Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ka yi abin da ransu ba zai ji dad'insa ba...q Ya tare ta kamar a 'kufule "Rumaisa'u sickle cell ne yakai girman da ba za a auri mai shi ba? Haba! Wannan maganar banza ki ke..." GORAN DUMA *****13 Ita ma ta tare shi a tausashe "Auwal babu yadda za a yi ni da kaina in 'kir'kiro abubuwan da zai nesanta mu da juna, amma duk abin da yake matsala ina guje mana shi kasancewara sickler na san da yawanmu irin matsalolin da suke fuskanta a rayuwa, ciki har da tsangamar da dangin miji ke masu matsaloli (sicklers) da za yi ta faman dawainiya da nauyi akan mijinsu ko kuma haihuwar dawainiya da su. Auwal wani lokacin ma mazajen ke tsangwamar matan akan sun zame musu nauyi... Kai wata ba sikilar ba ce idan suka taru ita da dangin mijin suka haifi sikila sai ya tattara laifin ya dora mata, wata mahaifiyar sikila da na sani ta ta6a bani labarin yadda mijinta ya fito kai tsaye yake 'kalubantarta akan cewa matansa hudu, amma ita kadai ta ishe da haihuwar sickler duk da cewa tare da mijin suka haifeta. Amma ka fahimta ba gudu nake a tsangwame ni ba ko ko kuma a 'kalubalance ni, na rantse maka babu wata wuya da ba zan iya jurewa ba, kawai dai bana sn ka yi abin da magabatanka za su yi kuka da kai. Idan aure zai shiga tsakaninmu ya kamata mu kori duk wani abu da muka san 'kalubale ne a rayuwarmu ta gaba dan a gaban ba mu da lokacinsa abin da ke gabanmu ma ya ishe mu". A sanyaye ya nisa, ya ce. "Na fahimce ki, in Allah Ya so zan yi abin da kika ce, amma dai dole mu hanzarta zuwa gwajin, ina son yin tanadin dukkanin wata juriya a kanki". Ta yi murmushin karfin hali cikin saduda ta ce. "To shikenan, Allah Ya za6a mana abin da fi alkhairi Auwal". Ya amsa cike da farin ciki. "Amin Rumaisa'u, Allah Ya sa mutuwa ce zata raba mu". Ta yi dariya ta ce. "Kuma ya zama ni zan rigaka mutuwa, na tabbatar rayuwa zata yi min 'kunci idan babu kai". Shima ya yi dariyar, ya ce. "To kin ga gara ni na riga ki mutuwar, saboda ni ba zan iya jure rayuwar da babu ke din ba". Da dad'i ya cikata kawai sai ta amsa masa da cewa. "Ina sonka Auwal!" Ya nisa cikin wani irin shauki ya ce. "Ni na san ina yi miki abin da ya fi So Rumaisa'u". Babu abin da ya motsa dan jua baya akan soyayyar da Auwal ke mata, sai ma wani 'karin tattali da tausayi da yake mata. Ya daura d'amarar sanin duk wani abu da ake gudunsa ga sickler, nisali ko a ina yake idan iska ta taso a wajen sai ya nemi Rumasa'u a waya, idan ta shiga motarsa sai ya zuge gilasai tsab, sannan duk wata sabga ta aljihu da zai mata ya juyar su kaf akan abubuwan da zai taimaki lafiyarta, dangin kayan sawa masu kauri da rufe jiki, dogayen riguna, hijabai, ni'kab har da safar 'kafa da hannu. Haka nan 6angaren abinci mawuyacin abu ne ya je mata ba tare da wani abinci da zai amfaneta ba, ko da mafi 'kan'katarsu ne wato rake. Tun daga nan hankalin Rumaisa da na iyayenta ya kwanta, suke ganin lallai ta sami mijin marainiya, Auwal ya zama dan gida a nan Kano, Rogo