Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ki sha magani, Hafsat taimaka ki murza mata tafarnuwar ki ta ce ki kaw mata". Hafsat ta tashi ta 6arin jiki tana yiwa Rumasa'u sannu ta wuce kicin ta d'ebo tafarnuwa masu kyau ta 6are, ta dandaka sannan ta zuba ruwa kofi daya ta tace da rariya ta kawowa Rumasa'u ta shanye. An fi awa daya kafin a samu ciwon cikin ya lafa, wannan ne kuma ya sa Hajiya ta tsokano maganar da ta ke jin yyinta ya zama dole dan ta fahimci Rumasa'u, so ya rufe mata ido tana shirin yin abin da za a ga laifinta. "Rumasa'u kun ta6a maganar ciwonki da Auwalu kuwa?" Alamun damuwa da nadama ya bayyana a fuskar Rumaisa'u, kwalla har ta cika mata ido, ta girgiza kai ta ce. "Ba mu ta6a ba Hajiya". Cikin zura mata ido, Hajiya ta ce. "Tyn farkon ne kika rasa hanyar sanar da shi Rumasa'u?" "Ban san za mu dore tare ba Hajiya". Hajiya ta yi shiru alamar nazari, sannan ta nisa ta ce. "Ni har na fara zargin ko ganin yawan laulayinki ya hana shi turo manyansa. Ga su Hafsa suna ta faman jiranki". Ta matse kwallar idonta tana amsawa. "Ni ce na ke dakatar da shi Hajiya, kuma na kasa sanar da shi dalili". Hajiya ta girgiza kai ta ce. "Wannan kuma ba dabara ba ce kika yi, za ki ta zama haka ne Rumaisa'u? Ai a rashin kira karen bebe yake 6ata, ki kokarta ku tattauna lamarin". Cikin sanyin jiki Rumaisa'u ta ce. "Shikenan zan kokarta Hajiya". Ta gama shin bacci ke nan ya mmako mata waya, ta dauka da kasalar rashin 'karfin jiki. "Auwal ba ka jin bacci?" Muryarsa a d'ashe ya amsa. "Na kwanta ya 'ki zuwa Rumasa'u, abubuwa barkatai sun cushe a 'kwa'kwalwata. Ga kadaici ga matsaloli". Ta dan yi dariya ta ce. "Me ya dami ranka haka Auwal?" Ya sauke numfashi..... "Kafin mu rabu na fahimci kamar ba kya jin dad'i, na taho da tauayinki da neman hanyoyin da zan samar miki waraka ko da na dauke kewa da 'karfafa gwiwa ne, amma duk kin bi hanyoyin da hakan za ta afku kin toshe. Na fara sarewa Rumasa'u dan na fahimci kamar kin raba zuciyarki biyu ne kin bar min daya na sani, dayar kuma kike wahalar dani da ita. Wata irin 'kaunarsa ta dingo bijiro mata, tana nemansa ta 'kwalla, tana kokawar daurewa yana gagara. "Auwal wannan ne zai hanaka bacci? To in dai ni ce ba za a haifi matsalolin da za su 6ata ranka da ni ba. Za mu sami lokaci nan kusa mu tattauna... Amma ina son ka a jiye a ranka soyayyarka ce ke hana ni yin abin da kake hasashe ina jinka da matsayin wani 6angare na jikina, wanda rashinsa zai gutsire rayuwata, amma na 'kure fatan hakan zai gaza faruwa". A raunane ya ce "Saboda me? Rumaisa'u duk yadda nake da matsayi a zuciyarki da sha'kar numfashinki d'igo ne na matsayinki a wata zuciyar, na kuma dami raina da son kai 'karshen buri a kanki kafin mutuwa ta runtse ganina, ke kuma kin kasa gane hakan..." Ta yi saurin tare shi. "Haba me ya kawo zancen mutuwa Auwal?" Shi ma ya tareta da nasa batun. "Ai ya zama dole, 'karuwar burika, cika wasu da su6ucewar wasu alamu ne na kusantar kabari sai raina yake ciwo da hasashen