Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ce, aljanna ba ta samuwa da wayo ko dabara sai da aiki". Nan ma cikin rawar murya ya ce. "Zan je gobe da sanyin safiya cikin yardar Allah. watakila anan motar ya zubda shawarar data basu.dan tunda sukai haka da ummanta baikara bi takanta ba har aka shi ga hidimar biki sosai.ruma duk wani farincikinta da ita da ummanta da balaraba duk yake suke kawai. aka daura auren ranar lahadi akakai hafsat gidanta dawaki road aka kai ruma nata gidan sallari kowa ya watse aka bar su da halinsu. kamar kowa ce amarya abokan ango sunkawo ango sunkuma danyi barkwanci sukai sallama da amarya suka tafi.ruma takasayin komai illa data tuna auwal amma a a wannan karan taki zubda hawaye musamman data tuna cewa ummanta taimata batun sayarda abunda ta ce ayi wannan kadai ya wuni yana faranta ran ruma agundure ya cemata ALLAH ya sauwaka kuma maganar gwaji ma aita wuce kamar yadda nafada,indai zuwa gwajin bazah. tankwabe alhji hana shi daura aurenba.... nibandauki ciwon ruma wata matsala ba a cikin auren.a da ita.. momi tajima kafin ta iya magana yushau bakasan auren nan alhajine ya matsamaka ko? cikin murmushin yake ya ce aa niba matsamin akaiba,kawai a inda muka sha banban ku abinda kuka daukeshi damuwa ko matsala ni awurina ba matsala bane. Momi fuskarta cike da damuma ta cemasa dan ALLAH yusha u meyasa baka bijirewa auren ruma ba tunda akwai matsa a cikin auren? abinda baka fahimta ba shine,kai baka kallon ciwon ruma matsala,nikuma a duniyar nam banida matsalar datafi shi girma,ko tattalin ciwon ruma nake,to na tabbatar ina yimasa tattalinda yake wa rayuwarta amfani dan ina kokarin kore dukkan abinda zai motsamata ciwon saboda inajin hakannyanadagamin hankali nandai yushau yagane yayi katobara kuma idan hakan yaje kunnen alhji da matsala danhaka ya gyara zancensa "Haba Momi ba ki fahimce ni ba ne, ko Rumasa'u ba ta aure ni ba, ai ni mai zage kwanji in kare mata abin cuta ne, balle ni in zame mata cutar, don Allah ki kwantar da hankalinki ki bi mu da addu'a... Ni fa babu wanda ya matsamin aurenta". Momi ta yi shiru kawai da alama zuciyarta ta fara sanyi, sai can jimawa ta ce. "To maganar zuwa asibiti?" Tana direwa ya amsa cikin kwantar da kai da murmushi. "A kyale maganar gwajin kawai, ko ya ya zata haifar min 'ya'ya ina son su haka zan kuma tanade su". ta ce koya zaku haifadai angaya muku mutum daya dai baya haifar sikila. hm..ya ce ko yaya zamu haifa momi kui mana adduar ALLAH ya bamu ikon kula dasu.. (kaji gulma kamar dagaske) ta ce amen amma tilasne kaje ga mashawartan sikila da jin irin dawai niyar dake gabanka. ya cemata zanje gobe da sanyin safiya insha ALLAH.... . To ai banda Yushau ko da mace lapiyar ta kalau ba sickler bace tana bukatar tattali da kulawa piye da yadda sarauniyar ingila take bukata, pls take note my guys. . Dan Aunty. GORAN DUMA (P 28) . . . watakila anan motar ya zubda shawarar data basu.dan tunda sukai haka da ummanta baikara bi takanta ba har aka shi ga hidimar biki sosai.ruma duk wani farincikinta da ita da ummanta da balaraba duk yake suke kawai. aka daura auren ranar lahadi akakai hafsat gidanta dawaki road aka kai ruma nata gidan sallari kowa ya watse aka bar suda halinsu. kamar kowa ce amarya abokan ango sunkawo ango sunkuma