Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
zai iya kusantar da shi dan rahamarsa a gare mu da ni'imarsa. Zai iya tankwa6ar da shi dan isarSa a kanmu da zartar da abin da ba mu ba mu san da shi ba, dan haka duk abin da ka ji na fada kar ka danganta shi da kanka Auwal, danganta shi ga son yiwa ubangiji biyayya da faranta ran Abba, a wani hannun kuma da 'kin biye zuciya sakokinta... Ina sonka Auwal". Ya kai 'koluluwan rauni da tausayin Rumaisa'u wanda ya 'kara masa miliyoyin 'kaunarta, ma'kogwaron ya cunkushe da su, shi yasa duk yadda ya yi 'kokarin ya ce wani abu ya kasa, kawai sai ya dauki takardarsa ya nemi hanyar fita. Ba ta takura kanta da binsa ko kiransa ba, kawai sai ta raka shi da mafi sau'ki cikin abin da zata yi, wato binsa da kallo har ya fice, sannan ta durkushe ta fara kuka mai dalilin. Kwana biyu babu labarin Auwal, babu wayoyinsa. Ta yi 'kokarin kira duk a kashe. Ta yi tunani ta yi issafin duk ta kasa cankar dalilin 6uyansa ko kuma abin da ya 6oye shi, duk canki-cankin da ta ji yana neman tafiya da numfashinta. Auwal ya janye neman aurenta, hasashen da ke kusan tafiya da numfashinta. Auwal ba shi da lafiya, zargin da yake tilasta mata son lallai ta san halin da yake ciki. Kwana na uku ya kama alhamis, ba ta yi shawara da kowa ba ta wanke 'kafa da yammaci ta dauki Hafsat suka tafi Na'ibawa gidan su Auwalu. Tun a hanya Hafsat ke tambayarta abin da ke faruwa, musamman ganin yadda hankalinta ya yi matu'kar tashi ba kamar a lokuta baya ba, inda ko ya shafe kwanaki bai zo ba bata damuwa. Rumasa'u ba ta 6oye mata komai ba ta zayyana mata yadda suka yi. Hafsat ta ce, "Ina ganin gara mu fadawa Inna gaskiyar lamari idan muka je". Rumasa'u ta dafe 'kirji ta ce, "Wai rufa min asiri, kada a ga za'kewata da wawancina." "Ba wawanci ba ne, Rumasa'u, yarda ce da nuna bu'katuwar al'amarin nan." Kallo daya Innar Auwal ta yiwa Rumaisa'u ta gane ta, duk da ba su ta6a haduwa ba. Amma ta yi mata farin sani a hotuna dan haka ta sauke su da rawar jiki kamar zata goya su. Kasala da kunyar da Rumasa'u ke bayyanawa ya sa Innar Auwal jin wani irin tausayinta ya ishe ta. Ta zauna suka gaisa cikin girmama juna. "Duk manyan naku lafiya ko?" Inji Innar Auwal, Hafsat ta amsa "Lafiya kalau". Rumaisa'u kai na 'kasa. Suka dauki shiru kowa da abin da zuciyarsa ke sa'kawa, Rumasa'u na jin tsanar kanta da kankambar zuwa gidan surukai, surukan ma wanda auren d'an nasu da damuwa da 'kila wa'kala, amma 'kaunar dan nasu da sanin halin da yake ciki ya kore nadamarta mai taurin kan da ta 'ki 'karuwa, sai ta tsaya suke ta damun zuciyarta tare. Yanzu abin da ta fi d'ko shi ne, ta ina labarin Auwal zai 6ullo mata? Can Inna ta nisa ta ce. "Ku sha lemon don Allah, Nuraddin nake jira ya shigo ya dubo shi ko ya farka, yanzu da abokansa suka zo duba shi suka ce yana barci". Wani irin tashin hankali ya bayyana a fuskar Rumasa'u. Ta dago ido ta dubi Inna, amma ta kasa cewa komai sai bakinta ne ya ke rawa. Hafsat ce ta yi mata abin da ta