Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Wata Murya Mara Dadi, To A Dawo Lfya Inkin Rike Adadin Rasitan Asibitin Nanda Waccen Yarinyar Ta Ci nawane? Alhji Ya Ce Na Kawo Masa Kudinsa Gobe,yafadi Hakan Ne Waiko Hajiya Zataga Rashin Kyautatwar Alhji,ko Ma Ta Taushi Zuciyar Sa Ya Janye Amma Sai Ga Shi Hajiyata Fadi Abindayanuna Tamafi Alhji Kulla Gabadashi To Idan Aron Kudin Zaizame Masa Da Rashin Burgewa Aisai Yadinga Nemoka Duk Lokacinda Bukatar Irin Hakantataso Kazo Asibitin Ka Biya Kaitsaye Basai Ka Sanya Wani Akin Yahada Maka Lissafiba,ko Kuma Kaji Haushin Wana Ya Ranta Maka, Allah Yabaki Hakuri Niba Hakane Nufina Ba Batatankashi Ba Ta Wuce Dole Ya Biyo Bayansu Suka Kebe Da Mubarak Ya Kirga Dubu Ashirin Ya Damkawa Mubarak Ransa A Bace Man Allah Idan Waccen Malalaciyar Yarinyar Tatashi Daga Bacci Ka Bata Ka Ce Na Rainon Cikine Yawuce Mubaraka Ruma Kwance A Gadon Asibiti Yammacin Kwananta Biyu A Asibitin Idanta Biyu Kuma Cikin Hayyacinta Fes Amma Ta Runtse Idonta Alamun Tana Bacci Tunanuwa Barkatah Na Ruda Kwakwalwarta Alhji Da Hajiya Da Mominta Kadai Ke Ciki Suna Sirri Acewar Su Itakadai Ce Ba Aso Taji Mominta Cikin Damuwa Ta Ce Alhji Acikin fargaba Nake Dan Allah Karka Boyemin Komai Melikitan Ruma Yakebe Dakai Yafada Maka Ya Ce Abinda Kika Riga Kikasanine Fa!Na Cutar Da Ruma Dana Gadata Da Wanda Baisan Darajarta Ba Duk Wannan Yawuce Alhji Ba Bu Wanda Yaisa Kankare Abinda Allah Ya Riga Ya Rubuta Yanzu me Likita Ya Ce Yaimin Tambayoyi Sosai Game da Asibitin Da Ruma Kezuwa Awo Na Sanardashi Amma Saiyanuna Mamaki Kwarai Da Yadda Batasami Isashiyar Kulawa Ba Momi Ta Girgiza Kai Cikin Takaici Sam Ba Laifin Asibitin Bane Dazu Ma Safe Nai Hira Da Ita Shigen Wannan Amma Yadda Na Fahimta Shine Tana Fashin Zuwa Asibitin A Kaidar Da Likita Yaimata Sannan Ba Bu Isashen Kudin Da Ake cajinta Irin Yadda Ake Cajin Sikila,hakane Alhji Ya Ce Tare Da Takahcin Yusha'u.... . To sai kuma gobe idan Allah ya kai mu. Na dan kara rubutun. Masu commnts da like godia marar adadi, wanda basayi ya kamata ku para koda like ne kapin ku pita a gidan. Dan Aunty. GORAN DUMA (P 41) . . Likita Yasanar Dani Ce Malyria Taiyawa Ajikinta Wanda Yake Ganin Harda Sakacin Liikitanta Na Baya Da Bai Zurfafa Bincike Ya Gano Cewa Yara Biyune A Cikin nata Ba,yan Biyu? Hajiya Da Momi Suka Fada Cikin Firgici Nandanan Hawaye Yafara Zarya A Idon Momi Ta Dora Hannu Biyu Aka Tana Kallon Ruma Dake Bacci A Gado Cikin Raunanniyar Murya Ta Ce Allah Kaika Halicci Ruma Kafimu Sonta Allah Ka Tsallakar Da Ita Ka Saukaka Alamuranta Kaimata Albarka Duniya Da Lahira Daga Hajiya Har Alhji Cikin Raunaniyar Murya Suka Amsamata Alhji Ya Ce Karkidamu Aita Dawo Hannunmu,muba Zamu Yi Sakacinda Yushau Yai A Baya Ba Zansami Ma Likitan Naimasa Bayanin Komai Cewa Sakacin Daga Garemu Ne Badaga Likitanta Na Baya Ba, Haka Har Sukai Shuru Da Maganar Da Suke Zaton Sirrine Amma Komai A Kunnen Ruma Sukayi Dan Haka Dasuka Yi Shuru Saitata Zuciyar Ta Hau Nata Aiki Na Fargaba.Tausayi,da Nadama zuciyarta Takai Kololuwar Ciwo Da Jin Inama Daga Wannan Kwanciyar Adau Gawarta Su Huta Da Radadin Rayuwar Wannan Kuntatar Duniyar,basu Ankara Ba Haka Da Safe Likita Yazo Duba Ta Hajiya Da Mominta Da Hafsat Ne A Dakin Suka Mike Suka Fita Itakuma Mominta Talike Ganin Likita Bai