Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Tabbas Masoyine Bata Shakkar Cewa Inbata Fara Shakuwa Da Sakonninsa Ba Sannan Inta Ci Gaba Da Nesanta Kanta Da Sakonninsa Dole Taikewa Kamar Yadda Ita Da Zuciyarta Suka Yarda Sunyi Kewa A Kwanakin Da Suka Gabata Tazauna Tajanyo Wasikar Datakarbo Daga Gidan Waya Adireshin ANNUR MIKYWAY CAFE DAGA ABUJA? CAFE DIN DAKE ABUJA INDA KUMA TASAI WAYOYIN HANNUNTA BIYU TASAI MODERN DINTA INDA TA SAI KYAMARARTA INDA TASAI......... KAI BAZATA IYA KIRGAWA BA. Inhar Taje Hankalinta Baya Kwanciya Tanaji Ajikinta Kamar Tana Da Nasaba Da Gurin, Tanata Tunani Ta Bude Wasikar Ko Kuma Kawai Ta Share Taikarfin Hali Ta Bude Taga An Rubuta ""RAYUWATA ZAN BAYYANA MIKI KAINA, NAKI MAHAUKACIN MASOYI"" TARE DA SA HANNUNSA,ta Ce Wato Mahaukacin Masoyi Daga Annur Mikyway Yake,ya Abinyake? Innalillahi Wa Inna Ilaihirajiun Tanamamakin Yaya Haka Tafaru,,dago Kan Nan Dazatayi Saitaga Alamun Mutum A Inuwar Labule Ta Taga ,yanaganin Ta Dago Da Sauri Ya Bar Wajen,takori Dukan Da Zuciyarta Take Cikin Zafin Nama Ta Isa Tagar Ta Yaye Labulen Tahau Leke Leke Amma Bataga Komai Ba Sai Motocinsu Dake Gurin Kwanyarta Tafara Dawo Mata Da Abindata Karanta A Takardar Mahaukacin Masoyi Zanbayyana Miki Kaina Shine Wato Yanzu Ya Bayyana A Labule Taja Baya Tana Raya Abubuwa Masu Wahalar Fassara Wanda Tagama Hakikancewa Mahaukacin Masoyi Ba Aljanibane Amma Abinda Mahaukacin Masoyi Keyi Yawuce Azaceshi Cikin Mutane,to Waye? Ta Fizgo Hijabi Ta Zira Ta Ce Zan Binciko Waye Kai,abindayakama Naikenan A Farko, kasha Zamanka Zan Nemoka, a Falo Ba Yushau Ba Hajiya Sai Sumoli Tafice Itakuma Sumoli Ta Tsargu Don Haka Ta Mike Ta Hau Lekenta Ta Taga Ruma Nafita Ta Hango Yushau Yafito Ta Tsakanin Motoci Kaitsaye Ya Nufota Take Ta Tsargu Da Ganinsa Kuma Ta Alakanta Hakan Da Mahaukacin Masoyi Fuskarta Daure Ta Tsaya Ina Zaki Haka? Ta daga Takardar Tsakaninka Da Allah Yaya Yushau Bakada Masaniya Akan Wannan Takardar? Yanamata Kallan Rashin Fahimta Ya Karba Yana Nazarinta Cikin Yamutsa Fuska Kirjinsa Na Dukan Uku Uku Basaikin Hadani Da Allah Ba Ruma Wallahi Bansan Komai Akanta Mene yafaru? Ta Amsa Takardar Tana Nazarinta Yanzu Ina Daki Naga Inuwar Mutum Naleke Nata Labule Ko Kaganshi Tunda Tanan Ka Bullo, Kallon Juna Sukai Ido Cikin Ido Wanda Yushau Yake Da Yakinin Hakan Baitaba Faruwa Tsakaninsa Hakanyasanya Masa Muguwar Kasala Kirjinsa Nata Bugawa Da Sauri Taja Baya Ayanzu Kam Tasan Yushau Ya Wanke Hannu Nezai Danna Maballin Kunno Mata Danjar Bakin ciki Wahala Da Kunan Zuciya, Tsoronta Daya Kada Hakan Yafaru Gaban Abbah Dan Zata Iya Keta Idan Alhji Ta Ce Batasansa Tajuya Zata Bar Gurin Ga Mamakinta Saitaji Yushau Ya Ruko Hannunta Yaja Ta Baya Dasauri Suka Shiga Tskanin Motoci Tsoro Da Shakku Tuni Sungama Mamaye Ta Yaya Yushau Menene Haka? Sai Ga Hawaye Daga Idansa So Nake Na Baki Kalmar Da Ban Taba Baki Ba Duk Tazo Kunnenki A Makare Saidai Niyanzu Take Shan Sharafinta A Kirjina Alhalin Ina Cike Da Jin Haushin Ciwan Rashin Zuwanta INASONKI RUMAISAU WALLAHI INASONKI Dasauri Ruma Ta Ce Kadaina Rantsewa Meyasa? Indaza A Laluba Zuciyarka Da Kyau Sai Antarar Da Kaffara Takamaka Bajinsona Kake Ba Illah,,, yatareta Ruma Duk Abinan Danakeji A Kirjina Game Dake Kicemin Baso Bane? Taja Baya Hawaye Suka Fara Zuba Daidai Lokacin Idanta Yakai Kan Sumoli Ta Ce SO DAYANE TAK TUNI NA SADAUKAR DA NAWA GA WANDA YA CANCANCESHI DUK DA UBANGIJI BAI NUFA ZAMUCI GAJIYAR SA