Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels GORAN DUMA Na Maimuna Idris Beli. Ebook Publish by http://hausaebooks.cf Izan kuna bukatan wasu litttafan sai ku ziyarci shafinmuu na yanar gizo akan adireshi http://hausaebooks.cf Farkon littafi. . . Rumaisa'u wankan tarwadar mace matsakaiciyar tsawo da kiba, fuskar ta nada alamun hakuri da sanyin hali a wajen wanda ya karanci mata, amma mai rashin matsaya ga mutumin da ya cikawa kansa zargi a cikin mutane saboda rashin son maganar ta da karancin fara'ar ta. Ta na xaune a matsakaicin palon gidan su ita kadai, a tsakiyar palon bisa kapet tayi kaca-kaca da takardu. Ga wayoyin ta da na'urar kwanfuta(laptop) dake kapet, ga kuma robar ruwa da kwalin lemo a gepe. Wannan yasa ba sai an padi ayyuka ke caja gabban ta wanda fuskar ta da gabban suka kasa nuna gajia, watakila dan juria da son aikin har zuci. Can daya daga cikin wayan ta dake zube ta saki wata siririyar kara amma abun mamaki duk da haka sai ta firgita, ta dubi wayar da sauri kuma a tsorace xuciar ta na bugawa, duk da haka ta latsa sakon ya pito. A pili cikin ta Ya bayar da wani kuuu... Har sai da ta dan rankwapa na alamar ba a karar ya tsaya ba har da haipar mata ciwo. Ga abun da ke rubuce a cikin wayar '' yaushe ne kika shirya barin nunpashi na ya huta? Duk yadda kike jin aiki da dawainiya a rayuwa bana jin kin kama kapa ta, amma kin san wani abu? Mamakin yadda kike share al'amra na ma wani tapkeken babi ne a kundin da na ware miki, wanda ko wannan babin aka barni dashi ya isa abin wahalar da xucia. Rumaisa'u bayyana min siririn ki wanda ya rike ni na kasa ampani da Karpi wajen maganin ku ke da zucia ta! Ware min ko sakan goma ne daga lokutan ayyukan ki kiyi min wannan aikin Rumaisa. Daga MAHAUKACIN MASOYI. Tayi wurgi da wayar kamar wadda ta galla mata cixo a bayan ta, bayan ta kammala karanta sakon, tana satar kallon wayar, san nan ta koma satar bin palon da kallo, musamman jikin labulaye, harshen ta pal ambaton Hasbun Allahu wa ni'imal wakil, ta dora da padin '' A uzu bi kalimatuLlahi tammat min sharri makhalak '' Duk illahirin gabobin ta sunyi sakayau, babu nauyi tamkar idan an yanketa jini baxai bullo ba saboda tsoro da wasi wasi Tsawon piye sati hudu kenan tana pama da sakonnin wanda ke Kiran kansa da MAHAUKACIN MASOYI mutun da a yanxu ta para shakkar mutun ne ko aljan, mutun da aljan din na xahiri ko kuma ifiritai ne (hackers) suka hauro layukan wayoyi kamar yadda akan same su a yanar gizo? Cikin zarginta uku kowanne ta canka babu dama a cikim sa, in mutum ne ta wanne bututun yake hango halin da take ciki a lokacin da yake turo mata sako? Kamar yanzu da yayi maganar cakudewar ayyuka. Idan aljani ne ma wani bakin tashin hankalin ne dan babu ta inda aka gwamutsa mu'amalar mutane da ta aljamu bare har a gayyato musu batun soyayewa a irin haka. Zargin 'hackers' din ne ma mai dam sauki wai idan ta kawar da kai ga rashin yawan bayyanarsu a layukan waya ta wannan sigar, ko kuma lissapin nemo manuparsu a kanta da suka dame ta ita kadai... Wata dattijuwar mace para mai tsawo da kiba , tayi sallama ta shigo