Koro Momi Ba Yasanya Ta Dubi Momi Cikin Sanyin Murya Ta Ce Momi Zan Iya Magana Da Likita Momi Ta Ce Menene Ke da Na Cancanci A Boyemin Shi Ruma Murmushi Tai Kawai Likita Yanuna Mata Hanya Tare Da Cewa Dama Yanzu Nake Shhrin Korarki Ta Ce Likita Ya'ya Biyu Ne Acikina Ko? Cikin Muryar Kwantar Da Hankali Ya Ce Hakane Ta Ce To Inajin ba Damuwa Ke Asassa Hawan Jiniba,da Ita Ce Sila Lallai Daga Jiya Zuwa Yau Da An Sami Labarin Cewa Yan Biyu Zan Haifa Yakamata Atarar Da Jinina Yai Bindiga Don Me? Don Ba Kya Murna Da Rahamar Da Allah Yaimiki Ta Kyautar Ya'ya Biyun? Ta Ce A A In Zanyi Murnar Na Haifi Ya'ya Biyu Ya Kamata Na Hada Ta Da Fargabar Kai Na Haifi Wahalallu A Rayuwa Irina Wannan Kuma Yin Allah Ne Ruma Likita Inaso Aimin Prenatal Diagnosis Gynotype Don Insan Makomar 'ya'yan Gwajine Da Ake Zukar Ruwan Da Jariri Ke Kwance A Ciki Yayinda Ciki Yakai Sati Goma A Gwada Ana Samun Sakamako Dan Gano Gynotype A Razane Likita Ya Dubeta Meyasa Ruma? Nafadi Dalili Inasan Insan Makomar 'ya'yana Matsayinki Na Musulma Baikamata Kinemo Wannan Mafitar Ba Inkinga Su Waye 'ya'yanki Mezakiyi? Kizubar Dasu? Ai Ina Tsammanin Kinsan Ko Haka Ne Lokaci Yakuremiki Tunda Bazaki Zubar Da Dan Da Ko Yanzu Kika Haifeshi Zai Izaci Gaba Da Rayuwa Ba, Ba Abinda Nake Nufi Ba Kenan Inason In Sami Murna Da Natsuwa Idan Abinda Zan Haifa Ba Sikila Bane Inason Yin Kuka Da Nadama Idan Bincike Ya Gano Sikila Zan Haifo Inyi Tir Da Kaina Danake Ganin Abin Danai Na Kirkine Bisa Auren Mahaifinsu Wanda Yaki Yarda Ayi Gwajin Gynotype Dan Sanin Matsayinsa Da Sanin In Munyi Aure Me Zamu Iya Haifa Indai Ba Kashesu Zaki Ba Kuma Ba Sauya Su Za Ai Daga Sikila Su Koma Masu Lfya Ba Ko Kamar Gara Ma A Bar Su Suzo Duniyar Ki Gani Ruma Musamman Dakike Maganar Kuka Da Nadama Idan Har A Ka Tarar Da Cewa Sikilane Lallai Kuwa Inhar Aka Barni Ba A Gano Ba Zuciyata Zata Iya Bugawa Kafin Na Hai Hu Duk Abinda Sakamako Zai Nuna Shinakeso Likita Inasan Yin Kukan Murnar 'ya'yana Sun Kubuta Kuma In Sun Girma Bazan Ji Ciwon Zaluncindanai Musu Na Kawo Su Duniya Yadda Suka Sami Kaiba Haka Ma In Kukan Ne Inasonyi Tare Da Godiya Ga Allah Wanda Yake Jarrabani Nida Ahalina Sanin Sikila Zan Haifa Bazai Tawayi Lfyata Ba,amma Zaisamin Karfin Gwiwar Data Wakalli To Shiken Karkidamu Za Ayi Ma Yardar Allah Haka Ruma Ta Ci Gaba Da Kwanciya A Asibiti Kudi Kam Ana Cinsu Komai Aka Nema Da Gudu Alhji Kan Bayar Haka Ko Zuwa Yayi Ya Tarar Da Wani Ya Bayar Saiya Mayar Masa Da Abinsa Ammafa Akwai Dirowa Ta Musammasan Daya Ware Yana Adana Wa Yushau Wanda Hidimar Aure Ta Dauke Wa Hankali Abin Haushi Ko Sau Daya Baije Asibiti Da Suna Duba Ruma Ba Yasan Tana Asibiti Bai Sani Ba Oho! Su Dai Sundage Suna Ta Kakkare Mata Musamman Maganar Aurensa Dasuke Sayawa Wai Ba Sontaji Itakuma Tanai Musu Kallon Rashin Sanin Dawan Gari Tare Da Mayar Da Allura Garma Shin Ita Data Mallaki Irin Auwal Tarasa Bata Mutuba,dan Irin Yushau A Doron Duniya Ya Saketa Ya Auri Wata Saitai Ciwon Kai,? Andaura Auren Yushau Da Kwana Daya Sannan Aka Bama Atika Alhakin Sanarma Ruma Tagayamata Kuma Taimusu Fatan Alkhairi Inda Sukuma Su Atikan Sukaji Haushin Abinda Ruma Ta Ce Akan Hakan Mominta Ta Sanarmata Da Sakamakon Likita Akan Gynotype Din Akwai Yuyuwar Duk Yaran Sikilane Saidah Kinsan Babu Yadda Allah Bai Iya Ba,sai Ki