Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
take zagayawa a cikin ta, duk kuma da girman nan nata sai ta zama bata isa abin iya kallo ba cikin abin da Ubangiji ya halitta amma sai ya kebance ita kankanuwar duniyar d niimomi masu tarin yawa, Ya karrama dan Adam a cikin ta sannan Ya bashi zabin makomarsa a hannun sa, a cikin ta aljanna ko wuta, wanda yabi Allah cikin ta yayi kunci a gare shi to muminancinsa ya bayya na, wanna ya ki yarda da AllantakarSa ko ya zama pandararren bawa to tayi masa yalwa rabonsa kenan. A yanzu hawaye ne ke diga a puskarta ba kuma wannan karatun kadai ya sanyata hawaye ba har da tuna yadda duniyar nan ta shude mata da mutun muhimmi a cikin ta, kamar yadda ta tabbatar ita ma wata raba zata shude. Rauninta kuma ke raya mata ba zata taba samun wanda zai maye mata gurbinsa ba, wannan tunanin ne ya pado mata da na sakon mahaukacin masoyi, a rikice ta zauna dandamalin dutse ta dauko wayarta a jaka cike da doki hannunta na karkarwa ta danna muryar... Rumaisau kin taba nazari akan zucia? Harumin gaske ne ke rike akalarta ya ja sabanin ta jashi, tawa zuciyar kamar ni take ja. Ma'ana ban cika jaurimi amma na kasa yarda ni rago ne dan na rike hujjar zuciyata na ja ne ga alkhairi ne wato ke. Zuciyar tawa na da karpin hali ko? Bana ganin bakinta ni kuma dan ta gamsu kin hada dukkan alkhairan da idan anyi paputuka a kanki ba a sarayar da lokutar a wopi ba, dan ma duniar nada abun tsoro ko? Gangancin shigar haske cikin duhu da shigar duhu cikin haske ya isa kada zuciyar mai imanin mutuwa wadda bata bukatar imani cikin sharudanta, ga wanda ya yarda da ita da wanda bai ma yarda da ita bam duk ba wanda take ragewa duk sanda na yi tsaye cikin lambu ina kallon sararin samania sai na cika da shakkar anya kuwa ozone layer da akce yana kekkecewa ne yake kara gudun dunia ba waccan mutuwar ke kusatoni ba? Duk sanda na tuna haka sai nayi kwalla ina ganin kamar zanyi mutuwar da babu gata, wato wadda na ke so bata yarda ina son ta ba. Mukwana lapia. Bata gama tantance matsayin da zuciyarta da azancin ta suka karbi sakon mahaukacin masoyi na yanzu ba ta hanga yushau ya nupo ta kai tsaye yana ta sauri kamar mai shirin tashi sama.. Ambaton MUTUWA wadda take da kishiyar rayuwa asakon mahaukacin masoyi ya sata kallon Yushau na tahowa garau! Saboda tunaninta da yake son tino rayuwar ta ta baya. Yau da gobe a rayuwarta. Mutuwa a cikin rayuwarta. Kaddarori marasa dadi na rayuwarta. ASALIN RUMAISA'U. Mahaipin ta... . in shaa Allahu gobe zamu ci gaba daga inda muka tsaya.. . Dan AuntyGORAN DUMA 5 . . ASALIN RUMAISAU Mahaipinta Aliyu Ahmad dan karamar hukumar Rogo ne a kano. Mahaipiyarta Khadija inyamura ce mutumiyar Enugu wadda ta musulunta a hannun mahaipinta sukayi aure da zama a garuruwa daban-daban kasancewarsa dan sanda. Mahaipinta dan dangi ne sosai a kauyen Rogo da cikin garin Kano duk da cewa su biyu ne kacal a gurin nasu mahaipan wato shi da kuma yayansa Usman mahaipi ga Yusha'u da kannensa mata hudu sai Mubarak auta, mahaipinta da mahaipiyar ta akwai zama na soyayya da pahimtar juna mai kwari a tsakanin su, Allah bai wadata su da iyali masu yawa ba daga yayarta Balaraba (Aisha) sai ita auta har a halin yanzu wajen uwa da uba. Bayan rauni na kasanxewarta a jinsin mata masu rauni sai wata jarrabar Ubangiji Yayi mata na kasancewarta daga masu pama da larurar nan ta sankarar jini (sickle cell ) cutar da gatan da iyayenta ke nuna mata bai