Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
abinda ya faru tsakanisa da dan uwansa uzaifat ya shaida mata. Koda jin haka sai ranta ya baci, kishi ya turnuketa ta sunkui da kanta kasa ta shiga tunani mai zurfi. Daga can sai ta dago kai ta dubeshi tace, yaki dana kayi sani cewa a duniya bani da wani buri wanda yafi naga ka gaji mahaifinka, wato ya zamana cewa kaine ka hau karagar mulkinsa. A shirye nake na fansar da raina don cika wannan buri, kuma duk abinda baka zato zan iya yi don samun biyan bukata. A yanzu haka akwai kulle kullen da nake yi akan hakan. Yayin da yarima ukashat yaji wannan batu sai ya cika da murna. Daga can kuma sai ya dubeta cikin damuwa yace, yake ummina kiyi sani cewa ni a ganina da ni da dan uwana uzaifat babu wanda zaici wannan gasa da yashirya mana domin naje wajen malamai sama da guda bakwai sunyi istihara akan hakan. Abinda suke gaya min shine zamuje wannan yaki, kuma zamu sha bakar wahala, da kyar ma zamu tsira da rayuwar mu. Yanzu wane matakin kike ganin ya kamata mu dauka akan wannan al'amarin?. Yayin da muzaira taji wannan batu sai ta bushe da dariya sannan tace, yaro man kaza, hakika ba ka san rana ba sai ka shigeta, ka nake tukunna. Ai na gaya maka cewa tuni na yi kulle kullena don haka ka Kwanar da hankalika, duk wuya duk rintsi komai gumu kai ne zaka gaji sarki. Abinda malamanka suka gaya maka gaskiya ne, zaku sha bakar wahala a wannan yaki, amma ina tabbatar maka da cewa kai bazaka mutuba. Abinda nake so da kai shine, duk umarnin da na baka kabishi kada ka kuskara ka kereshi indai kayi hakan zamu cika burinmu. Mahaifinku yace a gobe ne zai yi bayanin yadda tafi wannan yaki da yadda zaku gabatar da yakin, kuma a goben ne zakuyi shiri ku tunkari birnin shumbul. Kafin ku tafi ne idan zamu yi bankwana zan gaya maka umarnin da zaka bi. Cikin mamaki ukashat ya dubi muzaira yace, wai shin ya ke ummina wane irin kulle kulle kika yine akan wannan bukata tamu? Muzaira tayi murmushi tace, lokacin sanjnka bai yiba, idan yayi lallai zaka fahimaci komai bayan an kammala wanan yaki. Ukashat ya matsawa muzaira akan sai ta gaya masa irin shirin da tayi, ita kuwa taki. A karshe dole ya hakura ya tashi ya tafi izuwa bangaren da turakarsa take. A daren wannan rana sarki uwaisul karni a dakin muzaira zai kwana, amma a ka'ida kullum sai ya shiga dakin wadda bata da kwanan sa ya tambayeta ko tana da wata matsala kafin yaje daya dakin ya kwanta. Bisa wanann al'ada sarki uwaisul karni ya shiga dakin shulaifa inda ya isketa a zaune tayi tagumi kuma ta zurfafa a cikin tunani. Koda Yau sallama sai ga amsa, kuma ta mike da sauri ta taho gareshi ta tsaya daf dashi a bakin kofa suka fuskanci juna ya yin da fuskarta ke nuna alamun tsoro da damuwa karara. Kafin ma ya budi baki ya tambayeta abinda ke damunta sai ta fashe da kuka, al'amarin da ya dugunzuma hankalinsa kenan ya dubeta yace, yake matata ina dalilin wanann kuka naki? Maimakon ta bashi amsa sai ya rungumeshi ta sake fashewa da sabon kuka. Da kyar ya rarrasheta tayi shiru , sannan ya cire ji