palon, da sauri rumaisau ta gyara sahu ta hadiye maitarta ta amsa sallamar matar, purkarta da gabobinta suka nuna ladabi, tana murmushi ta amsa sallamar matar mai alamin zapin nama ta dubeta tace, '' Rumaisau ki saki aikin nan ki huta haka,ga pura mai kyau can Alhaji ya shigo da ita, kije ki dama kisha... Rumaisamu tayi kokarin tattare tashin hankalim da take ciki tabawa cikin ta ajiyarsa, ta tare matar da rawar murya dake kokarin komai ya zama ba komai ba, ''Oh Abba ya shigo Hajia? Hajia tayi murmushi ta amsa mata tun da hamida ta bar mu gidan ya zame mana kamar hurumi, kirikiri alhaji ke nuna pipiko tsakanin mu, ni kaina sai na zage nake sanin shiga da pitar sa. Rumaisau tabi wayar ta da kallo tana murmishin hadawa zuciyar ta ayyuk biyu, tunanin gudan jinin ta Hamida, da kuma tausayin ta a matsayinta na mace mai rauni, wanda kuma zata tsaso kila cikin ratuwar da tapi tata wadda take tapia a cikin ta yanzu muni. Sai kawai taji hawaye na son cika mata ido, amma ta dage ta dadiye, ta cewa hajia '' to hajia wannan dai tsakanin ku ne'' hajia ta bar amsawa Rumaisau maganarta tabi ruwa, saboda damum kanta da nazarin rumaisau'un da take sonyi wanda puskar ta ke son karyata abun da zuciyarta ke kokarin bayewa, amma data hada nazarin nata da wasu daban sai ta yi saurin sharewa gudun batawa kai lokaci, ta jima da sanin rumaisa duk inda ake neman mutun mai kawaici ta cika mizami, mawuyacin abu ne kaji korapi a bakin ta duk yadda ka kai ga kwarewa hilarsa wani ya amayar da abun da zuciyarsa ta boye. '' baki da bukata ko ta neman addu'a ce daga gare ni!'' hajia ta sami kanta da furta wa rumaisau cikin tsura mata ido, sai rumaisaun ta dan diririce saboda pargabar ko tayi wani abu da ya dago halin matsin da take ciki. Ta hau hada takardu tana cewa '' hajia kiyi min izinin gobe na kai rubutun nan abuja nayi submiting. Hajia taci gaba da kallon ta, kallo mai cike da tuhuma. '' rumaisau kwanan ki nawa da zuwa Abuja kuma tunda kike rubutun nan kin taba kai shi takanas? Ji nake ta Email kike tura musu?'' a ladabce Rumaisau ta shiga kokarin kare kanta. ''akwai matsala ne hajia, kinga ban gama bugawa ba kuma ka'ida gobe laraba mujallar ke pitowa. Ba wai lallai ya zama sai nakai din ba,amma dai ina neman alparmar zuwan hajia saboda muhimmanacin rubutun'' hajia tayi siririyar daria tana ci gaba da yi mata wani irin kallo, wanda rumaisau ta kasa daurewa har sai da hajia ta ci gaba. Ko dai alkunyarki ke son gazawa ba zaki iya rashin Hamida ba ko? Ni dai abun da zuciata ta karantar dani ke nan, da sauri rumaisau ta tareta cikin zaro idaon bijirewa batun hajiyar tace ''ah! Hajia to na pasa zuwa tunda kin zargi hakan.. Wallahi ko kadan ba dan hamida zanje ba hajia. Nan da nan hajia ta tareta da na yarda daje rumaisau zan kuma sanarwa Alhj amma da sharadin zaki tashi yanzu ki nemi wani abu kisa a cikin ki. Cike dq jin dadin kulawar da hajia take mata ta yalwata para'arta da murmushi tace "ai na bari tuni tun bayan pitar hajia ta janyo wayarta a gajiye tankar wadda tayi gudun shekara ta kasheta, ta jepa akan kujera samnan ta pice debo purar da