Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ni, Amman zan yi 'kokarin kammalawa da wuri naci gaba.... Shekararta ta 'karshe a B.U.K, Hafsat ta kammala N.C.E har ta fara aiki, mahaifanta sun dawo Abuja da zama. A wannan shekarar ne ta hadu da gwarzon masoyin da ta ke jin har duniya ta nad'e ba zata yi irinsa ba. Ba wai tana rasa masoya ba tuni, sai soyayyar ba ta wani nisa sabo rashin goyan bayanta, ko kuma in sun san matsalarta su kauce. Sun hadu a wata laraba ne tana tsaye a bus stop cikin B.U.K ner site tana jiran motar da zata kai ta old site, ita kadai ce tsaye a wajen, sai fama ta ke da ri'kon tafkekiyar lema (umbrella) a hannu saboda hadarin da ya fara d'aurewa, zai iya zubar da ruwa bagatatan, saukar ruwa a jikinta kuwa wani tushen tashin hankali ne da zai iya motsa ciwonta. Dai-dai wannan lokacin AUWAL ya zo giftawa ta gabanta da motarsa. Ta bi motar da kallo cikin tunanin yadda suke kwashe da Mominta a hutun da ya gabata. "Rumaisa'u da zaki iya tu'ko a Kano sai na sai miki mota, saboda yau da gobe, duk safiyar Allah da yammaci sai na tuno yadda za ki fita, ko za ki dawo gida. Sai na dinga jin kamar zan yi tsuntsuwa na zo na dauke ki, na san wahalar da d'alibai suke sha". Ta dubi mahaifiyarta cike da so da 'kauna, ta ce. "Momi ai kina min addu'a in Allah Ya so ba zan ta6e ba". "Duk da haka zan iya siyen motar?" Ta kad'a kai ta ce. "In hankalinki zai fi kwanciya ki siya mana..." Momin ta tareta da fad'in. "To wacce iri kike so, fad'a min idan kud'ina ba su kai bai in nemi taimakon Daddynki". Rumaisa ta yi dariya, ta ce. "Ta daidai kudinki nake so". Momi ma ta sake yin dariya ta ce. "Shikenan, zan ba ki mamaki". Auwal ya kula da kallon da Rumasa'u ta bi motarsa da shi ta madubi, kasancewar shi ma ya sa mata ido, kawai sai ya taka birki, sannan ya yo baya ya risketa. Ganin hakan ya sa ta dauke fuskarta zuwa kallon wani guri daban. Ta ma ajiye lema ta bude jaka ta ciro golas ta 'kwama. Auwal da ta 'kara jan hankalinsa, sai ya bude mota ya fito ya zagayo wajen tana share fuska. Ya dubeta sama da 'kasa ya ce. "Mece! Mace akwai waskiya, yadda kika yi fuskar nan ba dan na ga sanya kika zubo minido ba, in na kwana dubu ina rantsewa babu wanda zai yarda idan na ce kin 'kyasa". Da sauri ta dago ido ta dube shi, sannan ta dubi motar a ta'kaice, ta ce. "Ba kai nake kallo ba..." Ya tareta da sauri. "Wa kike kallo?" Ta nuna masa motar tana cewa. "Ga ta, ai ta fi ka kyau". Ya dan ja da baya baki bude na alamar shan mamaki. Ya kalli motar tasa, sannan ya dubi kansa yana gyara kwalar riga tare da gilashin idonsa, cikin dariya sosai ya dafa motarsa ya ce. "Yanzu wannan ta fini kyau don Allah" dube ni fa ki gani son kowa 'kin wadda ta rasa, ni ba dogo ba, ni ba gajere ba, ni ba fari ba, ni ba ba'ki can ba. Ga ido, ga dogon hanci, shape d'in ba irin na maza, komai ya ji fa kar ki bari ki yi asara yarinya. Mota ki kyaleta in kina raye sai ki ga kin yi wadda ta fi ta... Ni fa na ma tsaneta daga yau... Dan kishi ne da ni..." Yanzu