har ma da Abuja kowa a dangin Rumaisa'u. A nasa dangin ma Rumaisa'u, saboda haka na'am da girman gidan su Rumasa'u, saboda haka har sun amince da aurensu. Auwal ya kasa tarar mahaifansa ya sanar da su Rumasa'u sickler ce, saboda ta tsorata shi da yadda iyaye ke kar6ar lamarin dansu ya auri sickler, sai ya ke shakkar goyan baya daga nasa iyayen, musamman da yake shi kadai suka haifa, yadda suke zumudin aurensa ya fahimci yadda suka dora masa burin tara 'ya'ya saboda haka ya yi kirmisisi ya 'ki sanar da su, haka ma zuwa gwajin ya share shi saboda fargabar da ta cika ransa, alhalin ko me ma suka samo ba zai iya karya masa gwiwar auren Rumaisa'u ba. A haka manyansa suka je nemar masa auren Ruma aka yi duk yan hidimomi bisa al'adunsu aka sanya musu rana, in ta kammala karatu za'ayi. *BAYAN SHEKARU BIYU* Wata biyu ya rage aurensu, wanda za a had'a da na Hafsat da angonta Sani. Zancen duniya da ba ya 6uya, sai ga batun cewa, Rumaisa'u sikila ce a kunnen mahaifan Auwal. Kwatsam wani dare ya bar wajenta ya koma gida, ya shiga wajen Innarsa neman ruwan zafi, mahaifinsa ya yi kiransa fuska babu walwala a fuskarsa ko kad'an. Ya nemi guri ya zauna cikin sanyin jiki, mahaifin nasa ya ce. "Daga ina haka?" Sai ya ji tambayar ba wai, saboda babu irinta tsakaninsa da mahaifin nasa ko da can ma da ba shi da gurin zuwa ba a fiye tambayar ina ya je da dare ba ko dan yanayin aikinsa. Amma yau shi ne ake tuhumarsa inda ya je. Kawai sai ya yi 'kasa da kai, dan bai san abin fad'a ba, yana ji a cikin ransa nan da wata biyu Baban nasa ba zai ganshi a wannan lokacin ba ma bare ya tambate shi. Mahaifiyarsa ta shigo da fulas har da farantin kayan shayi ta dire a gabansa, zata fara hada masa ya yi sauri ya kar6e ta yana godiya. Ta nemi guri ta zauna, shi kuma jiki a sanyaye ya fara bude gwangwani yana sauraron mahaifinsa da ya dora. "Yaya me jikin?" Ya dago da sauri ya dubi mahaifinsa hankalinsa a tashe, amma fuskarsa ta kasa nunawa. Ya tattare 'kululun da ya taso masa a ma'kogwaro ya kora shi ta hanyar hamud'ar madarar ya hadiye sannan ya ce wa mahaifin nasa. "Abbba ina ka san ba ta da lafiya?" "Zancen duniya ai ba ya 6uya". Abban ya fada cikin rashin kulawa tun daga nan Auwal ya sha jinin jikinsa, kawai sai ya ci gaba da hidimar gabansa. Abban ya gyara zama ya ce. "Wato Auwal ka san yarinyar nan sikila ce ba ka sanar da mu ba, dan kawai ka na son abin da zaka sanya mu 'karanta?" Auwal ya dago cikin bugun zuciya ya dubi mahaifinsa bakinsa na rawa ya ce. "Abba... Mene ne 'karantar a auren sickler?" Cikin 6acin rai Abba ya ce. "Auren sickler ba 'karanta ba ne, kantafi ne kawai da rayuwar 'ya'ya da ta aljihu... In da 'karantar ta fito shi ne zuwan da zamu yi mu ce mun janye..." Tuni har hawaye ya fara zuba a idon Auwal, wanda ke kallon mahaifinsa garau da alamun rashin kwanciyar hankali bare kimtsa maganar da zuciyarsa ya kamata ta haifa, bakinsa kuma ya furta hakan ne kuma ya sa Innarsa ta sami sararin shiga maganar. "Wannan d'an ka yi wauta in dai ka san cewa yarinyar nan sickler ce, amma ka juya wa matsalolinta baya zaka aure ta... Muna zaune 'kalau ka kawo mana sickler dangi..." A yanzu ya sami ga6ar abin cewa wanda ra'ayin kansa da na zuciyarsa suka yi tarayya yana 'kokarin tsayar da hawayen ya tare mahaifiyarsa. 