kinsa daga cikin nata ya rike kafadunta yace, yanzu idan baki gaya min abinda ke damunki ba to wa zaki dayawa. Cikin sanyin murya shulaifa tace, yakai mijina kayi sani cewa jiya da daddare nayi wani mafarki mai ban tsoro wanda ya tsaya min a zuciya har izuwa daren yau ya hanani sukuni, domin a jiya yadda naga rana haka naga dare. A cikin mafarkin an nuna mini cewar ka shiga cikin wank irin mugun hali, wato rayuwar ka na tsakanin mutuwa da jinya. Sannan kuma an nuna mini yarima uzaifat a cikin tsakanin halin shan wuya tamkar shima zai rasa rayuwarsa. Tun da na farka daga barci sakamakon wanann mugun mafarki da tsakar dare sai nayi ta addu'o'i har gari ya waye ban rintsa ba. Ya kai mijina ka sani cewa mafi akasarin mafarkina yana zama gaskiya, bisa wanann daliline na shiga mugun tashin hankali. Shima baka tsammanin cewa wannan yaki da su uzaifat zasu tafi yana da nasaba da wanann mafarkin nawa? Sa'adda shulaifa ta zo nan a zanceta sai sarki uwaisul karni yayi murmushi a gareta yace, yaje matata kiyi Sani cewa dukkan wani mahaluki rayuwar sa ta kasance rubutaccen al'amari tun kafin ya zo duniya, saboda haka abinda nake so dake shine ki kwantar da hankalin ki kuma ki ci gaba da tayamu da addu'a bisa aikin alherin da muka sa a gabanmu. Ni yanzu tsufa ya riskeni, fatan kawai shine na cika da imani. Shulaifa ta dago kai ta dubi uwaisul karni a lokacin da hawaye ke sartu bisa kumatunta tace, ya kai mijina, to wai shin me yasa tun tuni baka zabi halifanka ba a tsakanin uzaifat da ukashat har zaka sanya wanann gasa a tsakaninsu mai tsananin hadaki? Kai da kanka ka yaki kasar shumbul yafi sau a kirga baka taba samun nasara akan su ba. Ta yaya kake tsammanin cewa 'ya 'yanka zasu iya samun nasara?. Koda jin wannan tambaya sai sarki uwaisul karni ya sunkui da kansa kasa yayi shiru baice komai ba. Daga can saiya dago kai ya dubeta, bisa mamaki sai taga hawaye na zuba a idanunsa. Al'amarin daya mutukar bata mamaki kenan ta dubshe cikin mutukar damuwa tace, ka gafarceni ya kai mijina idan wannan tambayar da nayi maka ta Sosa naka zuciya. Sarki uwaisul karni yasa hannu ya share hawayen sa, Sanna yace,yake matata kiyi sani cewa tambayar ki bata bata min rai ba face ta tuno min da qani kuskure da na tafka guda daya sa'adda na gaji ubana akan wanann karagar mulki, sa'adda nake da shekara talatin da Shifa a duniya. Ina so ki saurari labarin da zam baki da kyau domin ki fahimci kuskuren da nayi rauywata da kuma illar da kuskuren ya haifar a garenj wanda gashi har na mutu bazan iya magance matsalar ba face 'ya'yana sunci birnin shumbul da yaki. Mu hadu a DAKARUN MUSULUNCI 1 part C don Jin CIGABAN WANNAN KASAITACCEN KUMA GAGARUMIN LABARI 🩷🩷🥰**DAKARUN MUSULUNCI** LITTAFI NA DAYA. PART C 💯 NA:- ABDUL AZIZ SANI MADAKIN GINI TYPING:- UMAR FAROUQ ZANGO. POSTING: Najibullahi Muhammad 🥷🥷 MARUBUCIN yakara da:- Lokacin da sarki Nukaib da sarki Hurusul karni suka ware gefe daya suka fara fafata yaki sai da suka shafe sa'a guda cur! Suna kaiwa juna sara da suka akan dawakai, amma dayansu bai sami nasarar