Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kuka ya dinga fizgirta, amma ita ma ta dinga hadiye shi, a karshe cikin rawar murya ta ce. "Yaya Yusha'u me nake yi na zafi haka?".... Dan Aunty. GORAN DUMA (P 32) . . Ya tsare ta da ido, ya ce. "Tsakaninki da Allah idan Auwal ne za ki zauna da cikinsa tsawon wata biyu ba ki sanar da shi ya yi farin ciki ba?" Takaici da rauni ya cikata, dan haka ta saka masa ido ta kasa tanka masa. Ya ce. "Ki amsa min mana!" Ta girgiza kai tana dubansa kai tsaye da alama ya fara 'kure ta. Ta ce masa. "Idan na amsa wata'kila kai tsaye ka yiwa amsar tawa kallon wautacciya, in daga zuciyata kai tsaye amsa zata fito." Cikin gadara ya ce. "Idan ma a haukace zata fito ina jiranta. Na kuma tabbatar ba zata sauya daga yadda na zace ta ba". Hawayen idonta ya fara gangarowa, tana kallonsa kai tsaye ta ce. "In da Auwal ne ba zan kai tsawon wata biyu da ciki ba tare da ya binciko da kansa da kansa ba, cikin wata biyun nan wanne irin amai ne bana yi, wanne irin zazza6i ne ba na yi, wacce irin kasala ce bana yi? Yaya Yusha'u duk sanda zan gabatar maka da wadannan matsaloli 'kar'kari ka ce min ok Sannu, Allah Ya sauwa'ke sai ka ga na galaibata ne kake kawo min maganin shawara, ko kuma tarkacen magunguna daga kyamis... Saboda haka ne sam ba ni da 'karfin gwiwar sanar maka da wani abu da ya dangance ni..." Rumaisa'u bata kula ba ne, tuni Yusha'u ya zo wuya taf! Tana direwa kuma ya fara zubar da bala'in da ya 'kunshe. "Ka ji ba! Rumasa'u ni kike fadawa wannan maganganun saboda rashin ladabi ko? Saboda tsabar ke butulu ce wacce irin kulawa ce bana yi miki? Duk namiji ne zai jure wannan jarabar laulayin naki amma ina iyakacin kokarina kina nuna min na gaza, kuma saboda tsabar raini ki keta idona ki nuna Auwal ya fi ni matsayi a gurinki?... Dadin abin ya gama yi miki nisa, duk yadda kike jin fitsara dai ba zaki dauko gawarsa ki gina mata daki a cikin gidan nan ki ce kishiya ne shi ba...." Bai ko saurareta ba fuuu! Ya fice ya bar dakin sai ya bar ta da binsa da kallo, lokaci guda kuma hawayenta ya dauke saboda maimaita kalmar KISHIYATA da Yusha'u ya ambata tare da tuno yadda Auwal yake ambaton kalmar da KISHIYI. Kusan sati guda Yusha'u na gaba da Rumaisa'u, ba gabar magana ba har da na dauke hannu a shigo mata da abubuwan masarufi dangin ciye-ciyen kayan gina jiki, kaza, balangu, kifi da kayan itaciya, ''Inko hakane gwara ya daina fita. Don ni ban ga amfanin dukiyar da iyalina ba zasu amfaneta ba'' wadanda su kadai ne ba ta rasa ba a abin da ya kamata kada sickler ya rasa su, saboda haka 'kanjikinta ya 'karu, ga nata na asali ga na raunin ciki sannan ga na 6acin rai. Suka sake share wasu sati biyun a haka, bayan muguwar rama yanzu ta fara d'ashewa alamun jini ya yi mata 'karanci, babu ciwo dai sosai, sai yawan kwanciya da bin sanyi wanda shi ma alamu ne na 'karancin jini a jikin sickler. A karo na hudu da Innarta ta kirata dan ta ji batun zuwansu asibiti, sai ta fada mata gaskiya don 'karya ta kan fada mata cewa 'mun je', yau cikin kuka sai ta fada mata. "Wallahi Momi ko soron 'kofar gida ban taka da sunan asibiti ba, a halin yanzu kuma ina cikin wani hali dan ina ganin alamomin rashin jini... Amma don Allah Momi mu nemi wata shawarar kar ki yiwa Yaya Yusha'u magana, tuhumata yake da kai 'kararsa." Momi ta rasa abin