'Idan dai zan iya haihuwar da Rumasa'u, to lallai zan iya haihuwar sickler da wata mai lafiya wadda ba sickler ba ce..." Shi ma mahaifinsa da yake zazzafan mutum ne sai ya tare shi. "Idan Allah Ya hukunto hakan na tabbatar idan za ka haifi sickler goma da Rumaisa'u idan wata ce sai Allah Ya ta'kaita ka haifi hud'u..." Auwal kawai sai ya yi shiru ya ci gaba da shan shayin da ya fi kama da shan magani, 'kwalwarsa ta tsaya cak! Da 'kirkirar mafita ko ta 'kofofin da duk ransa ya raya masa har ya gama kushe masa aure da Rumasa'u tsab ya 'karkashe batunda da haramta aurem. Auwal dai bai tanka ba, har mahaifin nasa ya diga aya sannan cikin rashin hayyaci ya tashi ya fice daga falon. GORAN DUMA BY M.I.S.B *****14 Tsawon daren nan ba zai iya dorar da wani abin kirki da ya yi ko lissafinsa ya yi ba dangane da yadda zai 6ullowa al'amarin, ya san dai ya gurji kukan da tsananin 'kauna da tausayin Rumasa'u ya haifa, kuma su suka hana shi hasala komai bayan ya 'koshi da ji a ransa duk tsanani ba zai iya rabuwa da Rumaisa'u ba. Sai 'karshen dare ya sami runtsawa saboda haka bai sami sallatar asubahi ba, 'karfe shidda dai-dai wayar Rumasa'u ta farkar da shi. Yana ganin sunanta kan wayar sai da 'kwalla ta taru a idonsa, ya daga yana kokarin gyara muryarsa saboda daskarewar bacci da kuma ta ma'ka'kin tausayinta da ya ma'kale maasa a ma'kogwaro. "Rumaisa'u" Muryarta tar ta ce "Duk wadannan gaibu ne Abba, babu wanda ya san abin da gaba zata haifa, kamar yadda ba mu isa za6ar abin da muke so mu 'kyale wanda tanmu yake hasashen hadari cikinsa ba. Da dan Adam na da iko akan za6in abin da yake so na matar da ta zarce Rumaisa saboda abin da nake mata ya fi so, shi yasa ban san ko wacce irin matsala ba a kanta, amma da yake na san ba dukkan abin da mutum ke so yake samu ba, tun bayan umarninka na jiya na kwana ina gwajin yadda zan iya rayuwar da babu Rumaisa'u. Na yi ta cin karo da gazawa, har ta fara barazanar keta min zuciya. Ban fitar da rai zan iya din ko kuma zan kasa ba, na san a biyu daya ce zata faru, ko in iya d'in in wanzu bisa tsarin da ka za6a min, ko kuma in gaza ta dalilin in bijire maka ba, wanda babu irin haka a tarbiyyar da ka ba ni... Abba kar ka damu da yadda ka ganni har in mutu in Allah Ya so ba zaka had'u da abin kuka ta silata ba..." Yanzu hawaye ya fara cin 'karfinsa, kuma shi ne ya tilasta shi diga aya ba don ya rasa abin cewa ba. Duk jikin mahaifinsa ya yi sanyi, sai kallon Auwal yake shi ma kamar ya yi hawayen, amma wata zuciyar na tuna masa siyasar Auwal ta dadin baki da sadaukarwa har ka yi masa abu ba tare da kana da niyyarsa ba, wannnan ne yasa ya daure ya ce. "Abin har ya yi zafi haka Auwal? Ba zaka iya fitar da yarinyar