NIDA WANDA NASO DINBA,ILLA JIN KUMAJIN RADADIN DANAKE JI YAZAMA KAFFARA,AMMA NAKA SON KAGA INDA KA SARAYAR DASHI,TA NUNA MASA SUMOLI Yakalli Sumoli Baiji Zuciyar Sa Ta Sauya Ba...... Yaitsaki Yamaida Kallansa Ga Ruma, Ruma Ta Ce "Nikuma TAWA RAYUWAR BA A KIRKIRETA DAN TAZAMA FANSAR FARINCIKINKA BA YAYA YUSHAU MURUFE WANNAN CAFTAR AUREN JUNA DA MUKAI A BAYA KUSKURENE DA CIN AMANAR ZUCIYOYINMU WADANDA DUK BA HAKA SUKESO BA HAKA ZALIKA IYALAN DAMUKA SAMAR BA HAKAMUKASO BA NI NAI DANASANIN HAIHUWAR SU DOMIN TAUSAYIN RAYUWARSU KAI KANA BAKINCIKIN HAIHUWARSU DOMIN TAUSAYIN RAYUWAR SU KAIKANA BAKINCIKIN HAIHUWAR SU SABODA BASU FITO DAGA MACEN DATA CANCANCI HAIHUWAR 'YA'YANKA BA, KI Bar Maganar Nan Dan Allah Tafara Tafiya Ya Ce Zansa Karfi Da Lallashi Kidawo Rayuwata Zanbaki Abinda Ban Baki A Baya Ba Wato So Da Kulawa, Takada Kai Ta Ce ToGA HANYA NAN AMMA KAMAR AKWAI WANDA YAFIKA KARFI DA IYA LALLASHI AKAN HANYA WATO DAN AUNTY. . To en gidan nan ku zama shaida Ruma ni take so , kunji dai da bakinta..lol. . Sai jibi ma dora. . Dan Aunty GORAN DUMA (p 52) . . Takada Kai TaCe To GA HANYA NAN AMMA KAMAR AKWAI WANDA YAFIKA KARFI DA IYA LALLASHI AKAN HANYA WATO MAHAUKACIN MASOYI IN ALAMUN KARFI YANAGA MAI KIBA SAI INGA KAMAR ZAI IYA KAYARDAKAI Tunda tai maganar Tai Taga Yanayin Sa Ya Sau Dan taga Ko suna Da Alaka Da Mahaukacin Masoyi,ransa A Bace Ya Ce wanene Mahaukacin Masoyi? Wannan kuwa Ba cin Fuska Bane?Zakijerani Dawani waima Mahaukaci Asan Dan kinga Nafada Sonki Ruma? Saitasami Kanta Dayimasa Murmushin Mamaki Sannan Takauda Kai Batare Data Amsamasa Ba Tawuce Cikingida Ta Barshi Agurin Motocin Sumoli Naleke Ta Window,gabadaya Zuciyar Ruma Ta Zaku Da Sanin Mahaukacin Masoyi,tanazama Adaki Sai Ga Sakonsa Ta Waya Wanda Ke Nuna Shaidar Yagama Kallon Diramarta Da Yushau HANKALINA SOYAKE YA KWANTA ASHE BANI NAKE YAUDARAR ZUCIYATA BA? TAJIMA TANA RADAMIN ZAKI SOMU, Cikin Karkarwar Hannu Tasami Kanta Da tafa Gajeren Sako Taimasa Amsa A Karo Na Farko,WAYE KAI? INA SON IN SANKA, Taitajiran Amsa Har Karfe Goma Na Dare Tadinga Kiran Wasu Layiyyinkansa Bata samuba Taji Afuwar Son Tasan Mahaukacin Masoyi A Yau Tamkar Dandayaso Fitowa Cikin Mahaifiyar Sa Dan Haka Tanemi Abinda Yake Mata Dadi A Duniya Tarasa,sai Ta Hau Social Network Ta Tura masa KALAMANKA NA NUNA JARUMTA A SOYAYYA DA RAYUWA,AMMA AYYUKANKA SUN KASA TABBATAR DA HAKAN,YAKIN BOYE DAGA MUTUM BOYAYYE? LALLAI BUYA YAYIN CIMMA BURI ALAMACE TA RAGONTAKA,IDAN BA A CIKIN RAGWAYE KAKE BA INASON INSANKA, Tafi Awa Biyu Sannan Tasami Gajeriyar Amsa Ta Inbox Dinta A Facebook,LOl! BANSAN NI RAGONE KO JARUMI BA,ABINDA KAWAI NASANI NI MAHAUKACINE A SOYAYYARKI MAHAUKACINDA IN BAI SHIGA SAHUN DAKARU A KWANJI BA DA ADALCI ZA AKIRA SHI BARDE A SOYAYYA,KINA SON GANINA? NAZACI KINCI ALWASHIN GANONI DA KANKI, TANAKARANTA Wanna Sakon Nasa Tamike Zumbur Kawai Saitasami Kanta Da Kwankwasa Kofar Dakin Baccin Hajiya Tsawon Mintuna Biyar,sai Ga Hajiya Tafito Daga Sashen Alhji Cikin Magagin Bacci Fuska Cike Da Tsoro Tana Duban Agogo Wanda Yanuna Sha Biyu Da Rabi Lfya Jikin Ne Ruma? Arikice Take Idanta Fal Da Kwalla Takama Hannun Hajiya Inason Zuwa Abuja Gobe Indawo Jibi,kinemarmin Wannan Damar Wajen Alhji Dan Allah Meyafaru? Wani Abu Kike Da Bukata Kikejin Mu Bazamu Iya Yimiki Ba Sai A Abuja? Kina Girgiza Kai Kina Kuka? Amsarki Na Nufin E,h Da A,a Kenan,ba Abin Kuka Bane Hajiya,raunina Ne Kawai Yakawo Kukan,a Barni Inje Abuja