ta daga kai suna duban juna ita da shi, kai tsaye ba za zummar komai cikin ranta game da shi ba, sai game da maganganunsa, kasancewarta mai sanyin hali tana son mutum mai barkwanci. Ba ta sami abin cewa ba, ya rigata da fadin. "Ya ya na ji zaki d'an yi manejin tafiyar da ni?" Karon farko ta yi murmushi ta girgiza kai. "Ka yi ha'kuri a fatar bakina kawai kalmar ta tsaya, na bi motarka da kallo. Amma zahiri ba ita din nake nazari ba, wata duniyar tunanin na tafi daban ka san ana haka ko?" Ya kada kai yana murmuashi. "Na sani, amma dai kin ji na ce bana son kishiya". Ta sunkuya tana murmushi ta dauki lemarta ta mi'ke tana fadin. "Ko dai kishiyi?" Suka yi dariya su duka. Ya kar6i lemar hannunta. "Zo mu tafi kin ga ruwa na shirin sauka, kar ya daki fuskarki ya yi mata illa". Ta girgiza kai tana murmushi. "Na gode kwarai, amma ba na hawa lift.." Da sauri ya tareta. "Wa ya fada miki lift za ki hau? Ke da motarki... Na ramtse zaki iya shafe komai a duniyata saboda haka ke ce alfarmar tawa ba ni zan zama alfarmarki ba". Ta 'kara dubansa da kyau, a sanyaye ta ce. "Wannnan dokin fa? Daga ganin sarkin fawa sai miya ta yi..." Ya sake tare da fadin. "Wata 'kila ina daga masu afkawa rijiyar so farad' d'aya. Tun daga nesa fa na hango ki inuwarki kawai na kalla na ji wata 'kwa'k'kwar zumunta ta sar'kafe zuciyata, da na 'karaso na kalli fuskarki sai kawai na ji mun zama JINI DA TSOKA d'aya. TA Sake dubansa da kyau tana dariya, abin da ta ke ji a ranta game da shi, shi ne ya iya dad'in baki, da ba ta dandani shekaru da yawa a duniya ba, farat d'aya zai wafce imaninta. Ta lumshe ido kai tsaye, ta ce. "Ba na son 6ata maka lokaci ko juyar da karramammun kalamanka. Ga shi ciki dole na za6i daya". Kai tsaye shi ma ya amsa. "Kin za6i 6ata min lokacin in dai ba kishiya ne da ni ba, karramammun kalamaina kar ki wani kalli karamcinsu, yadda ya kamata su fito a kunnenki, wallahi ban tsara su dan in burge ki ba, zo mu tafi don Allah". Bai jira cewarta ba ya bud'e mata 'kofa. Ta d'an yi jim, sai ta kasa tankwa6ewa ta shiga motar.....GORAN DUMA ******10 Ya rufe sannan ya zagaya ya shiga yana mi'ka mata lemarta ya tashi motar. Har suka zo bakin gate kalma daya ta had'u su. "Mene ne sunanki?" Kai tsaye ta amsa masa. "Rumaisa'u Aliyu Ahmad". Ya ce, "Sunanki mai dad'i. Ni sunana Auwal Ibrahim Hadi". Ba ta tanka ba, shi ma bai kuma tankawa ba har suka zo bakin gate, wata iska mai 'karfin gaske ta taso da alamun yanzu ruwa zai sauka. 'Kirjin Rumasa'u ya fara dukan ukuuku cikin matsananciyar fargaba. Ta dubi maza da matan da ke tsaitsaye cikin tashin hankali. Ta tatabar duk yadda hankali zai tashi bai fice fargabar za su yi mura ba, ita kuwa in ruwa ya daketa zai wahala ba ta yi ciwon da ya kusantarta da ita da kabari ba. Rage gudun da Auwal ya yi ya sa fargabar ta 'karuwa, saboda zaton sauke zai yi, amma sai ta ga ya nufi titi zai haura. Ta sauke ajiyar zuciya, muryarta na sar'kewa ta dube shi ta ce. "Da ka taimaka ka dauki matan can, na san ba za a rasa wad'anda