ke son yi cikin jimami da sanyin murya, ta ce. "Ayya ba shi da lafiya?" Inna ta jinjina kai, ta ce. "Ba shi da lafiya, na yi tsammanin ma dubiyarsa kuka zo, kwana biyu ke nan yana fama da wani matsanancin ciwon kai". Rumaa'u a rikice ta ke amma ba ta fasa tambayar Inna ba "Inna dama yana yin irinsa?" Cikin nuna jimami Inna ta ce. "Dama yana da yawan ciwon kai, tun yana 'karami ya yi san'karau shikenan yawan ciwon kai ke bibiyarsa, sai dai bai taha tsananta masa irin wannan lokacin ba, amma yau da sau'ki ba kamar jiya ba. Yau har ya ci abinci an yi hira da shi, ftowar mu ke nan bacci ya dauke shi". Rumaisa'u ta sauke numfashi cike da dukan zuciya, duniyar gaba daya ta yi mata 'kunci ba ta san lokacin da kukan zucinta ya fito fili ba, had'e da hawaye har da shessheka. Hafsat da Inna suka bar yiwa juna jajen rashin lafiyar suka koma rarrashinta. Jikin Inna na 6ari ta mi'ke ta fita tana cewa. "Bari na sanar masa da kaina, ki je ki ganshi, jiki fa ya yi kyau". Bayan Inna ta fita Hafsat ta ci gaba da tausar Rumasa'u, yayin da Rumaisa ta d'ago da hawayen ta ce. "Hafsat ni kadai na san yadda na ke jin Auwal a kirjina, duk wani abu na illah ko mai nuna salwantarwa a Auwal ba na iya jure masa, ina son Auwal, kawai shi ne abin da na sani". Hafsat tsakaninta da Allah ta ce. "Yadda na ke addu'ar Allah ya bar ni da Sani, haka na ke addu'ar Ya barki da Auwal ko ma fiye, don na tabbatar kun yi dacewar da abokan burmi irinku su ke wahala". Shigowar Inna ya tsayar da maganar Hafsat, ta ce. "Yauwa ku 'karasa, ya farka na same shi yana sa wayarsa caji". Rumasa'u ta riga tashi suka fita cikin jagorancin Inna, har dakin Auwal, sannan ta yo baya.... . Dan AuntyGORAN DUMA 17 . . "Na yi zaton kin manta da ni". Da kalmar da Auwal ya tare ta ke nan duk da ya ga hankalinta a hargitse, sai kallon sa ta ke kamar in ta dauke ido daga kansa zai 6ace mata ne, saboda haka har ta zauna ba ta cikin hayyacinta, ta dai sami kanta da amsa masa. "Dan na yi maka wanne laifi kake ganin zan manta da kai Auwal?" Dole ya basar da zancen kasancewar da Hafsat a wajen ba ya son su dire zancen da matsalarsu zata bayyana kanta. "Hafsat yau ku ne a gidanmu?" Abin da ya ce ke nan, Hafsat ta nisa idonta a kan Rumasa'u ta ce. "Ai dole ce mai sa wa a kwana a ido Auwal, kamar Rumaisa'u ta san ba ka da lafiya kwana biyun nan in na ce maka ba ta cikin hayyacinta kar ka musa". Ya yi zuru yana kallon Rumasa'u da idanuwansa masu aika mata wasu sa'konni masu dad'i da marasa dad'i, da ta kasa jurewa kallon sai kawai ta yi kasa da ido 'kwallah ta cika ido taf! Ya ri'ke kai saboda taruwar hawaye, take ya ji ciwon kansa ya dawo sabo dal, ya fara kokawar ri'ko juriya tana silalewa har ya yi nasarar dam'karta, cikin son nuna jarumta ya ce. "Yi ha'kuri Rumasa'u...." Ta tare shi a raunane. "Ya ya jikin?" Jikinsa a sanyaye ya amsa. "Na ji sau'ki ai... sai godiyar Ubangiji, kin san rai da jini". Ta kada kai tare da nisawa dukkanin hankalinta na kansa. "Anya Auwal ba damuwa ka