hajia ke mata tayi. Ta kori hataniya da rudin wannan duniyar da tilastawa kanta shan purar sosai har ta gamsar da ita, tayi wamda ta sallaci Isha'i, sannan ta zauna azkar din yammaci da bata samu damar yun sa a kan lokaci ba, sai tayi shi a yanzu tana mai nutsuwa da kaskantar da kai ga Mahalicci. Abin da ya karpapa mata gwuiwar isa gadon baccinta da wuri tare da tsammanin zatayi barci a nutse shine a zacin da tayi na kashe waya tare da yunkurin barin kano a gobe dan ganin gudun ruwan MAHAUKACIN MASOYI , wayar da yake kiran ta ta kashe, garin kano idan ma kyamarar sirri (CCTB) ya makala a garin to ta bar shi, cikin kwana biyu kuma sai ta gani ta ina zai leko ya rikitata? ABUJA karpe biyu da rabi na rana ta pito ofishin da jaridar Aminiya dake jabi da komawa masaukinta wajen Innarta a anguwar wuse. Duk a rikice take tun saukarta Abuja taji wata bala'in rashin nutsuwa ya mamaye ranta har yake bayyana a gabban ta, wayi ayyuka. Misali. Tana sauka bus din da ta kawota garin a matsayinta na wadda ta taho Abuja a gaggauce, dan zuwa opis maimakon ta dauki shatar motar da zata kaita Jabi kawai sai ta buge da daukar wadda zata kaita gidansu Wuse cikin wasiwasi, a cikin tadi din ne ta budo naurarta mai kwakwalwa ta lalubo rubutunta tana nazari da shawarar ta tura shi kawai ta Email din ta wuce gidan ta kwanta, anan kuma ta lalubo Moderm dinta cikin jakar sai ta tarar ta baro shi a kano, nan take ta yanke shawarar tsayawa wani kataparen kantin harkokin sadarwa da ke nan titin da zai sada ta da wuse daga Utaho kawai, ta tsaya anan ta tura rubutun, ana isowa Annur ta yiwa direba umarnin ya tsaya anan ta shiga ta pito. Ta kwashi i laptop tayi ciki , kataparen waje mai kamar komai da ruwan ka a bangaren sadarwa, wayoyin hannu , layukan waya, katin wayam kwanputa da sauran tarkacen da suka dangance ta, modem din da ta baro a gida ma wancan zuwan nata ta saye shi anan, haka dai gurin yake bangare bangare ko ina da abubuwan da ya kunsa. Yau tana shiga bangaren cafe ta tunkara, amma kamar wadda tazo daga kauye duk kaparta rawa take sai sassarpa take har ta isa inda ta nupa. Ba wani abu ne ya janyo hakan ba sai gain yadda kamar kowa a wajen ya zuba mata ido ne, da yake yawancin katangar dake tsakanin bangarorin ta gilas ce, kamar duk ma'aikatan wajen sun doro hankalinsu akanta. A gajiye ta karasa wajen ta zube a kujera tana numparpashi tamkar wadda tayi gudun pampalaki, ta yar da jakar naurar gepe ta zube wayoyinta akan tebur, mai kula da bangaren ya dago kansa daga printer da yake zaro wasu takardu yayi mata wani kallo shi ya tsinke tunanin ta, ta shiga zargin ko wani mummunan abu ne a jikin ta da mutane ke binta da kallo haka? A dabarance ta para nazarin shigarta , tana sanye ne da bakar after dress mai sheki da abon shudayen kananan dumatsu kalar riga da siket din material dinta na ciki, kanta nade shi da mayapin rigar kuma da yake ba zata iya putowa a haka ba sai ta kara da nade kapadar ta da lallausan mayapi mai matsakaicin girma shi ma shudi, jakarta da takalmin ta duk shudaye , idon ta sanye da siririn parin gilas, a zatonta ko ba