danyi barkwanci sukai sallama da amarya suka tafi. ruma takasayin komai illa data tuna auwal amma a a wannan karan taki zubda hawaye musamman data tuna cewa ummanta taimata batun sayarda abunda ta ce ayi wannan kadai ya wuni yana faranta ran ruma Ango da amarya wato ruma da yushau,shi kallon tv ita kallom yatsun hannunta fiye da minti sha biyar .rumaisau dai bata da abin cewa amatsayinta na mace da akasani da karancin azarbabi da yawaita kunya yushau ne mai abin cewa inyayi kuma yai masa kyau amma girman kai da tattalin shugabanci yahana shi motsi a kar she saikawai ya mike yana nuna mata leda ya ce ganaman nan samo faranti kibani nawa. ta yunkura jiki a sanyaye ta je kitchen ta samo faranti biyu .yan shila ne guda shidda,ta zuba masa uku muryar sa narawa ya ce biyu ya isheni. ya wuce yana cewa to saida safe ALLAH Yatashemu lfya amsar data bashi kenan bayan fitar sa, kaitsaye bazata ce taji ciwon abinda yaimata ba.in ma hartaji ciwon to bazai wuce na bar mata sarari mai katon fadi ba wanda zataita sukuwar tunanin auwal da lissafin DAMA ACE (SUNAN WANI LITTAFI.) haka tawuce kitchen ta aje naman a frige dan tarasa abin ci ta garkame kofarta... tayi kuka iya yinta inda daga baya ta tuna da hudubar mahaifiyarta ayaudin kafin akawo ta gidan miji. babbar ALFARMAN DAZAKIMIN RUMA ITA CE MANTAWA DA AUWAL A FURUCI DA HAWAYENKI GABAN MIJINKI,KO BAYAN IDONSA,KIBAR GANIN BABU RAN AUWAL DAN HAKA BAI ISA A YI KISHI DA SHI BA,INA TABBATAR MIKI KO BAYAN KO BA TA BA AUWAL BA BAKINKINE YA KIRKIRE SHI YUSHAU ZAIYI IYA KISHI DA SHI ,MATAKIN DAZAI DAUKAKUMA WANI SANADI NE NA KORE ZAMAN LFYA A TSAKANINKU WANDA HAKAN KEME ZAI DAMI DUNIYARKI..DON ALLAH RUMA KARKI BANI KUNYA BANTA BA ZATON DUK WANI ABIN TIR A CIKIN SHAANINKIBA.DON ALLAH KICI GABA DA KORESHI A ZAMANKI DA YUSHAU KITOSHE DUK WATA BARAKA DAZAIKUKA DAKE MUSAMMAN TA KORAFIN KIN MALLAKAWA AUWAL ZUCIYARKI KINBAR MASA GANGAR JIKINKI.. SHIDAI AUWAL TASA TAKARE MUNA SAKA MASA RAN DA CE DA RAHAMAR ALLAH wannan nasihohin sune sukafi tsayamata a rai tsawon kwanaki bakwai abinda ke faruwa kenan tsaka. Tsawan wadannan kwanakin hajiya ke tada mubarak ya kaimusu abinci safe rana da dare.saboda haka ruma batakowani irin aikin wuya inbanda wanke wanke da shara saiko tafasawa yushau ruwan shayi a duk sanda yai umarni hajia nada azancin na dauke musu nauyin abinci,hikimar hajiya shine,daga cikin babban abinda yake motsawa sikila ciwonsu shine aikin wahala ko yin aiki mai yawa a lokaci guda.a wasu lokuta wasu dayawa ba asanin sikilane sai sunyi aure.dalili .anan shine.aure yasa dawainiya ta hau kansu na kula da gida da hidimar maigida.sannan basu saba kwanciya da namiji ba,kwatsam sai su wayi gari cikinta.musamman idan suka hadu da namiji mai yawan bukata.sai abin yafi karfin yanda zasu iya dauka.. a azancin hajiya babu da cewar akai ruma da mai aiki a halin yanzu ga amarci gakuma rashin fahimta dake tsakaninsu duk wadannan uzurorine dake bukatar kadaici saboda haka hajiya tadau nauyin basu abinci har na sati biyu sannan tai maganar yar aiki kuma duk lokacinda mubarak zaije takan masa kashedin idan yaje yaimata share share kuma yana kwatantawa to saidai abinda hajiya takewa hidimar shi kamar baima kama hanyar faruwar hakan tsakaninsuba danta koina kofofin alama a