sa wa ranka ba har ta janyo maka ciwon kai? Inna ta tabbatar min ba ka ta6a ciwon kai kamar haka ba, ka ga kuwa yadda ka rame Auwal?" Ya koma kujera ya yi rigingine ya dafe kai da hannun hagu sannan ya dafe 'kirjinsa da hannun dama saboda yadda ya ji shi ma ya dauki ciwon nan take fuskarsa na 'kokarin 6oye ciwonsa ya ce mata. "Sai da dalili Ubangiji zai jarrabi abin halitta Rumasa'u? Ki taya ni mu yi fatan zama kaffara kawai dole ya yi 'kokarin tashi zaune ya dubeta murya a sanyaye ya ce. "Rumasa'u idan ba ki dalafiya haka nake sanya ki gaba mu yi ta kuka, ko ciwona ne ya fi na kowa?" Ta yi saurin girgiza kai. "Ina jin abubuwa da yawa marasa dad'i a raina Auwal duk suna nuna min yadda ba zasu iya jure rashinka ba". Ya yi mata inkiya da Hafsat a wajen abin da ya fahimta matsalarsu ce a maganarta, saboda haka ya goce ta da cewa.. "Da ciwo ya san in da rai ya ke Rumasa'u ai da tuni kin tsufa a can, rayuwa da mutuwa duk Allah ne, kuma da yawan abubuwa na faruwa ne ba yadda mutum ya zace su ba, ni yanzu so nake ki kwantar da hankalinki mu yi hirarmu mu fanshe kwana biyun da muka rasa, kinga sai ta zame mana ta tarihi ko? Ina jin tunda muka had'u ba mu ta6a kwana uku ba mu ga juna ba". Ya 'kare maganarsa ne da dariya sai Hafsat ce ta taya shi, ta kalli Rumaisa'u taga fuskata a cunkushe. Tunanin halin da take ciki na rashin lafiyarsa da 'kila wa 'kalan aurensu, ba ta ga wani abu da zai ba ta dariya ba. Fahimtar hakan da Auwal ya yi yasa ya dinga daurewa yana ta tsaokano ta da hira, har saida ya ga abin ya faskara sannan ya dubi Hafsat ya ce. "Hafsat don Allah ki ba mu minti biyar akwai wata wuta d ana hura nake son kashe ta". Hafsat ta mi'ke tana dariya ta ce. "Ni ma na yi niyyar hakan cikin raina, ina da bukatar Rumasa'u ta sami nutsuwa." Ta wuce Auwal bin ta ya yi da cewa. "Yauwa Gimbiyar Sani, Allah Ya barku tare". Hafsat na fita ya baro kujerar da yake ya zo gabanta ya zauna cikin raunin murya ya ce. "Fad'a min abin da ya fi damunki yanzu na wanke miki shi Rumasa'u, idan dai ciwona ne aikin ga na ji sauki ko?" Ta goge hawayenta sannan ta sauko daga kujerar duk suka zauna a kafet suna fuskantar juna, tana ta faman goge hawaye, sannan da kyar ta 'ko'karta ta ce. Me yasa ka kashe wayarka?" Ya 'kura mata ido kawai ya kasa cewa komai har ta kuma dorawa ba tare da ta dube shi ba. "Ya ya kuka yi da Abba?" Kai tsaye cikin dakewa ya amsa mata. "Wannan rashin lafiyar tawa ta sa ba mu zauna mun tattauna ba, amma dai na nuna masa sakamakon gwajin". "Me ka fahimta a tare da shi?" Kai tsaye ya amsa mata "Fuskarsa ba zata iya bayyyana abin d ke fake ba, duk yada zai nuna 'karfi ko hangen nesansa ba zai sauya ba ko ya yi abin da Ubangiji bai nufa ba, zai sauya ba ko ya yi abin da Ubangiji bai nufa ba, na ba shi sakamako na kuma fad'a masaain da ke raina, ke ce farin cikina dan kin haifi 'ya'ya irinki na shirya zan tanada su a ha'kuiri na da juriyata da kuma yin tattalin aljihu iyakar iyawata ina da wannan burin a raina, na