Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
za a yi ta je asibiti kasancewar sickler kullum cikin na'kuda suke, na ce ta sanar da mijinta da kanta, sai ta nuna min tana jin nauyi. Ni na kira Yusha'u a waya na fada masa, na kuma sanar da shi dukkan hatsarin da ke tattare da rashin zuwanta asibiti ya amsa min za a je, amma har tsawon sati kusan uku ba a je asibitin ba. Rannan na kirata ina bincikar lafiyarta, sai tana kuka ta sanar min a halin yanzu ma jininta ya yi 'karanci. Na kuma kiran Yusha'u na gargade shi. Yau kwana uku ke nan jiya kwana biyu wannan hatsarin ya faru, Yusha'u bai nemi asibiti ba ni ban san wanne irin sakaci ba ne wannan". . To zamu shiga hutun sallah daga yau, sai kuma bayan sati biyu. Dan Aunty.GORAN DUMA (P 35) . . Ran kowa a dakin ya 6aci, musamman Alhaji da Hajiya, Alhaji ya yi kwafa cike da takaici da 'kunar rai kamar ya hadiye zuciya, ya ce. "Sakaci ko ganganci, 'kila so ya ke ya kasheta tunda na aura masa ita bisa tilas". Dannewa kawai Mummy ta yi ta amsa cikin sanyin murya. "Alhaji maganar duk ba ta yi zafin haka ba, amma dan kyautawa gaskiya Yusha'u ba ka kyauta ba. Ba a kan wannan lamarin ba Yusha'u na sha sanar da kai irin hatsarin da yarinyar nan ke ciki, dan na yi wasa da hankalinka ba zan dinga fada maka 'karya ba. Yarinyar nan na bukatar taimako ba na komai ba na taya ta kiwon kar ciwonta ya tashi. Ko ba 'yar uwarka ba ce ba kuma matarka ba ce ai ka yi mata taimakon musulunci, wanda ya hori musulmai da taikamon juna da yaye damuwar juna". SABODA tsabar takaici Yusha'u kasa magana ya yi, sai ya yi kwafa kawai ya kawar da kai, Hajiya ce ma ta cika shi da kallon tuhuma, Hafsat kuma take satar harararsa, dan ita kadai ta san wanne irin zama Yusha'u ya ke da Rumasa'u, gidan Rumaisa'u gidan zuwanta ne kwarai da gaske, tana kallon rashin shakuwar dake tsakaninsu tana kuma kallon yadda Rumasa'u ta ke fama da dawainiyar aiki tana da lafiya ko ba ta da ita, shi babu abin da ya shafe shi. Bayan wannan ta kula da jarabar ma'kon da Yusha'u ke yi ko a wajen abinci da kayan masarufi ballantana a sami Rumasa'u da kudi, bare a yi batun ta bugi kirji ta kai kanta asibiti. Yusha'u bai ta6a tsanar auren Rumasa'u irin yau ba. Ya fahimci Rumaisa'u ake so ta mallake shi ta dinga shimfida masa doka ba, a'a danginta ma so ake suna daga nesa su za su dinga tsara masa yadda zai yi a gidansa, shi yake hakuri da Rumasa'u ta ke juya shi son rai, ya ke hakuri da masifar laulayinta, ya ke hakuri da ita ya ke mata adalci alhalin ya san ba shi ne cikin zuciyarta ba. Duk wadannan manyan aibu ne ya ke jurewa sun kuma isa ya ci fuskar Rumasa'u a kansu, amma bai ci din ba ya ke kawar da kai amma duk da haka ana nuna gazawarsa, ba a dangin Rumasa'i ba ba kuma a nasa dangin ba. Wannan abu da yawa yake mutuwa ta je kasuwa! Rumaisa'u ta yi kwana biyar a asibiti aka mayar da ita gidan Hajiya, ta yi sati uku a can ta warware