za su yi hanyar da zaka yi ba. Za ka sami lada idan ka taimake su". Ya d'an ja fasali yana duban titi, ba tare da ya dubeta ba. Ya ce. "Allah Ya kawo mai taimakonsu, ni ba na daukar mata a motata". Ta d'an juma tana dubansa, duba na rashin fahimta, sannan ta ce. "Ni ba ka gane nawa jinsin ba ne?" Ya yi murmushi ba tare da ya dubeta ba. "`Ka'k'karfar ala'kar da zuciyata ta 'kulla da ke ya kori wancan 'kudurin nawa daga naki jinsin. Kin zama 'yar gida a zuciyata da duk wani abu da na mallaka". Ta gaji da kallonsa ta kawar da kai, ruwa ya fara sauka da 'karfi. Cikin sauri ta 6alle jakarta ta fito da rigar sanyi ta saka tana 'kumbiya-'kumbiya. Bai tanka mata ba, amma dai hankalinsa na kanta duk da idonsa na titi, tana bayyana alamun jin sanyi, amma kawaicinta ya hana ta 'karasa zuge gilashin 6angarenta, kuma da hakan yasa ya yi mata aikin da ta kasa yana cewa. "Na lura kunama ce ke, kawaicinki kuma na son hana ki abin da kike so..." Ta yi 'yar dariya ta amsa. "Ni da na zo ci rani har ga Allah bai kamata in za'ke ba". Ya watsar da wannann batun nata, ya ce. "Ina zan kai ki?" Ta yi dira-dira alamar canki-canki, sai ta kasa za6ar gurin zuwa ta yi shiru kawai sanyi na kad'ata. Hankalinta ya yi gida, amma ta ina zata bi ta je? Ina za ta fake ta sami motar? Ya juyo ya yi d'an nazarinta, cike da mamaki ya ce. "Ina zaki je?" Muryarta na rawa ta ce. "Ai na kasa za6a ne. Bana son santi, ruwa in ya dake ni illa yake min. Da makaranta zan je amma na fasa saboda sanyi. Yanzu in ka sauke ni kafin na sami motar ma ruwan ya yi min abin da ya ga dama". Ya ci gaba da kallonta cikin nazari, bai fahimci abin da yake son fahimta ba. Ya kad'a kkai ya ce. "Ni ma ba zan iya ajiye ki ruwan ya dake ki ba. Ina da ganawa 'karfe uku, sai dai a yi min uzurinta. Ina ne unguwarku?" Muryarta ta ci gaba da rawa, saboda laifin da ta ke jin zata yiwa kanta da gidansu. A ganta saurayi ya auketa kamar zubar da mutumci ne, amma kamar wannan za6in ya fi dukan ruwan. "Na gode Allah ya saka maka da alkhairi, a Gandun Albasa nake". Ya ce, "Hanyarmu daya ke nan, ni a Na'ibawa nake, ziyara na kawowa wani malamina, shekaru na biyu da barin makarantar na yi digiri na a nan na fara aiki a 'karkashin gwamnati. Ya kamata na ajiye iyali Allah bai kawo ba, sai yau Allah Ya yi min katarin d'aura d'amba". Rumaisa'u ta yi d'f! kamar ruwa ya cinyeta. Tausayin kanta ne ya hanata nazarin amsar da zata ba shi. Ta ji 'kaunarsa a ranta, sai dai ta 'ki yarda irin 'kaunar da ta ke d'orewa da aure ce, 'kauna ce kawai irin wadda d'an Adam ke wa wanda yake zaton mutumin kirki ne, ko kuma wanda ya yi maka alkhairi? Ta yi sororo tana kallonsa kawai yana jin kallon da ta ke masa a jikinsa, amma ya had'iye sn ya juya ya kalleta. Ta juya a hankali ta bi shi da kallo tare da sauke ajiyar zuciya, ba ta ce komai ba. "Ba ki da abin cewa akan abin da na fad'a?" Ta girgiza kai a nutse ta ce. "Kar ka 6atawa kanka lokaci na san ban cancanta zama iyali ba". Ya yi saurin yi mata duban rashin fahimta, amma ya