Ga Ya Sanyo Su Lafiyayu Ba Kamar Yadda Bincike Yanuna Ba Tayi Mutuwar Zaune Da Hawaye Tana Kallon Momi Nata Zuba Mata Maganganu Na Kwantar Da Hankali Ta Ce Ki Tuno Shekaruna Mana Momi Yakikejin Za Ki Binne Tunanina Da Abinda Bazai Yuwu Ba Tafarakuka Karki Yaudareni Da Cewa Zan Iya Haifar 'ya'yan Da Ba Sikila Ba,gara Kizo Kitaya Ni Mui Jimami Mui Kaico Da Nadamar Yadda Muka Amince Da Auren Yaya Yushau Alhalin Ta Ko Ina Bai Cancanta Ba Tabbas Mun Zalunci Yaran Dazan Haifa Indai Zasuyi Rayuwar Su Cikin Jinya Da Jin Ciwo Irin Wanda Nakeji,ruma Tasake Barkewa Da Kuka Tausayin 'ya'yan Cikinta Kamar Zai Kekketa Zuciyarta Momi Takasa Daurewa Danhaka Itama Tafara Tayata Momi Nason 'yarta Ruma Tanajin Tausayin Halinda Take Ciki Dakuma Wanda 'ya'yanta Dake Shirin Zuwa Duniya Zasu Shi Ga Ruma Na Tausayin Kanta Amma Ga Abinda Yafi Shi 'ya'yan Dazata Haifa Irin Rayuwarta Zasuyi Rayuwa Mai Wahala Irin Wadda Ko Makiyarka Bazakayi Wa Fatanta Ba Yan Biyu Zan Haifa Kuma Duka Sikila Momi Tausayinsu Zai Illantani Indah Irin Jinyar Da Nake Zasui Momi Nayi Nadamar Hakurina Da Biyayyata Wadanda Suka Saukaka Min Auren Yushau Harmuka Dau Wannan Hakkin Na Haifar Yara Masu Ciwo Haka Dai Ruma Taita Sumbatu Har Saida Wata Nurse Ta ShiGo Taita Musu NasiHa Yushau Kam Ana Cin Amarci Har Dakansa Yadinga Jin Asarar Rayuwar Auren Dayai A Baya,dakuma Sara Wakansa Wajen Kafewa Neman Dayazamo Masa Alkhairi, Dole Yakoyi Tattali Da Kalaman Kwantar Da Hankali Da Bayyana Soyayya,cikin Satin Bikinsu Da Aure Suka Zama Wasu Laila Majnun Duk Da Cikin Wadannan Sati Biyun Abubuwan Mintsinin Zuciya Akan Sumoli Tuni Sunfara Bayyana,amma Yanajin Jarumtar Sadaukar Da Son Ransa Ga Soyayya Wadda Ta Afko Masa Rana Tsaka Batare Daya zaci Abin Mamaki Ya Manta Da Komai Da Kowa Kaiko Bangajiya Baijewasu Alhji Dakuma Hajiya Ba Wata Safiyar Lahadi Yafarko Yatarar Da Missed Calls Din Alhji Dakuma Na Hajiya Gabansa Yadinga Faduwa Da Fargaba Tare Da Zargin Kila Ba Bu Lfya,kokuma Kiransa Ya Ke Yi A Nuna Masa Iyakar Sa Akan Ruma Hakan Yasa Ya Share Kiran Ya Ci Gaba Da Sabgoginsa,sunkarya Kumallo Kowa Cikin Kwalliya Suna Zaune Ana Hira Amma Dai Yushau Na Satar Hararar Kwanukan Da Suka Gama Da Abinda Ya Riga Ya Saba A Gidansu Ana Gama Cin Abinci Ake Kwashe Kwanuka A Wanke ,ruma Ma tana Kwatantawa Yaddako Bata Wanke A Lokacinba Musamman Lokacin Sanyi Saboda Ciwanta Takan Kwashe Ta Adanasu A Kichin Amma Sumoli Da Sauki,dayagaji Da Hararar Kwanukan Saiya Shirya Yimata Jirwaye Dakamar Wanka Inda Ya Kwashi Kwanukan Ya Nufi Kicin Yana Fitowa Tsakar Gida Sai Ga Almajirai Biyu Yadanji Takaicin Ganinsu Dantaimasa Maganar Daukan Almajiran Aiki Sudinga Yimata Aikace AikaCe Suka Gayamasa Cewa Aunti ce Tadaukesu Aiki Kullum Sudunga Zuwa Sunaimata Shara Da Wankewanke... . Hhhh... To pa. Yushau welcome to the world.. Yanxu aka para wasan. Muje zuwa.. Dan Aunty GORAN DUMA (P 42) . . Yaushe Kuka Fara Wanke Wanken,? satin Mu Daya Kenan Yaji Wani Mugun Amai Nataso Masa Ya Ce To Dan Allah Fita Bana Bukatar Sake Ganin Kowa Agidana Tuni Sumayya Na Tsaye Jikin Taga Tana Jinsu Haushin Duniyarnan Ya Isheta Ta Lalubo Mai Kudi Ta Aura Wanda Yakamata A Ce ta fantama Zai Iya Aje Mai Wanke mata Musamman Idanko Da Harabar Ajiyn Motocin Gidan Ubansa Ka Kalla To Amma A 'yan Kwanakinta A Gidan