da zata ce saboda mugun takaici, kawai sai ta ja numfashi ta ce. "Shikenan, ba ni awa daya na yi tunani zan kira ki". Ba ta ko jira cewar Rumasa'u ba ta kashe wayar, kai tsaye kuma ta kira Yusha'u cikin tsananin fushi, ko gaisuwarsa ba ta amsa ba, ta ce. "Yusha'u ka tuna na ta6a fada maka cewa, ina da juriya akan komai amma ban da akan Rumasa'u? Zan iya yi maka kawaici akan komai amma ban da na wasa da ranta, mun shiga sati na uku a maganar da na yi maka ba ku nemi hanyar asibiti ba, yanzu da na tuntubeta ta tabbatar min tana tare da alamomin 'karancin jini. Wallahi Yusha'u ba zan iya zuba ido ka yi min sanadin Rumasa'u ba..." Muryarsa a tausashe, amma maganarsa zazzafa dan cewa ya yi. "Ai babu mai iya kashe wani sai Allah!" A fusace Momi ta ce masa. "Au haka ka ce? Shikenan Allah Ya kaimu gobe ni kuma zan zo in nuna iyawata akan hanawa ka zama silar Rumaisa'u, in ma ka 6oye manufar shirya kasheta ne saboda an aura maka ita bisa tilas ni zan yi maka gatan rabaka da aurenta..." Ba ta ko jira cewarsa ba ta kashe wayar, nan take ya hada gumi kashir6an dan ya san Momi ba wa'ka take ba, zazzafar mace ce shigen mahaifinsa. Tsab zata zo kuma ta dauke Rumaisa'u dole kuma maganar ta je kunnen mahaifinsa, wanda zai iya mummunar sa6a masa. Bai yi dogon nazari ba ya hau kiran Momi tana 'kin amsa kiran nasa, shi kuma ya nace cikin tsabar dakan zuciya, amma yana mita. "Mahaifin Rumasa'u ya zama hoto, dama yawancin masu d'amarar nan matansu ke juya su, haba me za a yi da auren 'yar mace?" Ire-iren mitar da ya dinga yi ke nan yana nacin kiran wayar Momi, kusan sau ashirin sannan ta daure ta daga. A ladabce ya ce. "Don Allah Momi ki yi hakuri, wallahi za a yi yau din nan ba zamu kwanta ba sai an je asibiti, na rantse miki". Ta sauke hucin 6acin rai, sannan cikin lumana ta ce. "Yusha'u ka yi tunani da kyau, bai kamata sai an yi yun'kurin gwada maka 'karfi zaka tausaya wa 'yar uwarka ka yi mata abin da ya kamata ba, ko babu igiyar aurenka akan Rumaisa'u ai abar ka tausaya mata ce, yanzu ta ce min jininta ya yi 'kasa sosai, idan aka sake nan da kwana biyu, sai dai ka ji batun yi mata 'karin jini". Cikin 'kas'kantar da murya ya ce. "In Allah Ya so ba za akai wannan matakin ba Momi, ki yi hakuri". Cikin sakewar Murya ta ce."To na yi, Allah Ya yi muku albarka". Da ya koma gida da yamma, Rumasa'u ta kawo masa abinci a dakinsa sai ya dinga satar kallonta. Ta yi mugun ramewa, sannan ta yi wani irin fari, idanunta kuma sun yi wani 6ulu-6ulu sun kukkunbura. Ta zauna jim amma kafin ya 'karasa cin abincin sai ta tashi ta koma dakinta ta kwanta, yanzu babu abin da yake mata dad'i sai kwanciya, hatta dan karance-karancen jaridu da mujallun da ta ke samun yi a da yanzu gagararta yake, duk da ma dai Mubarak me daukar nauyin kawo mata jaridun jarabawa ta 6oye shi. A haka ta jiyo motsin shigowar Yusha'u, haka kawai sai ta ji gabanta na faduwa dan ta ha'ki'kance da kyar idan ba gadar mata da wani takaicin ya kawo shi ba. Sai dai ya shigo dakin cikin sakin fuska ya nemi stool ya zauna idonsa a kanta, ta dan dube shi da kyau sannan ta lumshe ido. Ya yanke shirunsa da cewa. "Kwanciyarki ta yi yawa, ko yaushe ke kenan a akwance". Ta bude ido ta dube shi, amma ta kasa cewa da shi komai. Ya sauke numfashi ya ce. "Jaridancinki dai a gidan aurenki da mijin aurenki kike sauke