Nai Alkawarin Da Nadawo Zansanar Dake Komai kuma Na Rantse miki Da Allah Sai Kaddarar Ubangiji Inzan Dara Jib Ruma Na Sauka A Tashar Utako Maimakon Ta Dauki Shatar Mota Zuwa Gidantake Wuse,kawai Saita Umarci Dan Tasi Dayakaita Milkway Cafe Bata Da Yakinin Zatajima A Ciki Ko Bazata Jimaba Dan Haka Tasallami Dan Tasi Tataka Cikin Barin Jiki Dana Zuciya Ta Shiga Kantin,babu Abinda Ke Yawo Aranta Irin Sakon Mahaukacin Masoyi Na Safiyar Yau INAJI A JIKINA A YAU ZANGA MASOYIYATA, Kamar Kullum A Milkway Na Baya BaBu Abinda Ya Ragu A Kallon Mayatar Da Ma,aikatan Gurin Kemata Saima Karuwa Datake Tsammanin Yi,itama Ta Dake Ta Janyo Daddatan Magani Ta Ci Kuma Tadinga Tafiyar Kasaita Har Taisa Bangaren Datafi Wayo Wato Yanar Gizo,ina Son Ganin Manajan Gidannan Malam Bayan Sallamar Ko Gaisuwa Bataimasa Ba To Madam Kira Shi Za Ayi Ko Kuma Kai Ki Gurinsa Za Ayi Akaini, Kaitsaye Tafada Cikin Cin Magani Tamike Tana Rataya Jaka,zo Muje,bayan Yagama Jimaminsa,har Ofishin Manaja Tai Arba Dashi Gajeren Mutumin Nane Wanda Ya Ce Kallanta Yafi Kallon Talabijin,suna shiGa Taga Fuskar Rashin Gaskiya Atare Dashi Lfya Garba? Yatambaya Arikice Bayan Tafiyar Garba Office Din Yai Shuru Shiyasakata A Kwandan Shara Yanata Tafa Sako A Wayar Sa Itakuma Tanata Nazarin Ofishin To Hajiya Inajinki, Nazo Ne Inji Dalilinda Yasa In Nazo Gidan Nan Nake Zama Muku Magiji In Ban Manta Ba Kaida Kanka Ka Taba Fadamin Nafi Majigin Dadin Kallo Mudin? Kalmar Dayafada Cikin Alamar Shakansa Ma Baiyarda Da Kansa Ba, Kudinfa Ta Amsa Rai A Bace,yai Kasake Hankalinsa Nakan Waya, Shikenan Abinda Kikeson Sani? A Amsa Min Wannan Tambayar Mana Sai Aji Idan Akwai Wata, Karon Farko Dayai Murmushi, Kin Tsargu Ne Kawai Amma Ni Ban San Munakallanki Kamar Majigi Ba,nidai Kawai Nasan Bama Iya Ganinki Bamu ShiGa Rudani Ba Amma Har Yau Bamu Gano Dalili Ba,duk Da Haka Kiyi Hakuri, ruma Taji Kamar Ta Kwarfa Masa Mari Saboda Haushi Amma Ta Hadiye Ta Balle Jaka Ta Fito Da Takardar Mahaukacin Masoyi Wadda Ya Aiko Ta Gidan Waya Kuma Daidai Wannan Lokacin Sakon Mahaukacin Masoyin Yashigo Wayarta, ASHE DA GASKE KINA SON GANINA DAN ALLAH MEYA KAI HAKA DADI A DUNIYATA TA YANZU? TA Hada Da Wayar Da Wasikar Duba Wasikar Nan Waya Rubuta Ta Agidannan Kuma Sa Hannun Watake Dauke Dashi Duk Taimasa Tambayoyine Cikin Hanzari Da Hadiye Rikitarta Manaja Yafi Minti Biyar Yana Juya Waya Da Wasika Sannan Yadago Muryar Sa Na Rawa Ya Ce,lambar Da Sanya Hannu Duk Na NAZIFI MUHAMMAD NE Nazifi Muhammad? NAZIFI MUHAMMAD? Tasake Maimaitawa A Rude Ganin Yakasa Amsa Mata Kuma Yana Bintada Wani Rudadden Kallo,amma Bakinsa Yakasa Furta Kalma Ko Guda,taja Kujera Datun Tuni Take Tsaye Rike Da Majin gininta Ta Zauna Inatambaya Kayi Shuru? Madam Tambaya Kikayi Kenan?Nazaci Maimaita Sunan kike Domin Yanamiki Dadin Fada? Ta Hadiye Doki Da Mamakinsa Kuma Datakara Saitajanye Dukkan Rudanin Da Fuskarta Ke Nunawa Ta Barwa Zuciyarta Tanaji Dasu,to Ba Bu Laifi Inason Ganinsa,baya Gari Takara Zuramasa Ido Kuri Tsawon Lokaci Ta Ce Menene Matsayinsa A Gidan Nan? Shine Mamallakin Wajen,da Sauri Tajuyo Amma Naji Kakira Sunanshi Kaitsaye? Yadan Fara Dariya Aikamawa Take A Daure Mai Daurewa,hakane Ina Son In Sani Mutum Ne Ko Aljan? Mamaki Ya Bayyana Karara A Fuskar Sa Bakinsa Na Rawa Ya Ce Wanne Irin Aljani Kuma? Dama Aljannu Abokan Huldarmu Ne Dahaar Zan Shaida miki Shi A Mamallakin Gidan Nan, tatareshi Cikin Ci Da Zuci Kukusani Ni Ba Matsayinsa Nazo A Sanar