koda lakutar jikin daya ba. Al'amarin da ya basu mamaki kenan, kuma ya fusata su. Bisa dole sai suka sauko daga kan dawakan nasu suka fara sabon yaki a kasa. Nan ma sai da suka sake shafe wata sa'a guda babu wanda ya sami nasara komai. Babban abinda da ya daure musu kai shi ne, karfi yazo daya, kuma dabatun yakinsu iri dayane. Nan kowannensu ya fusata ainun ya kara zage dantse suka ci gaba da fafatawa da dukkanin karfin su. A lokacin ne kowa ya sami nasarar yankar kowa. Sarki Nukaib ya yanki Hurusul karni a kafada, shi kuma ya yankeshi a cinya. Lokacin guda kowannensu ya dafe raunin sa gami da gyara tsayuwa. Kamar hadin baki sai kowannensu ya yagi rigar jikinsa ya daure raunin jikinsa, sannan suka sake kacamewa da sabon azababben yaki. Wannan karon sai da suka shafe sa'a uku cur!. Suna fafatawa amma dayansu bai gajiya ba, kuma basu fasa fi gaba da yakin ba. Ganin yadda suke wannan mugun artabune duk jama'ar tasu suka tsaya da yakin suka Kewaye su suna kallonsu, don aga wanda zai samu nasara akan wani. Hakika a wannan rana an ga jaruma taka da sadaukantaka gami da juriya irin wadanda ba'ataba gani ba a tarihin jaruman nahiyar gaba daya. Bayan jaruman biyu sun shafe sa'a uku ne suna wannan artabu, sannan suka fara samun nasarar ci gaba da yiwa juna rauni, har ta kai cewa kowannensu ya sami rauni goma sha uku a jikinsa, ya zamana cewa dukkanin su jikinsu yayi fata fata da jini har jiri na dibarsu, amma an rasa wanda zai je kasa. Kuma wani babban abin mamaki shine, a lokaci guda suke yiwa juna rauni, wato da zarar daya ya sami nasara akan dayan sai shima dayan ya sami nasara. Kai tun suna tsaye sai da suka durkushe kasa amma basu fasa kaiwa juna hadi ba. Abu dai har ta kai cewa makaman hannunsu sun lalace sun zubar da su suka kacame da kokawa, a hakan ne kowanne su rawaninsa ya tube fuskokinsu suka baiyana a fili. Koda suka yi arba da fuskokin juna sai suka kame kamar humaka suka kurawa juna ido cikin tsakanin takaici da nadama, daga can kuma sai aka ga sun fashe da kuka, suka rungume juna. Al'amarin da yayi mutukar baiwa kowa mamaki a wajen kenan, jikin jama'ar yayi sanyi aka kara marmatsowa kusa da su. Sarkin Naukib ya dubi Hurusul karni a lokacin da hawaye ke zuba a idanunsa yace, ya kai abokina ya ya akayi muka yi wannan babban kuskure, yanzu Ashe da kai nake yin wanann yakin ban saniba?. Cikin matukar karfin hali Hurusul karni ya share nasa hawayen sannan ya kara kankame Nukaib a kirjinsa yace, Hakika munyi babban kuskure da har muka rabu a makaranta bamu sanar da junanmu ainahin kasashenmu ba. Tabbas rashin sani yafi dare duhu, yanzu gashi abune mawuyaci mu rayu bare mu kawo karshen wannan yaki a tsakanin alummarmu, alhalin tun a baya munyi alkawarin tabbata da zaman lafiya a nahiyoyinmu gami da tsayar da yake yake a duk Sa'adda muka zamo shugabanni. Yanzu gashi mun kawo matsayin shugabancin amma kuna burinmu ya yanke anan. Sa'adda sarki Hurusul karni yazo dai dai man a jawabinsa sai shima sarki Nukaib ya sake kankameshi a kirjinsa duk su biyun suka sake fashewa da