ganin idon ta ba, ganin idon kowa ma babu kauyanci ko digo a cikin shigarta, duk da haka bata gamsu ba sai ta saci ido ta bude jaka da sunan lalube ta kalle puskarta tsab ta cikin jalar komai pes hatta hodar puskarta da man lebe (wetlips) babu abin da ya gigita su. Ta zuge jaka tana sauke ajiyar zucia cikin tsananin tashin hankali wanda ya karu lokaicn da ta lura mai wajen ya kapa mata ido ya pada da karpi laa kamar barauniyar da tazo tayi sata jiya... Lol. . GORAN DUMA 2 . . Ta zuge jaka tana sauke ajiyar xucia cikin tsananin tashin hankali wanda ya karu lokacin da ta lura mai wajen ya kapa mata ido kamar barauniyar da tazo tayi masa sata jiya yau ma ta dawo. Sai bakin su ya hau rawa shi da ita. '' madam... Madam.. Me kike bukata? Ita kuma tana rawar bakin cewa don Allah... Zan tura wani aiki... Ta na'urar kwanputa, ta me zan tura... Bai iya amsa mata ba sai gyada kai kawai yake kamar kadangare yana kallon ta kai tsaye , hannunta sai karkarwa yake ta parke jakar system dinta shi kuma da sauri ya karaso ya tura mata foot stool waiko zata dora kapa. Da wasa ba zata dorar da abun da tayi a naurar kwanputa ba, musamman da shi mai wajen ya dauki waya yana magana da wani harshe da bata samshi ba alamunsa kuma na nuna hankalinsa na kanta. Ba a dauki ko cikakken minti daya ba sai ga wani matsashi ya shigo mai matsakaicin tsayi da kaurin jiki puskarsa na da alamun para'a amma a halin yanzu kai tsaye ba za a yi masa passara ba , ya nemi guri ya zauna bayan sun gaisa da mai kula da wajen sai ya nemi kujerar da ke puskantarta ya zauna yana satar kallon ta, tana latselatsen keyboard, can tayi namijin kokarin dagowa suka dubi juna ido cikin ido shi ya kawar kamar a razane ita kuma ta hade puska. Ta nuna masa TV plasma dake makale a sama tace. '' bawan Allah kaga abun kallon can.' yayi pirgit ya dubi talabijin din sannan ya dube ta muryarsa na rawa yace ina... Patan dai ba tsarguwa kikayi ba? Ya mayar da kanta rai a bace tana matsawa siririn hancinta hura iska. Alamar dai haushin ta ji, amma bata tanka ba. Shi ma ya kawar da kai yana cewa batawa kai lokaci ne kayi abun kallo kace baza a kalle ka ba. Ta dago da sauri ta dube shi amma ba ita yake lallo ba balle ko a puskarsa ta karanci abun da yake nupi. Ta kokarta tace ko? Ya juyo cikin kada kai haka nace. Saboda haka kallon naki yapi kallon wannan akwatin da kike nuna min kaye... Yanayin yadda yake magana duk kwakwalwarta ta kasa gane inda ya dosa , puskarsa babu walwala bare ayi zargin irin mazan nan ne masu latselatsen yanmata. Tsam! Sai ta tattara kwanputarta ta mayar a haka ta zuge jaka tana cewa bari na bar muku wurin ko? Kila kuyi abin da zai ampane ku, dan kallona babu ma'anar da zai baku.. Malam nawane kudina? Ta mike rataye da jaka tana duban mai wajen ya girgiza kai kamar a darare me kika yi na kudi? Kije kawai . Ba ta ko tanka ba ta juya ta pice kaparta na hardewa kowa na damuwa da kallon ta har ta pice cikin sassarpa. Bata sami direban da ta bari cikin mota ba, sai kawai ta rungume hannu ta jingina da motar cikin rudani tana zuba idon ta inda zai billo. Cam sai gashi da