Dani Ba,shinakeso In Sani Dan Haka Karmu Ja Maganar Kasanar Dani Ranar Dazai Dawo, To Kahadani Dashi A Waya Cikin Jimami Ya Ce To Bara Nanemi Izini Agurinsa Yatafa Sako Yaturamasa Sannan Ya Tsaya Dako,can Sai Ga Amsar Amincewa Sannan Ubangida Nasa Yakirashi A Waya,kaitsaye Shikuma Bai Daga Ba Saiyamika Wa Ruma Tare Da Mikewa Yabar Falon Tadaga Wayar Dajin Karfin Gwiwar Juya Harshe Yadda Taso,amma Daga Sallamar Sa Ya Warware Mata Duk Notikan Laka Da Karfin Hali Baki Yahau Karkarwa Jiki Yadauki Bari,duk Da Haka Bata Iya Amsa Sallamar Ba,ranki Yadade Ance Kina Son Magana Dani,?Tattausar Muryar Tasa Takara Dukan Dukan Kunnenta Da Zuciyarta Kawai Saitaji Wani Irin Rauni Ya Mamayeta Dan Haka Batun Tai Maganarma Bata Tasoba Rumaisau Kinajina Kuwa? Cikin Mamaki Tadanyi Wani Nishi, Waye Wa,,,,wa Takasa Direwa Kawai Saita Hakura Rumaisau Yaya Jikin? Kawai Saitasami Kanta Da Sheshekar Kuka Itakanta Takasa Tantance Abinda Yasata Kuka baitankamata Ba Tsawon Lokacin dataji Kamar Bawa Kanta Hakuri Amma Kafin Tafadi Abindata Sak'a Fada Ya Rigata Cikin Wata Irin Murya Mai Rauni, "kin Dauki Hakki. . . Dan Aunty GORAN DUMA (P 53) . . Kin Nemi Tarwatsa Zuciyata Mai Sauraronki Kina Kuka,,dakin San Hakane Da Ba Kice A Hadaki Daniba Gara Yin Umarnin Duk Inda Nake Nazo Nasameki Zanyi Biyayya Nazo Kuma Ina Da Yakinin Inkinga Kaunarki Dake Kwance A Kwayar Idona Zaki Tabbatar Inkinyi Kuka Agabana Zaki Cutar Dani,maganganunsa Sunkara Rudata Ainun,data Lalubi Ilahirinta Sai Ta Tarar Ita Kanta Neman Manta Kanta Take,bare Ta Tuna Maganar Dazata Fadawa Wannan Majanunin Magana Wadda Ta Shafi Jiya Dayau Dinta Shida Ba A Toshe Masa Basirar Ba Saiyaja Sunanta A Hankali Tamkar Yaimata Allura Saigata A Farke,bakinta Yagaji Da Bari Ya Furta Abinda Kwakwalwartata Ta Kera Watakila Ina Kuka Ne Saboda Bansan Da Irin Mutumin Danake Tare Ba,,ina Kuka Bisa Yadda Kake Wahalar Da Zuciyata Tare Da Gangar Jikina Yakatse Ta Cikin Muryar Lallashi Kinga Yi Hakuri Ki Koma Gida Zanzo Nasameki Har Gidan Ya Katse Wayar, Ruma Tai Tsuru Da Wayar A Kunne Batare Data Iya Saukewa Zuciyarta Na Bugawa Fat Fat Hajijiya Na Dibanta Saidai Takasa Motsawa Nanda Can Sai A Manaja Ya Ya Ce Mata Kano Kika Nufa Ko Wuse? Ta Juyo Tana Binsa Da Kallo Da Alamar Tai Mamakin Jin Kanonta A Bakinsa Da Wuse Wannan Ya Tabbatar Mata Duk Shakiyancin Da Ake Mata Yana Da Masaniya Saitaji Ranta Yai Mugun Baci Ta Ajiye Masa Wayar Sa Takarasa Goge Hawayenta Kunnuwanta Kuma Na Sauraronsa Yace Yayi Umarnin Duk Inda Kika Nufa Idan Kina Da Bukata A Bayar Da Mota Akaiki Bata Tsinka Ba Kallan Dataimasa Yana Tattare Da Amsar Banida Bukata Ta Wuce Kai Tsaye Batare Data masa Sallama Ba Ta Bar Office Din, Shikuma Baidamu Da Basarwarta Ba Yatake Mata Baya Ya Rakota Har Bakin Titi Ya Tayata Jiran Tasi,bai Mata Magana Ba Itama Hakan Bayan Sun Tsayar Da Motar Shiya Sallami Mai Tasi Yaimata Bankwana Ita Ko Tankasa Bataiba, Tana Mota Tanata Lissafe Lissafen Yadda Nazifi Yake Da Yadda Har Ya Wuce Makadi Da Rawa A Sha'anoninta Har Dana Tsakaninta Da Zuciyarta Wadanda Suka Yi Kama Da 'ya'yan Cikin GORAN DUMA Wanda Sai Anfasa Za A Iya Lissafawa Tai Shige Da Fice A Duk Lungunan Zuciyarta Dakuma Magabatan Alamuranta Musamman Cikin Rayuwarta A Abuja Dakuma Milkway Danta Gano Ko Ta Taba Cin Karo Da Wannan Mai Kiran Kansa Mahaukacin Masoyi,amma A Sunan Manajansa Ya Shata Masa Wai Nazifi? Ta Shafa Sosai Ba Ta Tuna Shi Dinba Sai Can Ta Dan So Ta