niyyace shi duk wani abu sa6anin haka idan haka idan ya faru haka Ubangiji Ya 'kaddara mana, ke ma ki yi min uzirinsa". Rumaisa'u ta yi sakato tana kallonsa, saboda har yanzu ba ta tsinci abin da ya kamata ya faranta mata rai cikin maganarsa ba, idan al'kawuran sonta d akyautata mata ita da 'ya'yanta ne tun ta saba jinsu a bakinsa, tana kuma da ya'kinin daga zuciyarsa suke tasowa saboda haka yanzu abin da ya dame ta shi ne ya ya za su yi su kai ga cimma burin kasancewa tare bare har ta jefa wad'ancan al'kawaran nasa cikin abubuwan da ta ke jiran kasancewarsu a rayuwa? "Zan tafi". Abin da ta iya ce masa ke nan cikin hawaye. Ya d'an runtse ido cikin girgiza kai ya ce. "Yanzu sai ki tafi ki bar ni Rumaisa?" Ta mi'ke tana ci gaba da goge hawayenta ta ce. "Wata'kila gobe in dawo idan ba ka murmure ba, sai dai ka ba wa Inna ha'kuri wata 'kila ta ga rashin kunya ta da za'kewa ta, ni ma haka na tsinci kaina, in dai abu ba haramun ba ne, don sakaf nake ganinsa a fuskarka". Shi ma ya mi'ke yana dariya ya ce. "Inna za ta fahimce ki Rumaisa, kin ta6a zuwa gidanta ban da yau? In Allah Ya so ma goben ni zan zo ba ke za ki zo ba, ai idanuna sun ganki sun yi kwari". Ita ma ta yi dariya ta yi ajiyar zuciya. "Hum...!" Alamar har yanzu ba ta ware ba, suka jima suna kallon juna, sannan ta kad'a kai cikin hawaye ta wuce, jirin da yake ji ya hana shi yi mata ko taku daya da sunan rakiya, daga nan tsayen har ta je bakin 'kofa sannan da murya 'kasa-'kasa ya ce. "Rumaisa'u... Ina sonki, kar ki manta da wannan". Ta tsaya tare da juyowa suka yiwa juna murmushi, sannan ta fice, shi kuma ya haye kujera a gajiye yana lumshe ido, yana son Rumaisa'u tana sonsa, har yau bai ta6a yanke 'kaunar za su gaza kai wa ga burinsu ba. Ta sami Hafsat da Inna suna ta hira ko a fuska babu wanda ya nuna mata wani abu. Ta zauna a sanyaye cikin hawaye, wannan ya sa kowa ya yi dif a dakin tsawon kusan mintuna biyu, sai can Hafsat tayi ajiyar zuciya ta nisa ta ce. "Inna ashe tun tuni Auwal bai sanar da ku cewa Rumaisa'u sickler ba ce ko? Tuni kuma ta shawarce shi ya sanar da ku, amma bai yi hakan ba har sai da kuka ji a gari. Tabbas ba mu kyauta har da ni, amma don Allah Inna ku yi mana uziri, sun fiye son kansu ne shi yasa su ke juyawa matsaloli fuska... Auwal da Rumaisa'u sun fara son juna da radin kansu amma yanzu ga shi sun ya gaza rabuwa. Inna don Allah ki fahimtar da Abba kar ya raba su.. Zaku iya neman wata mafitar ta samarwa Auwal wasu 'ya'ya ba nata ba... Na tabbata za su iya lamuntar haka, raba sun ne kawai muke jinsa wani abu da na ha'ki'kance numfashinsu ya gaza dauka..." . . Dan Aunty.GORAN DUMA 18 . . Rumaisa ta yi sororo hawaye na kwarara daga idanunta. Wadannan kalamai ne a bunne cikin ruhinta, amma baki ya gaza furta su. Inna ta dubi Rumaisa'u da ke shesshekar kuka. Inna ta yi dif damuwar duniyar nan ta bayyana a fuskarsta, duk da tuni ta san da sha'kuwa a tsakaninsu raba su abu ne mai wahala wanda ko ita ba ta mafarkin haka duk da dangar da