hanata tasowa cikin wata irin mawuyaciyar rayuwa ba , alal alakka sun karbi kaddarar haihuwarta da Ubangiji Ya nupe su dayi suna godia a gare Shi tare da rashin gazawa ko kosawa cikin tarin dawainiya gare ta yadda ya kamata, duk wani sikila ya samu. Iyayenta naji da ita suna tausaya mata suna tattalinta ninkin yadda suke tattalin yayarta Balaraba sun jure duk wani alayi na ciwonta, kai karewa saboda ita innarta ta koma karatu bangaren lapia bayan tayi digirinta na parko akan Na'uwa mai kwakwalwa (computer engr.) kapin aure, bayan sun haipeta da shekara daya ta karkade zaninta ta koma makaranta inda ta karanto wanda ya kara taimaka mahaipiyar kwarai wajen yadda take kula da rayuwar ta. Tayi karatu a tape kuma cikin gata kamar yadda ya kamata har matsayin kammala babbar sakandire ta pito da sakamako mai kyau, saboda haka ta sa ran shiga Jami'ar Bayero ta kano dan karanta aikin jarida. A daidai wannan lokacin mahaipanta zaune a enugu saboda haka ta debo zaman karatunta ba dan son ran iyayen ba ta dawo wajen yayan mahaipin nata Alh Usman wanda ke zaune a kano kuma shahararren dan kasuwa a kasuwan kantin kwari. Daidai wannan lokacin Balaraba yayarta ta auri Mukhtar ma'aikaci a garin Abuja , shima Alh Usman Ya aurar da yayansa mata uku, Atika, asiya, maimuna sai Hapsat kadai wadda take tsararta sannan Mubarak sai ko babban yayan su Yusha'u da ya tasamma zama tuzuru babu aure. Yushau ba a gaban iyayensa ya girma ba tun daga yaye kakarsu ke rike dashi a Rogo har bayan rasuwarta ma sai yaci gaba da zama inda yapi wayo , can yayi firamare da sakandire yazo gidan su kano yayi NCE a FCE kano bayan kammalawan sa saboda sabo da rogo sai ya kuma komawa can ya kama aikin koyarwa amma idon kudi da ya gani lokacin zaman karatunsa a kano yake zuwa kasuwa gun mahaipin sai ya hana shi mayar da hankali ga koyarwar inda bai hada shakaru biyu cikinta ba ya ajiye ya dawo kano yaci gaba da harkokin kasuwanci. Duk sauran kannensa ma sunyi karatu daidai gwargwado na iyakar sakandire suka yi aure, Asiya da Atika da suka auri yan boko sun sami damar ci gaba har sun para aiki, amma Maimuna na zaune a gida da kasuwancinta, albarkacin Rumaisau yabawa hapsat damar dorawa daga sakandiri bayan nacin ta sami B.U.K ta gaza sai ta bige da sa'adatu Rimi collage. Hankali da nutsuwar Rumaisau tare da rashin kuzarinta wani abu ne da sam baya dada yushau da kasa, yana mata kallon wata muguwar shagwababbiya kuma mai shegen raki, wadda yake ganin ba a kanta aka para ciwo ba amma akwai alamar tapi kowa kururuta shi, kullun ita ke nan cikin ciwo da neman uzuri ayadda ta baro gidan su suke kirkirar mata shagwaba da mayar da kai baya haka anan gidan nasu babu wanda ta rage, alh da Hajia , hapsat da Mubarak kuma suka pi kowa taya bera bari a wajen su komai na Rumaisau na musamman ne kai saboda Rumaisau sun hakura da yawa daga jin dadin rayuwar su, saboda Rumaisau Alhi ya cire duk wani A.C a cikin gidan, panka idan Rumaisau na guri cikin su hudun nan babu mai shan iskarta, in kuwa shi ya guntse ido zai kunna duk zasu taso kansa da korapi. Duk wani aikin gida na mata babu ruwan Rumaisau da shi ko ta sa kanta zatai hajia kan hana, abincinta na musamman ruwan wankanta na musammam, duk inda zata pita kuma sai anyi dawainiyar da ba zata yi tapiar kasa ba, ba ta da aikin da ya wuce taci ta sha ta pita yawon makaranta, anjima kuma ta ishe su da rakin ciwo. Ba wannan ne kadai abin da ke damun Yushau akan