ta'kaita zar6a6i wajen ce mata. "Ai ina tsammanin ba a yin komai babu hujja ko? Ki fada min dalilin zan duba na gani". Ta muskuta ta ce da shi. "Don Allah ka yi ha'kuri". Ya ya yi kasa'ke yana kallonta, sannan ya ce. "In dai ba laifi zan wa Allah ba, to ba zan iya hakura ba.. Ta tare shi ta fadin. "Ina fatan nan gaba ba zaka zarge ni da rufa-rufa ko yaudara ba?" Ya 'ki daukar maganarta da muhimmanci. Ba tare da nuna damuwa ba ya ce. "Ina saka rai Alkhairi ya biyo baya, idan kuma akasinsa ya samu zan dogara ga Allah, amma ki sani akwai laifinki ciki Allah ne ba za barki ba, musamman da yake a rufe kike ba ni uzirinki". Ta yi shiru kawai shi kuma ya share wannan maganar ya shiga tambayarta karatu da wasu abubuwa da yake jin suna da muhimmanci a cikin ala'kar da yake son 'kullawa da ita. Cikin ikon Allah sun wuce Gadon Kaya babu ruwan babu iska, ko hadarin ma babu, saboda haka ta ji ranya ta afu da son ta sauka ta hau motar haya ta 'karasa, amma ta kasa yi masa magana har sai da aka kira shi a waya ana nemanta wajen taro ya bayar da uzirinsa, yana sauke wayar ta ce. "Kawai ka sauke ni a nan na shiga mota na 'karasa, sai ka wuce sabgoginka". "Da yake tun farko na ke kika 'kirkirar min sabgogin ba, kar ki yi mamakin in na 'ki bin umarninki". Dole ta yi dariya ta share zancen. Ya tsayar da motar a harabar gidansu yana d'an zuba mata ido saboda yadda ya ga kamar ta kad'u da ganin wani da ya tsaya da motarsa kusan lokaci daya da su. Da sauri ya kalli motar dan ganin tana rawar jikin ficewa. Ta juyo ta dube shi da duban rashin fahimta. Ya nuna Yusha'u yana fadin. "Wane ne wancan?" Ta dubi Yusha'u sannan ta dube shi, a takaice ta ce. "Yayana ne". Ya yi zuru yana kallon Yusha'u, haka kawai ya ji hankalinsa bai kwanta da shi ba. Ya kad'a kai bisa dole ya bude 'kofar suka fita lokaci guda. Da sauri ya nufi Yusha'u da ke 'kokarin rufe mota ya yi masa sallama tare da mi'ka masa hannu. A wula'kance Yusha'u ya amsa idonsa na kan Rumaisa'u, sannan ya ce. "Yaya kuke da wannan?" Auwal ya yi zuru yana kallon Yusha'u da Rumasa'u yadda Yusha'u ya yi mata magana fuskarsa babu walwala ne ya ba wa Auwal damar nutsuwa ya karance shi. Akwai alamar nutsuwa a tsaiwar Rumasa'u, sai dai a rikice ta d'ebo masa amsa. "Dan ajinmu ne... Ya taimake ni ne saboda ruwan da ya tare ni.. Hanyarsa ke nan shi yasa ban nemi sauka ba da muka wuce inda ake ruwan. A gadarance Yusha'u ya ce. "Kina fad'a min hanyarsa ce dan kin shirya kullum ya dauko ki yana kawo ki ko? Ban san iyakar tsawon lokacin da zan dinga fad'a miki nan Arewa ba kamar can Kudu ba ne. Babbar 'kazanta ce mu a nan mace ta dauki namiji aboki..."GORAN DUMA *****11 Ganin yana neman tsinkata ta tare shi. "Lalura ce yaya Yusha'u, na yi gudun dukan ruwa ne". Yusha'u ya yi tsaki tare da yin gaba yana cewa. "Duk illar da dukan ruwan yake da shi, ai bai kai na sarayar da mutumci ba, koda yake wayewarku ta halatta muku haramci". Rumaisa'u ta yi suguri ranta ya yi mugun 6aci. Ta san Yusha'u bai iya magana ba