sosai ta kuma murmure kamar ba ta yi cuta ba. Sannan aka mayar da ita gidanta bayan Alhaji ya wanke Yusha'u tas da nasiha da gori, ya nuna masa lallai Yusha'u na shirin ba su kunya a wajen iyayen Rumasa'u, kunyar da ta fi tun karfo ya tubure ya ce ba zai auri 'yarsu ba. Zaman ya sauya salo da wata irin rayuwa mara dadin labari, Yusha'u ya bude kofar zuwa asibiti da kashi saba'in cikin dari sai dai shigen je-ka-na-yi- ka, wato ba ya bayar da kwabonsa zuwa asibiti bare a kai batun siyo magani, ya kuma toshe dukkan kofar da zata iya tambayarsa saboda tsabar gizagonsa ya camfa Rumasa'u ta raina shi, kuma matakin da zai iya dauka a kanta shi ne ya toshe kofofin rainin ta daina ganin hakoransa a waje balle ta nemi kawo masa wargi. Ai kuwa sai ya kwana bakwai Rumaisa'u ba ta ga hakorinsa da sunan dariya ba, babu doguwar hira sai dai numfarfashi da bayar da umarni, in ta debo masa dogon batu sai ya numfasa da kyar ya ce mata, "To". Ko kuma, "Na ji". Gaba daya rayuwar Rumaisa'u ta kuntata, jikinta babu dadi, zuciyarta babu dadi sai gaba daya gidan ya zame mata kamar kurkuku, duk da tana iyakar kokarinta wajen ganin ta ribato Yusha'u. Cikin haka ta kuma wayar gari da ciki bayan watanni uku da komawarta gidan. Wannan karon ta yi jan namijin tuknararsa da maganar cikin tun kafin ya cika watanni biyun. "Allah Ya inganta, Ya raba lafiya. Ina fatan za a yi min hanzarin mu wayi gari lafiya kafin mu je asibiti?" Abin da ya fada mata ke nan cikin rashin walwala ba tare da ya dubi idonta ba. Sai dai fa yana neman shayar da ita mamaki, dan yanzu ya 'kara sauya taku na mayar da ita aljihun baya, kuma ba a bakin komai ba, sannan yanzu kullum ya dawo kasuwa zai fesa wanka da sabon dinki ya feshe jiki da turrare ya cife kullm cikin sabon dinki da daure fuska ya ke, sai kuma ya kai goma na dare har zuwwa sha daya a waje babu halin ta nemi ba'asi yanzu sai abin ya zame musu rigima, domin kuwa sai ya hau kanta da bala'i. "KO KE da nake da ikon in hana ki fita ban sami wannan sararin ba bare ni da duk lalacewa ba ke kike ciyar da ni ba balle ki iya saka wa 'kafata kwado". Ba'kar magana a tsakaninsu ta zama abin adon da kamar alfajari Yusha'u yake idan yana ya6a mata, komai na laifi da korafi ne, duk kuwa yadda ta zage masa da kyautatawa kullum bakin cikinsa ta ke hadiya tana korawa da ruwan hakuri, amma tamkar zuga shi ake yana 'kara gadara da izza tare da munana mata. Rannan ya dawo gida karfe goma kamar yadda ya saba, da sauri ta cimmasa a dakinsa ta yi kwalliya kamar 'yar tsana, amma bai ko yarda ya 'kare mata kallo ba, sai wani kawar da kai yake yana hura hanci. Ta yi masa sannu da zuwa ta gaishe shi, sannan ta ce. "Wanka zaka fara ko in kawo maka abinci?" Ya yi kicin-kicin ya daure fuska ya ce. "Wannan wacce irin tambayar rowa ce Rumasa'u?" Ta dan dube shi a sanyaye ta kawar da kai, ta kasa cewa komai, shi kuma ya ci gaba da mita. "Ina jin haushin