rumaisau ba, har da matsayin karatunta wanda sam baya kaunar wata mace ta taka matsayinsa, in kuma har ta taka din to yana mata kallon wata gagara kundila a duk wani nau'in halin tsiya. Wadannan dalilan ne suka hana shi iya boye kin da yake wa rumaisau wanda ya hada da hapsat saboda tattalinta ga rumaisau da kuma kama turbar rumaisau na zurpapa ilimin boko. Hakurin Rumaisau da zaton alkhairinta yasa bata taba hasashen yushau ya tsaneta ba, pahimtar da tayi masa kawai shine shi daban ne a cikin gidan mai wani murdadden hali da kake kasa passarawa, yana da pushi yana kuma da halin sauye-sauye, saboda haka ta koyi zama dashi, bata cika nuna shigarta wani hali a gaban sa ba dan gudun yaki bata muhummanci taji haushi, bata daguwar hira dashi , bata neman taimakonsa ko wanne iri, kuma idan hajia ko Alh sunyi masa umurnin kaita makaranta ko asibiti yana paman kumburi ta kan bashi hakuri tare da karawa kanta nustuwa dan kai yaga giggiwarta, amma duk da haka bata tsira ba, akwai wani lokaci da Alh ya sanya shi kai ta taronsu na masu ciwon sikila ya jirata har aka tashi taron, a hanya sun taho yana paman cika da batsewa har ya pashe da cewa '' inda zaka san ciwon nan shipcin gizo ne har da wata kungiyam wai dan tsabar lalacewar zamani ciwon ake wa kungida ko ya san ba ciwon ne ya dame ku ba wata hanyar neman kudi kawai kuka mayar da ciwon. Rumaisau tayi murmushi tana kallon tagar motar kapin da kyar ta samo abin cewa '' yaya yushau kamar yin kungiyar zai pi rashin ta ampani, ni dai tana kara min imani da godia ga Allah wanda ya halicce mu yadda Ya so ba dan kiyayya ba, sai dan Ya zamo jarrabawa a gare mu kawai dai kayi mana patan ya zama mana kappara. Yushau yayi wani tsaki sannan ya tsule bakin sa. Shekararta ta karshe a BUK hapsat ta kammala NCE har ta para aiki, mahaipanta sun dawo Abuja da zama a wannan shekarar ne ta hadu da gwarzon masoyin da take jin har dunia ta nade baza tayi irin sa ba. Ba wai tana rasa masoya ba ne, sai soyayyar bata wani nisa saboda rashin goyon bayanta, ko kuma in sun san matsalarta su kauce. Sun hadu a wata laraba ne tana tsaye a bus stop cikin BUK new site tana jiran motar da zata kai ta old site ita kadai ce tsaye a wajen sai pama take da rikon tapkekiyar lema a hannu, saboda hadarin daya para daurewa, zai iya zubar da ruwa bagatatan, saukar ruwa a jikinta kuwa wani tushen tashin hankalli ne da zai iya motsa ciwonta. Daidai wanan lokacin Auwal Yazo giptawa ta gabanta da motarsa. Tabi motar da kallo cikin tunanin yadda suka kwashe da Mominta a hutun daya gabata. ''Rumaisau da zaki iya tuki a kano sai na sai miki mota, saboda yau da gobe duk sapiyar Allah da yammaci sai na tuno yadda zaki pita ko zakii dawo gidam sai na dinga jin kamar zanyi tsuntsuwa nazo na dauke ki m na san wahalar da dalibai suke sha'' ta dubi mahaipiyarta cike da so da kauna tace momi ai kina min addua in Allah Ya so ba zan tabe ba. Momi ma ta zura mata ido tana murmushi tace duk da haka zan iya siyen motar? Ta kada kai tace in hankalinki zaipi kwanicia ki siya mana... Momin ta tareta da padin to wacce iri kike so pada min idan kudina basu kai ba in nemi taimajon dadinki. Rumaisau tayi daria tace ta daidai kudinki nake so. Momi ma ta sake yin daria tace shikenan zan baki mamaki. Auwal ya kula da kallon da Rumaisau tabi motarsa dashi ta madubi. Kasancewar shi ma ya sa mata ido kawai sai ya taka birki , sannan yayo baya ya risketa, ganin haka yasa ta