sam! Haka yake yinta kamar kashi, amma a yau ta fara shakkar dan ta zo cin arzi'ki gidansu ne. A sanyaye ta dubi Auwal da ya yi shiru rungume da hannu yana kallon 'kasa, ta ce. "Na fa gode zan shiga ciki". Ya dago da alamun tunani ya dubeta. "Me yasa kika 'ki fad'a masa gaskiyar matsayin da na za6a mana? Sai kika ala'kanta mu da jabun dangantaka?" Ta dan ja numfashi, sannan ta amsa. "Har yanzu kai kake kid'a da rawarka. Da zaka bi ta tawa za mu yi sallama ne mu rabu har abada. Karatu ya kawo ni garin nan, ya kamata na ji da shi shi kad'ai... Mts! Ni bana son hargitse-hargitse wallahi". Ya fahimci cikin 6acin rai ta ke, saboda haka sai da ya shirya kalaman da zai mata. "Kina da wanda kika tsayar? Ta girgiza kai, fuskarta a daure. Ya numfasa ya ce. "Idan haka ne na tabbatar kin zo KANO ne dan mu had'u mu auri juna ba tare da na yi gi6i a karatunki ba, ki daina gaggawar yanke hukunci akan lamarin rayuwa. Da hakan gara ki zama mai dabarar tsara al'amuranki, ina neman alfarmar kar ki kore ni, kuma ban matsa miki ki so ni ba, amma ki ba ni dama mu fahimci ko zamu iya tafiya tare". Yanzu idonta cike yake da 'kwalla saboda takaicin kalaman Yusha'u, gidansu kawai ta ke tunowa da yadda ta ke da kima da mutumci a cikinsa. Auwal na ganin kwallarta ya dan shiga damuwa, amma a nutse ya tausasa murya ya ce mata. "Idan akwai matsala dan Allah ki fad'a mi kuka na nufin damuwa. A kalamaina ban ga abin da na fad'a da zai 6ata rai ba". Ta 'kir'kiro murmushin 'karfin hali dole ta ce masa. "Babu komai, Allah Ya yi mana jagora". Tun daga wannan ranar Auwal ya zame mata wani 6arin rayuwa, ya 'kware da samar da muhallan farin ciki a zuciyarta da kirkinsa da kuma yadda yake kula da ita da damuwa a cikin abin da ya dameta. Tun daga wannan ranar Auwal ya zame mata wani 6arin rayuwa, ya 'kware da samar da mujallan farin ciki a zuciyarta da kirkinsa da kuma yadda yake kula da ita da damuwa a cikin abin da ya dameta. Kullum sai ya zo gidansu, tare da cewa yana 6ata mata da yawan lokutai a waya, haka kuma takanas yake binta makaranta ya daukota, babban zunubinsu da ya tsayawa Yusha'u a rai ke nan saboda imanin da ya yi na cewa, duk yarinyar da ta je jami'a sai ta lalace. Ya rasa yadda zai fahimtar da Hajiya da Alhaji a matsayinsu na wadanda kamar su ke waliyantar da Rumasa'u saboda kyan hali. Rumaisa'u ta fara nisa cikin abin da ba ta za6a tsarabarsa a rayuwarta ba, wato SO, tana ji a ranta ita nakasashiya ce duk yadda so zai zama in ta amince masa wata rrana zai zame mata mad'aciya, amma a yanzu Auwal ya ture wannan tsarin a ranta, sai ya barta da zulumin yadda rayuwa zata kasance musu a gaba, zai rabu da ita ne, idan ya san ita sickler ce, ko kuwa zai yi shahadar aurenta? Za6i na 'karshe ne fatanta, sai dai zuciyarta na wuyatantar da yiyuwarsa. A yanzu sun fice watanni uku tare, duk wani laulayi da alayin cututtukanta babu wanda Auwal bai gani ba. Yau 'kafa ciwo, gobe ciki, jibi zazza6i, gata mura... Kai shi bai ta6a ganin mutum mai laulayi kamarta ba, sai ma 