shi. A zamanmu dad'i da wahalarmu gaba daya babu na sirri kunnen iyayenmu da 'kawaye kaiconki Rumaisa'u, wallahi ba ki morre hali ba..." . Dan Aunty.GORAN DUMA (P 33) , , Ta kokarta ta tashi zaune ba tare da ta shirya ba ta ji kuka ya kwace mata babu kakkautawa, yana kallonta zuru yana dokin ta yi shiru har kukan nata ya fara ta6a ransa, babu shiri ya cimmata ya fara rarrashi. "Ki yi hakuri ni ban fada dan cin fuskarki ba, na fada ne dan ki ankara da laifi da cutarwar da ki ke min fisabilillahi ina mutunci a ce duk sirrin gidanmu a kunnen Hajiya, Momi da sauran dangi da 'kawaye..." Ta dakatar da shi cikin kuka. "Ba gudun cin fuska ya ba ni kuka ba Yaya Yusha'u, illa mummunar shaidar da ka yi min a matsayinka na mijina har kana tir da halina.... rayuwar nan ba ta da garanti musamman ta mutum irina... Idan Allah Ya kar6i raina yanzu wannan shaidar 'kila ta yi tasiri a kaina... Dole in yi kuka dan ban san yadda zan gyara ka yarda da ni ba". Ya 'kara tausasa murya ya ce. "Ki daina kai 'karata gurin Momi ko Hajiya, ki dinga 6oye sirrin gidanmu ba fa jahila ba ce ke Rumasa'u, kin sani yana daga nagatar mace 6oye sirrin mijinta..." Ta jima tana kallonsa cikin hawaye, sannan ta kwace kafadarta ta koma ta kwanta alamar ta ma rasa abin da zata ce. Ya yi saurin dagota ya ce. "Babu abin da zaki ce?" Yana rufe baki ta amsa. "Idan in ce dan in kare kaina ne ba zan ce din ba, dan kar mu ci gaba da 6atawa juna lokaci, amma zan iya cewar da zata iya zame maka wani nauyi a ayyukanka biyu na duniya da lahira cewar tawa ita ce, duk matsananin halin da zan shiga kuma duk yadda Momi zata kwakkwafe ni ta ji matsalata ba zan kuma fada mata ba, in ka kula da ni kanka Yaya Yusha'u, in ka yi sakacin da na rasa raina sai ka shirya amsa tambaya wajen Ubangiji fa'kat!" Yusha'u ya yi wuri-wuri ya rasa abin da zai ce mata, sai da kyar ya lalubo shi. "Abin da kika fadawa Momi ke nan ina sakaci da ranki? Amma sam ba ki yi min adalci ba Rumaisa'u". Ta goge hawayenta duk da wasu sun kuma kunnonwa, ta dube shi ta ce. "Kana dai so sai na kare kaina ko? To ka san dai mutum ba zai rayu ba sai da jini? Dube ni". Ta shiga gwale idonta fatar ba'kinta tare da nuna masa tafukan hannayenta, sannan ta dora. "Jinina ya yi 'kasa sosai, da ko ba ni da ciki dab nake da shiga mawuyacin halin da zai kai ni matsayin 'karin jini. An yi maka batun fa'idar zuwana asibiti tun sayi biyu da suka wuce ba ka dauki batun da muhimmanci ba, ban yi tsammanin zai zama laifi ba dan Momi ta binciki halin da nake ciki na sanar mata ina da matsalar rashin jini, ko babu komai ya fi sama ta ka a ce musu ga ni kwance ana 'kara min jini... ko su zo su bayar da jini a 'kara min". Da ya rasa bakin magana sai ya fanshe akan kalamanta na 'karshe. "Lokacin da ba ki karkashin ikona ma na ba ki jini Rumasa'u bare ki yi min gori... in leda goma ne zan iya baki ba leda daya ko biyu ba". Yana rufe baki ta amsa masa. "Rigafi ai ya fi magani". Ya ce, "Me kike nufi?" Ta amsa masa, "Ka yi tattalina kar na rasa jini ya fi burgewa akan ka bar ni na rasa ka bayar da leda goma a 'kara min". Yanzu ya rasa abin da zai ce mata bilha'k'ki, sai ya 6uge da duban agogo lokacin da aka rera kiran sallar magriba, ya wuce kai tsaye batare da ya kare kansa ba. Abin mamaki ba ya 'karewa a duniya, karfe tara na dare Yusha'u ya shigo