damke suke.shiyana takama da girmankai da tattalin shugabanci. hakadai suka cigaba da zama.ALLAH cikin ikonsa kuma saiya kwantarmata da ciwonta saudaya mukamukinta ya tayarmata da ciwo,kuma data shafa CONFO bai dauki lokaci ba ya saki. lokacin data dauki kwana shadaya a washegarin ranar waadin komawar ta asibiti game da ciwonta ya cika duk da barunta tarasa hikimar dazata fadamasa fita saboda taji aranta idan babu kofar dazasui nishadin jima'i to batun zuwa asibiti zai iya bada kofar dazasu kara tsanar junansu ita bazata iya hakura da batun ba haka bazata iya tsaga idonsa ta tambaye ba kawai saitakira hajiya suka gaisa taimata jajen jiki takuma sanya mata albarka.a ladabce ruma ta ce hajiya gobene nake ganin likita ko inyaya yushau yazo zaki tunamasa hajiya taji wani irin jiri na dibarta.lallai daliline kuma mara dadi zaisa mace ta biyo ta wata hanyar dan sanar da mijinta wani batu,alhalin tare dashi take kwana take tashi.bakin hajiya na rawa ta ce meyasa bazaki sanar masa ba? ruma tai dariya wanda hajiya taji kamar ta kunya ta ce wallahi hajiya narasa da hikimar da zanfada masane ba zan iya ba dan ALLAH kifadamasa. hajiya ta cemata to harma yazo yatafi amma zan masa waya waiko satinda wuce kinje ganin likita da gashin fuskarki kuwa? a sanyaye ta amsa a.a to meyasa? tafada adan fada ce.ruma tai shuru kintambaye shine ya hana? ta ce a.a bantambayeshi ba amma zandi ga tambayar sa. hajiya tai shuru tana tunani tajima da sanin ruma akan kawaicinta bata yinsa cikin abinda ya zama dole sai idan anfi karfinta saitaimata nasiha akan cewa tafi kowa kusanci da mijin ta. ta ce zankiyaye hajiya kitaimin addua cikin tausayamata hajiya ta ce ALLAH yaimiki albarka. da yamma yushau yadawo gida kamar yadda ya saba ya kulle dakinsa yadan huta yai wanka yana shirin fita hidar abinci wajen ruma sai ga hajiya takira shi a waya kana lissafe da cewa gobe ruma zata ganin likita ko? oh fuskarta ko? da wannan tunanin na shi go gida yanzu mts!ina ganin ma zamu sauya asibiti...kada ka cemin bakwa zuwa gashin fuskar ni akan sikilarta nake magana yaji wani bakin ciki da takaici ya rufeshi. . Dan Aunty. GORAN DUMA (P 29) . . kai tsaye dakin ruma ya nufa yana kwankwansawa ta bude a ladabce tai masa sannuda zuwa tanakokarin ta fito,amma sai ya tureta kadan ya wuce falon nata, ta bisa da kallo,har saida ya zauna.jiki a sanyaye..takara gaidashi haka yake ta kallonta bako kyafta ido itakuma saita buge da wasa da yatsun hannunta tsoro duk ya cikamata zuciya saida yagaji da kallonta zuciyar sa kuma tadan sassauta kunan laifin dayake ganin tamai. kawo min abinci.asanyaye ta mike tare da mamaki aranta.tamike harta wuce baidorar da abinda zuciyar sa take rayawa game da ita ba ammadai abine yasani shine sanyin jikinta, ya dauki hankalinsa yadade da sanin ruma kasaitacciyace ta nunawa gaban sarki,.amma baita ba kula da sanyin jikinta ba,in ma matantakarta takeson nunawa tabbas taci wasan dankuwa ta nunu. Ya ce mata abinda kikemin na tabbata baki taba ganinsa gurin alhji ko hajiya bako? ta ce menaimaka? ya ce tunda kikazo gidan nan na taba fita kin min .adawo lfya? ko indawo kimim sannu da zuwa? abincima saina roka balle insaka ran zaki zubamin ko ki zauna gabana inacin abinci ina kallanki. tagama cika damamaki da wannan tsabar