ta ke hangowa iyalansu a gaba, a yau sun ba ta tausayi su duka har ta fara jin sallamawa cikin ranta. Cikin 'karfin gwiwarta ta ce. "Ku manta wannan maganar, iyakacin Abba fad'ar da kuma nuna yun'kurin da zai iya ba dan nuna 'kiyayya ba, sai don gujewa wahalhalu a gaba. Amma komai ai sai Allah Ya kasantar 'yar nan, ko shi kansa na san yana shakkar ta inda zai kwaso ya hana ko ku aure, auren da ya rage kwanan wata guda da 'yan lamarinmu ga Allah, Allah Ya tabbatar mana da alkhairansa kin ji? Ni ban so ma ya sanar da ke ba wallahi". Yanzu hankalin Rumaisa'u ya kwanta ta kuma sami nutsuwa a cikin ranta, har ta saki wani raunannan murmushi. Suka yi shiru ba wanda ya iya furta wani. A 'karshe sai sallama suka yi da Inna suka nufi gida. Mahaifin Auwal na tare da Innar Auwal bayan dawowarsa da dare yana cin abinci ya ce mata. "Ya ya jikin danki?" Ta yi dariya ta ce. "Wai yaya jikin danki, to ya sami sauki har ya je masallaci sallar isha'i". Ya ce, "Ko kuma ya tafi zance ba". Ta yi saurin girgiza kai. "Ba na tsammanin hakan,dan juria kawai na hanga a idonsa, ciwon kan nan yana matsaya masa, ka je wajen likitan da ka ce zaka je neman 'karin bayani a kan auren nasa?" Cikin fuskar jimami ya ce. "Na je, labarin babu dad'i Asma'u. Likita ya tabbatar min mafi rinjiyaen 'ya'yan da zasu iya haifa da kashei 70% za su zamo sikila ne, sai dai wani hukuncin Ubangiji. Amma duk da haka dan sabar son kai ya ke shawartata kar a hana su aure. Yanzu tsakani da Allah hana su aure ba jihadi ba ne? Su a wahale 'ya'yan da za su haifa a wahale? Mene ne aibun dan ya auri mai lafiya ita ma ta nemo wand aba zasu haifi 'ya'ya masu cuta ba?" Inna ta sauke numfashi cikin alhini ta ce. "Ka bar su kawai Alhaji, yaran nan sun fara ba ni tausayi, ai dazu ta zo duba shi, in ka ga yanayinta sai ka tausaya mata, na tabbatar yadda ya damu da ita haka ta damu da shi. Nan gurin ta zaune min tana neman in ro'ka ka kar ka raba su, har tana bayar da 'kofar yana iya auren wata da zata haifar masa lafiyayyun 'ya'ya... Yarinyar ta ba ni tausayi wallahi sannan ina tsoron makomar da za su fad'a idan aka raba su, dan ni ina shakar babu taimakon wannan jumurd'ar cikin tsanantar ciwon kansa, ka san yawan tunani cikin damuwa babu abin da ba ya haifarwa". Abban ya jima cikin jan numfashi, sannan ya hadiye abin da ya tara, ya cigaba da cin abincinsa, har ya kammala can ya ji motsin shigowar Auwal, saboda haka ya kira shi a waya. Ya shigo idonsa zuru-zuru saboda rama, a yanzu haka ma da 'kyar yake sauke numfashi saboda azabar ciwon kai. Ya nemi guri ya zauna cikin sanyin murya ya gaishe su. Mahaifin nasa ya zura masa ido tsawon wani lokaci yana kallonsa cikin tausayawa a zuci, sannan ya yi gyran murya ya ce. "Auwal tuni na yi maka shaidar tawakkali, me yake son sauya ka har ka dami kanka cikin abin da ban isa in sa ba bare in hana?" Auwal ya yi masa shiru yana masa kallon rashin fahimta, saboda haka mahaifin nasa ya dora. "Fadata fadar Allah ce dan na kawo ra'ayina akan