidan suka ci karo da sani mai gai ya wangale masa kopa ya shigo. Suka tsaya jikin motar da Rumaisau tazo da ita suna jiran karasowar sani . rumaisau ta rungume hannu a kirji tayi puska ma'ana ta shiryawa shegantakar da sani mijin hapsat zai zo yayi mata, tunda ya saba, lallai kuwa idon masu hidima da ke karakaimar yi masa maraba da xuwa bai tsure shi ya kasa girgije su ya nupi su kai tsaye ba. Hapsat na dan boye puska tana satar daria tayi masa sannu da zuwa hankalinsa na kan rumaisau yana mata kallon sama da kasa a karshe yace a'a yau mutanen zuhdu ne suka tuno da mu? Ta tuno da ita dai Allah Ya sani ba dan kai nazo ba. Ta tare shi tana nuna masa hanyar wucewa ya tuntsire da daria yace matsalata dake kenan sai ki dinga dagewa sai kinyi pada kuma da yake ba dabiarki bane sai ba yayi miki kyau har tapia ke nan. Bazaki zauna mu gaisa ba gashi naga puskarki da abin karatu... Wannan kalaman nasa suka sata daria kawai ta bude kopar mota ta shige suna dan barkwanci har ta pice... Ta tattara duk wata sabga da zata iya dugunzuma mata hankali a ratuwarta ta watsar, in sako ya shigo wayarta ta daina budo shi inta hau fb ta share inboz sai komai nata ya dawo dadai. Sati daya a tsakani sai mahaukacin masoyi ya dawo kwado mata kira a waya da parko share kiran ta dingayi amma daga bisani sai ta yanke shawarar ta daga wayar suyi ta ta kare ita da mai kiran, amma idan ta daga sai iska shuuuu... Babu motsin murya sunyi haka ya zarce sau goma a karshe kawai sai tayi blockin din layin sa gaba daya a wayoyin ta ba tare da jin cewa zata yi nadama ko kaico ba. Sati na biyu akayi rasuwa a kauyen su Rogo hajia nada ganawa da liyitanta a Egypt daidai wannan lokacin bisa larurar ciwon sugar da take pama dashi, alh kuma tare dasu tapi saboda haka ta wakilta Rumaisau taje gaisuwar. 16/02/2013 tana zaune cikin yan uwa a gidan gaisuwar har bayan sallar azahar sannan ta tapi gidan Goggonta karpe uku take jira ta karasa ta dauko hanyar dawowa gida saboda haka ta kimtsa komai tana zaune kawai. Goggonta ta shigo tana mata wani irin kallo sannan tace Yushau bai san ke hajia ta turo ba sai yanzun nan nake pada masa. Rumaisau ta daidaita maganae goggo a memory dinta amma ta rasa gane ta inda maganar ko wani abu a cikin ta zai ampaneta, saboda haka ta hadiye a sanyaye tace ashe yazo? Goggon ta amsa mata eh tun sape yana nan ai ina tsammamin ma ya riga ki zuwa. A dai ci gana da hakuri Ubangiji Yana son bayinSa masu hakuri, rayuwar dai kina ganin yadda take hutsirewa kana tsaka da kara mata burika, wadanda kake kokaawar imma a sannu ko wadanda kake son sawa karpi rauwar Garbati nan ta isa mutun aya Ruma, shekaru goma sha shidda bai leko gidan ba yana can kudu da kyar akayi masa kiranye ya dawo gida anata parin ciki da murna har anyi masa matar aure kinga duka duka bai hada sati 2 da dawowarba Allah Ya karbi abinSa , ai wannan gudun dunia wajibi ga mai son cikawa da imani rumaisau jinta kawai take ta san waazi take mata abin da take waazi a kansa ma ta kasa tantancewa musamman da yake akwai batun yushau da aka yi shimpidar waazin a kasan ta kasa gane me goggo take son nusassheta akan hakuri da yushau, wanne tawaye take da bukatar ta yi hakri akan sa? Amma dai da yake baya da jayayya sai ta rausaya kai tace Allah Ya samu cika da imani. Goggo na amsawa hakan yayi dadai da shigowar Yushau cikin daikin puskar Rumaisau babu yabo ko pallasa ta taishe shi sannan ta mayar da hankali akan wayarta, tana dube dube goggo ta sa musu ido a pakaice yushau na satar kallon rumaisau yace nansan bada mota kika zo ba ko? Ta dago sarato tana kallon sa amma yanayin puskar hakurinta ta hana a gane yadda ta karbi batun muryarta na rawa tace hakane motar haya na hawo. Yadanyi dariar da yake tunanin zata sami matsuginni a zuciyarta yace aina sanki da tsoron tukin daguwar hanya. Ta share daria da batun nasa hanyar muyar da hankali a wayar ta tana nazarin sakonnin makaranta rubutun ta a jaridar Aminiya, karpe nawa zaki tapi? Ya pada kamar bai damu da yadda ta share shi ba ta dago agogon hannunta ta duba ba tare da ta bude shi ba tace ina jiran karpe uku ta karasa ne sai na komai shima ya duba agogon yana padin nima ita nake jira sai mu koma tare ta danyi kasake bukatar tasa na mata kururuwa a kwakwalwa sai pamar kwakwalwar cetayi aikin da zuciayar nata ta kasa, wato ta girgiza kai tace nayi alkawari da dan mashin zai zo ya kaini tasha, kai tsaye ya amsa mata sai na biki na dauke ki. Bai jira cwarta ba ya pice abinsa. Sararo ta hada binsa da kallo da sauraron wayarta mai take shigowar sakon murya, sai da ya pice ta sauke idon akan wayarta cike da rudani da mamaki shakarunta nawa da yankewar samun sakon murya a waya.? A lokacin da take samun sakon wayar ma daga wani muhimmin mutun ne a duniyarta. Wasa! Tana budewa sai ga lambar mahaukacin masoyi kawia sai ta mike ba tare data shawarci kanta ba , goggo ta dan bita da kallo ita kuma ta tsawaita muryarta tace goggo yau na manta banje hawa dutse ba, mintina ashirin bari naje na dawo. Goggo da yake ta san rumaisau da maganar son hawa dutse bata zargi komai a ranta bam ta santa duk sanda tazo ta kan ware lokaci ta shiga daji ta hau dutde shi yasa yanzu ta amsa mata da cewa ai da yake ba zuwan nustuwa yau kikayi ba kiyi sauri to ki dawo kije gidan gausuwar kizo ku tapi kar ya gaji da tsumayinki ya tapi. Ga yamma ga wahalar mota kinga babu dadi. Rumaisau na kokarin picewa tace idan ya gaji da tsumayi kawai yayi tapiyarsa dama ina da ajandar kwana idan hali yayi. Goggo bata samu amsa mata ba ta kule. Ba zata iya tantance yadda akayi ba ta isa wajen dutsen ba, ta sulale a sanyaye ta haye samansa sannan kamar yadda ta saba ta siga juyawa a hankali tana hango karshen gari (harizone ) wannan aladar muhimmiyar gaske ce a rayuwarta dan ta kan kara mata imani da tsoron Allah wanda Ya halincci wannan makekiyar duniyar da

Chapter 2 of 21