dauke puskarta zuwa kallon wani gurin daban, tama ajiye lema ta bude jaka ta ciro gilas ta kwama. Auwal data kara jan hankalinsa sai ya bude mota ya puto ya zagayo wajen tana share puska ya dubeta sama da kasa yace '' Mace! mace akwai waskiya, yadda kikayi puskar nan badan naga sanda kika zubo min ido ba in na kwana dubu ina rantsewa babu wanda zai yarda idan nace kin kyasa.'' da sauri ta dago ido ta dube shi sannan ta dubi motar a takaice tace ba kai nake kallo ba...'' ya tare ta da sauri wa kike kallo? Ta nuna masa motar tana cewa gata ai tapi ka kyau. Ya danja da baya baki bude na alamar shan mamaki ya kallo motar tasa sannan ya dubi kansa yana gyara kwalar riga tare da gilashin idon sa cikin daria sosai ya dapa motarsa yace yanzu wannan tapi ni kyau don Allah? Dube ni pa ki gani son kowa kin wadda ta rasa , ni ba dogo ba, ni ba gajere ba, ni ba pari ba ni ba baki can ba, ga idom ga dogon hanci, shape din ba irin na maza , komai yaji pa kar ki bari kiyi asara yarinya. Mota ki kayleta in kina raye sai ki ga kinyi wadda tapi ta... Nipa na ma tsaneta daga yau... Dan kishi ne dani... Yanzu ta daga kai suna duban juna ita dashi kai tsaye bada zummar komai cikin ranta game da shi ba sai game da maganganunsa kasancewarta mai sanyin hali tana son mutun mai barkwanci, ba ta sami abin cewa ba ya rigata da padin yaya naji zaki danyi manejin tapiyar dani? Karon parko tayi murmushi ta girgiza kai kayi hakuri a patar bakina kawai kalmar ta tsaya, bani motarka da kallo amma zahiri ba ita din nake nazari ba, wata duniyar tunanin na tapi daban kasan ana haka ko? Ya kada kai yana murmushi ma sani amma dai kinji nace bana son kisiya? Ta sunkuya tana murmushi ta dauki lemarta ta mike tana padin kodai kishiyi? Sukayi daria su duka ya karbi lemar hanun ta. Zo mu tapi kinga ruwa na shirin sauka kai ya daki puskarki yayi mata lilla. Ta girgizakai tana murmushi nagode kawai amma bana hawa lift. Da sauri ya tareta waya pada miki lift zaki hau? Ke da motarki.. Na rantse zaki iya shape komai a duniata saboda haka kece alparmar tawa ba ni zan zama alparmarki ba. Ta kara dubansa da kyar a sanyaye tace wannan dokin pa? Daga ganin sarkin pawa sai miya tayi...'' ya sake tareta da padin watalila na kalla naji wata kwakkwarar zumunta ta sarkape zucia ta, da na karaso na kalli puskarki sai kawai naji mun zama JINI DA TSOKA daya. Ta sake duban sa da kyau tana daria abin da take ji a ranta game dashi, shine ya iya dadin baki, da bata dandani shekaru da yawa a dunia ba , parat daya zai wapce imaninta. Ta lumshe ido kai tsaye tace bana son bata maka lokaci ko juyar da karramammun kalamanta, gashi ciki dole na zabi daya. Kai tsaye shima ya amsa kin zabi bata min lokacin indai ba kishia ne dani ba, karramammun kalamaina karki wani kalli karancin su, yadda ya kamata su pito a kunnen ki ne, wallahi ban tsara su dan in burge ki ba, zo mu tapi don Allah. Bai jira cewarta ba ya bude mata kopa. Ta danyi jim sai ta kasa tankwabewa ta shiga moyar. Ya rupe sannan yazagaya ya shiga yana mika mata lemarta ya tashi motar,.har suka zo bakin gate kalma daya ta hada su, menene sunan ki? Kai tsaye ta amsa masa Rumaisau Aliyu Ahmad. Yace sunan ki mai dadi, ni sunana Auwal Ibrahin Hadi. Bata tanka ba shima baii kuma tankawa ba har suka zo bakin gate wata iska mai karpin gaske ta taso da alamun yanzu ruwa zai sauke, kirjin Rumaisau ya para dukan uku-uku cikin matsananciyar pargaba ta dubi maza da matan