kuka, sannan Nukaib yace, ya kai abokina kayi sami cewa duk da cewa mutuwa zamuyi a yanzu ina matakur Farin ciki da zan mutu ina kan kirjinka, domin a ko yaushe burin masoyi shine ya kasance tare da masoyinsa. In da ace ka kadai ne zaka tafi ka barni da tabbas sai bakin ciki ya sa na kashe kaina, domin kaine abokina na farko a duniya kuma kaine na karshe, domin tun da muka rabu ban sake yin wani abokin ba. Kayi sani cewa kaine mutumin da na shaku da shi ainun fiye da iyayena da suka haifeni, amma idan baka manta ba mun rabu a makaranta ba tare da sanin cewa zamu rabu ba, domin mahaifina ne yazo a rana daya ya daukeni daga makarantar saboda kawai ya sami labarin cewa ni da kai mun shaku ainun. Lokacin da muka isa gida sai ya rufeni da da matsanaicin fada yana mai cewa saboda me zan yi abota da ma'abocin addinin musulunci? A wannan lokaci yayi ta nuna min illolin jama'ar ku da addininku da irin gabar dake tsakanin mu da ku tun iyaye da kakanni. Nan dai kawai ina sauraronsa ne kawai amma ko kadan a zuciyata ban gamsu cewa ku mutanen banza bane domin a zaman da nayi da kai ban taba ganin mutum mai kyawun hali ba kamarka da sanin yakamata da kuma tausayi da taimako. Ya kai masoyina kayi sane cewa tun a bayan rabuwarmu nake ta bincike a sirrince domin na gano sunan kasarku na kawo maka ziyarar ba zato, amma sai na kasa samun wanda yasan a inda kake. Ni kam tuntuni na gamsu da addininku, don haka a yanzu take inason ka shigar dani cikin wannan addini mai albarka. Koda jin wannan batun sai Hurusul karni ya cika da tsananin farin ciki. Na taje ya soma bi yawa sarki Nukaib Kalmar shahada. Allah sarki! Hakika idan mutum yana da rabo to fa komai rintsi sai rabonsa ya riskeshi. A dai dai lokacin da Hurusul karni ke biyawa Nukaib Kalmar shahada yana maimaitawa ne Allah ya karbi rayukansu a lokaci guda. Koda gainin abinda ya faru sai gardama ta kare a tsakanin rundunar biyu. Mutanen Hurusul karni suka ce ai duka gawar biyu ta zama tasu tinda sarki Nukaib ya karbi musulunci. Su kuwa mutanen birnin shumbul suka ce A'a Sam Sam basu yarda ba, sia dai a basu gawar Nukaib su tafi da abarsu. Al'amarin da yajanyo akaci gaba da yaki kenan, yakin ya zamo mai tsananin gaske, jar sai da kowa ya mutuba wajen, mutum daya bai tsira da rayuwarsa ba bare a sami wanda zai kai labarin hakikanin abinda ya faru a filin yakin. Sai bayan kwana guda da faruwar yakin ne iyayen su sarki Hurusul karni suka yi shiri suka zo filin yakin saboda sun ji shiru babu wanda jama'arsa ta koma gida. Koda aka da iso filin yakin kowa yaga dukkanin mayakansa sun zama gawa, haka ma 'ya'yayensu sai suka cika da tsananin bakin ciki suka kama kuka kamar bazasu daina ba. Tsananin bakin cikin rashin yayan nasu ne ya hanasu yin wani sabon yakin a wajen, don haka kowa sai ya dauki gawar dansa yabtafi da ita izuwa kasarsa akan cewa daga baya za a sake yin sabon shirin yakin. A wanann lokaci ne sarki uwaisul karni bai fi shekara bakwai ba a duniya. Mu hadu a DAKARUN MUSULUNCI 1 part D don Jin CIGABAN WANNAN KASAITACCEN KUMA GAGARUMIN