Tunano Shi Bayanta Tariyo Sha Biyar Ga Watan Nuwamba Na Shekarar Dubu Biyu Da Sha Biyu A Kwakwalwarta Shugaban Milkway Ya Fado Mata,amma Acikin Basaja Yadda Yanzu Zata Kasance Cikin Shakkunshine Nazifi Kokuma Wani Daban 15 Nov 2012 Sunyi Da Nusaiba Kanwar Mijin Yayarta Balaraba Zatazo Raka Ta Milkyway Dan Ta Siyo Ipad Satika Kadan Da Fara Rubutunta A Jaridar Aminiya Don Saukaka Mata Aiki,sai Nusaiba Taimata Waya Cewa Suhadu A Milkyway Ta Tsayar Da Motar Innarta Honda A Harabar Milkyway Tanemi Kiran Nusaiba A Waya Amma Saita Tarar Wayarta Ba Bu Ko Kobo Haka Tajima Zaune Cikin Motar Tana Waige Waigen Shigowar Nusaiba Dazama Yafara Gundurarta Saita Fito Ta Rumgume Hannu Ta Jingina Da Motar Tana Ta Faman Baza Idon Kan Motoci Da Mutanen Dake Shige Da Fice A Wajen,cikin Haka Wata Shudiyar Jeep Ta Shigo Harabar Milkyway Hade Da Tagumi Ta Tsura Mata Ido Har Tazo Ta Gifta Ta Kadan Tatsaya Kafin Kuma Ta Gifta Ta Din Ne Suka Hada Ido Da Matukin Motar,wani Matashi Baki Mai Dogon Hanci Da Fararen Idanuwa Yana Sanye da Bakin Wando Da Shudiyar Tshirt Da tambarin Mikyway Cafe Ta Kawar Da Kai Saidai Jikinta Ya Ci Gaba Da Batashi Baidauke Idanuwansa Daga Kanta Ba Harya Wuceta Kamar Mintuna Goma Bai Bude Motar Sa Yafito Ba Tana Tsaye Tana Ci Gaba Da Waige Waigenta Har Idonta Yazo Zagaye Kan Motar Sa Adaidai Lokacin da taGa Yana Gyaran Madubi Da Alama Ita Yake Karewa Kallo,ranta Yai Mugun Baci Har Ta Zabga Masa Harara A Duhu Tayi Tsaki Tare Da Duban Agogo Cikin Takaicin Nusaiba Asannanne Tasami Azancin Shiga Ciki Tasanya Kati A Wayarta Dan Kiran Nusaiba Ta Rufe Motarta Tanufi Ciki Agurguje Ya Rufe Mota Ya Biyo Bayanta Don Haka Takara Daga Kafa Dab Da Isarta Ta Waiga Saitaga Manaja Nadan Rusunawa Matashin Nan Yana Masa Barka Da Zuwa Tasake Hada Ido Da Shi Tadan Motsa Baki Alamar Bataji Dadi Ba Ka Share Yallaban Nan Yau Malam Kakira Ni Da Muhammd Kawai Domin Acikin Tarko Nake Neman Maitayani Yakin Kubuta Nake Batare Da Daddawar Da Na Kamo Ta Subuce Ba,bata Damu Da Zantikanta Da Suka Biyo Baya A Tsakanin Matashin Da Manaja Ba Domin Zaurance Suke Harma Da Sauya Harshe Zuwa French Wanda Gaisuwa Kawai Ta Iya Dashi A Cikin Zafin Nama Kuma Sai Gasu Gaban Kantar Lokacin da take Mika Dubu Dayan Katin Sun Dauke Hankalin Mai Bata Katin Dayimasa Zance Shima Cikin Harshen Da Bata Lakanta Ba Dan Haka Yakasa Dauko Mata Katin,ranki Yadade Barka Da Yau,inji Matashin Nan Wanda Yadamu Da Kallonta Bayan Yazo Dab Da Ita Ya Tsaya,,yauwa Barka Dai Kamar Nasan Fuskar Nanfa Afuwa Cankowa Nakeson Nayi Yasa Nadamu Da Kallanki, Ta Gyara Tsayuwa Da Kyar Ta Ce Hmm,,kamar Munyi Karatu Da Kyar Ta Ce,,hmm,,kamar Munyi Karatu Tare?Bata Tankamasa Ba,hm,,,bani Katin Mana,,, yadan Yi Turus Cikin Kallanta Sannan Ya Ce Ranki Yadade Kozaki Miko Min Wayar Na Kwashe Miki Lambobin Ansami Matsala A Katin munan Idan Ba Ai Taka Tsantsanba Batai nazarin Komai Ba Tamika Masa Wayar Karaf Manaja Ya Amshe Wai Shizai Samata Da Alama Na Takuramiki Ko? Ba Haka Bane Wai A Ina Mukai Karatun Tare? Alamar An Kureshi Ya Ce A Bayero Univer Sity Mun Karanci Aikin Jarida Wannan Yasa Tadan Sauko Harda Murmushi Hakane Yaya Bayan Rabu Sai Alkhairi Tuna Min Suna Ta Ce Cikin Kwanciyar Hankali Rumaisau Aliyu Ahmad Haka Kuwa Na Tuna Takara Dubansa Da Kyau Da Alama Tanada Shakku Saidai Yadda Yayi Fuska Saitaji BaBu Bukatar Ta Tambaye Shi Kokuma Tayi Ja Inja Dashi To Hausawa Sunce Bata Karya Wuya To Kuwa Ta Yafo Ta Harzuwa Lokacinda