karfin hali natake laifinkai.da abokin mayar da maganarta ne sai itama ta tambaye shi KATABAGANIN ALHJI KO DADY YA FITA BA TARE DA SANIN MATAR SABA? IDAN YADAWO BATA KUSA SAI YA NEMO TA WATAKILA SHIYASA TAKE ZAMA A GABANSA YA CI ABINCI,KO BA .HAKA BA. todake bazata iya fadi infada dashi ba saitaja bakinta ta kulle ta ce to ni menake dashi daza a kallah.? yajima yana kallanta tare da murmushi a fuskar sa..meyasa kika watsar da korafina na farko kika za bi amsa ta karshe kikaimasa sharhi? ba watsarwa naiba,abinda nadauka kawai shine rashin sabo ne.murmushi kamar a mafarki ya tausasa murya ya ce kuma bakyaso musaba ko? Nayimamaki ace waike dakanki bazaki iya min maganar zuwa asibiti ba saikin sanarma hajiya,kuma kisan da wuya , na fahimcima ke gabadaya wannan fuskartaki bata damunki.niko bakiji yadda nake tausayinki akanta ba, tai shuru..danko maganar tausayin ce ruma bazata daUKeta ba. yana tausayintane zata kwana go ma sha a gidansa amma baita ba yimata ko sannu akan ciwan ba. badan ransa yasoba washegari yakaita asibiti tagama yadawo da ita ya tafi Sabgoginsa. haka dai suka ciga ba da zama .duk dare adakinta ya ke cin abinci.haka zaita takalo hira ita kam amsawar atakai ce dukkansu sai suke wa kansu kallan girman kai shiyanaganin dan bai isa bane tanashare shi.itakuma tanaganinsa a mai daukar dala ba gammo na kwanciya yasami soyayyar mace da mulkinsa daya saba shikenan sai suka zarce a cinaka in ci nawa , watansu guda ta fara shi ga matsalolinta na yau fari gobe baki.amma baisan tanayiba saboda rashin kulawa.agida idan tawayi gari da ciwo kamar yadda ka'ida yake,zata garzaya asibiti amma agidan yushau babu wannan dantawayi gari taga idanta yazama dorawa daya daga cikin alamar tashin ciwanta kenan.haka tai shirin zuwa asibiti da zumar zuwa tanajin motsinsa taje suka gaisa tafadi matsalarta amma sai yaki daukar hakan da mahimmanci.saiya ce ba wani abubane shawara ce zantaho miki magani baiko saurareta ba yai gaba saida tai kuka musamman ma data tunada auwal tun ma kafin yasan ita sikila ce. akwai lokacin dayazo ya taradda idanta yai hakan cikin tsananin kulawa ya ce ya kyautu kije asibiti wannan sauyawar idan naki ya wuce a ce shawara ce tadanyi murmushi batare da ta tankaba.ya ce inbabu damuwa muje inkaiki asibiti.tacemasa babu matsala gobe zanje asibiti akwai magungunan danake sha.watakila kafin goben makaga idon ya washe kaitsaye ya cemata mekika sha ta ce ina zuba glucose a cikin ruwan dazansha,inyawaita shan ruwa,da rake..ALLAH ya sauwake. dan bawan ALLAH washegarin dazai dawo sai gashi da gwangwanin glocuse,biyar da yankakkun rake Auwal ALLAH YAJIKANKA.. tare da kokarin yanke tunaninta.dan tana tuna asarar data tafka na rashin auwal. haka ta hakura ta zauna ta tilasta wa kanta shan ruwa bako glucose din a ciki. dan wanda tazo dashidin yakare da dare sai gashi da tulin magunguna shawara iri iri.dan takaici tana karba tai kitchen ta watsa su friege tadawo hannunta nadukan cinya taizaune tana karatun jaridar aminiya. yana gamawawda abincinsa ya cemata da anayiwa na miji kishiya da sai ince ko kukan ina da kishiyoyi jaridun nan ko kunya bakyaji kullum ni ina zaune ke kina karatun jaridun nan Yushau ya ce ina magungunan naga kin aje ko ciwan be dameki bane? ransa yai mugun baci,itama