mata da Dan'Isiya mai kyamis a nan unguwarsu dauke da akwatin magunguna da allurai. Dan Isiya ya tsare ta da lacca da hudubobi bayan ya gama karade ta da tambayoyin da ake wa sababbin zuwa awon haihuwa, mata masu lafiya ba sicklers ba. Kallonsa kawai ta ke kamar wani duron ya'kin neman za6e, wani lokacin kuma ta sauke ganinta akan Yusha'u wanda ya hakimce shi a dole ya yi abin arzi'ki. A karshe Dan Isiya ya ce, tun da cikin bai kai ko wata uku ba ba sai an yi awo ba, yanzu zai dauki jininta ya tafi da shi lab. gobe zai kuma yi mata allura yanzu sannan ya bata magunguna musamman na 'karin jini. Duk Rumaisa'u na kallonsa bambarakwai har ya fito da sirinji ya zu'ki jininta, sai da ya zu'ko allurar da zai mata ne sannan ta magantu. "Tun safe ban ci abinci ba bai kamata a yi min allura ba, zai fi kyau a bari sai gobe". Dan Isiya ya mayar da ruwan allura cikin kwalba yana cewa. "Eh gaskiya ne, in Allah Ya kaimu goben sai na zo na yi miki". Yusha'u kuma ya ce. Amma kina kallonsa ya zu'ko? To ya zauna ya jira kici abincin mana ya yi miki..." Ta girgiza kai ba tare da ta dube shi ba, ta ce. "Nidai sai gobe". Dole ya kyale ta, ya mayar da hankali ga Dan Isiya da ke zube masa magunguna yana masa bayaninsu. Yusha'u ya ce. Ina fatan akwai na 'karin jini?" "Akwai". Yusha'u ya ce masa. "Yauwa, ka hada mata da maganin kasala da na 'karfin jiki ba ta da aiki sai kwanciya". Nan ma Dan Isiya ya ce. "Duk akwai". Ya dure musu magunguna tuli a leda ya mi'kawa Yusha'u, shi kuma ya mikawa Rumasa'u ya wuce raka Dan Isiya. Ya dawo mata da gasasshen nama da nonon roba mai sanyi. Da kansa ya nemi faranti a kicin ya zuba naman ya kawo ruwa da lemo ya zube, sannan ya ce mata. "Ki zo ki ci ki samu ki sha magani". Tun da ta ga 6arin jikin da ya ke ta san ba na Allah da Annabi ba ne, tattalin raya darensa kawai yake, dan haka ta zage ta yiwa naman cin 'koshi cikin 6oye 6acin zuciya, dan ta san idan ma ba ta taimaki kanta ta ci ba babu abin da Yusha'u zai raga mata, gara ma ta kori yunwa ko ta rage wa kanta wahala. Har ta gama cin naman da fargabar abubuwa biyu, wato yadda zata ji jiki a shimfidarsu da kuma yadda zata gujewa shan wadannan magungunan da wata 'kila in ta sha su yi ajalinta. Bayan ta gama ya dauke farantan da tarkacen kayan da ta sha lemo da yagot, sannan ya dawo ya janyo ruwa ya janyo ruwa ya tsiyaya mata a tambulan kana ya janyo ledar magunguna ya fara 6alla. Kijrinta sai dakan uku-uku ya ke ta dube shi ta ce. "Yaya Yusha'u har na gaji da gaya maka ba na shan maganin da duk ba likita ne ya rubuta min ba". Ya tsayar da 6allo maganin sororo yana kallonta, cikin hadiye bacin rai ya ce. "Da yake nan ya ba ki wadannan magungunan? Dauko miki shi da na yi har gida bai zama garkuwar da zaki zarge ni da shi ba musan abin da muke ba?" Ta girgiza kai a raunane, tace. "Likita daban mai kyamis daban Yaya Yusha'u, in ya san abin da yake yi na tabbatar ba lallai ya san yadda ya kamata tafiyar da sickler ba...." Ya tare ta da alamar rarrashi, Rumaisa'u bata zargi karya ba, ya yi kewarta yana kuma son ya fanshe a yau, dan haka ya 'ki su yi fada, ya ce mata. "Tun da kin iya karatu kin kuma san kan magungunan me yasa ba zaki dube su ki gani idan ya yi miki ganganci ba?" Tun da an ce Mutum ba ya 'kin ta mutane, ta mika hannu ta kar6i magungunan na farko da ta dago sai