Za A RaBu Saura Dame? Sai In An Kuma Haduwa Haka,nikuma Sunana Nazifi Muhammad To Madallah Ta Tattara Dukan Hankalinta Ga Abokinsa Gajere Wanda Take Tsammanin Abinda Yake Da Wayarta Ya Wuce Loda Kati Ta Tsuke Fuska Ta Ce Masa Malam Yayadai? Kar Ka Wuce Gona Da Irifa!Yaki Dagowa Ya Dubeta Yana Bata Amsa Habadai Aimu Bamu Da Irin Ma Shimuke Nema Madam Yana Rufe Baki Yamika Mata Wayar Ta Karba Tana Tura Baki Bata Tanka Wa Kowa Ba Ta Bar Gurin Kwaji Dashi Tafada A Fili Ta Fice Daga Farfajiyar Tana Neman Nusaiba ,nusaiba Takaraso Suka Shiga Sayen Wayar Inda Batasamu Siyen Ipad Din Datai Niyya Bama Sakamakon Garabasar Waya Mai Tsada Da Suka Yi A Kananun Kudi Abinda Ta Iya Tunowa Kenan A 15 Nov 2013 Amma Tayi Ta Tuno Fuskar Sa Takasa Ballantana Ta Iya Tuno Ko Ta Kalli Kafarsta Taga Kofato Shiyasa Data Tuno Hakan Baiwani Sanyaya Mata Raiba Yadda Ranta Ke Jagule Saitaji Inama Ace Ta Wuce Kano Yau? Duk Tsiya A Yanzu Kano Tafi Abuja Kwanciyar Hankali Domin Basajar Kano Ta Waya Da Social Network Kawai Ake Mata Amma Ta Abuja Bayan Rainin Hankali Tattare Dake Databa Rai, Ta Karkare Ta Hadiye Damuwarta Bayan Ta Tarad Da Gudan Jininta Hamida Ba Bu Lfya Wani Kurji Ya Fito Mata A Kirji Tanata Faman Jinya Saita Fake Da Tausayin Hamida Ta Hada Kukan Tausayin Da Basajar Mahaukacin Masoyi Ta Ci Kuka Ta Koshi A Zuwan Ciwon Hamida Ki Gode Allah Kawai Da Ba Kauye Kika Bayar Da !Yar Riko Ba,munyi Tunanin Huda Mata Kirjin Nana A Gida Amma Muka Nufi Asibiti ashe Damunyi Hakan Da Danyen Hukunci Muka Yanke,inji Momin Ruma Ruma Ta Tsayar Da Kuka Tazaro Ido Cikin Mugun Kaduwa Lallai Allah Ya Tseratar Da Hamida Domin Da Anyi Hakan Akwai Matsala Saita Biyewa Momi Wajen Hamdala Ga Allah Har Washegarin Momi Najiran Jin Wani Abu Daga Ruma Akan Zuwanta Abuja Domin Hajiya Tasanar Mata Komai Amma Ruma Taki Tankawa Duk Da Cewa Ko Gabadaya Aka Duba A Jikinta Tana Nuna Damuwa Da Kasala Amma Iyakarta Haka Cikinta Mai Hadama Ya Hadiye Shi Kadai ya Hana Bakinta Furtawa Sai Ga Tama Tana Shirin Komawa Kano Momi Takasa Daurewa Saita Tareta Da Zancen Tunjiya Nake Kawaici Inajiran Jin Kin Furta Abinda Ke Damun Zuciyarki Da Rayuwarki Amma Ga Alama Kina Son Na Karya Billena Na Tambaya, Ruma Tayi Walai Da Ido Tana Murmushin Yake Lah! Mekika Gani Momi? . . Dan Aunty. GORAN DUMA (P 54) . . Ni Ba Bu Abindayake Damuna,kinganki Kuwa? Komai Naki Yana Nuna Damuwa Inana Ture Wayar Damukai Da Hajiya Kenan,ruma Tayi Kasake Bata Da Ta Cewa Tunda Hajiya Ta Burma Mata Ciki,momi Ma tadan Ja Fasali Fadamin Ruma Meke Faruwa? Naso Ace Saida Kikazo Gidan Nan Sannankika Nufi Sabgar Taka Kawoki Abuja Nayi Niyyar Sanyawa Abiki A Boye Aga Abinda zakiyi,amma Saikika Shammaci Niyyata Har Yanzu Ruma Bata Da Niyyar Tankawa So Ma Take Ta Fashe Da Kuka Saboda Tunano Yadda Tayi Kwanar Jinya Da Zuciyarta Kowa A Kuntace,kame Kamen Tashoshin Ainihin Mahaukacin Masoyi Ya Cunkushe Wa Kwakwalwar Amma Har Cajinta Yakare Bata Canko Wadda Zata famata Shi Tar Tar Ba Anya Wannan Rayuwar Zata Dore Ciki? Ta Ina Zata Bi Ta Kubuta? Kawai Sai ta sami Kanta Cikin Hawayen Momi Kam Tausayin Da Rauninta Akan Ruma Tana Hadiyewa Har Taci Nasarar Data Bata Kwarin Gwiwar Yimata Nasiha Zanyi Murna Idan Ba Tarkon Soyayya Kika Fada Ba Ruma Dan Banasan Kifada Tarkon Son Mutumin Da Bai Cancanta Ba Dan Baisan Muhimman cin ki Ba Haryaja Ragamar Rayuwarki Cikin Son Zuciyar Sa Kawai,mace Irinki Datafi Sauran Mata Rauni Tana Bukatar Taka Tsantsan