Tafara Tsintar Kamar Ta Gina Ne Bata Shi Ga Ba Ne Mijinta Furar Dankoneya Shigo Rai A BaCe Yadauki Remote Ya Sauya Gurin Zama Kwatsam Ta Jefo Masa Wani Batu Mai Cike Da Rainin Hankali Wani Abu Na Dauremin Kai Darling Sama Da Sati Biyu Da Auren Mu Amma Ban Taba Ganin Wani Ko Wata Ya Zo Gidan Na Ka Gabatarmin Shi A Matsayin Dan Uwanka Ba,duk Sai Tarkacen Abokai Da Makota Ya Ce Sumayya Aini Ki Ka Aura Ba Dangina Ba Saboda Haka Karki Wani Fitini Kanki Da Rashin Ganin Dangina Kai Haba Honey Ni Har Dasu Na Aure Ka Wallahi Ai Abin Alfaharine Ace Mutum Ya Auri Dan Dangi Ba Kamar Wanda Yafado Daga Sama Ba Wani Irin Rudu Yashiga Sai Ga Kiran Alhji Nandanan Ya Daga Ko Dan Shawarar Da Zuciyar Sa Ta Bashi Na Tuntuntuni Akan Amsar Bawa Sumoli Saboda Ma Kar A Fitar Da Gurbin Raini Ko Kuma Aci Amanar Soyayya Alhji Ya Ce Kaga Malam Ba Alfarma Zan Nema A Wajenka Ba Ruma Ce Ba Bu Lfya Tunjiya Zuwa Yanzu Dai Ta Hai Hu Muna Son Ganinka Da Gaggawa Ya Katse Wayar Yushau Ya Cika Da Farincikh Ruma Ta Haifamasa 'ya Amma Gauraye Da Fargabar Ance Bata Da Lfya Yana Tsoron Ta Mutu Yanzu Ba Bu Makawa Dangi Sai Sun Masa Sharrin Shiyakasheta A Rude Ya Dinga Kiran Alhji Yaki Dagawa Darling Me Ke Faruwa? Kishirya Muje Gidan Mu Yanzu Inki Ka Ga Gidan Kila Kisan Dan Dangi Kika Aura Ba Wanda Ya Fado Daga Sama Ba Kadauki Maganar Da Zafi Allah Ya Baka Hakurh Darling ,Tadan Bugi Shi A Kafada Ta Wuce Tana Dariya Bari Na Shirya Cikin Ransa Ya Ce Meyakamata Ya Tunana Akanta Kodayake Yaudarar Kansa Kawai Yake Tuni Ya Tunanadin Abinkuma Ya Tunoshi Ne Sumoli Kuma Wadda Ko Secondry Bata Cika Ba Ita Ce Burinsa Amatar Aure,yakuma Dace Ya Aura, Gata Kyakyawa Ma Amma Abinda Abinda Yakasa Ganewa Wanda Yake Zato Da A Budewar Idon Bokone Yanzu Ya Fara Shakkar Kamar A Dabi'ane Wato Rashin Jin Kunyar Miji Da Fadamasa Magana Kaitsaye Sumoli Na Iya Kallon Kwayar Idansa Kaitsaye A Kowanne Irin Lokaci Tafada Masa Ko Wanne Irin Magana Ta Soyayya Har Na Can Karshe Wanda Duk Dadewar Sa Da Ruma Bata Taba Iya Bude Ido Tafadamasa Ba To Anji A Bar Wannan Dama Ruma Bata Sonsa Amma 'yan Boko Akasani Da Lakabawa Miji Sunaye.Darling. Dear.Honey,sweety Da Sauransu Da Sunayen Nan Take Kiransa Tun Ma Kafin Suyi Aure Dan Haka Ya Cire Su A Layin Halin 'yan Bokone Dan Kawai Abin Na Burge Shi Duk Daya Kasa Cinkar Dalilin Burgewar To Amma Tsayayyar Da Sumoli Taimasa Dazufa? Yafi Zatonta A Mace Data Gama Wayewa Wadda Mata Dauki Kanta Daidai Da Mijin Itakuma Dabiar Ina Sumoli Ta Fincikota? Baisan Haka Ba Saida Sumoli Ta Fito Cikin Shirin Fita Fuskarta Cike Da Kwalliya Kamar Mai Shirin Fita Gasar Sarauniyar Kyau Tasha Matsatsun Riga Da Siket Na Leshi Ga Kuma Yalolan Mayafi Ta Yafa Tana Ta Taunan Cingam Yaji Haushi Kamar Ya Kashe Shi Ya Ce Amma Bada Wannan Shigar Zamuba Ko? Ta Ce Haba Sweety To Gidan Naku Masallacine Daza Ce Bazanje Haka Ba? Ba Masallaci Bane Haka Zalika Ba Mashaya Bane Tajuya Adan Kufule Tadawo Sake Da Mayafi Wanda Yadan Fi Na Dazu Yafito Dauke Da Key Yana Cemata Wai Duk Ina Mayafan Dana Zuba Miki A Lefe Haba Wadannan Saika Ce Wata Matar Limami Washegarin Ranar Da Akakawosu Na Mayar Dasu Kasuwa Na Sauyosu, Ya Tadda Gidan Ba Bu Kowa Sai Megadi Ya Basu Tabbcin Duka Suma Asibiti Ance Ruma Ta Sauka Ko? Ansami 'yan Biyu Allah Ya Raya,yan Biyu? Yushau Ya Tambaya