ta tarar capsil ne na 'karin jini. Ta daga maganin tana duban Yusha'u fuskarta cike da takaici ta ce. "Daga inda ya dauki maganin karin jini ya ba ni na san bai san aikinsa ba..." Yusha'u ya tareta cikin tsabar mamaki. "Amma dai ke kika ce kina da 'karancin jini ko?" Ta amsa masa cikin sabawa da takaici. . Abbas Abdulkadir Hada Hada ( Dan Aunty.) GORAN DUMA (P 34) . . Ta amsa masa cikin sabawa da takaici. "Ba zan iya 'kirga sau nawa na yi 'karancin jini daga haihuwata zuwa yau ba, amma ko sau daya likita bai ta6a ba ni maganin 'karin jini ba, sickler ba ya bu'katar maganin 'karin jini, domin cikin kowanne irin maganin yana dauke da sinadarin Iron, su kuma sicklers suka sha maganin 'karin jini to jininsu zai daskare kamar gasara, abin da zai faru da su kuma Allah ne kadai zai iya faru da su kuma Allah ne kadai zai iya iyakance shi". Yusha'u ya yi shiru kawai yana kallonta, ba wai bai yarda a ita ba, amma in ya bi ta kamar ya fadi, sai dai dole faduwar zai yi, dan a yanzu rashin dabara ne ya jagula mata rai, sai ya daure kamar wani soko ya ce. "Shikenan sai ki duba sauran". Ta mayar da maganin 'karin jini cikin ledar, tana cewa. "Ka yi hakuri Yaya Yusha'u, babu maganin da zan iya sha a ciki, in na sha na jefa rayuwata cikin hatsari". Yanzu Yusha'u ya kasa hadiye 6acin ransa, dan har ga Allah yana ganin Rumasa'u amfani ta ke da zurfin iliminta tana nuna masa iyakarsa, komai ya yi bai iya ba dan tsabar rainin hankali ita da ta karanci jarida wai ita ce zata kushe wanda ya karanci lafiya. Ta kushe wannan ta kushe wancan komai cikin gadara kamar wata uwar mutane. Ya yi kokari ya rage zafin 6acin ransa a muryarsa, ya ce mata. "Amma dai idan kin yi min haka ba ki yi min adalci ba, kawai dan ki nunawa duniya kina iko dani, kina kallo in kawo mutumin duk ba ki musa ba sai bayan tafiyarsa ki ce ba kya son aikin in mayar masa da magungunansa? Wannan ai ya yi kama da wulakanci..." Ta katse shi a sanyaye. "Yaya Yusha'u idan na katse hanzarinka a gabansa shi ne wulakanci, gara in bari ya tafi muyi komai mu biyu... wai ma don Allah Yaya Yusha'u har sau nawa zan fada maka ba na shan magani kai tsaye? Tsawon zama a gidanku ka ta6a ganina a kyamis...?" Shi ma ya tare da tsawa. "Ban sani ba! Ni dai kin wulakanta ni, abin da nake ta gudu ke nan, duk mai zurfin karatu ta 'kalubalanci mijinta, ta yi jayayya da shi, ko ta raina masa azanci sunnarta ce, kamar ni ma ban ta6a allin nan ba.... Haba! Ban da kaddara me zai kai ni? Ba gara ma mutum ya tafi kauye ya auro ba". In dai da sabo ya kamata Rumaisa'u ta saba da wannan gori da cin fuskar, duk kuma 6igiren son zuciya da rashin gaskiya. Tun kafin abin ya yi tsawo ai ta mi'ke ta bar masa falon ba tare da ta ce ci-kanka ba, ta shiga bandaki ta wanke baki, sannan ta bi lafiyar gado tana addu'ar Allah Ya sa ma ya yi zuciya ya tafi dakinsa ta huta. Sai dai addu'ar tata ba ta kar6u ba, dan ko mintuna ashirin ba ta yi da kwanciya ba ya shigo ya sauya kayan kwanciya, ya zauna bakin gado ya ce mata. "Yanzu ya ya kike so a yi?" Ta dan zura masa ido sannan ta ce. "Da me?" Ya ce, "Da maganar 'karancin jinin bana son a kai ga maganar sai an 'kara miki jini". Ta yi murmushin gajiya da abu daya, ta ce. "Idan ba zan yi laifi ba kuma ba zai zama umarni na ba ka ba, asibiti ya kamata na je gobe". Ya janye mata abin rufa