tambayar nan da kike min kullum! Ki kawo min mana idan ba na bukata ba sai na barshi ba?" Ta jima kanta a sunkuye, sannan ta yi murmushin takaici ta ce. "Allah Ya ba ka hakuri". Jiki a sa6ule ta wuce ta kawo masa abincin sannan ta nemi guri ta zauna har ya gaji da hararar abincin sannan ya zauna ya fara ci. Ita kuma ta ci gaba da satar kallonsa tana tuna yadda suka yi rannan. Ya dawo da yamma ya fito da kudi yana kirgawa ta kawo masa abinci, kawai sai ya hau ta da masifa. "Wallahi matsi ne ba na so. An gaya miki babu abin da na zo yi duniya sai cin abinci? Ke babu arzikin da zaki yiwa mutum sai dai ki yi ta tura masa abinci?" Idon ta rau-rau ta ce. "Yaya Yusha'u kamar me zan yi maka yanzu? Ka dawo na yi maka sannu da zuwa, na kawo maka ruwa kai da ka fita tun safe sai in kasa kawo maka abinci? Haba Yaya Yusha'u!" Ya kara tarar numfashinta a 'kufule. "Amma dai lissafi kika tarar ina yi ko? Idan abin kirki ne sai ki zauna ki taya ni ba wai ki yi ta tura min abinci ba". Ta dube shi da kwallarta ta ce. "Ka tuna ranar da ina hada kayan wankinka na ciro kudi a aljihunka na ajiye maka ka zo kana tuhumata da cewa, ba su ke nan ba? Har kana min gargadin kar na 'kara ta6a maka kudi?" A nan sai ya yi zugudi, kuma da yake uwarsa ba ta rasuwa ita kadai sai ya yi fuska ya ce. "Ni ba na son 'kullaci". Dan haka yanzu da ya yi mata maganar rowa ke sa ta yi masa tayin abinci ya sa ta tsaya tana ta faman satar kallonsa, shi dai wanda ke 'kinka babu abin da za ka yi ka iyar masa. Zuciyarta ta 'kara rauni da ta kula da yadda yake ta faman muzurai kamar mai zaune da mayya, kawai sai ta ji hawaye ya su6uce mata, can ma sai shesshekar kuka. Ya dago ya dubeta cikin muguwar 'kufula, ya ji ransa ya yi mugun 6aci dan babu abin da ya kaddara shi ne, ta tuno marigayi Auwal. Ya jima yana mata kallon tuhuma me kuma ya tuna? Oho! Sai ya sauke kai murya a sar'ke ya ce. "Haka Allah Ya 'kaddaro min, Alhaji kuma ya jaza min, ina aurenki zuciyarki na auren wani ko? Hmm MUTUM DA ZUCIYARSA ko? Ba zan gaji da gaya wa Allah neman Ya bi min ha'k'kina ba". Ta tsayar da kuka ta zuba masa ido kamar numfashinta zai dauke saboda takaici ta motsa baki da niyyar magana sai kuma ta hadiye abarta ta yi 'kasa da kai tana girgizawa. Sai kuma ya sha jinin jikinsa ya dan kafa mata ido, sannan ya ta6e baki ya ce. "Ki fadi duk abinda ranki ya raya miki, kar ki 'kullace ni. Abin da na fada gaskiya ce idan kina da wadda zata tankwa6e ta ba sai ki kawo ba, in ma rashin kunyar da kika saba za ki yi min ai ba wani saban ba ace a gurina ki yi iyakar son ranki ran da na kawo wadda zata bi ni sai 'kila ta zame miki darasi" . Allah sarki Ruma. Mata Allah Ya raba ku da na miji irin Yushau, Aamiin. . Dan Aunty GORAN DUMA (P 36) . . Ta hadiye dun'kullallen ba'kin cikin da ya tokare mata a 'kirji, da murmushin 'karfin Hali ta ce. "Ba na tuna Auwal a hurimin muzguna maka Yaya Yusha'u, domin ban aure