dariya har ya gaji sai ya hade fuskanci ya dubi sazirat da ukashat yace, ku tashi kuke kuyi shiri yanzunnan zamu kama hanya mu tafi izuwa birnin Darul husuf domin cika burinmu. Tabbas dan uwanka Uzaifat sai ya hallaka a cikin wannan daji na mashaarul kais, ita ma Lafirat nasan cewa tuni wannan maridi ya gama da ita. Hakika yanzu ne muje da cikakkiyar dama, wacce zamu iya tafiya mu ci birninsu da yaki ba tare da mun fuskanci wata matsala ba.
Koda jin wannan batu, sai ukashat da sazirat suka mike zumbur cikin murna suka nufi hanyar fita daga cikin fadar. Har sunje bakin kofar sai ukashat ya juyo ya dubi sarki shaaran yace, ya shugabana me zai hana yanzu ka duba mana a cikin madubin tsarin ka mu ga halin da birnin Darul husuf ke ciki.
Nasan halin mahaifina yana da wata irin baiwa tayin mafarki bisa duk irin abinda zai same shi. Babu mamaki a halin yanzu tasan da zuwanmu, kuma ya dauki mataki akan hakan.
Koda jin wannan batu, sai sarki shaaran ya tuntsire da dariyar mugunta, sannan ya tako kafafunsa yazo daf da ukashat ya tsaya ya dafa kafardarsa, yace, kwantar da hankalika ya kai sarkin Darul husuf na gobe. Ina tabbatar maka dacewa, duk irin sihirin da sarki uwaisul karni zaiyi, sai mun sami nasara a kansa domin abin dogarona ya bani sa'a. Abinda nakeso da kai kawai shine ka tabbatar da cewa ka tone wadannan layu guda hudu da aka binne a kasar katangun birninku kafin mu fara Yaki dasu. Ka sani cewa a duk sa'adda na yi yunkurin ganin abinda ke faruwa a birninku, sai mudubin tsafina ya fashe nayi asararsa saboda karfin sihirin mahaifinka.
Sa'adda ukashat yaji wannan batu, sai yayi shiru bai ce komai ba, ita kuwa sazirat sau ta kama hannunsa ta jashi suka fice daga cikin fadar da sauri suka wuce izuwa can harabar gidanta, inda suka shiga shiri da kimtsawa domin gagarumin yakin da zasu tafi.
Shi ma sarki shaaran sai ya shiga hada dakarunsa aka rinka fito da makaman yaki iri iri ana rabawa dakarun, sannan aka yi ta shirya dawakai da guzuri ba adadi. Idan mutum ya ga yawan dakarun sarki shaaran wadanda zasu tafi wannan yaki da kuma yawan dawakan da aka ta Nada da guzuri, dole ne ya cika da mamaki, domin an kashe dukiya mai tsananin yawan gaske.
Wannan shine mugun tanadin da sarki shaaran sukayi, abinda basu sani ba shine abokan gabar tasu ma sunyi shiri, sun taho gareku saboda haka sai dai a hadu akan hanya a gwabza kazamin yaki da za a fidda raini mai sa'a ya cika burin sa.
* * * * * *
Al'amarin yarima Uzaifat kuwa, lokacin da ya kunna kai cikin dajin mashaarul kais yana neman ruwa, sai ya shafe sa'a guda bai ga wani tafki ko koramaba, al'amarin da ya dugunzuma hankalinsa kenan ainun, saboda tunanin halin da ya Bari Lafirat a ciki, don haka sai ya kara kaimin tafiya, har ma yana gudu gudu yana waige waige ko zai hango rafi ko korama.
A wannan lokaci Uzaifat ya ma manta da cewa a cikin dajin mashaarul kais yake, dajin da Lafirat ta basu labari cewa, akwai wadan su muggan tsuntsaye a cikinsa manya manya masu tsananin karfi da hikimar kai hari. Uzaifat yaci gaba da gudu yana waige waige har tsawon wata rabin Saar.