ta hadiye duk wani bacin rai ta ce masa irin wadannan magungunan da matsala a jinina na gazawa wajen tace abinci shine dalilin taruwar abinda kagani a idona.innasha illah zaimin. ya cemata amma kinsan hakane kika barni na siyo? batare data dubeshi ba ta amsa baka bani damar naimaka bayani ba kana yanke hukunci kai tafiyarka.hakane ammadai bayan natafi kya kirani ki gayamin.taimurmushi kawai ya ce mata ruma kinki sakin jikinki dani ko?bansan yadda kike kallan hukuncin ALLAH a tsakaninmu ba. a zuciyarta ta ce yakasa gane matakin datake dauka haka ta kasa gane abinda yake nufi a yanzu.a farin sanin dataimasa ba bu dadin baki ko agidansu a tsakaninsu dalilin kirkirar su a yanzu kuma takasa gano danya amfanetane.hawayen ta ne yai dalilin baro nasa mazaunin zuwa inda take idan wani laifi nake miki sai ki gayamin wata irin rudewa da kidima yau ya bayyana atare da ita yau ita ce a jikin wani namiji wanin ma yushau? sai tarasa inda zata tsoma ranta,a kidime ta ce ba bu wani laifi in ma akwai nayafe yushau baidamu da kidimewarta ba saiya kamo hannunta yana murzawa Da yawan lokuta ciwanta na tashi.amma idan yushau yakai kololuwar nuna kulawar sa kawai ya ce mata ruma daurewa zakiyi dayawan mutane inzasu samii gado da likita kwanciya zasui,nikaina nan bakiji yadda nake fama da abu kaza ba..... . Ina yiwa en uwa barka da shan ruwa, Allah Ya amsa ibadun mu da addu'oin mu na khairi baki daya. Allah Ya sa muna daga cikin bayin da aka enta su xuwa Aljannah, Aamiin. Dan Aunty GORAN DUMA (P 30) . . nikaina nan bakiji yadda nake fama da abu kaza ba..... hakan shine kadai furucinsa. watansu biyu da aure hajiya takawo musu ziyara ganin yadda ruma tai muguwar rama kuma takara kasalancewa saboda gigitar ayyuka ba yan ta ko ma gida da yushau ya zo taimasa magana kan yanema wa ruma yar aiki, ransa yai mugun ba ci saiya tattaro korafinsa yayo gida da niyyar karewa akan ruma Tunda haushin ruma yakeji ko kallan dakinta baiyi ba itakam aranar ta wuni zazzabi.ammadake tasan uzurin ciwo agurin yushau ba uzuribane haka ta daddage tai abinci jalof din taliya da lemon kwakwa ta ri ga ta aje abincin adakinta dataji shuru saita kaddara ya hadiyotane saboda haka ta kokarta ta kwashi kayan abincin ta bishi dashi. ya fito wanka ta gaidashi ya amsa fuska ba ya bo ba fallasa suna zaune shuru har yayi rabin plate sannan yadaga kai ya dubeta yanzu dan ALLAH ruma mene ne abin wahala a irin wannan girkin sai 'yan wanke kwanuka da aka ci.? tai shuru tana kallansa kirjinta na bugawa ta ce masa meyafaru? cikin gatsali ya cemata kinfini sani.kuma niba wannan yadameni ba.wai duk lokacindakike son wani abu saikin hadani da hajiya? kodake kinsan ba bu gaskiya a batun in samo miki 'yar aiki ina kudan yake balle romonsa? dan ALLAH ina aikin yake a gidan nan bare a nemo wata mai hidima mamaki da takaici ya ishe ruma amma dake jaruma ce sam fuskarta bata nuna ba.kamar cikin jimami ta ce dashi kaga kuma bani naimata maganarba.rannan datazo ta tarar banida lafiya ina aikin gida a wahalce watakila wannan ya sanyata hasashen samo mai aikin amma bani nasa ta ba yaya yushau. kunya taso takamashi amma dake sarkin ki fadine.sai ya maza yai fuska. Ya ce mata babu wata mai aiki da za asamo kodan saboda dalilai biyu,kisami damar mike kafa,shawara takara