LABARI 🩷🩷🥰🥰❤️**DAKARUN MUSULUNCI** LITTAFI NA DAYA❤️ PART D ✍️💕 NA: ABDUL AZIZ SANI MADAKIN GINI👮 TYPING:- UMAR FAROUQ ZANGO. POSTING: NAJIBULLAH MUHAMMAD 🥷🥷 YACI GABA DA CEWA:- Lokacin da kakana ya dawo gida dauke dagawar mahaifina rungume a kirjinsa yana ta faman rusa kuka muna tsaye a harabar nan gidan ni da uwata muna ya wasan birin birin ta daure min fuskata da yanki. Koda uwata ta hango gawar mijinta a hannun ubansa sai ta tafka salati da karfi. Nan take zuciyarta ta buga ta sulale kasa matacciya. Cikin hanzari na cire yankim dake fuskata. Koda naga mahaifiyata a kasa ta zama gawa kuma naga mahaifina a kirjinsa kakana shima ya zama gawa sai na fada kan gawar uwata na fashe da matsanaicin kuka. Duk mutum mai imani dole ne ya tausaya min a wannan lokaci, domin bani da kowa face kakana. Kuma na shaku matuka da mahaifina domin a kullum shi ke koya mini yaki kafin su fita wannan yakin da aka kashe shi. Lokacin dana fashe da matsanaicin kuka sai shima kakana ya kama mikan aka rasa wanda zai rarrashi wani a tsakanin mu. Sai da muka jima a hakan sannan ya ajiye gawar mahaifina yazo gareni ya kamani ya rungumeni a kirjinsa ya shiga karfafa min gwiwa yana cewa. Ya kai jikana kayi sani cewa ni tsufa ya riskeni don haka a koda yaushe ta Allah zata iya kasancewa a kaina. Idan ka gajeni ka tabbata cewa ka ci gaba da yaki da birnin shumbul har sai izuwa ranar da ka rushe birnin su ka kashe dukkanin mazansu da matansu. Lallai inaso ka daukar min wannan alkawari. Koda naji wannan batu sai na shiga rantsuwa da girman Allah ina mai cewa, ya kai kakana na dauki alkawari komai dadewa kamar yadda na ga gawar uwata da ubana yanzu sai naga gawar duk abinda ke da rai a cikin birnin shumbul kuma sai na naje birnin su. Idan kuwa abin ya gagareni ba zan mutuba face na dora 'ya'yana akan wannan turba. Sa'adda sarki uwaisul karni yazo dai dai nan a labarinsa sai hawaye ya zubo masa ya dubi shulaifa yace, kinji asalin abinda ya haddasa yaki tsakanina da kasar shumbul kuma har kwanan gobe ina son na cika alkawarin da na daukarwa kakana duk da cewa na san kuskure be yin hakan tunda mahaifina da sarki Nukaib bai mutuba ba face sai da ya karbi musulunci. Koda jin wannan batu sai shulaifa ta cika da tsananin mamaki tace, ya kai mijina lg akayi kasan cewa sarki Nukaib ya karbi musulunci alhalin kowa ya mutu a filin yakin ba a sami wanda ya kawo labarin abinda ya faru ba?. Uwaisul karni yayi ajiyar zuciya sannan yace, yake matata hakika kinyi tambaya mai matukar mahinmmanci kuma mai Ma'ana. Ina son ki sani cewa bayan kimanin shekaru arbain da mutuwar mahaifina na tsinci wata wasika a cikin irin tufafinsa da na gada wadanda ban taba sauyawa ba. Wannan wasika na kunshe da wasiyya ce ta mahaifina a gareni. Ashe kafin ya mutu a wannan filin yaki ya sami damar rubuta wannan wasiya, domin ya kawo karshen yakin a tsakanin kasashen biyu. A cikin wasikar ne ya bukaci da nayi tallan addinin musulunci ga mutanen kasar shumbul, kuma a cikin wasikar ne yayi min bayanin dangantakarsa da sarki Nukaib bisa