ka ta silar so ko kuma ta dole ba, na aure ka ne dan na yi bautar aure wato bautar Allah, saboda haka ban ta6a hada zaman gidanka da wani 'kyalli ba. Halin da na sami kaina a cikin gidanka da irin ri'kon da kake min wani nufi ne daga ubangiji. Yadda kake nuna munin halina da kasawata a cikin rikon da nake maka Allah Shi ne shaidata ina kuma ro'konSa kafin Ya dau raina ya nuna maka 'kir'kirarmin munin hali kawai ka yi ba dan ya cancance ni ba. Sai dai duk yadda na ke da 'karfin halin tsayar da zuciyata a kanka kar na tuna baya in wuya ba na kasa tuna Auwal tunda MUTUM DA ZUCIYARSA bashi da iko da ita, sai dai ina ro'kona wata alfarma, ko ma dai menene, Auwal ya mutu babu komai tsakanina da shi, sai fatan alkhairi. Ina ro'kon ka janye shi daga cikin al'amuranmu, mu muka saura a duniyar muke taka irin rawar da muke so a cikinta, kuma ha'ki'katan ta ishe mu riga da wando...." Cikin kuka ta tashi ta bar masa dakinsa, in da ta bar shi da shanya baki yana kallon wajen da ta tashi. Ya yi niyyar ya share ta, amma da ya tuno tashin hankalin da suka yi har ta kai ga 6ari sai ya sauya shawara, ya gaggauta shiryawa ya sameta a dakinta. Hankalinsa ya dan kwanta da ya same ta ba cikin kuka ba kamar yadda ya yi zato, sai ya same ta a zaune bakin gado tana murza confo a gwiwar hannu tana cije le6e, akwai alamun hannun ne ya motsa. Ya zauna kan sofa yana binta da kallo fuskarsa babu yabo babu fallasa. Ya jima yana shan 'kamshi kafin ya taro abin da zai ce. "Ki yi hakuri na daina sako Auwal a lamuranmu, amma magana ta gaskiya ba zan ta6a lamintar..." Ta yi saurin dakatar da shi cikn muryarta da ke sha'kewa saboda son fashewa da kuka da kuma alamun zafin ciwo. "Yaya Yusha'u ka taimake ni ka tashi ka koma dakinka ciwon hannuna ya kori ciwon da zuciyata ke ji saboda takaicin da kake 'kunsa mata. Bai kamata ka biyo ni ka kuma daga min hankali ba, in dai baka dokantu da na bar maka duniyar a yanzu ba" Bai yi mamakin yadda ta ke magana cikin fada ba. A sanin da ya yi mata in dai tana ciwon hannu ko 'kafa ya ta6ota harshenta kan yi kaifi a wadannan lokutan, Allah basshi idan ta warke sai ta ba shi hakuri ta ce zafin ciwo ne. Sai ya yi shiru ya tsaya yana kallonta, ta ci gaba da mur'kususu tana 'kugi, nan da nan ta hada gumi sharkaf! Dole zuciyar musulunci ta sanya shi zuwa ya ri'keta yana mata sannu yana ta faman shafa mata confo a hannun. Sun fi awa daya suna abu daya, ba ita ba ba shi kansa sai da ya yi muguwar jigata saboda ri'kon da ta ke masa. Ya tambayeta ta sha magungunanta na kullum? Ta nuna ba ta sha ba, ya nemi ya bata sai wajen karfe daya ta samu runtsawa a cinyarsa ta barshi da sa'ke-sa'ke da 'kare mata kallo, har ta kai shi ga lissafin tsawon lokacin rabonsu da kusantar juna kamar haka, lissafin kuma da ya tuna masa kishinta har ya kai ga farkar da ita. Amma Rumaisa'u 'yar halak duk da gajiya da baccin da ya cika mata ido ba ta 'ki amsa tayinsa