Cikin Farinciki AlhamduliLlah Megadi Yaimusu Kwatance Da Cewa Aitana Asibitinsu Datake Kwance Tuntuni YuShau Kam Ya Girgiza Dakin Ruma Tadade A Asibiti Na Gyadi Gyadine Yushau Kam Yasan Zaiji Ajikinsa Aljihu Zai Yi Bayani Gashi Hidimar Biki Dayayi Ba Bu Mataimaki Kasuwa BaBu Ciniki Bugu Da Kari Alhji Neke Bashi Kaya Kwasha Kwasha Tunda Ya Sakarmasa Ruma Ya Make Hannu Satin da yawuce Ma Hanashi Bashi Yai Wai Sai Ya Bayar Da Kudi Kamar Kowa,, Fice Yushau Ya Zagayesu Da Ido Saida Yaji Fitsari Na Neman Kubcemasa Inka Cire Su Hafsat Gaba Daya Manyan Surukansa Ne A Dalilin Ruma Saboda Rashin Kyautatawar Da Sukejin Yai Musu Mahaifansa Biyu Na Ruma Biyu Goggo Daga Rogo Saikuma Wadda Baiji Dadin Ganinta Ba Innar Marigayi Auwal Yadda Kafafuwansa Suka Sarke Hakama Na Sumoli Saboda Kwarjinin Da Mutanan Sukaimusu Tare Da Jin Raunin Karbar Ko Inkula Da Akaimusu,haka Dai Aka Gaisa Inka Cire Goggo Dataimasa Barka Da Momin Ruma Dataima Sumoli Fatan Alkhairi Tare Da Bayar Da Hakurin Rashin Halartar Zuwa Ganin Amarya Dakin Yai Tsit Saboda Rashin Sanin Halinda Take Ciki Hardai Lokacin Sallah Tai Maza Suka Fice Sumoli Tayo Alwala Cike Da Fargabar Wanda Zata Tambaya Aron Hijabi Kinyi Sallarne Hijab Nake Jira Su Aramin Momin Rumaisau Ta Mika Mata Wani Yayinda Hafsat Karaf Wanda Dama Tadade Tana Jifanta Da Harara Nifa Farkon Shigowarkima Na Zata Budurwa Ce Wallahi Sam Bakiyi Kama Da Matar Aureba,hajiya Tatare Ta Rai A Dan Ba Ce Kai Ke Dai Hafsat Kincika Shishigi Kowa Bada Yanda Yaza Barma Kansa Rayuwa Ba Yushau Ya Kule Da Haushin Hafsat Wadda Yake Ganin Ta hadashi Da Mahaifansa Amma Hakan Ma Yasa Hafsat Takara Matsawa Tana Hararar Yushau Ta Ce To Hajiya Ai Gara Afadawa Mutum Gaskiya Dankar A Zageshi A Bayan Idansa Yushau Kam Yakasa Magana Sai Ga Alhji Ya Shigo Yamikamasa Takarda Cajin Dasukaimana Na Yanzu Kenan Maza Jeka Biyasu Abinsu Yushau Kam Yaga Kudi Sama Da Dubu Hamsin Yadago Ya Dubi Alhji Baki Na Rawa Alhji Ai Yau Lahadi Ba Bu Bankuna Alhji Ya Ce Baka Aje A Gida Ba,yanzu Yaya Za Ayi, Sum Sum Ya Fice Daga Dakin Goggo Ta Yunkura Ta Ce Tsaya Kaci Abinci Alhji Ya Ce Barshi Munan Yaushe Rabon Mu Da Abinci,yushau Dama Baiyi Niyyar Tsaya Wa Ba Danyasan Anyi Niyyar Tsinkashine, Nan Ya Bar Sumoli Dan Yasan A Gida Ko Cikakkiyar Dubu Ashirin Baida Ita Saiwajen Bayan Isha'i Yadawo Cike Da FargaBa Ya Taradda Hafsat Momi Da Alhji Ko Zama Baiyiba Alhji Ya Ce Ka Biyasu Ko? Ya Kada Kai, Kuma Sai ka dawo Mana Hannu Na Dukan Cinya Kana Nufin Hakan Yaran zasu Zauna Bako Rigar Sawa Yushau Yadaga Kai Yadubi Alhji Saboda Yadda Maganar Taimasa Ciwo Ya Ce Aima Bansan Abinda Akasamu Ba Cikin Zafin Rai Alhji Ya Ce Kuma Bakaso Kasaniba Kila Donkar Kai Wahala Sai Can Momi Ta Ce Kanemo Masa Alfarma Mana Ya Shiga Ya Dubasu Ya Cemata Ya Cemiki Yanason Ganin sune? Dankar Na Cika Damunkune Yasa Ban Tambaya Ba Amma Dama Na Matsu Nasan Halinda Suke Ciki Alhji Yai Tsaki Momi Ta Tashi Tadawo Tadubi Yushau Cike Da Kulawa Ta Ce Kashi Ga Hafsat Ta Mike Da Sauri Nifa Momi? Kibari Ya Fito Karkuje Kuiwa Mutane Hayaniya Inji Alhji,jikin Yushau A Sanyaye Ya Tura Kofar,ruma Kam Kwance Take Magashiyan A Gado Tan Karbar Karin Jini A Gefe Ga Jarirai Biyu Bisa Kananan Gadaje Nade Cikin Lallausan Farin Bargo Daga Wani Barin Kuma Ga Nurse Tanaganin Yushau Ta