mujalla a hanu cikin zapin nama ya bude motar yana neman apuwar ta , ta hango wannan gajeran mutumin da yake kallonta yapi talabijin yana doso inda suke. A hanzarce ta cewa direna sauri mubar wajen nan, cikin direba ya dauki wani kugi da yasa shi kasa bin umarninta yanayin yadda tayi maganar ya sa yayi zargin babu gaskia a tare da ita, tsoro ya ke ko wani abun ta sato tasa shi taka sawun barawa. Yakai ta ya sauke lambar motarsa kuma ta shiga kundin masu laipuka. Saboda haka kawai sai yaki tapia har gajeren mutumin ya karaso ya mika mata wayoyinta ta windon motar. Madan sanyin AC wajenmu ya sabbaba miki mantuwa.? Ta karba tana mayar masa da raddi haka ne musamman da yake daga kauyen mahudar rana na pito ba. Ya juya ya koma da karamin murmushi a puskar sa. ''Allah ya baki hakuri idan gaskiar tawa zapi tayi miki. Direba yayi ajiyar zucia ya tashi motar yana cewa kinga gara ma da muka tsaya. Ko kala bata ce masaba har suka hau titi, sanan tayi masa umarnin ya kaita opishin jaridar Aminiya kai tsaye ta gyara shirmen da tayi. Acam kuma ta watsar da dimuwarta tayi abin da ya kamata, karpe biyu da rabin nan ta pito da dokin zuwa gida don samun nustuwar zucia amma dai ta san wahalar da kai ne dan gaba daya tsarge take, sai kissipawa kanta take wani na biye da ita, bata jima bakin titi ba ta samu mota kuma da yake tsakiyar rana ne titin babu cunkoson ababen hawa, sai nan da nan tapiyar tayi musu sauri suna kan Berger flyover kiran innarta ya shigo wayarta da ke kunne ta dag cikin muryar ladabi tace Momi ina hanya kusa da isowa tana sauke wayar sai tabi ta da sabon sako hankalin ta kwance ta bude shi, dan a amintacciyar wayarta sakon yake, wayar da bata taba hadata da gigitaccen sakon Mahaukacin masoyi ba, saboda haka karsashinta ta para karantawa.'' Rumaisau garin Abuja ni'imtaccen gari ne ma'abocin dauke kewa da gadar da nutsuwa tankar yadda salihar puskarki take, amma yau na shiga rudani da nake ganin puskarki da ayyukanki a gigice. Kila kin halarci Abuja ne bisa radin kanki ban kuma cire tsammanin dan ki samarwa kanki nustuwa bane, amma yaya kika hana zuciyarki da gangar jikinki hakan Rumaisa? Laipin me wayarki tayi kika kashe ta? Inajiran amsa. naki MAHAUKACIN MASOYI. A Uzu bi kalimatuLlahi Tammat min sharri ma khalak. Wannan adduar ta karabto tana juya wayar duk da kuwa tayi mata nauyi a hannun, a yau kam taji a ranta ba bil'adama bane mahaukacin masoyi ba, kuma ba hackers bane duk yadda ake yi yana daga shaidanun aljanu da zata tashi tsaye neman tsarin Allah da shi har ta shiga gida cikin wannan ruwanin biyu take na mahaukacin masoyi da kuma na son canko dalilin da yasa ta zama madubin mutane a yau. Bakinta da Ayatul Kursiyu har da wattaba'u ta shiga gidan, innarta ce kadai a palon tana mata marhabin amma sai ta wayance da matsuwar shiga toilet, inda ta ajiye jaka a palo cikin sauri ta shige bandaki. Tayi tsaye gaban katon madubi tana kallon kata daga sama har kasa iyakar ganin da kwakwar juya bayanta ta kallo bataga abun kushewa ko abun kayen da za a damu halittarta da kallo haka ba, wannan yasa taji tausayin kanta ya