samun gurin zama a jikinki,ko kuma kici gaba da mike kafa kina abinda na tsana.wato karatun jarida ta hadiye ciwan maganar sa cikin sanyin murya tace to naji abar maganar. haka ta kwashe kwanukan taje ta kwanta gashi jikinta da zazzabi,ga sanyin iskar fankar dake kadata gashi ba dama taRAGE DAN Yushau mutum ne mai matukar jin zafi shiyasa yake kallon nata gudun iskar a matsayin wata tsirfa yana shan lemon kwakwa ya dubeta meyasa baki yi lemun shinkafar nan ba yafi wannan dadi.? murmushin yake kawai tai aranta ta ce yushau komai kai baka burgeshi ranar datai na shinkafar ma cewa yai wannan menene marabansa da kunun zaki.? ya cemata akwai nama dana shi go dashi kiyima farfesu. tai shuru tana tausayawa kanta yushau baisan yakamata da kawaici ba. yaya yushau wallahi inafama da zazzabi, kadan min uzuri zuwa gobe. baiko dubeta ba ya wuce yana cewa aidaurewa zakiyi, bari nakawo miki PANADOL karfi da yaji kin mayar da kanki 'yar kwaya..yakawo mata tare da ruwa tasha tanufi kitchen tafara aikin.dan yanzu ruma talura indai tana son lallai sai yushau ya damu da lalurartane to ranta yadunga baci kenan.... gab da sallar magarib ta kammala yushau yashigo kichen din da shirin zuwa masallaci. Har kingama ya shigo yafara dauraye kwanunka yana kifewa..yana cewa laulayinki idan aka biyemasa sam baza a morekiba..tai shuru bata tanka ba tana ta numfarfashi har tagama wanke wanken dayaga shurunta yayi yawa yasa yakai hannu wuyanta yaji zafin zazzabin cikin jimami ya ce zazzabin yakaru ruma sannu.kawai saitaji kwalla na zuwamata amma haka ta daure tahana kwallar fitowa can sai gashi ya shigo da maganin boska ya mikamata yana cewa maza balla biyu kisha yanzu zakiji zazzabin ya sauka.ta amsa ta aje gefe ta cemasa na cemaka banashan magani kaitsaye batare da umarnin likita ba sai kilu tajawo min bau idan nai ganganci. ALLAH yasauwake ya ce sannan ya koma kan abincinsa itakuma tashi ge dakinta yana cin nama tunaninsa nakanta kullum mace babu lfya da aurensa amma yana hada kafada da gwauro duk yadda yake da bukata sai dai bukatun subi ruwa sai lokacin barci ya shiga dakin ya tadda tai barci yataba wuyanta yaji haryanzu da dumi ya dinga shafa kanta har saida tafarka... duk abinda zai saukar da zazzabin kin koreshi, kiyi wanka da ruwan sanyi kinki,kisha boska kinki,yanzu dankinsha sau daya sai wani abu yafaru? itakam takasa magana sai yarike mata hannu yana matsamata zuwa kafada .tasan dukkan manufar sa saboda haka takawad da kai cikin bata fuska. haka yadafa ruwa ya tilasta mata wanka dashi. data fito wanka zazzabin yadan sauka.hakan kuma ya bama yushau damar ji da ita.iyakar yadda yaso wanda ko mai cikakkiyar lfya ce zataji a jikinta.yahau barcinsa ya barta da mayar da numfashi adaidai. hakadai suka ci gaba da zama wanda yushau saiyana da bukata yake lallabarta tare da tattalinta.har kullum ruma kukanta bai wuce naganin zata kare rayuwarta cikin Rashin 'yanci dasafe ruma tatashi. da matsanancin ciwan baya hartakai saidai yushau yaimusu karin kummalo amma ya bar na ruma a kichen. yasame ta adaki kidaure kitashi ga abincinki can akitchen kidanci kisha magani ninatafi kasuwa haka ruma tadaure duk wani bacin rai tace masa adawo lfya. kogama ficewa gidan baiyi ba tarushe da kuka..tunda ta auri yushau ko saudaya