'kari saboda tsabar tausayin da ta ke ba shi. Kuma laulaye-laulaye nta ne ya koya masa tarin hanyoyin da zai nuna mata kulawa. Dan haka ya zama dan gida, dan gidan gaske a zuciyarta da zuciyar kowa ma a gidan in aka yi gefe da daya da murd'ad'd'e Yusha'u. Sai dai duk wannan sha'kuwar tasu ya rasa dalilin da yasa Rumasa'u ta 'ki amince masa manya su shigo maganar. Ya bata lokaci ya 'kara mata, amma har yanzu ta kasa gabatar masa da uziri, sai dai hakan ya 'ki ya dame shi dan yana da ya'kinin ya kai matsayin da ya fi 'karfin yaudara a zuciyar Rumasa'u, sai kawai ya zuba mata idon ganin gudun ruwa, musamman da yake karatun nata ya zo 'karshe. Wata rana sun fice goma na dare suna hira a zahiri daurewa kawai ta ke saboda cikinta da ke ta faman murd'awa. Ta daure din har suka yi sallama ta shiga gidan a birkice, zta wuce ciki Hajiya ta yi kiranta. "Zo nan Rumaisa'u, me yake faruwa na ga kina yamutse fuska?" Ta 'karaso ta zauna a gajiye. "Wallahi cikina ke min ciwo". Hajiya ta dubeta cikin tausayawa, ta ce. "Sannu, sai ki yi 'kokari ki sha magani, Hafsat taimaka ki murza mata tafarnuwar ki ta ce ki kaw mata". Hafsat ta tashi ta 6arin jiki tana yiwa Rumasa'u sannu ta wuce kicin ta d'ebo tafarnuwa masu kyau ta 6are, ta dandaka sannan ta zuba ruwa kofi daya ta tace da rariya ta kawowa Rumasa'u ta shanye. An fi awa daya kafin a samu ciwon cikin ya lafa, wannan ne kuma ya sa Hajiya ta tsokano maganar da ta ke jin yyinta ya zama dole dan ta fahimci Rumasa'u, so ya rufe mata ido tana shirin yin abin da za a ga laifinta. "Rumasa'u kun ta6a maganar ciwonki da Auwalu kuwa?" Alamun damuwa da nadama ya bayyana a fuskar Rumaisa'u, kwalla har ta cika mata ido, ta girgiza kai ta ce. "Ba mu ta6a ba Hajiya". Cikin zura mata ido, Hajiya ta ce. "Tyn farkon ne kika rasa hanyar sanar da shi Rumasa'u?" "Ban san za mu dore tare ba Hajiya". Hajiya ta yi shiru alamar nazari, sannan ta nisa ta ce. "Ni har na fara zargin ko ganin yawan laulayinki ya hana shi turo manyansa. Ga su Hafsa suna ta faman jiranki". Ta matse kwallar idonta tana amsawa. "Ni ce na ke dakatar da shi Hajiya, kuma na kasa sanar da shi dalili". Hajiya ta girgiza kai ta ce. "Wannan kuma ba dabara ba ce kika yi, za ki ta zama haka ne Rumaisa'u? Ai a rashin kira karen bebe yake 6ata, ki kokarta ku tattauna lamarin". Cikin sanyin jiki Rumaisa'u ta ce. "Shikenan zan kokarta Hajiya". Ta gama shin bacci ke nan ya mmako mata waya, ta dauka da kasalar rashin 'karfin jiki. "Auwal ba ka jin bacci?" Muryarsa a d'ashe ya amsa. "Na kwanta ya 'ki zuwa Rumasa'u, abubuwa barkatai sun cushe a 'kwa'kwalwata. Ga kadaici ga matsaloli". Ta dan yi dariya ta ce. "Me ya dami ranka haka Auwal?" Ya sauke numfashi.....GORAN DUMA ****12 "Kafin mu rabu na fahimci kamar ba kya jin dad'i, na taho da tauayinki da neman hanyoyin da zan samar miki waraka ko da na dauke kewa da 'karfafa gwiwa ne, amma duk kin bi hanyoyin da hakan za ta afku kin toshe. Na fara sarewa Rumasa'u dan na fahimci kamar kin raba zuciyarki biyu ne