ba. Sai dai tir! Lokacin da ya fara gigicewa sai ya ke ambaton sunan wasu mata. "Sumayya, Sumoli, Ummi". Tuni ta kwaci kanta da ambaton. "Lahaula wala 'kuwata illa billah". Ta barke da kuka lokacin da ta tattaro bargo ta tashi zaune. Ya bi ta da kallo cikin fuskar mamaki ya ce. "Kan ki daya Rumasa'u, lafiya kike?" Ta ci gaba da kuka cikin tsare shi da ido, sannan ta kattse shi cikin shesshekar kuka, ta ce. "Abin da ka yi yau ba ka da sanin yana daga nau'in zina? Wace ce Sumayya, Sumoli, Ummi? Mene ne hukuncin kawo mana su a shimfida?" Zuciyar Yusha'u ta yi wani mugun bugu da ya fahimci abin da yake rayawa ya fito fili, amma da yake ya iya fargar jaji, sai yayi fuffukar borin kunya. "Kin ga malama bana son sharri, wacce mace na sani bayan ke? Kawai ki ce min kin zaci kowa ma irinki ne da kike suffanta ni da na kabari...." Ta toshe baki ta tashi tsaye cikin tsananin tashin hankali tana kallonsa. Da sauri ta juya ta shiga bandaki ta turo 'kofa ta fashe da kuka. * Bakwai safiya bata cika ba, Yusha'u ya silale ya buga mota ya bar gidan inda ya doshi gidansu kai tsaye. Ya kamata ya ture shakka ya bude kwanjinsa dan yin abin da yake so ba wanda ake so masa ba, wanda ya dace da shi ba wanda aka datar masa ba. Kai gara ma ya tunkari Alhaji kai tsaye ya sanar da shi zai yi aure tun kafin kwa6arsa ta zaureye tunda a yanzu dai ta fara ruwa. "Alhaji ina neman amincewarka ka yarje min na 'karo aure, ina da muradin hakan sannan na kamu da son wata yarinya, bugu da 'kari auren zai taimake ni ya taimaki Rumaisa'u a matsayinta na mai yawan larura ba ta ko iya daukar nauye-nauyen kanta balle ta dauki na wani". Ran Alhaji ya 6aci gaya, sai dai ya hadiye shi a ciki. Ya yiwa Yusha'u wani kallon wulakanci ya ce. "Cikin dalilai ukun da ka gabatar min wanne ne kake jin ya fi gamsar da kai na lallai ka yi aure?" Cikin karfin hali Yusha'u ya ce. "Duk Alhaji ina son in 'kara auren, ina son yarinyar, sannan dan in taimaki ita Rumasa'u" Nan da nan Alhaji ya ci mur, ya tare shi. "Ni karya ce ba na so, kawai dai kana muradin ka yi aure yanzu ne ka sami matar da kake so ba wadda ake so maka ba, kar ka 'kara sako Rumasa'u a cikin dalilanka". Yusha'u ya dauko buhun rantsuwa ya fara saukewa, Alhaji ya tare shi. "In ka rantse min zan iya kwada maka mari a banza a wofi Yusha'u, kana son taimakonta ka kasa nemar mata 'yar aiki? Hajiya ma ta yi zuciya ta kai muku 'yar aikin, ka ke neman korarta da mugun hali? Duk halin da kuke ciki ina sane Yusha'u zuba maka ido kawai na yi na ga iyakar gudun ruwanka, in gani shin da gaske kasheta kake shirin yi, ka sami sararin auro wata.....?" Yusha'u ya tari numfashin mahaifinsa da doguwar rantsuwa. "Na rantse da Allah Alhaji ba 'karamin hakuri nake da munanan halayen Rumasa'u ba...." "Kafin ya sauke huci Alhaji ya sharara masa wani bahagon mari, Yusha'u ya dafe kuncin, wani irin radadi ya isa har kwanyarsa ya hadu da bakin da