bata taba zuwa taronsu na sikila ba kwatsam tawayi gari da zaton tana da ciki saboda rashinganin aladarta. . Eh uwa barkan ku da sallah, da fatan ana shan shagali da hidiman sallah lafiya, Allah Ya amshi ibadun mu Ya maimaita mana, Aamiin sannan barka da sallah na, ban daukewa kowa ba ina jira ehe.. Dan Aunty. GORAN DUMA (P 31) . . Ruma tai kuka hartagaji kamar ranta zaifita.dan ta tabbatar a yadda yushau ke tafiyar da ita,lallai rayuwarta na cikin hatsari domin mace in sikila ce a duk lokacinda tasami ciki tun cikin na na wata biyu zata kasance karkashin kulawar likita duk bayan sati biyu har zuwa watannin sannan tako ma antenatal. wajibine ba bu ita ba bu aikace-aikacen masu nauyi da yawa kuma wajibine ta haihu gaban likita saboda matsaloli barkatai musamman game da jini Duk wad'annan dokokin suna nufin gata, ita kuwa ta san bata dashi, Yusha'u ba mutum ne mai fahimta ba duk yadda ake fahimtar da shi ba a sauya masa ra'ayi da fassara. Har cikin ya yi wata biyu tana cikin halin kuka da damuwa ta kasa sanar da kowa, mafita a wajenta ita ce ta sanar da Hajiya, amma idan ta tuna jan idon da Yusha'u ya ke idan Hajiya ta yi masa wani Umarni bisa tunaninta a kanta, ya kan zo ya yi ta zabga mata gori da goruba, to ina ga yanzu ta sanar da ita. Da ta rasa mafita kawai sai ta yiwa Innarta waya cikin kuka ta sanar da ita tare da neman shawararta. Hankalin Mahaifiyarta ya yi mugun tashi duk da dama a tashen yake kasancewar duk 'karshen wata sai ta ziyarci Rumaisa'u, kuma ganin da ta ke mata tana tabbatarwa Rumasau ba ta cikin kwanciyar hankali da 'koshin lafiya. Cike da 6acin rai Mummy ta ce. "Ni dama na san sai auren Yushe'u ya cutar da mu, Yusha'u mutum ne mai mugun girman kai, babu wanda ya iya sai shi". Rumasa'u ta kasa cewa komai sai shesshekar kuka, dan ta san gaskiya Innarta ta fada. Momi ta yi dogon tunani, sannan ta ce. "Ki kwantar da hankalinki, zan same shi a waya". Rumasa'u ta tsayar da shesshekar kukanta tare da fadin. "A'a Momi ki ba ni shawarar yadda zan fahimtar da shi, ba na son ya yi ta tuhumata da maganar ina kai 'kararsa...." Ita ma Momin ta tare da fadin. "Dole hakuri zaki yi ki bar ni na yi masa magana, Yusha'u na da raina mutane ko ni din ma ba lallai in yi nasarar ya ji maganata ba amma dai na san duk tsiya zan fi ki, tunda zan iya bibiyarsa idan na nemi ba'asi idan ya 'ki abin da na ce". Rumasa'u na cikin fargaba, amma dai dole haka ta yarda da batun Momi suka yi sallama kowa rai babu dad'i. Yusha'u na kasuwa wajen azahar Momi ta yi masa waya, cikin zaton faruwar wani abu ya daga wayar dan sanin da ya yi Momi ba ta kiransa a irin wannan lokacin. Ta fi kiransa da daddare ko da safe lokutan da ta tabbatar yana gida. Ya gaishe ta cikin ladabi da ci-da-zuci, ita kuma ba ta ja masa rai ba ta fadi abin da ke tafe da ita. "Cikin Rumasa'u ya cika watannni biyu ko? Ya wajaba lallai ku je asibiti ka san sickler mai ciki preterm labor ce, watau kullum tamkar cikin na'kuda take. Dole sai da kulawar likita zata raini cikin dan ceto ranta da na abin da ke cikinta". Ya ji maganar banbarakwai wai namiji da suna Hajara, dan shi dai bai ma san Rumasa'u na da ciki ba, kuma bai iya boyewa ba ya ce wa Momin. "Ni walllahi ban ma san tana da ciki ba". Ba tare da ba wa maganarsa muhimmanci ba