aurenka zaka dinga neman kashe kanka Auwal?" A sanyaye ya ce masa. "Me na yi Abba?" Abban ya nuna Innar Auwal din ya ce. "Ga ta nan, yanzu nan ta gama zargin shigata lamarin aurenka ke jaza maka ciwon kai. Ni ma na gaskgatata, ai duk yadda kake ciwon kai ba ka ta6a fita hayyacinka irin haka ba". Auwal ya 'kokarta ya yi murmushi, ya ce. "Wallahi ba haka ba ne Abba, hankalina a kwance yake da ina da ya'kinin in dai ni mijin Rumaisa'u ne, babu abin da zai hana ni aurenta, ko ina da damuwa ba zata wuce na tausayinta saboda rauninta na mace da kuma lalurarta ba, wanda wannan zai raunana zuciyarta ya iya yi mata illa. Ina kuma cike da tausayinta idan ban zamo mijinta ba yadda na ga ana gudun aurenta, ina tsoron mata auren wanda zai kasa kyautata mata da kyautata rayuwarta... Gaba daya damuwata akan yadda Rumaisa'u zata samu rayuwarta ne.... Na san kuma wannan bai isa dalilin jaza min lalurar da Allah bai gadar min ba, saboda haka ku kyautata zato a gare ni, ku cika ni da addu'arku ta fatan alkhairi, har kullum ina alfahari da kasancewar iyayena. Ni addu'arku kawai nake bu'kata da cire zarge-zarge a cikin jarrabawar da Ubangijina ke min". Su duka jikinsu ya yi sanyi, kaunar Auwal ta 'kara mamaye zu'katansu, Auwal dan halak ne wanda akwai wahala ka ji sharri ya fito bakinsa, duk yadda kake jin abu mummuna ne in ya gifta shi ba zaka ji raknsa ba, kuma ba zai sauya masa manufa ta son zuciya ba, mutum ne shi mai jarumtar mayar da lamari ga Ubangiji. "Allah Ya yi maka albarka, Ya rabaka da duniya lafiya ka ki". Innarsa ta riga mahaifinsa magana, tana direwa shi ma mahaifin nasa ya dora da cewa. "Allah Ya kyautata rayuwarka duniya da lahira Auwal, Ya rabaka da 'kuncin duniya da lahira, Ya 'kara fadada 'kirjinka da halayen kwarai, da son Allah da ManzonSa. Ta shi ka je, Allah Ya ba ka lafiya Ya hore maka dukkan alkhairan da kake ha'ko". Ya dan dakata yana musu godiya, sannan ya tashi ya fita cike da dokin kiran Rumasa'u a waya ya ba ta albishir, dan ma kansa na mats amasa da ciwo saboda haka ya fara shan magani, sannan ya kishingid'a na wasu mintuna wai ko kan nasa zai dan sassauta ciwo, amma da hakan ba ta samu ba, sai ya kira wayarta a haka, sai dai kash! Wayarta a kashe ta ke, amma da yake ya 'kagu da jin muryarta haka ya yi ta gwadawa har bai san adadi ba. *** Washegari da hantsi 'karfe goma da minti hamsin Rumaisa'u da Hafsat da Hajiya suna tare a falonta suna hira, Rumasa'u dai ta kasa hankalinta fiye da dari ma idan ana kasawa, a hirarsu a tunanin lafiyar Auwal, aurensu, 'ya'yansu, da kuma wayarta da duk bayan minti biyar sai ta kira wayar Auwal din, ta yi ta faman rurinta bai daga ba. Tun asuba ta ke nemansa a waya bayan ta kunna wayarta ta tarar da 6oice mail na ya kirata kusan ashirin, tun sannan ta ke gwada kiran wayarsa har kawo wannan lokacin da 'kila in ya zo zai tarar da 100 missed calls. Babu itin tunanin da ba ta yi ba, ya saka wayar a silent, ko kuma jikinsa ne ya matsa masa, sai dai wata zuciyar tata