zuciyarsa ta yi suka sabbaba masa zubar hawaye. Yaushe rabonsa da dorar da zafin duka gemai-gemai da shi? A dake shi akan matar da yake zaman laurara da ita? Sai ya ji ya 'kara tsanar Rumaisa'u, zuciyarsa ta 'ke'kashe, ya dubi mahaifin nasa cikin kwalla ya ce. "Alhaji ni na san matsalolin da nake shiga a cikin auren Rumaisa'u, idan dai ina da damar in auri wata bayanta to don Allah ka amince min auren nan..." . . Yushau dai dakikine inji wani a gidan nan, idan kuna so ku bani dama na sheke shi kamar yadda nayiwa Awwal kowa ya huta da bakin cikin sa... Abbas Abdulkadir Hada Hada (Dan Aunty) GORAN DUMA (P 37) . . Alhaji ya hadiye rud'anin da ya shiga cikin zafin murya ya ce. "Ba ka da damar! Ka tashi kuma ka bar min gida, sannan ina maka godiyar halaccin da ka yi min. Na aura maka Rumasa'u dan ka ji 'kanta ashe kai auren jeka-na-ka ka yi da ita, kake zage 'karfinka da iyawarka kake muzguna mata dan ta gaji da kanta ta ce ba ta aurenka ta jure, sai kake son kinkimo aure dan ka nuna mana iyakarmu. Auren da kadan ya haure shekara daya kake shirin dan'kara mata kishiya? To ban laminta ba, in kuma ka ga na laminta to ciki aikinka ka yi ka sako min Rumaisa'i, fa'kat! Ka 6ace min da gani na gaji da ganin mummunar fuskarka". Yusha'u bai wami karfin gwiwar wucewa kasuwa ba saboda zafin zuciya, fushi, 6acin rai da radadin a fuskarsa ta ke. Ya shiga gidan shiru babu motsin Rumasa'u ko na talabijin dinta, sai Adama da ke kara-kainar aiki a kicin, ya yi tsaki 'kasa-'kasa ya wuce dakinsa cike da dokin Allah Ya kawo Rumasa'u ta ta'kalo shi ya sauke mata kwandon rashin kirki. Amma fiye da awaya biyu babu ita babu motsinta, ga yunwa na addabarsa saboda ko karyawa bai yi ba, ga ciwon kai da zafin mari ya sabbaba masa. Amman fiye da awa biyu babu ita babu motsinta, ga yunwa na addabarsa saboda ko karyawa bai yi ba, ga ciwon kai da zafin da marin ya sabbabasa masa. Da kyar ya lalla6a da azahar ya je sallah ya dawo ya kuma kwanciya yana sanyo idon shigowar Rumaisa'i. Da gangan ya dinga kaki da gyaran murya a tsakar gida dan ta san da zuwansa, amma har la'asar ba ta shigo ba. Bayan ya dawo sallar la'asar sai ya wuce dakinta kai tsaye cike da fushi. Ya same ta a zaune gaban sofa tana jinyar hannunta wanda ya yi ciwo jiya, yau ya kumbura suntum, da ya kalli fuskarta sai da gabansa ya fadi saboda yadda ta yi wata muguwar rama idonta kuwa ya jeme da kuka. Sai dai yana tuno yadda ya sha mari a kanta a wajen Alhaji sai ya ji kamar ma ya yi mata Allah Ya 'kara. Ya nemi guri bakin gado ya zauna ya dubeta fuskarsa a daure. "Ki tashi ki dafa min abin da zan ci yunwa na ke ji". Cikin wahalallen kallo ta dan tsura masa ido, muryarta a dashe. "Yau daya Yaya Yusha'u.... ina neman alfarmar ka ci abincin Adama, lallai ina takaicin kasa tashi in girka maka abinci. Ba zan iya ba Yaya Yusha'u, dubi hannuna ya dame ni da matsanancin ciwo kamar na cire shi na jefar..." Ya