abotarsu a makaranta da kuma duk abinda ya faru a tsakaninsu a filin yaki. Lokacin da na gama kiranta wannan wasika sai na fashe da kuka domin bakin alkalami ya Riga da ya bushe babu abinda zan iya yi a kan al'amarin. Bazan iya tsaida yakin ba tsakanina da birnin shumbul saboda na rigaya na dauki alkawarin ci gaba da yaki ga kakana, kuma har a ranar da kakana zai mutum yana kan cinyata babu abinda yaje maimaita min face na cika alkawarin da ke tsakaninmu. Yake matata tabbas bazan taba janye wannan alkawari ba, don haka dolene naci gaba da karfafawa su uzaifat gwiwa akan wannan yaki kuma duk wanda ya sami nasarar cin birnin shumbul da yaki shinea zai gajeni. Wannan itace wasiyyatr da zan bari kuma ko a bayan raina da ita za'ayi amfani. Koda gama wannan jawabi sai uwaisul karni yayiwa shulaifa sallama ya tafi izuwa dakin muzaira domin ya bata kwananta. * * * * * * Kashe gari bayan an yi kalacin safe sarki uwaisul karni ya tura aka kirawo yarima uzaifat da yarima ukashat suka gabata gareshi. Bayan sun durkusa a gabansa sun kwashi gaisuwa sai ya dube su a nutse yace yaku 'Ya'yana ina son nayi muku nasiha guda daya kafin nayi muku bayanin yadda zaku gabatar da wannan yaki da mutanen shumbul. Nasihar da zan muku itace, duk abinda zaku yi kada kuyi gaggawa, domin ita gaggawa taba kai mutum izuwa ga nadama. Sannan kuma ku kasance masu bincike bisa duk al'amarin da yazo muku saboda bincike na iya haifar da fahimtar juna gami da samun zaman lafiya ba tare da kun aikata abin da zaizo ya dameku ba. Dan gane da batun yakin da zaku tafi, ina son kuyi shiri kowannenku ya jagoranci rundunar dakarunsa a lokacin guda ku tafi yakin inda aka saba fafatawa muda mutanen birnin shumbul a gobe. A yanzu zan yi muku kacici kacici domin fitar da rundunar da zata fara tarar abokan gaba. Koda gama fadin haka sai sarki uwaisul karni ya sanya hannunsa a cikin aljihun rigarsa ya fiddo wadansu takardu dunkulallu biyu ya ajiye a gabansu yace kowannenku ya zabi takarda guda. Wanda ya dauki takardar da aka rubuta daya a cikinta dakarunsa ne zasu fara fita filin daga. Koda jin wannan batu sai uzaifat da ukashat suka tsirawa takardun biyu idanu aka rasa wanda zai fara dauka. Sarki uwaisul karni ya daka musu tsawa yace, me kuke jirane. Koda jin tsawar sai jikin su ya kama kyarma, cikin sauri uzaifat ya kai hannunsa ya dauki takardar dake gabansa sannan ukashat ya dauki dayar, sarki yace to ku warware takardun don muga abinda ke ciki. Ba tare da fargabar komai ba uzaifat yayi bisimillah ya bude tasa shi kuwa shi kuwa ukashat sai ya kama nuku nuku da kyar ya bude tasa. Sarki uwaisul karni ya karbi ta uzaifat ya duba sai ga lamba biyu a rubuce, kawai sai ya nunawa ukashat yace, to kaine zaka fara tarar abokan gaba. Nan take bakin ciki ya turnuke ukashat saboda shi a tunaninsa idan su uzaifat ne suka fara yin yakin nan da nan za a fara cin lagonsu uzaifat sai su kasa samun nasara inyaso daga baya sai su tsinci dami a kala. Yayin da sarki uwaisul karni yaga alamun damuwa karara a fuskar ukashat sai ya dubeshi