ya fara murza tafin kafarta yana cewa. "To ya ya zan yi? Ai kawai na zama mijin ta ce sam-sam ba na yi miki kwarjini. In Allah Ya kaimu gobe sai mu je asibitin." Ta janye kafarta tana 'karamar dariya. "Allah Ya kai mu goben. Yanzu sai ka tashi ka tafi dakinka..." Ya tare ta lokacin da ya fara nade su cikin bargon. "Haba yarinya kin ma isa, ai rashin kwanjin nawa bai kai nan ba". Da sapiyar ranar sai ya nemi hanzarin cewa na manta yau akwai ni da zuwa rogo, satin da ya wuce Alh yayi min maganar kaddamar da wata rijiya da yake a waya ne bai min cikakken bayani ba, sai naje naji, ki bari idan na dawo da yamma sai muje asibitin, ta kada kai da sauri cikin bugun zuciya , rijiyar Awwal ce ta kuma tabbatar idan Yushau ya jiyo gaskiyar maganar Allah ne kadai ya san yadda zai tashi hankalinsu. Saboda haka ta wuni cikin zullumi da tashin hankali gami da pargaba, lallai kuwa' yushau ya shigo gida karpe goma na dare puskar nan tasa kamar an saukar masa sakon mutuwa ko hutawa baiyi ba ya para surparta da bala'i irin wanda bai taba yi mata kamar sa ba, tun tana kokarin kare kanta har ta zubo masa ido tana kallo cike da tsabar bakin ciki a tsukun wannan lokacin da za a kawo mata tayin mutuwa babu abin da zai hana ta amsa, sai sha daya da kusan rabi ya hakura ya tapi dakin sa yana ta mita, wai don me tana auren sa tana auren soyayyar wani har da irin wadannan sadaukarwar da ya rantse kuma ko kwatar abin da tayiwa Awwal shi bazata iya yi masa ba, lokacin da yake bala'in idon Rumaisau a kekeshe yake babu alamun kuka saboda masipar bacin rai, sai bayan pitarsa ta samu kukan ya goce mata, ta dinga yi babu kakkautawa dan ta hakkake duk rashinsa ya jepata cikin wadannan masipun auren Yushau ke wa sila. Da akwai Awwal kila da yanzu tana daga cikin matan da za a lissapa su a sahun parko na jin dadi da sa'ar miji, amma yanzu ratuwarta da lapiyarta na wani hali na tsaka mai wuya, wajen karpe biyun dare ta nupi dakin kwana saboda jin numpashinta na shakewa, da zummar tilasta kanta bacci dan ta manta wadannan bacin ran ko dan kai lapiyarta ta sami nakasu. Sai dai da alama ta makara dan numpashinta yaci gaba da shakewa lokaci daya kuma cikinta yayi wani irin juyawa tape da ciwo sai ga damshi-damshi ta sami kanta a ciki, nan da nan ta para ambaton Innalillahi wa inna ilaihi rajiun . Ta san lallai tana cikin tsaka mai wiya, bari zatayi, zata bubar da jini alhali dama bai ishe ta ba, ta barke da kuka ta isa bandaki kamar dama ana jiran ta shiga bandalin ne jini ya balle , tun tana tararradin rasa gudan jininta (wato danta) har ta dawo pargabar tsira da ran ta, saboda yadda xiwon ciki ya addabe ta ,jini kuma yaki tsayawa har numpashinta na neman daukewa. Da rarrape ta sawo dakinta ta janyo waya sai ta rasa ma wanda zata buga ta sanarwa , ko yushau bai gargade ta sanar da iyayen su halin da take ciki ba, ita kuma tai alkawarin ko zata mutu ba zata kuma sanar da su din ba. To idan ta kira wani a yanzu ta pada masa wannan mummunan labarin sai sun tuhumi ina yushauu ? Ko wacce irin laya za a yi musu sai sun parke. Numpaninta na kokarin kubucewa ta dinga kiran yushau yana kallon kiran yana sharewa, kusan sau goma sai da kyar ya daga cikin tsaki sai dai a wannan lokacin ta para pita hayyacinta sai ta kasa magana illa wata irin sheshsheka,,,, nan da nan yushau ya dawo