nan a ranka cikin ruwan sanyi da dalilin matsalarta a rayuwarka da ta 'ya'yanka ba?" Auwal ya muskuta da murmushin ya'ke alamar akwai magana fal a cikinsa, sai dai yadda zai furta ya yi girma, don haka ya hadiye ta kawai ya bi mahaifinsa da shiru, har mahaifin nasa ya gaji da jiran cewarsa ya nemi guri ya zauna idonsa akan Auwal. "Tun farko ka san Rumasa'u sickler ce?" Auwal ya kad'a kai, mahaifin nasa ya dora wata tambayar. "Wanne mataki ka dauka akan yadda za ku rayu tare, ko kaucewa yadda za ku haifi 'ya'yan sicklers?" Auwal ya jima kafin ya tattaro abin cewa. "Ta yi 'kokarin hana ni aurenta tun ranar da muka had'u na dage. Duk matsalolin da ka lissafo min da bakinta ta lissafo min su, amma ba su gigita ni yadda suke gigita ku ba... Da ta ga haka sai ta shawarce ni yin gwaji dan sanin makomar 'ya'yanmu, na amince a sannan amma sai na ga gwajin 6atawa kai lokaci ne da tanadar wa kai fargaba, don na ji a raina ko wane irin sakamako gwajin zai haifar ba zan iya barinta ba, saboda haka na ce ta bar maganar gwaji". Mahaifinsa ya jima cikin shiru yana jiya maganganunsa, kafin ya yanke hukuncin d ayake jin shi ne na 'karshe. "Gaskiya ta yi hange mai kyau saboda haka shawararta ita ce abin bi. Ka je ka yi gwaji idan akwai matserar 'ya'yanku sai ku yi aure, idan kuma babu, to ku dubi girman Allah ku ceci 'ya'yanku ta hanyar ha'kura da juna". Duk da Auwal ya ji maganar mahaifinsa da kamar maimaici kawai, ma'ana babu wani sassauci haka ya cije a ladabce ya gyad'a kai. "To na gode Abba". Ya m'ke kuma salin-alin ya fice ya shiga 'kwan'kwasa falon Innarsa. Auwal bai 6oyewa Rumaisa'u komai ba dangane da yadda suka yi da mahaifinsa da hujjarsa ta sanin kukanta nasa ne, kukansa ma nata ne. Tuni suka yiwa juna wannan al'kawarin na tarayya akan matsalolinsu dan nemo hanyar araka. Rumasa'u ta jima ba ta yi magana ba, ba dan rashin abin cewa ba sai dan saisaita maganar don gudun kada tayi muni a kunnen Auwal ko kuma ya zama wani mataki na karyar masa da gwiwa. "Kin 'ki cewa komai Rumasa?" Ya fada bayan ya gaji da jiran cewar tata. Ta gyara tsaiwarta ta 'kara jingina sosai da motarsa saboda tana jin jiri. Ta yi murmushin 'karfin hali ta ce. "Abin da Abba ya yi shi ne ya kamata Auwal, so ne tun farko ya ke runtse mana ido alhalin wani dad'in gushi ne kawai a cikin rayuwar aure, wanda ake 'kulla si domin kammaluwar iyali. Ya wajaba ne mu samarwa iyalanmu makoma ta gari, ba ya kamata ba Auwal". Shi ma ya yi murmushin 'karfin hali bayan ya ji a ransa kawai 'karfafa masa gwiwa ta ke so ta yi ba ainihin abin da ke cikin ranta ke nan ba, ya ce. "Kamar ke da Abba kuna mantawa ba a yiwa Allah wayo, ke kanki aya ce Rumasa'u, Innarki da Abbanki babu sickler ciki, amma suka haife ki..." Ta tare shi da dariya. "Ba 'kokarin yin wayo ba ne, 'ko'karin amfani da hankali ne, wanda Ubangiji Ya hore mu da shi dan za6ar abin da zai amfane mu da gujewa abin da zai cutar da mu, abin da ya faru da mu cikin akasi mun yarda daga Ubangijinmu ne ba