mutuwa zata iya riksta ba tare da na cika burin samunki ba." Ta fara hawaye sosai, dan haka ta jima ba ta tanka ba, har ta fitar da sautin kukanta kadan, sannan a cikinsa ta ce masa. "Ba na fatan dai-dai da kwayar zarra in cutar da kai Auwal, kuma bana son rabuwa da kai.." Ya tare ta a dan 'kuntace. "Shikenan sai ki bar mu muyi ta bulayi a soyayyar da ba ta da rana, wadda ta ki ta zuciya ta saba da ta fatar bakinki, kina sona amma kin kasa ba ni damar mu kasance 'karkashin sunna... wannan makahon so ne..." Ta yi kokarin tare kukanta, ta ce. "Akwai matsala ne Auwal, ni ke nan yau lafiya, gobe babu. Zan zame maka dawainiya in gundure ka, shi yasa ba na son cin karo da kukanka Auwal". Ya yi dariyar da ta fad'ad'a masa 'kirji ya ce. "Wa ya ke dorawa wani lalura Rumaisa? In Allah Ya so sai Ya yaye miki, ai babu cutar da ba ta da magani. Ita kanta cutar ma wani maganin ce, domin tana kankare zunubai... Ni ma da nake son daukar dawainiyarki ladan zan samu idan na kula da ke, duk sanda aka ce ba ki da lafiya sai na ji da tare muke sai na fi samun nutsuwa..." Ta 'kara fashewa da kukan da ya tsorata shi. A rikice ya ce. "Wai don Allah me yake faruwa ne? Rumaisa na kaa canko dalilan wannan kukan naki". Cikin kukan ta ce "Na gode da niyya da fatanka, amma ciwo na mutuwa ce kadai zata raba... Saoda haka aurena da kai yana nufin ka yi ta danniya da hakuri a kaina har 'karshen rayuwata, domin haka Allah Ya halicce ni, haka kuma Ya so ya ganni..." Ya rasa fassarar da zai wa maganganunta, rashin yanke shawarar ya sa shi yi mata tambaya a gajarce. "Wai wanne irin ciwo ne?" Kai tsaye cikin dakewa ta yi karfin halin amsa masa. "Sickle cell" Ya ji kamar ta doka masa guduma a 'kirji, cikin 'yan sakanni wasu miliyoyin tausayinta da fargabar yadda lamuransu zai kasance ya mamaye masa 'kirji, dan ya san ciwon sickle cell ba da wasa ba kasancewar wani abokinsa sikila ne ya dad'e da sanin yadda masu ita suke shan kashi sai dai wannan 'karamar matsala ce idan aka kwatanta da neman makomar 'ya'yan da za su haifa. Duk da a rikice yake bai kasa 'ko'karin tattara kalaman da zai 'karfafa mata gwiwa ba. "Mene ne matsala a kasancewar sickle Rumaisa, ko ke kika yi kanki dan me za ki raba kanki da ni ballatana Ubangijin da Ya yi ni Ya yi ki, ba domin na fiki ba? Ki zama mai tawakkali da ha'kuri da rayuwa sai matsalolinki su zame miki kaffara. In kuma domin wannan kike gina katanga tsakanin da kasancewa tare, to ni ban fahimci gatan da kike son yi min ko kike son son yi wakanki ba". Yanzu ta rage kukan da ta ke, dan a zahiri hankalinta ya soma kwanciya, duk da ta san bai kamata ya kwanta din ba. Ta nisa ta ce. "Kar ka yi gaggawar yanke hukunci Auwal, ka zauna ka yi tunani da kyaun duk matsaloli a kaina ka lissafo suka ga yadda zaka iya tarbarsu, yadda zaka dinga dawainiya da ni, dawainiyar aljihu da ta KWANJI, ha'kuri da ni wajen kukan ciwo da hakurin wasu kulawa daga gare ni lokacin ciwo in duk wadannan sun zama sau'ki a gareka Auwal makomar 