dake tsaitsaye cikin tashin hankali , ta tabbatar duk yadda hankalin su zai tashi bai pice pargabar zasuyi mura ba, ita kuwa in ruwan ya daketa zai wahala batayi ciwon da ya kusantarta da ita da kabari ba. Rage gudun da Auwal yayi yasa pargabar ta karuwa, saboda zaton sauketa zaiyi amma sai taga ya nupi titi zai haura, ta sauke ajiyar zucia muryarta na sarkewa ta dube shi tace da ka taimaka ka dauki matan can nasan baza a rasa wadabda zasuyi hanyar da zakayi ba, za ka sami lada idan ka taimake su. Ya dan ja pasali yana duban titi ba tare da ya dubeta ba yace. allah ya kawo mai taimakon su ni bana daukar mata a motata. Ta dan juma tana duban sa duba na rashin pahimta sannan tace ni ba ka gane nawa jinsin bane? Yayi murmushi ba tare da ya dubeta ba. Kakkarpar alakar da zuciya ta ta kulla dake ya koro wancan kudurin nawa daga naki jinsin, kin zama yar gida a zuciata da duk wani abu da na mallaka. Ta gaji da kallon sa ta kawar dakai . Ruwa ya para sauka da karpuli cikin sauri ta balle jakarta ta puto da rigar sanyi ta saka tana kumbiya-kumbiya. Bai tanka mata ba amma dai hankalinsa na kanta duk da idonsa na titi, tana bayyana alamun jin sanyi amma kawaicinta ya hana ta zuge gilashin bangarenta, kuma da hakan yasa yayi mata aikin da ta kasa yana cewa na lura kunama ce ke, kawaicinki kuma na son hanaki abinda kike so... Tayi yar daria ta amsa nida na zo ci rani har ga Allah bai kamata in zake ba. Ya watsar da wannan batun nata yace ina zan kai ki? Tayi dira-dira alamar canki-canki sai ta kasa zabar gurin zuwa tayi shiru kawai sanyi na kadata. Hankalinta yayi gida amma ta inda zata bi taje? Ina zata pake ta sami motar? Ya juyo yayi dan nazarinta cike da mamaki yace ina zaki je? Muryarta na rawa tace ai na kasa zaba ne, bana son sanyi, ruwa in ya dake ni illa yake min, da makaranta zanje amma na pasa saboda sanyi, yanxu inka sauke ni kapin na samu motar ma ruwan yayi min abinda yaga dama. Yaci gaba da kallon ta cikin nazari bai pahimci abin da yake son pahimta ba ya kada kai yace nima ba zan iya ajiyeki ruwan ya dake ki ba, ina da ganawa karpe uku sai dai ayi min uzurinta, inane unguwar ku. Muryarta taci gaba da rawa saboda laipin da takejin zata yiwa kanta da gidansu, a ganta saurayi ya sauketa kamar zubar da mutunci ne, amma kamar wannan zabin zaipi dukan ruwan. Na gode Allah Ya saka maka da alkhairi, a Gandun Albasa nake. Yace hanyarmu daya kenan ni a Na'ibawa nake, ziyara na kawowa wani malamina shekaru na biyu da barin makarantar nayi digirina na para aiki a karkashin gwammanti, ya kamata na ajiye iyali Allah bai kawo ba sai yai Allah Yayi min katarin daura damba, Rumaisau tayi dip kamar ruwa ya cinyeta tausayin kanta ne ya hanata nazarin amsar da zata bashi taji kaunarsa a ranta, sai dai taki yarda irin kaunar da take dorewa da aure ce, kauna ce kawai irin wadda dan Adam ke wa wanda yake zaton mutumin kirki ne ko kuma wanda yayi ma alkhairi? Tayi sararo tana kallonsa kawai yana jin kallon da take masa a jikin sa, amma ya hadiye ya juya ya kalle ta. Ta juya a hankali tabi tagar da kallo tare da sauke ajiyar zucia ba tace komai ba. Bakida abin cewa akan abin da na pada? Ta girgiza kai a nuste tace kar ka batawa kanka lokaci nasan ban cancanta zama iyali ba. Yayi saurin yi mata duban rashin pahimta amma ya takaita azarbabi wajen ce mata Ai ina tsammanin ba ayin komai babu hujja ko? Ki pada min dalili dan duba na gani. Ta muskuta tace dashi don