yace, ya kai dana kayi sani cewa komai na duniya rabone. Babu wanda ya isa ya hanaka samun nasara a wannan yaki idan kana da rabo, haka kuma babu wanda ya isa ya sa samu idan baka da rabo. Koda sarki uwaisul karni ya zo nan a zancesa sai tari ya sarkeshi. Abu kamar wasa sai tarin yaki tsayawa, sai kuma ya fara aman jini. Nan da nan hankalin uzaifat da na ukashat ya dugunzuma suka dimauce. Cikin karaji uzaifat ya kwalawa wani hadimi kira wai shi amzabu. A guje Amazabu ya shigo cikin turakar, uzaifat ya umarci amzabu daya ruga gidan likitan sarki abu sharaz ya ki rashi yanzu yanzu. Koda jin wannan umarni sai amzabu ya sake juya wa wajen ya kama dokin ya haye ya zabureshi. Jima kadan sai ga amzabu tare da abu sharaz sun shigo cikin turakar sarki. Da shigowar su abu sharaz ya ga halin da sarki ke ciki, a wannan lokaci sarki na numfashi sama sama kuma idanunsa sun kada sunyi jawur babu kyan gani, sai shima hankalinsa ya dugunzuma nan take ya bude jakarsa ya fiddo wadansu magunguna ya hadasu a cikin kofi sannan ya durawa sarki a baki. ****** ***** ****** Najibullah Muhammad 🥷🥷🥷 ****** ****** ****** Lokacin da kakana ya dawo gida dauke dagawar mahaifina rungume a kirjinsa yana ta faman rusa kuka muna tsaye a harabar nan gidan ni da uwata muna ya wasan birin birin ta daure min fuskata da yanki. Koda uwata ta hango gawar mijinta a hannun ubansa sai ta tafka salati da karfi. Nan take zuciyarta ta buga ta sulale kasa matacciya. Cikin hanzari na cire yankim dake fuskata. Koda naga mahaifiyata a kasa ta zama gawa kuma naga mahaifina a kirjinsa kakana shima ya zama gawa sai na fada kan gawar uwata na fashe da matsanaicin kuka. Duk mutum mai imani dole ne ya tausaya min a wannan lokaci, domin bani da kowa face kakana. Kuma na shaku matuka da mahaifina domin a kullum shi ke koya mini yaki kafin su fita wannan yakin da aka kashe shi. Lokacin dana fashe da matsanaicin kuka sai shima kakana ya kama mikan aka rasa wanda zai rarrashi wani a tsakanin mu. Sai da muka jima a hakan sannan ya ajiye gawar mahaifina yazo gareni ya kamani ya rungumeni a kirjinsa ya shiga karfafa min gwiwa yana cewa. Ya kai jikana kayi sani cewa ni tsufa ya riskeni don haka a koda yaushe ta Allah zata iya kasancewa a kaina. Idan ka gajeni ka tabbata cewa ka ci gaba da yaki da birnin shumbul har sai izuwa ranar da ka rushe birnin su ka kashe dukkanin mazansu da matansu. Lallai inaso ka daukar min wannan alkawari. Koda naji wannan batu sai na shiga rantsuwa da girman Allah ina mai cewa, ya kai kakana na dauki alkawari komai dadewa kamar yadda na ga gawar uwata da ubana yanzu sai naga gawar duk abinda ke da rai a cikin birnin shumbul kuma sai na naje birnin su. Idan kuwa abin ya gagareni ba zan mutuba face na dora 'ya'yana akan wannan turba. Sa'adda sarki uwaisul karni yazo dai dai nan a labarinsa sai hawaye ya zubo masa ya dubi shulaifa yace, kinji asalin abinda ya haddasa yaki tsakanina da kasar shumbul kuma har kwanan gobe ina son na cika alkawarin da na daukarwa kakana duk da cewa na san kuskure be

Chapter 2 of 21