Kwatsam ba zato ba tsammani sai ya hango wata babbar fadama a gabansa ruwa na ta gudu a cikinta. Cikin tsananin farin ciki ya karasa cikin fadamar wacce ruwanta ke kwararowa daga sama takan duwatsu. Da shigar Uzaifat fadamar sai ya tsuma salkarsa a cikin fadamar da nufin ya cikata taf da ruwa, sannan shima yasha ya koshi. Kwatsam uzaifat yaji wata irin gagarumar iska kafin ya dago kai yaga ko menene sai kawai yaga wadansu irin jibga jibga tsuntsaye guda biyu dai dai kansa.
Tun da Uzaifat ya zo duniya bai taba ganin irin su ba. Kafin Uzaifat yayi wani yunkuri tuni tsuntsayen sun cafi kafadunsa sunyi sama da shi, sun luluka. Uzaifat ya yunkura da nufin ya zare takobinsa daga cikin kufenta, amma sai yaji ya kasa motsa hannayensa duka biyun, sakamakon mugun rikon da tsuntsayen suka yi Masa da kafafunsa, kawai sai ji yayi yana ta wutsil wutsil da da kafafunsa, amma babu mafita ko dabara. Koda ganin haka, sai Uzaifat ya saduda ya zubawa sarautar Allah ido kawai yana jira yaga inda tsuntsaye zasu kaishi.
Sai da tsuntsayen suka yi doguwar tafiya da Uzaifat a sama, har gaji likis yaji kamar kafadunsa zasu gutsure, sannan tsuntsayen suna ido kan wani dogon katon tsaunin wanda akan sama akwai wadansu manyan duwatsu. Kwatsam sai Uzaifat ya hango wata babbar sheka ta tsuntsayen cike da jira jiran 'ya'yansu.
******""""********"""""''**
Najibullah Muhammad 🥷🥷
*******"""******"""*****
Su kansu 'ya'yan tsuntsayen girman su abin mamaki ne, domin ko wanne dayansu ya kai girman katuwar damisa. Koda 'ya'yan tsuntsayen suka hango iyayensu dauke da Uzaifat a sama sai suka kama tsalle suna kokarin cafko Uzaifat tun gabanin a sauki masu da shi kasa.
Nan taje Uzaifat ya gane cewa wadannan yayan tsuntsayen yunwa suke ji, don haka da zarar anjefashi cikin wannan Sheka zasu dasa masa wawa su cinyeshi. Koda fahimtar haka sai hankalin Uzaifat ya dugunzuma bai san sa'adda ya kwarara kabbara ba yana mai neman taimakon Allah.
Faruwar hakan ke dawuya sai tsuntsayen suka saki kafadun Uzaifat ya rikito daga sama zai fado cikin shekarsu. Cikin hanzari Uzaifat ya zare takobinsa, ai kuwa yana fadowa cikin shekar sai yayan tsuntsayen suka yanyameshi zasu cinyeshi.
Shi kuwa sai ya hausu da sara da suka ba kakkautawa, ya zame musu alakakai suka kasa cinyeshi, shi ma kuma ya kasa hallakasu domin duk sa'adda ya sari jikinsu sai ya ji kamar dutse yake karta har tartsatsin wuta ne ke tashi. Su kuwa iyayen tsuntsayen da ke sama koda suka ga abinda ke faruwa tsakanin Uzaifat da yayansu sai suma suka yo kasa suka rinka kaiwa Uzaifat mugun farmaki don yayyagashi.
Nanfa Uzaifat ya shiga cikin mugun hali, domin ana kawo masa hari ne ta sama da kasa, ya rasa inda ya kamata yafi bada karfinsa, domin duk ta bangaren daya sakwa sakwa nan da nan zai hallaka.