Allah kayi hakuri. Yayi kasake yana kallonta sannan yace indai ba laipi zanwa Allah ba to bazan iya hakura ba... Ta tare shi da padin ina patan nan gaba ba zaka zarge ni da rupa-rupa ko yaudara ba? Ya ki daukar maganarta da muhimmanci ba tare da nuna damuwa ba yace ina saka rai alkhairi ya biyo baya, idan kuma akasinsa ya samu zan dogara ga Allah, amma ki sani idan akwai laipinki ciki Allah ne baZai barki ba. Musamman da yake a rupe kike ba ni uzurinki. Tayi shiri kawai shi kuma ya share maganar ya shiga tambayarta karatu, da wani abubuwa da yake jin suna da muhimmanci a cikin alakar da yake son kullawa da ita, cikin ikon Allah suna wuce Gadon kaya babu ruwan babu iska ko hadarin ma babu saboda haka taji ranta ya apu da son ta sauka ta hau motar haya ta karasa, amma ta kasa yi masa magana har sai da aka kira shi a waya ana nemansa wajen taro ya bayar da uzurin sa yana sauke wayar tace kawai ka sauke ni anan na shiga mota na karasa, sai ka wuce sabgoginka, da yake tun parko ke ika kirkiramin sabogogin ba, karki yi mamaki inna ki bin umarninki. Dole tayi daria ta share zancen , ya tsayar da motar a harabar gidan su yana dan zuba mata ido saboda yadda yaga kamar ta kadu da ganin wani da ya tsaya da motarsa kusan lokaci daya dasu. Da sauri ya kallo motar dan ganin tana rawar jikin picewa, ta juya ta dube shi da duban rashin pahimta ya nuna Yushau yana padin wanene wancan? Ta dubi Yushayu sanan ta dube shi atakaice tace Yayana ne. Yayi zuru yana kallon yushau haka kawai yaji hannkalinsa baikwanta da shi ba sam ya kada kai bisa dole ya bude kopar suka puta lokaci gidam da sauri ya nupi yushau dake kokarin rupe mota yayi masa sallama tare da mika masa hannu. A wulakance yushau ya amsa idon sa na kan rumaisau sannan yace Yaya kuke da wannan? Auwal yayi zuru yana kallon Yushau da rumaisau yadda yushau yayi magana puskarsa babu walwala ne yabawa Auwal damar nustuwa ya karance shi. Akwai alanar nutsuwa a rumaisau sai dai a rikice ta debo masa amsa dan Ajin mune.. Ya taimake ni ne saboda ruwan da ya tare ni..hanyarsa kenan shi yasa ban nemi sauka ba da muka wuce inda ake ruwan. A gadarance yushau yace kina pada min hanyarsa ce dan kun shirya kullun ya dinga dauko ki yana kawo ki ko? Ban san iyakar tsawon lokacin da zan dinga pada miki nan arewa ba kamar can kudu bane, babbar kazantace aga mace ta dauki namiji aboki.. Ganin yana neman tsinkata ta tare shi da cewa larura ce yaya yushau nayi gudun dukan ruwa ne . Yushau yayi tsaki tare da yin gaba yana cewa duk illar da dukan ruwa yake dashi ai bai kai na sayar da mutumci ba, koda yake wayewarku ta halatta muku haramci. Rumaisau tayi suguri ranta yayi mugun baci, ta san yushau bai iya magana ba sam, haka yake yinta kamar kashi, amma a yau ta para shakkar dan tazo cin arziki gidan sune, a sanyaye ta dubi Auwal da yayi shiru rungume da hannu yana kallon kasa tace na pa gode zan shiga ciki, ya dago da alamun tunani ya dubeta me yasa kika ki pada masa gaskiyar matsayin da na zaba mana? Sai kika alakanta mu da jabun dangantaka? Ta dan ja nunpashi sannan ta amsa har yanzu kai kake kidi da rawarka, da zaka bi ta tawa zamuyi sallama ne mu rabu har abada, karatu ya kawo ni garin nan yakamata naji dashi shi kadai. Mts! Ni bana son hargitse-hargitse wallahi. Ya pahimci cikin bacin rai take saboda haka sai da ya shirya kalaman da zai mata sannan yace kina da wanda kika tsayar? Ta girgiza kai , puskarta a dauke, ya numpasa