mamayeta, duniyar nan kamar ba ta karbeta ba, duk inda ta shiga sai rayuwa ta zame mata kwado, ta rasa abun da take so ko kubucewarsa in ta samu, ko kuma puskartar kiyayya daga wanda rayuwa ta yarda su rayu tare. Da kyar ta rarrashi kanta yayin da zuciyarta ta samu dan wani sarari sakamakon jiyo kawar diyarda Hamida. Tayi alwalar sallar la'asar ta pito palon innarta da mai aikin dauke da kyakkyawa hamida yar kimanin shakara biyu da rabi, sa'a mai aiki ta dire Hamida da sauri tana cewa Yauwa tapi da gudu ki yiwa momi oyoyo. Kamar Hamida ta gane manuparta ta tahi a guje ta tari Rumaisau wadda kunyar idon tata uwar ya hanata tarar hamidan, sai ta bige da rike mata hannu kawai, idon ta akan sa'a tace. Sa'a ta amsa. Muna ciki uwar dakina daga wasa jiyo Hamida tayi bacci kawai sai kwantar da ita wajena. Suka karasa kujera Rumaisau ta zauna tana yar daria, yanxu wannan katuwar yarinyar kike goyawa Sa'a? Sa'a tayi daria tace ai shi yasa nace miki wasan goyo. Duk sukayi daria har innar Rumaisau wadda hankalin ta ke kanta, tana yi mata wani irin kallon tausayi. Sa'a ta mike tana cewa dan Allah dora yar nan a cinyarki taji sanyi kin kama kin wani rike mata hannu kamar yar awo, wannen abinci zan kawo miki? Ba ni ruwan zapi kawai, wato ta share korapin sa'a a parkon maganarta. Momi ina wuni, mun same ku lapia? Momi tayi murmishi irin na manya masu son karantawa kai korapi tace lapia kalau rumaisau yaya ayyuka? Taki duban momi kai tsaye saboda tsarguwa da tayi da kallon da momin take mata ta amsa AlhamduliLlahi momi, yaya Abba yana lapia? momi ta amsa lapiyarsa kalau ya halarci taron karawa juna sani a lagos sai jibi zai dawo ranar da zaki tapi kenan, kila ki dan jira shi ko? Tunda na san da sapiya zai dawo. Da sauri Rumaisau tace ai na pasa kwana biyun gobe da sape zan koma... Nan ma sai momi ta bita da kallon nazari amma sai ta kasa cigaba da yi mata kawaici. '' rumaisau kina tare da wata matsala ne? A dan gigice Rumaisau ta para girgiza kai A.a momi, me kika gani? Kai tsaye momi ta amsa puskarki na nuna babu nutsuwa a cikin ta, yakenki na nuna karpin halinki kawai, hajia ta sanar min kwana buyi kika ce mata zakiyi, yanxu kina dira kince da sanyin sapia gobe zaki tapi me ya kawo wannan sauye sauyen ko kina puskantar wata barazana ne? Rumaisau ta daddage ta bayyanar da karpin halin ta a puskarta da muryarta tace babu komai momi, wani aiki ne zai mayar dani kano a geben wanda ban san da shi ba sai da nazo yau, momi ta rausaya kai gepe cikin saduda ba tare da rai ya so ba tace ai shike nan idan hakane wannan aikin ba karami bane kamar yadda kika pada mana kapin para shi, in dai kuwa ojan-ojan din tapiyetapiye za su dinga padowa cikin sa ai yapi karpin karami rumaisa u... Rumaisau ta tare innarta da daria mai sauti. Momi bai canja ba daga yadda na pada muku ni dai kuci gaba da yi min adduar patah alkhairi a dukkan al'amurana sanyaye momi tace shikenan Allah Ya yi miki albarka, Ya yi miki katanga da kuncin dunia dana alkiyama. Cikin murna da parin ciki ta amsa da Aamiin na gode. Momin tace da ita to dauketa taji duminki mana wata