na kore wadannan hasashen da wasu hujjojin, su ne. Idan jikinsa ne ya matsa masa, ina wadanda ke tare da shi da ba za su daga wayarta ba? Da wadannan dalilai ta dogara ta kasa cira 'kafa dan nemo wani hasashen, kuma gabanta ya dinga 'kuntata zuciyarta. Haka ta ke zaune cikinsu tana yake da faman kiran wayar Auwal, har ma lokacin da Hajiya ta dubi agogo ta sauke numfashi ta ce. "Oh ni 'yan nan kawaici ne fa ya fara 'karewa, Alhaji tun fita sallar asuba bai shigo ba, Yayanku ma bai shigo cin abinci ba, Murabak kuma da shirme na tambaye shi ya tsaya min shirme, wai abokinsa ya bi suka fita". Rumasa'u da Hafsat suka yi saurin duban agogo, Hafsat ta riga magana da cewa. "Kin kira shi a waya kuma?" Hajiya ta ce, "Yo ai a gida ya bar wayoyin na fada miki tun sallar asuba". Cikin alhini Rumasa'u ta ce. "Wani lokacin wayar ma ai hoto, kun ga tun safe nake neman wayar Auwal tana shiga amma ba amsa..." . Jama'a ku bani shawara, Ina shirin shiga neman auren Ruma tunda naga da Auwal kamar da wuya kuma gashi jini na A.A ne, daman na jima da jin son ta har cikin xucia ta, gudun kada na raba kauna da Auwal ne na danne xuciar, amma yanxu abun ya xo min har wuya . Ko ya kuka gani? Lol. . Dan AuntyGORAN DUMA 19 . . Kafin ta rufe baki sai ga Alhaji ya yi sallama ya shigo fuskarsa na kokawar 6oye sa'konnin tashin hankali iri-iri, komai nasa a birkice ya ke, sai dai akwai alamun yana tilasta kansa gayyato nutsuwa. Duk suka yi masa barka da zuwa, Hajiya ta dora da tambayarsa cikin kulawa. "Alhaji lafiya kuwa?" Ya wuce zuwa ciki yana cewa. "Lafiya mana, me kika gani?" Ta bishi cikin sauri suka shige falonsa a tare. Ya nemi kujera ya zauna cikin dafe kai hannu biyu. Nan take jikin Hajiya ya dauki 6ari ita ma ta silale kujera ta zauna tana sakin numfashi cikin sauri ba ta katsi hanzarin shirinsa ba, saboda haka ta raka shi suka yi tare". Tsawon wasu mintuna, sannan ya mi'ke ya je ya murzawa 'kofa mukulli sannan ya dawo cikin kasala, ya zauna ya dubi Hajiya ya ce. "Allah ne Ya yiwa yaron nan Auwalu rasuwa!" Tsawon wasu mintuna, sannan ya mi'ke ya je ya murzawa 'kofa mukulli sannan ya dawo cikin kasala, ya zauna ya dubi Hajiya ya ce. "Allah ne Ya yiwa yaron nan Auwalu rasuwa!". Hajiya ta dauke numfashi tana dubansa. "Alhaji wanne Auwalun?" Ya amsa mata yana kallonta. "Auwalun Rumaisa'u". Sai ga Hajiya a tsaye cikin wani matsanancin firgici, sai dai ta had'a shi da fadin. "Innalilahi wa'inna ilaihi raji'un, Alhaji hatsari ya yi, dama ba shi da lafiya?" Alhaji ya yi zuru yana kallonta tsawon fiye da minti daya, ita kuma tana ta faman kai wa da komowa tana ambaton innalilli wa inna ilaihi raji'un har sai da ya fahimci ta kai adadjin da ya kamata ta nemi wani abin, sannan ya tare ta. "Zauna mana, wannan muryar da kike son ki daga mana zata 6allo mana ruwa". Ta koma ta zauna amma kuka mai keta zuciya ya bijiro mata, sai dai ta hana shi fitowa ya sake. "Alhaji ba shi da lafiya ne?" A sanyaye Alhaji Ya amsa mata. "Wai Hajiya sai mutum ya