'ya'yanmu ba zata zama sau'ki ba matu'kar ba ka kasance wanda ba zai bayar da gudunmowar da ba zaka haifi sickler ba". Ya ja numfashi sosai saboda rashin abin cewa, amma dole ya nemo shi. Ya ja numfashi sosai saboda rashin abin cewa, amma dole ya nemo shi. "Yin daainiya da ke, da kuma hakuri da laulayinki ni ba zan ta6a kiransu matsala ba Rumaisa, ina son ki soyayyar da nake jin ko mugun hali ne a jininki ba zata gaza ba, bare wannan jarrabawar ta Ubangiji da idan kika haye ta da tawakkali, na haye ta da jurewa dawainiya da ke zamu iya samun aljanna da ita. Batun 'ya'yanmu shi ne hanzari, amma wannan zai hana ki aure har abada ke nan Rumasa'u? Kafin haduwa da ni wanne tanadi kika yiwa kanki a fannin aure, me yasa kike ganin zan bayar da gudunmowar da zamu haifi sickler?" Ta amsa masa a raunane. "Ban ta6a fitar da rai zan yi aure ba, sickle cell kuma ba ciwo ne da za a ce ka auri mai shi ya zama waraka ba, domin za ku samar da iyali irinku ne gaba daya, amma dai ban ta6a hasaso aurena da rayuwar auren wani abu ne mai sau'ki ba. Ina sonka Auwal wallahi ba na fatan duk wani abu da zai cutar da kai, na san kuma ko yaya ne aure na zai iya zame maka matsala ko ta fannin 'ya'yanmu..." Ya tare ta da sauri. "Shi yasa na tambaye ki, wacce irin gudunmowa zan bayar da kike ala'kanta ta da haihuwar sickler?" Ta jima cikin shiru, sannan ta ce. "Idan ka ji a ranka zaka iya aurena, kuma a gidanku za a barka, shi ne zamu tuntu6i likitoci dan samun shawarwari, a iya maka gwaji kuma a gano kai waye, ta nan zamu iya sanin makomar 'ya'yan namu". Yanzu ya fara samun nutsuwa, saboda haka cikin doki ya ce. "In Allah Ya so cikin satin nan sai mu je asibitin, amma ki sani duk yadda bincike zai nuna ba na ji zai iya yi min katanga da aurenki. Ki cire shakku daga ranki Rumasa'u, ina yi miki soyayyar d aban san matsaloli a tare da ke". Ta yi shiru tsawon wasu sakanni sannan ta ce. "Abin da na fi so da kai Auwal ka fara tuntu6ar magabanka shawara a kaina, kar ka biyewa soyayyar zuciyarka ka yi abin da ransu ba zai ji dad'insa ba...q Ya tare ta kamar a 'kufule "Rumaisa'u sickle cell ne yakai girman da ba za a auri mai shi ba? Haba! Wannan maganar banza ki ke..." . Dan AuntyGORAN DUMA 7 . . Ita ma ta tare shi a tausashe "Auwal babu yadda za a yi ni da kaina in 'kir'kiro abubuwan da zai nesanta mu da juna, amma duk abin da yake matsala ina guje mana shi kasancewara sickler na san da yawanmu irin matsalolin da suke fuskanta a rayuwa, ciki har da tsangamar da dangin miji ke masu matsaloli (sicklers) da za yi ta faman dawainiya da nauyi akan mijinsu ko kuma haihuwar dawainiya da su. Auwal wani lokacin ma mazajen ke tsangwamar matan akan sun zame musu nauyi... Kai wata ba sikilar ba ce idan suka taru ita da dangin mijin suka haifi sikila sai ya tattara laifin ya dora mata, wata mahaifiyar sikila da na sani ta ta6a bani labarin yadda mijinta ya fito kai tsaye yake 'kalubantarta akan cewa matansa hudu, amma ita kadai ta ishe da haihuwar sickler duk da