kin bar min daya na sani, dayar kuma kike wahalar dani da ita. Wata irin 'kaunarsa ta dingo bijiro mata, tana nemansa ta 'kwalla, tana kokawar daurewa yana gagara. "Auwal wannan ne zai hanaka bacci? To in dai ni ce ba za a haifi matsalolin da za su 6ata ranka da ni ba. Za mu sami lokaci nan kusa mu tattauna... Amma ina son ka a jiye a ranka soyayyarka ce ke hana ni yin abin da kake hasashe ina jinka da matsayin wani 6angare na jikina, wanda rashinsa zai gutsire rayuwata, amma na 'kure fatan hakan zai gaza faruwa". A raunane ya ce "Saboda me? Rumaisa'u duk yadda nake da matsayi a zuciyarki da sha'kar numfashinki d'igo ne na matsayinki a wata zuciyar, na kuma dami raina da son kai 'karshen buri a kanki kafin mutuwa ta runtse ganina, ke kuma kin kasa gane hakan..." Ta yi saurin tare shi. "Haba me ya kawo zancen mutuwa Auwal?" Shi ma ya tareta da nasa batun. "Ai ya zama dole, 'karuwar burika, cika wasu da su6ucewar wasu alamu ne na kusantar kabari sai raina yake ciwo da hasashen mutuwa zata iya riksta ba tare da na cika burin samunki ba." Ta fara hawaye sosai, dan haka ta jima ba ta tanka ba, har ta fitar da sautin kukanta kadan, sannan a cikinsa ta ce masa. "Ba na fatan dai-dai da kwayar zarra in cutar da kai Auwal, kuma bana son rabuwa da kai.." Ya tare ta a dan 'kuntace. "Shikenan sai ki bar mu muyi ta bulayi a soyayyar da ba ta da rana, wadda ta ki ta zuciya ta saba da ta fatar bakinki, kina sona amma kin kasa ba ni damar mu kasance 'karkashin sunna... wannan makahon so ne..." Ta yi kokarin tare kukanta, ta ce. "Akwai matsala ne Auwal, ni ke nan yau lafiya, gobe babu. Zan zame maka dawainiya in gundure ka, shi yasa ba na son cin karo da kukanka Auwal". Ya yi dariyar da ta fad'ad'a masa 'kirji ya ce. "Wa ya ke dorawa wani lalura Rumaisa? In Allah Ya so sai Ya yaye miki, ai babu cutar da ba ta da magani. Ita kanta cutar ma wani maganin ce, domin tana kankare zunubai... Ni ma da nake son daukar dawainiyarki ladan zan samu idan na kula da ke, duk sanda aka ce ba ki da lafiya sai na ji da tare muke sai na fi samun nutsuwa..." Ta 'kara fashewa da kukan da ya tsorata shi. A rikice ya ce. "Wai don Allah me yake faruwa ne? Rumaisa na kaa canko dalilan wannan kukan naki". Cikin kukan ta ce "Na gode da niyya da fatanka, amma ciwo na mutuwa ce kadai zata raba... Saoda haka aurena da kai yana nufin ka yi ta danniya da hakuri a kaina har 'karshen rayuwata, domin haka Allah Ya halicce ni, haka kuma Ya so ya ganni..." Ya rasa fassarar da zai wa maganganunta, rashin yanke shawarar ya sa shi yi mata tambaya a gajarce. "Wai wanne irin ciwo ne?" Kai tsaye cikin dakewa ta yi karfin halin amsa masa. "Sickle cell" Ya ji kamar ta doka masa guduma a 'kirji, cikin 'yan sakanni wasu miliyoyin tausayinta da fargabar yadda lamuransu zai kasance ya mamaye masa 'kirji, dan ya san ciwon sickle cell ba da wasa ba kasancewar wani abokinsa sikila ne ya dad'e da sanin yadda masu ita suke shan kashi sai dai wannan 'karamar matsala ce idan aka kwatanta da neman