tare da sakacinmu ba, sai mu yi fatan zamowarsa kaffa". Auwal ya yi zuru kawai yana kallonta sannan ya nisa ya ce. "Ban sna me yasa duk cikin lissafinku ba kwa duba uban yaran da samun su yake 'kila wa 'kala ba, sa ku kuka himmata sarayar da shi alhalin shi ne a hannunku. To zan fada miki abin d ana fada Abba jiya na kwana da 'kokarin lissafa yadda zan yi rayuwar da babu ke, na ji kamar numfashina zai yanke daga lissafin kawai ba tare da fitar da sakamako ba, amma dai ban cire rai daga rahamar Ubangiji ba, duk za6in da ya yi min ina fatan rahma da jin 'kanSa a ciki". Ta zuba masa ido, dauriyarta na kokarin 'karewa. Kasa gajiya da kalonsa da ta yi ne ya sa ita ma ta tabbatarwa kanta wa'ka kawai ta ke, amma tursasa kanta za6ar tsaka-tsakin al'amura, sai dai kuma ta kasa hana zuciyarta rauni da son nuna gazawa da ta tsaya kawai ga bayyanawa ta hanyar 'kura masa ido cikin hawaye. Haka suka tsaya ita kuka, shi hawaye, har daga 'karshe ya zagaya mota ya shige yana cewa. "Zo mu je asibitin". Ta yi saurin duba agogon hannnunta da ya nuna 'karfe sha daya da mintoci sha hud'u. Ta bude motar ta sunkuya a tausashe ta ce masa. "Bari na sanar da Hajiya". Ya yi saurin tare da fadin. "Rumaisa'u kar ki sanar da kowa matsalarmu fa, umarni ne da kuma kokarin kwantar da hankalinku ke da Abba zai kai ni gwaji, ba dan na yarda da iya raba ni da ke ko ya yi wani abu a cikin sonki ba. Ya kamata ki ri'ke wannan kada ki yi 'kokarin raba ni da kanki, son da nake miki mutuwa ce kawai zata iya raba ni da shi". Ta sororo cikin sanyin jiki tana kallonsa. Ta hadiye kwallarta ta ce masa. "Auwal wai me yasa ka damu da kira mana mutwa? Ai ba sai ka kirata zaka bayyana min kana sona ba,.." Ya tareta cikin kyalkuala dariya. "Me yasa ba kya so na kirata? In akiranta ne dan na sna ita ce mai YANKE 'KAUNA, duk yun'kurin raba mu da kuke ni dai na tabbatar ita kadai ce zata iya raba ni da son da nake miki. Amma na san ba ni da karfi ko dabara a cikin aurenki yadda Ubangiji Ya so haka zai yi". Ta murza yatsu tana dariya, ita ma ce. "Shikenan. In Allah Ya so ni da kai mutu ka raba". Ba ta jira cewarsa ba ta wuce. Ya bi ta da kira, ta tsaya ba tare da ta juyo ba, ya dan daga murya. "Na fa gaya miki kar ki fad'a". Sai kawai ta kad'a kai ta wuce tana dariya.GORAN DUMA 15 . . Dr. Hadiza ta gyara zama ta janyo wani fayil cikin murmushi ba tare da dubansa ba ta ce. "Soyayyar da kake mata da amincewarka na aurenta a matsayinta na mai sikila shine matakin farko na magance matsaloli ko yi musu kallon 'kanana a cikin aurenku, idan duk kun yarda da wannan to kamata ce ku zo min tare, duk abin da zan fad'a tare zai amfane ku, idan ma 'karfafa gwiwa ne tare zai 'karfafa muku". Auwalu ya jima bai tanka ba, sannan ya ja numfashi cikin kasa hankula barkatai ya amsa. "Haka Allah ya tsara na riga na taho ni kadai d'in, amma na daura damarar zantar da ita komai kamar yadda kika zantar da ni, hikimia ko ta aro ce zan aro in yi 'kokarin fahimtar da ita". Ofis din ya dauki