Ajiye Wayarta Tataso Da Sauri Tanamasa MaraBa Murya Kasa Kasa Ya Amsa Ta Dauko Masa Na Farko Yadauka Yana Lallabawa Kamar Kwai Mace Ce Ko Namiji? Fuskar Sa Dan Firit Bata Da Mara Ba Dana Ruma Da Kallonsa Ansan Bashi Da Koshin Lfya, namijine Ga Macen Nan Yajima Yana Kallon Yaron Dake Maida Numfashi Daidai Yamaidashi Yadau Macen Da Kwarin Guiwa Ganin Tafi Namijin Kuzari Yaga Alamar Cutar Tafiyawa Ga Namijin Akan Macen Canyaji Ruma Na Magana Kasa Kasa Dasauri Yadubi Nurse Ya Ce Kinji Magana Take Ta Ce A Tausaye Sambatu Take Kawai,cikin Nannauyan Bacci Take, Kamarfa Ana Iya Gane Abinda Take Cewa Hakane Kakarasa Kusa Da Ita Zaka Iyaji Yamikamata Yaran Yakara Sa Kusa Da Ita Farat Daya Yaji Ta Ce KUYI HAKURI BANSO HAKA BA,BAN SHIRYA HAKA BA,DAN ALLAH KU YAFEMIN.. a Razane Yadube Nurse Din Meyafaru Dawa Take? Saida Nurse Tadauke Kwallah Ta Nuna Yaran Da Yaranta Take Tana Tausayinsu Da Nadamar Ta Haifesu Sicklers Amma Ba Abin Mamaki Ba Ne Kasancewarta Sikila Ita Kadai Tasan Azabar Datakesha... . Ayya masoyiya ta Allah Ya baki lapia.... Ba komai ya tsaida ni ba illa tausayin ta.. Sai jibi muci gaba kapin nan ta dan samu sauki.. Dan Aunty GORAN DUMA (P 43) . . Ita Ce Kadai Zatafi Tausayamusu,a Razane Ya Bar Gadonta Yakoma Na Yaran Yahau Kallonsu Yadaga Kai A Gigice Ya Ce Dukansu Sikilane? Ai Ba Dauka Ake Ba, Uwa Da Uba Ke Tarayya Su Haifi Sikila Ita Kadai Bazata Iya Haihuwar Sikila Ba Sai Idan Mijinta Ma Nada Irin Wannan Nauin Jinin A Sakarce Yace Gaskiya Ni Lfyata Kalau Nurse Kam Tafara Lissafin Daga Kauyen Dayafito Da Kyau Ta Daure Ta Tambayeshi Au Kaine Mijinta Yakada Kai Amma Dai Kafin Aurenku Baku Ziyarci Mashawarta Sikila Ba Kilama Bakui Gwajin Gynotype Ba,kuma Bayan Auren Ma Baka Shiga Lamarin Asibitinta Sosai Ba Kunya Ta Hana Yushau Amsawa Yana Ma Fargaba Kar Allah Ya Jefo Wani Cikin Danginsa Yaji Haukar Wannan Matar Donsu Ma Haka Suke Girmama Asibiti Tamkar A Can Aka Buso Wa Ruma Rai Ya Fice A Can Kuma Alhji Yatareshi Dawata Bakar Magana Kaganka Da Sikila Har Kala Biyu Ko? Allah Kenan Sai Mugani In Haka Rami Zakai Ka Binnesu Ko Kuma Suma Zaka Ce Shagwabar Ce,yushau Kam Yakasa Magana Yaimusu Sallama Yatambayi Ina Sumoli Aka Ce Tabisu Hajiya Gida Dan Takaici Kiranta Yai A Waya Tafito Suka Tafi,a Hanya Ne Ma Yadinga Samun Karin Haske Gurinta Yaji Tun Washegarin Ranar Dayasaki Ruma Take Kwance A Asibiti Yaji Cewa Tasha Wuya Lokacin Haihuwarta Sannan Bayan Haihuwar Tasami Karancin Jini Kuma Ga Jininta Ya Hau Ba Bu Halin A Yimata Karin Jini Har Sai Ya Sauka Ya Ji Cewa Har Kukan Mutuwarta Anfasa Sai Daga Baya Aka Fahimci Da Ranta Likitoci Sukai Kokarin Shawo Kan MatsalarTa Har Jininta Yakoma Daidai Aka Hau Yimata Kari,kuma Tafara Dawowa Hayyacinta,haka Kuma Yakarajin Yaran Basa Da Koshin Lfya Musamman Ma Na Mijin Wanda Aka Haifa Da JUNDICE Ajininsa Dayawa Har Ake Tunanin Kila In Ba Ai Sa A Ba Sai Anyimasa Juyen Jini Da Sauran Wasu Labaran Duka Kuma Sun daga masa Hankali Dan Daliline Wanda Dangi Zasu Kara Tsanarsa Wahalar Aljihu Da Tashin Hankali Na Wuyar Da 'ya"yansa Zasu Sha Kokuma Suke Kanci Amma Me Suna Gab Da Wuce Wani Store Sai Sumoli Ta kara masa Wani Takaicin Honey Mubiya Store Dinnan A Sai Kayan Abinci Ya Dubeta Da Shakka Amma dake Ance Amarya Bata laipi, Buhun Shinkafa Daya,katon Din Taliya