Haka dai aka ci gaba da wannan gumurzu har tsawon sa'a guda tsuntsayen kai masa hari da bakunansu da kafafunsu yana gocewa, kuma shi ma yana kai musu sara da suka da takobinsa. Nan fa gajiya ta fara riskarsa har tsuntsayen suka fara samun lagons ya zamana cewa sun fara masa raunika a jiki, jini na zuba. Tun Uzaifat na tsaye sai da ya fara durkushewa kasa yana mikewa, a sannane jiri ya fara dibarsa.
Baiyi aune ba, daya daga cikin su yayi masa wata muguwar mangara da fukafukinsa nan taje ya fadi kasa magashiyan yana mai ganin dishi dishi, kawai sai yayan tsuntsayen suka sake yo kansa gaba dayansu cikin wani irin zafin nama Uzaifat ya kwalla kabbara ya sake mikewa ya kuma tararsu aka ci gaba da fafatawa, wannan karon sai ya fara karanta wata addu'a a cikin zuciyarsa cikin ikon Allah kuwa ya fara samun nasara akan su ya fara yi musu rauni a wannan karon duk wanda ya sara sai dai kaji karar ballewar kashi kasss! Koda ganin wannan nasara da ya fara samu sai ya kara zage dantse ya ci gaba da kabbara yana saransu da takobinsa, koda ganin irin barnar da Uzaifat yaje musu sai suka tsorata da shi suka fara baya baya amma kuma duk da haka basu fasa kawo masa hariba.
Ana cikin wannan gumurzu ne Uzaifat yayi wani irin yunkuri cikin shammace na bazata ya daka tsalle sama ya sare kawunan iyayen tsuntsayen atare a lokaci guda suka fado kasa suka kife matattu, tamkar giwaye biyu sun fadi.
Koda ragowar yayan nasu suka ga abinda ya faru ga iyayensu, sai suka nutsu suka koma gefe daya a cikin shekar tasu suka noke aka cigaba da kallon kallo tsakanin su da Uzaifat, ya zamana cewa, su basu afka masa ba, shi ma bai afka musu ba. Jima kadan sai Uzaifat ya koma gefe daya ya zauna yana haki, sakamakon tsananin gajiyar dake tare da shi. A sannane kuma ya bude jakarsa ya fiddo magani ya shafa a jikin raunikansa.
Bayan ya sami nutsuwa, sai ya mike tsaye ya leka kasan shekar da yake ciki. Koda ya ga nisan dake tsakanin saman tsaunin zuwa kasa sai hankalinsa ya dugunzuma ya rasa abinda ke masa dadi, domin bai ga ta yadda zai iya sauka kasan ba, do ko igiya zai daunra ya bi sai ya shafe sama da sa'a goma ya na sauka kasa, tabbas bazai iya jure hakan ba, ba tare da ya gaji ba ya saki igiyar ya hallaka a banza ba.
Duk wannan nazari da Uzaifat ke yi yana lura da wadannan ragowar yayan tsuntsayen kuma yana ruke da takobinsa, jira yake kawai yaga sun yunkuro masa ya gama dasu. Uzaifat ya sake komawa ya zauna ya shiga tunani mai zurfi cikin tsanani damuwa da tashin hankali. Abu na faro dai yanzu bai dan dabarar da zaiyi ba ya sauka kasan wannan tsauni ba. Abu na biyu, bai san halin da Lafirat da Abul shaja'a suke ciki ba a yanzu. Shin kinshirwa ta zamo ajalinsu ko kuwa wani balai ya afko musu?
Koda gama aiyana haka, sai zuciyar sa ta karaya, ya tabbatar da cewa, yana cikin tsaka mai wuya . idan ya ci gaba da zama a cikin wannan shekar tsuntsaye har ya kuskura barci ya sace shi, to tabbas wannan tsuntsaye cinyeshi zauyi, tunda suma a cikin balain yunwa suke. Me ya kamata yayi? Shin zai karasa kashe ne? Idan ya ka shesu ya zaiyi da gawarwakinsu? A yanzu haka ma gawar iyayensu da ta sauran yan uwansu ta kusan cike shekar, samun inda zai mike ma ya kwanta aikine, kuma tabbas bazai iya ture wadannan gawarwaki ba.