shiru sai 'karar takardun da likitan ke bud'awa da kuma bugun zuciyarsa da ya cika masa kunne da rud'u. Likita ta dago kai ta dube shi da wata takarda a hannunta tana juyawa. "Sakamakon gwajinka ya nuna cewa, kai AS ne, ma'ana zaku iya haihuwar mai AS za kuma ku iya haihuwar mai SS, wato ranar da ka bayar da A ta bayar da S dinta za ku samar da d'a irinka (AS). ranar kuma da ka bayar da S din ka dama ita abin da zata bayar ke nan, to za ku samar da d'a SS (sickler) irinta. Abin da zan 'karfafa muku gwiwa da shi a nan shi ne, ku shiga cikin hankalinku ku kyautata zaton alkhairi ga rayuwar 'ya'yan da zaku samu a gaba, wanda Ubangiji ne kadai Ya san yadda za su kasance. Idan Allah Ya ga dama sai ya azurta ku da 'ya'ya goma babu sickler ko daya a ciki, ikonSa ne Ya umarce ka ka yi ta bayar da A dinka har ku gama haihuwarku, idan kuma Ya si zai iya jarabtarku da haihuwar sickler, Allah babu yadda bai iya ba. Kai kanka zaka iya haifar sickler ba tare da ka auri Rumaisa'u sickler ba. Idan wadda ka aura din AS ce kamai ai za ku iya tarayya wajen bayar da S zalla ku samar da sickler. Abin da ya ke a rubuce dai babu wanda ya isa kankare shi, dukkanmu ba dan ba damarmu muke, Ubangijin da Ya yi ka AS shi ya yi A. Ba don ya fi sonsa da kai ba. Kuma shi ya yi S.S ba dan Ya yi masa laifi ba, sai dan haka Ya so, haka Ya ga dama. Dan haka babu wani dalili da zamu dogara da shi wajen hana aurenku ina fatan ka fahimce ni? A 'karshe ina shawartarka da kwantar da hankali da mayar da lamari ga Allah, na tabbatar zai saka maka da dubun alkhairi idan ka dogara da shi ka auri wannan baiwar Allah ba tare da ka guje ta ka gadar mata da takaici a zuci ba, kai kuma ka saka 'karfi da dabara a cikin taka rayuwar ba, yadda kake nuna wa ina fahimceka da cewa ka dauki ciwonta naka, wannan ko wanne sickler ke bu'kata. A yarda da rauninsa, a tausa masa idan ciwonsa ya taso, a yi masa uziri a taimake shi ta wadannan hanyoyin kula da maganinsa, kaucewa abin da zai motsa ciwonsa, hana shi aikin wahala tare da 'karfafa masa gwiwar cutar da yake bautar Ubangiji ce. Idan ya yi tawakkali ladansa ba zai lissafu ba. A yarda in an haifi d'a sickler da shi ba shi kadai ya haifa ba, da sauransu. Duk wadannan dabi'un taimakon na zace su a kai malam Auwalu dan Allah ka yi 'ko'kari kar ka ba ni kunya". Tunda ta ke magana hankalinsa ya kasu uku, daya a kanta, daya akan batun mahaifinsa (ka je ka yi gwajin idan akwai matserar 'ya'yanku sai ku yi aure, idan babu to ku dubi girman Allah ku ceci 'ya'yanku ta hanyar ha'kura da juna), daya kuma wanda ya ke da kawo mafi tsoka akan 'kauna da tausayin Rumaisa'u, wanda a yanzu shi ya sa shi fitar da 'kwalla bayan Dr. Hadiza ta dire, zuciyarsa ta dame shi da son ya fad'a mata 'dama can ba ni ne matsala ba, mahaifina ne'. Sai kuma ya ga fada matan wani rage karsashi ne a dogon lokacinta da ta 6ata tana ba shi shawarar rayuwa da Rumasa'u, wanda ko ba a shawarce shi ba, abin da burika da ra'ayoyinsa ke zartarwa ke nan. Ya