Biyu,indomi Katan Din Madara,galan Din Mai Uku,fari Da Ja Da Sauransu Wai duk A Cikin Sati Basu Kai Ukun Nan Ba Muka Hadiye A Cikinmu? Kai Abin Kamar Mafarkifa,fuskarta Ta Sauya Zuwa Dan Tsoro Tsoro Amma Tashare Kasan Dai Ba Araba Gidan Amarya Da Baki Ko Taron Idine Suke Zuwa Maiya Hadasu Da Kayan Tea Ko Sabulun Wanka Dana Nema Dazun BaBu? Kaga Allah Ya Baka Hakuri Bansan Abinda Kake Nufi Dani Kenanba Suna Karasowa Wani Kanti Ya Shiga Bai ko Dubeta Ba Kijirani Nafito Dan Ba Bu Kudi Sosai,yadauko Karamin Buhun Shinkafa,25kg Garwar Turkey Daya,sukari Rabin Kwano.A Leda,peak Gwangwani Uku Kayoyin Sabulu Uku,yana Kallan kifin Gwangwani Ya Wuce Bai Siya Ba,yadauki Kwallin Kus Kus faya Fahimci Taimugun Tsanar Sa Sai Bread Kwaya Daya Jal,ashe Sumoli Ta Shaka Da Safe Karin Kumallon Saita Tafasa Ruwan Zafi Kawai Ko Kayan Kamshi Ba Bu Tajuye A Fulas Ta Hada Madara Guda Ta Dire Masa Tare Da Tilon Bredin Daya Sawo Sukarin Ma Haka tadire Masa A Leda Takirashi Karin Kumallo Haka Sumoli Taita Satar Kallansa Dantaga Yadda Zaiyi,amma Yushau Ko Ajikinsa Ya Kwance Leda Ya Debi Sukari Ya Juye Fiye Da Rabin Madarar Sannan Yaja Bredi Yafara Cinsa Hankali Kwance Takaici Yai Mugun Shake Sumoli Ta Zuba Tagumi Tana Hararar Abincin Har Saida Yakusa Kammalawa Ya Ce Wai Ke Ba Kyajin Yunwane? Idan Inajin Yunwa Sai Inci kar in Mutu? Ci Karki Mutufa Kika Ce?Ba Ke Kika Girka Da Kankiba? Yo Dafa Ruwan Zafi Kawai Honey Haba Saika Ce Wasu Mayunwata Tea Da Gayan Bread Ya Ce Ba Bu Dai Kyau Fariya Wani Kamar Haka Yake Nema Baisamuba,nan Ma Takaici Ya Rufeta Ya Nunamata Kudi Naira Dari Uku,ki Bayar Asawo Maki Tumatir Da Magi Tunda Kince Ba Bu Zan Aiko Da Nama Ayi Farfesu Tadinga Juya Kudin Kamar Ta Watsamasa A Fuska Ammadai Kasan Dai Ba Bu Maganar Sayen Wani Abu Ainaga Ka Kan Bani Sama Da Dari Uku Na Sallamar Baki Bare Bamu Da Komai A Dangin Kayan Miya Yai Gaba Ya Ce Ai Juyin Duniyar Dana Gama Yimiki Magana Akansa Kenan Yanzu Inkin Yi Bakin ki Basu Hakuri Sainadawo, Yau Ko Rakiyar Bataimasa Ba Karfe Goma Sha Daya Mahahfiyar Sumoli Ta Dira Agidan Suka Kacame Da Murnar Ganin Juna Suna Zama Mamanta Tafara Mata Fadar Barin Gida Ka Ca Kaca Wallahi Almajiran Dake Tayani Aikin Ne Yau Basuzoba, Dama Wasu Almajirai Nezasu Miki Aikin Kirki Mezai Hana Ki Shawarci Mijinki Asamo Miki 'yar Aiki Kudinga Biyanta Kawai Akawota Cike Da Murna Sumoli Tace Ba Sai An Shawarce Shi Ba, Har Karfe Daya Momi Na Gidan Suna Hira Sumoli Tamike Tana Dariya To Niyanzu Mezambaki Wai Amrya Guda Azo Gidanta Tadinga Mizata Bada Ni Inkuna Da 'yar Fulawa Dan Sammin Dan Wake Nake Sha Awa Danaje Na Jefa Akwai Ragowa Bari Na Debo Miki Anti Jamila Ce Duk Ta Karbeta Tana Kyallara Ido Taganta Shikenan Ta Huta Zuba Jari Suna Fitowa Tsakar Gida Yaron Da Yushau Ya Aiko Kawo Nama Yazo Bayan Fitar Sa Momi Ta Ce Aidanasan Farfesu Za A Sha Dana Bari Gobe Nazo, to Ko In Dibarmiki Danyene? Ayi Haka? To Ai Bazanki Ba Nan Sumoli Ta Kwashe Rabin Nama Ta Bata Itakuma Ta Karbe Tana Godiya Kamar Gadon Tsohonta,hakama Yau A Asibiti Ya Wuni Dadadi Badadi Ruma Dai Jikinta Yafi Na Jiya,dan Yau Ido Biyu Ta Wuni,kuma Har Akanyi Musayan Gajerun Hira Da ita, ya Ci Gaba Dashan Kyara Wajen Alhji Bayan Kyarar Kuma Yakemiko Masa Duk Wata Bukatar Kudi Da Ta Taso Ya Biya,ciki Harda Karamin Alhaki Pure Water