Koda gama aiyana haka yaga bashi da mafita kawai sai ya shiga rokon Allah akan ya fitar da shi daga cikin wannan hali na kaka ni kayi da yake ciki.
Kafin Uzaifat ya gama shafa addu'a sai kawai ya ga wadannan ragowar yayan tsuntsayen sun afkawa yan uwansu matattu suna cin namansu, al'amarin da ya mutukar bashi mamaki kenan, yace a ransa, lallai yunwa balai ce, domin in ba masifar yaunwa ba, me zai sa wadannan tsuntsaye su afkawa mushe yan uwansu da ci?
Babban abinda yafi daurewa Uzaifat kai shine, yadda tsuntsayen suka kusan cinye naman yan uwana nasu gaba daya a cikin kankanin lokaci, wato suka gwaguye kafa naman jikinsu sai kasusuwa suka bari.
Uzaifat ya gama shafa adduar, sai ga wani narkeken tsuntsu ya taho a sama zai gifta ta saman tsaunin. Koda ya hango Uzaifat a durkushe sai yayi kasa kasa ya sureshi yayi sama da shi da nufin Shima ya samowa nasa yayan abin tabawa.
Sa'ar sa Uzaifat yayi a wannan karon shine, tsuntsun ba jikinsa ya cafka ba, rigarsa ya cafka.
Tsuntsun yaci gaba da tsala azababben gudu a sama, har ya iso saman fadamar nan wacce Uzaifat ya so ya debe ruwan ta ya cika salkar sa, bai sami dama ba. Koda Uzaifat ya leko kasa yaga zasu gifta ta kan koramar sai ya zare takobinsa yana mai yin kabbara ya dan karawa tsuntsun sara a kafa.take kafar ta guntule, bai san sa'adda yayi wata irin kara ba abin firgitarwa ya saki Uzaifat ya rikito kasa.
Sai da Uzaifat yaji kamar iskar sama zata yayyagashi saboda nisan da ke tsakaninsa da kasa, sannan ya fado cikin wannan fadama. Ji kake tinjim... Uzaifat ya nutse izuwa can kasan fadamar sannan yayi linkaya ya taso sama. Cikin sauri Uzaifat ya cika salkar sa da ruwa ya rufeta ruf sannan ya fito daga cikin fadamar ya daga hannunsa sama yayiwa Allah godiya bisa saukar dashi kasa kasa da yayi daga kan wannan dogon tsauni, inda shekar tsuntsaye take, kuma ya tareshi daga sharrin tsuntsayen.
Bayan ya gama wannan godiya ga Allah ne ya shiga farautar abinda zaicu dokin yunwa ta sashi yafara ganin dishi dishi. Cikin ikon Allah kuwa bai dade yana nemana, ya yi kicibus da wani maciji wanda ya hango abisa wata bishiya yana shirin hawa can saman bishiyar, kawai sai Uzaifat ya zare wata yar wuka da ke daure a cinyarsa ya cillawa maciji. Take wukar ta huda idon dama kuma ta cake macijin a jikin bishiyar, nan take macijin ya zama gawa.
Cikin farin ciki Uzaifat ya ruga ya cire macijin daga jikin bishiyar sannan ya nemi duwatsu kanana guda biyu yayi kyastu da su ya kunna wuta bisa kan wadansu kirare, bayan ya fede macijin kenan. Ba tare da lokaci ba ya gasa macijin, Sannan ya ci namansa ya koshi ya zuba ragowar a cikin jakarsa a matsayin guzuri, sannan ya mike tsaye yana mai hamdala ga ubangiji ya falfala da gudu ya koma can baya inda Lafirat da Abul shaja'a.