Acikin Soyayya Kinfi Kowa Sani,aranta Ta Ce Kamar Momi Nasan Cinka Abinda Ke Wakana A Tsakaninta Da Mahaukacin Masoyi Saidai Kurkuren Lis Cewa Ita Tafada Tarkon So Ba Wata Hallitar Ce Tafada Tarkon Son Nata Ba Kila Momi Bata Taba Hasaso Ko Tarkon Sonka Aka Fada Kana Iya Shiga Hadariba Ta shiGa Goge Hawayenta Batare Data Kammala Tunaninba Inafatan Dazara Kinkoma Zaki Cikawa Hajiya Alkawarin da kika Daukar mata? Da Sauri Ruma Tadago Tayi Ma Momi Duban Rashin Fahimta Momi Tamike Tana Shirin Barin Wajen Tana Amsa Mata Tafadamin Kin Mata Alkawarin Kina Komawa Zaki Sanar Da Ita Dukkan Abinda Ke Akwai Ruma Tashi Ga Gyada Kai Batare Da Hayyaci Ba To To,,,,dama Bazan Karya Alkawari Ba, ************ tana Isa Kano Daidai Lokacindatake Shiga Harabar Gidansu Sakon Mahaukacin Masoyi Nafado Kasancewar Wayar Na Hannuta Cikin Dukan Zuciya Ta Kashe Ido Ta Hau Dubawa BARKA DA ISOWA RANKI YADADE,IDANKIN HUTA KILA ANJIMA NA SHIGO MUGA JUNA MAHAUKACIN MASOYI Bataji Bakinciki Kofargaba Game Da Sakonsa Ba Tadai Samikanta Cikin Saurin Shigewa Cikingida Wanda Batafara Mamakin Neman Dalilinsa Ba Sai Gata Tashiga Gidan Mutangida Nata Hidimar Murnar Yimata Maraba Rashinki Ko Na Awa Dayane Agidan Nan Kufai yake Mayaimin Da Gidan,inji Mubarak Koyai Dariya Amma Ruma Murmushin Yake Hajiya Tun Daga Shigowar Ruma Tadora Mata Ido Ta Cemasa Idan Tai Aure sai Muga Yadda Zakai Mubarak Zaiyi Magana Tatare Shi Kajira Nai Sallar Magariba Bar Tadin Ka Wuce Alwala Yawuce Yana Dariya Aima Zan Barta Ta Huta Sai Gobe Zamu Fanshe Hirar Kiyi Sallah Kici Abinci Muzauna Ko? Fuskarta Ba Bu Alamar Wasa Kilatayi Hakan Ne Dan Kar Ruma Takawo Mata Wargi Hakanyasa Ruma Tadinga Komai Cikin Fargaba Tana Saka Yadda Zata Sanar Da Hajiya Murdadden Labarinta Da Mahaukacin Masoyi A Kar She Tatarar Da Bata Da Zabi Illai Tasanar Mata Komai Tinda Tai Alkawari Da Wayarta Akai Tattaunawar Tadinga Nunawa Hajiya Komai Na Sakonninsa Duk Da Hajiya Takidime Amma Bai Hanata Magana Anutse Ba Meyasakika Ci Gaba Da Rike Wannan Abin A Zuciyarki Kekadai? Kuma Mekikaje Yi Abuja? Hajiya Taimata Karin Bayani Ikon Allah HajiYa Tafadi Cikin Jinjinawa Tare Da Nanata Kalmar Duk sunyi Shuru Zuciyar Kowanne Tai Nisa A Saka Wani Aikinda Zuciyartata Ta Hada Cikin Lissafin Shine,fargabar Allah Yasa Anjima Din Nasa Karta Zamo Tsakar Dare Dan Karya Bayyanar Mata Abinda Tafi Zatonsa,wato Aljani Ko Kadan Batason Ya Bayyana A Haka Batare Da Dalilin Tsoronsa A Aljani Ba Saitare Da Dalilin In Aljanin Ne Sun Rabu Kenan,inkin Amince In Sanar da Alhji Wanna Katon Labari In Ganin Dole Maza Su Shigo Ciki Hajiya Ta Katsewa Ruma Tunani Duk Da Ita Ma Bata Hattama Nata Tunanin Ba,amma Tasanya Masa Karfi,mujira Yau Da Gobe Da Jibi Dan Ganin Abinda Zai Biyo Baya,karmu Tashi Hankalin Kowa Hajiya Kila Lamarin Baikai Natashin Hankali Ba,yaya Zanyi Da Mominki Mai Jiran Nakai Mata Kanun Matsalarki? Hankalin Momi Atashe,,,rumaisau Rumaisau Tamike Cikin Alamun Son Ficewa Daga Falon Fuskarta Na Nuna Gajiyar Jiki Data Zuciya Ki Kyale Ta Kawai Hajiya Yadda Momi Take Damuwa Cikin Matsalolina Inason Duk Abinda Zataji Akaina Indai Zan Iya To Taji Mai Dadi,,shikenan hajiya Ta Fada Badan Taso Ba Ta Bi Ruma Da Kallo Har Ta Kule Tanadan Dingisa Kafarta Wadda Kem Bayan Kwanar Fargaba Tare Da Tsammanin Bango Zai tsage Mahaukacin Masoyi Ya Bullo Ruma Batasami Bacci Ba Saikarfe Hudu Saura Hakan Ya Janyo Da Kyar Ta Iya Katse Bacci Ta Gabatar Da Sallar Asuba Akan