cewa tare da mijin suka haifeta. Amma ka fahimta ba gudu nake a tsangwame ni ba ko ko kuma a 'kalubalance ni, na rantse maka babu wata wuya da ba zan iya jurewa ba, kawai dai bana sn ka yi abin da magabatanka za su yi kuka da kai. Idan aure zai shiga tsakaninmu ya kamata mu kori duk wani abu da muka san 'kalubale ne a rayuwarmu ta gaba dan a gaban ba mu da lokacinsa abin da ke gabanmu ma ya ishe mu". A sanyaye ya nisa, ya ce. "Na fahimce ki, in Allah Ya so zan yi abin da kika ce, amma dai dole mu hanzarta zuwa gwajin, ina son yin tanadin dukkanin wata juriya a kanki". Ta yi murmushin karfin hali cikin saduda ta ce. "To shikenan, Allah Ya za6a mana abin da fi alkhairi Auwal". Ya amsa cike da farin ciki. "Amin Rumaisa'u, Allah Ya sa mutuwa ce zata raba mu". Ta yi dariya ta ce. "Kuma ya zama ni zan rigaka mutuwa, na tabbatar rayuwa zata yi min 'kunci idan babu kai". Shima ya yi dariyar, ya ce. "To kin ga gara ni na riga ki mutuwar, saboda ni ba zan iya jure rayuwar da babu ke din ba". Da dad'i ya cikata kawai sai ta amsa masa da cewa. "Ina sonka Auwal!" Ya nisa cikin wani irin shauki ya ce. "Ni na san ina yi miki abin da ya fi So Rumaisa'u". Babu abin da ya motsa dan jua baya akan soyayyar da Auwal ke mata, sai ma wani 'karin tattali da tausayi da yake mata. Ya daura d'amarar sanin duk wani abu da ake gudunsa ga sickler, nisali ko a ina yake idan iska ta taso a wajen sai ya nemi Rumasa'u a waya, idan ta shiga motarsa sai ya zuge gilasai tsab, sannan duk wata sabga ta aljihu da zai mata ya juyar su kaf akan abubuwan da zai taimaki lafiyarta, dangin kayan sawa masu kauri da rufe jiki, dogayen riguna, hijabai, ni'kab har da safar 'kafa da hannu. Haka nan 6angaren abinci mawuyacin abu ne ya je mata ba tare da wani abinci da zai amfaneta ba, ko da mafi 'kan'katarsu ne wato rake. Tun daga nan hankalin Rumaisa da na iyayenta ya kwanta, suke ganin lallai ta sami mijin marainiya, Auwal ya zama dan gida a nan Kano, Rogo har ma da Abuja kowa a dangin Rumaisa'u. A nasa dangin ma Rumaisa'u, saboda haka na'am da girman gidan su Rumasa'u, saboda haka har sun amince da aurensu. Auwal ya kasa tarar mahaifansa ya sanar da su Rumasa'u sickler ce, saboda ta tsorata shi da yadda iyaye ke kar6ar lamarin dansu ya auri sickler, sai ya ke shakkar goyan baya daga nasa iyayen, musamman da yake shi kadai suka haifa, yadda suke zumudin aurensa ya fahimci yadda suka dora masa burin tara 'ya'ya saboda haka ya yi kirmisisi ya 'ki sanar da su, haka ma zuwa gwajin ya share shi saboda fargabar da ta cika ransa, alhalin ko me ma suka samo ba zai iya karya masa gwiwar auren Rumaisa'u ba. A haka manyansa suka je nemar masa auren Ruma aka yi duk yan hidimomi bisa al'adunsu aka sanya musu rana, in ta kammala karatu za'ayi. *BAYAN SHEKARU BIYU* Wata biyu ya rage aurensu, wanda za a had'a da na Hafsat da angonta Sani. Zancen duniya da ba ya 6uya, sai ga batun cewa, Rumaisa'u sikila ce a kunnen mahaifan Auwal. Kwatsam wani dare ya bar wajenta ya koma