Lokacin da Uzaifat ya ido dai dai wajen da ya bar su Lafirat, sai ya isje wajen wayam babu su Lafirat babu alamun su. Ya duba gabas da yamma kudu da arewa babu alamar inda suka taka da sawayensu suka wuce. Uzaifat ya budi baki ya kwala musu kira har sau uku a lokacin da muryarsa ta cika dajin gaba daya da amsa kuwwa, amma shiru baiji sun amsa ba.
A sannane hankalinsa ya dugunzuma ainun ya tabbatar da cewa lallaiba lafiya ba. Uzaifat ya sami wuri ya zauna yana tunani, yace a ransa, to wai shin menene ya faru dasu Lafirat? Inda wata dabbarce tadaukesu ko kuma wata halitta mai kafafun tafiya da tabbas ya ga sawunta. Idan kuwa ba dabba bace, kuma ba halitta bace mai tafiya a kasa bisa kafafunta, to sai dai idan mai fuka fukai ce, wato mai iya tashi sama.
Bayan Uzaifat yayi dan dogon tunani akan lamarin, saiya mike tsaye ya fara yawo a cikin dajin yana mai karanta wadansu adduoi yana mai rokon Allah ya bayyana masa inda su lafirat suke.
Ya na wannan hali ne ya ido gaban wata katuwar bishiyar kuka, mai tsananin girman gaske.
Koda Uzaifat yayi arba da wannan bishiya sai ya tsaya cak! A gabanta yana nazarinta cikin matukar mamaki. Uzaifat ya daga kansa sama don ya ga iyakar tsawon bishiyar, amma sai ya ga ashe bata da karshe. Zagaye da bishiyar tun daga kasanta har izuwa inda ido ka iya gani wata matattakala ce, yace a ransa, to wai shin wane ne ya gidan wannan matattakala haka, kuma a yaushe akayi wannan gagarumin aiki? Duk yadda akayi dai ba aikin bane na mutane sai dai aljanu.
Koda gama aiyana haka, sai Uzaifat ya haukan matattakalar benen a jikin bishiyar ya fara hawa yana yin Sama batare da sanin inda zai je ba. Haka dai ya ci gaba da hawa matattakalar yana kara yin sama, har tsawon sa'a biyu, amma kuma sai ya ga ya kasa kure matattakalar, kuma har a sannan bai je karshen bishiyar ba, al'amarin da ya kara bashi mamaki kenan.
Haka dai Uzaifat yaci gaba da hawa matattakalar dake jikin bishiyar har ya sake shafe wata sa'a biyun. Kwatsam sai ya tsinci kansa a gaban kofar wani makeken gida, a sannane ya gane cewa, ashe gidana akan saman bishiyar. Abin mamakin shine, gidan an ginashi ne da zallan duwatsun wuta, kuma ya kasance mai girman gaske. Yaya akayi wannan gida ya zauna daram akan bishiya? Amsar da Uzaifat ya kasa baiwa kansa kenan.
Mu Hadu a DAKARUN MUSULUNCI 2 PART D don Jin CIGABAN WANNAN KASAITACCEN KUMA GAGARUMIN LABARIN 💯❤️❤️💯**DAKARUN MUSULUNCI*
LITTAFI NA 2
PART D 💯
NA: ABDUL AZIZ SANI MADAKIN GINI
TYPING UMAR FAROUQ ZANGO
POSTING NAJIBULLAH MUHAMMAD 🥷🥷
GORON JUMA'A ❤️❤️💯
Uzaifat ya kasa kunnensa a jikin kofar, amma sai yaji shiru tamkar babu kowa a cikin gidan, ko sautin gyare baiji na. Ya dubi kofar gidan da kyau wadda aka yita da zallan karfe mai kaurin gaske, ya tabbatar da cewa ba zata ballu ba da karfin tsiya, sai kawai ya sa hannunsa ya kwankwasa kofar. Shiru baiji ance komai ba, sai ya kara kwankwasawa da kotar takobinsa. Wannan karon sai yaji ance, wanene nan yake kwankwasa mana koda haka da sanyin safiya?