Lokaci Sannan Ta Koma Ta Ci Gaba Da Ramuwar Bacci,karfe Tara Daidai Wayarta Ta Farkar Da Ita Da Shigowar Kira Saidata Koshi Da Kallon Agogo Har Kiranya Katse Sannan Tasami Taba Wayar Daidai Lokacin Wani Kiran Yasake Shigowa Ta Daure Ta Hadiye Kasalarta Ta Daga Tare Da Sallama Yushau Ya Amsa Cikin Kuzari Nayi Ta Baza Ido Inganki Gidan Atika Jiya Har Dare Bangankiba Kuma Naji Atika Ma Na Mitar Baki Zo Dubata Ba,ta Basar Ta Ce Yau Zanje,yushau Yadan Jinkirta Sannan Ya Ce Karfe Nawa? Ina Son Mu Hadu Ne Akwai Muhimmiyar Maganar Danake Son Mu Tattauna,bansan Lokacin Dazan Shiga Ba Tafada A Raunane,amma Ta Raunana Muryar Tatane Dan Ta Basar Da Zuciyarta Wadda Ta Dauki Zafi Inta Bar Muryarta Dazafi Kila Ya Rage Mata Kima Shikuma Saiya Marairaice Kidaure Ki Tsara Lokaci Shigar Taki Ko Saboda Ni, Ba Lokaci Zanzo In Batamiki Ba Ruma Ragowar Rayuwarmu Nakeson Muyi Wa Garambawul, tayi Iyakar Bakin Kokarinta Tai Magana Amma Takasa Don Kar Ta Cika Rashin Mutunci Da Kyar Ta Ce Ok Yushau Baidamuba Yasake Zagewa Da Rarrashi Ko Wuni Zakiyi? E,h Wuni Zanyi Toki Saka Idan Ganina Bayan Laasar Yayi Kyau Ta Amsa Masa Ta Kashe Wayar ******* A Gaggauce Yushau Yahau Shirin Fita Alhali Ya Shaidawa Sumoli Yaukansa Ciwo Yake Kodake Da Biyu Ya Ce Haka Dankartadameshi Yasamu Damar Yin Tunani Hanyar Dazasu Samo Masa Ruma Na Biyu Kuma Mugun Haushinta Yakeji,jiya Ya Dauketa Yakaita Gidan Atika Da Kwadayin Haduwa Da Ruma Yadinga Zarya A Gidan Tsammanin Ganinta Amma Har Dare Ba Bu Labarinta Ta Ce Masa Kaikuwa Dan Allah Ko Bazaka Sauya Motar Nan Ka Daure Kakai Ta Gareji Adan Kwaskware Injinta Ayimata Sabon Fenti Fisabilillahi Kai Ko Kunya Bakaji Kowa A Danginka Shar Shar Da Motocin Nunawa Sa,a Amma Kaikana Fama Da Karfen Shekaru Aru Aru Haka Zuciyar Yushau Ke Tafarfasa Daidai Yadda Sumoli Take Masa Magana Tunda Uban Wani Bai Sayi Shar Ya Baniba Sai A Kalleni Da Wanda Allah Ya Bani Sai Dai Idan Anga Ban Cancanci Zama A Irin Wannan Duniyar Da Wannan Motar Ba To A Iya Kokarin Rufe Ido A Bude Kar Aganni, ai Bakafadi Ba Yushau Idan Ka Saka Wa Ubana Da Zagi Da Cin Fuska Tunda Yadauki Aure Yabaka Da Wuya Ba Bu Dadi Ina Zaune Ina Rufa Maka Asiri Yakada Kai Cikin Fushi Sumoli Takara Da Cewa In Ma Sake Zagina Zakai Yushau Zageni Mana,,,, insauran Gashin Kumarka Bai sanyani Kuka Zaginka Ai Bazai saniba Karamin Misali Auranmu Kusan Shekaru Uku Banta Ba Batan Wata Ba Amma Dan Masifar Mammako Sha Katafi Kakasa Kai Ni A Nemo Dalilin Rashin Haihuwata,,.,,ta Dawo Cikin Kwalliya Malam Inakake Shirin Zuwa Bayan Kace Bakajin Dadi Ya Cemata Yasamu Kiran Gaggawa Daga Office Ta Ce Bara Nadauko Mayafi Mufita Tare Inba Gidanku Zakaje Ba,gidan Dakana Rabe Rabe Kana Komai Amma Baka Kasa Motsa Kwanjin Son Zawarci Ba,yafice Bai Tanka Ba Tadawo Da Mayafi Ya Ce Wai Malama Ina Zakibine? Muje Kasaukeni Gidan Atika mana Kashiga Ka Biya Kudin Lesunan Ankon Suna.... , dan kari, ni ma dole naje gidan Atikar nan nasha kallon yadda zata kaya, ko da akwai pasinja anan gidan?? . Dan Aunty. GORAN DUMA (P .55) . . Dubu Nawa? Dubu Arbain Da Takwas Mana Ta Amsa Masa Kai Tsaye Tana Taunar Cingam Kas Kas,cikin Tsawa Ya Ce Daga Dubu Goma Bazan Karamiki Ko Ficika Ba In Baki Da Kudi Ki Mayar Musu Kayansu Ba Bu Jimawa Sai Gata Tadawo Dauke Da Lesunan Ta Zube Masa Kan Gado Cikin Fusata Gasunan Katafi Dasu Ka Mayar Bani Dubu Goman Zanbi Wata Hanyar In Samo,ai In Na Ce Dakai Zan Dogara Har Abada Araba Danni Zan

Chapter 17 of 21