gida, ya shiga wajen Innarsa neman ruwan zafi, mahaifinsa ya yi kiransa fuska babu walwala a fuskarsa ko kad'an. Ya nemi guri ya zauna cikin sanyin jiki, mahaifin nasa ya ce. "Daga ina haka?" Sai ya ji tambayar ba wai, saboda babu irinta tsakaninsa da mahaifin nasa ko da can ma da ba shi da gurin zuwa ba a fiye tambayar ina ya je da dare ba ko dan yanayin aikinsa. Amma yau shi ne ake tuhumarsa inda ya je. Kawai sai ya yi 'kasa da kai, dan bai san abin fad'a ba, yana ji a cikin ransa nan da wata biyu Baban nasa ba zai ganshi a wannan lokacin ba ma bare ya tambate shi. Mahaifiyarsa ta shigo da fulas har da farantin kayan shayi ta dire a gabansa, zata fara hada masa ya yi sauri ya kar6e ta yana godiya. Ta nemi guri ta zauna, shi kuma jiki a sanyaye ya fara bude gwangwani yana sauraron mahaifinsa da ya dora. "Yaya me jikin?" Ya dago da sauri ya dubi mahaifinsa hankalinsa a tashe, amma fuskarsa ta kasa nunawa. Ya tattare 'kululun da ya taso masa a ma'kogwaro ya kora shi ta hanyar hamud'ar madarar ya hadiye sannan ya ce wa mahaifin nasa. "Abbba ina ka san ba ta da lafiya?" "Zancen duniya ai ba ya 6uya". Abban ya fada cikin rashin kulawa tun daga nan Auwal ya sha jinin jikinsa, kawai sai ya ci gaba da hidimar gabansa. Abban ya gyara zama ya ce. "Wato Auwal ka san yarinyar nan sikila ce ba ka sanar da mu ba, dan kawai ka na son abin da zaka sanya mu 'karanta?" Auwal ya dago cikin bugun zuciya ya dubi mahaifinsa bakinsa na rawa ya ce. "Abba... Mene ne 'karantar a auren sickler?" Cikin 6acin rai Abba ya ce. "Auren sickler ba 'karanta ba ne, kantafi ne kawai da rayuwar 'ya'ya da ta aljihu... In da 'karantar ta fito shi ne zuwan da zamu yi mu ce mun janye..." Tuni har hawaye ya fara zuba a idon Auwal, wanda ke kallon mahaifinsa garau da alamun rashin kwanciyar hankali bare kimtsa maganar da zuciyarsa ya kamata ta haifa, bakinsa kuma ya furta hakan ne kuma ya sa Innarsa ta sami sararin shiga maganar. "Wannan d'an ka yi wauta in dai ka san cewa yarinyar nan sickler ce, amma ka juya wa matsalolinta baya zaka aure ta... Muna zaune 'kalau ka kawo mana sickler dangi..." A yanzu ya sami ga6ar abin cewa wanda ra'ayin kansa da na zuciyarsa suka yi tarayya yana 'kokarin tsayar da hawayen ya tare mahaifiyarsa. 'Idan dai zan iya haihuwar da Rumasa'u, to lallai zan iya haihuwar sickler da wata mai lafiya wadda ba sickler ba ce..." Shi ma mahaifinsa da yake zazzafan mutum ne sai ya tare shi. "Idan Allah Ya hukunto hakan na tabbatar idan za ka haifi sickler goma da Rumaisa'u idan wata ce sai Allah Ya ta'kaita ka haifi hud'u..." Auwal kawai sai ya yi shiru ya ci gaba da shan shayin da ya fi kama da shan magani, 'kwalwarsa ta tsaya cak! Da 'kirkirar mafita ko ta 'kofofin da duk ransa ya raya masa har ya gama kushe masa aure da Rumasa'u tsab ya 'karkashe batunda da haramta aurem. Auwal dai bai tanka ba, har mahaifin nasa ya diga aya sannan cikin rashin hayyaci ya tashi ya fice daga falon. . Dan Aunty.GORAN DUMA 8 . . Tsawon daren nan ba zai