Muryar Sam irin ta mutane ba ta aljanu ba. Batare da fargabar komai ba Uzaifat yace, nine bakon ku Uzaifat dan sarki uwaisul karni. Na zo ne ku bani abokan tafiyata Abul shaja'a da Lafirat. Idan kuwa kun taba lafiyar su, sai na kashe duk wani mahaluki da ke cikin gidannan, sannan na ruguje gidan naku gaba daya na konashi.
Koda jin wannan batu, sai aka kyalkyale da dariya. Dariyar dai ta matace wadda ta kasance sirirya mai dadin sauraro. Nan take kofar ta bude da kanta, shi kuwa gogan naka, sai ya ruke takobinsa tsirara a hannu ya kunna kai ciki.
Da shigar Uzaifat cikin wannan gida, sai ya tsinci kansa a cikin wata makekiyar fada kasaitacciya, wadda ko a labari bai taba jin mai kawatuwarta ba. Wadansu kyawawan 'yan mata ya gani kimanin su dubu uku a tsaitsaye, sunyi sahu biyu dama da hagu sun ci ado da wani Korean tufafi duk iri daya mai gaske da kyalkyali, kuma mai daukar ido sai kamshi suke.
Wani abin mamaki shine, gaba dayan 'yan matan kammaminsu iri dayane Sak, tamkar an tsaga kara. A nan saman wani gini mai tudu an ajiye wata luntsumemiyar karagar mulki.
Zaune akan karagar wata kyakkyawar budurwa wace ta gaban kwatance wadda kyawunta ya ninka na ragowar 'yan matan sau goma. Tana da cika haiba da matukar kyawun dirin jiki da kyawun sura. Babu wani da namini da zai ga wannan budurwa bai kamu da sha'awarta ba, amma bisa mamaki tana hada ido da Uzaifat, sai ta ga ya daka mata harara bai na damu da kyanta ba, bare taka hankalinsa ta rudeshi.
Koda ganin haka, sai kyakkyawar budurwar ta mike tsaye daga kan karagarta ta taho ga Uzaifat a lokacin da wadannan kuyangi nata suka dare suka bata hanya. Koda ta zo daf Uzaifat sai ta tsaya ta kura masa idanu tana murmushi, kuma tana kallonsa sama da kasa sannan ta kewayashi tana mai dada yi masa wani irin kallo, wanda za'a iya fassarashi da kallo ne na sha awa ko na hilata.
Asannane ta dawo gaban Uzaifat suka fuskanci juna ta dubeshi cikin tattausan murmushi mai karya zuciya tace, haba gwarzo uban sadauka, haba jaurmin jatumai saboda me zaka shigo fadar sarauniyar kyau ta matan duniya, kana turbine fuska alhalin ba a bakin ciki a fadata, kuma ba a yunwa da kishirwa anan, sannan ba a rashin lafiya ko wata lalura da ka iya kefa mutum cikin damuwa? Ka sani cewa, wannan gidana nawa aljannar duniya ce, babu wani abu na jin dadin duniya da babu shi, duk wanda ya dace ya shigo nan bazai tsufa ba kuma bazai mutuba har abada.
Koda sarauniyar tazo nan a zancenta, sai Uzaifat ya daka mata tsawa, yace, ke munafukar Allah karya kike yi, babu wannan rayuwa da kika siffanta a wannan duniya tamu. Ubangijin musulunci shi kadai ne ya shirya wannan rayuwa ga bayinsa, wadanda suka bishi a bayan rayuwar su ta duniya, wato a can makomarsu aljanna.