hadiye duk wata damuwarsa ya yi mata godiya sosai, tare da nuna 'karfin imanin babu abin da zai raba shi da Rumasa'u, suka yi sallama dukkansu suna yiwa juna godiya. Bayan ya fito asibitin ya yi mazantakar wucewa ofis dan gwada 'karfin hali da na zuciyarsa da koyawa kai jarumta cikin lamarin d ake fin 'karfin iyawa, mahaifinsa ne abin jinsa, wanda alamu ke nuna yana son saka 'karfinsa wajen taruwar iyalai da babu tahalikin yadda za su samu. Rayuwarsu zata kai ga haihuwar ko zata gaza, za su haifa din ko ba'kararru ne su? Duk wadannan gaibu ne babu wanda ya san shi sai Allah, idan ya sa wa kansa damuwar rana guda a kansu ya had'a wautar da zata kamanta shi da rashin hankali. Suna zaune a falon da suke hira, idan sun so jimawa suna hirar ke nan, idan ba za su jima ba dama a motarsa suke jingina su yi tad'insu. Rumaisa'u ri'ke da takardar sakamon gwajinsu tana juyawa, idan akwai abin da ya fi 'kunci da d'aci to ranta shi ya yi. Abin da ke shirin faruwa da ita zuciyarta ta 'ki yarda zata iya daukarsa duk yadda ta yi 'ko'karin gwadawar. Auwal ma ko da gwaji ya kasa ce mata wani abu. Tunda ya ba ta takardar har sai da ta gaji ta tsinka, cikin yi masa kallon kai tsaye. "Auwal ban ta6a jin kaico da nadamar kasancewa ta sickler ba sai a yau. Na tsani kaina da duk wata tawaya da ta ke son raba ni da kai Auwalu..." Ya tare ta cikin dakewar 'karfin hali. "Kar ki yi sa6o Rumasa'u, wannan wacce irin wauta ce? Ki shiga cikin hankalinki, duk yadda za ki so ni bayan Ubangijin da ya halicce ki ya wajabta in bi. Tsanar kanki da tsanar kasancewarki yadda Ubangiji Ya tsaro ki tawaye ne da butulci gare Shi..." Ta dam'ke bakin da ya yi mata amfani biyu, hana sautin kukanta fitowa da nuna nadamar abin da bakin ya fad'a, cikin raunanniyar muryar kuka ta ce. "Astagfirullah, Allahumma gafirni war hamni..." Ta zare da shesshekar kukanta. Shi ma duk yadda ya so ya daure sai dauriyar ta fi 'karfinsa ya fara hawaye, ba dan yana zatar musu rabuwa ba, sai dan shaukin yadda suke son juna da tausayin Rumasa'u wadda ake son raba su ta dalilin aibun da ba ita ta 'kaga wa kanta ba. Mace mai sanyin halin da ta kasa fitowa kai tsaye ta ga laifin mahaifinsa da ke son raba su, 'karfinta da yaji ta ke juyawa aibata mahaifinsa baya. Sun jima suna 'yan koke-kokensu kafin ita da ta fi shi sharafin damuwa ta kuma soko wata kato6arar. "Da za a ba ni za6in rayuwar da babu kai ko mutuwa, Auwal da gudu zan za6i mutuwar, har yau ni ban san ta inda zan fara rayuwar ba, shi yasa ka ji na kasa 'karfafarka bin umarnin Abba don Allah ka yi min wannan uzirin... Ina sonka ban san babu a kanka ba Auwal, wannan ciwon ya fi sickle cell ciwo a raina..." Ya tare ta cikin kasa tattara kalaman da za su fidda ma'ana sosai, saboda rud'ani. "Ba zamu rabu ba Rumasa'u ki daina ambato mana rabuwar... Ni duk maganar nan ma ta gundure ni wallahi". Ta dago ta bi shi da kallo cikin hawaye. "Haka ne burina Auwal, amma ba zan yaudari kaina na dorar da shi da fatar baki ko ture