iya dorar da wani abin kirki da ya yi ko lissafinsa ya yi ba dangane da yadda zai 6ullowa al'amarin, ya san dai ya gurji kukan da tsananin 'kauna da tausayin Rumasa'u ya haifa, kuma su suka hana shi hasala komai bayan ya 'koshi da ji a ransa duk tsanani ba zai iya rabuwa da Rumaisa'u ba. Sai 'karshen dare ya sami runtsawa saboda haka bai sami sallatar asubahi ba, 'karfe shidda dai-dai wayar Rumasa'u ta farkar da shi. Yana ganin sunanta kan wayar sai da 'kwalla ta taru a idonsa, ya daga yana kokarin gyara muryarsa saboda daskarewar bacci da kuma ta ma'ka'kin tausayinta da ya ma'kale maasa a ma'kogwaro. "Rumaisa'u" Muryarta tar ta ce "Duk wadannan gaibu ne Abba, babu wanda ya san abin da gaba zata haifa, kamar yadda ba mu isa za6ar abin da muke so mu 'kyale wanda tanmu yake hasashen hadari cikinsa ba. Da dan Adam na da iko akan za6in abin da yake so na matar da ta zarce Rumaisa saboda abin da nake mata ya fi so, shi yasa ban san ko wacce irin matsala ba a kanta, amma da yake na san ba dukkan abin da mutum ke so yake samu ba, tun bayan umarninka na jiya na kwana ina gwajin yadda zan iya rayuwar da babu Rumaisa'u. Na yi ta cin karo da gazawa, har ta fara barazanar keta min zuciya. Ban fitar da rai zan iya din ko kuma zan kasa ba, na san a biyu daya ce zata faru, ko in iya d'in in wanzu bisa tsarin da ka za6a min, ko kuma in gaza ta dalilin in bijire maka ba, wanda babu irin haka a tarbiyyar da ka ba ni... Abba kar ka damu da yadda ka ganni har in mutu in Allah Ya so ba zaka had'u da abin kuka ta silata ba..." Yanzu hawaye ya fara cin 'karfinsa, kuma shi ne ya tilasta shi diga aya ba don ya rasa abin cewa ba. Duk jikin mahaifinsa ya yi sanyi, sai kallon Auwal yake shi ma kamar ya yi hawayen, amma wata zuciyar na tuna masa siyasar Auwal ta dadin baki da sadaukarwa har ka yi masa abu ba tare da kana da niyyarsa ba, wannnan ne yasa ya daure ya ce. "Abin har ya yi zafi haka Auwal? Ba zaka iya fitar da yarinyar nan a ranka cikin ruwan sanyi da dalilin matsalarta a rayuwarka da ta 'ya'yanka ba?" Auwal ya muskuta da murmushin ya'ke alamar akwai magana fal a cikinsa, sai dai yadda zai furta ya yi girma, don haka ya hadiye ta kawai ya bi mahaifinsa da shiru, har mahaifin nasa ya gaji da jiran cewarsa ya nemi guri ya zauna idonsa akan Auwal. "Tun farko ka san Rumasa'u sickler ce?" Auwal ya kad'a kai, mahaifin nasa ya dora wata tambayar. "Wanne mataki ka dauka akan yadda za ku rayu tare, ko kaucewa yadda za ku haifi 'ya'yan sicklers?" Auwal ya jima kafin ya tattaro abin cewa. "Ta yi 'kokarin hana ni aurenta tun ranar da muka had'u na dage. Duk matsalolin da ka lissafo min da bakinta ta lissafo min su, amma ba su gigita ni yadda suke gigita ku ba... Da ta ga haka sai ta shawarce ni yin gwaji dan sanin makomar 'ya'yanmu, na amince a sannan amma sai na ga gwajin 6atawa kai lokaci ne da tanadar wa kai fargaba, don na ji a raina ko wane irin sakamako gwajin zai haifar ba zan iya barinta ba, saboda haka na ce ta bar maganar