tareta cikin halin ko'in kula. "Wallahi ba zan ci girkin Adama ba, dole ki tashi ko abu mai sauki ki dafa min. Taliya ko ki soya min dankali da kwai, na ba ki minti talatin." Bai ko saurari hanzarinta ba ya fice ya barta. Dole ta mike tana kuka ta sami dankwali ta daura a wuya, ta tare hannunta ta nufi kicin. Ta dinga aiki da hannu daya cikin matsananciyar wahala da zubar da hawaye, in ciwo ya ishe ta ta tsaya ta yi mur'kususu da 'kugi har sai ya lafa sannan zata tashi ta ci gaba. Da yake jalob din taliya babu wahala ba ta dauki wani dogon lokaci ba ta gama, ta iske shi daki ta kai masa. Ya nuna mata firji. "Ki dauki fura ki dama min". Ta daure hawayen da ya cika mata ido tana duban hannunta ta ce. "Sai dai in da hannun hagu zan dama maka, kada furar ta samu matsala.... hannuna yana ciwo." Ya kawar da kai yana ta6e baki. "Yaushe za ki dama min fura da hannun hagu? Yanzu duk girkin nan da hannun hagu kika yi? Damun fura sai ya gagare ki....?" Da ta dan tsura masa ido ta ga ya soko maganganu a 'kasa sai ta fahimci shi kansa bai yarda da kansa ba. Ba ta ce masa komai ba dan haka ya kuma samun ta cewa. "Ina son in sha furar nan da gaske, ki lalla6a hannnun ki dama min..." Cikin 'kufula akan rashin tausayinsa ta tare shi da cewa. "Ba zan iya ba wallahi". Ya dago kai cike da haushi da 'kufula ya dube ta amma ba ta bashi sararin cewa wani abu ba, ta tashi ta bar masa falon. Wannan abin da ta yi ya 'kara 'kufular da shi. Ya fito zai je sallar magriba ta fito tsakar gida cikin hawaye ta tare shi. "Don Allah Yaya Yusha'u in ka yi sallar ka dawo ka kai ni asibiti..." "Ba zan iya ba wallahi". Ya tari numfashinta da irin furucin da ta yi masa dazu yana ta faman hura hanci. Cikin raunin murya ko zai tausaya mata ta ce. "Don Allah ka taimake ni Yaya Yusha'u". Ya yi gaba cikin fuffuka ba tare da ya tanka mata ba. Ta ce. "To na je ni kadai...?" Ya sake tare ta da fadin. "Allah Ya ba da sa'a". "To ba ni kudin magani". Ta fada cikin tsananin tausayin kanta. Ya fice abinsa yana cewa. "Ba ni da su". Kawai sai ta dur'kushe a wajen ta rushe da kuka ta jima tana yi sannnan ta koma daki tana kuka tana ambaton Allah, babu halin ko Hafsat ta kira a waya ta taimake ta saboda al'kawarin da ta yi na ba zata 'kara sanar da wani halin da ta ke ciki ba ko zata mutu. Har sha daya na dare tana cikin tashin hankali, sannan Yusha'u ya shigo amma shi da kansa ya san bai kyauta ba, tare kuma da tsoron 'kila Rumasa'u ta kira wani ta sanar da shi yadda suka yi, 'kila Alhaji ya la'ance shi, yana kuma cike da tsoron wannan dan rikicin da suka yi kar ya yi sanadin zubewar cikinta kamar yadda ya faru a cikinta na baya. Wadannan dalilan suka sa bayan ya gama shirin bacci ya doshi dakinta ya same ta cikin mawuyacin halinta. Girman kai da masifar haushinta da yake ji ya hana shi yi mata kulawar kirki, ya dai yi mata sannu, ya ajiye wayarsa kan durowa ya haye gado ya ja