Ina so ki sani cewa, duk wannan kawar taku da kyawunnan naki bai burgeni ba, kuma ban yarda cewa ku mutane ne ba. Maza ki fito min da abokan tafiyata su Lafirat don tabbas kune mini kuka daukko su daga can inda na barosu, ko kuma yanzunnan na hallakaku ke da kuyangin naki.
Koda gana fadin haka, sai Uzaifat ya daga takobinsa sama, sannan ya budi baki da nufin zai kwala kabbara, kawai sai yaga wanna kyakkyawar sarauniya ta fashe da kuka. Nan take ta dauki Wata 'yar karamar wuka da ke cake a jikin tuffa bisa wani teburi ta yanki damtsen hannunta.
Take wajen ya dare jini ya zubo cikin fusata ta dubi Uzaifat, tace, shin yanzu ka yarda cewa ni bil adama ce kamarka? Jikina irin nakane, zuciyata irin takace. Ina son ka sani cewa asalina na kasance 'ya ga sarkin birnin hindu, aljanune suka satoni suka kawonj nan saboda a duniya babu Wata 'ya mace mai kyawuna. Ka saki jikina ka yarda dani a sannane zan iya gaya maka yadda zaka iya saduwa da abokan tafiyar ka, ka ceto rayuwar su domin suna can a cikin halin tsaka mai wuya.
Sa'adda sarauniya tazo dai dai nan a zancenta, sai jikin Uzaifat yayi sanyi, yaji kamar abinda ta fada gaskiyane, amma duk da haka sai yaji zuciyar sa tana wasuwasi akan hakan. Nan dai sarauniyar ta baiwa kuyanginta umarni da akai Uzaifat izuwa masaukinsa ya huta. Nan take wasu kuyangi hudu suka kama Uzaifat suka ja shi suka kai shi izuwa cikin wani kasaitaccen daki daban mai dauke da wani luntsumemen gado, suka zaunar dashi akan gadon, sannan suka fita suka barshi.
Jim kadan sai ga wasu kuyangin biyu daban, sun shigo da manyan farantan abinci guda biyu. Farantin farko a cike yake da nama kaji kala uku soyayyu gasassu da kuma farfesu. Shikuwa faranti na a cike yake da 'ya 'yan itatuwa kamar su, tuffa lemon zaki ayaba baure da fasadabur.
Bayan kuyangi biyu sun ajiye farantan biyu a gaban Uzaifat sai suka fice daga cikin dakin suka barshi shi kadai.
Uzaifat ya dubi wannan abinci yaji yana shaawar ci, amma kuma sai yaji hankalinsa bai kwanta ba da abincin, kawai sai yayi bismillah gami da karanta wata addu'a ya hau abincin da ci, hat sai da yakoshi.
Wani abu da Uzaifat ya lura da shi shine, lokacin da ya fara wannan adduar sai ya jiyo kamar ana ihu a can wajen dakin da yake ciki, amma kuma da ya kammala addu'ar sai ya dai na jiyo ihun. Bayan Uzaifat ya kimtsa cikinsa sai ya sake yin wata adduar ya tofa a gabas da yamma kudu da arewa da sama da kasa, sannan ya mike kafafunsa akan luntsumemen gadon yayi kwanciyarsa.
Abinka da gajiyayye, kuma ga shi ya ci ya koshi, nan da nan barci ya kwasheshi bai sani ba.
A can fadar wannan sarauniya kuwa tana zaune tare da kuyangin ta sai ga wata kuyangarta ta taho daga bangaren dakin da aka kai Uzaifat.
Da zuwan kuyangar sai ta zube kasa gaban sarauniyar tace, ya ke uwar mayi ta aljanu ai hakanmj ya cimma ruwa, tuni wannan bako yaci wannan abincin da muka kai masa, don haka dafin dake cikin abincin yayi tasiri a jikinsa, ya zama gawa
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 8 Chapter of 21