gwaji". Mahaifinsa ya jima cikin shiru yana jiya maganganunsa, kafin ya yanke hukuncin d ayake jin shi ne na 'karshe. "Gaskiya ta yi hange mai kyau saboda haka shawararta ita ce abin bi. Ka je ka yi gwaji idan akwai matserar 'ya'yanku sai ku yi aure, idan kuma babu, to ku dubi girman Allah ku ceci 'ya'yanku ta hanyar ha'kura da juna". Duk da Auwal ya ji maganar mahaifinsa da kamar maimaici kawai, ma'ana babu wani sassauci haka ya cije a ladabce ya gyad'a kai. "To na gode Abba". Ya m'ke kuma salin-alin ya fice ya shiga 'kwan'kwasa falon Innarsa. Auwal bai 6oyewa Rumaisa'u komai ba dangane da yadda suka yi da mahaifinsa da hujjarsa ta sanin kukanta nasa ne, kukansa ma nata ne. Tuni suka yiwa juna wannan al'kawarin na tarayya akan matsalolinsu dan nemo hanyar araka. Rumasa'u ta jima ba ta yi magana ba, ba dan rashin abin cewa ba sai dan saisaita maganar don gudun kada tayi muni a kunnen Auwal ko kuma ya zama wani mataki na karyar masa da gwiwa. "Kin 'ki cewa komai Rumasa?" Ya fada bayan ya gaji da jiran cewar tata. Ta gyara tsaiwarta ta 'kara jingina sosai da motarsa saboda tana jin jiri. Ta yi murmushin 'karfin hali ta ce. "Abin da Abba ya yi shi ne ya kamata Auwal, so ne tun farko ya ke runtse mana ido alhalin wani dad'in gushi ne kawai a cikin rayuwar aure, wanda ake 'kulla si domin kammaluwar iyali. Ya wajaba ne mu samarwa iyalanmu makoma ta gari, ba ya kamata ba Auwal". Shi ma ya yi murmushin 'karfin hali bayan ya ji a ransa kawai 'karfafa masa gwiwa ta ke so ta yi ba ainihin abin da ke cikin ranta ke nan ba, ya ce. "Kamar ke da Abba kuna mantawa ba a yiwa Allah wayo, ke kanki aya ce Rumasa'u, Innarki da Abbanki babu sickler ciki, amma suka haife ki..." Ta tare shi da dariya. "Ba 'kokarin yin wayo ba ne, 'ko'karin amfani da hankali ne, wanda Ubangiji Ya hore mu da shi dan za6ar abin da zai amfane mu da gujewa abin da zai cutar da mu, abin da ya faru da mu cikin akasi mun yarda daga Ubangijinmu ne ba tare da sakacinmu ba, sai mu yi fatan zamowarsa kaffa". Auwal ya yi zuru kawai yana kallonta sannan ya nisa ya ce. "Ban sna me yasa duk cikin lissafinku ba kwa duba uban yaran da samun su yake 'kila wa 'kala ba, sa ku kuka himmata sarayar da shi alhalin shi ne a hannunku. To zan fada miki abin d ana fada Abba jiya na kwana da 'kokarin lissafa yadda zan yi rayuwar da babu ke, na ji kamar numfashina zai yanke daga lissafin kawai ba tare da fitar da sakamako ba, amma dai ban cire rai daga rahamar Ubangiji ba, duk za6in da ya yi min ina fatan rahma da jin 'kanSa a ciki". Ta zuba masa ido, dauriyarta na kokarin 'karewa. Kasa gajiya da kalonsa da ta yi ne ya sa ita ma ta tabbatarwa kanta wa'ka kawai ta ke, amma tursasa kanta za6ar tsaka-tsakin al'amura, sai dai kuma ta kasa hana zuciyarta rauni da son nuna gazawa da ta tsaya kawai ga bayyanawa ta hanyar 'kura masa ido cikin hawaye. Haka suka tsaya ita kuka, shi hawaye, har daga 'karshe ya zagaya mota ya shige yana cewa. "Zo mu je asibitin". Ta yi saurin duba agogon hannnunta