cikin azancinsa da gudu ya watsar da wayar ya doshi dakinta ya same ta kwance gaban gado cikin jini a sume. Halin da ya same ta shi kansa ba dan yana jar zuciya ba kila ya sume cikin tsabar rikita da barin jiki ya dago ta yana padin na shiga uku zan kashe yar mutane,babu bata lokaci ya janyo durowa ya dauki ID card dinta na shaidar kasancewarta sikila da gudu ya pice ya pita da mota, sannan ya dawo ya dauke ta ya nupi asibitin nasarawa, da yake akwai group din jininta a jikin Id card dinta ba a tsaya jiran diban na yushau ba aka makala mata wani. Har azahar na washegarin ranar Rumasa'u tana cikin wani hali na kasa gane kai, Yusha'u ya yi nadamar abin da ya yi matu'ka, musamman da ya sami tabbacin cikin Rumasa'u ya zube, hannun agogonsa ya koma baya a matsayinsa na mai dokin ganin dan kai. Tun sha biyun rana Mummy ta sauka cike da tashin hankali wanda ta yiwa Yusha'u kallon tsana a fakaice ba, babu wanda ya san tana yi idan ka dauke shi Yusha'u. Da azahar da suka sami damar shiga dakin kowa cikin jimami, Hajiya da iyalanta kaf in ka dauke Mubarak da tilas ya je makaranta, ga Alhaji ga Mummyn Rumasa'u tare da Balaraba. Ko zama Mummy ta kasa yi tana tsaye rungume da hannnu ta 'kurawa ledar jinin da ake 'karawa Rumasa ido, idon Mummy ya fara fitar da kwalla saboda tsabar tausayin 'yarta. Ta ji a ranta akwai sakaci cikin hatsarin da ya faru da 'yarta, sakacin da ta tabbata ba 'karshensa ke nan ba, za a kuma wani dan Yusha'u mutum ne mai taurin kai da wasa da al'amura cikinsu har da rai. An dai gaya mata silar hatsarin daga bakin Hajia iya ma kamar yadda Yusha'u ya fada mata cewa. "Ana dan zafi, ita kuma kin san ba a kunna mata fanka, sai na ce ta tafi dakinta ni ina son kunna fanka. Ina bacci kwatsam ta kira ni a waya na ji muryarta cikin wani hali kafin na 'karasa dakin na tarar da ita a sume." Sam Momi ta kasa gamsuwa da wannan fatawar. Ranta kuma ya yi mugun 6acin da ta ke jin lallai sai ta bude kwanji a kan 'yarta in ba haka ba Yusha'u zai yi mata sanadinta ko da yake cuta ba mutuwa ba ce, amma zai iya yiwuwa ta 'kare rayuwarta cikin wahala saboda rashin kulawa. Idonta cike da kwalla ta sauke ganinta a kan Yusha'u da ke zaune kan kujerar da ke gaban gadon Rumaisa'u, ta ce masa. "Yusha'u me ya faru ne wannan tsausayin ya afku?" Yusha'u ya kasa hada ido da ita, ya kwaso in'ina. "Wallahi Mummy... Muna kwance ta tashi ta.... shiga bandaki kawai ta fara kwala min kira kafin na farga ta fadi a nan wajen..." Hajiya da su Atika suka ware ido suna kallonsa, tun daga nan jikin Hajiya ya yi sanyi ta tabbatar akwai wani abu da Yusha'u ke 6oye wa tunda har ya yi baki biyu haka, Alhaji ma ya dan kalli Hajiya ya basar cikinsu babu wanda ya tanka. Mummy ta 'kara tayar da ganinta sosai akan Yusha'u, ta ce. "Shin kun je asibiti kuwa kamar yadda na ro'ki alfarmarka a waya?" Nan ya shiga kame-kame cike da borin kunya. "Ranar ban koma gida akan kari ba. Jiya kuma mun je bikin bude rijiyar nan... Damadai yau na ke shirin ta je asibitin..." Alhaji da takaici da fargaba ya fara kaiwa bango ya tare shi ta hanyar shiga maganar ya cewa Mummy. "Wai me yake faruwa da kika sanshi kina Abuja mu ba mu sani ba?" Kai tsaye cikin raunin murya ta fada masa. "Lokacin da cikinta ya yi wata biyu ta kira ni ta fafa min, amma da sigar neman shawarar yadda

Chapter 11 of 21