yace idan haka ne na tabbatar kinzo kano ne dan mu hadu mu auri juna ba tare da nayi gibi a karatunki ba, ki daina gaggawar yanke hukunci akan lamarin rayuwa da hakan gara ki zama mai dabar tsara al'amuranki, ina neman alparmar kar ki koreni.kuma ban matsa miki ki so ni ba, amma ki bani dama mu pahimci ko zqmu iya tapia tare. Yanzu idonta cike yake da kwalla saboda takaicin kalaman yushau gidan su kawai take tunawo da yadda take da kima da mutunci a cikin sa. Auwal na ganin kallarta ya dan shiga damuwa amma a nutse ya tausasa murya yace mata idan akwai matsala dan Allah ki pada min kuka na nupin damuwa. A kalamaina banga abin da na pada da zai bata rai ba. Ta kirkiro murmushin karpin hali dole tace masa babu komai Allah Yayi mana jagora. Tun daga wannan ranar Auwal ya zame mata wani barin rayuwa ya kware da samar da mahallan parin ciki a zuciyarta da kirkinsa da kuma yadda yake kula da ita da damuwa a cikin abin daya dame ta. Kullun sai yazo gidan su tare da cewa yana bata mata da yawan lokutai a waya, haka kuma takanas yake binta makaranta ya daukota, babban zunubinsu da ya tsayewa yushau a rai kenan saboda imanin da yayi na cewa duk yarinyar da ta je jami'a sai ta lalace, ya rasa yadda zai pahimtar da hajia da Alh a matsayinsu na wadanda kamar su ke waliyantar da Rumaisau saboda kyan hali. Rumaisau ta para nisa cikin abind a bata zaba tsarabarsa a rayuwar ta ba wato SO, tana ji a ranta ita nakasasshiya ce duk yadda so zai zo mata in ta amince masa wata rana zai zame mata madaciya, amma a yanzu Auwal ya ture wannan tsarin a ranta sai ya barta da zullumin yadda rayuwa zata kasance musu a gaba. Zai rabu da ita ne idan ya san ita sikila ce ko kuwa zaiyi shahadar auren ta? Zabi na karshe ne patanta, sai dai zuciyarta na wuyatantar da yiyuwar sa. A yanzu sun pice watanni uku tare duk wani laulayi da alayin cututtukanta babu wanda auwal bai gani ba, yau kapa ciwo gobe cikim jibi zazzabi, gata mura... Kai shibai taba ganin mutun mai laulayi kamarta ba, amma wannan bai gutsuri komai cikin soyayyarta ba sai ma kari saboda tsabar tausayin da take bashi, kuma laulaye-laulayenta ne ya koya masa tarin hanyoyin da zai nuna mata kulawa, dan haka ya zama dan gida dan gaske a zuciyarta da zuciyar kowa ma a gidan in aka yi gepe daya da murdadden Yushau. Asai dai duk wannan shakuwar tasu ya rasa dalilin da yasa rumaisau taki amince masa manya su shigo maganar, ya bata lokaci ya kara mata amma har yanzu ta kasa gabatar masa da uzuri, sai dai hakan yaki ya dame shi dan yana da yakinin ya kai matsayin da yapi karpin yaudara a zuciyar rymaisau sai kawai ya zuba mata idon ganin gudun ruwa, musamman da yake karatun nata yazo karshe.. . Dan Aunty. July 31 at 8:26 PM · PublicGORAN DUMA 6 . Ya bata lokaci ya 'kara mata, amma har yanzu ta kasa gabatar masa da uziri, sai dai hakan ya 'ki ya dame shi dan yana da ya'kinin ya kai matsayin da ya fi 'karfin yaudara a zuciyar Rumasa'u, sai kawai ya zuba mata idon ganin gudun ruwa, musamman da yake karatun nata ya zo 'karshe. Wata rana sun fice goma na dare suna hira a zahiri daurewa kawai ta ke saboda cikinta da ke ta faman murd'awa. Ta daure din har suka yi sallama ta shiga gidan a birkice, zta wuce ciki Hajiya ta yi kiranta. "Zo nan Rumaisa'u, me yake faruwa na ga kina yamutse fuska?" Ta 'karaso ta zauna a gajiye. "Wallahi cikina ke min ciwo". Hajiya ta dubeta cikin tausayawa, ta ce. "Sannu, sai ki yi 'kokari

Chapter 3 of 21