Momi ta ce. "Allah Sarki, ka san Rumasa'u da kunya, ni kaina ba dan akwai wannan dalilin ba na tabbatar ba zata sanar da ni ba. To don Allah ina rokon arziki kar ka yi wasa da lafiyarrta ku je asibiti a shirya mata fayil, kuma abi dokokin likita". A sanyaye ya ce mata. "Babu komai, in Allah Ya so za a yi, Allah Ya inganta, Ya sauke ta lafiya". Momi ta amsa, "Amin". Sannan suka yi sallama. Ya wuni da abubuwa biyu, tsabar murnar cikin Rumasa'u saboda dokin samun magaji, da kuma takaicin yadda Rumasa'u ke yawan hada shi da iyayensu. Da ya dawo gida da yamma ya jima a dakinsa Rumaisa'u ba ta shigo ba, saboda haka ya sameta a dakinta, sai ya tarar da ita a bandaki tana kwara amai, dole ya sassauta 6acin ransa ya yi tsaye a bakin kofa yana mata sannu, har ta gama aman, ta gyara wajen ta wanke baki sannan ta wuce firji ta ciko tambulan da ruwa ta zuba glucose ta shanye sannan ta dawo ta zauna yana bin ta da kallon da ya sanya ta tsarguwa shi yasa ta kasa hada ido da shi, shi kuma ya 'ki tanka mata. Can ta mi'ke ta kawo masa lemo da fura sannan ta koro masa bayani. "Don Allah ka yi hakuri yaya Yusha'u, wallahi na sha ciwon 'kafa dazu shi yasa ban sami sararin yin abincin ba". Ya jima cikkin shiru sannan ta tsinka bayan ya tsiyayi leman ya sha. "Ya ya zan yi Rumasa'u, tururuwa ta yi jidon banza ma ballantana ranar garar 'yarta". Tana 'kila wa 'kalan fahimtar inda maganarsa ta dosa duk da ko ta fahimta din ba ta da kalmar amsa masa dan haka ta kyale kanta da damuwa da sai ta fahimta. Sai da ya gama shan furar sannan ya dubeta da kyau, ya ce. "Yanzu tsakani da Allah Rumaisa'u kina dauke da cikina in rasa arzikin ki sanar da ni? Duk lamurana ba kya daukarsau da muhimmanci idan ba wandanda ba ki 'kudurta kai ni 'kara wajen mahaifanmu ba". Ta yi shiru 'kirjinta sai bugawa yake saboda tsoro, bakinta sai rawa yake ta kasa samo hanyar kare kai saboda haka shi kuma ya sami sararin fitar da dukkan zargin da zuciyarsa ta sa'ka masa. "Tun kafin auren nan fargabar a ta dame ni ke nan, ni na san zurfin iliminki ba zai barki daukata wata tsiya ba bare ki kimanta ni, duk wani abu na ha'k'kina ko naki kina ganin na yi tsororo ki cika min shi ko ki gabatar min. Babu wani abin arziki da nake tsinta a wajenki sai na 'korafi da kaiwa iyayenmu magana... Takardar jarida ko mujallarki ta fi ni kima da daraja..." Yanzu kwallar da ta taru a idonta ta fara saukowa, cikinta kuma ta dago ta dubi Yusha'u murya a raunane ta tare shi. "Wallahi Yaya Yusha'u ban ta6a kai 'korafinka ko 'kararka ba, wannan kuma da na fadawa Momi ba 6ata ka nake nufin yi ba, kawai dai na yi tunanin ita zata fi iya fahimtar da kai matakin da za a iya dauka a kaina. Yadda aurenmu ya zo bagatatan ne duk ya janyo wannan matsalar, tun kafin mu yi aure ya kamata ka san yadda rainon cikina zai kasance..." Ya tare ta a zafafe. "Karki sauya min magana ko ki yi min gori Rumasa'u, yadda aurenmu ya zo ni ban ta6a daukarsa wani daban da yadda ya kamata aurena ya kasance ba, Allah ne Ya za6a min ke ban kuma yi butulci ba na kar6a, na ri'ke ki da iyakar adalcin da zan iya. Duk wani abu daban sai dai in a wajenki ya ke, ba kuma a baibi kike ba ni yadda na kabari ya fi ni daraja a wajenki ba..." Sai ta bude baki cikin tashin hankali tana dubansa,

Chapter 10 of 21