Da Masu Dubiya Zasu Sha,akan Kayan Jarirai Kuwa Da Hafsat Alhji Ya Jonashi,waitayimasa Lissafin Wasu Makudan Kudade Wanda Suka Sashi Mikewa Tsaye Ya Kurma Mata Tsawa,tundani Ba Manajan Banki Bane Irin Mijinki,me Zai Hana Kikai Ni Kasuwa Ki Sayar,kamar Ta Fashe Dadariya,ya Buga Tsaki Yamike Ya Barmata Wajen Tafito Tana Dariya Tana Cewa Ina Ruwan Yaya Bala'i Saika Ce Na Kashe Masa Yar Fari Washe garin Sumoli Tanemi Binsa Asibiti Don Ta Dubo Ruma Baimusa Mata Ba Amma Yau Yayi Niyyar Bazai Wuni A Asibitiba Kasuwa Zai Wuce,ya Ce Mata Inafatan Kinsanya Ragowar Naman Nan A Gidan Kankara A Sanyaye,wanne Naman? Ragowar Na Jiya Mana,dan Nasan Yafi Karfin Cikin Mu Lokaci guda, Cikinta Yakada Kamar Ta Cemasa Eh Yana Gidan Kankarar Saikuma Ta Tuna Kalatar Sa Akan Nama Kila Suna Da Ta Cemasa Ba Bu Wani Ragowar Nama Wallahi Dan Jiya Momi Tazo Narasa Abinda Zanbata To Lokacin An Kawo Naman Nan Kawai Saina Dibar Mata, Saboda Da Kudinki Nasiyoko? Mamaki Ya Cikata Momin Tawa Yushau? Momin Taki Ni Gaskiya Kifadamata Banasan Yawan Zirga Zirga Datakemana A Gidan Nan Ta Dakata Haka,nandanan Sai Ga Sumoli Na Hawaye Bakinta Na Ta Karkarwa Tana Ce Honey,honey,,,ya Cemata Ni Bansan Rainin Hankali Malama Ko Kina Nufin Ni Bawan Gidan Kune? Ke Kanki Kinsan Abinda Ake Min Ba A Kyauta Min Har Yaushe Akai Auren Da Mahaifiyarki Zata Mayar Da Gidannan Na Kawarta? Inafa Sane Tazo Gidan Nan Yakai Sau Takwas To Me Take Zuwa Yi? Sumoli Takasa Magana Kallonsa Kawai Take,dan Bata Taba Tsammanin Lambar Rashin Mutuncin Yushau Yakai Haka Ba Wai Gyatumarta Yake Zagi . Kwanaki Sukadinga Dauki Daidai Suna Wucewa Ruma Nasamun Sauki Yaranta Nadan Warwarewa Duk Da Har Yanzu Ba A Janye Tunanin Yiwa Namijin Juyen Jiniba Dazarar Yakara Wasu Kwanaki,yushau Kuma Nata Cin Kwakwa Wajen Alhji Na Kyara Da Kawo Kawo... . Dan Aunty.GORAN DUMA (P 44) . Dan Ma Har Yanzu Alhjh Bai Debo Masa Maganar Bashi Ba Amma Aljihun Yushau Yayi Mugun Girgiza Ta Yadda Har Kudin Mutane Ya Shiga Tabawa Kuma A Bangaren Sumoli Wadda Itama Take Huro Masa Wuta Wadda Har Zuwa Yanzu Yakejin Kunyar Yaji Nadamar Aurenta Ko Da Acikin Zucine Duk Yadda Yake Zaton Sumoli da Tarbiyya Da Saukin Kai Tare Da Bin Miji Saboda Rashin Wayewar Kan Boko Bata Doshi Nan Ba,amma Har Yau Ya Rasa Dalilin Dayasa Yakejin Kamar Bahaguwar Fahimta Yakemata Yanzu Kam Yakosa A Sallami Ruma Yasamu Sauki Ta Wurin Alhji Ana Gobe sati Da Haihuwar Ne Alhji Yakirasa Takanas Gida Ba Bu Irin Adduar Da Bai Karanto Ba Amma Bata Ciba To Malam Ko Daga Sunan Nan Za Ayine? Banga Hakika Ba Gobe Kuma Sati Da Haihuwar Hakan Kuma Ya Tsorata Yushau Gudun Bacin Rai Ya Ce Yakarka Ce Ya Sheko Karya Alhjh Na Siya Suna Can Kasuwa Na Ce A Bar Su Gobe Da Safe Sai Akawo,alhji Ya Ce To Ko Danaji Saidai Kuma Batun Sunan Daka Rada Wa Jariran Ko Bakai Musu Hudubane,? Alhji Ainazaci Anyi Musu? Uban Waye Zaimusu? Waka Ajiye Bawanka? Cikin Bacin rai Alhji Ya Ce Ai Dama Hakane Sai Mutum Ya Karta Son Zuciyar Sa Yana Fakewa Da Allah,tabbas Komai Nufin Allahne Amma Ka Bar Mutane Masu Hankali Sui Wanna Togaciyar Bawai Irinka Masu Butulcema Rahamar Ubangijiba Ubangiji Yaimaka Baiwar Mace Tagari Dan Ni Na Maka Dolen Aurenta Kasakomin Ita Kazabi Wadda Na Hakikance Fitinace Ga Rayuwarka,wallahi Yushau Ba Dan Umarnin Musulunci Na

Chapter 14 of 21