bargo. Rumaisa'u na zaune har sha biyu da rabi sannan ta samu hannunta ya rage zogi, zuciyarta kuma ta dau nata ciwon na zama da ma'kiyi wanda ba ya tausayin dan Adam, duk hawayen da ta ke a yanzu na wannan takaicin ne. Cikin haka ta ji take shigowar sa'ko a wayar Yusha'u, haka kawai ta ji ta cika da dokin ganin sa'kon. Ban da tana cikin halin ciwo wanda kan mantar da ita tuna wasu tunane-tunanen duniya babu yadda za a yi ta kasa lissafinta da Sumoli, Sumayya, Ummi. Duk lokacin da ciwo ya sake ta tunanin matan nan da ala'kar da ke tsakaninsu da mijinta ta ke. Cikin sand'a ta janyo wayarsa ta budo sa'kon cikin doki da dukan zuciya ta bud'a. 'Ya Habibi, wani mafarki na yi mai 'kayatarwa, mun yi nutso cikin burikanmu, mun tabbatar da mafarkanmu na mallakar juna. SUMOLINKA'. RUMAISA'U ta maimaita karanta sa'kon nan ya fi sau ashirin masa'ki, hade da kallon 'keyar Yusha'u da ya juya mata baya yana sharar baccinsa. Yanzu tunaninta ya fi tafiya juya maganganun sa'kon tare da misalta daga irin macen da ya kamata su fito. Sumoli! Sunan ya yi kama da na wadanda ba Hausawa ba 'kila kuma ba musulmai ba. To karuwa ce? Tana shakkar in karuwa ce dan Yusha'u ba shi da kamannin neman mata ko ta ina aka juya shi.... . . To da ganowa idon ta, shi yasa yanzu naji ance an daina yiwa mata padan komai idan za'ayi auren su sai padan ''kiyi hakuri, banda duban wayan sa' lol. Dan Aunty.GORAN DUMA (P 38) . . In Sumoli ba karuwa ba ce mecece? Ba ta ta6a kawo matar da Yusha'u zai nema da aure zata zo da irin wannan sunan ba bare a same ta da irin wadannan maganganu a tsakiyar dare haka! Abin ya daure mata kai matu'ka. Ana cikin haka sai ga lambar sa'kon ta kwado kira, Allah Ya sanya wayar a silent ta ke, kawai sai ta suri wayar ta yi falo, ta daga wayar ba tare da ta tanka ba. Sai mai kiran ce ta fara magana cikin yau'ki da sautin 'karamar dariya. "Yi hakuri na tashe ka bacci ko? Zuciyata ce ta kasa hutawa da begenka. Ka ga sa'kona? Wani mafarki mai dad'i na yi mana tunda na farka na kasa komawa....." Zuciyar Rumaisa'u ta dinga bugawa fat-fat! Hannunta ya dinga karkarwa ri'ke da wayar, amma da yake tana da dauriya sai ta amsa muryarta tar! "Ayya! Shi kam kin ga har ya fara jan rago, amma idan ya farka da safe zan sanar da shi". Ba ta jira cewar Sumoli ba ta kashe wayar ta zube a kujera cikin haki tamkar wadda ta yi gudun famfala'ik, abin da ya cunkushe mata numfashi ta ma rasa ta inda zata kwashi wannan 'kalubalen yadda zai zame mata maslaha. Da safe Yusha'u bai sami sararin fita kasuwa ba saboda kansa da ya matsa masa da ciwo. Da Adama ta iso kasancewar da safiya take zuwa, ta zauna har la'asar, yau da ta zo sai Rumasa'u ta sallame ta da cewa sai gobe yanzu zata je asibiti daga can kuma ta wuce gida sai dare zata dawo. Ta sami Yusha'u da maganar asibiti kamar jiya dai ya furje. "Ki dawo lafiya, ni ma ba lafiyar ce da ni ba in zan sami mai kai

Chapter 12 of 21