abin da ya kamata na duba ba". Suka kuma daukar shiru sannan ta goge hawayeta 2a fuskance shi "Ka sanarwa Abba?" Ya yi saurin girgiza kai yana kallonta sararo. Ta 'kokarta ta ce. "Sai ka yi gaggawar sanar da shi, ya yanke mana hukuncin da Ubangiji Ya za6a mana, fara shirin zama tare ko kuma shiga makarantar koyon juriya da rashin juna, ko wanne Ubangiji Ya za6a mana muna fatan ya zama alkhairi a gare mu".Ba ta jira cewarsa ba ta mi'ke zata bar falon.... . Dan Aunty August 4 at 9:12 PM · PublicGORAN DUMA 16 . . Ya yi saurin dakatar da ita da cewa" Duk kurin da na gama yi na cewa babu abin da zai sauya a cikin soyayyarmu da auren kin fayalar da shi kenan, dama kin tura ni gwaji ne dan ki rabu da ni Rumasa'u?" Ta yi saurin dawowa gabansa ta dur'kushe tana girgiza kai cikin hawaye. Ta kasa magana sai kallonsa da hawayen, shi ma ya motsa baki, ya yi maganar amma ya kasa, har sai da ta gama nata alayin ta riga shi samo abin cewa. "Ina sonka Auwal... aurenka shi ne babban burin da da ace ina da iko zan kusantar da shi tunda ba ni da ikon na yi imani aurenko rashinsa da ni kaina da kai duk muna shawagi ne cikin hukuncin Ubangiji, zai iya kusantar da shi dan rahamarsa a gare mu da ni'imarsa. Zai iya tankwa6ar da shi dan isarSa a kanmu da zartar da abin da mu ba mu san da shi ba, dan haka duk abin da ka ji na fad'a kar ka yiwa ubangiji biyayya da faranta ran Abba, a wani hannun kuma da 'kin biyewa zuciya sakokinta... Ina sonka Auwal".... Ya kai 'kololuwan rauni da tausayin Rumaisa'u wanda ya 'kara masa miliyoyin kaunarta, ma'kogwaron ya cunkushe da shu, shi yasa duk yadda ya yi 'kokarin ya ce wani abu ya kasa, kawai sai ya dauki takarda ya nemi hanyar fita. "Ba zamu rabu ba Rumaisa'u ki daina ambato mana rabuwar... Ni duk maganar nan ma ta gunudure ni wallahi". Ta dago ta bi shi da kallo cikin hawaye. "Haka ne burina Auwal, amma ba zan yaudari kaina na d'orar da shi da fatar baki ko ture abin da ya kamata na duba ba". Suka kuma daukar shiru sannan ta goge hawayenta ta fuskance shi. "Ka sanarwa Abba?" Ka yi saurin gaggawar sanar da shi, ya yanke mana hukuncin da Ubangiji Ya za6a mana, fara shirin zama tare ko kuma shiga makarantar koyon rashin juriya da rashin juna, ko wanne Ubangiji Ya za6a mana muna fatan ya zama alkhairi a gare mu". Ba ta jira cewarsa ba ta mi'ke zata bar falon. Ya yi saurin dakatar a ita da cewa. "Duk kurin dakatar da na gama yi na cewa babu abin da zai sauya a cikin soyayyarmu da auren kin fatalar da shikenan, dama kin tura ni gwaji ne dan ki rabu da ni Rumaisa'u?" Ta yi saurin dawowa gabansa ta dur'kushe tana girgiza kai cikin hawaye. Ta kasa magana sai kallonsa da hawayen, shi ma ya motsa baki, ya yi maganar amma ya kasa, har sai da ta gama nata alayin ta riga shi samo abin cewa. "Ina sonka Auwal... aurenka shi ne babban burin da da ace ina da iko zan kusantar da shi tunda ba ni d aiko na yi imarin aurenko rashinsa da ni kaina da kai duk muna shawagi ne cikin hukuncin Ubangiji,

Chapter 6 of 21