da ya nuna 'karfe sha daya da mintoci sha hud'u. Ta bude motar ta sunkuya a tausashe ta ce masa. "Bari na sanar da Hajiya". Ya yi saurin tare da fadin. "Rumaisa'u kar ki sanar da kowa matsalarmu fa, umarni ne da kuma kokarin kwantar da hankalinku ke da Abba zai kai ni gwaji, ba dan na yarda da iya raba ni da ke ko ya yi wani abu a cikin sonki ba. Ya kamata ki ri'ke wannan kada ki yi 'kokarin raba ni da kanki, son da nake miki mutuwa ce kawai zata iya raba ni da shi". Ta sororo cikin sanyin jiki tana kallonsa. Ta hadiye kwallarta ta ce masa. "Auwal wai me yasa ka damu da kira mana mutwa? Ai ba sai ka kirata zaka bayyana min kana sona ba,.." Ya tareta cikin kyalkuala dariya. "Me yasa ba kya so na kirata? In akiranta ne dan na sna ita ce mai YANKE 'KAUNA, duk yun'kurin raba mu da kuke ni dai na tabbatar ita kadai ce zata iya raba ni da son da nake miki. Amma na san ba ni da karfi ko dabara a cikin aurenki yadda Ubangiji Ya so haka zai yi". Ta murza yatsu tana dariya, ita ma ce. "Shikenan. In Allah Ya so ni da kai mutu ka raba". Ba ta jira cewarsa ba ta wuce. Ya bi ta da kira, ta tsaya ba tare da ta juyo ba, ya dan daga murya. "Na fa gaya miki kar ki fad'a". Sai kawai ta kad'a kai ta wuce tana dariya. . Allah sarki soyayya... Sai gobe in shaa Allahu. Dan AuntyGORAN DUMA ****9 Akwai wani lokaci da Alhaji ya sanya shi kai ta taronsu na masu cikon sankarar jini (sickle cell) ya jirata har aka tashi taron. A hanya sun taho yana faman cikarsa da batsewa, har ya fashe da cewa. "Inda za ka san ciwon shifcin gizo ne har a wata 'kungiya, wai dan tsabar lalacewar zamani ciwon ake wa 'kungiya, kowa ya san ba ciwon ne ya dame ku ba, wata hanyar neman kud'i kawai kuka mayar da ciwon!" Rumaisa'u ta yi murmushi tana kallon tagar motar kafin da kyar ta samo abin cewa. "Yaya Yusha'u kamar yin 'kungiyar zai fi rashinta amfani. Ni dai nan na 'kara min imani da godiya ga Allah wanda Ya halicce mu yadda Ya so ba dan 'kiyayya ba, sai dan Ya zamo jarrabawa a gare mu. Kawai dai ka yi mana fatan ya zamo kaffara". Yusha'u ya yi wani gajeran tsaki, sannan ya tsuke bakinsa. Shekararta ta 'karshe a B.U.K, Hafsat ta kammala N.C.E har ta fara aiki, mahaifanta sun dawo Abuja da zama. A wannan shekarar ne ta hadu da gwarzon masoyin da ta ke jin har duniya ta nad'e ba zata yi irinsa ba. Ba wai tana rasa masoya ba tuni, sai soyayyar ba ta wani nisa sabo rashin goyan bayanta, ko kuma in sun san matsalarta su kauce. Sun hadu a wata laraba ne tana tsaye a bus stop cikin B.U.K ner site tana jiran motar da zata kai ta old site, ita kadai ce tsaye a wajen, sai fama ta ke da ri'kon tafkekiyar lema (umbrella) a hannu saboda hadarin da ya fara d'aurewa, zai iya zubar da ruwa bagatatan, saukar ruwa a jikinta kuwa wani tushen tashin hankali ne da zai iya motsa ciwonta. Dai-dai wannan lokacin AUWAL ya zo giftawa ta gabanta da motarsa. Ta bi motar da kallo cikin tunanin yadda suke kwashe da Mominta a hutun da ya gabata. Wani Uziri na son tsaida

Chapter 4 of 21