yi cuta Allah ke kar6ar ransa? Ji nake lokacin mutum na cika yake komawa ga Ubangijinsa? Irin wannan tambayoyin ba su da wani hurumi tunda ba za su ta6a dawo da wanda ya tafi ba tare da cuta ba". Hajiya ta ci gaba da kuka cikin jero kalmomin yabo tare da kururuta halayen Auwal na kwarai, tana had'awa da nemo masa rahamar ubanhiji. Tsawon wani lokaci Alhaji ya yi dif cikin tsabar alhini, har sai da ya sami ga6ar abin cewa da ta fara sambatun halin da Rumasa'u zata shiga. Alhaji ya sauke numfashi ya ce. "A halin yanz abin da ya fi zafafa zuciyata ke nan, ko bayan dawowarmu ma'kabarta duk san da mahaifinsa ya dube ni cikin kuka ya ke maimaita min. Rumaisa'u ta yi rashin masoyi... duk wanda zai yi kukan rashinsa bayanta zai bi... maganata ta 'karshe da shi a kanta ne, inda yake ce min...idan ina tare da damuwa ba zata wuce na tausayinta saboda rauninta na mace, da kuma lalurarta ba. Wanda wannan zai iya raunana zuciyarta ya iyayi mata illa, ina kuma cike da tausayinta idan ban zamo mijinta ba yadda na ga ana gudun aurenta... Ina tsoron mata auren wanda zai kasa kyautata mata ya kyautatawa rayuwarta... Gaba dayan damuwata akan yadda Rumasa'u zata sami rayuwarta ne..." Hajiya ta 'kara fashewa da kuka ta ce. "Yanzu zancen da nake maka tun safe ta ke neman wayarsa, in ka ga yadda hankalinta yake tashe sai ka rantse ta sami labarin rasuwar tasa ne..." Innalillahi wa inna ilaihi raji'un". Alhaji ya fad'a cikin dafe kai, sannan ya dago ya dubi Hajiya ya ce. "Yanzu yaya za mu yi?" Hajiya ta ware hannu cikin kuka. "Ban sani ba Alhaji". Falon ya 'kara daukar shiru, ya mi'ke ya shige wanka, har ya fito Hajiya na zaune gurin tana faman sharar hawaye, shi kansa ya rasa da kalmar da zai ce ta yi hakuri har ya kintsa ya zo ya kuma zauna wa. Falon ya 'kara daukar shiru, ya mi'ke ya shige wanka, har ya fito Hajiya na zaune gurin tana faman sharar hawaye, shi kana ya rsa da kalmar da zai ce ta yi hakuri har ya kintsa ya zo ya kuma zauna. "Ki bar kukan nan haka, mu taru mu samo wa yarinyar nan mafita, ta ina za a shero mata wannan mummunan labarin? Ina tsoron shide mana wallahi, ga ta dama ba mai isasshiyar lafiya ba". Hajiya ta dago ta dube shi idanunta jawur ta ce. "Mu 6oye zuwa gobe, ko jibi kafin sannan mun samo abin cewa". Alhaji ya yi kasa'ke, sannan ya ce. "A yi waya a sanar wa mahaifinta, inda hali su zo nan mu taru mu san ta inda za mu 6ullo mata". Hajiya ta yi saurin gyada kai cikin amincewa. Hafsat da Hajiya sun wuni suna kuka a 6oye, yayin da Rumaisa'u ta wuni cikin muguwar kasala da hasashe iri-iri akan Auwal, wanda wayar da ta ke masa ma ta daina shiga, ma'ana an kasheta ko da kashe kanta. Ko kwayar abinci ba ta kai bakinta ba, hana rantsuwa ta wuni tana makar ruwa sai rake ga6a hhudu da ta sha. Su kansu saboda lalurarta ta damu da shan su bisa dole. Bayan sallar la'asar dai hakurinta ya 'kare, tana sanye da hijabin da ta yi sallar ta za'kulo Hafsat a can dakin baccinsu tana kudundune akan sallaya ta

Chapter 7 of 21