kila ma kewar ganinta ya kawo ki.. Raimaisau ta sa hannu ta dauki Hamida tana daria tace zolayata kawai kike momi yarinyar da ta pi sonku dani zan batawa kaina lokacin zuwa ganinta takanas? Suna daria su duka Sa'a ta shigo da parantin kayan ruwan zapi. 25/12/2012 ratar kwanaki goma sha hudu aka samu da zuwanta Abuja cikin kwanakin nan duk yadda mahaukacin masoyi ke son muna mata hatsabinbancinsa ta hanyar sakonninsa ya muna mata kwarewarsa a wayoyinta biyu, ta kala-kalar tsoro da hasashe babu wanda bata gayyatowa zuciyarta ba har idan abun yayi tsamari sai ta kashe wayoyi duk lokacin data kunna kuma shayar da ita tsoro da mamaki a tsarin kalamansa. Wannan pargaba da tashin hankalin suka dinga motsa mata larurarta ta hawan jini da ta gamu da ita wasu shekaru da suka wuce, abin boyewar ya zamar mata biyu, wato boye barazanar mahaukacin masoyi da take puskanta da kuma boye cutar da barazanar ke haipar mata gudun kada ta tashi hankalin iyayen ta da marikanta. Cikin dabara take zuwa asibiyi ganin likita haka zalika cikin dabara take shan magungunan ta, akwai wani ciwon nata mai hadari da ta taba haduwa da shi na rudewar kwakwalwa da gazawar wasu sassanta a cam lokacin baya. Paruwar wannan rudani da motsawar hawan jininta ya sa likitanta ya bata shawarar ta rika kwantar da hankali da bawa kwakwalwarta hutu saboda gudun motsawa wancan ciwon. . GORAN DUMA 3 . . Likitanta ya bata shawarar ta rika kwantar da hankali da bawa kwakwalwarta hutu saboda gudum motsawan wancan ciwon. Sanin girman hatsarin ciwon a tare da ita yasa take son watsar da captar mahaukacin masoyi ta dauke ta miyar da babu gishiri, amma sai hakan ya paskara wani lokacin sai ta zabi kashe waya in ta kashe kuma sai ta rasa abun dauke kewa ko sadarwa tsakanin ta da mutane, 30/01/2013 yau laraba da dare wajen karpe tara, ta gundura da kallon talabijin sai ta dauko na'ura mai kwakwalwarta ta lika modem ta hau yanar gizo kai tsaye ta nupi kapar sada zumunci ta facebook cike da dokin shiga dandalin duniyar marubuta da wata kawarta marubucia mai suna kamshi ( Hawwa Abubakar Lawam maiturare) ta gayyace ta. Dandalin duniar marubuta na fb cike yake da daruruwan marubuta da makaranta ana ta harkokin arziki tare da kuma abubuwan karuwa da na nishadantarda, tana shiga taci karo da wani rubutu da marubuci Muhammad Lawan Barista yayi mai take '' zaman 'ya 'yana nake'' duk lokacin da wani sabani ya shiga tsakanin Mamuda da matarsa Aliya sai ta bude baki ta ce masa Mudi nipa zaman yayana nakeyi in bandan su ba Wallahi da tuni ka manta da ka taba sanina, abun na damunsa kwarai tun yana ji yana hadiyewa abun a ransa yau dai ya yunkura ya sanar dani yana kuma jira yaji daga gareni shin matar tasa tana sonsa kenan? Kuma wane mataki ya kamata ya dauka akanta? Ni dai ya rantse min yace babu wani abu da yake mata na cutarwa sai dai ma tsabar kyautatawa ,wacce shawara ya kamata na bashi? Da dokinta ta shiga rubutun tana juya abun a ranta '' zaman yaya kamar wata kalmar ado ce ko ta panshe takaici a bakin mace lokacin da sabani ya shiga tsakanin su da mazajensu, duk da

Chapter 1 of 21