makomar 'ya'yan da za su haifa. Duk da a rikice yake bai kasa 'ko'karin tattara kalaman da zai 'karfafa mata gwiwa ba. "Mene ne matsala a kasancewar sickle Rumaisa, ko ke kika yi kanki dan me za ki raba kanki da ni ballatana Ubangijin da Ya yi ni Ya yi ki, ba domin na fiki ba? Ki zama mai tawakkali da ha'kuri da rayuwa sai matsalolinki su zame miki kaffara. In kuma domin wannan kike gina katanga tsakanin da kasancewa tare, to ni ban fahimci gatan da kike son yi min ko kike son son yi wakanki ba". Yanzu ta rage kukan da ta ke, dan a zahiri hankalinta ya soma kwanciya, duk da ta san bai kamata ya kwanta din ba. Ta nisa ta ce. "Kar ka yi gaggawar yanke hukunci Auwal, ka zauna ka yi tunani da kyaun duk matsaloli a kaina ka lissafo suka ga yadda zaka iya tarbarsu, yadda zaka dinga dawainiya da ni, dawainiyar aljihu da ta KWANJI, ha'kuri da ni wajen kukan ciwo da hakurin wasu kulawa daga gare ni lokacin ciwo in duk wadannan sun zama sau'ki a gareka Auwal makomar 'ya'yanmu ba zata zama sau'ki ba matu'kar ba ka kasance wanda ba zai bayar da gudunmowar da ba zaka haifi sickler ba". Ya ja numfashi sosai saboda rashin abin cewa, amma dole ya nemo shi. Ya ja numfashi sosai saboda rashin abin cewa, amma dole ya nemo shi. "Yin daainiya da ke, da kuma hakuri da laulayinki ni ba zan ta6a kiransu matsala ba Rumaisa, ina son ki soyayyar da nake jin ko mugun hali ne a jininki ba zata gaza ba, bare wannan jarrabawar ta Ubangiji da idan kika haye ta da tawakkali, na haye ta da jurewa dawainiya da ke zamu iya samun aljanna da ita. Batun 'ya'yanmu shi ne hanzari, amma wannan zai hana ki aure har abada ke nan Rumasa'u? Kafin haduwa da ni wanne tanadi kika yiwa kanki a fannin aure, me yasa kike ganin zan bayar da gudunmowar da zamu haifi sickler?" Ta amsa masa a raunane. "Ban ta6a fitar da rai zan yi aure ba, sickle cell kuma ba ciwo ne da za a ce ka auri mai shi ya zama waraka ba, domin za ku samar da iyali irinku ne gaba daya, amma dai ban ta6a hasaso aurena da rayuwar auren wani abu ne mai sau'ki ba. Ina sonka Auwal wallahi ba na fatan duk wani abu da zai cutar da kai, na san kuma ko yaya ne aure na zai iya zame maka matsala ko ta fannin 'ya'yanmu..." Ya tare ta da sauri. "Shi yasa na tambaye ki, wacce irin gudunmowa zan bayar da kike ala'kanta ta da haihuwar sickler?" Ta jima cikin shiru, sannan ta ce. "Idan ka ji a ranka zaka iya aurena, kuma a gidanku za a barka, shi ne zamu tuntu6i likitoci dan samun shawarwari, a iya maka gwaji kuma a gano kai waye, ta nan zamu iya sanin makomar 'ya'yan namu". Yanzu ya fara samun nutsuwa, saboda haka cikin doki ya ce. "In Allah Ya so cikin satin nan sai mu je asibitin, amma ki sani duk yadda bincike zai nuna ba na ji zai iya yi min katanga da aurenki. Ki cire shakku daga ranki Rumasa'u, ina yi miki soyayyar d aban san matsaloli a tare da ke". Ta yi shiru tsawon wasu sakanni sannan ta ce. "Abin da na fi so da kai Auwal ka fara tuntu6ar magabanka shawara a kaina, kar ka biyewa soyayyar zuciyarka

Chapter 5 of 21